Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

min ajiya ko kema danake gani kamar wata nutsatstsiya kin fara shan giya dayawa ne?

Aliya ta dube ta cikin kaduwa tafara girgiza kai kamar zatayi kuka Haba uwani kada kiyi min haka mana amana bata ce haka ba kefa kamar uwa ce agurina yaya zakiyi min haka?

Uwani ta tafa hannu tace yau ni uwani na Shige su da haukar ya'yan zamani ta dubi bangis tace kai ku fice min daga gida wannan yarinyar taka batada hankali ku fita can ta nemo ma inda ta kai ma takardunka yanzu haka giya ta sha ta bugu tabaiwa wani dan iskan.... Nasan halinta yanzu haka ma batasan wanda tabawa ba tunda a buge take.

Da'ace bangis baisan duniya ba da'ace baiyi gwagwarmaya dayawa ba da babu abunda zai hana ya amince da wannan BINDIGAR KWALIN ba to amma ina ta makara domin a daren ma da Aliya takawo mata ajiyar jakar yana biye da ita abaya har ta shiga gidan tun kuma daga wancan rana yasa wa gidan idanu yana lura yaga ko Uwani zatayi wani yunkuri na rashin gaskiya to amma shiru bai ga ta fita da jakar ba saidai ganin tafara shiga sababbin kaya shiya jefa zuciyarsa cikin zargin mai yiwuwa tafara barnatar da kudin wannan dalili shiyasa yadawo wajen Aliya yace tabashi ajiyar sa amma ayadda ya tsara tun farko baiyi niyyar karbar kudin ayanzu ba har sai kura ta lafa.

Bangis ya dubi Aliya wacce ke tsaye tana girgiza kai kamar zata fashe da kuka yace zo mu je nan muyi shawara. Yana gama fadin haka sai ya kama hannunta suka fito daga dakin suka koma gefe can wajen kofar fita daga gidan.

Haba ko kaifa kaga kai dayake wayayye ne har ka fahimci abinda nake nufi uwani tace dasu daga can cikin dakin.

A can gefe bangis ya dubi Aliya fuska a murtuke yace kwantar da hankalinki ni nasan kudina suna gurin ta sai kuwa ta fito dasu don haka abinda nake so dake shine Koma waje ki jirani kada ki bari kowa ya shigo in namiji ne ki hilace shi kada ki bari yashigo har sai na gama da ita

Aliya ta kalli yanayin fuskarsa sau daya tak sannan ta gyada kai tafita Simi Simi ba musu.

Bangis Yakoma cikin dakin ya fuskanci uwani hannayen sa biyu cikin aljihunsa.
Ina ganin ya kamata ki dauko min kudina kada ki bata min lokaci.

Haba yaro kaida nake ganin ka kamar mai ilmi ina kai ina sauraren maganar wannan shashashar yanriyar.

Duk fa wannan bazata kai miki ba tsohuwar guzuma ki dauko min kudina kawai sauri nake in kuma bahaka ba yanzun nan zan fara sassaba kamanni ki.

Uwani ta fusata don haka saita Harare shi ta rike tsantsa tace Haba yaro yaushe barikin ta haife ka da har zaka wani bude min idanu to bari kaji kurwata kurr naci na sha ba domin ka ba dan dagizge saidai kaci kanka wallahi badai ni ba nice nan
UWANI UWAR MUGU NACI DUBU SAI CETO.

Bangis yayi murmushi. Kina nufin kice kenan bazaki bani kudina ba?

Eh an hana ka din kaje ka fadawa yan sanda mana kace na kwace ma kudin daka sato.

Bangis ya sunkuyar dakai kasa

Ganin haka sai uwani taga kamar ta sami lagonsa ne don haka saita dada matsowa kusa dashi zata ci gaba da masifa inda tayi kuskure kenan.
Bata ga zuwansa ba saitaji wani abu kamar guduma ya daki gefen kunnen ta tayi sama ta fado akasa Tim zaman yan bori sannan wasu abubuwa masu kama da gare gare suka fara juyawa acikin kwakwalwarta.
Uwani ta kwalla kururuwa ta dafe fuskarta da hannayen ta biyu.

Bangis ya durkusa akanta ya dubeta yace a tausashe in kudina?

Bansani ba dan iska she.....
Bai bari ta karasa ba sai ya dada mangare ta har saida kanta ya daki jikin bangon dakin.
Jini yayi tsartuwa daga bakin uwani tareda hakoranta uku na gaba ta dada kwalla kara a gigice tace Allah ya isa dan iska kuma wallahi saidai ka kashe ni bazan fada ba!

Bangis ya Mike tsaye abin ya wuce yadda yake tsammani wannan mata kwararriya ce da gani ta saba da wahala gashi kuma sauri yake dole ne saita sa shi yayi abunda baya so ace sai daga karshe ne idan zasu rabu zaiyi mata.

Ina kudina?

Bansani ba!

Bangis yasa hannu cikin aljihu
Uwani bata ga abinda ya zaro ba sai jin wani mahaukacin sauti tayi ya mamaye dakin dodon kunnenta kamar zai fado sannan ne to taji wani matsanancin ciwo ya soki tafin kafarta nan da nan taji kamar ma ba'a jikinta kafar take ba uwani ta kwalla kara cikin firgici sa'ar data gane abinda ke faruwa tabbas harbin ta yayi koda idanunta suka dawo kan tafin kafarta saita ga yayi rugu rugu ya tabe kamar an take amala jini yafara tsartuwa kamar ruwa tsoro da firgici suka cika mata kwakwalwa sai Awannan lokaci ne uwani ta gane cewa rayuwar ta tana cikin Hadari.

Bangis ya sake daga bindigar sama yakara ta akan goshinta nan da nan uwani tafara girgiza kai a razane jini na zuba ta baki ta hanci ciwo ya hanata magana sai hannunta ne ke nuni da waje.

Bangis ya fahimci abinda take nufi don haka saiya kama wuyan rigar ta da hannu daya yafara janta akasa kamar mushen kare yayi waje da ita saida ya kai ta tsakar gidan ya jefar.

Ina kudina? Yakuma maimaita tambayar

Awannan karon babu musu ba dogon surutu cikin sauri numfashinta sama sama uwani ta nuna masa inda turmin yake sannan tace bakinta na rawa cikin kuka kayi haka akasan turmin... Suna kasa...

Bangis ya daga hannu ya mangare ta sannan yafara neman abun haka.

Uwani yafadi agurin sumammiya.

********* ******** ******* ******* ***** *********

Wata farar kora kirar fijo ta shigo lungun yayinda wasu motoci guda hudu ke biye da ita suka durfafo cikin bakin lungun....

Aliya na nan kofar gidan tsaye jikinta na rawa kamar ana kada mata gangi lokaci lokaci saita Dan kara kunnenta aikin kofar gidan wai ko zataji abinda ke gudana amma shiru.

Bayan kusan mintuna biyar ne to taji wani irin mummunan sauti marar dadin ji ya....UWAR MUGU-30

Bayan kusan mintuna biyar ne to taji wani irin mummunan sauti marar dadin ji ya gauraye gidan ciki sauri ta rufe kunnuwanta sannan saitaji kafafunta duk sunyi rauni bazata iya daukarta ba don haka saita zauna a kasa ta kifa kanta akan cinyoyinta tafara kuka.

Tana zaune bata san iya lokacin da ta bata agurin ba can saitaji sautin motoci sun nufo kofar Gidan abin yabata mamaki cikin sauri ta mike tsaye a razane adaidai lokacin da hasken fitilun motoci suka haske mata idanu tana nan tsaye har motocin suka karaso suka tsaya adaf da ita sannan ne to abinda yasa yawun bakin ya kafewa yafaru..

Kofar motar ta bude jami'an tsaro suka fara fitowa dauke da makamai suka nufo ta Aliya ta dauka mafarki takeyi domin taga Usman ne agaba suna binsa abaya.

Usman ya matso inda take ya dubeta yace ki gafarce ni Aliya.....

Bai karasa ba kalmar sa ta makale akan fatar bakinsa adaidai lokacin da suka ji sautin harbin bindiga har sau uku daga can cikin gidan uwar mugu.

Jami'an tsaro suka dana kunamar bindigar su suka duru gidan cikin gwaninta irin na aiki.

Ba'a fi minti biyu da shigar su ba suka fito da bangis sun buga masa ankwa a hannu.

Wacece wannan ta cikin? Wani jami'in tsaro ya tambayi Aliya sa'ar da suka fito.

Aliya cikin kuka tace Uwar Dakina ce...

To ya kasheta jami'in tsaron yace sannan ya gyara jakar kudin dake hannunsa kana suka tusa kyeyar bangis da Aliya zuwa inda motocin su suke.

Koda suka tusa kyeyar bangis sai ya juyo ya dubi Aliya cikin tsananin kaduwa a fusace yace kin bani mamaki ban taba zaton zaki min haka ba.

Aliya ta fashe da kuka tariga ta sani koda ace hannun agogo zai koma baya a barsu daga ita sai shi babu wani bayani aduniya wanda zatayi ya gamsar dashi cewa ba ita ta kira jami'an tsaron ba.

Jim kadan da faruwar wannan sai ga gawar uwar mugu an fito da ita an nufi wata motar asibiti da ita kamar wasa sai ga jama'a sun cika lungun dankam suna kallo cikin Kaduwa.

Ni Daman nasan watarana a shige-shigen uwar mugu saita janyo abinda za'a kamata wani dan tsololon saurayi mai katon kai yace da abokinsa.
Abokin ya Harare shi yace kai fa baka rabuwa da shirme in banda abin ka wa yake wani zancen kamu bayan ga gawarta nan an fito da ita.

***** ******* *********** ********** ************

Da misalin karfe goma da yan mintuna.
Usman yafito daga wanka.

Salamun Alaikum wai ana kiran Usman wani yaro yace daga can farfajiyar gidansu.

Usman yaji gabansa yafadi kai nashiga Uku yace cikin zuciyarsa yanzu haka wasu ne suka sake zuwa...
Jeka kace ina zuwa Usman yace daga can cikin daki.

Tun ranar da aka kama bangis makwanni uku da suka wuce har zuwa wannan lokaci Usman bai huta ba Abokai iri-iri sai zuwa suke yi domin su ji labarin yadda akayi yagane barayin da suka sace kudin alhaji Sambo dayawa daga cikin wasu ma bai san su ba amma saboda tsabar tsurku da son jin labari sai tururuwa ake tayi...

Tuni an mika bangis ahannun hukuma yafara fuskantar shari'a Aliya kuwa tun ranar da yan sanda suka wuce da ita basu kara magana da ita ba amma ya sami labarin wai an sake ta to sai dai kuma har zuwa wannan lokaci bai iya samun wayar ta ba kullum ya kira wayar ta a kashe ita kuma taki takira shi.

Cikin sauri Usman ya shirya sannan yafita domin yaga mai kiran idan yan jin labari ne ya sallame su yadawo.

Fitarsa keda wuya sai yayi turus cikin mamaki...UWAR MUGU-31

ƘARSHE...

Fitarsa keda wuya sai yayi turus cikin mamaki ba wadanda yake tsammani bane domin wannan wani dogon mutum ne siriri baki tsaye ajikin wata katuwar mota baka kirar Honda saidai kuma ko kusa ko alama motar batayi kama da ta mutumin ba.

Barka da zuwa Usman yace dashi.

MUTUMIN ya matso da sauri cikin ladabi ya dan rankwafa yace ranka ya dade Barka da asuba... Ah.. Alhaji ne yace nazo mu tafi dakai yana son ganin ka yanzu.

Usman ya dube shi cikin mamaki.
Wani Alhajin?

A'a baka gane shi ba? Alhaji mana.. Alhaji dai?

Alhaji Sambo kake nufi?

MUTUMIN ya gyada kai cikin murmushi yace shi mana.. Kasan mu bama kama sunansa kai tsaye.

Usman ya gyada kai yace hakane to yanzu ya za'a yi.?

Shiga mota kawai Zakayi mu tafi ya bude masa kofar.

Usman ya shiga motar sannan suka tafi zuciyarsa cike da tunanin dalilin kiran ya tuna ranar da suka dawo Kano bayan an tabbatar da cewa kudinsa ne acikin jakar nan ta bangis babu irin godiyar da bai yi masa ba kai daga karshe ma dai tara masa mutane yayi yan uwa da Abokan arziki yana nuna musu shi daga karshe da zai tafi yabashi kudi naira dubu dari yace yaje shima zai neme shi nan gaba kadan bada dadewa ba don haka ayanzu da Usman ke zaune cikin motar baiyi mamakin neman da yake masa ba saidai dalilin neman ne bai sani ba.

Karfe goma da rabi suka isa gidansu Samira.
Sannan aka wuce kai tsaye da Usman cikin wani katon falo Usman yaga kamar acikin majigi yake.
Usman yaci gaba da zaman jira yana ta zazzare idanu yana tunanin ko zai ga Samira rabonsa da ita tun ranar da ya kawai mahaifinta labari mai dadi bayan wannan sunyi waya da ita sau biyu daga nan kuma bata sake kiran sa ba idan ya kira ta ma bata daukar wayarsa.

Alhaji Sambo sanye da doguwar riga fara Sol kai ba hula gashin sa rabi baki rabi fari ya shigo dakin cikin fara'a gamida gyaran murya ya zauna ya fuskanci Usman.

Usman ya gyara zama cikin sauri ya fuskance shi sosai.

Alhaji Sambo ya dan yi shiru na tsayin lokaci sannan ya dube shi yace sannu da kokari Usman godiya nake.

Usman ya danyi murmushi sannan ya sunkuyar dakai.

Ah... Abinda yasa Daman nakira ka shine domin nayi ma kyauta ta musamman shiyasa wancan lokacin nace ka jira zan neme ka to nagama tunani sakamakon binciken danayi akan ka na fuskanci ka gama karatu babu aikin yi wannan ma shi yayi sanadiyar bin motar ka zuwa kudanci Allah yasa kaine sanadiyyar dawowar dukiya ta data jama'a ya danyi shiru sannan yaci gaba.
Kanada aure Usman?

Usman ya girgiza kai cikin mamaki.

Alhaji Sambo ya gyara zama sannan ya dubi Usman yace to Daman so nake Naji daga bakinka domin da farko inason zan baka MANA JAN wani sabon kamfanina na chanji da zan bude a Abuja tunda kai kayi karatu mai zurfi.

Usman ya dago kai cikin sauri bai taba zaton haka ba
Godiya Nake alhaji Allah saka da alkhairi.

Alhaji Sambo ya dube shi sannan yaci gaba da cewa
Kuma tunda bakada aure zan baka daya daga cikin ya'yana biyu domin tuni ma na fada musu kodayake ita dayar na bawa dan gidan wani Abokina kai kuma da izinin Allah zan baka dayar indai ka amince kana sonta.

Usman yaji numfashinsa ya dauke nan da nan yafara gumi Samira ya kira sunanta a zuciyarsa Samira murdaddiya ce yana sonta amma ya fahimci tanada wahalar sha'ani kuma idan har ba ita take son sa ba toh ya shiga uku koda mahaifinta ya matsa ayi auren bazai taba jin dadin zama da ita ba abunda ta taba aiko masa ta cikin waya ya tabbatar da hakan.

Bari na kirawo ma ita ku gana ko? Amma idan kuma kaga baka so don Allah malam Usman ka sanar dani ba wani damuwa bane saika samo duk wacce kake so ni yanzu uba ne agurinka zan iya shige ma gaba har agama komai yana gama fadin haka saiya Mike tsaye.

Idan kun gama ganawa zansa akai ka sabon gidan dana baka a JAMBULO.
Inda zaku zauna idan an gama biki.

Ya dubi kofar wani daki sannan ya daga murya yace FADILA kina ina? Sannan sai ya dubi Usman yace idan kun gama kasa ta kirani da haka ya fice daga dakin yabar Usman a rudani.

Usman yayi mutuwar tsohuwa a zaune yana sauraron ikon Allah fadila.?

FADILA yar ajinsu.

FADILA yayar Samira.

FADILA kyakkyawa.

FADILA kawarsa a jami'a.

FADILA abar tsoro ga wanda bashida gidan Rana.

FADILA dayake gani in banda darajar karatu da zama aji daya babu abunda zai taba hada hanyar jirgi da mota a tunanin Usman auren Fadil agare shi kamar auren kuturu ne da balarabiya diyar wani sarki saiga shi wai yanzu shi za'a bawa fadila wannan kuskure ne bazai taba yiwuwa ba to Samira ma da bata kai ko rabin Fadila ba ta kishi ballantana FADILA.?

Tunanin me kake ne kaifa halin ka kenan ko a makaranta. Tattausar muryar fadila ta katse masa tunani.

Usman ya juyo firgigit. Fadila ta fashe da dariya tace menene na ga Kanata gumi ko tsorona kake.?

Fadila ta tsaya a kansa tana dubansa da faffafan murmushi sanye take da doguwar riga da wando nawani irin yadi mai santsi da kyalkyali.
Usman bai taba ganin Irinsa ba ballantana ma yasan sunansa kamshin turarenta ya gigita shi.

Bakinsa na rawa ya dubi fadila yace kiyi hakuri don Allah kawata wallahi ba laifina bane kin san ko a makaranta bama irin wannan wasan da ke.... Shine yace wai......

Fadila ta daga masa hannu tace menene na wani nayi hakuri saikace kayi min wani mugun abu? Tana gama fadin haka saita zauna akusa dashi cikin murmushi.

Kada ka damu Usman ka saki ranka ita matar mutum ai kabarinsa ce.

Usman ya dubeta cikin kaduwa yace kina nufin kin san komai?

Kwarai kuwa mijina... Kuma ina farin ciki kasan ku maza kunada matsala wai wani lokacin duk irin alamun da mutum zai nuna muku duk tsayin zaman ku dashi saiya furta da bakisan wai yana KAUNARKU.

Usman ya kalleta cikin rudani yace Samira kuma fa.?

Kada ka damu da ita baba yayi mata miji bari ma na kira maka ita ku gaisa suna wancan dakin tana gama fadin haka saita daga murya yace TAHIR zo ku gaisa da maigidana. Sannan ta Mikawa Usman hannu tace bani wayar ka na goge sakon da Samira tayi ma nasan haryanzu yana ciki.

Usman jiki na rawa ya mika mata wayar adaidai wannan lokaci ne Tahir ya shigo dakin.
Usman ya dube shi cikin kaduwa abinda yafara zuwa zuciyarsa shine Lallai Samira ta SHIGA UKU lallai ruwan idonta ya janyo mata.

TAHIR yashigo dakin yana dingisawa da alama kafarsa daya INNA TA SHANYE.

Dan gajere ne fari mai katon kai kamar masaki idanunsa kwala kwala ne jajaye to amma idan ka dubi fatar jikinsa zaka san cewa lallai yana jin dadi.

Tahir wannan shine FIENCE dina Usman.

Oh wannan shine? Tahir yafada sa'ar daya dingiso ya Mikawa Usman hannu.

Usman ya mika masa hannu suka gaisa amma bashi yake kallo ba can bakin kofar dakin daya fito yake kallo.

A tsaye abakin kofar idanunta sharaf da hawaye Samira ce tsaye tana kallon sa cikin tsananin takaici.

Tahir ya lura da cewa bashi Usman yake kallo ba don haka saiya dawo da kallon sa kan Usman cikin murmushi yace. Ga matata can Samira kaga ita tuni har tafara kukan amarci saboda tsabar azarbabi.

Usman yayi sauri ya dauke kai kadan ya rage ya fashe da dariya......

ƘARSHE

ALHAMDULILLAHI

ALHAMDULILLAHI

ALHAMDULILLAHI

YARIMA A. GANGARIYA.
(jikan sidi mai jaka)
0803883****
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment