Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

UWAR MUGU-01

Daga Littattafan Nazir Adam Salih.

*KIBIYAR AJALI*
*ME YAFI KUDI*
*TA LEKO TA KOMA*
*BIRNIN SARAUNIYA*
*MUTUWAR KASKO*
*NAIRA DA KWABO*
*ACI BULUS*
*ALAKAKAI*
*WA NA KAMA*
*HINDU*
*RUHINA*
*DARE DA RANA*
*KARYA LINZAMIN SHAIDAN*
*CUTA TA DAU CUTA*
*ISKA MAI KADA RUWA*
*BINDIGAR KWALI*
*DAMISAR TAKARDA*
*AZIZA*
*TSOHON ALKAWARI*
*KAI DA JINI*
*ALJANI YA TAKA WUTA*
*KUDI DA MACIJI*
*KISAN BOKO*
*KURA DA KAN RAGO*
*MURMUSHIN ALKAWARI*
*ZAYYANA*
*ZABIYA*
*MUGUN JI*

DON ABOKINA
Engr Auwal Sani Kabo.

UWAR MUGU
Copyright © Nazir Adam Salih 2010
Hakkin Mallaka (h) Nazir Adam Salih 2010

TARIHIN DABA'INSA
An fara Buga shi a Kamnas Publishers Dakata
Kano A shekarar 2010

GARGADI
Ba'a yarda wata kungiya ba ko wani mutum ya juya wani bangare na wannan littafin ta hanyar wasan kwaikwayo da majigi ko kuma wani abu daban saida tabbataccen izinin marubucin.

ADIRESHI
Abubakar Saddik Islamiyya Dakata Kano.
Akwatin Gidan Waya 4792.

UWAR MUGU
Nazir Adam Salih
(Nas)

BABI NA DAYA
ALIYA na zukar sigarin dake hannunta saita dafe makogoro cikin kaduwa sannan tafara tari kufur kufur nan da nan jikinta ya dauki rawa. Cikin sauri ta fice daga da'irar yan matan dake gaban makadin takoma can gefe guda sannan tafara nazarin su daya bayan daya tana mai addu'ar Allah yasa dai babu wanda ya lura da ita ballantana ma har ace tayi abin kunya ita dai ta sha fadi cikin zuciyarta cewa wannan abu ba dadinsa take ji ba mutum yayi ta hurawa cikinsa hayaƙi makoshinsa ya shake kamar zaka mutu amma don masifa sai an sha tunda yazama al'adar duk wata karuwa dake gurin abin kunya ne a ganki ma baki iya busa hayaƙi sama ba don haka wannan gudun abin kunyar shiyasa Aliya tafara busa hayaƙi sama amma ba wai don tana so ba.

Aliya ta tofar da yawu sannan tayi jifa da guntuwar tabar dake hannunta gamida ajiyar zuciya daga inda take tsaye tana iya hangen samari da yan mata dakuma dattijai masu budurwar zuciya sunata cashewa agaban DAN INDO wani dattijo dan duniya sanye da katon wando buje da dogon gemu kamar saman jinka ga tarin gashin baki kamar ciyawa yana tsakiya da mataji a hannunsa ana kida yana rawa lokaci guda kuma yana taje gemunsa da matajin yan duniya na ta watsi da Nairori a kansa kai ka rantse da Allah babu sauran talauci acikin kasa.

Mafi yawan daga cikin matan sanye suke da kaya iri daya sunyi Asin-da-Asin musamman don wannan ajo na FATI ZAFI ZAFI yan tsirarin karuwai masu rangwamen gata da wadanda ta karewa sune kawai suka fita zakka a cikinsu harda Aliya duk kuwa da cewa tafi duk wata karuwa dake gurin kyawun sura nesa ba kusa ba amma halayyar na tayi-da-fasawa ita ta ja mata shiga halin bakin talauci a halin yanzu talaucin daya hana mata ankon ajon kawarsu fati zafi-zafi.

Aliya ta dubi agogon kan fuskar wayar dake hannunta karfe biyu saura na dare. Adaidai lokacin ne dan indo yafara hada kayansa da komotsansa yan duniya suka fara kama gabansu suna shiga cikin garin TAFA domin cigaba da cin kasuwar dare.

Wannan shagali anyi shine cikin wani katon fili na wasan kwallo kafa dake bayan garin Tafa. Tun farko ita fati zafi zafi wadda ta shirya bikin ajon domin tara masu gidan rana bahaka taso ba taso ne ace acikin farfajiyar wata kayatacciyar otal aka yi bikin to amma sa'ar data lalubi aljihunta taji babu tudu saita ga batada zabi illa ta tara mutane a cikin katon filin a cashe akalla dai tayi imani ko mai zaije yadawo sai ta sami RIBA.

Daga filin kwallon kafan idan ka dubi bangaren kudu babu komai sai tarin bishiyoyi da kuma ciyayi gamida wani tsohon gidan mai wanda ya jima a rufe ba'a sayar da komai acikinsa sai beraye ne ke ta gada aciki.

Adab da inda wannan gidan mai a tsugunne yayi tagumi sanye d kaya dukun dukun kamar anyi barin mota dashi wani saurayi ne ya zurawa dandalin bikin idanu yana kallon jifa jifan mata da maza nan da can ana ta hira ana karawa sararin samaniya hazo.

Wannan saurayi yafi sa'o'i shida zaune agurin yayi zuru kamar mujiya yana kallon duk shagalin dake faruwa agurin dayawa daga cikin yan duniyar dake kai kawo a filin sun dauke shi ne amatsayin tababbe.

Tsakanin inda saurayin dake tsugunne zuwa inda Aliya take tsaye baifi taku goma ba.
Aliya ta dubi saurayin dake tsugunne agurin kana ta dauke kai cikin tausayi a zuciyar ta tana cewa.
Mutane dai basuda kirki gashi dai kyakkyawa da kuruciyarsa amma sai da aka samu wani marar imani ya haukata shi Aliya tayiwa kanta murmushi adaidai lokacin da wasu kawayen ta suka nufo inda take ta sake duban saurayin ta dauke kai.
Yanzu haka shaye shaye ne tace da kanta adaidai lokacin da su LARABA suka karaso inda take.

Laraba na karasowa saita dubi Aliya a yatsine
Kedai wallahi kinji kunya Shikenan don kawai bakiyi dinkin anko ba sai ki wani koma gefe kamar wata marainiya?

Aliya ta Harare ta.
Ke banza bakya ganin gurin ya cushe da kyar ake numfashi shiyasa na koma gefe na sha iska.

ASABE ta fashe da dariya shegiya Aliya akwai ki da iya kwana kamar mota to meye in baki yi anko ba akanki aka fara?

Aliya ta tafa hannu tace oh Ni Aliya na shiga uku to wai ina ruwan ku ne? Zan fa ci uban yarinya Wallahi ta dube su a fusace.

Laraba ta fashe da dariya Haba ƙawata ke baki san wasa bane?

Toh Ai ku ne da abin haushi Aliya tace sannan ta sake duban agogon dake wayarta

Laraba ta turo dankwalin ta gaban goshi sannan ta lalubi aljihu jakarta ta dauko karan taba ta cinna masa wuta ta busa hayakin sama kana ta dubi Aliya tace.

Kai gaskiya zafi zafi ta sami kudi yau anya kuwa ni ma ba ajon nan zan shirya ba.?

Kin rigani afili na riga ki a zuciya kinga yanda shegen nan alhaji DAN ABU yayi ta lika mata yan dubu dubu? Yafa taba nemana amma saboda yanzu yaga sabuwar fuska sabon jini ko kallo ban ishe shi ba. Asabe tace tana zazzare idanu.
Laraba ta Busa hayaƙi sama tabi shi da kallo.

Kedai abar tone tone kawai Amma in wannan ne Nima yataba nemana kuma har......UWAR MUGU-02

Kedai abar tone tone kawai Amma in wannan ne Nima yataba nemana kuma har... Tayi shiru bata karasa ba sa'ar data ji motsi abayansu cikin sauri ta juya sannan ta rike numfashi Sa'ar data ga saurayin nan dukun dukun tsugunne abayansu.
Laraba ta dube shi a wulakance ta tabe baki tace

Oh Ni Laraba nashige su!
Wannan kuma wanene kamar an tono shi daga kabari?
Asabe da Aliya suka juya lokaci guda suka dubi saurayin

Asabe ta tabe baki... Wayasan masa uban naci tun magariba yake nan yana rarraba idanu kamar dillalin kaji dube shi dukun-dukun wannan in ba asararriya ba wacce karuwa ce zata kula shi? Ta tsartar da yawu.

Laraba ta dube ta tace kika sani ko.... Tayi shiru sannan lokaci guda ta juya a tsorace sa'ar data ji ana ja mata riga ta baya.

Mutumin nan ne a tsaye a bayanta.

Yan matan..... Don Allah acikin ku wata ta taimaka min mana da dan abinci da gurin kwana kafin safiya.

Kawar Laraba ta Harare shi ta daka masa tsawa tace Kai! Kada ka dauki karuwa yar iska mana bayan tanada sana'a. An fada ma a caca aka ciyo mu da zamu dauke ka haka dukun dukun mu kai ka har daki ina abin yake wai maye yaci jariri. Ta zare masa idanu malam don Allah kama gabanka wannan ai sai ka sa a raina mu.
Ta juya sannan takama hannun Laraba tace zo mu tafi kawata kada wannan yasa jinina ya hau.
Suka juya suka fara tafiya sannan ne Laraba ta sake juyowa ta dubi Aliya cikin mamakin ganin ta tsaya bata biyo su ba.

Aliya.... Zo mu tafi mana
Aliya ta girgiza kai kuje Ina zuwa ni sai anjima zan karaso.

To Wallahi kidai bi ahankali kada wannan dan dukununun ya sure ki ta fashe da dariya sannan ta rataya hannunta a kafadar Laraba suka bace acikin duhun daren.

Aliya tayi ajiyar zuciya bayan sun bar gurin sannan ta sake nazarin katon filin da aka gana cashewa babu kowa a filin duk jama'ar sun watse sai yan daidaiku acikin duhun tareda Masoyan su suna kuskus.

Aliya ta juya ahankali ta dubi saurayin dake bayanta adaidai lokacin da wani mai tsohon mashin yazo wucewa ta kusa dasu. Aliya tayi nazarin fuskar saurayin na yan dakiku acikin hasken fitilar mashin din daya gifta taji gabanta yafadi ras meke damuna ne? Ta tambayi kanta tabbas Kodai tasan saurayin awani waje kokuma tasan wani mai kama dashi.

Aliya ta sake nazarin saurayin akaro na biyu sannan ne to ta fahimci abunda yasa gabanta faduwa da'ace bata riga taga gawarsa ba kafin a binne shi da babu Abunda zai hanata cewa saurayin dake tsaye yayanta ne AMADU ba duk dayake akwai duhun dare sai da kamar ta bayyana karara kamar su daya sak Haba gaskiya fa Naji gabana ya fadi ta sake fadi cikin zuciyarta. Acikin dan takin lokacin da taga fuskarsa cikin hasken fitilar mashin din daya gifta ta lura yana cikin tashin hankali domin taso ta ga wani abu mai kama da hawaye ko kuma busashshen jini a gefen fuskar sa wannan shiyasa har ta juya zata bi bayansu Laraba saita tsaya ta sake juyowa ta dubi saurayin kana ta matsa kusa dashi kadan a tsorace.

Sannu... Malam....
Saurayin yayi mata murmushin yake yauwa Sannun ki dai ya dan yi shiru sannan saiya dubeta yace bakya tsoron zan iya cutar dake kika tsaya dani ke kadai?

******* ******** ******** ******** ***********

Tsawon lokaci Aliya na tsaye tana dubansa a tsorace cikinta ya duri ruwa a zuciyarta tana cewa yau na gamu da gamona karambani na ya janyo min da nasani dana bi su Laraba sannan sai ta Dake zuciyarta ta dube shi cikin duhun daren tace don ne zanji tsoro kana mutum ba dodo ba?

Saurayin ya saki wata shakakkiyar dariya irinta wanda ya sha wahala yace. An gaishe ki mace mai kamar maza... Na dauka ai zakiji tsorona kokuma ki raina ni kamar yadda yan uwanki sukayi min ya dan yi shiru yana dubanta.

Kasan kowa da irin tunaninsa nasu tunanin kenan ta gyara tsayuwa tana dubansa hakane.

Ya sake yin murmushi yana kallon ta sannan sai yayi kasa kasa da murya yace idan zaki iya zan so ki taimaka min da dan abinci... In kuma da hali harda makwanci kafin gari ya waye nayi gaba don wallahi ina cikin matsala kanwata.. Kinsan in ba dole ba babu abunda zaisa na nemi irin wannan taimako.
Ya shafi fuskarsa da tafin hannunsa na dama yaci gaba da kallon ta yana jiran yaji abunda zata ce.

Aliya ta shiga rudani abinda yace ya jefa zuciyarta cikin wasi wasi tariga tasani ba karamin ganganci bane ta dauki mutum irin wannan dukun dukun dashi takai shi dakinta cikin wannan uban daren duk da dai cewa tasha saukar mutane iri daban daban abaya to amma su sunada kyawun gani ba kamar wannan ba dake gabanta amma duk da haka lokacin da ta sake dubansa sai taga bazata iya juya masa baya ba domin kamar ta isa sak kamar MARIGAYI AMADU.

In kuma kina ganin da takura to ki bari kawai KANWATA.... Bana son matsalata ta shafe ki... Nagode da tsayawar ma da kikayi har kika saurare ni yayi mata murmushin yake.

Wannan shiyasa Aliya ta dube shi sannan ta girgiza kai tace BAKOMAI YAYANA ZAN TAIMAKA MAKA...... AMMA FA.....UWAR MUGU-03

Wannan shiyasa Aliya ta dube shi sannan ta girgiza kai tace BAKOMAI YAYANA ZAN TAIMAKA MAKA...... AMMA FA abincin dake dakina ayanzu sai ahankali kuma shi kansa dakin nawa ma ba wani haduwa yayi ba don haka in kana ganin zaka iya maneji to zo mu tafi.

Saurayin ya dubeta da murmushi yace in banda abinki kanwata maroki ai ba shi da zabi nagode sosai.

Aliya ta dubi kayan dake jikinsa cikin damuwa ta ce to Shikenan mu tafi.
Saurayin ya kura da irin kallon da takeyi wa kayansa don haka saiya dube ta yace kayana ko? Ni kaina abunda nake tunani kenan domin nasan muna shiga cikin gari zan iya zama abin kallo ya danyi shiru ina ganin ko gaba zakiyi sai na bi ki abaya basai mun jera ba ko?

Aliya ta juya ahankali tayi nazarin jerin gidajen dake fuskantar katon filin da suke ciki sannan tayi ajiyar zuciya ta juyo ta dubi saurayin.
Ina ganin ma ai ba matsala nuna iya tafiya tare ashe na an dauke wuta tana gama fadin haka saita juya tafara tafiya.

Saurayin yayi jim na yan dakiku sannan saiya bi ta abaya cikin sauri na mamaki Idan akayi la'akari da irin yanayin dayake ciki koda ya karasa kusa da ita sai ya dube ta yace kafin mu karasa inaso na roke ki wata alfarma ta karshe.

Aliya ta dan tsaya kana ta dube shi cikin mamaki.
Alfarmar me?

Idan zai yiwu bana son wani ko wata ya shigo yau sameni cikin dakin ki.

Aliya ta dube shi cikin kaduwa
Kana nufin ko da ƙawata bazan bari ta shigo dakin ba?

Saurayin ya gyada kai eh gaskiya haka nake nufi indai zai yiyu.

Ganin tayi shiru a tsorace saiya ci gaba da cewa cikin sauri kiyi hakuri nazo miki da tsarabobi amma ina son ki sani cewa ina cikin matsaloli ne masu yawan gaske wadanda bazan so mutane su gane fuskata ba ayanzu... Kiyi hakuri kinji kanwata sannu ahankali zaki fahimci abunda nake nufi.
Aliya ta dube shi dogon kallo na yan dakiku sannan sai taci gaba da tafiya
To ni dai nayi niyyar taimakon ka bansan ko kai wanene ba bansan daga ina kake ba bansan abinda ke tafe dakai ba koma dai kai wanene ni nayi niyyar taimaka ma duk abunda kayi niyya saidai ka yi min.

Taci gaba da tafiya.
Kanwata saurayin ya kira ta a tausashe.
Aliya ta juyo ahankali ta fuskance shi.
Bazan cutar dake ba kinji.
Aliya ta yi masa dogon kallo kana tayi ajiyar zuciya.
Akwai wani abu a muryarsa dayasa ta amince da abinda yafada mata alokacin tabbas muryarsa ma tana sauti kusan daya da na marigayi Amadu.

***** ***** ****** ****** ******* ****** *******

In ka dauke wani dan siririn farin haske na fitilar kwai yar Cana da yayi wa kansa hanya ta karfin da yaji ta tsakankanin labule da rufaffiyar wata Munafukar kofar daki duk farfajiyar gidan cikin duhu take hakan ya farantawa Aliya rai wacce Daman tun da suka shigo gidan duk da dai dare yayi Aliya tasan wata sa'ar Abokanan kwanan ta basa dawowa sai Asuba to amma tasan wata sa'ar a farfajiyar gidan suke shimfida idan babu wuta sai su kunna fitilar kwai su sa karta agaba suyi ta caca watarana har sai gari ya waye don haka ayanzu da suka shigo taga farfajiyar gidan cikin duhu sai tayi ajiyar zuciya.
Cikin sauri ta lalubi saman asabarin dake kofar dakin ta dauko dan makullin sannan ta juya akaro na farko tun sa'ar da suka shigo gidan tayi masa murmushin yake.
Munyi sa'a ba kowa sai wancan dakin ta nuna kofar dakin nan da hasken yake ratsowa ta kofar sa da baki.

Saurayin yayi nazarin farfajiyar gidan dakuna uku ne agidan har na Aliya farfajiyar gidan ba wani abin Kuzo ku gani bace domin kuwa sau uku yana tuntube kafin su karaso kofar dakin Aliya saboda farfashewa da daben farfajiyar gidan yayi daga bangaren yamma na gidan wasu Tsofaffin mashina ne guda biyu da wani tsohon keke rali haka nan duhun daren bai hana saurayin hangen wata tsohuwar jarka ba cike da bola har baki. Saurayin ya lura da halama daya dakin babu kowa aciki domin a rufe yake babu alamar haske sabanin daya kofar dakin.
Nayi sa'a zakice saurayin yace gamida rama mata murmushin datayi masa.

Aliya ta bude kofar dakin cikin sauri ta shige saurayin yayi jim kadan bai bita ba ganin dakin cikin duhu.

Ka Shigo mana yanzu zan kunna fitila Aliya tace dashi cikin duhun.

Tun kafin saurayin yagama shiga dakin ya gauraye da haske sannan ne to akaro na farko suka yiwa juna kallon tsaf.

Matasan biyu suka dubi juna na dan wani lokaci kowa na sakar zuci gamida kokarin fahimtar abunda ke kai kawo a zuciyar juna.

Zaka zauna kokuwa saika gama kallon nawa?
Aliya tace dashi da murmushi kadan a bakinta.

Saurayin ya danyi dariya sannan ya sunkuyar dakai tabbas yayi mamaki bai taba zaton kyakkyawa ce haka ba gashi dai fitilar yar Cana dake dakin ba wani hasken kirki ne da ita ba amma saida saurayin ya fasalta kyawunta cikin zuciyarsa.

Tabbas bafilatana ce ya fadawa kansa bata da tsayi sosai jazur da ita kamar tsada gashin ta kadan ya rage ya sauka adoron wuyanta me yiwuwa ma rashin gata kokuma rashin daurin gindin bariki ne ya hana gashin karasa sauka akan dogon wuyanta mai kamar na barewa idanunta masu fadi ne manya. saurayin ya lura lokacin data dube shi tana murmushi sai idanunta suka lumshe kamar tana jin barci hancinta dogo ne daga can karshensa yayi tsini ainun kamar an fike alkalami wannan shiyasa shi kama da hancin mage Aliya tana daf dan faffadan baki wani saurayi dan duniya yataba cewa da ita wai bakinta irin na shan ice cream ne rashin isashshen haske bai bar saurayin yakare mata kallo ba har zuwa kasa ba.
Saurayin yayi ajiyar zuciya sannan ya sunkuyar dakai yace abun ne yabani mamaki.

Aliya ta dube shi cikin mamaki mamakin me?
Saurayin ya dubi tsarin dakin da suke ciki a takaice kana ya dauke kai mamakin ganin tunda muka shigo bamu hadu da kowa ba agidan nan.

Aliya ta zuba masa idanu na dan tsayin lokaci akwai wani fatalwar murmushi Agefen bakinta tasha jin irin wannan kalamai daga bakin maziyartanta da dama tabbas tasan karya yake yi.UWAR MUGU-04

Aliya ta zuba masa idanu na dan tsayin lokaci akwai wani fatalwar murmushi Agefen bakinta tasha jin irin wannan kalamai daga bakin maziyartanta da dama tabbas tasan karya yake yi.

Baikamata mu fara da karya ba tun daga haduwar mu tace dashi cikin Dariya.

Saurayin yayi dariya sannan ya dubi tumemiyar katifar dake cikin dakin yace ki gafarce ni kanwata gaskiya ne abin da kikace amma dai yanzu na iya zama?

Da dai zafi.
Ta zauna abakin katifar.

Saurayin ya danyi Jim kadan kana shima ya zauna kusa da ita yana nazarin yan komatsan kayan dake dakin cikin mamaki.
Babu wani abun azo agani acikin dakin wata tumemiyar katifa ce kawai shimfide akan ledar tsakar dakin amma taji jiki domin rigar katifar yafara yayyagewa acan kusurwar dakin ta gabas maso arewa wasu akwatuna ne guda biyu yar karama dakuma wata katuwa sai kuma wasu yan kwanuka masu launin azurfa adab da akwatin gamida wasu yan tsummokara na kaya masu datti warwatse atsakar dakin. Saurayin ya lura da wasu takalma biyu masu tsinin dunduniya akan wani dan karamin teburi wanda ke dauke da kayan kwalliya da kwalaban turare masu araha.

Aliya ta Lura da yadda yake nazarin dakin don haka saita kalle shi tace Daman fa na fada maka saidai hakuri.... Dakin nawa ba wani haduwa yayi ba.

Saurayin ya gyada kai cikin damuwa shine abunda yabani mamaki.
Ya danyi shiru yana dubanta ganin bata ce komai ba saiyaci gaba da cewa Awannan zamani kyakkyawa irin ku basu cika zama cikin talauci ba....amma ke sai gashi abun mamaki dakin naki kamar anyi miki sata

Aliya ta fashe da dariya cab lallai nagode wato dakin nawa ne kamar anyi min sata ko?

Saurayin ya girgiza kai cikin sauri yace kiyi hakuri bana fada bane da niyyar cin mutunci ba.. Na dai fadi Abunda ke raina ne kawai.

Kada ka damu nima wasa nake.. Bakaga ma ina dariya nafada ba? Aliya tace lokaci guda kuma ta tashi tsaye ta nufi inda kwanukan nan suke ta dauko daya daga cikin su sannan ta dawo ta zauna akusa dashi ta dube shi da murmushi.
Ga abincin amma fa saidai kaci shi da halin sa don yayi sanyi.

Saurayin ya dube ta yace ai nafada miki tun farko shi maroki bashida zabi.

Aliya ta dube shi kana ta zunkuda kafada sannan saita bude kwanon alale da mai da yaji ne aciki.
Bismillah
Saurayin ya dubi abincin sannan ya dube ta kefa bazaki ci ba? Ta girgiza kai tace a koshe nake naci abinci a wurin uwar dakina dazun da magariba.

Saurayin ya yi mata dogon kallo sannan ya janyo kwanon gabansa.

Aliya ta mike tsaye adaidai lokacin daya fara cin abincin ta nufi katuwar akwatin dake kusurwar dakin ta bude sannan ta tsugunna tafara bubbude suturun dake ciki bayan wasu yan dakiku tafito da riga shat irin ta maza da wando jeans ta mike tsaye ta nufi inda saurayin yake tana zuwa saita jefa su akusa dashi kana ta dube shi tace
Idan ka gama cin abincin saika tashi ka sauya wannan kayan dake jikinka ka bani su na wanke ma.

Saurayin ya dauko loma zai kai bakinsa tayi kalamin don haka sai hannunsa ya makale a sararin samaniya cikin mamaki.
Kina nufin zaki wanke min kayan dake jikina?

Aliya ta gyada kai
A'a wahalar tayi yawa ina ganin kibar shi kawai in don mutane ne ni da asuba ma nake son ficewa Nabar miki dakin ki.

Aliya ta girgiza kai
Ni ba don mutane bane danayi wannan ai da ba bazan kawo ka dakina ba ta danyi shiru tana kallon sa ai ko don kaji dadin jikin ka ma a wanke su ko?

Ya danyi shiru sannan saiya gyada kai yace hakane nagode.
Bayan yagama cin abincin ne to ya mike tsaye yafara cire tsohon jeans din dake jikinsa.

Aliya na gefe a tsaye tana kallon sa cikin mamaki domin ta lura ba'a nutse yake cire kayan ba.
Bari nafita waje idan ka gama saika kira ni.

Saurayin yayi dariya yace ashe dai kin gane ni.
Aliya tayi dariya tace kai ka sani ta nufi kofar dakin zata fita...
TAYAYA zan kira ki bayan ko sunan ki bansani ba?

Aliya ta juyo ta dube shi da murmushi tace sunana Aliya.... Kaifa?

Saurayin yayi dan Jim da Wandon sa ahannu
Toh kina iya kirana da BANGIS..

BANGIS.. Aliya ta maimaita sunan.
Aliya tayi murmushi ta fita.

Nan da nan Bangis yafara cire suturan dake jikinsa cikin

Please Login or Register in order to submit comment