Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shakar barci a kafadata. Muna fita waje muka jiyo horn din mota a gefenmu, muka juya. Wata jar mota er karama da Ita mai kyau, Anty tace muje, Harith ne zai mika mu gida. Sai dana turo baki kafin na bi bayanta, haka kawai naji gayen bai kwanta min a rai ba. Na bude gidan baya na zauna a gefen Anty, Harith ya juyo ya kalli Antyn kafin ya kalleni ya sake kallonta, "amma dai ina fata ba Driver zaku maida ni ba ko Sis?" Anty tace min dan Allah tashi ki koma gaba diyata. Ba yanda na iya na fita na koma gaban, ya tashi motar muka tafi. Babu wanda yayi magana a cikinmu har muka isa kofar gidanmu, yayi parking muka fita, Anty tace mishi "sai da safe koh?" bai amsa ba sai kallona da yayi, "enmata babu godiya ne?" ban san lokacin dana wurga mishi harara ba na juya na wuce abina, na kula he's very arrogant. Anty ta biyo bayana tana ce min wai kar in damu dashi, haka halinshi yake. Ban ma tanka mata ba don a tunanina ai sai ka damu da mutum ne sannan al'amuran shi suke damun ka. Sai da muka shimfidar da Mukhlis sannan na mata sai da safe na wuce dakina, cikin mintuna sha biyar na gama duk shirin da zan yi na kwanta barci.

Washegari aka fara bikin gidan su Anty Shafa, tun da safe ta tafi ni kam ko wajen bikin ban leka ba Mommy ce ma taje. Ina gida da yamma Malamin dake koya min karatu yazo ya kara min, lokacin Mommy ta dawo muka shiga kicin muka girka Jollof macaroni da fried chicken, muna girkin nake tambayarta Mama Sauda da yake kwana biyu ta sha rashin lafiya don haka suka maidata kauyen su tace ai taji sauki tuni, Daddy ne yace tayi zamanta a can kawai, na gyada kai.

Ni kadai ce a cikin falon lokacin da Anty Shafa ta dawo, na mata sannu da zuwa tace "tare muke da Harith wai yunwa yake ji, Allah sa akwai abincin?" na kalli dinning nace "akwai, sai dai ban tunanin zai ishe ku ku biyu" tace "nooo, ni nace abinci a gida, shine wai ba zai ci abincin biki ba, he can be picky about foods sometimes" na tabe baki nace shi ya sani ai. Anty tayi murmushi tare da juyawa don mishi iso ni kuma na leka dakin Mommy na fada mata. Ina dawowa falon yana zaune a daya daga cikin kujerun falon, Mukhlis yana cinyar shi, yaron yana ganina ya sauka daga kan cinyar shi ya rugo ya rungume ni, na tare shi ina dariya nace "mun shirya yanzu kenan?" Anty tace dama shi ai kwana daya ake Sabo dashi. Saboda idon Anty ne yasa na kalli sashen da Harith yake, "sannu" kawai nace, ban tsaya jiran amsawar shi ba na wuce dinning nayi serving dinshi abincin a plate na kai gaban shi na ajiye, kan kujera na koma na zauna na ja Mukhlis jikina ina jan shi da hira. Ya kalleni yace 'enmata baki bani ruwa ba" sai dana kalleshi kafin na tashi kicin naje na dauko ruwa mai sanyi a fridge na kawo na ajiye mishi, yace "sorry! Bana shan ruwa mai sanyi" na ciza lebe tare da dauke goran ruwan na je na canzo mishi da mara sanyi na kai mishi ya sake kallona yace "Baku da lemu ne haka kamar fanta ko peach?" zuwa lokacin nasan cewa he's doing it on purpose, ban ko kalleshi ba na koma na zauna abina, ya kalli Anty ya wani lankwashe murya, "Anty lemu nake so" tace Bari in dauko maka to, wanne kake so? Yayi saurin cewa "no no Anty, da girman ki ki dauko mun lemu haba! Bari yarinyar can ta dauko min mana" ban san lokacin da wani irin murmushin takaici ya subucewa fatar bakina ba, lallai ma Harith! Wai yarinya! Anty da bata kula da game din da yake bugawa ba ta tashi tsaye tace "Ummiey don Allah taimake shi da lemu, bari in rage kayan jikina" ta shige dakinta ni kuma naci gaba da wasana ni da Mukhlis, kallona yayi yace "baki ji abinda Sis tace ba? Ki bani lemu!" ban kalli sashen da yake ba nace "the kitchen door is over there...." na nuna mishi da yatsa ta, "zaka iya zuwa ka dauko da kanka, m not someone da u can be ordering around ni kuma in biye maka kamar wata er aikin ka" yayi wani irin smirking tare da dan shafa gefen wuyan shi, "seems like u r one Rude babe, I like it!" a xafafe na jefa mishi harara, "hey watch ur mouth!" ya tsuke baki yana jifana da wani irin kallo, "if not ki raba ni dashi?" tsaki kawai naja na kauda kaina gefe don na kula da neman magana ne kawai yake yi. Anty ta fito daga dakinta ta zauna a gefen Harith, ganin yadda nake jifan shi da harara ta dube shi cike da tuhuma tace "Me ka mata Harith?" ya kalleta kafin ya kalleni cikin dage gira, "Me na miki?" tashi kawai nayi na bar musu falon don na kula idan na zauna Harith zai iya sawa in zage shi a gaban Yayar shi abinda bana so kenan. Dakina na koma na fara chatting, a facebook na ga wani page da wani daga cikin friends dina yayi liking, *Hon. Ibrahim Galadanchi Official Fans Page* cikin mamaki na shiga page din, da gaske Abbu dinne. A Profile pic din da aka dora Abbu ne ya saka wata shadda Skye blue dinkin Abacha, shaddar ta matukar yi mishi kyau, kwarjinin shi da kyawun shi sun fito kamar ka kira shi a hoton ya amsa saboda yadda hoton ya dauku sosai. Na kura mishi ido na dan lokaci kafin na janye kaina, jikina yayi wani irin sanyi wanda ganin hoton Abbu da nayi yanzu ya haddasa min, sai kuma wani tunani daya darsu a raina, kenan Abbu har yanzu yana kan bakan shi akan fitowa siyasa? Ni dana ji shiru kwana biyu ban ji zancen ba nayi zaton ko ya hakura ne ashe bai hakura ba. Kenan idan har na aure shi sai dai in janye kiyayyar siyasa dana sawa raina, kenan zan zama matar dan siyasa? Murmushi nake yi kamar wata doluwa da nayi wannan tunanin, na sake janyo wayata nayi liking din page din. Ranar haka na bata Lokaci na wajen saving din pics din Abbu da suke cikin page din, sai wajen karfe sha biyu na kashe wayar na kwanta.





*♡Jeedderh♡*
[12/8, 7:35 AM] ‪+234 816 390 1222‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*27*



*When you run too fast to get to Somewhere....., You Miss the fun of getting There.... Life is not a race, so take it slower and enjoy The Music Before The Song Is Over!*


Sati biyu tsakani muka koma makaranta, ba wani bata lokaci muka shiga lectures ba sauki, Ramlah tuni ta dawo, muka hadu da sauran abokan mu muka fara karatu ka'in da na'in ba sassautawa. Wajen karfe biyar na dawo daga makaranta, mai adaidaita din da nayi shata ya ajiye ni a kofar gidanmu. Na fito ina karewa jar Renault Clio dake fake a kofar gidanmu, dan siririn tsaki naja sanin mamallakin motar; Harith ne. Kwana biyu ya maida gidanmu kamar wani gidan zuwan shi, ya saba dasu Mommy da Daddy sosai cikin dan lokacin sau tari idan bai je gida ba zaka ji Mommy tana ta jajen shi, yayin da a gefe guda har zuwa lokacin mun kasa getting along dashi. Harith yana da yawan tsokana, ni kaina wani lokacin idan yana tsokanata I couldn't resist murmushi duk da is hardly in dara, matsalar Harith daya zuwa biyu, girman kai da son showing up Baban shi mai kudi ne kuma yana karatu a kasar waje, gashi bai iya magana ba, magana duk yadda tazo mishi zai kwabawa mutum ne yayi gaba abinshi duk da dai na fahimci hakan a jinin shi yake but still ni fa sam mutane masu halayen Harith basu cikin en kayana. Kudin mai adaidaitan na ciro na bashi na wuce cikin gida. Sanye nake da wandon jeans pencil da shirt mai tsawo wadda ta sauka har kuguna, na dora bakar rigar kimono a kai tana daya daga cikin tsarabar da Anty Shafa ta kawo min. A hankali nayi ssallama na shiga falon, Harith na zaune akan kujera ya baje shi da Mukhlis suna shan tangerine, Gabadaya sun lalata wajen da bawon lemu, yana ganina ya saki murmushi tare da dago min hannu, "Hii Rudie!" harara na jefa mishi na zauna akan kujera ina kokarin daukar Mukhlis daya xo min oyoyo, na bude jakata na ciro chocolate din Milk Dairy na fasa na mika mishi, Harith bai daddara da hararar dana jefa mishi ba yace "Chocolate aka kawo mana yau? A miko min nawa to" ko kallonshi ban sake yi ba. Mommy ta fito daga kicin hannunta dauke da goran ruwa, ta miko min na amsa tare da dauke Mukhlis daga kan cinyata, tana ganin chocolate din hannunshi ta fara mita, "Ummiey na hana ki ba yaron nan chocolates da sweets amma kin ki, kina so ki lalatawa yaro hakori tun yanzu koh?" nace "Mommy babu abinda zasu mishi yanzu, bayan haka ma ai idan ya girma zai zubda hakoran wasu su fita ne koh?" ta Harare ni "Allah ya shirya min Ke Ummiey, ban san yaushe zaki girma ba" Harith yayi tsulum yace "Mommy kin san wauta irin ta en fari sai a hankali, musamman ma Ita da abun ya hade mata biyu ga faranci ga autanci" kallonshi nayi cike da takaici, nace "wai don Allah meye matsalata da kai ne Harith? Bana shiga harkar ka ka daina shiga tawa pa!" ya wani rausayar da kai innocently, "haba Ummiey, me na miki? Daga fadar gaskiya?" tashi nayi kawai na dauki jakata na shige daki, kayan jikina na cire na duba Lokaci naga da saura kafin a kira Magriba don haka na fita. Tuni Mommy ta gama girki don haka nayi joining dinsu a kallon da suke yi, mommy na tambaya ko ina Anty Shafa? Tace taje gidan su ne yini, Mom ta miko min tangerines masu kyau a bare an shirya su cikin plate tace Harith ne ya kawo musu su ci, na saci kallon inda yake zaune, idanunshi fes suna kaina, muna hada ido ya kanne min ido daya da sauri na janye kaina na dora su akan Mommy.
Ina kwance ina sana'ar chatting dina, naga wata sabuwar number ta turo min comment akan hotona dana dora akan status dina na Whatsapp ranar da safe, kayan dana saka ne ranar nayi murmushi hannuna dauke da mug din coffee, cewa aka yi "you look so cute n gorgeous Nafeesah" na danyi frowning tare da tura "who?...." ba a dauki lokaci ba sai ga reply, Hoton Harith ne ya wani kashe ido daya yana smirking da alamun a lokacin ya dauke shi, tsaki naja na tura mishi, "what? Are you a stalker? Or may be a pervert??" bai turo amsa ba, na tabe baki naci gaba da chatting dina. Wayana tayi kara, number ce duk da haka ban fasa dauka ba, ina kara ta a kunne muryar Harith ta doki dodon kunnena, "Ba a taba jifa na da kalma mai muni a rayuwa irin wannan ba, amma naji dadin sunayen, ban sani ba kila na cancance su ne!" nayi rolling idanuna kamar yana gabana, nace "meye na kira na da daren nan?" yace "just...... Manta kawai. Amma you seems to be avoiding me tunda na shigo rayuwar ki Nafeesah, why? Or may be are you afraid to fall for me??" wata mahaukaciyar dariya na saki har ina kwarewa, "stop being ridiculous Harith. You are not my type, rashin zama kusa da kai da bana yi ba avoiding dinka nake yi ba ko tsoron fadawa tarkon son ka ne ko wace shirme kake fada, i found you very annoying and I don't want to get along with annoying people" ya danyi shiru, cikin raina naji babu dadin maganar dana mishi ba sai dai Harith yana shigar min hanci da yawa I really want to get rid of him. Gyaran murya yayi yace cikin murya mai sanyi kamar ba tashi ba, "and I promise to become your type Nafeesahh, I promise you that.... Nooo, challenge you, deal??" bai jira amsa na ba ya kashe wayar ya bar ni da waya a hannu baki a bude cike da mamakin maganganun shi.


Washegari sai karfe tara da kwata na fito daga dakina cikin shirin makaranta saboda ranar sai karfe goma nake da Lecture, nawa Mommy da Anty Shafa sallama na fita. Shiru-shiru ina tsaye a bakin titi babu alamun wucewar abun hawa, na kara hangar tsawon titin da zai sada ni da Babban titi inda zan samu bus na tabbata idan nace sai na fita bakin titi zan makara ne, na kara duba agogon hannuna karfe tara da rabi ta wuce, na danyi siririn tsaki tare da daga kafa na fara tafiya ina tuhumar kaina dalilin daya hana ni ajiye direba kamar yadda Daddy yaso tun farkon shigata KadPoly ni kuma na kekashe kasa nace A'ah. Motar Harith kawai na gani a gabana kamar wanda aka jefo daga sama, ya tsaya a daidai saitina tare da zuge gilashin motar ya leko da kanshi waje, "will you mind a lift en mata?" ban tsaya neman magana ba na zagaya daya gefen na shiga, yaja motar muka fara tafiya, sai dana mula na mule sannan nace mishi "ka tashi lafiya?" yayi murmushi, "kamar yadda kika tashi ba" daga haka yaja bakin shi yayi shiru har muka isa makaranta, ba karamin jin dadin hakan nayi ba. Yana yin parking na bude murfin motar na fita, dan dukawa nayi ina kallonshi yayin da shima yake kallona, nace "thanks pa!" thumbs up ya min da hannunshi, "Always baby..... Yaushe zaki gama lectures?" nace Four in shaa Allah" yace "idan na samu lokaci zan biyo in dauke ki" nace "noo, you don't have to do that plss" bai amsa ba ya tashi motar ya tafi, a hankali nima na juya na tunkari hall din da zamu yi lecture din.

Karfe hudu dai dai muka fito daga lecture hall din da muka yi na 1-4, ni da Ramlah muke tafe a hankali a cewarta sai ta raka ni bakin gate, muna gab da fita daga parking lot kawai muka ga tsayuwar mutum a gabanmu kamar daga sama., Muneer ne! Na daga idanu na kalleshi a hankali, tunda abun nan ya faru ban kara waya dashi ba haka tunda muka dawo school bamu taba haduwa dashi ba. He was still the same Muneer kamar yadda na san shi, dogo, wankan tarwada....., Ramlah ta jefa mishi wata irin harara, "Malam Lafiya zaka tare mutane a hanya kamar wani tsoron thug?" bai kula da Ita ba idanuwanshi na kaina, ya kira sunana cikin sanyayyar muryar shi wadda ada nake jinta tamkar busar sarewa amma a yanzu, jinta nayi kamar kukan jaki. Yace "Nafeesah! Dan Allah zaki iya bani minti biyar muyi magana?" Ramlah ta yunkuro zata yi magana nayi saurin dakatar da ita, "it's okay Ramlah I've got this. I'll talk to him" ta kalleni sosai kafin ta dan matsa gaba ta bamu waje, na kalleshi a tsaitsaye, "so me kake son fada Ango-Muneer??" na fada sarcastically. Yace "Nafeesah I am really sorry akan abinda ya faru that night, sai daga baya na fahimci I acted rudely towards you, am sorry. Ba niyya na kenan ba na in tozarta ki, ban...." nayi saurin katse shi, "kaga Muneer! Idan akan wannan maganar ne kada ka damu, I've move on already, ni kaina sai daga baya na fahimci kuskuren da nayi na makalewa wanda baya sona. Kai ni sai daga baya ne ma na fahimci ashe ba sonka ne nake yi ba, burge ni kawai kake yi ni kuma da yake I was stupid then I thought it was love ashe it wasn't...." fuskar shi dauke take da wani irin expression wanda ya kusa saka ni dariya a take, daga ganin yadda yayi bai ji dadin maganar da nayi ba. Ko yana tunanin dana ganshi zan zube a gabanshi ina rokon ya aure ni ne? Ya kalleni da fuskarshi cike da damuwa, "Nafeesah......! Would you please give me a second chance? I promise to be what you want me to be, wallahi sai daga baya na fahimci cewa ina son ki, plss ki bani wata dama" ga mamakina maimakon farin ciki sai naji zuciyata tayi wani irin baki, lallai ma Muneer ni zai rainawa wayau? Fuska na hade nace "Muneer ka riga kayi wasa da damar ka in which I am very grateful for that don haka tun wuri kaje ka rungumi amaryar ka kafin kwado ya maka kafa itama ka rasa ta. All the best!" na zagaya ta gefen shi na wuce, da sauri ya tari gabana, "plsssss Nafeesah! Just a second chance! I know u love me, and I know that u didn't get over ur feelings for me!!" cike da wani irin jin haushin shi da kuma kaina ma gabadaya nace "feelings my a**!! Yaudarar kan ka kake so kayi Muneer, I don't Love you any more!!" na fada cikin daga murya, "now if u can please fuck the hell out of my sight plsssss, you are disgusting!!" amma da alamun ko kadan maganganuna basu shiga kunnen shi ba, kokarin matsowa gare ni ya fara yi da sauri naja da baya, just when he was about to take another step closer na jiyo muryar Harith daga bayan mu, "Nafeesah my Love!!"





~So What did you think about today's Chapter?
~What did you think about Harith sudden appearance in the story?
~Don't forget, recommendation door is open to me, so feel free to recommend and correct me anytime you spot a mistake in my writings
~Follow me on Wattpad @Jeeedorhh
~♥~Much love Ni Da Abokin Baba Na Fan's.....~♥~




*♡Jeedderh♡*

*NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*28*

A hankali na juya na kalleshi, ya sake wanka yasa wani wandon jeans din Vogo da rigar CK mai V-neck, ya matso kusa dani ya tsaya gab dani yana kallon Muneer fuskar shi a cunkushe, sun dauki lokaci suna kallon-kallo shi da Muneer babu wanda yayi magana a cikin su, sai da naga shirun yayi yawa sannan na daga kafa na fara tafiya, na kalleshi nace "muje koh?" babu musu ya biyo bayana muka jera muka tafi, muna fara tafiyar ya tsaya cak tare da juyawa ya kalli Muneer da shima ya juyo yana kallonmu, yatsa ya nuna mishi cikin kashedi yace "and dude, stay out of my Fiancé side, if not....." ya juya ya cigaba da tafiya cikin takama har yana hadawa da wani bouncing, na bi bayan shi ina dan murmushin jin dadin shocked and horror expression din dana gani akan fuskar Muneer. Ramlah dake tsaye a gefe tana kallon dramar da muke bugawa ta kamo hannuna taja gefe tana tambayana wai da gaske na daina son Muneer? In ka kalli fuskarta a lokacin sai ta baka dariya, grinning take ear to ear kamar yaron da aka ba kyauta alewar bounty. Na sabule hannunta daga nawa nace mata "kinga jirana ake yi, anjima zamu yi magana" muka yi sallama na wuce na shiga motar Harith har ya tashe ta don haka ja kawai yayi muka wuce. Harara na jefa mishi, ya juyo ya kalleni "what??" nace "what was that for? That fiancé thing??" yayi rolling idanunshi, "baki gane bane? I was just trying to save you from him so that next time ba zai kara damun ki ba koda bana nan, by the way waye shi?" na danyi sighing softly kafin na kalleshi fuskana a dan hade don ya dauki maganar da zan mishi seriously nace "sanin waye Muneer ko rashin sa babu abinda zai tsinana maka don haka stay out of it, maganar fiancé kuma kada ka kara koda cikin wasa ne kuwa ko trying to help kamar yadda kace" ya kalleni yana murmushi cikin tsokana, "ko dai baki son inji cewa crush dinki ne yayi dumping dinki kuma ya dawo yace yana son ki?" kaina na kawar gefe naki kallonshi, naki jinin a tuna min da tarin yarinta da rashin hankalin da nayi akan Muneer. Amma Harith bai kyaleni ba cewa ya sake yi "tunda baya sonki me zai hana ki zo mu sasanta dake?" a fusace na kalleshi "stop messing with me fa Harith!!" ya tabe baki, "well, m not ai dama" nace "to ni nan da kake gani na I am taken ka gane?" ya juyo ya kura min ido na dan lokaci kafin ya maida hankalin shi ga tukin da yake yi yana chuckling, ban kula shi ba na janyo wayata ina latse-latse har muka isa gida. Yau ko godiya bai samu albarkacin jin ta ba, na fita daga motar har ina banging nayi cikin gida. Kai tsaye dakina na shige, nayi jifa da jakata akan gado kafin nabi bayanta nima na kwanta a rigingine ina tariyo abinda ya faru a makaranta ranar.

Vibrating din da wayata ya dauka daga cikin jakata ne ya dawo dani cikin hankalina, na danyi tsaki lokacin da nake laluben wayar, da kyar na iya bude idanuna da suka fara min nauyi saboda gajiya da barci na dora su akan fuskar wayar, sunan dana gani yana bouncing a jikin screen din wayar ne yasa naji zuciyata ta fara daka tsalle cikin wani irin farin ciki. Ya Allah! Yaushe rabona da inji muryar Abbu a rayuwa har na manta, Kun ganni nan kullum ina cikin page dinshi a facebook ina bibiyar rayuwar shi amma na kasa samun kwarin gwiwar kiran shi duk da cewa nayi kewar shi kuwa fiye da tsammanin mai karatu. Ganin kiran yana shirin katsewa yasa nayi saurin dagawa, sallama na mishi a nutse kuma cikin Karya murya, ya amsa cikin wannan muryar tashi cike da kasaita da wani irin huskiness daya kusa saka ni narkewa akan katifata saboda yadda naji wani electricity yana yawo a magudanar jini na. Daga can naji yana magana wadda tayi sanadiyar dawo dani duniyar Earth daga tafiyar da nayi zuwa Mars, cewa yayi "wato Nafeesah idan shekara zamu dauka ba tare da mun gaisa ba hakan bai dame ki ba koh? Ba kya neman mutane idan ba neman ki aka yi ba koh?" da sauri nace "Abbu ba haka bane ba fa!" yayi wata irin sassanyar dariya, "to ya ne Nafeesah?" na dan sosa wuyana tare da dan gyara muryata ina kokarin boye yadda dariyar Abbu ta kassara min gabbai, nace "Abbu muna karatu ne kuma dai bana so in kira ka ko kana aiki ko wani abu in takura ka" 'ina tsoron ka gaji dani, ina tsoron yin sabo da abinda zai zo yayi hurting dina daga baya" yace "that's not an excuse Nafeesah, when you feel like calling me just don't hesitate and call, zan amsa a duk inda nake no matter what m doing" na gyada kai kamar yana ganina nace "toh Abbu" ya sauya akalar hirar zuwa ta harkar karatuna, mun dauki lokaci muna hira kafin yace "Jiya muka dawo daga Beijing, nayo miki lodin tsarabar

Please Login or Register in order to submit comment