Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abun zai bata miki rai da ban bashi number din ba, kiyi hakuri sis kinji?" na ajiye numfashi tare da kallonta, "ni fa ba bashi number din da kika yi bane ya bani haushi sai zuwa da kika yi kina yada sirrina a wajen stranger. Saboda Allah meye na zuwa kina gaya mishi wai ina crushing din wani?" tayi fuskar tausayi "Nima nasan ban kyauta ba, da gaske ban san lokacin dana gaya mishi ba wallahi, hira ce tayi hira ni kuma na saki baki ina bashi labari, amma don Allah kiyi hakuri" nace shikenan ya wuce, ta rungume ni tana er dariya, thanks sissy. Na harari Ramlah nace "ke kuma ba zaki bani hakurin bane?" ta zaro ido waje, "ni kuma me nayi?" nace waye ya gayawa su Ni'ima cewa ina crushing Muneer idan ba ke ba?" ta ta6e baki, "dadin ta ma ba karya nayi ba" nayi murmushin yake, zan ga ranar da Ramlah zata yi abu like a good girl in dai akan zancen Muneer ne, she's always playing bad, making it obvious that bata son gayen ko kadan, to amma ya zan yi? A gani na Allah ne ya dora min son Muneer bani na dorawa kaina ba. Da haka dai muka shirya muka hau hira har Malam Bala yaxo muka tafi har su Ni'ima din zasu je su ga jikin Abbu. A can muka Tarar dasu Anty Rahina suma sun zo, nan muka wuni dasu muna ta hira har Yamma tayi kafin Suka tafi. Tun daga ranar kuwa ban sake ganin kiran wayar Fahad a waya na ba.

Satin Abbu uku yana jinyar kafar shi kafin ya warke ya fara fita harkokin shi. Naje gida weekend muka je Malumfashi, Malam Inuwa kanin baban su Daddy ya rasu, kakanni na na ainihi sun jima da rasuwa ban yi wayo na ganni dasu ba, shi yasa su Hafsy suke burge ni ba kadan ba, suna da kakanni ta kowanne fanni abin su. Wato naji dadin zuwa Malumfashi wannan karon ba kadan ba, cousins dina duk sun dawo daga makaranta wasu hutu suka zo wasu kuwa sun zo wajen gaisuwa ne, nan muka hadu muka yi ta yawace-yawace da ziyara har ban so lahadi tayi ba, haka dai muka yi sallama da dangina muka wuce gida. Muna isowa na wuce Kano Saboda yamma tayi don haka a gajiye likis na isa gida, babu abinda na iya tsinanawa, ina gama sallah na bi lafiyar gado sai da gari ya waye.

Mun je lab Ramlah take bani labarin wata er ajinmu a Kasu zata yi aure wannan week din, er Kano ce, ta tambaye ni zan je nace ai dole ne, Sahiba mutuniyar mu ce ta sosai. Tun a ranar na kira daddy na fada mishi ba zan samu zuwa weekend wannan satin ba saboda bikin abokiyar karatun mu yace shi kenan Allah ya kaimu wani satin. Nayi shiru ban kashe wayar ba, tuni ya fahimci abinda nake nufi, "kudin anko koh?" naji ya tambaye ni, na saki murmushi mai sauti, wato Daddy ya karance ni kamar bayan hannunshi, yace "I will wire you the money in the next few minutes" nace "to Daddy nagode, Allah ya bar min kai!" yayi dariya tare da cewa "uwata kenan". A ranar muka shiga kasuwa muka sayo ashoben bikin, muka biya ta wajen telan Ramlah muka ajiye dinkin. Ranar juma'ah muka je saloon aka mana wankin kai da kitso, ni har kunshin hannu aka min, dama gani da son lalle kamar me. Ya kuwa yi min kyau sosai, sai da Ramlah taga na hannuna wai take cewa data sani da an mata itama, na kuwa dinga mata dariya. Daga nan muka yi shatar taxi muka wuce gida, sai da muka ajiye ta kafin muka wuce. Ina shiga falon naci karo da buhunan Irish, plantain ne, kayan marmari dasu doya, tunda na gani nasan cewa Abbu ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa Ibadan taron Doctors na fadin Nigeria, Allah ya taimaki rayuwata na mishi text na gaya mishi zamu biya ta saloon daga lab, yau da na shiga uku na ai. Na taimakawa Harira muka kai kayan kicin muka ajiye su a inda ya dace kafin na wuce dakina nayi sallah. Ina xaune Hafsy ta leko dakin tace in fita mu ci abinci, bana ma jin yunwa amma haka nan dai na fita don nasan bani da wani excuse din badawa. Na dauki gyale mai fadi na dora akan doguwar rigar jikina. Bana yarda in fita daga dakina ba tare da mayafi ba matukar nasan Abbu yana gari sai dai by mistake. Suna kan dinning table a zaune, Abbu na fara hangowa. Sanye yake da shirt din KC brown da bakin Jeans, ya kara wani irin kyau na musamman a kwanaki shida din da nayi ban gan shi ba. Na tafi da dokina na durkusa na gaida shi, shima cike da fara'ah ya amsa min, na gaida Anty Mubeenah kafin naja kujera na zauna muka fara cin abinci. Da muka gama Abbu ya fita, Anty ta wuce daki mu kuwa muka zauna a falo muna kallo har wajen karfe goma da rabi, har lokacin Abbu bai dawo ba. Na kashe kayan kallon kowannen mu ya nufi dakin shi ya kwanta.
[12/8, 12:53 PM] ‪+234 810 910 7052‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*18*

_'Turn to Allaaah he's never far away......_
_'Put your trust in him, raise your hands and pray..... Ohhh Ya Allah! Guide my steps don't let me go astray..... You're the only One Who can show me the way..... Show me the way........ Show me the way...........'_
*In Shaa Allah by Maheer Zayn*

Da kyar na samu na sauka daga kan gadona ganin na gaji da juye-juye barci yaki zuwa misalin karfe tara kenan na washegarin ranar Assabar. Na fito daga dakina sanye da wandon Sports da rigar shi cotton ruwan madara, na dora hular beanie akaina wadda na nannade gashin kaina na saka a ciki. Wandering na fara yi a cikin falon hannuwana saye cikin aljihun wandon. Na tsaya a kasan staircase din dake falon, tunda nake a gidan ban taba Hawa saman ba, jifa-jifa dai na kan ga ko dai Abbu ya hau ko kuma yara sun sauko kuma ban taba tambayar me suke yi a wajen ba. Out of curiosity na fara takawa ina hawa saman, Tun kafin in karasa na saki baki galala ina kallo. Gym zan kira shi ko kuwa amusement park?? Kayan wasan yara kala-kala da different types of exercising machines ne birjik a wajen, wasu na san su saboda nima ina zuwa gym duk weekends lokacin da ina gida. Na fara zagaye wajen cike da mamaki, as in Abbu will never cease to amaze beings. Kan Dip station na hau na fara kokarin dagawa amma ko motsi, da alamun yafi karfina ne don haka na sauka. Daga bayana naji ance "hey! What are you doing here??" da sauri na juya, yana tsaye a jikin wata kofa sanye da sportys ya rataya dan karamin tawul a wuyanshi, na sadda kaina kasa cikin rashin abin cewa. Ya fara takowa a nutse har yazo gab dani, ya jingina da station machine din, jin yayi shiru nasan sauraren amsar da zan bashi ne yake yi, nace "umh! Dama kawai ina zagaye ne sai kuma naga na shigo nan" yace "this is your first time here I believe?" na gyada kaina. Yace I see. Are you interested in exercising?? Da sauri na dago ina kallon shi, "sosai ma Abbu! A gida ma ina zuwa gym duk sat...." wani irin kallo yake wata min babu shiri na kama bakina na bame, na sadda kaina kasa ina jin kafafuna suna dan shaking. Kokarin fita ya fara yi yana cewa "sai ki dan motsa jikinki ko? Ni zan sauka kasa..... By the way, I like your lalle!" nayi murmushi ina kara kallon hannuna, ni kaina nasan lallen yayi kyau sosai. Yana fita na fara wasa da karafa, sai wajen karfe goma da rabi na sauko falo, break nayi na koma dakina, sai lokacin naji gajiya da barci sun tarar min na kwanta. Kiran wayar Ramlah ne ya tashe ni daga barcin da nake yi, tace gata nan ta shigo layin mu daga amsar dinki in fito waje, na tashi da sauri na dora hijabi akan kayana na fita. Abbu da maigadi da wani makocin Abbu din suna kofar gida akan dan benci suna hira, na gaidasu. Ina tsayawa sai gata cikin napep, ta fito ta biya mai napep din, ta gaida su Abbu kafin muka shige cikin gida. Muna shiga ta fara jefo mun tambaya a rikice, "ke waccan giant gaye din waye? Anan gidan yake zaune?" cikin alamun tambaya nace wa kenan? Tace "wani farin gaye haka da jallabiya baka a jikin shi??" dariya na kwashe da ita nace "wai dama baki san Abbu ba duk abinnan da ake yi?" tayi turus! Da gaske wancan ne Abbu? Na gyada mata kai, "Ya Allah! He's cool babe, dan dai yana da mata wallahi....!" duka na kai mata ina dariya, "da bashi da mata fa sai kiyi me maras M? Kina da mijin aure a hannu dai shegiya" ta turo baki. A dakina muka zube, ta fiddo kayan sun yi kyau sosai, "sai dai rigar tayi show me da yawa" na fada cikin korafi ina kara juya rigar, ta harare ni, "to sheikha. Ina cewa gyale zaki saka?" na turo baki kafin na daga kafada sama.

Wajen karfe hudu muka isa wajen shagalin bikin. Tuni an fara shagalin, yawancin en makarantar mu sun je abin an jima ba a hadu ba nan muka hadu aka yi ta hirar yaushe gamo ana hotuna. Ana gama sallar ishai'i aka fara daukar mu zuwa wajen dinner. Mun sake wata kwalliyar cikin doguwar rigar gown ta ankon zuwa dinner, purple ce sai rose head maroon color da heel shima maroon sai er karamar jaka maroon. Mun sha kyau abinmu kamar ka sace. Mun fito muna kokarin shiga mota zuwa wajen dinner nace karo da Bilyamin abokin Muneer, da mamaki ya min magana na juyo ina kallon shi, nima mamakin ne ya kama ni kafin muka gaisa dashi yake gaya min angon abokin shine. Ya Kalle ni tun daga sama har kasa yace "amma kinyi kyau sosai Nafee" nayi murmushi sosai har da fari, I'm a sucker for compliments. Yace "naga kina yawo ke kadai, Zan iya rokon alfarmar ki zama date dina for today?" nace "y not?" na kira Ramlah tazo muka shige mota abin mu muka wuce. Muna tafe muna ta hira har wajen dinner, wajen ya tsaru sai sautin kida ke tashi muka samu waje muka zauna, amarya da ango ana kan high table. An fara shagali kawayen couple din suka fita fili muka dan taka rawa da liki muka koma wajenmu muka zauna, ana ta shagali har ban san lokaci ya tafi ba sai dana ji karan shigowar message a wayana ta hanyar vibrating, na daga karfe goma da rabi gabana yayi mummunan bugawa, na duba message din daga Abbu ne, *"Where are you now?"* na mike da sauri jikina yana rawa, su duka suka juyo suka kalleni, Ramlah tace meye? Cikin rikicewa nace "Abbu..... Gida. Gida zan tafi yanxu" tace haba! Ki jira a tashi mana dan Allah kinda fa sauran mutane suna nan" nace "noo Ramlah. Abbu just texted me, nasan ma sai na sha fada yau wallahi" ta kalle ni sosai, "to sai me? Ina ce ba Daddy bane? Nasan ko daddy ne ba zai miki fadan kinyi dare a wajen dinar biki ba" na girgiza kai, "baki san Abbu bane Ramlah..... Bilyamin don Allah ko zaka taimaka ka mika ni gida? Babu nisa daga nan" na maida maganar ga Bilyamin don nasan idan nace zan tsaya fahimtar da Ramlah zamu iya kwana a wajen bata fahimta ba, ya mike yana lalubar makulli a cikin aljihun wandon shi, ya ciro key din ya Kalle ni, "muje koh?" na wa Ramlah da wasu daga cikin mates dinmu dake kusa da inda muke muka tafi. A cikin mota Bilyamin yana ta ja na da hira amma sam hankalina baya wajen ko kadan, da kwatance yayi parking a kofar gate. Na bude murfin motor na fita shima ya fita, na zagaya ta gefen shi nace "to Bilyamin ka gaida gida, thanks for the ride" yace "Kar ki damu.... Me za a cewa mutumin ne?" na danyi murmushi nace "kyale mutumin nan naka, kwana biyu shiru amma bai neme ni ba" yayi dariya yace to sai da safe. Sai dana shiga cikin gidan kafin ya tashi motar shi ya tafi. Bakina dauke da addu'ah da komi na shiga falon, babu kowa a ciki, da sauri na shige dakina na rufe, na tuge dankwalin kaina na zauna a gefen gado ina ajiyar xuciya cikin samun relief. Wayata ta dauki kara, ganin Sunan Abbu a jiki sai dana yi kamar Kar in dauka, na dai daure na daga na kara a kunnena tun kafin inyi magana muryar shi ta doki dodon kunnena, a fusace yake maganar, "wato Nafeesah kin raina ni koh? Karfe nawa na kafa miki dokar dawowa gida idan kin fita?" jikina yayi sanyi, naji dama ban je wajen dina din ba da ran Abbu bai baci Saboda ni ba, nace "Abbu don Allah kayi hakuri, wallahi dinner din ne ba a fara da wuri ba" yace "sai kuma aka ce dole ne sai kin je wajen dinner din koda zaki kai karfe sha biyu ne a waje koh?" na girgiza kai kamar yana gabana, yayi shiru. Har ina murna ya gama fadan shi sai kuma naji yace "waye ya kawo ki yanzun?" nace "Bilyaminu ne, dan makarantar mu ne" yace "dan makarantar ku? Kawai Saboda yana dan makarantar ku zaki kwashi kafa ki shiga motar shi babu tsoron komi a matsayin ki na diya mace?" nayi saurin cewa "ai abokin....." sai kuma nayi shiru, harshe na yayi min nauyi sosai na kasa fadar kalmar. Shiru ya biyo baya, bai yi magana ba ni kuma na kasa karasa abinda nayi niyar fada, "it's okay!" naji yace daga can a hankali kamar ba shine wanda yake daga murya yanxu ba, "goodnight!" ya kashe wayar. Na bi wayar da kallo cikin sanyin jiki, da kyar na iya sauka daga kan gadon na cire kayan jikina nasa na bacci na kwanta.

*♡Jeedderh♡*
[12/8, 12:55 PM] ‪+234 810 910 7052‬: Kamar yadda suka ce, yini sur suka mana a gidan. Da rana Abbu yace kar mu yi abinci, oda aka mana daga Chicken Delicacy peppered chicken da spaghetti lasagna sai yoghurt mai sanyi, muka ci muka yi nak tare dasu Hafsy. Bayan mun gama cin abincin na ja su kicin muka yi baking din cupcakes, babu kayan icing don haka bamu yi icing din shi ba. Da yamma likis Abbu yace su fito ya maida su gida, na rataya gyale a kafada ta muka fita tare dasu zan musu rakiya, cikin motar Abbu picnic su Qaseem ne a ciki sun hakimce Hafsy tana gaba su kuma suna baya Abbun yana jingine da motar yana amsa waya cikin hadadden turancin shi hannunshi daya saye cikin aljihun wandon shi, su Sa'adiya suka shige mota ni kuma na tsaya daga waje muna er hira har ya gama wayar ya shiga motar ya tayar, na ja baya kadan ina daga musu hannu, ya zuro kanshi ta cikin motar yace "yah? Baki zuwa ne ke?" na kalli su Ni'ima kafin na kara kallon shi, "can I?" ya tabe baki, "that is idan kina son zuwa fa" na bude motar nima na shiga ya ja motar. Hira muke dasu Ni'ima amma jifa-jifa idanuna su kan sauka akan Abbu dake tuki hankali kwance, wata dagawa da nayi idanuna suka sauka cikin kyawawan sparkling eyes din shi masu cike da kwarjini ta cikin madubin gaban motar, kamar wadda aka zarewa kuzari haka naji jikina yayi sanyi, gashi na kasa janye idanuna daga nashi sai shine ya janye nashin. Nayi ajiyar zuciya a hankali tare da sauke kaina kasa, ina kallon su Ni'ima suna kus-kus suna en da-re-re-ku a raina nayi fatan Allah yasa ba jirgina suka harbo ba. A gidan muka yi sallar magriba da ishai'i muka ci dambun couscous sannan muka musu sallama muka tafi. Dawowar tamu shiru, su Hafsy kadai su ke shan hirar su ni kam ina kan wayata ina buga game din piano tiles saboda bana son satar kallon Abbu da idanuna suke yi har ga Allah. Muna shiga falo ban tsaya a falo ba nayi hanyar dakina, Abbu ya tsaida ni ta hanyar kiran sunana, na juya a hankali. Cewa yayi "Plss dafa mun shayi mana" nace toh. Kayan hannuna kawai na ajiye a dakin na shiga kicin na dafa shayin da kayan kamshi a ciki, na matsa dan lemun tsami na zuba a cikin butar shayi na dora akan tray tare da kofi na kinkima na kai mishi. Yana zaune ya sa system dinshi a gaba da tulin takardu a gefen shi da alamu aiki zai yi, na ajiye akan coffee table dake gefenshi na durkusa a gaban shi, ya dago a hankali ya kalleni, "lafiya Nafeesah?" na sadda kaina kasa nace "Abbu don Allah kayi hakuri da abunda ya faru jiya, in shaa Allahu ba zan kara ba. Don Allah ka daina fushi dani!" shiru yayi yana kallona kafin ya nisa, "ba fushi nayi ba Nafeesah. Kawai ban ji dadi bane yadda kika biyo namijin da baki sani ba cikin dare, what if God Forbid, something bad happens to you Nafeesah? Bayan wannan kin duba shigar dake jikin ki kuwa? Haba Nafeesah!! Ke da nake ganinki da hankalinki da komi, how could you walk in front of many people with that dressing? And you were smiling and laughing in front of that guy, me yasa??" na sake yin kasa da kaina, ina mamakin ta yadda aka yi har Abbu ya ga irin shigar da nayi da kuma hirar da muka yi da Bilyamin, sai dai yanxu is not the right time to think about that, fata na daya kawai shine Abbu ya daina fushi dani. Last 20 to 23 hours has been like a hell to me, sukuni da walwala sun kaurace min saboda fushin mutumin nan daya; Abbu. Ji nake idan na kai gobe ba tare da na ga murmushin shi a gare ni ba zuciyata zata iya bugawa. Kaina na kara yin kasa dashi nace "kayi hakuri Abbu, ba zan kara ba" yace "dadi na dake Nafeesah kina da saurin admitting mistakes naki ki kuma yi repenting immediately, Allah yasa ki dore a haka" nayi kasa da kaina zuciyata ta fara washewa, da alamun ya huce. Yace "tashi ki je ki kwanta, ki daina damun kanki kuma ba fushi nake yi dake ba kin ji?" na dago a hankali na kalle shi kamar mai son karanta gaskiyar abinda yake fada, ya sakar min murmushin shi reassuringly. Naji wani irin sanyi ya mamaye min zuciyata, nima murmushin na sakar mishi sosai cike da farin ciki nace "Abbu nagode sosai, Goodnight!" na mike cike da kuzari da kwarin jiki na tafi, ya bini da kallo yana murmushi sai dana shiga daki sannan yayi ajiyar numfashi ya dauki shayin dana hada mishi ya fara kurba a hankali yana gyada kai cike da nuna gamsuwa. Ni kam ina shiga daki har sai dana yi dan tsalle cike da murna, na shiga bayi nayi brush na fito ina en wake wakena cike da farin ciki nayi shirin kwanciya barci, tsalle nayi na fada kan gadona, na mirgina daya gefen inda wayata take na bude, sai dana yi chatting na shiga accounts dina na twitter ne, instagram, facebook duk nayi posting ina cikin muudu mai dadi kafin na kashe wayar, na kashe wuta, na balle ma6allan gaban rigata na gaba guda uku naja bargo har wuyana, nayi addu'ar kwanciya barci na shafa na rufe idanuna, ba dadewa barci mai dadi ya yi awon gaba dani.

*♡Jeedderh♡*
[12/8, 1:32 PM] ‪+234 810 910 7052‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*19*

Juyi kawai nake yi na kasa barcin, na rasa abinda yake min dadi a cikin raina. In normal sense nasan cewa da ace wani ne ya min ihu da daga muryan da Abbu ya min yau sai naji bacin rai saboda ni fa na tsani kawai mutum ya dinga nuna he has control over me alhalin baya da, abunda nasan cewa koh a gida nake Daddy ba zai min kwatankwacin fada da tuhumar da Abbu ya min ba, yes! Daddy zai min fada amma ta cikin lumana da nasiha ba irin na Abbu ba. Amma me yasa? Me yasa ko kadan ban ji cewa Abbu bai kyauta ba a cikin raina?? Na juya daya gefen ina kallon wani frame, hoton mu ne ni da Hafsy, ni na dauke mu ya min kyau sosai shi yasa na kai aka wanke min shi. I was extremely confused a lokacin, kwata-kwata na ma rasa a wani matsayi na ajiye Abbu balle in yanke hukunci. I never, even in my dreams wai inyi mafarkin ajiye shi a cikin jerin abokan Baba na, to amma idan ba Abokin Baba na bane shi ba to waye?? Da wadannan tunanukan barci ya dauke ni cike da wadansu irin mafarkai marasa kan gado. Ranar har so nayi in makara sallar Asubahi, sai wajen karfe shida da rabi nayi sallah, ina gamawa na koma na sake kwanciya. Yatsun kafata naji ana ja, cikin barci na janye kafafuna na maida su cikin blanket tare da kara kankame pillow. Tafiyar tsutsa naji ana min a wuyana, da sauri na bude idanuna tare da hantsilawa kasan gado har ina dan buge kaina, na dago da sauri, yanayin fuskana ya canza daga harara zuwa na mamaki. Da mamaki nake kallon su, Ni'ima ne da Sa'adiya. Zaune suke a gefen gadon suna kallona, nayi tsalle a kansu muna shewa, sai da muka gama na zauna a gefen su nace "me kuke yi ne anan yammata?" ni'ima tace ziyara muka kawo, ko it's not allowed? Nace "ni na isa in ce? Amma da safe haka?" idanuna ya sauka akan agogo, karfe goma da rabi. Sa'adiya tayi murmushi tace "Abinci fa muka kawo wa babban Yaya." na Kalle su "Abbu?" Ni'ima tace "to da wa?? Funkasu ne da mijin taushe mai dadi wallahi, tashi kixo ki ci kafin ya huce" na sauka daga kan gadon ina cewa "yanxu kuwa" toilet na shiga nayi brush, na fito na bude wardrobe na janyo bakar BF jacket ta cotton na dora akan vest din dake jikina, na nannade kitson da aka min na daure da ribbon na saka hular beanie muka fita falon, dama nasan yara suna makaranta don haka ban yi mamaki da naga falon babu kowa ba, sai da muka shiga second falo ne na ga

Please Login or Register in order to submit comment