Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannan ta dubi inda jakar take.

A irin wannan lokacin ne tana kwance tana juyi ta kasa barci kawai sai taga an banko kofar dakinta da karfi Aliya ta tashi firgigit saita ga ashe ABASHE ne.

Me ye haka fita min daga daki bana son rashin mutunci.

Anki a fita din Abashe yace yana tangadi kamar zai fadi hamamin giya sai tashi yake a jikinsa.

Aliya ta mike tsaye a fusace ta dube shi wani zamanin kadan daya wuce sun taba abota alokacin bai lalace kamar haka ba.

Kafita min daga daki kaji.. Ba ruwana dakai.

Anki nace nida ruwana dake anan zan kwana yana gama fadin haka sai yafada kan katifar da niyyar kwantawa sai kafarsa ta daki tsohuwar Fanteka. Nan da nan sai fantaker tafadi jaka baka ta fado daga ciki.

Ke dan uban ki ina kika samu jaka haka mai kyau?
Abashe yace sannan cikin zafin nama na ban mamaki saiya sa hannu ya zari jakar.

Aliya taji yawun bakinta ya kafe ta dubi jakar dake hannunsa jikinta yafara rawa.

Kai menene haka aciki... Mai nauyi... Ko kudi ne... Kodayake shegiya matsiyaciya ina zaki sami kudi?

Yakoma ta kwanta kafin kifitawa da bisimillah ya fara munshari da jakar ahannunsa.

Aliya tayi tsaye a tsakiyar dakin jikinta na rawa kamar mazari daman saida da yi tunanin haka tun farko taso ta fadawa bangis cewa akwai hadari ta ajiye wadannan makudan kudaden Awannan dakin nata da babu gurin buya Awannan lokacin ne ta yanke shawarar ta fitar da kudin daga dakin domin idan ta hana wani shigowa wasu bata isa ta hana su ba don haka jikinta na rawa ta dauki hijabinta tasa sannan ahankali ta janye jakar kudin daga hannunsa tasa jakar acikin hijabinta ta fita da sauri tabar Abashe yana munshari.

Karfe biyu da mintuna goma sha uku ta isa kofar gidan uwani. Bata sha wata wahala ba bugu daya sai ga uwani uwar mugu a kofar gidan ta bude itama bata jima da shigowa gidan ba ta dubi Aliya cikin mamaki.

Lafiya Aliya naganki da uban hijabi cikin dare... Ko SHARI'AR MUSULUNCI ce mu ma tazo mana nan?

Aliya ta girgiza kai cikin damuwa sannan tace mu shiga daga ciki.

UWAR mugu bata yi musu ba sai ta juya Aliya tabi ta abaya.

Bayan sun zauna suna fuskantar juna sai Aliya tafito da jakar daga cikin hijabinta ta ajiye agaban uwani sannan ta sunkuyar dakai.

Toh ya akayi? Uwani ta tambaya tana kallon ta cikin zargi sannan ta dubi jakar dake gabanta.

Amana ce aka bani to kuma ni naga ajiyar ta awurina akwai hadari saboda kinsan irin yan iskan dake zuwa gidan mu yanzu haka ma Abashe ne yashigo ya tayar min da hankali to shine nace bari na kawo miki ajiya kafin mai ita yadawo... Wasu takardu ne masu muhimmanci aciki... Wani saurayina ne dan boko yakawo min ajiya.

Uwani tafara nazarin fuskar Aliya cikin mamaki shin me ya tsorata ta haka indai don wannan ne me zaisa ta acikin tashin hankali haka saboda kawai an bata ajiyar wasu takardun banza na boko? Uwani ta tambayi kanta.

To Shikenan ai don wannan babu matsala har kin tayar min da hankali wallahi na dauka ma wani abu ne...

Aliya tayi dariyar karfin hali ta girgiza kai
Bakomai wallahi wannan dan iskan ne Abashe yabata min rai shiyasa kika ganni haka.

Uwani ta gyada kai tace hakane amma aranta tasan Aliya karya takeyi akwai wani abu dai amma tunda akwatin tana hannunta zata gane ko ma dai menene.

MINTUNA UKU DA FARUWAR WANNAN ALIYA TA KOMA GIDA.

Babban ladanin masallaci daya jal dake unguwar ya kwalla kiran sallar farko

Uwani tayi mika gamida hamma. Tunda Aliya ta tafi bata kwanta ba tana nan zaune kamar an dasa ta tana ta Sakar zuci sau biyu tana tashi da niyyar ta bude akwatin saikuma wata zuciyar tace da ita Um Um uwani kada ki sha wahalar banza takardun wofi ne kawa aciki.

Lokacin da taji an sake kiran sallah na biyu sai taga bazata iya jurewa ba tabbas tunda ta kasa barci akwai wani abu a tattare da akwatin nan tacewa kanta sannan saita mike tsaye ta dauko akwatin ta dawo kan katifar ta zauna kana ta fara jujjuya akwatin ahannunta tana neman ta inda zata bude.
Ba'a dade ba saita ga wani koren dan madanni uwani ta kai dan yatsanta kan koren madannin zuciyar ta na harbawa das das das tana dannawa sai akwatin ta bude abin kamar aikin aljanu saita yi ido biyu da daloli fal aciki.

Uwani tayi mutuwar tsohuwa saida tayi sama da mintuna arba'in kafin ta iya motsawa jikinta na rawa ta Mike tsaye sannan tafara safa da marwa a farfajiyar dakin tana kallon dalolin dake cikin akwatin. Ni Daman nasan a Rina ta fadawa kanta kai da ganin yada fuskar yarinyar nan ke gumi nasan da walakin goro a miya.

Uwani ta share gumin daya fara sartu akan fuskarta wannan ita ce damar dana dade ina jira KUDI BA.

Da wannan kudin duniya zata iya dawowa kan tafin hannunta duk da dai uwani batasan adadin dalolin dake cikin akwatin ba amma tayi mahaukacin kiyasin cewa idan aka canza dalolin zuwa kudin Najeriya sai ta cika dakin.

Tunanin farko daya fara zuwa zuciyarta shine ta dauki jakar kudin nan bakinta Alaikum ta gudu tun kafin gari yayi haske to amma sai wani tunani yazo mata kwarewar ta dakuma yawan mu'amala da yan duniya da barayi su suka sa tafara tunanin cewa tabbas ko wanene yakawo wa Aliya ajiyar kudin nan shima sato su yayi tasan babu wani mutumin kirki da zaizo ya baiwa karuwa ajiyar naira dubu hamsin ma ballantana wadannan makudan kudi.

Wani tattausan murmushi ya bayyana akan fuskar uwani uwar mugu nasan me zanyi tace cikin ranta.
Sannan sai ta ace a fili ai babu shaida lokacin data bani kudin tana gama fadin haka sai ta fita waje.

Idanunta sun fara nauyi barci na barazanar rufe mata idanu cikin sauri saita dauki ruwa mai sanyi daga cikin wata randa ta kwarara wa kanta ta girgije sannan ta zagaya bandaki Jim kadan sai ga ta da DIGA ahannu ba tare da bata lokaci ba ta nufi gindin wata bishiya dake farfajiyar gidan inda wani katon turmi yake ta janye turmin gefe guda sannan saita kunce zanin dake kugunta tayi daurin kirji sannan ta dauki digar nan tafara haka rami a gurbin da gindin turmin yake.

****** ****** ****** ******** ******* ************

Ba kamar yanda Indararo yayi tsammani ba tun farko basu sami isowa cikin garin Tafa ba sai wajen karfe goma da yan mintuna suna isowa sai Indararo ya dubi Usman da murmushi yace zaka gane gidan mutumiyar taka ne?

Usman ya girgiza kai yace bazan gane ba amma bari na kira ta.

Indararo yafito daga motarsa ya rufe adaidai lokacin da Usman yafara magana da Aliya.

Yaya ka same ta? Indararo ya tambaya

Eh gata nan tace na jira ta anan zata zo mu tafi.

To Shikenan kada dai ka biye mata ka makara don gobe Karfe shida zamu kama hanya.

Usman ya dube shi da murmushi yace kaifa ka cika fassara da yawa.

Indararo ya fashe da dariya sannan ya kunna sigari Yakama Hanyar zuwa cikin garin abinsa..

ALIYA ANYA BAKIYI KUSKURE BA KUWA?UWAR MUGU-27

Usman ya dube shi da murmushi yace kaifa ka cika fassara da yawa.

Indararo ya fashe da dariya sannan ya kunna sigari Yakama Hanyar zuwa cikin garin abinsa..

Usman zaune yana fuskantar Aliya cikin mamaki don yaa fuskanci hankalin ta a tashe yake matuka domin babu irin walwalar nan daya gani farkon haduwar su hakanan duk dayake akwa duhun dare ya lura da cewa kamar ma ta dan rame duk sa'in daya dauko hira saiyaji Aliya ta yanke hirar ta hanyar gyada masa kai kawai abin ya zame masa biyu daman yana ta tunanin halin da Samira tace mahaifinta ya shiga yazo garin gashi kuma Aliya wacce yake jin dadin hira da ita tayi masa shiru.

Ganin har yanzu Aliya bata bashi wata kyakkyawar kulawa ba sai Usman ya mayar da zuciyarsa kan tunanin abinda Samira ta fada masa.

Indai har abinda tafada masa gaskiya ne to lallai mahaifinta ya hadu da babbar jaraba. Usman ya tausaya masa domin duk dayake Samira bata taba yarda takai shi kusa da mahaifinta ba amma ya lura makwabta suna yabonsa to amma abinda yafi damun zuciyarsa shine dalilin dayasa Samira takira shi domin tabbas yasan bawai don kawai tafada masa anyi wa mahaifinta sata bane yasa ta kira shi..

Usman yayi ajiyar zuciya sannan ya dubi Aliya yace wai me ke damun ki ne duk kin sauya sam- sam bakiyi min kama da Aliyar dana sani kwanaki biyar da suka wuce ba.

Aliya tayi murmushin yake ta sunkuyar da kai.

Kinyi shiru ba kice komai ba in kuma zuwan nawa ne ya Dame ki bari na tashi na fita babu mamaki na tare miki hanya. Ya Mike tsaye ransa a bace.

Aliya ta dube shi cikin sauri tace ka gafarce ni don Allah... Wallahi Usman akwai abinda ke damuna kuma Idan kaji shi zaka fahimce ni.

Usman ya tsaya yana dubanta.

To ai saikiyi min bayani.

Abin ne akwai matsala.

Matsalar me?

Aliya ta dube shi labarin ba zai fadu ba har sai ka min alkawarin bazaka fadawa kowa ba.

Usman ya dubeta cikin mamaki sannan yakoma ya zauna yace wannan wane irin abu ne da har sai na dauki alkawari za'a fada min?

Kanta a sunkuye tace zan fada ma Usman domin ayanzu aduk duniya banida wanda hankalina ya kwanta dashi kamar ka tunda kai kana da Ilmi nasan bazan sami matsala ba idan nafada ma mai yiwuwa ma ka bani shawara ko?

Usman yayi shiru yana dubanta kawai a rude.

Aliya ta muskuta cikin damuwa.

Ina sauraren ki Usman yace yana dubanta cikin mamaki azucutarsa yana fadin yanzu haka wani shashashan ne acikin mutanen su yabata mata rai.

Aliya tayi ajiyar zuciya tafara....
Ka tuna ranar da wani yayi min waya muna tare dakai har ka........

****** ******* ******** ******** ******* *********

Tun karfe goma sha biyu saura suka shigo kanon dabo Usman yayi sallama a gurguje da Indararo sannan ya wuce gida kai tsaye.

Babu hasken rana. garin yayi dadi sakamakon bakin gajimaren daya rufe fuskar rana wannan shiya baiwa jama'a damar yawatawa cikin jin dadi ba kamar jiya ba inda aka wuni ana zuba rana jama'a kamar zasu soyu da ransu

Usman yana tafe abayan mashin yana ta tunani shi bai ma san ana zafin rana ba kokuma lullumi ba.
Ahaka har aka zo kofar gida ya sauka.

Bayan ya huta yayi wanka suka gana da mahaifiyarsa da yan uwansa sannan yafito kofar gida yasa benci ya zauna yafara tunanin abinda Aliya ta basu labari abin yafi kama da almara.

Lokacin da Samira ta bashi labarin tsautsayin da ya sami mahaifinta bai yi niyyar zuwa mata jaje ba don ayanzu Allah daya kawai samira zata ce ya amince da ita bayan cin mutuncin da tayi masa satin daya gabata to amma ayanzu yafara tunanin lallai zuwa jaje ya kama shi Badon wai Samira ba sai don wani abu dayake son ya tabbatar.

Usman yaci gaba da juya labarin da Aliya tafada masa jiya da daddare Idan har abinda tafada masa gaskiya ne to lallai babu shakka yanzu haka kudin mahaifin samira yana dakin uwar mugu.

kai shashasha wata zuciya tace dashi mutum nawa ake yiwa fashi aduk kwanan duniya? Kuma Shikenan kawai don kaji ɓarawo yakawo ajiyar kudi saikace na mahaifin samira ne? Usman ya muskuta cikin damuwa abunda zuciyarsa take fadi gaskiya ne ya fadawa kansa yanzu haka ma ba abunda yake tunani bane to amma ai Samira tace dashi daloli ne cikin wata jaka abin kuma da Aliya tace dashi ke nan.... Acikin Abuja aka kwaci kudin nan menene marabar TAFA da ABUJA babu nisa sosai kai lallai biri yayi kama da mutum.

Ajiya dai sun rabu da Aliya akan cewa zai dawo nan da sati guda idan yayi musu tunanin abunda ya kamata tayi.

Usman ya san karya yakeyi domin babu wani abu da zai sake mayar dashi Tafa don ya lura duniyar bariki ba irin tasu bace koda zai koma tafa to ba zai koma bangaren su UWAR MUGU ba.

Usman yaci gaba da jujjuya abubuwan cikin ransa can wajen goshin azahar sai dabara ta fado masa nan da nan ya dauki waya ya Danna lambar Samira.
Hello Samira nadawo...

Oh Usman sannu da zuwa wallahi har Naji dadi yanzu kana ina? Samira ta tambaya daga can bangaren cikin doki.

Ina gida ina tunanin ko nazo ne nayi....

Kazo kawai idan anyi sallar la'asar ina jiranka Samira ta katse shi.

Usman ya ajiye wayar sa cikin mamaki shin me ya sauya ra'ayin samira ne?

Da magariba sa'ar da Usman ya isa gidansu Samira saiya isketa tayi wanka taci ado tana jiran sa abin yabashi mamaki. Sannan ga dadin mamakinsa sai Samira tasa ya shiga daga ciki ta kai shi wani makeken dakin shakatawa mai kamar filin wasan kwallon kafa.

Iko sai Allah. Usman yafada cikin ransa tunda suke bata taba shigo dashi har cikin gida ba.

Usman kenan yaya hanya? Samira ta tambaya.

Mun godewa Allah.

Wai me ya kai ka Lagos ne?

Usman ya danyi murmushi yace NEMAN AIKI NA TAFI.

Samira taji gabanta yafadi sa'ar data tuna sakon wayar data aika masa nan da nan taji tana mai kunyar hada idanu dashi.

Samira baba yana ciki ne? Usman ya tambaya.

Samira ta gyada kai cikin murmushi azuciyarta tana fadin wallahi na kusan na cuci kaina Usman kyakkyawa ne.

Yana ciki amma da baki kasan haryanzu ana ta zuwa masa jaje.

Usman ya dan yi shiru Samira ta dube shi cikin damuwa a tunanin ta ko abinda tayi masa ne yasa yake dari-dari da ita.

Usman ka saki jikin ka abinda ya wuce ya riga ya wuce.

Usman ya girgiza kai yace ni ba abinda ke damuna kenan ba ya dan yi shiru sannan yaci gaba da cewa satar da aka yiwa baba ita ke damuna.

To ya za'a yi.. Haka Allah yaso ya jarrabe mu.

Usman ya sunkuyar dakai sannan ya tausasa murya yace kince kudin da aka sace acikin akwati suke ko?

Samira ta shafi dogon hancinta tace Eh acikin akwati suke daman na sha fada masa ya daina zuba kudi acikin akwatin nan saboda tsohon yayi ce amma ya nace mata wai kawai saboda ya gaje ta a wajen wani kakan mu Samira tayi tsaki gamida tagumi.
Kasan Tsofaffin nan sun cika gardama yanzu gashi nan muna zaman mu lafiya ya janyo mana talauci.

Usman yayi Allah wadai da ita a zuciyarsa abunda tace ko Aliya dake zaune a tsakiyar bariki bazata fadi irin wannan kalamai akan mahaifinta ba.

Koda ya dubeta sai yayi mamakin abinda yasa tun farko ma yake kaunar ta.

Wace irin akwati ce wannan?

Samira ta kashe masa idanu cikin kisisina ta tabe baki sannan ta Mike tsaye wata tsohuwar akwati ce baka irin ta iyaye da kamanni nan bari na dauko ma kaga yadda take akwai wata irin ta agida daga can ma sai na dauko ma abin sha ta fice daga falon.

Usman na nan zaune kirjinsa na Dakan uku uku jim kadan Samira ta dawo dauke da wata bakar akwati ta ajiye akusa dashi.

Gata nan yanzu saboda Allah idan ba alhaji ba wanene zai zuba kudi anan?

Usman ya dauki akwatin ya kura mata idanu a zuciyarsa yana kokarin bijiro da irin kamanni waccen akwatin da Aliya ta bashi labari tabbas kamar irinta ce.

Je ki dauko min abin sha don Allah Naji bakina duk ya bushe.

To Samira ta amsa cikin gaggawa duk dai don kokarin ta faranta masa.

Tana fita sai Usman ya dauki wayarsa cikin sauri ya buga lambar Aliya ya kara a kunne.

Hello Aliya tace daga can bangaren...

Saurara da kyau Aliya... Ahhh... Wai akwatin kudin nan da kika bani labari an kawo miki ajiya tana da wani abin dannawa KORE....

Eh tana dashi menene

Usman bai amsa mata ba sai yace akwai wani abu kamar daurin kalangu a tsakiyar da wani jan kyalle ko? Usman ya tambaya yana kallon akwatin da ke hannunsa.

Eh hakane wai menene

Usman yaji numfashinsa ya fara daukewa...UWAR MUGU-28

Usman bai amsa mata ba sai yace akwai wani abu kamar daurin kalangu a tsakiyar da wani jan kyalle ko? Usman ya tambaya yana kallon akwatin da ke hannunsa.

Eh hakane wai menene

Usman yaji numfashinsa ya fara daukewa.
Babu komai... Ah...wata akwatin kakana ce nan nagani shine na tuno da labarin da kika bani saboda akwatin kudin nan ta tsaya min Arai.

Aliya tayi dariya Usman kenan ai kudin ne na cizo ne ta dan yi shiru Yaushe zaka zo din kaifa nake jira kuma wallahi nayi missing dinka.

Nan da sati biyu kamar yanda nafada miki ke dai ki kwantar da hankalin ki ina nan ina tunani yana gama fadin haka bai jira tace wani abu ba sai yayi maza ya kashe wayar sa don baya bukatar wani dogon bayani daga bayanin ta.

Samira ta shigo dakin dauke da farantin kayan shaye shaye.

Usman ya mike tsaye.

A'a ina kuma zaka ga shi na kawo ma abin sha zaka tashi?

Bakomai muje ciki nayiwa alhaji jaje.

Samira ta ajje farantin tana kallon sa cikin mamaki tace to kafara sha mana tunda kana jin kishi in ka gama ba sai mu shiga ba.

Usman ya girgiza kai yace gaskiya idan nayi haka ban kyauta gara mu dai shiga din na gaishe shi sai mu dawo.

Samira cikin mamaki ta wuce gaba Usman ya bita abaya.

Alhaji Sambo zaune abakin wani katon gado dauke da kofi a hannunsa yana shan wani abu sanye yake da babbar riga kansa babu hula hakanan gajeren wando ne a jikinsa idanunsa sunyi jazur alamun ya dade bai runtsa ba ya dubi Usman cikin mamaki domin baisan shi ba acikin yan uwansu amma Samira tace wani ne yazo wai zaiyi masa jaje.

Yanzu haka dan makwabta ne ya fadi a ransa ya riga yasan duk unguwar babu labarin da akeyi ayanzu sai na asarar da yayi.

Sannu baba.. Yaya Akaji da wannan abu?

Mun gode Allah ya amsa kai tsaye.

Wannan jaje duk ya gama isar sa babu abunda yake saurare ayanzu daya wuce akawo masa labarin an kama yan fashin nan.

Usman yaa lura halinda yake ciki don haka saiya tausasa murya yace bakinsa na rawa baba.. Ina tunanin nasan inda kudin ka suke.. Banida tabbas amna ina zaton yakamata a bincika.

Kadan ya rage alhaji Sambo ya fado daga kan kujera saboda kaduwa.

Uhm.... Me kace sake maimaitawa banji ka ba sosai yaro.

Nace ina tsammanin nasan inda kudin ka suke ayanzu haka.

Alhaji Sambo ya dauki waya ya fara kira yana yiwa jami'an tsaro magana cikin ƙaraji.

****** ******** ******** ******** ******* ********

Ruwa yafara sauka kadan kadan hadari ya lullube sararin samaniya gashi babu wuta a unguwar yayi bakikirin da kyar mutum yake iya ganin ko da tafin hannunsa.

Aliya ta biyo lungun cikin sauri tuni har ruwa yafara wanke mata fuska sanye take da doguwar riga sabuwa data saya.
Kasan rigar wando ne jeans baki sannan kyakykyawar kafafunta sanye cikin takalmi fari mai tsinin dunduniya lallai kudi da dadi suke tafada cikin ranta duk kuwa da cewa kullum kwanan duniya a tsorace take.

Aliya taci gaba da tafiya dauke da wata bakar jakar leda ahannunta biredi ne da madara aciki.

Adaidai lokacin data kawo Kwanar wani lungu ne aka saki wata katuwar tsawa sannan wani walkiya ya haskake duk farfajiyar gurin.
Sannan ne to ta hange shi tsaye cikin wata rumfar kwano hannayensa cikin aljihunsa sanye yake da katuwar riga mai gashi irin na sanyi da'ace bata tunanin ganinsa ako wacce sa'a da babu abunda zai sa ta gane shi amma dayake kullum dashi take kwana Arai kallo daya tayi wa surarsa cikin duhu ta gane shi.

Aliya ta yi turus tana kallon sa cikin duhun adaidai lokacin data fara tunanin ko kuskure tayi saita ga ya nufo inda take saida ya matso kusa sosai ta lura ashe ma wai murmushi yake yi.

Ashe dai zaki gane ni ko da acikin duhu? Bangis yace da tattausar muryarsa.

Aliya taji bakinta ya kafe.

Kiyi hakuri nazo miki a wani irin lokaci ko.? na zo karbar ajiyar dana baki ne.

Aliya tayi sororo a tsorace tana kallon sa ta rasa abinda zata ce masa bata taba tsammanin zai dawo haka da wuri ba.

Kinyi shiru muryar sa ta katse mata tunani.

Aliya ta rasa abinda zata ce dashi don haka saita wuce gaba tace zo muje na baka lokaci guda kuma tana ta zullumin yadda zata sanar dashi cewa kudin basa gurin ta.

Bangis ya fashe da dariya sannan yace Haba Aliya bansan ki da karya ba me zai hana ki fada min gaskiya... Nasan fa ajiyar bata gurin ki shiyasa ma na dawo da wuri domin ban amince da inda naga kin kai ta ba ni Daman tunda na ganki da hijabi cikin dare nasan akwai matsala.

Aliya tayi mutuwar tsohuwa agurin bakinta na rawa ta dube shi.

Kana nufin kace duk abinda nake kana gani na?

Kwarai kuwa Koda wanka kika shiga.

Aliya ta dube shi cikin kaduwa na tsayin lokaci Takasa cewa komai.

Ganin ta kasa magana sai bangis yace muje mana inda kika bayar da ajiyar ki karbo ki bani abina.

Aliya ta juya babu musu ta nufi gidan uwar mugu bangis na biye da ita abaya.

Aka saki wata katuwar aradu kamar zata tsaga sararin samaniya gida biyu..

1. YANZU YAYA USMAN ZAIYI TUNDA AN AMSHE AJIYAR.?

2. YANZU YAYA ALIYA ZATAYI IDAN UWANI TACE BATA KAWO MATA AJIYA BA?

3. YANZU WANI MATAKI BANGIS ZAI DAUKA DON KARBO KUDINSA?

4. IDAN AKAZO BA'A SAMU KUDIN BA YAYA ALHAJI SAMBO ZAIYI

5. MENENE MAKOMAR SOYAYYAR SAMIRA DA ALIYA AGURIN USMAN.?UWAR MUGU-29

Aliya ta juya babu musu ta nufi gidan uwar mugu bangis na biye da ita abaya.

Aka saki wata katuwar aradu kamar zata tsaga sararin samaniya gida biyu.

****** ******* ******* ******* ******** **********

Tun daga ranar da uwar mugu tayi ido biyu da kudin nan bata sake dafa abincin sayarwa ba kafin ta boye kudin saida ta zari wasu adadi ta canza su a wajen wani mutum ta sami akalla dubu dari don haka kullum tana gida abinta tana barci babu abunda ya Dame ta idan yamma tayi saita caba ado ta tafi kallon dambe kokuma ta tafi kallon gurmi.

Awannan rana bata jin dadin jikinta sosai wannan shiyasa tun karfe goma saura ta dawo gida sakamakon hadarin data gani gashi ma har an fara yayyafar ruwa tasan Idan ta sake ruwan ya doke ta sai ta kwanta.

Akayi rugugin Aradu. Uwani tayi murmushi daga kwance sa'ar data bijiro da irin motar da take son saya kwanan nan daga bana dai ruwan sama ya daina dukana har abada. Tafada wa kanta sannan ta lumshe idanu tana tunanin irin gidan da zata gina acikin Abuja idan ta mayar da duk kudaden nan zuwa kudin Najeriya cikin Abuja zan koma na sayi gida a Maitama ta sake fadawa kanta adaidai wannan lokaci ne to taji ana kwankwasa kofa.

Uwani ta sauko daga kan gadon a fusace tana kwafa tsiyar talakawa kenan na kusa dai tafiya na huta daku tsinannu matsiyata bazasu bar mutum yayi barci ba tafada cikin zuciya. Yanzu haka yammairo ce.

Uwani ta bude kofa saitaji gabanta yafadi rassss!
Sa'ar data ga Aliya tsaye abakin kofar ba ganin Aliya ne ya sata Faduwar gaba ba sai ganin dogon saurayin dake tsaye a bayanta sanye da riga mai gashi irin na sanyi idanunsa boye cikin wani irin bakin tabarau. Kallo daya uwani tayi masa ta tabbatarwa da kanta cewa wannan shine wanda Yaba wa Aliya ajiyar kudin.

Bi ahankali uwani tafada wa kanta tasan wannan saurayi ba wani abu da zai iya yi mata yasa tabashi kudin don tasha gwagwarmaya da irin su a shekarun baya tunda sauran kuruciyar ta. To barayi dai Allah na tuba wadanne iri ne ban gani ba?
Manyan arna ma sun barni ballanta wannan dan tsakon uwani tace cikin zuciyarta sannan saita dubi su Aliya da faffadan murmushi.
Sannun ku da zuwa kannena ku shigo daga ciki mana. Uwani taji haushin kanta da kanta lokacin da taji kamar bakinta na rawa.

Aliya da bangis suka bita abaya har zuwa cikin daki. Hannayen bangis sanye cikin aljihunsa.
Sannun ku da zuwa tace dasu Aliya sa'ar da suka shiga dakin suna fuskantar juna.

Badai sabon saurayi kika kawo min ba 'ya ta.?
Uwani tace cikin fara'a tana dubansu.
Aliya ta girgiza kai sannan tace wannan sakon dana baki Nazo karɓa ga mai shi nan yazo zai karbi abinsa ta nuna Bangis.

Fuskar uwani ta nuna tsananin mamaki.
Ban fahimce ki ba yata wane sako kenan ko kina nufin keken dinkin da kika aiko dashi wajena ran nan?

Aliya takuma girgiza kai tace a'a Bakar jakar nan dana kawo miki ran nan.. Na.. Ah.. Wacce nace dake takardun makarantarsa ce aciki takuma nuna bangis.

Bangis na tsaye yana kallon duk abinda ke faruwa yana nazarin su daya bayan daya cikin zuciyarsa tabbas yasan kudinsa na wajen uwani.

Uwani ta harari Aliya tace ke! Bana son zancen banza wacce jaka kika kawo

Please Login or Register in order to submit comment