Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk da cewa bai fara fita ba, kuma har zuwa lokacin Tafiyar shi bata koma irin ta normal people ba. Cikin wannan lokacin mun ga jama'ah ba kadan ba, ko wace rana sai mun ga bakin fuska cikin masu zuwa duba shi gaskiya Abbu yana da jama'ah sosai. Saurayin Ni'ima zai kawo mata ziyara ranar alhamis, ranar a lab muka wuni tare dasu suna jira mu tashi su wuce gidan su dani, na gaya musu Abbu ya hana ni yawo amma ina! Suka ce they wouldn't take no for an answer, dole suka saka ni kiran shi. Na fita daga cikin lab din bayan na danna mishi kira, bugawa daya biyu ya dauka ana uku, a sanyaye na gaida shi tare da tambayar jikinshi ya amsa da lafiya, nayi shiru ina kamo bakin zaren daga inda zan mishi maganar har sai daya tambaye ni ya? Sannan na gaya mishi kamar wadda take tsoron tayi maganar, shiru ya biyo baya kafin ajiyar numfashi mai nauyi, "amma kada ki wuce karfe bakwai baki dawo ba" da sauri nace "in shaa Allahu Abbu" daga nan muka yi sallama. Ranar tun kafin lokacin tashin mu yayi muka tafi. Unguwar Galadanchi muka nufa, ashe mahaifin su shi yake rike da sarautar Galadanchi ta garin Kano, babban gida ne wanda ginin shi na asalin gidajen sarauta ne, sashen Hajiya Fati muka fara shiga ita ce mace ta biyu a gidan, mace mai karimci ta tarbe mu da faraarta, na kula su Ni'ima kamar babbar Yaya suka dauketa don a sashenta ma suka ce zasu saukar da Bashir din. Cike da girmamawa na gaidata ta amsa da fara'ar ta tare da sawa aka kawo mana ruwa, mun dan jima a sashen nata kafin muka mata sallama muka wuce sashen Hajiya Siyama mahaifiyar su Abbu. Sashen nata in ka shiga baka taba cewa dakin er dattijuwa ka shiga duk da cewa shima sashen Hajiya Fati babu laifi. Babban falo ne wanda yasha saitin royal kujeru ruwan zuma, muka zube a kan wani tattausan carpet muna gaishe ta tana zaune akan sallaya tana lazumi, kana ganin kamilalliyar fuskarta zaka san cewa ka kalli fuskar ma'abociyar addini, babu abinda Abbu ya baro nata sai dogon siririn hancinshi, ita nata yana da dan fadi, sai data gama lazuminta kafin ta amsa mana cike da kulawa. Daga nan su Ni'ima suka jani muka je dakin su muka yi sallah, kayan jikina na canza muka shiga kicin muka fara shirya kayan abinci kala kala. Na bata shawarar mu yi snacks wanda zamu basu a matsayin tsaraba idan zasu tafi gobe, don haka muka yi doughnuts wanda muka yi icing dinshi muka watsa shredded cheese da chocolate akai. Karfe biyar suka karaso shi da abokin shi, mun riga mun kai komi sashen Hajiya Fati, mun shirya koina sai kamshi kawai dake tashi a wajen. Ita uwar gida ta musu rakiya zuwa inda aka tanadar musu mu kuma muka tsaya karasa gyara kicin din, sai da muka gama gyaran jikinmu sannan muka je muka gaisa dasu. Bashir din nata kamar yanda take fada dan kyakkyawa dashi ga barkwanci, abokin nashi ne ma bai mun ba ko kadan, sai wani shisshige min yake yi yana jana da hira duk ya takura min don haka na mike nace musu zan wuce gida, duk suka kalleni da mamaki ni kuwa Na Kauda kaina gefe don ma kar suga fuskar hana ni tafiya. Sa'adiya ta taso ta kama hannuna muka fita, abokin Bashir da naji yana kira da Fahad ya taso ya biyo mu, ganin babu fuska yasa ya juya. Na saki tsaki kasa kasa, Sa'adiya tayi dariya tace da alamun gayen bai miki ba, kai kawai na girgiza mata muka wuce sashen Hajiya Siyama. Tana kan daya daga cikin kujerun falon tana kallon tashar Saudi, ta kalle mu cike da mamaki, "lafiya dai ko?" Sa'adiya tace "wai gida tace zata wuce!" tace Haba ai kin tsaya kici abinci koh?" nace "Hajiya Abbu...." tayi saurin katse ni, "kyale shi kawai, ba zaki tafi ba sai kinci abinci fa" bani da zabi dole na wuce dakin su Ni'ima don bazan iya komawa wajen su nataccen abokin Bashir ba kuma bazan iya zama kusa da Hajiyar ba.

Sai wajen karfe bakwai da rabi sannan muka fito ni da direban da xai maida ni gida, bayan naci tuwon tsakin masara da miyar kalkashi wadda taji yajin daddawa, tantakwashi da man shanu ga kunun aya mai sanyi da Gardi a gefe. Tare dasu Ni'ima muka ci abincin bayan Tafiyar su Bashir, ta bude tarkacen kayan tsarabar daya kawo mata ta ciro min kayan shafa, turare ne da kayan makulashe naki amsa, sai da suka yi kamar zasu yi fushi sannan na saka hannu na dauko turaren 'splendid' tsohon turarena ne tun a secondary school, daga baya ya bata na gaji da nema na komawa kamfanin lily cool, Sa'adiya ta kara min da tarkacen sweets muka fita falo. Kicin na shiga na dauko doughnuts din dana debar wa su Hafsy, Hajiya na falon a zaune na durkusa a kusa da ita na mata sallama, ta min godiya sosai har sai dana ji kamar in nutse a kasa. Ta mikawa Ni'ima wata karamar silver grey din jaka tace ta bani, na mata godiya sosai kafin muka tashi, sai da muka je ta sashen Hajiya Fati na mata sallama kafin muka fita waje inda direba yake jira na, na shiga motar muka kara yin sallama dasu kafin muka tafi. Nayi shiru a bayan mota ina tunanin abinda zan fadawa Abbu, a raina addua nake ina karawa akan kada Allah yasa yayi fushi dani, naki jinin fushin Abbu kamar yadda na tsani bacin ranshi. Har cikin gida direba ya shiga dani, na fito daga motar ina mishi godiya tare da sai da safe, iska ake yi sosai kamar ta dauki mutum tayi yawo dashi, idanuna a rufe saboda kasar da iskar guguwa ta watsa min na shiga falon bakina dauke da addu'ar da ake yi idan guguwa ta tashi, kamar hadin baki ina shiga aka dauke wuta. Na bude idanuna da kyar ina murza su, kafin inyi adjusting da dan guntun hasken falon wanda ya ratso ta cikin shara-sharan labulayen dakin daga farfajiyar gidan wanda lantarkin solar ta samo dashi, naji kafana tayi stepping akan wani abu mai tsananin sul6i, kafin in tantance meye naji ni na fara tafiya sululuuuu.....!! A tsakiyar dakin, na kwala ihu sosai ina salati tare da laluben abinda zan kama in rike tunanin farko daya fado min a cikin raina shine hango ni da nayi na kai da bakina, kyawawan kananun hakora na guda biyu na gaba malale a cikin jinin dake fita daga bakina....... Karo na kaiwa wasu hard muscled chest wadanda ko a cikin duniyar mafarkina ban taba hangoni a kansu ba, sai ga gangar jikina a jikinsu yau kamar a mafarki, dogayen tausasan hannuwa suka zagaye bayana, daya a kuguna daya a gadon bayana, jikina yake dauki rawa kamar wadda ta rungumi kankara cikin hunturun sanyi yayin da naji wasu dogayen zara-zaran yatsu suna suna tapping din gadon bayana a hankali., ban san lokacin dana saki ledojin hannuna, purse dina da wayata akan tiles din dake cikin falon ba.....!!.





*♡Jeedderh♡*
[12/8, 7:36 PM] ‪+234 813 546 1890‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*16*

*-Search across the Oceans for who are been lost for two long......*
*'Searching for a secret in coming home we find we have what we need.....!'*
*-New Empire-* _Across the Ocean_

Hankalina gabadaya ya dauke daga jikina, babu abinda nake fahimta sai tattausan kamshin dake fita daga jikin Abbu, bugawar da zuciyar shi take yi da dan sauri-sauri, dumin dake fita daga jikinshi....... Ya dago fuskata daga jikinshi yana kallona kamar hadin baki, aka dawo da wuta lokacin. Na samu kaina starring at his brown oily eyes da suke wani irin sheki kamar zaiba, "Nafee, are you ok??" cikin daukewar tunani na daga baki nace "umh???" ba tare dana yi kokarin dauke idanuna daga kanshi ba, ya dan jijjiga kafadata, "hey!" kamar wadda aka daddaba daga barci, nayi firgigit ina kallon cikin falon, Ya Allahu! What the heck just happened?? Da sauri na durkusa na tattara kayana da suka zube nayi hanyar dakina a sukwane, da sauri ya riko tsintsiyar hannuna, nayi cik ina sauraren abinda zai ce ba tare dana juya na kalleshi ba, "lafiyar ki kuwa Nafeesah?" da sauri na gyada kaina, "lafiya lau, kayi hakuri dan Allah" ina jin sautin murmushin daya saki, ya sakar min hannu dama abinda nake jira kenan don haka na bazama dakina a sukwane. Kofar dakin na maida na rufe tare da murza key, nayi wuri-wuri a tsakiyar dakin kamar wadda take neman wajen buya kafin na zube a kasan dakin akan gwiwa na, zuciyana wani irin gudu take yi, na rasa abinda yake min dadi a lokacin. Ban san iya lokacin dana dauka a wajen ina zaune ba, tare da taimakon Innalillahi.... Dana dinga ja na dan samu sukuni a cikin raina, tashi nayi na fara bandaki na watsa ruwa mai sanyi a jikina duk da sanyin da ake yi sakamakon iskan da aka gama yi. Na fito daure da tawul a jikina na tsaya a gaban mirror, lotion na shafa na saka rigar barci wadda ta tsaya min a gwiwa, duk abinnan da nake yi idanun Abbu suna cikin memory na, na rasa abinda zan yi da zai dauke min tunaninshi daga cikin raina, chatting! Zuciyata ta tuna min, da sauri na tafi inda nayi jifa da kayan hannuna tare da wayar na dauko ta, ina daga ta na dan saki kara ganin yadda screen dinta ya tsattsage, na ciza tattausan lebena na kasa ina ji kamar in dora hannu aka in saki ihu saboda yadda nake son wayata dinnan, bana so ko datti ya hau kanta. Ganin chatting din ma bai mun abinda nake so ba yasa na janyo system dina na kunna na fara kallon Baywatch, ajiyar zuciya na dan saki ganin hankalina ya dauke zuwa ga film din.


Sai Washegari na ba su Hafsy doughnut din dana kawo musu, tare dasu ma muka cinye shi a cikin mota. Yau Daddy da kanshi yazo daukata, yazo duba jikin Abbu ne. Sai da aka yi sallar la'asar muka wuce Kaduna, bakin daddy bai yi shiru ba a hanya yana ta bani labarin kirki da mutunci irin na Abbu, bai san cewa yanzu bana cikin mood din sauraren labarin Abbu bane, ko sunan Abbu aka ambata sai naji faduwar gaba, shi yasa yau nayi duk kokarin da zanyi wajen ganin na kaucewa haduwa dashi, nayi, sai dai dole sai da na ganshi lokacin da muke mishi sallama ni da daddy. Kaina na jinginar da jikin seats din da nake kai na lumshe idanuna kamar mai barci, hakan yasa daddy ya kama bakinshi ya bame har muka isa Kaduna.

Da dare Ni'ima ta kira ni, bayan mun gaisa take fada min wai Fahad dinnan ne abokin Bashir ya dame ta akan ta bashi number na, na tabe baki nace "kada kiyi kuskure bashi Ni'ima" tace me yasa? Nace ban gane ba? Waye a cikin ku bai san cewa Akwai wanda nake dating ba? Taja tsaki, dallah dating ko crushing?? Waye bai san cewa crushing din Muneer kike yi shi baya son ki ba?? Na dan dakata kadan kafin inyi magana, "Ramlah mai bakin Aku!! Ita ta fada muku koh?" daga can tace that doesn't matter ko kadan ai, ni ai zan bashi number! Nace cikin gatse, "ki bashi din toh, zaki gani ne" na katse wayar tare da jifa da ita akan gado. Muneer!! Na maimaita sunan, it's kinda strange. Rana bata taba fita ta koma ga ubangijinta ba ba tare dana tunana bawan Allahn nan a cikin raina ba, amma har ga Allah yau dai, yau gabadaya na manta da existing dinshi a duniya, Anya lafiya ta lau kuwa??! Tashi nayi na koma falo wajen su daddy muka sha hirar mu, sai dana fara hamma sannan na musu sallama na wuce dakina.

Da safe na ba daddy waya na nace a canza min screen din, Koda ya tambaye ni dalilin tsagewar ta cewa nayi faduwa tayi, to me zan ce mishi? Kafin azuhur sai gashi da sabuwar Samsung edge plus, nayi tsalle, nayi ihu na rungume shi, wayar da nake masifar so kenan sai dai bana so in takurawa iyayena da zancen wayar da nasan kudin abincin wani na shekara daya ne, shi yasa nayi shiru, sai gashi yau Allah ya bani ba tare dana roka ba. Daddy kam yasha addu'a ranar kamar bakina zai tsinke, haka nake ni kam, idan aka min kyauta sai in wuni ina wa mutum godiya. Mommy na cewa ta bada ayi fura don na kula Abbu yana so sosai, duk ranar dana kai fura ranar ita ce abincin shi har ta kare. Washegari na doshi hanyar Kano cike da tsaraba don sai da muka shiga shago na saiwa Hafsy dasu Qaseem sannan muka wuce, cike kuma da wani longing, longing to see someone wanda na ma rasa a wane matsayi zan ajiye shi cikin raina., abokin Babana ko kuwa Abokin Rayuwata??!


Aunty Mubeenah da wata kanwarta Shakirah kadai na taras a gidan, ina ga Abbu ya fita zagaya unguwa kamar yadda yake yi lokaci zuwa lokaci da er sandar taimaka tafiya, na durkusa na gaida su, Anty Shakirah ta mun sannu da zuwa har tana tsokanata da ina tsarabar ta tunda Allah yasa tana nan nazo. Matar tana da kirki, duk tafi sauran en uwan Anty Mubeenah da suke zuwa gidan, wasu idan suka zo ko kallon mutane basa yi balle su amsa gaisuwar su, wasu kuwa kallon mutane suke yi kamar kiyashi shi yasa nima bana kula da kurar data debe su. Dariya na dinga yi tana tsokanata, na ciro chocolate din kit-kat babba na bata nace ta kaiwa yara, na ciro wani hadadden turaren wuta na asalin en maiduguri na ba Anty Mubeenah inji Mommy na, ta amsa babu yabo babu fallasa, babu godiya ba komi kamar wadda ta bani ajiya, naji haushin abun ba kadan ba, na mike daga zaunen da nake na dauki jakar hannuna na wuce dakina. Kayayyakina na ciro na shirya komi a inda ya dace, na ciro fura da nonon da aka wa Abbu na Kai fridge na ajiye, daga kicin ina jiyo hirar dasu Anty Shakirah suke yi saboda a falo na biyu suke wanda yafi kusa da kicin din, Anty Shakirah ce take tambayar Anty Mubeenah mai yasa bata son turaren? Tace to mai zanyi dashi? Idan baki so ki bani ai ban rasa wanda zan ba bane, da sauri naji tace ina so wallahi, turaren ne yana da tsada naga gashi yana da wahalar samu shi yasa! Nayi kwafa ina girgiza kaina, wato kyauta ma tayi da turaren wutar da babu yadda ban yi da mommy akan ta bani in kaiwa Anty Haleemah ba mommyn taki ita ala dole sai ita, to ga abinda ya faru nan ai!. Dakina na koma cike da takaici ban jima da shiga ba naji hayaniyar su Hafsy a falo, da sauri na fita. Suna gani na suka kwashi ihun murna duk suka rugo, kowannen su so yake ya rungume ni, ni kam dariya kawai nake ina ihun su sake ni daga cakumar da suka kin kar su kayar dani amma ina! Sai da suka gaji dan kansu sannan suka sake ni, Abbu yana bayansu ya jingina bayan shi da kujera yana kallonmu cikin murmushi, da sauri na zube a kasa ina gaida shi, can kasan zuciya ta wani irin farin ciki yake mintsini na. Yaran naja muka tafi dakina tun kafin inyi abinda zan zo ina dana sani don wani sashen na zuciyata wai rada min inje in rungume shi yake yi. A daki na baza musu tsarabar dana kai musu, nan muka baje muka ci wasu a gun wasu kuma suka diba suka tafi daki lokacin da aka kira Magriba, ni da Hafsy kuma muka yi tamu a daki.

Muna gama dinner na mike da niyar inje in kwanta, Abbu ya kalleni yace "Nafeesah Akwai fura ne?" na gyada kaina a hankali, wata irin kasala ta rufar min saboda yadda ya kira sunana, yace dama min pls. Na wuce kicin na dama mishi furar, nasa ayaba lokacin da nake damawa dana gama kuma na watsa kankara a ciki na dauki bowl din dana juye furar a cikin na koma falo, yana sec parlour a kishingide akan kujera da alamu waya yake amsawa, cikin harshen turanci yake wayar. Na ajiye a gabanshi na fara kokarin zubawa a cikin cup ina satar kallonshi, wayar yake amsawa cike da wata irin yanga yana yi yana wani lumshe ido, accent din turancin shi ko kadan bai yi kama dana bahaushe ba, idan kana ji sai kayi zaton ko rainon kasar Ingila ne, to waya sani? Naji ance a LA ya kammala digiri dinshi na farko. Na danyi murmushi ina girgiza kai, sau tari ina mamakin yadda Abbu yake da yanga kamar wata mace, zaka iya mistaking kace yanga ce kam idan baka zauna dashi ba don a zahirin gaskiya haka yake naturally. Ya ajiye wayar hannunshi akan kujerar yana zama sosai, "what's funny?" da sauri na girgiza kaina "ba komi?" na mika mishi cup din, ya kura min idanu kamar yana so ya karanci abinda ya saka ni murmushin da kanshi, nayi kasa da kaina, ina jin sighing din daya saki kafin ya amshi cup din, da sauri nayi niyar tashi ya tsayar dani ta hanyar tambayana ya Daddy na? Nan fa na zauna na fara zuba mishi labari har na wayar da daddy na ya canza min, ya daga girarshi yana dan murmushi, "inye! Her daddy's girl!!" na sadda kaina kasa ina murmushi in ma zan iya cewa kila har da blushing, ya jefo min tambayar data kada min ciki, "garin yaya har screen din wayarki ya fashe?" na yi wuki-wuki da idanu kamar wadda aka kama tayi karya, ya sake tambayana, kafin in lalubo abinda zan ce wayar shi tayi kara, yana dauka na lallaba na mike da sauri sai dakina. Ina shiga na ajiye numfashi da karfi, Allah ya cece ni yau. Kayan barci na saka, na dauko log book dina na bude na dan dudduba kafin na janyo system dina na cigaba da kallon Pinocchio dana fara yi. Wajen karfe tara da rabi naji wayana tayi kara, na daga ganin bakuwar number yasa na daga da sallamata, daga can wata familiar murya ta amsa sallamar tare da karawa da "gorgeous!" cike da mamaki nace "waye?" sai dana kusa dakin zagi lokacin da naji yace "Fahad ne, abokin Bashir Saurayin Ni'ima" na hade fuska kamar yana gani na, jin nayi shiru yasa yace "gorgeous, baki gane ni bane?" a raina nayi exclamin kalmar 'wai gorgeous!' cike da jin haushi nace na gane ka mana, and please suna na Nafeesah ne ba wani abu wai gorgeous ba ka gane!" ya saki wata dariya data kara kular dani, "Haba gorgeous! To me kin cancanci abinda yafi wannan sunan ma. Kawai ki bani dama in nuna miki how precious you are to me, wallahi tun ranar dana saka ki a idanuna naji cewa na samu macen dana dade ina nema a rayuwata, tun daga ranar na baki wani matsayi mai girma a cikin raina, Gorgeous, wallahi u've become a very special part of my being, you are my happiness, you've got everything I need from my wife you are classy, beautiful, hafiza.....!!" blah-blah-blah ya shiga jero labarai har na gaji da saurare, ganin yaki dasa aya yasa na tsaida shi, "please Malam! Ita wadda ta baka number dina bata yi maka bayanin ina da Mijin aure bane?" ya kara sakin dariya, "ta dai fada min cewa kina da wanda kike so and unfortunately though to my relief baya sonki in return, baby just leave him, bai san ciwonki ba. I promise you zan so ki fiye da yadda yake sonki, na miki alkawarin mantar dake cewa kin so gayen can baby, just give me a chance kinji?" ni kam ina baki? Zuciyata cike da takaicin tonon sililin da Ni'ima ta min. Da kyar na saisaita kaina daga ihun da nake ji a cikin kaina na son in sossoka mishi zagi na dai yi kokari nayi calming din kaina, after all ai ba laifin shi bane, zamu gauraya da mai laifin. Duk da haka ban iya tsaida tsakin daya fito min ba, nace "Malam I don't need your love or whatever trash you are talking about ka gane? Don Allah Kar ka sake kira na!" na kashe wayar da sauri. Ni'ima na kira, cikin sa'a ta dauka a ringing din farko, ko sallama ban bari tayi ba na fara zazzaga mata ruwan masifa, daga farko hakuri ta fara bani, daga kuma sai ta fara tsokanata wai akan ta ma taimake ni? Nace taimakon ki din banza? Nace miki ina so ne? Tace baki fada ba, zuciyar ki ta fada min. Ganin ta maida abun wasa na kashe wayar ina kara maimaita mata ta kira Fahad ne koma uban waye sunan shi ta gaya mishi kada ya sake kiran wayata don duk ranar daya kuma sai naci Mutuncin shi, ita kuma ta jirayi haduwar mu gobe!! Tace "Allah ya kaimu" cike da izgilanci, na kashe wayar ina kwafa. Ajiyar zuciya nake saukewa cike da takaici kamar zan hadiyi zuciyata in mutu. Karan wayata naji, da sauri na wawuri wayar ina tunanin kalar zagin da zan narka, ganin sunan Mommy ne yasa na dan saki fuskata kafin na dauka, gaisawa muka yi ta tambaye ni na sauka lafiya? Na amsa mata da lafiya lau. Mun danyi hira da ita kafin muka yi sallama, na dora wayar akan bedside drawer ni kuma na kwanta bayan nayi dimming din wutar dakin.




*♡Jeedderh♡*

[12/8, 12:46 PM] ‪+234 810 910 7052‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*17*

*HADITH*
Abdullah bin `Amr bin Al-`as (May Allah be pleased with them) reported: A man asked the Messenger of Allah (PBUH): "Which act in Islam is the best?'' He (PBUH) replied, "To give food, and to greet everyone, whether you know or you do not.''
[Al-Bukhari and Muslim].

Washegari kam su Ramlah sun ga tsiya a lab, Tunda muka zo na samu gefe daya na zauna fuskana a cune, ban mata magana ba balle sauran en lab din, su Ni'ima ma Suka zo naki kallon inda suke, ina ji suna tambayar Ramlah meke damuna ne tace itama tunda taxo a haka ta same ni. Har muka tashi a ranar ban kalli inda suke ba, sunyi maganar sunyi tsokanar duk a banza. Muna fita na fara kokarin wuce su, Ramlah tayi saurin tare ni tana harara ta, "wai ke dallah malama meye kike wani yazga mutane tun dazu?" nima na harareta, nace "ban sani ba dallah bani hanya!" Ni'ima ta matso tace "in dai akan zancen Fahad ne don Allah kiyi hakuri, wallahi dana san

Please Login or Register in order to submit comment