Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na tashi saboda bani da yadda zanyi na fito su Ni'ima suka biyo bayana, dakin Anti Rahina na shiga da niyar mata sallama. Abbu na zaune a cikin falonta kusa da Anti Ameenah yayinda maijegon take zaune a kujera daya rungume da babynta da alamun hirar en u want aka ce ake yi na durkusa na gaida Abbu tare da yiwa su Anti Ameenah sallama, Abbu ya mike nabi bayanshi. Su duka har maijegon suka fito mana rakiya, su Qaseem na jikin motar Abbu din suna jiran mu, duka muka shiga cikin motar. Su Ni'ima suka leko suna kara min sallama dama mun yi exchange din number waya dasu, Anti Ameenah ta miko min wata Leda mai dan girma tana kara min godiya tare da jaddada min in fa nemi maganin ciwon jiki in sha ina amsa mata da toh, Mai jegon MA ta leko tana min Allah huta gajiya da godiya sosai. Abbu kam baki a sake yake kallon en uwan nashi cike da mamaki, wannan shine karo na farko da suka fito wai da sunan mishi rakiya, sai daga baya ya kula ashe ma ba shi aka yiwa rakiyar ba, kulawar daya kamata ace matar shi ce suke wa sun kare da ba wata can, abinda yakamata ace matar shi ce tayi suke mata wannan yabawar wata can ce ta samu romon. Koda yake bai ga laifin su ba, Mubeenah ita tayi wasa da garinta har yayi ruwa, shi kanshi yaji haushin abinda tayi yau a wajen sunan nan, ance tunda taje ta gaida mai jegon bata kara yiwa kowa magana ba ko Anti Ameenah bata gaida ba, daga baya ma suka ce wai ta ajiye musu dubu goma ta tafi tun kafin ayi Azuhur abinda ya bata ran Anti Ameenah kenan, ya girgiza kai cike da takaicinta, duk iya kokarin shi na ganin Mubeenah ta ra6u da dangin shi don su saba abin yaci tura. Shi har bai san me zai mata ba kuma.

Sai da muka gama sallamar mu sannan suka koma gefe suka tsaya suna kallonmu tare da daga mana hannu har Abbu yaja mota muka tafi. Tunda muka fara tafiya babu wanda yayi magana, su Hafsy tuni tayi barci akan cinya ta. Muna isa gida na ciccibe ta muka wuce Abdullahi ya dauko min ledar da Anti Ameenah ta bani, dakin Hafsy na fara wucewa na kwantar da ita. Closet dinta na bude na ciro mata kayan barci na dawo na cire mata na jikinta na saka mata wadannan, addu'ar kwanciya barci na tofa mata tare da sauka daga kan gadon a hankali gudun kar in tashe ta daga barci, ina juyawa naci karo da Abbu a bakin kofa a jingine yana kallon mu. Na sadda kaina kasa na je zan wuce ta gefenshi, packet din magani ya miko min, nasa hannu na amsa ina kallon shi cikin alamun tambaya, yace maganin ciwon jiki ne Anti Ameenah tace in baki, ki sha kafin ki kwanta. Na gyada mishi kaina, "sai da safe koh?" ya fada yana kaucewa daga bakin kofar dakin, na bi ta gefenshi na wuce ya bini da kallo. Ina shiga dakina kayan barci kawai na saka na afa maganin a baki, sai dana bata mintuna kusan goma yadda maganin zai yi settling a jikina sannan na kwanta, babu dadewa barci ya kwashe ni, ni kaina nasan cewa a matukar gajiye nake saboda ba karamin aiki muka sha a gidan sunan nan ba.

Sai karfe goma na safe na tashi, nayi mika mai tsawo ina jin ga6o6ina kamar an bubbuge min su, kai tsaye toilet na fada nayi wanka da ruwa mai dumi, nayi brush kafin na fito. Wandon jeans na saka wanda bai kama jikina ba da shirt, na daure kitson kaina a cikin tafkeken hair band na dora hula a kaina. Falo na fito saboda wata mahaukaciyar yunwa da take nanikata, babu kowa a cikin falon haka babu hayaniyar yara nasan suna makaranta. Anti Mubeenah na hakimce a kan kujera a falon da takardu a gabanta tana buga lissafi, na durkusa a gefenta ina gaidata. Hankalinta yana kan takardun ta amsa min, baki na dan tabe na mike, har ga Allah halayen matar basa burge ni, wata na daya a cikin gidanta amma wani idan ya ga yadda take yazga ni sai yayi zaton bakuwar jiya ce a wajenta. Kan dinning table na wuce kaina tsaye sai dai kwalam! Babu komi, cike da mamaki na tsaya ina kallon wajen a raina ina tambayar ko lafiya? A iya sani na ni dai a gidan nan ko an gama cin abinci ba a dauke kayan sai idan za a sake shirya wani meal din. Daga bayana naji Antin tana cewa "Yau bamu yi girki ba, Harira bata nan taje garinsu wajen biki. Yara ma sai oats na dama musu, kije kicin kema ki dama anjima kadan zan bada a yo take away" na jinjina kaina cike da mamaki, oats? Yaushe rabona da in sha Abinnan? Kicin din na wuce, kulolin da aka yi amfani dasu ba a wanke ba suna cikin sink har sun fara wari, nayi iya dube dube na a kicin din ban samu abu mai sauki da zan saka a bakina ba don bazan iya dama oats Inci ba, kawai ledar da Anti Ameenah ta bani jiya ta fado min a rai da sauri na koma daki na janyo ledar na bude, tarkacen su doughnuts, cake, cincin dasu biscuits ne a ciki har da naman suna, falo na koma na bude fridge na dauko lemun exotic na dawo nayi daidai a tsakiyar daki na fara ci, sai da naji nayi nak sannan na tattare sauran na ajiye a gefen gado. Waya na dauko na bude, missed calls na gani bila adadin nasu Ni'ima dana Daddy sai wata bakuwar number da ban sani ba, su Ni'ima na fara kira suka min ban gajiya sannan na kira bakuwar number nan ashe Anti Ameenah ce, itama dai ban gajiyar ta min har sai data saka ni jin kunya yadda take ta yaba min tana sa min albarka, muna yin sallama da ita na kira Daddy, nan muka kwashe lokaci mai tsaye ina bashi labarin abubuwan da suka faru cikin week din, bayan mun yi sallama kan gado na koma na kwanta ina sake-sake, ban san iya lokacin dana dauka ina tunanika ba sai dai na bude ido naga karfe sha biyu tayi, a raina nace su Hafsat karfe biyu suke dawowa daga makaranta, and I can't stop imagining ya suke manejin oats a cikinsu fiye da awowi biyar. Cimak na tashi na fita falo, Anti ta gama lissafin nata tana zaune ne kawai tana kallon tashar CBN, na zauna a gefenta nace "Anti me za a girka ne na rana naga su Hafsat sun kusa dawowa?" dagowa tayi tana kallona cikin wani kallo dana kasa gane ma'anar shi, ta yamutse baki kafin tace "ke har kin iya girki ne dama?" nace sosai ma, ina taya mommy idan tana yi. A raina kuwa cewa nake "a yadda nake jina akan girki Allah na tuba ai gani nake zan iya karawa ko da wani irin chef ne!" saboda ba yabon kai ba, dishes dai tun daga kan na hausa, na Yoruba da abinda ya danganci na mai jajayen kunne na kware a yin su don mommy na gwana ce in dai akan girki ne. Sai daga kare min kallo kafin tace ki dafa shinkafa da miya to, zaki iya kuwa? Na danyi murmushi kawai, da alamu gani take girki wani katoton aiki ne bata san a wajena kamar shakar ruwa ne, nace "zan iya Anti" tace to shikenan, je ki fara" babu musu na tashi na fada kicin din ina tattare hannun riga ta.





*♡Jeedderh♡*
[12/9, 8:51 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*10*

*You're the right time at the right moment...., You're the sunlight, keeps my heart going.... Know when I'm with you, can't keep my self from falling...... Right time at the right moment It's You...., You....., It's You....!*
A song by; Henry, It's_You dedicated to My Fans.



Tsaye nayi a tsakiyar kitchen din ina tunanin ta Inda zan fara, sai dana danyi sighing kafin na tunkari freezer na bude, kayan vegetables da nama ne da dangin kifi a shirye kala-kala a ciki saboda tsabar ajiya duk da cewa a cikin freezer suke amma sun fara sauya kama musamman vegetables din. Kashe freezer din nayi yadda zan samu in ciro kaya ta sauqi, na shiga store nan ma kayan abinci ne dankare kamar a super market babu nau'in da babu daga na gida har na waje. Maimakon shinkafa da miya sai nayi fried rice wadda na wadata ta da dangin veggies, na yanka hanta kanana a ciki. Na dauko fresh sardines na wanke na yanyanka shi na soya wanda zan yi decorating din shinkafar dashi. Ina tsaye ina slicing din albasa wadda zanyi onion sauce da ita, ban ji shigowar mutum kicin din ba sai magana naji a baya na, "what are you doing here?" na juya a firgice na kalli wajen da sautin maganar ya fito. Abbu ne tsaye a kofar kicin din ya rungume hannuwa a kirjin shi yana kallona, naji na diririce da kyar na iya cewa "ammmm.... Girki?!" na fada kamar ina tambayar shi, ya shaki numfashi yana lumshe idanu, yace "woah! What a delicious smell!! meye kike dafawa haka ya cika mana hanci da kamshi?" dan murmushi na saki kadan, "fried rice ne" yace I hope kin kusa saukewa? I can't wait to taste it. Na gyada kai nan ma, nan da en mintuna zan sauke. Ya juya zai bar kicin din, "OK! I'll go and take a shower then sai in dawo" ya karasa fita daga kicin din yana uttering "thank Goodness!" a kasan zuciyar shi, dama dawowa yayi yayi wanka ya fita ya samo musu abincin da zasu ci sai kuma yana shigowa yaji wani mahaukaciyar kamshin abinci yana fitowa daga kicin wanda ya taso mishi da yunwar shi ta kwana da kwanaki da yake dannewa da lemuka, yana shiga kicin din yaci karo da "beautiful sight' a cewar shi, tana yanka albasa a cutting board cikin kwarewa kamar irin chief cook dinnan a 5 stars hotel, da kyar ya iya suppressing din urge din daya taso mishi na aikata wani abu da yasan will never ever be appropriate, wanda yasan mawuyaci ne idan bai zubar mishi da kimar shi ba a idon yarinyar na har Abadan. Sai kawai ya buge da jingina da bango.

Ina gama yin sauce din na juye shi cikin wani kwanon tangaran, itama fried rice din sauke ta nayi don ta gama, ta min yadda nake so kuwa, wara-wara, yellow shar sai tashin kamshi take yi, na fito da babban food flask na zuba ta a ciki. Oranges na dauko manya da apple da water melon, na bare lemun na saka a juicer ta markada min shi na tace ruwan, na yanka kankanar itama na cire yayan tas, na yanka ta kanana a cikin lemun tare da tuffa, na kawo syrup sugar na zuba a ciki na watsa kankara na fara ciccibar kayan zuwa dinning table. Ina gama shiryawa su Hafsy suka fado falon a guje da alamun gajiya a tare dasu, lokacin dana tare su sai na dinga jina kamar wata Mummy dinnan mai jiran 'ya'yanta su dawo daga makaranta, nayi kokari na kauda weird tunanin daya lullube min zuciya na karbi jakar hannun Hafsy na kai mata daki, ai ko kayan makaranta basu cire ba kowa yayi settling akan kujera na fara serving dinsu kafin na zauna a gefen Hafsy nima na fara ci. Zo kaji santi kuwa, Qaseem har da cewa wai shekarata nawa a makarantar koyon girki? Dariya kawai nake musu acan kasan zuciyana kuwa jin kaina nake a sama, me yafi yabo dadi a duniya?? Abbu ya fito daga dakinshi sanye da wandon jeans da shirt na shan iska, Shima kan dinning din yazo ya zauna. Na mike na fara serving din shi abincin yayin da yake gaisawa da iyalan shi, na zuba mishi komi na ajiye a gaban shi na koma mazaunina na zauna muka ci gaba da cin abincin mu. Wajen cin abincin ya koma shiru, Abbu bai yi magana ba sai kai kawai da yake girgizawa, rashin magana ma yabawa ce. Sai da kowa ya cinye abincin plate din shi duka, suna gamawa kowa ya wuce dakinshi saboda ranar ba zasu koma makaranta ba. Na fara tattare plates din da muka yi amfani dasu na kai kicin, Abbu yana zaune a har a lokacin yana cin dura abinci a cikinshi cikin alamun rashin saurarawa, na fahimci matsananciyar yunwa a tattare dashi. Na kai hannu da niyar dauke jug din juice din da nayi, cikin rashin sa'a shima ya kai nashi hannun don haka nayi saurin janye nawa hannun amma duk da haka sai da hannunshi ya dan gogi hannuna, Ya Allah!! Wani irin current naji ya taba ni kamar na taba budaddiyar wayar wuta. Naja baya da sauri ina shivering, shi kam hannunshi ya kurawa idanu yana kallo kamar wani bakon abu kafin ya dago idanunshi yana kallona mai cike da ma'anoni wadanda na kasa pathorming abinda suke nufi. A hankali ya maida kanshi ga plate dinshi ya cigaba da cin abincin amma fa cikin rashin kuzari, ganin haka yasa sumi-sumi na wuce dakina kafafuna na shaking. Ina bada baya ya maida kanshi ya jinginar da kujera yana ajiyar numfashi da sauri-sauri, what the hell did he just felt??! Yake tambayar kanshi embarrassingly.


Ina shiga dakina na zube a bakin kofa rawar da jikina yake yi ta karu, Innalillahi!! Kadai naji bakina yana furtawa da karfi, da kyar na iya daidaita natsuwa ta. Wannan wani irin abu ne haka? It's not as if ban taba gogar hannun namiji bane, God Forgive me amma ni har hugging dinsu nayi amma ban taba jin rabi rabin abinda naji ba yau da Abbu ya taba ni, ban taba jin hakan a tattare da ko wane namiji ba sai shi, ko me yasa hakan?? Ban zurfafa tunani na ba na mike na fara gyara daki na ba wai don yayi wani abu ba sai don bani da aikin yi kawai. Har bayan la'asar ina gyara, dana gama wayata na dauka na shiga dakin Hafsy, tana zaune a kasan carpet tana kokarin warware kitson kanta, na zauna a gefen gado ina kallonta, "ya ne pretty?" as usual sai data yi pouting kafin ta kalleni da dara-daran idanunta, "na manta ban fadawa daddy a kaini saloon ba har ya fita, kuma idan Anty Kate taga kaina a haka gobe sai ta dake ni!" na shafo kitson kaina nima ina kallonta, yakamata ma in tsefe shi don ya fara tsufa. Nace "to taho in taya ki" ta waro hakora, "yauwa, kin iya kitso ai koh?" na girgiza mata kai, ta 6ata fuska, nace "noo, kar ki damu, zamu san dabarar da zaa yiwa kan yadda Anti Kate ba zata taba min ke ba koh?" ta gyada kai tare da zuwa ta zauna a kusa dani. Haka kuwa aka yi, muna gama tsifar ta dauko kayan kitso dasu ribbons na fara gyara mata kai, kalba na mata manya wadanda na kayata da ribbons din da dutsunan kitso kuma ga mamaki na yayi kyau sosai, ita kanta data kalli kanta a madubi tsalle-tsalle ta hau yi. Ni kam dariya na mata na tashi na fada kicin don yamma tayi sosai, sakwara nayi da miyar ganye, na wadata miyar da nama da busasshen kifi, na hada fruit salad na kai komi kan dinning na ajiye. Da wuri na tattaro kan yaran muka ci abincin mu kowa ya koma daki ya kwanta duk a dabara ta na kaucewa haduwa da Abbu, sai Allah ya taimake ni har na koma daki bai dawo gidan ba. Sai da na gama shirin kwanciya barci sannan na jiyo tashin muryar su shi da Anti a falo da alamun tare suka dawo gidan.

Washegari tun da safe na fada kicin, potato chips nayi da egg sauce sai ruwan shayi wanda yasha kayan kamshi, na soyawa su Qaseem doya da kwai wanda zasu tafi makaranta dashi na zuba musu a lunch boxes dinsu, yin komi nake yi cike da kuzari da walwalata. Aikin daya jima yana burge ni kenan, kullum naje gidan Aunty Uwani ina ganin tana hadawa yaranta abincin tafiya makaranta irin haka, abin yana burge ni ba kadan ba, at last yau gashi dai nima na hadawa nawa. A gurguje na shirya na fito saboda lokaci daya fara wucewa, yanzu ma mu hudu kadai muka karya don daga Abbu din har ita Aunty din babu wanda ya fito, muka gama karin mu muka wuce makaranta.


Gabadaya kwanakin girkin gida da kula da gidan ya koma hannuna yayin da ita uwar gida mai gayya mai aiki kullum sai dai tayi rashe-rashe sai dai a dafa ta zauna taci ta tashi ta kara gaba abun ta babu godi bare na gode, dama dama ma Abbu. Yana nuna jin dadin shi kwarai game da hakan, ina kuma shan godiya a wajen shi sosai wanda ina ga hakan ne yasa nake dagewa tun karfi na ina musu dadadan girki wadanda zasu sa zuciyar shi a farin ciki yayi ta mun addu'ar daya saba, halin Aunty kam tun ina damuwa dashi har na daina. Matar is really complicated, gane halinta da Inda ta saka gaba abu ne mai wahala kam, to mai wahala mana. Ban ka kula da cin abincin miji, baka san shan miji ba, Baka san gyara muhallin mijinka ba, ba ido na saka musu ba, amma nasan bata kwanan dakin miji, ko ina suke ko a gaban wa suke she is always making it obvious that bata damu da mijinta, rayuwar Aunty Mubeenah fa tana bukatar gyara sosai da sosai. Allah Allah nake juma'a tazo in wuce Kaduna, va wai don na gaji da hidimar da nake yi dasu ba in fact, kwanaki biyar zuwa shidan da nayi ina yiwa Abbu da iyalan shi girki has been the best and happiest moment na rayuwata, sun kara min kusanci da iyalan, sun kara min so da qaunar su kamar yadda suka kara musu sona da qaunata. Kawai dai nayi kewan su Mommy da Daddy ne don haka ranar juma'a da wuri na dawo na hada kayan da nasan zan bukata, Abbu baya gari yayi tafiya ranar Thursday. Direba yana zuwa na fito tare da kulle gidan don babu kowa, Hajiya Aunty Mubeenah an tafi neman kudi bayan babu abinda ta nema ta rasa a gidan auren ta.





*♡Jeedderh♡*

[12/9, 9:09 PM] ‪+234 816 965 3238‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*11*

*"Paradise is a home of Honor, Dignity, Rest, Satisfaction, Beauty, Joy and Peace., May Allah make it to be your permanent Home Ameeeen, Jumma'at Kareem!!"*
Abinda na karanta kenan daga wayana bayan na shiga dakina, Kimanin awowi biyu da dawowa na kenan. Na duba kasan message din inda nake zaton zan ga sunan wanda ya turo text din saboda babu suna a jiki sai number kawai. *'_Galadanchi!'* shine sunan dana gani. Crap! Abbu ne!! Zuciyata ta hau fadi ina jin tana wani tsalle-tsalle, wayar na zurawa idanu ina lalubo abinda zan tunana amma komi ya tafi blank, na lalubo su da kyar na shiga jefawa kaina su kamar ni ce Abbu din, "Friday message kuma? Why would he?" zuciya ta tace stupid! Kuma ba zai miki message ba kike nufi ko me? You know this is a normal thing tsakanin mutane yanzu, ke da Daddy da sauran uncles dinki ba kuna exchanging irin wannan messages din a tsakanin ku ba?? Na gyada kai a hankali kamar wawiya, sai a lokacin kuma na gano shirmen da nayi, God! I can be silly sometimes, saboda Allah addu'a ya min mai dadi amma ban amsa mishi ba na hau tuhumar dalilin da yasa ya turo min sakon. Da kwarin gwiwa ta na tura mishi amsa, *'Ameen Abbu, and same to you. How's your presentation? Allah ya dawo daku lafiya Ameen!'*. Shiru har aka dauki lokaci babu reply, na daga kafada ta, watakila I've gone too far ne, meye nawa na wani tambayar yadda harkokin shi suke tafiya kamar wata shakikiyar shi? Na tabe baki na tashi daga kan kujerar dana zauna don wai da zama nayi ina jiran amsar shi kamar wata sakara. Kayan jikina na shiga cirewa ina jifa dasu cikin laundry bin, na daura towel a jikina nazo fada bathroom.

☆☆☆☆☆☆☆☆

Idanunshi kur akan wayar yana kallo cikin wani irin yanayi, kalmomi ne da rabon daya jisu daga bakin matar auren shi har ya manta su, anya ma ya taba jin su kuwa? Ta yaya ma aka yi tasan cewa presentation yaje? He can't recall telling her, wani sashe na zuciyar shi yace ba mamaki wajen su Pretty taji don ya kula tana son yarinyar sosai, yana mamakin yadda idan suna hira da Hafsy take maida kanta kamar yarinyar har ka kasa tantance yaro da babba a cikinsu. Ya lumshe idanu a hankali...... Bai san cewa ya zurfafa a tunani ba sai daya ji muryar Chairman dinsu ta microphone, "Dr. Galadanchi?? Anything from you??" yayi firgigit ya dawo daga duniyar imagination daya tafi, "yeah of course Mr. Collins..." ya jefa wayar shi a aljihu ya dauki wasu takardu ya tafi kan step fara bayani a nutse....

●●●●●●●●●●

Wannan weekend din ziyara nayi, naje gidan Anti Uwani na musu yini a can, daga nan ni da AbdulJalal muka shiga gari sai bayan isha'i ya sauke ni a gida bayan mun tsaya a Mcbae mun sayi tarkacen chocolates da ice cream. Washegari lahdi sai wajen karfe biyar na bar gida cike da kewar Mom da Dad, amma fa can kasan zuciyana wani farin ciki da doki ne dankare a cikinta, dokin in koma inci gaba da yiwa Abbu dadadan girki na yana ci yana yaba min har da santi. Sai dai koda na isa sai na tarar Hareera ta dawo daga biki, Abbu kuma baya gari, gwiwa na yayi sanyi sosai, jiki a sanyaye na shige daki na.
Washegari a tsaitsaye muka ci abinci muka wuce makaranta, ranar mun sha ayyuka a lab kamar me! A matukar gajiye muka zauna akan dakalin da muka saba zama ni da Ramlah cikin dan garden din da muke hutawa, na kalle ta ina dan murmushi, "ke jiya fa muka hadu da Muneer" bata nuna alamun abun ya dadata da kasa ba kamar yadda nayi zato, tayi fuskar shanu tace a ina? Nace "McBae, mun shiga siyayya ni da AbdulJalal. God! Baki

Please Login or Register in order to submit comment