Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauri ya lalubi aljihunsa ya dauko wata yar siririyar kwalba mai fadi cikin zafin nama ya kunce murfin kwalbar sannan yafara zubo da ruwan wani abu akan hannunsa yana gogawa ajikin rigar sa sannan saiya daga kwalbar ya kwankwadi ruwan dake ciki sannan ya zazzaga sauran ruwan a kansa. Nan da nan warin giya ya gauraye gurin.

Jin warin giyar keda wuya sai Aliya ta fahimci abinda yake nufi zan fara tangadi idan mun karasa gurinsu ki fara zagina nikuma duk abunda yazo bakina zan fada.

Aliya ta dada matse akwatin dake cikin hijabin ta sannan ta gyada kai hantar cikinta na rawa gumi sai zuba yake kamar ruwa a jikinta.

Idan kin shirya sai mu tunkare su.

Na shirya Aliya ta sami kanta tana mai fadi.

Yansandan biyu ko wane da fitila a hannunsa suka zuba musu idanu sa'ar da suka ga sun nufo inda suke.

Daya daga cikin yan sandan dogo ne kakkaura mai gashin baki sunansa INUSA dansanda ne mai kwazo da basira duk inda yaga mai laifi ko da acikin duhu ne yana iya ganewa to saidai kuma kamar kowane dan adam yanada wata illa guda daya shi aduniya bashida jimirin yunwa don haka ayanzu da suke tsaye da abokin aikinsa JAFARU babu abunda cikinsa ke yi sai kugi rabonsa da abinci tun da rana kafin yabaro gidan saida masifaffiyar matarsa BARIRA ta caje shi ta kwashe dan abunda ya rage bai damu ba domin yasan zai dauki bashin abincin agurin MAMA inda yayi kuskure kenan zuwansa gurin mama keda wuya sai ya tarar shagon abincin a rufe wai anyi mata mutuwa a kauye ta tafi garinsu.

Don haka ayanzu da suke tsaye dakyar ma yake iya ganin gabansa saboda yunwa ga juwa ta fara daukar sa gashi cikinsa sai goge da garaya ake kada masa.

Wadannan kuma su wanene? Jafaru ya tambayi Inusa Jafaru dan gajere ne mai fadin kai kamar gindin turmi sau da yawa idan za'a dinka masa kayan sarki na aiki sai an auna kansa da abin awo sannan ake dinka masa hular sa zatayi daidai dashi Jafaru bashida basira ko ta sisin Kwabo daman aikin na alfarma ce tasa aka dauk shi domin tsayinsa ma bai kai ba akwai lokacin da Abokan aikin sa suke zolayar sa da cewa bai dace da komai ba sai noman doya.

Inusa yaji cikinsa yakara kugi akaro na shida don haka saiya dubi Jafaru yace wayasan musu yan iskan gari ne kawai ka fa san gurin nan baya rabuwa da kilakai.

Jafaru ya gyada kai yace hakane Inusa yasake dafe ciki yace kai abokina zo mu je can mu dan sarara wallahi yunwa nakeji kamar zan fadi.

To ka bari mana wadancan yan iskan su karaso muji daga inda suke cikin wannan dare.

Inusa ya gyara tsayuwa gumi na zuba daga fuskarsa domin iskar dake kadawa ta tsaya cak.

Aliya da bangis suka karaso bangis yana tangadi yana ta tambele.

Allah ya tsinewa uban daya kara kudin masara... Banzaye kawai to ba gara ma su kara kudin giya ba ko mayi zuciya mu daina sha ya fashe da dariya sannan yayi taga taga kamar zai fadi Aliya ta tokare shi.

Kaidai wallahi ka shiga uku shiyasa na ce kada ka sa kada ka sha yanzu ga irinta nan sai hauka ka....

Kai daga ina kuke Jafaru ya buga musu tsawa sannan ya haske su da fitila.

Daga gidan wasa muke Aliya tace

KARYA takeyi daga fashi da makami muke ku kama mu kawai ku tafi damu mutum dubu muka kashe bangis yace sannan ya sake yin taga taga kamar zai fadi cikin sauri Aliya ta tare shi.

Inusa na gefe yana jin su cikinsa na kugi warin giyar dake hurowa daga jikin bangis yafara damunsa ji yake yi kamar zaiyi Amai.

Don haka cikin gaggawa yace da Jafaru dan Allah kyale su su wuce yan iska ne kawai zasu bata ma lokaci zo mu karasa can ko zan sami dan wani abu nasa acikina yana gama fadin haka sai yayi gaba.

Jafaru ya dubi Aliya yace idan kuka kara yin dare haka sai mun tafi daku.

Aliya ta dube shi bakinta na rawa tace to nagode yayana bazamu sake ba.

Suka wuce yansandan suma suka wuce suna shiga wata yar kwana sai bangis ya Mike sosai ya daina tangadi sannan yace yi sauri mu karasa nayi wanka.

******* ******* ******* ******* ******* **********

SO nake ki ajiye min jakar nan kafin nadawo bangis yace da ita yana duban ta ido da ido babu alamun fara'a a fuskarsa.
Kusan sa'ar su guda da dawowa tuni har zakarun makwabta sun fara Cara da halama alfijir ya keto kokuma yana dab da fitowa. Suka yi sa'a alokacin da suka shigo gidan babu kowa yan cacar dake farfajiyar gidan duk sun watse kowa Yakama Gabansa don haka babu wata damuwa bangis ya shiga bayan gidan da Aliya ta nuna masa yayi wanka sannan ya wanke kayan dake jikinsa ya shanya su awaje ayanzu da yake zaune yana fuskantar ta daga shi sai gajeren wando kafi shanu wuya yake zaune.

Aliya ta dube shi cikin damuwa a tsorace tace to bazan ce ba zan ajiye ma ba... Amma gaskiya duk da dai kace baka son yawan tambaya ni ina bukatar karin bayani idan kuma bahaka ba to agaskiya baka min adalci ba kuma ka cutar dani domin ka sanya zuciyata cikin wasi wasi da taraddadi... Kaga ban ma san ko kai wanene ba.

Jin haka keda wuya sai bangis ya kyalkyale da tattausar dariya.
Aikin jima da sanin ko ni wanene saidai in so kike na fada miki da bakina ya dan yi shiru sannan saiyaci gaba da cewa in banda abin ki wanene ke yawo da bindiga? Daga jami'an tsaro sai ɓarawo... Ni kuwa ba jami'in tsaro bane.

Aliya ta dube shi cikin kaduwa duk da cewa daman tun farko ta tsammaci haka.
Kana nufin kace min... Kai ɓarawo ne.?

Bangis ya dubeta da dogon kallo sannan ya gyada kai.

Aliya ta sunkuyar dakai sannan saita sami kanta tana mai cewa yanzu kai ko kunya Bakaji ka kira kanka da ɓarawo?

Bangis ya sake fashewa da dariya yace Ai saboda na yarda dake ne saboda nasan bazaki tona min asiri ba saboda kuma ke ma baki boye min kanki amatsayin KARUWA ba don me ni zan boye miki kaina amatsayin BARAWO? Kinsan kowa da hanyar cin abincin sa idan ke bakiji kunyar bayyana hanyar cin abincin ki gareni ba don me ni zanji kunyar bayyana tawa agare ki.?UWAR MUGU-23

Don me ni zan boye miki kaina amatsayin BARAWO?

Kinsan kowa da hanyar cin abincin sa idan ke bakiji kunyar bayyana hanyar cin abincin ki gareni ba don me ni zanji kunyar bayyana tawa agare ki.?

Aliya tayi shiru kamar ruwa ya cinye ta batasan abinda kuma zata ce dashi ba.

To Allah ya kyauta tace sannan ta dubi akwatin dake ajiye akan katifar ta ce menene aciki.?

Bangis ya kalle ta fuskarsa a murtuke yace kina son ki sani ne?

Aliya ta gyada kai.

Bangis ya girgiza kai yace zan iya fada miki ko kuma in nuna miki abinda take ciki amma da sharadi.

Aliya ta dube shi a tsorace tace tace sharadin me?

Sharadin idan nafada miki bazaki fadawa kowa ba idan kuma kika yi haka to duk abinda ya biyo baya kada ki zargeni ki zargi kanki.

Aliya ta sunkuyar dakai na tsahon lokaci can sai ta dago kai tace na yarda fada min... In dai ni zan ajiyeta zan so jin abinda ke ciki.

Bangis ya mika hannu ya janyo akwatin kusa da shi sannan ya danna wani waje ba wuya akwatin ta bude.

Matso ki gani.

Kirjinta na Dakan uku uku ta matso don taga irin bindigogin dake ciki tana lekawa sai taji numfashinta yau dauke bata taba tsammanin abunda zata gani kenan ba duk da dai bata san ko nawa ne ake sayar dasu ba ayanzu amma tasan wadannan ba kananan kudi bane DALOLI ne na Kasar Amurka sababbi fil acike da dan karamin akwatin Aliya tasan dalar amurka domin wani saurayin ta dan birni yataba bata dala dari alokacin batasan menene ba sai ta raina saida taje gurin da ake chanji taga an bata dubu goma sha... sannan mamaki ya rufe ta don haka ganin wannan kudi ayanzu shiyasa taji huhunta yana neman ya toshe iskar da take shaka tafara yi mata karanci indai har abinda idanunta ke gane mata gaskiya ne to wannan kudi idan aka chanza su zuwa kudin Najeriya sun wuce kidaya saidai Malala gashin tunkiya jikinta na rawa taja da baya a tsorace ta dube shi.
Kai bangis a ina ka samo wadannan... Kudi... Haka?

Bangis ya zaro bandir daya na yan dala dari-dari sannan ya mayar da akwatin ya rufe ya dubeta yana wasa da bandirin kudin yace yakamata ki takaita tambayar ki haka domin yafara yawa bazaki so kiji yadda akayi na sami wadannan kudade ba.

Aliya ta gyada kai kamar kadangaruwa tace to Shikenan.

Tsawon lokaci suna zaune suna kallon juna bangis na wasa da dala idanun Aliya akan dala can sai bangis ya mika mata bandir din dalolin dake hannunsa.

Aliya ta dubi bandir din kamar ya mika mata maciji tace..
Iya wannan kawai zan ajiye ma?

Bangis ya girgiza kai yace wannan naki ne shine ladan mutuncin da kikayi min idan kin chanza su zasu kai naira miliyan daya da rabi kudin Najeriya.

Aliya ta karbi kudin a tsorace tana jujjuya su kamar waina.

Bangis ya rufe akwatin ya mika mata yace ga wannan ita nake son ki ajiye min da amana kamar yadda kika ajiye min bindigata idan kura ta lafa kowane lokaci zan zo na karɓa ya dan yi shiru yana nazarin dakin.

Yanzu ina kike tsammanin zaki ajiye wannan batareda wani ya ganta ba? Don Naga dakin naki babu maboya.?

Aliya tayi masa murmushin yake sannan tace kada ka damu zan san inda zan ajiye ma.

Bangis ya gyada kai yace na yarda dake Aliya bazaki yi nadamar taimakona ba yayi shiru yana sosa kyeya sannan yaci gaba da cewa kada ki kara kawo wani kato dakin nan har sai na karbi ajiya ta.

Aliya takuma gyada kai.

Kada ka damu babu wanda zan kawo ta dauke kai cikin sauri domin tasan babu abunda zai hana ta kawo Usman idan yadawo. Duk duniya ayanzu bata ga abinda take so kamarsa ba idan har akwai wani mutum da ta yarda dashi aduniya ayanzu to Usman ne.

Adaidai wannan lokacin sai bangis ya zaro bindigarsa daga aljihun gajeren Wandonsa ya dubi Aliya da fuskar katako yace mai yiwuwa kiyi tunanin guduwa da wadannan kudi kokuma ki hada baki da wani kinsan tsakanin dan adam da kudi sai Allah saboda haka ina mai yi miki albishirin da cewa sai kin gwammace dama ba'a haife ki ba domin daga yanzu duk inda zaki ina kula dake kada ki ga kamar na tafi duk abinda kikeyi ina kallon ki.... Don jiya da daddare kinga alama ko.?

Aliya ta kuma gyada kai jikinta na rawa azuciyarta tana fadin kai na janyowa kaina jaraba.

Bangis ya gyara bindigar dake hannunsa yana kallon Aliya sannan sai fuskarsa ta washe da wani faffadan murmushi.
Kodayake ma ni nasan bazata kai mu ga haka ba.

Ko kusa ko alama murmushin sa bai yaudari Aliya ba yanzu kam ta tabbata wannan saurayi dake gabanta yana iya yi mata komai tabbas tasan bashida imani akwai wani abu a yanayin kallon sa daya tabbatar mata da hakan.

Bangis na lura haryanzu baka yarda dani ba ko.?

Bangis ya fashe da dariya yace Aliya kenan ai a sha'anin kudi ko uwar data haife ni ban yarda da ita ba ballantana ke.

Aliya ta sunkuyar dakai ga mamakinta saita ji duk zamansa cikin dakin ya isheta hakan shiyasa ta sami kanta tana mai addu'ar asuba tayi sauri ta zo ko ya tafi yabar mata dakin. Kwakwalwarta ta cushe ta kasa tunanin komai babu shakka tana bukatar lokaci ita kadai domin ta sami damar yin tunani don rayuwarta na cikin hadari.

DUK FA WANDA YA TAIMAKI ƁARAWO TO SHIMA ƁARAWO NE. Ta fadawa kanta.

********* ********* ********** ******************

Aminu dan lukuti mai katon ciki da dan karamin kai yashigo falon gidan aguje yana jefa kwallo kafa sama yana cafewa babu abunda ya Dame shi.
Shekarunsa bakwai kawai aduniya kuma shine dan auta agidan.

To amma sa'ar daya lura duk kusan kowa a falon zaune yake yayi jugum sai shima hankalinsa yabashi cewa lallai yau babu lafiya don haka sai ya fice aguje yakoma farfajiyar gidan abinsa yaci gaba da wasa yana ihu..

Mutane shida ne acikin falon gidan a cikinsu akwai Samira da yayarta fadila sai kuma mahaifiyarsu da kanwarsu Amira dakuma kawu Hilal da alhaji Hambali babban abokinsa.

Mutanen dake dakin sunyi jugum suna jimamin dimbin asarar data fadawa Alhaji Sambo mahaifinsu Samira.UWAR MUGU-24

Mutane shida ne acikin falon gidan a cikinsu akwai Samira da yayarta fadila sai kuma mahaifiyarsu da kanwarsu Amira dakuma kawu Hilal da alhaji Hambali babban abokinsa.

Mutanen dake dakin sunyi jugum suna jimamin dimbin asarar data fadawa Alhaji Sambo mahaifinsu Samira.

Alhaji SAMBO dogo fari kakkarfa alokacin dayake yaro ya taba yin dambe a kauye kafin daga bisani wani kawunsa a birni ya dauke shi yadawo dashi yasa shi a makaranta mutane dayawa a kauyen su sunyi bakin cikin barin sa dambe domin sunyi hasashen daya ci gaba da yi da babu abunda zai hana ya zamo zakara cikin zakarun damben kudawa.

Lokacin daya kammala karatun sa na sakandire sai ya wuce kai tsaye kwaleji inda yayi difloma a bangaren kasuwanci. Gamawarsa keda wuya sai kawunsa yahada shi da wani abokinsa dake chanjin kudin kasashen ketare ashe abincinsa ne agurin.

Nan da nan sai Allah ya albarkace shi da duk Abunda ya taba saiya zama tsaba cikin dan kankanin lokaci ya zama miloniya sannu ahankali likkafa taci gaba don haka saiya bude wani katon kamfani a Abuja na chanjin kudin kasashen ketare.

Harka taci gaba da tafiya shekara da shekaru kullum sai dada gaba yakeyi arzikinsa na ta hauhawa bai taba haduwa da masifa ba sai Awannan yammaci da yan fashi sukayi masa dirar mikiya.

Alhaji Sambo yana cikin ofishin sa a zaune ya gama sallamar wasu bakin turawa alokacin wasu yaransa suna can cikin babban falo suna lissafin kudade kawai kamar daga sama saiyaji wani ya kwada kara sannan saiyaji shiru ba'a jima ba sai ya gansu sun shigo ofishinsa cikin sauri su biyar ne hudu daga cikin su jibga jibga ne kamar giwaye dayan kuma dan siriri ne bashida kauri kowanne su da bindiga.

BAMU DALOLIN.... Wani mai murya kamar aradu yace dashi.
Alhaji Sambo ya kasa magana saboda tsananin kaduwa jikinsa na rawa ya dubi wata akwati dake gabansa babu komai acikinta sai daloli a makare.

Wani daga cikin yan fashin ya lura da cewa duk hankalinsa yana kan akwatin don haka baiyi wata-wata ba sai kawai ya matso yasa gindin bindiga ya doki tsakiyar kan alhaji Sambo lokaci guda kuma ya dauke jakar dalolin ya Mikawa dan siririn cikinsu anan take alhaji Sambo yafadi fuskarsa ta kife akan teburinsa a sume. Iya abinda zai iya tunawa kenan.

Bayan da alhaji Sambo ya farka a asibiti ne ya samu labarin cewa Tsofaffin sojojin da suke gadinsu sun kashe hudu daga cikin yan fashin har ma sun kwace buhun nairorin da suka dauka amma daya daga cikin yan fashin ya gudu da akwatin kudin da suka dauka a gurinsa. Jim hakan keda wuya sai alhaji Sambo ya sake sumewa akan gadon asibitin domin yasan sun kashe shi ya riga yayi mutuwar tsaye. Ayadda ya karanta a jarida ance wai yan fashin sun tafi da kudi sama da Naira BILIYAN GUDA.

Amma shi yasan kudin sun haura Naira BILIYAN BIYAR kwanaki kadan da farfadowarsa aka mayar dashi gida domin ya dan huta sannan jami'an tsaro suka ci gaba da neman dan fashin daya tafi da kudin amma har zuwa wannan lokaci shiru makatau balaguron lahira babu labarinsa.

Don haka ayanzu dasu Samira da yan uwanta ke zaune jugum kowa yayi tagumi jimamin halinda alhaji yake ciki sukeyi don tun da asuba yake sambatu abun har yafara zame masa kama da tabin hankali. Daya farka saiya buga wayar ofishin yan sandan ciki dake Abuja idan akace dashi ya dada hakuri babu labari saiya fashe da kuka saikace kankanin yaro idan yagama kukan sai yayi ta sambatu kamar mahaukaci.

Bawani abu ne ya sashi cikin wannan mummunan hali ba sai tunanin yadda zai yi da dukiyar jama'a dake hannunsa domin sama da kashi saba'in daga cikin dari na kudin da aka sace na jama'a ne ba nasa bane idan har ba'a kama dan fashin daya dauki kudin nan ba to shi kam yagama talaucewa.

Samira ta mike tsaye daga cikin yan uwanta sannan ta nufi dakinta ta rufe kana ta kwanta rigingine tana kallon sararin samaniya.

Hankalin Samira yafi na kowa tashi idan har baban mu ya tsiyace to na shiga uku ta fadawa kanta idan akwai abinda take tsoro fiyeda komai aduniya to talauci ne wannan na daya daga cikin dalilin dayasa ma ta guji Usman duk kuwa da cewa shi tafi so acikin samarinta to amma ita akullum kudi ne farko a zuciyarta saikuma duk wani abu da zai biyo baya. Yanzu kam tafara nadamar dama tuntuni ta zabi miji anyi mata aure gashi yanzu talauci yana neman ya mamayi gidansu
Shikenan bikina ko fati baza'a yi ba?
Ta tambayi kanta sannan cikin sauri ta kawar da wannan tunanin daga cikin zuciyarta.

USMAN. Ta furta sunan cikin zuciyarta wai shin menene illarsa? Rashin kudi ta ba wa kanta amsa.
To ai idan kudi ne baba yana iya bashi indai har ya aureni. Takuma fadawa kanta nan da nan sai taji zuciyarta tana mai karkata akan Usman duk dai wani kame kame tagama amma haryanzu bata ga wanda yayi mata ba kamar Usman kuma ta fahimci indai har bazata sauya ra'ayi ba to saidai ta auri mai kudi wanda bata so kokuma ta hakura da talauci ta auri Usman dinta da take so.

Samira ta muskuta akan gadon cikin damuwa tana murkususu cikin nadama. Abunda yafi damun ta ayanzu shine hanyar da zata bi ta lallami Usman tasan ba karamin rashin mutunci tayi masa ba Rudin shaidan ne kawai ta fadawa kanta Awannan lokaci sai dabarar yadda za'a yi ta lallami Usman yafado mata jikinta na rawa ta dauki waya da niyyar zata kira Usman sai ta tuna ashe ta goge lambar cikin sauri ta sauko daga kan gadon ta nufi falo tasan baza'a rasa lambar Usman ba agurin yayarta Fadila Jim kadan ta samo lambar sannan ta dawo kan gado ta kwanta rigingine ta kara wayar a kunne wayar tafara ruri acan daya bangaren.

******* ******* ******** ******** ***** **********

Usman ya bude idanu a firgice lokacin da motar su tafada cikin wani katon rami.

Indararo ya dube shi yayi murmushi kaidai ka cika tsoro.

Usman yayi dariya yace ai dole ne naji tsoro saboda tunda nake bantaba ganin bala'i irin na ranar nan ba.

Kwanaki hudu da suka gabata a hanyar su ta zuwa Ikko suka sami wasu mutane goma sha uku barayi sun yi musu yankan ragoUWAR MUGU-25

Kwanaki hudu da suka gabata a hanyar su ta zuwa Ikko suka sami wasu mutane goma sha uku barayi sun yi musu yankan rago.

Wannan al'amari ba ƙaramin tashin hankalin Usman yayi ba a ranar har suka shiga Ikko baici abinci ba Indararo yayi ta bashi baki akan ya fitar da abin daga ransa yaci abinci domin irin wannan ba wani sabon al'amari bane saidai Idan baka bin hanya zuwa kudancin Kasar nan.

Kwanansu biyu a ikko aka sauke musu lodi ga al'ada mafi yawan wadanda suke Rakiyar kayan ridin da an sauke kayan sai su shiga motar haya su taho gida abin su to amma dayake Usman yana son ya sake ganin kyakkyawar fuskar nan ta Aliya sai da ya sake jira har Indararo yayi lodin wasu kayan masarufi sannan ya biyo shi suka kamo hanya amma a tsorace duk sa'in da ya ji sun fada rami saiya zabura kai akwai lokacin da ko chanjin giya Indararo yayi idan motar yayi zillo sai Usman ya zabura a tsorace.

Wai haryanzu bamu kusa ba.? Usman ya tambayi Indararo.

Ka matsu muje ko? Lallai na fahimci Aliya ta same ka inda take so.

Eh to haka din ne amma da gajiya ma wallahi ji nake kamar kuguna zai cire yafadi ya danyi shiru yana tunanin Aliya kusan kullum sai tayi masa waya kamar sau uku wata sa'ar ma sai ya farka daga barci zaiga ashe ma takira cikin dare tun baya kira har dai yafara kiranta shima ayanzu haka zaman da ake ciki ya kashe sama da Naira dubu daga cikin dubu goman da aka bashi a kamfanin Ridin.

Ai nan da karfe bakwai ko takwas na dare in Allah ya yarda muna cikin TAFA.

Usman yaji gabansa yafadi idanunsa suka zazzaro.
Kai... Chab Kace da sauran tafiya?

Kwarai kuwa gara ma ka koma ka kwanta abin ka tafiyar tafi ma sauri.

Usman yakoma ya jingina bayansa da jikin kujerar sannan ya lumshe idanu.
Wayarsa ta dauki ruri cikin mamaki ya dauko wayar.

Indararo ya dube shi da murmushi yace mutumiyar ce ko?

Usman ya gyada kai kaima ai ka sani yanzu haka so take taji ko mun kusan zuwa.

Ai fa kai ka hadu da aiki. Indararo yace adaidai lokacin da ya rage gudu ya kaucewa wata barewa data fito daga cikin dajin aguje ta tsallaka titi
Usman ya dauki wayar zai kai kunnen sai yaga sunan dake fuskar wayar bana Aliya bane gabansa yafadi sa'ar daya ga SAMIRA.

Abin yabashi mamaki abubuwa dayawa sun faru cikin kwanaki shida tun lokacin da yayi ido biyu da Aliya bai sake tuno da Samira ba sai yanzu.

Cikin tsananin mamaki saiya danna wajen amsawa kana ya kara wayar a kunne a zuciyarsa yana cewa ko wane cin mutunci kuma zata yi min?

Hello... Yace bakinsa na yar rawa.

Usman.... Sannu.. Ina kwana? Samira tace acan daya bangaren amma da sauri sauri.

Mamaki ya kama Usman wai Samira ce ke cewa dashi ina kwana......?

Lafiya Samira ya danyi shiru.

Usman.. Samira ta kira ji jin yayi shiru.

Ina jinki.

Oh to ya kayi shiru?

Abin ne yabani mamaki bantaba tsammani ba.

Samira tayi shiru na yan dakiku sannan tace.
Gaskiya ne ai bakada kirki.

Usman yaji zuciyarsa ta harba yanzu shi zata cewa wai bashida kirki?

Nine banida kirkin Samira?

Eh mana in banda rashin kirki ba yanzu saboda Allah mugun abin nan daya sami babana amma ko ka bugo waya kayi min jaje Haba ai ko gaba muke ka kira ni kayi min Allah ya kiyaye koda bai kai zuciya ba.

Meyafaru da baban? Usman ya tambaya cikin mamaki.

Oh baka ma san abinda ya same shi ba bayan duk abin ya cika gari?

Ai bana gari.. Nafi kusan sati bana gari.

Haba gaskiya fa shiyasa ashe to shikenan na yafe ma tunda baka sani ba da har zanyi fushi dakai.
Ta dan shi shiru sannan tafara fada masa abinda ya sami mahaifinta.

Usman yaci gaba da saurarenta cikin mamaki shin me ya sami Samira ne ko ta gane abinda tayi masa bata kyauta bane.? Abinda ya tabbatarwa da kansa shine Samira bawai ta kira shi ne don kawai ta fada masa matsalar da mahaifin su ya shiga bane. DA AKWAI WANI KWAKKWARAN DALILI ....

BABI NA SHIDA

Kimanin sa'o'i tara da suka wuce kafin wannan al'amari acan garin Tafa Aliya tana cikin dakinta tana fama da wani saurayinta tsohon dan giya..

Karfe biyu saura yan mintuna na dare Aliya ta........UWAR MUGU-26

BABI NA SHIDA

Kimanin sa'o'i tara da suka wuce kafin wannan al'amari acan garin Tafa Aliya tana cikin dakinta tana fama da wani saurayinta tsohon dan giya..

Karfe biyu saura yan mintuna na dare Aliya tana zaune ita kadai acikin daki tayi jugum abin duniya ya isheta Badon komai ba kuwa sai don halin zullumin data shiga tun bayan Rabuwar ta da bangis tariga tayi imani da cewa rayuwarta tana cikin hadari ada lokacin da suka fara haduwa ta dauka saurayin mutumin kirki ne har ma yafara burge ta amma ayanzu daya bayyana mata kansa saita lura da cewa akwai wani abu acikin idanunsa dayake bata tsoro a washegarin ranar daya bata ajiyar kudin bata iya hada idanu dashi ba har ya tafi.

Yanzu Abunda yafi damunta shine rashin yanci domin na farko dai ya hanata kawo kowa cikin dakinta na biyu kuma shine babu dama tayi nisa da dakin don gudun kada bata nan wani dan iskan ya shiga ya dauke ajiyar da aka bata don lokaci- lokaci Daman akan yi mata yan dauke dauke acikin dakin to amma dayake tasan ba wani abin kirki ne acikin dakin ba bata damu ba yanzu al'amura sun canja an bata ajiyar kudi fam taba sama Malala gashin tunkiya don haka ko cikakken barci bata iya yi ko bera ne yayi motsi sai ta farka ta zauna

Please Login or Register in order to submit comment