Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauri yarinyar wayayyiya ce ya fadawa kansa wannan itace macen data dace dashi macen dake iya fahimtar halinda mutum ke ciki ta taimaka masa lokacin dayake bukatar taimako.

Da'ace bata fita daga dakin ba da bangis baisan yadda zaiyi ya cire kayan dake jikinsa ba domin akwai wani abu da baya so ta gani kai bama ita ba duk wani mutum a halin yanzu har sai lokacin da ya cimma manufar dake boye a zuciyarsa..........UWAR MUGU-05

Da'ace bata fita daga dakin ba da bangis baisan yadda zaiyi ya cire kayan dake jikinsa ba domin akwai wani abu da baya so ta gani kai bama ita ba duk wani mutum a halin yanzu har sai lokacin da ya cimma manufar dake boye a zuciyarsa.

Aliya ya kwalla mata kira bayan yagama sauya kayan.

Aliya ta shigo sannan ta dube shi cikin dariya
Ashe dai kayana zasuyi ma daidai?

Bangis yayi murmushi sannan ya taba hantsarsa.
Kugun ne kawai yayi min yawa

Aliya tace oh Eh hakane fa kasan Daman Wandon mata haka yake.

Alokacin ne to bangis ya dubeta da ido na tsawon lokaci sannan yace da ita a tausashe.
Aliya wai me yasa kike yi min duk wannan taimakon.?

Aliya ta dube shi kana ta sunkuyar da kai na tsawon lokaci can sai ta dago kai ta dube shi tace
Saboda Kamarku daya da yayana amadu...amma ya rasu shine rumfa daya dake hana min jin zafin rana bayan rasuwar iyayen mu rashin sa aduniya shi ya jefa ni a tsakiyar zafin ranar danake sha alhalin yanzu tayi shiru gamida sunkuyar dakai.
Bangis ya lura da hawaye na kokarin subucewa a kyakkyawar fuskarta don haka sai ya nufi wata tabarma dake can kuryar dakin ya dauko ya shimfida sannan ya dauki daya daga cikin matasan kai biyu dake kan katifar ya jefa akan tabarmar daya shimfida sannan ya zauna.
Aliya ta dube shi cikin mamaki lokacin guda kuma ya share hawaye a wayance kana ta girgiza kai A'a dawo kan katifar ka kwanta idan bazaka iya kwanciya tare dani ba ni na kwanta akan tabarmar.

Bangis ya girgiza kai yace A'a ina kika taba ganin haka?

To ai kai bakona ne don Allah kadawo kan katifa ka kwanta kada kayi min haka.

Bangis ya girgiza kai yace kiyi min alfarmar karshe ki kyale ni anan ke ki kwanta akan katifarki kinji kanwata.?

Aliya ta buda baki kamar zatayi magana sai ta fasa ta dauki kayan daya cire ta nufi waje.

Tsawon lokaci kansa a sunkuye bayan fitar ta sannan sai yau dago kai. Alokacin ne to yake ganin lambar waya a rubuce ajikin bango akasan lambar an rubuta ALIYA.

Da safe misalin karfe bakwai Aliya ta farka firgigit ta dubi tabarmar da bangis yake kwance babu shi babu alamarsa cikin mamaki ta mike tsaye sannan tayi taga taga kamar zata fadi saboda barci bai gama sakinta ba INA YA TAFI NE?
Ta tambayi kanta sannan ne to amsar tambayar ta tazo mata cikin zuciya Daman ai sai da yace da ita da asuba zai fita to amma abunda yabata mamaki shine anya kuwa bayan duk alkhairin datayi masa zai iya tafiya batareda yayi mata ko da sallama ba?

Aliya ta sake duban tabarmar da bangis ya kwanta sannan ne to ta hangi kananan suturunta da ta bashi yasa jiya da daddare wannan shi ya tabbatar da cewa ya tafi. Abin yayi matukar kona mata rai yaya zai tafi babu ko sallama? Ta tambayi kanta kai lallai mutanen duniya sai abar su. Ta fadawa kanta cikin fushi saita warci kayan dake kan tabarmar da niyyar ta mayar dasu cikin akwati adaidai lokacin ne to wani abu yafado daga cikin aljihun jeans din data bashi aro.

Nashiga Uku. Aliya tace cikin kaduwa lokaci guda taja da baya a tsorace sa'ar da abun yafado akan kafarta ta dama tunda Aliya take bata taba ganinta a zahiri ba sai yau a film ma idan taga ana harbe harbe tashi take domin bata fiya son tashin hankali ba. Aliya ta sake kallon abunda ke kan tafin kafarta a tsorace tana fatan ina ma ace ta roba ce tabbas BINDIGAR GASKE CE.

BABI NA BIYU
USMAN yayi ajiyar zuciya Sa'ar daya gama karanta sakon wasikar dake kan fuskar wayar sa akaro na biyar. Gumi kamar ruwa ya fara sartu akan fuskarsa kai ka rantse da Allah kunama ya hadiya.
Lokacin da ya fara karanta sakon ya dauka idanunsa ne ke yi masa gizo don haka saiya sake karantawa Yakuma sake karantawa har sau biyar amma duk abanza wai an girmi sarki. Sakon yana nan dai babu sauyi.

Yaya SAMIRA zatayi min haka? Usman ya tambayi kansa ga mamakin sa saiyaji hawayen bakin ciki yafara sartu akan kumatunsa an sha fada masa abaya cewa SOYAYYA KARYA CE bai yarda ba amma ayanzu akan dole ya yarda da wancan batu tabbas soyayya karya ce domin da gaskiya ce da babu abunda zai sa Samira ta aiko masa da sakon.
Me zaisa tayi min haka tunda dai tasan halinda yake ciki ya sake maimaitawa cikin zuciyarsa.

Shekara uku kenan suna tare babu dare babu rana kaddara ce ta hada su a jami'a Alokacin data rako yayarta zata yi rijistar karatu zango na farko shi kuma alokacin yana dalibi a makarantar

Usman yana sauri dauke da littattafansa ya ratsa ta filin fakin zai wuce dakin karatu adaidai lokacin ne ya hangi wata budurwa a tsaye ajikin wata mota kirar Honda prelude tana rawar sanyi hakoranta suna dukan juna Usman yayi mamaki domin ganin shi a lokacin zafi ma yake ji amma ga wata tana rawar sanyi don haka har ya wuce saiya dawo da baya ya dubeta cikin damuwa domin ya lura duk idanunta sun kawo kwalla.UWAR MUGU-06

Usman yana sauri dauke da littattafansa ya ratsa ta filin fakin zai wuce dakin karatu adaidai lokacin ne ya hangi wata budurwa a tsaye ajikin wata mota kirar Honda prelude tana rawar sanyi hakoranta suna dukan juna Usman yayi mamaki domin ganin shi a lokacin zafi ma yake ji amma ga wata tana rawar sanyi don haka har ya wuce saiya dawo da baya ya dubeta cikin damuwa domin ya lura duk idanunta sun kawo kwalla.

Sannun ki Usman yace yana kallon ta cikin tausayi bakida lafiya ne? budurwar ta gyada kai wallahi zazzabi ne ke damuna gashi kuma wacce muka zo tare tun dazun ta shiga ciki haryanzu bata dawo ba nikuma bansan inda zan shiga na same ta ba.

Usman ya dubeta cikin damuwa yace to ki kira ta awaya mana.
Wallahi wayar tawa ce ba caji shiyasa duk na rasa yadda zanyi ta Durkusa agaban motar ta dafe kai.

Ita wacce kuka zo da ita din wane department take? Usman ya tambaye ta.

A sociology take budurwar tace sannan ta dafe kai gamida cije baki.

Sociology? Ai department dinmu ne menene sunanta.?

Budurwar ta mike tsaye ta jingina da motar sannan ta tofar da yawu tace FADILA... Fadila Sani

Fuskar saurayin ta washe.
Fadila sani! Ai kusan kullum muna tare bari na shiga ciki na nemo miki ita inajin departmental registration take yi don nasan bata gama ba.

Kai amma danaji dadi wallahi nagode sosai

Bakomai Usman yace sannan ya juya cikin sauri dan jirani ina zuwa.

Budurwar na nan tsaye tana rawar sanyi bayan wasu yan mintuna sai ga Usman da fadila cikin sauri sun nufo inda take.

Aikin ga irinta Daman saida nace dake kiyi zamanki tunda ba wata cikakkiyar lafiya ce dake ba kika nace saikin biyo ni to ga irinta nan.
Tana gama fadin haka saita bude kofar motar a fusace ta shiga ta tashi motar sannan ta dubi Usman tace Usman Thanks Bari na mayar da ita gida nadawo ko sai mu karasa maganar mu ta rannan.

To Shikenan Allah yabata lafiya sannan ya dubi budurwar yace Allah ya sauwake my sister.

Budurwar ta dube shi da murmushin karfin hali tace Amin Nagode sosai.

Bayan sati biyu da faruwar wannan rannan Usman da fadila suna zaune a dakin karatu sai Usman yake tambayarta wai ina marar lafiyar nan kuwa ta samu sauki ne?
Tun yaushe mantawa nayi ma ban fada ma ba kullum saita tambaye ka kokuma tace na gaishe ka.

Usman ya dubi fadila cikin dariya yace amma yanzu saboda tsabar bakin cikin bakya so nayi budurwa shi ne ko ki fada min gaisuwar sai yanzu dana tambaye ki ita?

Fadila ta zaro idanu cikin kaduwa ta dube shi cikin dariya tace kai Are you serious? Kamar kun hada baki wallahi itama abinda tace dani kenan wai kana burge ta.

Da gaske? Usman ya tambaya

Allah kuwa fadila tace sannan ta danyi shiru tana dubansa malam idan kana sonta kayi magana sister dina ce da mamanta da mamana uwa daya uba daya suke

Usman ya dubeta cikin murmushi yace gaskiya bazan boye miki ba fadila ke ƙawata ce inason ta amma ina tsoro.

Fadila ta dube shi cikin mamaki tace tsoron me?

Usman ya sunkuyar dakai Yana wasa da biron dake yan yatsunsa ni gani nake kamar tafi karfina... Kin san a nan makaranta matsayin mu na dalibai kusan duk daya muke amma idan aka koma gida akwai bambanci mai yawa tsakanina daku fadila.

Fadil ta girgiza kai tace Haba Usman don Allah ka daina wannan magana wannan ai zance ne irin na mutanen da. kasan ita mace Idan tace taji ta gani tana son ka babu wata matsala koda acikin dokar daji ne zaku iya zama da ita soyayya ai ba karya bace Usman.

Tun daga wannan romon baka sai Usman da Samira suka fara soyayya har zuwa lokacin da ya kammala karatu duk bayan kwana biyu sai sunyi hira acikin wani katon dakin shakatawa mai kama da filin wasan kwallo kafa. Sannu ahankali har suka fara maganar aure.

Akwai wani abu gameda sha'anin Samira dake damun Usman duk lokacin da zai zo sai Samira ta bashi lokaci kazo gobe Karfe shida ko takwas ko tara hakan nan Takan ce dashi. to amma idan ya saba wannan lokacin yana zuwa sai ya same ta acikin wata katuwar mota ita da wani alhaji mai katon ciki suna hira wannan shiyasa Usman yaa fahimci dalilin dayasa take bashi lokacin zuwa wato don dai kada su hadu da wannan alhaji don haka rannan da yamma suna hira sai Usman ya dubi Samira yace
Samira ina ganin lokaci yayi daya kamata mu fara magana akan auren mu ko?

Samira ta hade fuska da farko amma daga baya sai ta sai fuska cikin sauri ta dube shi da murmushi tace ka shirya ne?

Usman yaji gabansa yafadi ya manta da wannan tabbas yasan ko allura bai tanada ba don haka sai ya girgiza kai A'a amma dai za'a san adda za'a yi babu abinda zai gagara in Allah ya yarda.

Samira ta fashe da dariyar izgili Uhm Usman kenan tayi shiru tana kallon sa.

Kamar yaya Usman kenan? Ya tambayeta zuciyarsa na harbawa jikinsa yabashi cewa wani abu marar dadi yana dab da Faruwa.

Samira ta dauke kai gefe guda na Kusan dakiku talatin bata ce dashi komai ba.
Baki ce komai ba Usman yace muryarsa na rawa.

Samira ta dago kai amma bata yarda sun hada idanu ba.UWAR MUGU-07

Samira ta dauke kai gefe guda na Kusan dakiku talatin bata ce dashi komai ba.
Baki ce komai ba Usman yace muryarsa na rawa.

Samira ta dago kai amma bata yarda sun hada idanu ba.
Kasan akwai ganganci mutum ya tunkari aure Awannan zamani batareda da wata kwakkwaran sana'a da yake yi ba.
Ta danyi shiru kanta a sunkuye ko ka sami aikin?

Usman yaji wani abu ya zo makogoronsa ya tsaya dakyar yake hadiyar yawu jikinsa na rawa ya girgiza kai.
Ina dai nema amma nasan nan ba.....

A'a Usman ta katse shi abunda ke hannun ka dashi ake lissafi amma wannan abun da kake kokarin yi shi ake cewa lissafin dokin rano wai da mai rai da matacce.
Tana gama fadin haka saita Mike tsaye ta dube shi
Ina ganin mu bar maganar nan haka har sai ka samu aiki sai mu ga ta inda zamu bullowa zancen auren ko Usman dina?

Usman ya rasa abunda zai ce da ita tuni numfashinsa yafara daukewa ya dago kai ya dubeta wannan shine kawai abunda zaki iya cewa dani Samira?

Samira ta dube shi da mamaki sannan ta bare wata cingam da ta dade tana wasa da ita ahannunta ta jefa baki ta tauna kas-kas.
To me zance dakai? Ni Aganina ko kai bazaka so muyi aure cikin halin kaka-ni-kayi ba kuma kaga iyayena bazasu so su sayar da akuya tadawo tana ci musu danga ba ko?

Usman ya gyada kai yace hakane ya cusa hannayen sa biyu cikin aljihun Wandonsa yafara juye juye kamar cinnaka ya cije shi.

Samira ta dube shi kana tayi masa murmushi tace meye naga ka wani bata rai? Kaga Usman don Allah ka sanya ranka a inuwa ni samari matarka ce don haka ka daina wata fargaba babu abunda zai hana ka aura na.

Usman ya dago kai ya dubeta tsahon lokaci sannan yayi ajiyar zuciya.

Da wannan Suka rabu da juna kuma shi wannan al'amari yafaru ne kwanaki biyu kafin wannan bakin sako ya sauƙo acikin wayar sa don haka ayanzu da Usman ke zaune gumi na zuba hawaye na kwarara a kan fuskarsa saiya sake kallon sakon sannan ya sake karanto sakon tun daga farko akaro na shida.

**Usman rannan bayan Rabuwar Mu dakai sainaga agaskiya baka dace dani ba domin na lura ahakikanin gaskiya babu abinda na sama yaci ballantana ma har ya baiwa na kasa. Ada na kaunace ka abisa kuskure makahon so ne irin na yarinta amma ayanzu na fahimci ashe dai kowace ƙwarya da abokin burminta don haka ina mai baka hakuri da ka mance dani kawai kamar ma bamu taba yin wani abu wai shi soyayya ba nasan bazan taba fita daga cikin zargin ka ba amma dai ina fatan nan gaba kadan zaka gane abinda nake nufi. Nagode
DAGA KAWAR KA SAMIRA**

Usman ya share hawayen dake sartu akan fuskarsa sannan ya dubi saman dakin dayake ciki gamida ajiyar zuciya jikinsa ya dauki rawa lokaci guda zazzabi ne ke neman rufe shi.
Abinda tafada gaskiya ne Usman yafadi cikin zuciyarsa tabbas kowace ƙwarya da abokiyar burminta Daman tun farko abunda yake gudu kenan shiyasa yayiwa fadila togaciya tun kafin ma yafara zuwa wajen Samira to ga irinta nan amma dan bakara ya fadawa kansa.
Jikinsa na rawa ya Mike tsaye ya dubi dakin da yake cikin damuwa dakin dan kankane ne babu komai aciki sai wata katifa mai kamar silifa da wasu Tsofaffin takalma uku da'ace zai dauke takalman idan yayi sa'a saiya samu gurin sallah saman dakin rufin azara ne wanda ya rufto kasa kasa kamar zai fado acan gefe kadan Manne da jikin bango wata tsohuwar akwatu ce mai kama da ta gawa dauke da dan abin da ya rage na daga suturun Usman.

Tun bayan rasuwar mahaifinsu MALAM DANGANA
Al'amura basu sake tafiya yadda yakamata ba kullum sai jerin masifu iri iri daga wannan sai wanna kamar ya'yan carbi tuni Daman tun watan daya gabata aka koro kannensa mata biyu daga makaranta saboda rashin biyan kudin makaranta haka nan akwai wani kaninsa HABU wani saurayi marar jin magana shekaranjiya ya yi wa wani yaro dan makwabtan su duka ayanzu haka yana ofishin yan sanda a tsare rashin kudin beli ya hana a karbo shi to ba ma ta wannan ba kawai ke damun Usman domin matsalar habu shi ya janyowa kansa amma rashin lafiyar mahaifiyar su shiya fi damunsa ayanzu.
Tun bayan rasuwar mahaifinsu bata sake lafiya ba Daman ta dade da Cutar hawan jini amma abin bai tsananta ba saida mahaifin su ya rasu don haka kullum a taraddaddin inda zai sami kudin sayen magani yake ga shi duk akansa aka dogara tunda dai kannensa biyu mata ne shi kuwa Habu bai ma amnafawa kansa ba ballantana ya amfanawa wani wadannan abubuwa da ma wasu su suka taru suka yiwa Usman rubdugu yama rasa inda zaisa kansa don haka ayanzu dayake tsaye zazzabi na barazanar rufe shi saiya lallaba ahankali yafita daga dakin cikin sauri ya nufi dakin mahaifiyarsa.

Kayi hakuri domin dukkan wata jarrabawa da Allah yayiwa bawan sa alheri ce idan yayi hakuri mahaifiyarsa ce ke fadin haka tana dubansa cikin damuwa bayan ya gama fada mata halin da suke ciki da Samira.
Don haka abinda nake so da kai shine ka fita dag batun wannan yarinya tunda ta raina ma arziki don ba matar aure bace sannu ahankali idan kayi hakuri Allah zai baka wata daidai da kai kana ji na ko?

Usman ya gyada kai..

Kafita batun ta kada ka sake kasa abun cikin zuciyar ka sai yayi ta damun ka amma idan ka dake zuciyarka ka mika komai ga Ubangiji sai ka ga yakawo ma mafita mafi alheri.
Wannan shine nasihar da mahaifiyarsa tayi masa ita tasa Usman ya dan ji sanyi sanyi a ransa har ma ya sami damar fitowa kofar gida zuciyarsa nata kokowa da tunanin sakon da Samira tayi masa adaidai lokacin ne to abokinsa HASHIMU direba yake zuwa ya same shi.

Hashimu gajere ne fari mai kyawun fuska yakaraso inda Usman yake sanye da riga da wando duk na jeans Amma sunyi dukun dukun da bakin mai Hashimu abokin Usman ne tare sukayi makarantar allo suna yara shi Allah bai sa zaiyi karatun boko ba don haka daya girma saiya fara bin manyan motoci zuwa kudancin Kasar nan sannu ahankali yanzu har ya zama cikakken direba wani ubangidan sa yaa saya masa babbar mota gwangwaro...

Salamu Alaikum...
Yaya na ganka kai kadai?

AYI MIN AFUWA BISA SHIRUN DA AKAJJ KWANA 2
ABUBUWA BIYU NE SUKA HANANI POSTING NA FARKO DAI RASHIN LOKACI NA BIYU KUMA GASKIYA RASHIN
ISASHSHEN KUNSHIN HAWA YANAR GIZO-GIZO
Inafatan An Fahimta.
Engr Murtala
Sabiu Muhammad
Sabitu UsmanUWAR MUGU-08

Salamu Alaikum...
Yaya na ganka kai kadai?

Ku fa yan boko nan kunada matsala sai ku fita daga cikin jama'a ku koma gefe kuyi ta tunane tunane wallahi saika haukace idan bakayi ahankali ba.

Usman ya dago kai ya dube shi da murmushin yake yace kai bafa na son iskanci ni zakayiwa tashanci?

Bawani tashanci wallahi gaskiya ce don me zaka zo nan kai kadai kayi tagumi?

Usman ya danyi shiru sannan saiya dago kai ya dubi hashimu adaidai lokacin daya zauna akusa da shi kan wani sabon benci.

Wato ka gane abokina wallahi ina cikin matsala don CASE din dayake kaina ayanzu ko ofishin yansabda sai haka.

Hashimu ya fashe da dariya yace kai ofishin yansanda fa kace.

To ai ni abun ne yabi ya rikice min... Talaucin garin nan ta ishe ni don ina cin ƙari a garin nan.

Allah malam? Usman ya tambaya Yana girgiza kai amma cikin damuwa.
Suka danyi shiru suna kallon junansu sai Usman yayi ajiyar zuciya ya dubi Hashimu yanzu kaga saboda rashin abun duniya Samirata ma ta guje ni.?

Hashimu ya dube shi cikin kaduwa
Kai kabari don Allah duk yadda kuke da Samira.?

Usman ya lalubi aljihunsa ya dauko wayar sa ya daddana yamika wa Hashimu wayar.

Hashimu ya karbi wayar yafara karanta sakon fuskarsa ta yamutse sa'ar daya gama karanta sakon.
Kai amma dai bata kyauta ba.

BA laifin ta bane... Laifin talauci ne
Hashimu ya gyada kai yace to hakane din kenan za'a ce amma dai batada mutunci.

Hashimu ya sunkuyar da kai na tsawon lokaci sannan saiyace batareda ya dubi Usman ba to Mudai a bangaren mu na direbobi akwai yan ayyuka da akeyi wadanda za'a iya rufa wa kai asiri dasu to amma bansani ba kasan ku yan boko mai yiwuwa kai bazaka iya jure irin aikin ba.

Usman ya dago kai cikin sauri yace kaga ayanzu ko kwasar kashi ne ni dai zanyi indai zan sami kudi babu Abunda zai hana ni yi.

Hashimu ya girgiza kai
Abun ma bai kai haka ba ya dan yi shiru sannan yaci gaba Ah akwai ESCORTS da akeyi awani kamfanin riɗi Daman shi nake tunanin ko zaka iya tunda ba wani aikin wahala bane motar kawai zaka bi zuwa kudu amatsayin Wakilin kaya kai zaka na lura da ha'incin mu na direbobi har sai ka tabbatar kayan sun sauka lafiya kuna isa za'a biya ka kudin ka naira dubu goma cif cif.

Usman ya gyara zama ya dubi Hashimu bakinsa na rawa yace wannan aiki yayi min indai zan samu wallahi zanyi.

Me zai hana? Zaka samu indai zaka iya jurewa zama don sai kunyi wajen kwana uku ko hudu ahanya.

Ko sati biyu za'a yi ahanya nidai zan iya don yafi wannan zaman bakin cikin danake yi babu aiki kuma da zan samu tafiya gobe ma da wallahi nafi so don kaga yin hakan zai dan rage min tunanin Samira daga cikin zuciyata

Hashimu ya gyada kai yace hakane ya danyi shiru.
Ah Ina ganin abunda za'a yi gobe zan zo da safe saimu tafi na hada ka da wani abokin ubangidana shi zai iya yi maka hanya koda a gobe ne Idan ka shirya zaku iya tafiya.

Usman ya Mike tsaye cikin sauri ya dubi abokinsa.
Nagode Allah saka ma da alkhairi wallahi ka ceci rayuwata bari yanzun nan na shiga na fadawa babata in Allah yaa yarda gobe zan bar garin nan.

Hashimu ya Mike tsaye ya dube shi da murmushi amma ka bani mamaki don ni wallahi ban dauka dan boko kamar ka zai yi irin wannan aikin ba.
Usman ya dubi Hashimu cikin mamakin jin abunda yace sannan ya matsa kusa dashi ya dube shi ido da ido yace a tausashe abunda baka sani ba shine akwai yan boko akwai kuma mai yin boko kuma ko acikin irin ku ana samun yan boko. ya danyi shiru yana mayar da numfashi sannan yaci gaba ni ba dan boko bane ni mai yin boko ne kuma shi arziki da kake ganinsa ba'a karatu yake ba ba'a gida yake ba ba'a kasuwa yake ba Allah shine arziki domin aikinsa ne ya azurta ko ya talauta wanda yaso. yayi murmushi sannan ya daki Hashimu a kafada.
Mu tafi na raka ka gara na dawo ko zan samu isashshen barci don nasan gobe warhaka muna kan hanya ko?

Hashimu ya fashe da dariya yace cab wannan fa wai shine zakin mazallako wai ɗa daga ciki yana rokon uba kwabon dan wake.

****** ******** ******* ******** ****** **********

SA'IDU sunansa na gaskiya amma yan duniya sunfi kiran sa da INDARARO wannan ita tasa sannu ahankali sunansa sa'idu tuni ya dade da bacewa rabon da Akira shi da wannan sunan tun yana saurayi dan shekara ashirin da wani abu.
INDARARO ALLAH NABAKA KANA ZUBARWA AKASA.
Haka yan duniya ke yi masa wannan kirari tun zamanin kuruciyarsa har zuwa wannan lokaci daya tunkari shekara hamsin aduniya.

Indararo dogo ne baki kakkaura a zamanin kuruciyarsa kyakkyawa ne bakinsa har sheki yakeyi amma ayanzu saboda rinewa da hayaƙin taba na shekara da shekaru gamida dogon sankon daya faro tun daga goshinsa har zuwa kyeyarsa su suka taru suka sa shi munin karfi da yaji.
To amma fa a wajen maza kawai yake mummuna domin mata yan duniya basu taba ganin wannan munin nasa ba domin hannun dake bayarwa fuskarsa bata taba yin duhu a idanun masu karɓa ba.

Indararo yayi hamma sannan ya dubi jerin dogayen motoci tireloli sannan ya lalubi aljihunsa da niyyar ya dauko kwalin taba cikin sauri ya sauya niyya domin yayiwa kansa alkawarin rage shan taba.

bara warhaka yana asibiti yana fama da ciwon huhu likita yariga ya gargade shi cewa in har bai rabu da shan taba da giya ba to su zasu zama ajalinsa.
Indararo bai daina shan taba ba amma ya rage yanzu yakan sha kwali guda ne a rana maimakon da dayake shanye sama da kwali takwas arana giya kuwa idan ya zauna sai an tashe shi.

Don haka ayanzu dayake zaune sai yayi tsaki cikin damuwa domin ya so ya kunna tabar amma babu yadda ya iya tunda baya son mutuwa...

AMMA FA BAISAN CEWA.....UWAR MUGU-09

Don haka ayanzu dayake zaune sai yayi tsaki cikin damuwa domin ya so ya kunna tabar amma babu yadda ya iya tunda baya son mutuwa.

Daga inda yake zaune yana iya hangen farfajiyar katon kamfanin Ridin wanda ke cike da manyan motoci tirela duk sunyi layi ana tayi musu laftun buhunan ridi wasu daga cikin yaran motocin kwance a karkashin motocinsu suna jiran kafin layi yakawo kansu yayinda yan mata kanana mafi yawa kwailaye ke ta kai kawo dauke da farantin tallar gyada da goro kai har da mai rogo.

Indararo yayi tsaki sannan ya dubi katon agogon dake hannunsa karfe goma da rabi na safe shikam duk wadannan kayan ciye ciye basu dame shi ba da'ace yanzu zai sami koda kwalbar giya guda ce ya kwankwada ya busa sigari koda kara uku ce to da duk duniya bashida wata damuwa.

Indararo ya Mike tsaye cikin damuwa adaidai wannan lokacin ne to wayar dake aljihunsa ta dauki kara cikin sauri ya dauko wayar zai amsa kenan saiya ga sunan daya

Please Login or Register in order to submit comment