Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ga yanda gayen nan ya kara kyau ba, yayi fari yayi kiba sosai, I think he misses me so much, kin kuwa ga irin fara'ar daya dinga min? Rabona da in....." tayi saurin katse ni, "ai fa kin kika fara bada labarin Muneer kamar wata radio mai jini ba kya ko son kiyi shiru, to sai ki tashi an zo daukar ki" na kalli inda suka saba tsayawa idan suka zo, gabana ya fadi sosai, Abbu ne yazo daukar mu! Ganin Qaseem ya fito yana tunkarar wajen da nake yasa na mike ina lalubar jakata nawa Ramlah sallama. A hankali kuma a sanyaye na bude bayan motar na shiga, "Abbu ina yini?" na furta cikin siririyar murya ta, ya amsa "lafiya qalau Nafeesah, ya kika baro Kaduna?" na amsa da lafiya lau. Yaja motar muka tafi babu mai furta uffan. Hafsat ce ta ciro drawing book dinta daga cikin school bag dinta tana nuna min Assignment din dana taya ta jiya akan zanen gidaje da motoci, tace "Kuma Uncle Jamilu yace ni na cinye 20 over 20 duk cikin class din" na shafa kanta ina murmushi, "Ohh that's very good princess, am proud of you" tayi dariya tana kwantowa a jikina na rungume ta. Muna isa gida sallah muka yi, na bude fridge na ciro fura da nono dana kawo daga gida, musamman Mommy ta bada aka yi, na zauna na dama ta da dan kaurinta na saka kankara da dan sugar, cups na dauko na zuzzubawa su Abdullahi. Muna zaune a falo muna sha kafin lokacin zuwa Islamiyar su yayi. Abbu ya fito daga daki hannunshi dauke da jakar laptop dinshi, dan karamin coffee table din dake gefen mu ya janyo ya dora laptop din nashi akai, kasa kasa yake kallon mu har ya zauna. Ya kalli kofin dake hannuna yace meye wannan kuke sha haka babu tayi? A kunyace nace fura ce! Idanunshi suka dan ware cikin mamaki, "wow, daga ina muka samu fura?" Hafsat tayi caraf tace "daga gidansu tazo da ita jiya!" ya jima sosai idanunshi suna kaina ban san ko tunanin me yake yi ba, ya kauda kanshi ya maida shi ga laptop dinshi, "tunda ba a mana tayi ba ni zan yiwa kaina, a bani idan da akwai" da sauri na tashi naje na dama mishi na kawo na ajiye mai a gefenshi. Su Hafsy suna wucewa makaranta na koma dakina na zauna ina kallo.
[12/9, 9:48 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*12*

Ya Allah! Cheerful Abbu din dana sani ya tafi, wannan Abbu din ban taba ganin shi ba, a fusace yake sosai kamar wanda zai tashi daga zaunen da yake ya hau ni da bugu, gabadaya jikina ya dauki rawa hawaye suka ciko idanuna, bana son fada ko kadan a rayuwata. Cikin rawar murya irin ta wanda yake so ya fashe da kuka nace, "Naje saloon ne shine na biya gidan su kawata Ramlah" ya galla min harara, "da ixinin wa??" nace "umh, ai na fadawa su Malam Bala da suka zo dauka na dazu", yayi shiru kawai yana kallona. Malam Bala ya fada mishi tun dazun, that means he have no right to be angry at her, but still, he's just pissed up. Dan siririn tsaki yaja ganin har na fara shesshekar kuka, ya shafa tattausar sumar kanshi da a koda yaushe a gyare take tana sheki, "it's okay.... Bani ruwa a fridge" da sauri naje na dauko na kawo mishi, yasa hannu ya amsa fuskar shi har lokacin a murtuke, ganin nayi tsaye naki in tafi yasa ya juyo yana kallona, "what?" he sounds so pissed up at me, da sauri na hau share kwallar data fara xubo min again nace "Abbu don Allah kayi hakuri, wallahi ba zan kara ba don Allah" ya lumshe idanunshi a hankali, "it's okay Nafeesah, banji dadin abinda kika yi ba, a gidanku kina kai har Magriba a waje?" nayi saurin girgiza kai, "to me yasa a gida na? Saboda kin raina ni ne ko kuma don kin baro gidanku kina tunanin zaki yi duk abinda kike so anan ba tare da an miki fada ba?" nan ma kai na girgiza a hankali nace "tun dazu muka taho, gidan Akwai dan nisa ne daga yau" yace "bana tolerating abubuwan nan Nafeesah kin gane? Daga yau kada ki sake wuce bayan Magriba a waje...... No! Duk inda zaki fita you must tell me first indai kina cikin garin Kano, understand?" nayi saurin jijjiga kaina, yace "you can go now!" kamar wadda take akan kaya, da sauri na wuce dakina. Sallah na fara yi kafin na kira mommy muka gaisa, labarin abinda ya faru na shiga bata, budar bakinta cewa tayi "ai yayi min daidai wallahi, wato har kin fara yawo barkatai ko?" sai lokacin naga wautata dana fada mata, na batan fuska kamar ina gabanta tare da turo baki, "mommy! Saloon fa naje saboda Allah daga can na wuce gidan su Ramlah, Ramlah ce fa kawata ke kanki kin shaida sau nawa take zuwa gidan mu ta kwana?" tace "but still baby, bai kamata ki tafi ba tare da kin fada mishi ba, kin san dole ranshi ya baci dama" na shiga diddira kafata a kasa ina gunaguni, "ni dana sani dama ban fada miki ba tunda ba zaki goyi bayana ba" ta sassauta muryar ta, "Ohh Nafeesah baki fahimta koh? Ba goyon bayan shi nayi ba, it's just the fact. Ke yanzu amanar muce a hannunsu, kina ganin ya dace ya barki ki dinga fita kina dawowa duk lokacin da kika ga dama a garin da yake bakon ki iye? Ko kina ganin girmamawa ce ki kama hanya ki fita ba tare da kin sanar dashi ba? Wani Malam Bala is not an excuse tunda ba a karkashin kulawar shi kike ba kin gane?" na gyada kaina a hankali she's right. Muryar daddy na jiyo ta cikin wayar, "Habibty ke da waye kuke waya kika kyale ni ni kadai a falo?" da sauri na shiga mata magiya akan Kar ta fada mishi hirar da muke don nasan kadan daga cikin aikin Mommy ne, ta ba daddy din muka gaisa. Hira muka shiga yi yawanci ta wajen aikin shi ce, mun jima sosai kafin muka yi sallama dasu. Kayan barci na na zura na bi lafiyar gado ko abinci ban nema ba.

Ina kan sallaya ina lazumi bayan nayi sallar asubahi, ban cika komawa barci ba a irin wadannan lokutan, kofar dakin naji ana kwankwasawa, na tashi naje na bude, Harira ce. Muka gaisa da ita a mutunce tace "dan Allah Nafeesah ko zaki taimake ni da girkin yau? Bana jin dadi ne" nayi fuskar tausayi nace "Eyyah sorry pa! Meye za a dafa?" tace "ki dafa duk abinda kika ga ya dace nace "to shikenan" tace nagode ta wuce dakinta. Daki na koma na dauko karamar hijabi data tsaya a kuguna na saka na fita zuwa kicin, yam delight nayi, kafin dahu sai na dauko fresh kifi a cikin fridge na fara shirin yin farfesun kifi.

(Kuyi hakuri da wannan zuwa gobe please, da kyar ma na samu na warci lokaci nayi typing dinshi wollah)

*♡Jeedderh♡*
[12/9, 9:50 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*13*

Hankalina gabadaya ya tafi ga tsame doyar da nake yi daga cikin frying pan naji motsi a bayana, da sauri na juya har mai na fallatsan min a hannu na danyi kara kadan. Abbu ne sanye da wandon Jersey me layi layi irin na sport navy blue da top grey, gaban rigar zuwa tsakiyar kirjinshi ya jike da sweating alamun daga exercise yake. Yadda kayan nan suka mishi kyau suka mayar dashi kamar wani matashi at his Twenteth, you might even mistook him da wani modeler a babban kamfanin nan dake saka kayan sports, ko kuwa..... Ban san cewa na dulmiya cikin tunani ba sai dana ji saukar tattausan hannunshi a dantsen hannuna, tingling feeling din dana ji bashi da maraba da irin wanda naji ranar nan da nayi mistaking taba hannunshi. Na zabura nayi tsalle gefe guda tare da sakin matsamin dake hannuna ya fadi a tsakiyar kicin din, Abbu ya dube ni cike da mamakina, "hey! Are you ok??" cikin zaro idanu da rawar murya nace "ehh?" yace mai ya fallatsan miki a hannu, are you ok? Baki kone ba?" sai lokacin na tuno, sai kuma a lokacin naji zafi a wajen. Na dago hannun na kalli Inda man ya taba, thankfully bai yi komi ba sai dan ja da wajen yayi, nace "lafiya lau babu abinda ya same ni.... Ina kwana Abbu?" na fada ina dan dukawa, ya amsa, tare da dorawa da, "ya aka yi kike girki tun da safe?" na duka na dauki matsamin dana yar a kasa ina cewa., "Harirar ce bata jin dadi, shine tace in kama mata" ya gyada kai. Nace Akwai abinda kake bukata ne? Ya zuba min ido kamar mai tunani, "abinda yake bukata?" me yake bukata exactly? Shi dai yasan yana cikin yin exercise dinshi yaji kamshin girki mai dadi yana bi ta cikin hancinshi, kamar maganadisu haka yaji ana jan shi har cikin kicin din..., ganin bai amsa ba yasa na juya na fara kwashe doyar dake cikin kaskon na fara tsoma mata. Yayi gyaran murya tare da fitar da dan sautin tari, "ehhhem, ruwa nake so" na bude fridge na dauko mishi mara sanyi na mika mishi da hannuna biyu ya amsa idanunshi na kaina. Na sadda kaina kasa saboda wasu particles da naga suna fita daga cikin idanunshi nashi suna shiga ta nawa kamar mashi, dan murmushi yayi ban san me yake nufi da hakan ba. Sai daya shanye ruwan tas ya miko min goran, na amsa na jefa ta cikin dustbin. "What can I help you with?" na jiyo muryar kamar daga sama, da sauri na dago ina kallonshi cike da mamaki, ta wani bangaren kuma ina tantamar Anya shine ya furta maganar? To amma waye zai furta idan bashi ba? Mu biyu ne kadai a kicin din. Kai na girgiza mishi a kunyace, ya daga kafada, "k! Let me go and take a shower then" ya juya ya bar kicin din, ni kuwa me zanyi ba kallonshi ba? Har ya fita daga kitchen din. Na maida bayana na jinginar da canter, idanuna a lumshe ina kokarin tantance abinda ke faruwa da jijiyoyina, kwalwa da zuciyata.
Bakwai saura na gama shirya komi akan dinning table, a gurguje na watsa ruwa na fito. Yau kam ban tsaya yin kwalliya ba balle bata lokaci wajen ciro kaya, simple kwalliya nayi daga hoda sai janbaki, na janyo wata atamfa English maroon color, dinkin rigar fitted ne sai zani 6-pieces, na kashe saurin dankwali kaman inji ne yayi ba hannu ba, na fesa turare tare da daukar jakata na zura flat din takalmi baki naja gyale na fita falon. Gabadaya kowa ya hallara akan dinning, nima sahun su nabi. Naja kujera kusa da Hafsy kamar yanda nake yi na zauna, Anty Mubeenah na gaida wadda yau er kwalliyar safen ma da take yi ba tayi ba da alamun ba zata leka wajen aikinta ba yau kenan. Shima Abbu sai dana sake gaida shi, shi kam a shiryen shi yake cikin Kaftan riga da wando ruwan madara bai san hula ba amma fa yayi kyau kamar ka sace shi, su Qaseem suka gaida ni kafin muka fara cin abinci a nutse. Abbu ya kaimu makaranta yau, sai da muka ajiye su Hafsy kafin muka wuce. Ina zaune a gaban motar kaina a kasa, a darare nake kamar ace kyat! In zura da gudu, kira'ar Sheik Sudeis ce take tashi a cikin motar cikin suratul-Anfal, munyi nisa sosai babu mai yin magana a cikin mu. Ya kalle ni yayi dan murmushi, "me yasa ba kya sakewa ne idan ina kusa dake Nafeesah?" ya tambaya idanunshi akan titi kamar ma bashi ne yayi maganar ba, na kara sadda kaina kasa, Ya Allah! M I making it too obvious?? "umh?!" ya kara tambaya jin nayi shiru ban amsa ba, "ko kina jin tsoro na ne Nafeesah?" da sauri na girgiza kaina, yace to meye? Da kyar na iya cewa "babu komi Abbu?" ya kalleni sosai da idanuwanshi masu kama da wanda yake jin barci, da sauri na janye idanuna daga cikin nashi, yace "anya kuwa Nafeesah?" na gyada kaina da sauri, "da gaske nake Abbu, ba tsoronka nake ji ba" ya tabe baki yace "koma dai menene Nafeesah kiyi kokari ki rage shi, bana son hakan ko kadan kin gane?" na gyada kaina, yace good! Daga haka muka yi shiru har cikin makaranta, na bude murfin motar zan fita ya miko min kudi yan dubu dubu sabbi kar da ban san adadin su ba, kallonshi nayi cike da alamun tambaya, yace karbi mana! Na dan girgiza kaina, "amma Abbu me zanyi dasu?" yace ki badda mana. Na girgiza kaina da sauri, "no Abbu. Akwai kudi a hannuna wallahi, nagode sosai" ya dan hade fuskar shi, "to dama nace dake babu kudi a hannunki ne? Karbi nan tun kafin raina ya baci mana!!" a kunyace nasa hannu na karba, nace nagode Allah ya saka da alkhairi Abbu. Yayi murmushi kawai, sai dana ga bacewar motar shi daga idona sannan na shiga cikin lab. Ranar kam muka shiga shopping complex a cikin makarantar, sai da muka ga karshen 10k din daya bani tas ni da Ramlah, tarkacen kayan kwalam dana shafawa kamar zamu bude tireda.

Will update you with the remaining part real soon, I'm kinda busy ne this days wallahi shi yasa amma komi ya kusa zuwa karshe da izinin Mai Sama
[12/9, 11:27 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*14*

A

Da gudu na karasa wajen shi na riko hannunshi dake rike da brief case, tambayoyi nake watsa mishi ba kakkautawa, "Abbu lafiya? Abbu mai ya samu kafar ka? Abbu accident kayi a kan hanya?!....." ya zauna akan kujera yana maida numfashi, "it's just a minor targade, an gyara min. Kar ki damu" jin hanyaniya su Hafsy duk suka fito daga dakunan su, ganin halin da yake ciki tuni Hafsy ta fara kuka, sai da Abbu ya jata jikinshi ya rarrashe ta sannan tayi shiru. Ya kallemu duk munyi carko-carko a gabanshi muna muzurai, bai san sanda ya saki dan murmushi ba. "nace muku lafiya ta lau guys, oya Nafeesah dauko min abinci anan zan ci" jiki ba kuzari na koma na zubo mishi iya wanda zai iya ci na dora akan karamin coffee table na kai mishi, na koma kicin na dauko ruwa shima na ajiye mishi. Mu kuma muka koma kan dinning table muna cin abincin amma fa hankulan mu suna kanshi, muna cikin ci Anty Mubeenah ta fito daga dakinta, hankalina yana kanta har ta tsaya kusa da Abbu kamar suna yin magana ne, ta kalli kafar shi da yake nuna mata ta yi magana kafin ta nufo kan dinning din. Duk muka gaishe ta kafin muka koma wa cin abincin mu. Muna gamawa na tattara komi na kai kicin na wanke kayan tas na dawo falo, Abbu baya falon, na zauna ni dasu Abdullahi muka danyi kallo kafin na musu sallama na tafi dakina. Shirin kwanciya barci nayi na janyo wayana na shiga chats da friends dina ta whatsapp, dp din Muneer naga ya dora hoton wata kyakkyawar yarinya matashiya da alamun ta dan girme ni, naji wani abu ya soke ni a makogaro, kasa daurewa nayi na tura mishi tambayar "who is she?" mintuna biyu kyawawa kafin reply ya shigo, "a sister" nayi ajiyar numfashi lokacin dana ji wani sukuni yana ratsa ni, "Ohh! Ashe sistern ka ce.... Ya kake?" muka danyi chatting sama sama kafin ya min sai da safe wai barci yake ji, ni kuwa har da tura mishi hearts da clouds. Yana sauka nima na kashe wayana don dama saboda shi na tsaya.

Washegari ta kama daya ga watan mayu, public holiday ne don haka muna gida. Sai wajen karfe goma na fito daga dakina, nayi break fast na koma daki nayi wanka na sake fitowa falon. Su Qaseem suna zaune yanzu suna game, na zauna a tsakiyar su muka fara bugawa. Muna nan zaune muka ci karan intercom, Abdullahi yaje ya bude, sai gasu sun shigo shi da Aunty Ameenah. Da sauri na mike tsaye ina mata sannu da zuwa har ta zauna akan kujera, na shiga kicin na dauko mata lemu da ruwa na kawo mata, gaishe ta nayi ta amsa da fara'ar ta na koma gefe inan kallonta, wannan shine karo na farko da naga wani dan uwan Abbu a gidan tunda nazo. Qaseem ta tura yaje ya gayawa Abbu tazo, tare suke fito dashi, har yanzu yana dingisa kafar shi. Na bishi da kallo cike da tausayi har ya zauna, na gaida shi tare da mishi ya jiki ya amsa. Aunty Ameenah tace "tare muka zo da Abban Ikhlas, zai shigo ya duba maka kafar" na kai dubana ga kafar tashi, sai da cikina ya kada ganin yadda kafar ta kumbura suntum! Ya yamutsa fuska "kema na fada miki ba wani abu bane ba, targade ne an gyara min shi kuma, kumburin saboda targaden ya dade a jikina ne shi yasa" ta Harare shi, "ai ba cewa nayi kayi lecturing dina ba koh?" ta daga wayarta ta kira wata lamba, ba a jima ba wani kamilallen mutum da zai yi sa'an daddy na ya shigo falon, ya ba Abbu hannu suka gaisa. Kafar tashi ya kalla yana girgiza kai, "Anya haka zamu yi da kai kuwa Farfesa?" Abbu ya rausayar da kai kamar wani karamin yaro, "Abban Ikhlas kawai neman rigima ne irin na matar nan taka, sai dana fada mata targade ne amma taki yarda" ya kara kallon wajen, "anya targade anan wajen kuwa? Bari dai mu duba mu gani" ya fiddo kayan aiki, wata er karamar naura ya fiddo ya jona da wani abu, ya kara abun a kafar Abbu sai ga komi na kafar dake kasan fatar shi ya fito a jikin na'urar, amma babu abinda muka fahimta tunda ba profession dinmu bane, ya gama dube-dubenshi ya daga ido ya kalli matar shi, "tsagewar kashi ce!!" ta zaro idanu yayin dana dafe kirji, yace yanzu bari in kira mai gyara yazo tukun. Muna nan zaune jugum-jugum har mai gyaran yazo, har kuma zuwa lokacin bamu ga ko giccin Anty Mubeenah a cikin falon ba. Wani dan tsamurmurin farin dattijo ya shigo falon, maigadi wanda ya rako shi ya duba jikin uban gidan shi kafin ya juya ya fita. Mai gyaran ya fiddo kayan aiki ya fara, yana taba kafar Abbu na saki kara saidsai da duk suka juyo suka kalleni, jikina rawa yake, tsigar jikina tana tashi, Ji nake kamar nice naji ciwon. Abbu yace mu tashi mu koma daki amma fir naki, ganin mun ki tashi yasa ya kyale mu. Tunda aka fara gyaran kuka nake har da jan shessheka, ganin ina kuka sai Hafsy itama ta fara, nan da nan falon ya karade da kukan mu ni da ita, Anty Ameenah dariya ma ta hana ta lallashe mu. Mai gyaran ya gama gyaran da zai yi yawanci fara maida tarkacen kayan gyaran cikin jaka yana dan murmushi, "da alamun amaryar ce koh?" ya tambaya yana kallon Abbu, kusan a lokaci guda shi da Aunty Ameenah suka ce "ehhh?? Aah!!" ya bisu da kallon mamaki kafin ya murmusa yace to Allah ya kara sauki. Ya dauki jakarshi ya saba a kafada ya mike, mijin Anty Ameenah ta rufa mishi baya. Abbu ya kalleni a sanyaye, "bani ruwa Nafeesah!" da sauri na mike har ina hardewa, na dauko ruwan na kawo mishi na koma kusa da Hafsy na zauna.
[12/8, 7:35 PM] ‪+234 813 546 1890‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*15*


*'In a nation where the Poor face hardships, suffering and fears, only the riches and the one's that has power lives in peace, thrives and prospers....... Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah Ya Ibaadullaheessaaliheen!!!......'*


Sai gab da Magriba su Anty Ameenah suka mana sallama zasu tafi, na leka dakin Anty Mubeenah wadda tunda aka kira sallar la'asar ta tashi da niyar zuwa tayi sallah bata dawo ba, na gaya mata zasu tafi ta leko suka yi sallama ta koma dakinta. Ni dasu Hafsy har Abbu mai kafa sai da muka taka musu har gaban motar da Anty Rahina tazo da ita. Anty Ameenah ta kalleni na goya baby Jameel a bayana yana ta shakar barci abin shi, tayi murmushi cike da tsokana tace "to Hajiya Nafee a bamu baby din koh?" na fara kokarin sauke yaron daga bayana, "Allah Anty ji nake kamar ku bar min shi!" su duka suka kwashe da dariya, Anty Raliya tace "kina son yara ne har haka?" nayi dan murmushi, "sosai ma! Amma mommy taki ta haifo mana wasu" na karasa ina pouting kamar inyi kuka dana tuno diramar da muke sha da ita idan ina mata maganar me yasa bata kara haihuwa daga kaina ba? Sai tace ai Allah ne bai kawo ba, ranar nan ma dana takura mata da tambaya zagi ta dankara min tace in cewa daddy na ya karo aure mana sai a Haifa min yaran, na tuna lokacin kuka na fashe dashi saboda zagin data min, shi kuwa daddy dariya ya dinga mana. Daga ranar ban kara mata korafi ba, sai dai in yiwa daddy. Su Anty Ameenah kam dariya suke min, sun fahimci tsantsan yarinta da sokancin da aka san Yaya irinmu nayi a tare dani. Anty Ameenah tace "Kar ki damu, in shaa Allah kema zaki haifi naki, kinga kin huta kenan koh?" na gyada kaina ina murmushi, "daddy ma haka yace ranar nan!" suka kara sakin dariya kafin suka shiga motar, na mikawa Anty Ameenah babyn tare da maida murfin motar na rufe mata tare da daga musu hannu, suka ja motar suka tafi. Na dan saci kallon Abbu kallona yake sosai with astonishment in his eyes, murmushi yake yi kamar kunnen shi zai zage, na samu kaina da tambayar dalilin sudden change dinshi curiously. Na kama hannun Hafsy muka koma cikin gida ya biyomu a baya. Muna gama dinner na musu sai da safe na koma dakina, sosai nake jina a gajiye ga wani barci daya rufe min idanu.


Kwana uku muna jinyar Abbu ni da yaran shi, ba laifi ya warke

Please Login or Register in order to submit comment