Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma har sunanta ya sani. Aliya ta buda baki zatayi magana sai kuma tayi shiru nan da nan taji gabanta yafadi rassss da farko bata san ko me yasa ta Faduwar gaban ba can kuma saita tuna da muryar ce ta sa ta Faduwar gaban tabbas muryar taso tayi kama da ta wani cikin sauri ta kawar da wannan tunani daga cikin zuciyarta.

Kinyi shiru kin gane ni kenan? Muryar ta sake fadi daga can bangaren.

Aliya taji gabanta yafadi yawun bakinta ya kafe nan da nan taji numfashinta yafara yin sama sama bakinta na rawa tace wanene kai ban gane ka ba.

AKA dan yi shiru acan daya bangaren na yan mintuna sannan sai tattausan muryar tace Haba Aliya yaya zakice baki gane ni ba bayan Naji alama acikin muryar ki amma duk da haka idan so kike na tuna miki ne to nine BANGIS ina fatan ajiyata dana manta agurinki tana nan domin yanzu haka ina kusa da gidanki Daman so nake Naji ko babu kowa na karaso zan kawo miki wata sabuwar Ajiyar.

Aliya ta dubi Usman a tsorace Usman ya dubeta cikin mamaki domin baisan abunda ya tsorata ta ba. Kafin kiftawa da bismillah yar hodar dake kan kyakkyawan fuskar Aliya ta Dame da Gumi.

***** ****** ******* ***** ******* ****** ********

Kaifa ka cika bincike-bincike saikace wanda ya bani ajiya uwani tace da Indararo tana harararsa sannan taci gaba da cewa ni na rasa irin wannan bincike saikace tsohon dan sanda kazo ka tsayamin aka sai bude bude kake min cikin daki in Mariyar zan kirawo ma gara ka fada min na kirawo maka ita kabar min dakina na sha iska.

Indararo ya dago kai ya dubeta da murmushin izgili.
Lallai gaskiya ne mai hali dai baya daina halinsa.

Halin me uban sa ido?

Indararo ya dubeta na dan tsayin lokaci sannan ya dubi manya manyan kwalayen dake tare acan karshen dakin kusan guda ashirin kana ya dawo da idanunsa kanta yace wato dai uwani bazaki daina karbar KAYAN SATA BA KO?

Uwani ta zazzaro idanu cikin kaduwa tace wane munafikin ne yace dakai wannan ma kayan sata ne?UWAR MUGU-19

Uwani ta zazzaro idanu cikin kaduwa tace wane munafikin ne yace dakai wannan ma kayan sata ne?

Indararo ya hade fuska yace kada ki raina min hankali mana bansan halin ki bane ko yau na fara ganin irin wadannan kaya acikin dakin nan? Ya danyi shiru yana duban ta ransa a bace.

Uwani ta sunkuyar dakai batayi masa magana ba
Dakin da suke ciki ayanzu shine gurin kwanan uwani uwar mugu.
Shekaru kadan da suka gabata ko karenta LUCKY bazata Bari ya kwana acikin wanan dakin ba amma dayake ayanzu tagama kare mata duniya ta juya mata baya dole ta hakura ta dawo wannan dakin wanda duk daminar duniya idan ana ruwan sama a tsaye uwani take kwana saboda tsabar zuba da dakin yake akwai lokacin da idan ruwa yayi ruwa ma saida lema take shiga dakin dakin dan madaidaici ne babu komai acikinsa sai wata katuwar katifa dakuma wasu yan tarkace gamida wadannan kwalaye da suke can kuryar dakin a jere.

Babu wanda yasan takamaiman daga inda uwani take wasu dai sunce wai mutumiyar Bauchi ce wasu ko suka ce yar Adamawa ce musamman ganin bafilatana ce doguwa kyakkyawa yayinda wasu kuma suka yi ta rantsewa wai barauniya ce daga jihar Katsina duk wannan cece ku ce da akeyi uwani bata taba cewa dasu komai ba duk abinda aka kira ta dashi sai ta amsa.
A zamanin da take kan ganiyarta an ce babu wanda yataba tsammanin akwai wata rana da zata zo wa uwani da wai har gidan kwana mai kyau zai gagareta kodayake wasu daga cikin Tsofaffin bariki wadanda suka ga jiya sukaga yau saida sukayi mata hasashen haka domin sun sha ganin ire iren ta.

Uwani uwar mugu ta taba mallakar motoci bus na haya guda takwas da tifofin daukar kasa har guda shida gamida gidajen haya guda hudu ance alokacin da da duniya take bare mata gyada akan tafin hannunta. kullum sai samari sunyi fada akanta sau uku A tarihi an taba kashe mutum saboda ita. Ana cikin wannan hali sannu ahankali dakiku da sa'o'i gamida watanni da shekaru suna shudewa sai kyawun da take takama dashi yafara gushewa musamman ma dayake yara sababbin jini sun dada barkowa yawon duniya to amma al'amura basu damewa uwani ba sai lokacin data fadi wata doguwar rashin lafiya har kusan shekara tana fama duk ta rame ta kanjame ta lode kamar atamfa. Nan da nan sai jita jita yafara yawo a gari ana cewa lallai uwani ta kamu da Cutar kanjamau.

Wannan shine mafarin duk wani hali da uwani take ciki ayanzu domin tun daga wannan lokacin sai jama'a suka dinga gudun ta wasu ma ko gaisuwa saida ta daina shiga tsakanin su domin aganin su hakan kawai na iya sawa su kamu.

Sannu ahankali uwani tafara sayar da kadarorinta daman ance zara bata barin dami sai igiya cikin dan kankanin lokaci duk kadarorinta suka kare sai wata tsohuwar mota guda daya da ake mata haya acikin gari itama tagama gajiya da duniya domin duk inda ta wuce saika ce anyi gobara saboda hayaƙi Awannan lokacin ne to uwani ta yanke shawara ta sayar da wannan tsohuwar mota tafara kafa jarin sayar da abinci lakacin data fara abincin kamar abin kirki saidai kuma bakinta yayi sabo da cin dadi amma bata iya juya kwabo ba nan da nan jarin ya dulmiye don haka saita fara fashin sana'a wata rana ayi watarana kuma baza'a yi ba.

Da tafiya tayi tafiya sai uwani ta sauya dabarar da zatake samun jari a saukake dabarar da tayi itace saita hada dan abunda ya rage mata takoma can bayan gari ta kama katon gida mai dakuna uku acikinsa duk macen data baro gidansu akace da ita taje ta gani to uwani uwar mugu zata gani duk wacce ta zo sai uwani ta sauke ta agidan idan yan duniya sun zo saita ke yi musu kawalcinsu tana samun yan kudi tana dada dora jari sannu ahankali har uwani ta ganewa ajiyar kayan sata duk wanda ya sato kaya yake son a boye masa su kafin kura ta lafa kokuma a sayar masa dasu to uwar mugu zai nema ana cikin haka ne watarana rana ta baci aka kama uwani uwar mugu a lokacin sun dade da sanin juna da Indararo don haka Indararo Najin labari sai ya tafi yayi belin ta akan kudi wajen Naira dubu talatin.

Tun daga wannan lokaci saiya zama dan gaban goshinta duk lokacin da aka sami wata sabuwar yarinya sai ta fara masa talla kafin ta yi wa wani.

Ahaka suka ci gaba da wannan yarjejeniya shi yana biya mata bukatun ta na kudi ita kuma tana yi masa kawalci har zuwa wannan lokaci da suke tsaye yana tuhumar ta akan sayen kayan sata.

Gaskiya uwani idan wani abu ya sake faruwa babu abunda zan iya yi akai tunda dai bakya jin magana kinga dai bariki babu irin wacce bamuyi ba amma sata bata cikin tsarina Uwani.
Indararo nagama fadin haka saiya nufi kofa.

Uwani ta bishi cikin sauri ta tsare masa hanya tace bakinta na rawa tsaya don Allah Wallahi tunda baka so daga yau bazan sake ba gobe za'a dauke kayan nan... Don Allah kayi hakuri wallahi idan ka gujeni bansan yanda zanyi ba don sanin kanka ne kaine gatana a garin nan da babu kai da yanzu na bar garin nan.

Jin haka shiyasa Indararo ya juyo ya dubeta.
To ai na fahimci kamar bakisan da hakan ba shiyasa.

Uwani ta girgiza kai tace bahaka bane Indararo kagane? Ta danyi shiru tana dubansa da murmushi a fuskarta.

Na gane me? Indararo ya tambayeta yana dubanta cikin zargi.

Ni arayuwata babu abunda nake so fiyeda KUDI. Ta sunkuyar da kai kamar zatayi kuka.UWAR MUGU-20

Uwani ta girgiza kai tace bahaka bane Indararo kagane? Ta danyi shiru tana dubansa da murmushi a fuskarta.

Na gane me? Indararo ya tambayeta yana dubanta cikin zargi.

Ni arayuwata babu abunda nake so fiyeda KUDI. Ta sunkuyar da kai kamar zatayi kuka.

Dubeni ka gani dubi yadda na koma saboda rashin kudi kana ganin yadda duk aka juya min baya yanzu kana ganin da inada kudin da zan gyara kaina za'a gujeni kamar haka?

Indararo ya dubeta ya fashe da dariya yace uwani kenan bazaki taba girma ba.

Bahaka bane wallahi gaskiya ce kaima kanka kasan amfanin kudi.
Kwarai kuwa don ina jin ma wallahi nafiki son su saidai kawai ni ina tsoron abinda za'a kamani a kulle domin banga amfanin badi ba rai ba
Kuma daga an kama ka Shikenan har ka mutu?

Indararo ya dubeta yace bakida hankali yanzu idan aka kama ki sai an talauta ki sannan a rufe ki idan kingama watanni ko shekaru kin fito kici gaba da zaman talaucin dai da kike gudu.

Uwani tayi shiru tana dubansa sannan saita tausasa murya tace yanzu dai kana son kace dai ba gudun saɓo kake yi ba ma'ana da baza'a kama ka ba da kaima zaka iya yin wannan sana'a tawa ta sayen kayan sata ko?

Indararo yakai mata duka uwani ta goce cikin dariya tace oh! Indararo ka shiga uku ta danyi shiru sannan ta dube shi tace to yanzu dai meye abin yi kaga dare yayi Mariya zan kirawo ma na bar muku dakin kokuwa yaya?

Indararo ya girgiza kai sannan ya dubi agogo cikin damuwa yace toh Ai ni ban ma ga ma'anar na kwanta yanzu ba Daman kinsan abinda yasa muka biyo ta nan don kawai mu dan tsakuri kayan nan ne tunda kuwa mun gama da dan bokon can ni ina ganin gara kawai mu sa gyara. (ma'ana mu tafi)

Uwani ta dube shi cikin mamaki tace me kake nufi kenan?
Indararo ya gyara tsayuwa Yakuma sake duban agogo.
Ai ina ganin zuwa zakiyi ki taso min dan bokon nan kawai muyi gaba don banga amfanin zaman mu anan ba tunda mun gama cimma burin namu.

Uwani ta girgiza kai cikin damuwa tace a'a Indararo gaskiya idan kayiwa yaron nan haka baka kyauta masa ba tunda kun kawo haryanzu me zai hana ka hakura idan gari ya yayi haske saiku tafi amma kaga yanzu haka Wallahi yayi barci.

Kinga taso min shi kawai Daman ai ba barci ya rabo shi da gida ba ya dan yi shiru sannan saiya sake duban ta yace je ki taso min shi kice dashi mun sami labarin hanya yayi kyau don haka zamuyi gaba.

Uwani ta dan yi Jim na dakiku cikin damuwa tayi kamar zatayi magana saita fasa don gudun kada ta harzuka shi daman basu dade da shiryawa ba.
Don haka saita juya tace to Shikenan bari naje Allah sa dai basu yi barci ba ta fta daga cikin dakin.

Indararo ya zauna akan katifar ya dan juya kadan saiya hangi kwalin taba a gefensa cikin sauri ya zari kara daya ya kunna mata wuta sannan ya busa hayaƙi sama ya lumshe idanu meke damuna ne samsam banajin barci? Ya tambayi kansa.

******* ******* ******* ****** ****** ************

Aliya ta Mike tsaye jiki na rawa abinda ta dauka amatsayin wani mummunan mafarki ya sake dawo mata azahiri. Ta dauka bazata sake ganinsa ba ta dauka ya tafi kenan Shikenan.

Yanzu haka ina kusa da gidanki Daman so nake Naji ko ba kowa na kawo miki wata ajiyar.

Kalmomin sa suka fara kururuwa cikin kwakwalwarta Aliya ta share gumi. Na shiga uku wace ajiya kuma zai sake kawo min?
Ta tambayi kanta sannan saita juya ta dubi katifarta bindigar daya manta tana boye a tsakiyar soson katifar.

Usman ya Mike tsaye cikin damuwa domin ya lura tana cikin mawuyacin hali musamman ma sa'ar da yaga gumi sai sartu yake akan kyakkyawar fuskarta.

Me ke faruwa ne.... Lafiya?

Aliya tayi firgigit kamar wacce ta farka daga barci ta dube shi samsam ta manta dashi in banda yanzu dayayi magana.

Abinda yafara zuwa ranta shine ta fitar dashi daga dakin domin bazata so su hadu da bangis ba mutumin da ayanzu ta tabbatarwa da kanta cewa yanada hadari ita kanta ayanzu fata take Allah ya raba ta da shi lafiya.

Kinyi shiru kinata kallona Usman Yakuma cewa.
Aliya ta dube shi cikin damuwa tace Usman akwai wata matsala amma bazan iya yi ma bayani yanzu ba ta dan yi shiru sannan saita dube shi tace zo muje na kaika dakin wata kawata saika kwana acan.... Zanzo da safe na kawo ma karin kumallo.

Usman ya dubeta cikin mamaki a tunaninsa ya fahimci abinda ke faruwa don haka sai ya yi murmushi yace kada ki damu na fahimta kice maigidan naki yazo?

Aliya tayi sauri ta girgiza kai ba abinda kake tunani bane Usman bazaka taba ganewa ba har sai nayi ma bayani amma gobe in Allah yaso kafin ku tafi zan yi ma bayani.

Usman ya kura mata idanu cikin shakka sannan sai ya zunkuda kafada yace to Shikenan sai abinda kikace ranki ya dade mu tafi.

Aliya nagaba Usman na bin ta abaya suka fito kofar gidan da niyyar su shiga lungun da zai kaisu gidan su kawar Aliya. Adaidai lokacin ne to Aliya ta hangi uwani ta ratso cikin duhun dare tana sauri. Aliya taji gabanta yafadi domin ba kasafai uwani kanzo gidanta ba sai dai ita taje kuma idan har akwai wani abu da take tsoro ayanzu shine uwani tayi ido biyu da bangis.

Uwani ta karaso inda suke cikin sauri ta dubi Usman da murmushi tace Au ashe ma bakuyi barci ba?

Usman da Aliya suka dubi juna ba magana.
Uwani taci gaba da cewa lallai ashe dai kun fahimci juna har yawo zaku fita? Ta dubi Usman ta kashe masa idanu cikin duhun daren sannan ta girgiza kai cikin damuwa.
Kayi hakuri zan rage ma jin dadi.

Usman ya dubeta cikin mamaki yace ban fahimce ki ba.

Toh kasan halin direban naka yace wai kazo ku tafi yanzun nan wani abokinsa yayi masa waya wai hanya ta gyaru... Yan fashin sun tashi.

Usman yayi ajiyar zuciya sannan ya gyada kai yace Shikenan sainayi barcina acikin mota.

Aliya ta dube shi cikin damuwa tace amma dai idan zaku wuce zaka dawo ko.?

Usman ya gyada kai yace me zai hana in dai kina son ganina.

Kaima ai ka sani..... Tayi shiru bata karasa abinda take son fada ba saboda tunanin bangis dake kai kawo cikin zuciyarta tunda suka fito take waige waige ko zata hange shi tunda yace yana kusa da gidanta amma batayi dacen ganin koda kare ba sai uwani yanzu da ta tare su.

Uwani takoma gefe kadan tana latse latsen waya ta basu guri su gana.

Aliya ta dube shi cikin damuwa tace don Allah Usman ku biyo ta nan... Wallahi tunda nake ban taba jin dadin hira da wani ba kamar ka.

Usman ya dubeta da murmushi sannan ya sunkuyar dakai tabbas shi ma irin abinda ke ransa kenan to amma yasan duniyarsu ta sha bambam da ta juna.
Zan dawo... Indai direban nawa ya biyo damu ta nan.

Zai ma dawo nasan halin sa dole ne sai ya biyo ta nan tana gama fadin haka saita miko masa wayarta yace Sa min lambar ka.

Usman ya karbi wayar yasa mata lambar sa.

Aliya ta karbi wayar bayan yagama sa mata tace idan nasa kudi zan yi ma flashing saika yi saving.

Usman ya gyada kai yace to nagode sosai yayi shiru ya kura mata idanu ga mamakinsa saiyaji Sam Sam baya son rabuwa da ita.

Usman zo mu tafi ko jiranmu fa yake yi kasan shi da masifa yanzu haka yana can yana ashar kamar tsohon bamaguje.

Usman ya kalli Aliya sannan ya juya da murmushinsa yabi uwani.

Har suka bace acikin duhu Aliya na tsaye tana kallon su.
Aliya ta juya ahankali da niyyar ta koma cikin gida lokaci guda kuma tafara lallatsa waya.

Bama sai kin kirani ba duk abinda kuke ina kallon ku Daman so nake su tafi saina karaso wata murya tace da ita daga baya.

Aliya ta juya a tsorace sannan ne to ta ganshi.

Bangis yayi murmushi. Awannan karon ba'a cikin tsumma yake ba sanye yake da riga shat fara da wani damammen wando jeans wanda duhun dare bai iya baiwa Aliya damar ta gane launinsa ba idanunsa boye cikin bakin tabarau.
Kiyi hakuri naga kamar na tsorata ki ko?

BABI NA BIYAR

Kin tsorata ko? Bangis yasake maimaita tambayar yana dubanta cikin duhun daren.UWAR MUGU-21

BABI NA BIYAR

Kin tsorata ko? Bangis yasake maimaita tambayar yana dubanta cikin duhun daren.

Aliya ta girgiza kai domin bazata iya cewa komai ba a lokacin.

Bangis ya dubeta sannan ya dauke kai bai yi mamakin ganin tsoron dake bayyane karara akan fuskarta ba yasan laifin sa ne dayayi sakaci har ya manta bindigarsa agurin ta to amma yaji dadin hakan domin yasan yana bukatar neman taimakonta akaro na biyu kuma bindigar daya mantata tagama yi masa sama da kashi Casa'in daga cikin dari na bayanin dayake son yi mata wannan tunani shiyasa ya dubeta da kwarin gwiwa yace.

Mu shiga daga ciki mu danyi magana don yanzu zamu fita zaki rakani unguwa.

Aliya ta dube shi a tsorace bakinta na rawa tace ina zamu?

Bangis yayi mata murmuahi yace muje dai daga ciki muyi magana zanyi miki bayani ina kuma son ki cire tsorona daga ranki idan har akwai mace daya aduniya da bazan iya cutarwa ba to kece.

Aliya ta buda baki kamar zatayi magana saita fasa sannan ta juya ta nufi cikin gidan bangis na bin bayanta hannuwansa biyu acikin aljihu suna tafiya yana taunar cingam.
Koda suka nufi gidan sai bangis ya kada baki yace Inafatan kinada babban Hijabi.?

Aliya ta gyada kai kamar kadangare taci gaba da tafiya sumi sumi kamar tunkiya ba magana.

******* ******* ****** ******* ******* ***********

Lokacin da suka shiga dakin. bangis bai wani bata lokaci ba saiya dubeta cikin sauri ya ce dauko hijabin ki zaki rakani unguwa.

Aliya ta dube shi a razane tace wai ina zamu ne na tambaye ka ka ki fada min.

Bangis ya gyara tsayuwa sannan ya dubeta yace a tausashe amma fuskarsa babu alamar fara'a.
Da zaki yi duk abinda na ce batareda kin takura da yawan tambaya ba da kin kyautawa kanki.

Aliya ta ayi shiru tana dubansa cikin kaduwa tayi kamar zatayi magana sai kuma ta fasa sa'ar da bindigar nan ta fado mata Arai.

Bangis ya dubeta kamar wanda ke karanta abinda ke kai kawo cikin zuciyarta.
INA BINDIGATA ?

Jikinta na rawa ta nufi inda wasu tarkacen kwanuka suke ta dauko wuka sannan ta hau kan tsakiyar katifar dake shimfide a tsakiyar dakin ta durkusa sannan tafara yanka yadin katifar da wukar.

Bangis ya zuba mata idanu cikin mamaki a zuciyarsa yana cewa lallai in ta fito da bindigar nan daga nan ta cika mai basira tabbas wannan abokiyar tafiya ce.

Sannu ahankali hannunta na rawa Aliya ta barke yadin katifar sannan ta buda tsakanin soson katifar inda ga alama a tsage yake ta dauko bindigar ta mika masa hannunta na rawa.

Bangis ya karɓa sannan ya dubeta da murmushi yace Nagode. bazakiyi nadamar taimakon nan da kikayi min ba kuma yanzu na kara amincewa dake yayi taku kadan zuwa kofar dakin dauko hijabin ki mu tafi yanzun nan zamu dawo ba wani dadewa zamuyi ba.

Aliya ta Mike tsaye ta nufi akwatinta ta bude ba'a jima ba ta fito da wani katon Hijabi kore amma duk ya kode agurin mahaifiyarta ta gaje shi tun kafin ta fito yawon duniya.

Mu tafi ko? Bangis ya tambaya gamida daga mata girar idanu.

Aliya tana son ta tambaye shi takamaiman inda zasu amma tsoro ya hanata buda baki.

Bangis ya dubi bindigar dake hannunsa yaja wani karfe bindigar tayi kara kasss sannan ya nufi kofa. Aliya ta bishi abaya zugum zugum.

Sannu ahankali suna tafiya daga wannan loko zuwa wancan sai Aliya taga sun nufi titin da zai kaisu filin wasan kwallon kafar nan inda suka fara haduwa da shi.

Bangis ya dan juyo ya dubeta kana yace a tausashe yakamata ki saki jikin ki muna yin hira ki dauka ayanzu amatsayin saurayi da budurwa muke ni dake muna hira.. Ko da shirme ne kina fada min idan kinga mun hadu da yan sanda kada ki damu ke dai kawai kici gaba da hirar ki kina ji ko?

Aliya ta gyada kai a tsorace.

Ganin ta tsorata saiya dada da cewa bawai dole bane zamu hadu da yan sanda ba amma idan hakan ta kasance inason su dauke mu amatsayin saurayi da budurwa yan duniya suna shan iska.

Aliya ta kuma gyada kai akaro na biyu.

Bangis Yakama hannunta suka ci gaba da tafiya.
Wai yaushe ne za'a sake wani wasa irin wanda aka taba yi a filin nan?
Nan da wata guda Aliya ta amsa bakinta na rawa batareda tasan takamaiman abinda take cewa ba fatan da take azuciyarta shine ina ma ace wannan wani abinda ke faruwa akanta ya kasance wani mummunan mafarki ne kawai ke faruwa tana farkawa zata ga ashe ma barci take yi.

Sannu ahankali suka shiga katon filin wasan da suka fara haduwa da juna bangis yaci gaba da tafiya har suka karasa wani tsohon gidan mai dake daf da filin. Gidan man babu kowa anjima ba'ayin komai acikinsa rabon da a sayar da mai Awannan gidan mai har an manta wannan shiyasa duk ya lalace daben farfajiyar sa ya farfashe hakanan dogayen ciyayi duk sun firfito acikin gidan man wata sa'ar idan bama kusa da mutum ya karaso ba sai ya rantse da Allah babu komai agurin daji ne.

Aliya tayi turus a tsorace sa'ar data ga bangis yana neman ya shiga dasu cikin wannan tsohon gidan mai wanda ke cikin duhu baki kirin kamar kabari.

Bangis ya dubeta da murmushi yace yakika tsaya?

Aliya ta girgiza kai tace maganar gaskiya bazan iya shiga cikin wannan duhun ba.... Kace kada na Dame ka da tambaya to amma dai... Tayi shiru bata karasa ba.

Bangis ya dubeta na yan dakiku sannan ga mamakinta sai taga yayi murmushi yace nace ki saki jikin ki bazan cutar dake ba wannan alkawari ne ni da ke idan ina son cutar dake acikin dakin ki ma zan iya cutarki.
Ya danyi shiru yana mayar da numfashi sannan saiya sassauta murya yace bakomai to basai kin shiga ciki ba amma ki dan shigo ciki kadan inda zaki buya banason wani yazo wucewa ya ganki anan ke kadai zai iya zargin wani abu ni zan shiga wani abu zan dauko ki boye min shi a cikin hijabin ki sai mu tafi dakin ki mu kwanta.

Sukayi yi shiru suna duban nuna na tsayin lokaci Aliya ta kasa cewa komai saboda kaduwa wani katon bera mai kamar bushiya ya surnano aguje ta cikin ciyayin yayi kansu. Aliya tayi tsalle gefe guda gamida dauke numfashi cikin kaduwa.

Bangis ya girgiza kai cikin takaici yace Haba Aliya kada ki bani kunya mana wacce bindiga bata tsorata ta yaya wani abin Allah Sarki bera zai tsorata ki? Yana gama fadin haka saiya nufi cikin tsohon gidan man da sauri.

Aliya na nan tsaye tana tsuma tagama tsorata ji takeyi kamar ta kurma ihu duk sa'ar data ji koda ciyawa ce saita yi tsalle gefe guda a tsorace.

Hasken farin wata yafara mamaye gurin sakamakon bakin gajimaren daya fara yayewa ahankali daga kan fuskarsa. Iska ta fara kadawa kadan-kadan tana tafiya da gajimaren daya fara kadawa kadan kadan tana tafiya da gajimaren adaidai wannan lokacin ne Aliya ta hangi kan bangis ta cikin hasken farin watan ya nufo inda take da sauri dauke da wani abu ahannu baki.
Lokacin daya karaso sai taga ashe wani dan karamin akwati ne baki.

Bangis na zuwa saiya mika mata yace boye shi acikin hijabin ki mu tafi.

Hannunta na rawa ta karbi akwatin tayi mamakin abinda ke ciki don taji da nauyi sosai gabanta yafadi sa'ar data fara tunanin ko bindigogine aciki tabbas sune. Ta fadawa kanta NASHIGA UKU.
ta sake fada cikin zuciyarta.

Bangis ya kama hannunta daya yayinda daya hannun kuma ke boye cikin hijabin dauke da akwati. Suka nufi hanyar da suka bullo. Awannan karon cikin sauri.

Suna cikin tafiya babu zato babu tsammani sai suka hangi wani abu kamar fitila yana wal-wal da haske acan gabansu....

Aliya ta tsaya turus a tsorace domin ta tabbata ko menene acikin wannan akwatin ba abin kirki bane kayan laifi ne yanzu idan yan sanda suka kamata da bindigogi cikin jaka yaya zatayi da ranta.

Cikin sauri bangis ya matsa Yakama hannunta wanda baya rike da akwatin ya matsa da kyau sannan yayi kasa-kasa da muryarsa yace dakata kadan ki saki jikin ki idan kuma KIKA NUNA ALAMUN TSORO SUKA KAMA MU TO HARDA KE ACIKIUWAR MUGU-22

Cikin sauri bangis ya matsa Yakama hannunta wanda baya rike da akwatin ya matsa da kyau sannan yayi kasa-kasa da muryarsa yace dakata kadan ki saki jikin ki idan kuma KIKA NUNA ALAMUN TSORO SUKA KAMA MU TO HARDA KE ACIKI

Cikin

Please Login or Register in order to submit comment