Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

fito afuskar wayar na matarsa ne nan da nan yayi tsaki ya kashe wayar sannan ya jefa ta cikin aljihu wannan ita tasa ya sake komawa karkashin motarsa inda tabarma ke shimfide ya kwanta rigingine cikin damuwa a zuciyarsa yana fadin nidai wannan shegiyar mata wallahi ta ishe ni gara ma dai na sake aure.

AMINA itace matar Indararo sunyi aure irin na soyayya na saurayi da budurwa tunda kuruciyarsu alokacin yana direban Hayis suka hadu da ita tana tallar abinci abakin kasuwa kamar wasa sai sukayi aure saboda tsabar kaunarta da Indararo yakeyi a lokacin ya dauka ba zai sake kaunar wata mace ba aduniya to amma daga lokacin data fara zubo masa ya'ya sai Indararo ya fuskanci kamar duk kyawunta yafara gushewa musamman ma lokacin da ya sami babbar mota domin haka yabashi tikitin haduwa da kyawawan mata yan duniya gwanayen iya shafa Hoda ga shedan na bin su abaya yana dada ƙawata masa su wannan su suka taru suka dada masa tsanar wannan mata tasa a zuciyarsa tun daga wannan lokaci sai ya kasance Amina bata wani jin dadin zama dashi tana dai zama ne irin zaman nan da ake cewa wai zaman ya'ya.

Indararo bai damu da rayuwar iyalansa ba gashi dai yana samun kudu kamar banza amma daya sayawa iyalinsa abincin naira dubu biyu gara ya baiwa karuwa dubu arba'in ta dora jari ahaka rayuwar taci gaba da tafiya har zuwa daren jiya inda matarsa tayi masa korafin cewa abincin su ya kare kuma yar autarsu batada lafiya yakamata aka ita asibiti.

Shawara ce adafa mata Maina mana ayi mata surace zata ware Indararo ne ke fadawa matarsa haka.
Wannan shi ya harzuka ta har ta kai su da cacar baki wanda daga karshe dai ya jefe ta da dari uku yafito cikin daren bai ma kwana agida ba saiya dawo cikin motarsa yayi kwanciyarsa suka kwana suna waya da wata karuwarsa dake can kan hanya a wani gari tana jiran ya karaso domin yayi mata alkawarin zai dora mata jari. Wannan shi ya sa loakcin daya fuskanci matarsa ce ke kira saiya kashe wayar.

Maigida Barka da hutawa.
Indararo ya dago kansa cikin mamaki sa'ar daya ga mutane tsaye a kansa cikin sauri yafito daga karkashin motar sa'ar daya lura samarin biyu tare suke da Manajan kamfanin.

Ranka ya dade Indararo yace yana kallon Manajan cikin murmushi Manajan ya dubi hashimu da Usman sannan ya dawo da kallon sa kan Usman sannan saiya nuna motar Indararo yace da wannan motar zaku tafi daga mun gama yi wa wancan lodi sai wannan.

Indararo ya dubi Usman cikin zargi ga kuma mamaki domin kwata kwata bai yi kama da irin mutanen da suke bin sa a yan rakiya ba abin kuma da yafi damunsa fiyeda komai shine yanayin Usman ya lura dan boko ne idan kuwa hakane to abunda yake shirin yi ya samu matsala don yasan yan boko da ra'ayin rikau idan aka basu umarni basa bari ayi cuta sai sun bi abin daki daki kamar aya. Tabbas an hadu da matsala bakinsa na rawa ya dubi Manajan da murmushin yake yace DASHI ZAMU TAFI NE?

Manajan ya gyada kai Yace Eh dashi zaku tafi.
Hashimu da Usman suka dubi juna cikin farin ciki basusan abunda ke kai kawo cikin zuciyar Indararo ba.

Toh yayi kyau Indararo yace afili sannan a zuciyarsa yace yau na hadu da jaraba. Amma bakomai ai tsiyar nasara sai zashi gida.

BABI NA UKU.

Kyakkyawar budurwar taci gaba da bin sa aguje dauke da doguwar wuka gayawa jini na wuce shi kuwa sai gudu yake kamar ransa zai fita idan ya waiga sai ya hangeta ta kusa cim masa gashin kanta har gadon baya yana yawo acikin iska abunda ke bashi mamaki shine gashi dai yana iya ganin gashin kanta amma baya baya iya ganin fuskarta gashi kuma sai kiran sa takeyi ga wuka tsirara ahannunta tana cewa wai ya tsaya itace SAMIRA.

Zancen banza kenan Usman yace sannan yakara yakara wuta......

ZAN DAKATAR DA WANNAN LITTAFIN DAGA WANNAN KASHIN DON BANGA AMFANIN YIN SAN BA DON BA'A SHARHI (comments) WALLAHI.UWAR MUGU-10

Abunda ke bashi mamaki shine gashi dai yana iya ganin gashin kanta amma baya baya iya ganin fuskarta gashi kuma sai kiran sa takeyi ga wuka tsirara ahannunta tana cewa wai ya tsaya itace SAMIRA.

Zancen banza kenan Usman yace sannan yakara yakara wuta yana gudu adaidai lokacin ne to yakawo gabar wani makeken kogi nan da nan yayi turus cikin kaduwa domin abin ya zame masa gaba kura baya siyaki.

Usman ya dubi kogin sannan ya juyo ya dubi yarinyar data nufo shi da wuka gadan gadan zata yanka wannan shiyasa shi yanke shawarar gaggawa cikin zafin nama sai ya buga tsalle da niyyar kurma nutso cikin kogin Kwatsam saiyaji kamar wani abu ya cafke masa kafada cikin mamaki yajuyo a razane.
Tashi mana wannan wane irin barci ne haka kamar ka mutu. Indararo yace da Usman batareda ya dube shi ba adaidai lokacin daya rage wa motar wuta.

Usman ya farka firgigit jikinsa na rawa tabbas mafarki ne ya fadawa kansa.
Wallahi wani nannauyan barci ne ya dauke ni. Yace da Indararo yana mutsutstsuke idanu.

Indararo ya dube shi kadan sannan ya mayar da hankalinsa kan tukin dayake.
Rashin sabo ne hala wannan shine tafiya mafi tsayi daka taba yi a rayuwar ka.?

Usman yayi hamma sannan yayi murmushi ya gyada kai eh to haka din za'a ce tunda naje bautar kasa.

A ina kayi bautar kasa ne ?

Indararo ya tambaya gamida yage baki cikin fara'a a zuciyarsa kuwa yana ta zullumin dabarar da zai yiwa wannan dan bokon da aka hada shi da shi.

Usman ya sake hamma sannan ya dube shi yace a jihar IMO nayi.

Ah lallai ashe dai ka taba zuwa kudu.

Kwarai kuwa amma dai iyakata kawai imon itama ba ko ina naje ba ya danyi shiru yana kallon gaban motar karfe goma sha daya na dare lallai na jima ina barci ya fadawa kansa.

Kusan sa'a uku kenan suna tafiya don karfe takwas da yan mintuna suka baro KANO a lokacin ana yayyafar ruwa kuma da fara tafiyarsu ya bingire da barci har da mafarki.
Usman ya shafi fuskarsa a hannu sannan yafara dawo da mafarkin dayayi cikin zuciyarsa kai mafarki dai baya rabuwa da shirme ya fadawa kansa ya tabbata har yanzu Samira na nan cikin ransa shiyasa ma yayi mafarki da ita.

Yanzu a ina muke? Usman ya tambayi Indararo.

Mun dab da shiga TAFA yanzu nan da mintuna goma zamu shiga shiyasa ai na tashe ka don zamu dan tsaya mu ga abunda hali zaiyi don hanyar babu kyau.

Usman ya dube shi a tsorace yace hanya babu kyau me ya faru?

Indararo ya rage wa motar wuta sannan yace in ka lura ai tunda muka taho hanyar babu kowa motoci da mukayi kiliya dasu basu fi a kirga su ba wannan shi yake nuna alamar hanya babu kyau yanzu haka shegun ne suka tare hanya.

Idanun Usman suka zazzaro cikin kaduwa
Kana nufin wai yan fashi ne akan hanyar?

Indararo ya gimtse dariya ganin yagama tsorata wannan dan bokon dake zaune kusa dashi daman duk yan boko ai zabi ne ya fadawa kansa sannan yace da Usman afili kwarai kuwa amma wannan ba wani abun damuwa bane mu mun saba kaima idan dai tafiya tayi tafiya zaka saba ne. Ya danyi shiru sannan yaci gaba kada ka wani tashi hankalinka muna zuwa tafa zamu tsaya bazamu yi gaba ba har sai mun tabbatar dacewa hanya ta gyaru sannan zamu yi gaba saboda wallahi yan fashin nan basuda imani basu dauki ran mutum abakin komai ba tunda kaga kwanaki fa haka suka tare wata mota suka kwashe musu kudi don rashin imani duk wanda bashida kudi sai suka fito dashi suka kwantar dasu akan titi suka sa mai motar yabi ta kansu.

Usman ya zabura cikin kaduwa yace Innalillahi.... Kai wai da gaske kake yi wannan labarin?

Haba Usman babba dani zanyi ma karya ne? Ai rashin imanin yan fashin Kasar nan saidai addu'a kawai ai don ku agida kuke a zaune shiyasa bakwa sanin irin wannan rashin imanin da muke gani akan hanya... To amma in Allah ya yarda babu abunda zai faru damu

Usman ya gyada kai a tsorace sannan ya dada manna bayansa da kujerar motar ya lumshe idanu jikinsa na rawa sannan ya dan dafa naira dubu goman da aka bashi kafin su taho don ya tabbatar da zaman su.

Da'ace idanunsa biyu sa'ar da suke tafiya daya gane cewa duk abinda Indararo yafada karya ce kawai ya kirkira babu wasu Barayi yayi haka ne kawai don ya sami uzurin tsayawa a garin Tafa. ahanya kafin su zo nan sun hadu da motoci sama da dari takwas.

Indararo ya dubi agogon motarsa karfe goma sha daya da yan mintuna goma sha daya adaidai lokacin ne to ya dan juya kadan ya saci kallon Usman wanda ke kwance ya lumshe idanu a tsorace. Indararo ya kuma gimtse dariya akaro na biyu yace shege zabo na tsorata shi....

******** ******** ******** ******** *************

Samira ta dubi dogon saurayin fari mai dogon wuya kamar igiyar shanya tace malam ni fa na gaji zan shiga gida.

Saurayin mai suna AWAISU ya dubeta cikin mamaki da kaduwa kamar yaya kin gaji wannan wace irin magana ce ni kinsan daga inda na debo kafa nazo har nan wajen ki?

Samira ta tsuke baki sannan ta kada masa idanu cikin duhun dare tace in ma daga bayan duniya kazo ni dai nafada ma zan shiga gida tunda ba Goron Gayyata na aika ma kazo ba.

Wannan dirama a farfajiyar gidansu Samira ake yin ta. Daman tun kafin wannan saurayi yazo Samira ta shirya masa takakkiya don tagama gajiya dashi ya ishe ta tayi masa kora da hali amma saboda nacinsa ya kasa ganewa dalilai biyu suka sa ta tsani wannan saurayi.

Na farko dai ya cika mita idan ya dauki magana daya yayi ta juya ta kenan yana nanatawa kamar karatu.

Na biyu kuma idan suna hira duk kusan minti guda sai ya tofar da yawu idan kuwa akwai wani abu guda daya aduniya da Samira ta tsana shine yawan zubar da yawu..UWAR MUGU-10

Na biyu kuma idan suna hira duk kusan minti guda sai ya tofar da yawu idan kuwa akwai wani abu guda daya aduniya da Samira ta tsana shine yawan zubar da yawu..UWAR MUGU-11

Na biyu kuma idan suna hira duk kusan minti guda sai ya tofar da yawu idan kuwa akwai wani abu guda daya aduniya da Samira ta tsana shine yawan zubar da yawu wannan shine dalilin dayasa ta tsani zuwa gidan kakar ta ta wajen uba hajiya yar tsohuwa don haka ayanzu da Samira tasa wannan saurayi awaisu agaba saita ji duk ma ta tsani kanta.

WAI ME KE DAMUNA NE? ta tambayi kanta duk saurayin dayazo saita ga baiyi mata ba Kodai taga yayi mata tsufa kamar alhajin nan mai katon ciki da yake zuwa gurin ta kokuma taga wata dabi'ar da batayi mata ba duk acikin samarinta babu wanda take so kamar Usman to saidai kuma shima Yanada illa illarsa kuwa agurin ta shine bashida aji saboda shi kadai ne acikin samarinta yake zuwa a kasa haka nan kuma ta lura shi kadai ne idan zaizo gurin ta yake sake maimaita rigar daya taba zuwa da ita tuntuni tagama gane yawan suturunsa guda goma sha daya ne baki daya in ka hada da tsinanniyar rigar nan data tsana mai katon wuya kamar ta mata don haka kullum tambayar da take yiwa kanta itace shin idan Usman ya aureta yaya zaiyi da ita? Inama ace shi ke da ajin mai katon cikin nan ta fadawa kanta babban abunda ke damunta ahalin yanzu shine an fara matsa musu ita da yar uwarta Fadila domin su fito da miji agida ga shi kuma haryanzu ta rasa tudun dafawa tunda dai Allah ya zuba mata ruwan ido.

Tariga tasan cewa mahaifinta na dawowa daga tafiyar da yayi za'a tayar da zancen gashi kuma saurayin ma da take so har zuciya ta kore shi wannan dama wasu boyayyun dalilai su suka sa Samira take huce akan wannan saurayi.

Yanzu me kike nufi kenan? Awaisu ya tambaye ta bakinsa na rawa cikin kaduwa.
Abinda nake nufi shine kawai ka kama gabanka ni gida zan shiga tana gama fadin haka saita juya ta shige gida abin ta.

Awaisu yabi ta da kallo cikin kaduwa yana girgiza dan mukullin motar dake hannunsa bai taba tsammanin zata iya tafiya ta bar shi agurin ba.
Oh my God! Yace cikin takaici.

Acan cikin gida lokacin da Samira ta shiga saita sami duk yan uwanta da mahaifiyarta zaune cikin dakin shakatawa sun zagaye ta kowa yayi jugum jugum mahaifiyarsu tana zubar da hawaye ana ta bata baki.

Jikinta na rawa Samira ta shiga cikin dakin ta durkusa agaban mahaifiyarta cikin razani tace Mama.. Menene kike kuka?
Mahaifiyarta ta dubeta tana sharar hawaye sannan tace babanki.... Baban ki ne aka... Bata karasa ba saita fashe da kuka...

****** ****** ****** ******* ****** ****** *******

UWANI sunanta amma an fi saninta da UWAR MUGU duk da yake dai itama uwanin ba suna ne na gaskiya ba to ahaka dai aka san ta akwai wani dan daudu daya taba cewa ita kanta uwani bata san sunanta na gaskiya ba don tun tana karama haka ta taso taji ana kiranta.

Wasu daga cikin Tsofaffin yan duniya sa'anninta suna yi mata kirari da uwar mugu domin duk wata marar gata wacce ta fito daga gidansu a tsine a tanbade to uwar mugu ce gatanta ita ce cinta itace shanta har zuwa lokacin da itama za'a nuna mata hanyar zuwa bakar kasuwa.....UWAR MUGU-12

****** ****** ****** ******* ****** ****** *******

UWANI sunanta amma an fi saninta da UWAR MUGU duk da yake dai itama uwanin ba suna ne na gaskiya ba to ahaka dai aka san ta akwai wani dan daudu daya taba cewa ita kanta uwani bata san sunanta na gaskiya ba don tun tana karama haka ta taso taji ana kiranta.

Wasu daga cikin Tsofaffin yan duniya sa'anninta suna yi mata kirari da uwar mugu domin duk wata marar gata wacce ta fito daga gidansu a tsine a tanbade to uwar mugu ce gatanta ita ce cinta itace shanta har zuwa lokacin da itama za'a nuna mata hanyar zuwa bakar kasuwa.

Uwani doguwa ce fara kakkaura mai doguwar fuska ma'abociyar manyan idanu farare a zamanin kuruciyarta idan tana dandalin rawa duk sa'ar data kadawa makadi manyan idanun sai aji ya sauya kida koda kuwa baiyi niyya ba kodayake ayanzu daya daga cikin idanun ya jirkice yayi jazur dashi sakamakon dukan tsiya da wani dadironta yayi mata tun da sauran kuruciyarta yan duniya sun sha bata shawarar taje asibiti abata maganin da zaisa jan idon ya washe to amma sa'ar da wani cikakken dan duniya ya dubeta saiyace da ita wai ahaka tafi kyau da farko uwani ta dauka tsokanarta yake yi amma sa'ar data kalli Mudubi sai taga jan idanun da farin sun hadu sun bata wani irin siffa mai burgewa tun daga wannan lokacin ta share guri taci gaba da iya shegen ta adoron kasa babu abunda ya Dame ta har zuwa wannan lokacin data samu mukamin zama uwar mugu.

Tanada tsagen kalangu akan fuskarta wadanda ada basu fito sosai ba amma da shekaru suka fara tsawaita sai suka bayyana afili baro-baro.

Uwani zatayi kimanin shekaru arba'in da biyu aduniya ko ma fiyeda haka babu dai wanda yasan takamaiman shekarunta suma arba'in da biyun wani dan daudu ne ya dubeta ya kirkiro yafada. Aka dace kuwa duk wanda ya dubeta idan aka fada masa shekarun sai ya ga sun dace da ita.

Uwani ta gyara zama cikin damuwa tana leken waje ta cikin wata taga mai raga raga acikin wani matsaikacin dakin sayar da abinci take da kwana za'ayi aciki dakin baifi ya dauki mutum uku ba amma saboda karfin hali da rinton alhaki ahaka aka kukuta akasa wani dogon teburi da wasu kujeru uku daya ta katako biyu kuma na roba a kansu ne ake zama idan za'a ci abinci jama'a da yawa sunfi ganewa su fito waje ta shimfida musu tabarma saboda daman unguwar ba wani jama'a ne da ita ba karuwai ne da yan daudu. Mafi yawa direbobi ne baki yan duniya suke tsayawa agurin su sheke Ayarsu.

Uwani taci gaba da leken tagar cikin damuwa wai yaushe zai karaso ne? Ta tambayi kanta sannan ta dubi agogo karfe goma sha daya ta wuce in ba don shi ba da tuni ta dade da tashi daga kofar dan karamin shagon tana iya jin hayaniyar yan duniya sunata hira da cashewa yayinda acan kuma gefe guda wasu sun shimfida katuwar tabarma suna ta kada kati ga al'ada in har ba Yan sanda suka zo kame ba kwana suke suna caca.

Akwai dalilin wannan leke leke da takeyi jarinta ya riga ya yi kasa sosai domin tun kusan watan daya gabata kudin hayar gurin da take sayar da abinci ta kare gashi kuma saboda rashin kudi abincin ma iri biyu kawai takeyi agurin.

Awani zamani daya gabata ana dafa abinci sama da kala goma aciki harda su naman shanu dana rago soyayyun kaji da zabi amma ayanzu idan kayi sa'a shine ka samu naman dan akuya wanda aka dan tsakuro shi daga kasuwa wannan ita tasa uwani cikin damuwa take neman kudin da zata kara jari takuma biya kudin haya..

Uwani tayi wata doguwar Hamma barci take ji oh duniya kenan tace cikin zuciyarta jiya ba yau ba uwani ta tuna zamanin da take da kuruciyarta lokacin da samari har fada sukeyi akanta kowa kokari yake yi yayi mata kyauta don kawai ya burge ta amma sai gashi wai har anzo lokacin da idan ba kawalci zatayi ba na yaran karuwai babu wanda zai ko iya kallon ta sau biyu in har ba abinci zata zuba masa ba.

Nayi sa'a ma da haryanzu nake da irin su Indararo Ta sake fadawa kanta.

Adaidai lokacin ne to taji hayaniya an nufo kofar shagon cikin sauri ta mike tsaye da murna tabbas Indararo ne yakaraso don taji yan duniya na ta yi masa kirari daga can nesa.
Indararo ya shigo shagon shi da wani motsatstsan mutum mai hannu daya biye dashi ada can kafin a yanke masa hannu makadin gurmi ne.

Indararo na tabawa Allah na baka kana bamu.
Uwani tace dashi sannan ta tare shi cikin murna.

Indararo ya dubeta cikin dariya sannan yace uwani uwar mugu ina wacce akace da ita je ki kya gani to tazo nan ku zata gani uwani.

Uwani ta Harare shi tace to tsohon dan iska ka fara ko?

Indararo da mai hannu dayan nan suka bushe da dariya Indararo ya dubi uwani yace kawo mana tabarma waje nan babu iska ya dan yi shiru sannan yaci gaba da cewa gaskiya wannan shagon naki

Please Login or Register in order to submit comment