Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zura
mata ido dauke da
murmushi mai isar da sako
barkatai.
A nutse ta bude fuskarta ta
dubeshi "sannu da
zuwa" taushin muryarta
yasa jinin jikinsa ya
tsinke yaji son Mama ya
kara malale kowane
lungu cikin zuciyarsa
tamkar ya hadiyeta yakeji
kai bai tabajin azababben
so irin wanda ya kama
hsi ba, ya numfasa yace
gimbiya ta kenan. An
fito lfy? Tace kalau ya
hanya? Yasu Baba sukaje
gida? Ya amsa duka lfy lau,
tace mungide Allah.
Yanzu ka ban minti daya
zan bude maka inda
zaka zauna, yace ni kadai?
Gsky ban yarda ba!
Tayi dan murmushi to inda
zamu zauna. Yauwa
yanzu naji batu gara da
kika gyara.
Ta wuce tana 'yar drya. Shi
kuma yayi wawan
ajiyar zcya, ya dawo jkn
motrsa ya harde.
Jimawa kadan ta budo
babban kofar get da ke
can wani bangare na
katangar gidan, ta fito tace
dashi, "bismillah!". Bai yarda
ta tsere masa ba,
jerawa suka yi suna tafe
yana fadin, "ga Amarya
ga Ango!". Ta ballo masa
harara, fuskarta kunshe
da kyakkawan murmushi,
har suka shige falon.
Ta nuna masa kujera ya
zauna, ita ma ta koma
gefen damarsa ta zauna,
suka sake gaisawa.
Yace, "to Alhamdu lillah,
godiya ta tabbata ga
Allah wnda ya nufi al'ameen
ya zama angon
sakeena. Ko kinsan cewa
jiya banyi barcin kirki
ba?". Ta kada kai, "me
yasa?" "ban taba zaton
abba zai saurari kukana ba,
shi yasa na kasance
tamkar maraya, ni kadai
cikn daki, bana aikn
komai sai na addu'a,
idanuwan nan sun fidda
hawaye gaban Ubangiji don
neman biyan bukata.
Beliete me ma jinina ya hau
kfn dady ya
dawo......." ta katse shi,
"amma da ya dawo fa?"
yace, "albishir din da ya
dawo min dashi ya hana
min barci sbd tsabar murna
da farin ciki, cnt
explain sakeena" tace, "ka
mamayi abba, kuma ni
kaina nayi mamakin
amincewarsa, koda yake
abba mai saukn kai ne,
kuma bai cika jayayya
ckn al'amarn rayuwa ba"
"na yarda da ke. allah
ya sakawa abba da alkhairi,
domin ya ceci
rayuwata. Ko har da taki?"
Ta dube shi suka hada ido,
ta dan kauda kai.
Tayi 'yar drya. Yace, "ban
damu ba, tnda ni nayi
nasara". Tace, "ni kuma
bazan yarda da kai ba,
sai naga alkawari na". Ya
zuro mata ido, "a
tunaninki zan manta ne? No
sakeena, kece komai
nawa, bazan taba mantawa
da wani abu wnda ke
alaka da ke ba, balle kuma
ace alkawari ne......,"
Ya tura hannu aljihu ya
dauko wani dan karamin
mazubi ya bude, ya nuno
mata wani gangariyan
zoben zinari yace, "ina jin
wannan shine
alkawarin ko?"
Baknta yaki rufuwa, ya
matso gabnta ya
tsugunna ya miko mata,
tasa hannu ta dauka ta
zurawa yatsanta. Wayyo!
Al'ameen zuru kawai
yayi yana kalln zara-zaran
yatsnta, zoben nan ya
zauna kamar da shi aka
halicce ta. "tsarki ya
tabbata ga Ubangijn da ya
halicce ki sakeena".
Ya dago ido ya dubeta, "kiyi
min alkawari har
abada ba zaki daina sona
ba". Tace, "insha
Allahu zaka sameni mai cika
alkawari komai
wuya, komai tsanani zan
jure akan alkawarinka.
Har abada kai kadai ne, ba
wani sai kai"
Idanuwnsa suka kawo
kwalla, murya sanyaye
yace, "na gode sakeena"
tace, "kar ka damu". Ya
mika mata gidan zoben ta
karba. Ya koma
mazauninsa ya zauna, abba
ya gaya wa dadyna
kema irin karatu zaki yi,
kinga ta kwana gidan
sauki, wai matar likita ta
haifi panadol"
Ta fara drya, "oh, drya na
baki ko? To shikenan,
ai ba ke matar likitan zaki
haifi panadol din
ba........" tace, "au son kai ne
abin?" "eh mana.
Nawa bouncing baby ne,
baby boy ko girl? Zabar
min". Ta mako masa harara,
ya hau drya. "well,
daga nan idan na tashi
zariya zan wuce, sai
kuma nxt week zan dawo
in sake ganin
gimbiyata" tace, "Allah ya
kaimu lfya, nima
anjiman zan wuce minna
wajn yayana zanyi hutu"
Ya bude ido, "owk, kuma
shine tnda nazo baki
gaya min ba, ai sai in juya in
kaiki, daga can in
wuce". Ta kada kai, "bana
son ka wahala, ka
wuce wurin aiki abinka.
Babu komai". Yace,
"uhm...... To na gode, amma
ina fatan akwai
phon number a can, kin ga
sai mu rika gaisawa
ko?" tace, "eh akwai land-
line zan baka"
Yayi ajiyar zuciya, sannan
yace, "yanzu ki bani
labari, ku nawa ne a
daknku?" tace, "mu hudu,
yaya abdul-kadeer soja,
shine babba, sai yaya
abdul-kareem yana CBN
Minna, shine zani hutu
gunsa, then yaya Abdul-
rahman yana kadna, lst
year ya fara aiki da
ma'aikatar kimiyya da
fasaha
ta jiha, shi kadai ne bai yi
aure ba......" "sai kuma
ke ko?". Tayi 'yar dryar nan
da yake so. Yace,
"kun burgeni, Abdul 3, ni
kuwa tilo ne ckn gdnmu,
bani da yaya balle kani.
Kadaicn yayi min yawa
sakeena". Tace, "kamar
ynda gata yayi maka
yawa ba" "haka kike gani?
No ba zaki gane ba,
naso ace akwai wasu,
musamman kanne, na rika
yi musu 'yan mazurai ina
cewa, kai ku bari mana!
You knw, smthn like that
dai. Amma ka zauna
shiru babu mai maka fada,
babu wnda zaka yi
wa? Babu dadi abin".
Ckn tausayi tace, "ai shirin
na Allah ne" yace,
"yes haka ne, na yarda.
Amma very soon zan
samu many babies, su
zagayeni, dady kalla! Dady
bani wannan! Dady sa min
riga! Kin gane? Ina
son hayaniyar yara sosai"
Tana drya tace, "kana da
aiki" "come on, muna
da aiki dai. Ai mu biyu ne
muna tsakhya, sun
zagaye mu, na 6 can 6.
Wuu! Confusion! Wa zai
gane min ke?"
Hannunta tallafe da kunci,
ta zuba masa ido tana
kallnsa yana ta zuba bayani,
idanuwanta suna
nuna mata yaran zagaye da
shi. Shi yasa yana
sa aya ta fashe da drya.
Yace, "drya ma na baki
ko? Yarnya gudu zanyi in
kyaleki dasu"
Ta dan tabe baki, ta tashi
tsam! Zata bar falon,
yace "ina za ki? Har kinji
tsoro ne?" tace, "tsorn
me? Ruwa zan kawo maka,
kaji dadin santin".
Sosai yayi drya, har ta bar
falon.
Ya koma a hnkali ya jingina
bayansa da kujera,
ya rufe ido tamkar mai
barci. Wani kasaitaccen
taro yake hangowa, wnda
cikarsa baya
misaltuwa. Jimawa kadan
ya keto taron rike da
hannun sakeenarsa, da ka
dube su kaga amarya
da ango. Jama'a na musu
tafi, su kuwa baki yaki
rufuwa. Bisa wasu
kasaitattun kujeru suka
zauna,
ta tsiyaya lemu a kofi ta
mika masa a baki, ya
dauka zai fara sha......
"Assalamu alaikum!". Ya
bude ido a hnkali, tana
tsugunne gabansa rike da
kofin ruwa. "barci
kayi? Lallai na dade da
yawa, ayi min afuwa". Ya
saki wani wawan numfashi,
ya girgiza kai, "dogon
tunani ne ya dauke ni. A
duniya bani da wani
burin da ya wuce aurenki
sakeena.....". Yayi dan
shiru jim! Yana kallnta, ya
kada kai, sannan ya
karbi kofin hannunta, "na
gode".
Ya shanye ruwan, ta zuba
masa lemu, ta koma ta
zauna, ilahirin jiknta ya
mutu. Wane irn so
al'ameen ke mata? Ta
tambayi kanta. Tana ganin
ita ma irnsa take yi masa,
domin itama burinta ta
zama mata a gareshi. Ko
don ita kunya na maida
ita kurma, shi yasa yake
ganin shi kadai ke da
buri a kanta?
Zurun da tayi masa a rashn
sani, shi ya jawo
hnkalnsa ya daina kurbar
lemun. Ya matso
gabnta yasa mata kofn a
baknta, ta sha kadan ta
dube shi, "ba kai kadai ke
da buri ba Dr., sanin
kanka ne mu duka muna da
bukatar kasncewa
tare. Idan baka sani, ynzu
na gaya maka ka sani,
don ka daina damuwa". Ya
numfasa yace, "Allah
ya tabbatar mana da
wannan buri" tace, "amin".
A natse suka zauna suka ci
gaba da faranta wa
junansu rai da dad'ad'an
kalamai. A nan yayi
sallar azahar, ya ci abnci,
sannan yayi shirn
wucewa zrya. Ita ta
jagorance shi ya shiga ya
gaida umma, don ya matsa
kwarai yana son kai
mata gaisuwa. Ta kuwa ji
dadi, ta kuma yaba da
tarbiyyar sa, yanaynsa da
alkunyar sa.!
Suna tsaye jikin motarsa
sallama taki karewa
Ya Ali ya danno kofar gidan
da jakarsa akafada,
bakinta har kunne ta
tarbeshi Ya Ali! Sannu da
zuwa, ya kalleta ya kalli
wanda take tsaye dashi
kafin ya amsa. Ya mikawa
bako hannu tare da
sallama (Allah Sarki ubana
akwai jarumta!). Ita
kuma tana fadin Ya Aliyu
kenan cosin dina ne,
Allah sarki inji Al-Ameen an
dawo lfy? Yace lfy
lau! To madalla. Aliyu yace
dauke da
matsanancin kishi da
mamaki a ransa.
Al-Ameen kuwa fadi yake
kuna satar kama da
juna da an ganshi an ga
dan'uwanki, tace ko? To
ai da Baban shi da Abba duk
dakinsu daya. A
Birnin gwari yake aiki.
That's gud' ina ganin ya
kamata in lallaba in barki ku
wuce ko? Kar dare
yayi. Tace hakane, kai din
ma bana son dare yayi
maka. To shikenan karfe
tara ISA zakiji wayata.
Allah ya yarda a sauka lfy.
Ameen. Ya shiga
mota ta rufe masa tana
kara fadin kayi tuki a
hankali, yace thank U. Ta
juya zata wuce yayai
kiranta Skaeena! Ta juyo
tare da murmushi yace
"I love you!" Ta kara
fadada murmushinta ta
rausaya kai ta juya zata
wuce Sakeena! Ta sake
juyowa. I love u! Tayi jim
kafin tace I love U too!
Ta ruga cikin gida ya rakata
da kallo bakinsa
kamar gonar auduga kasala
ta rufe ya kasa tada
motar.
Ta sake lekowa tayi masa
bye-bye shima ya
daga mata hannu sannan ya
sami karfin tada
motar yayi ribas yai kwana
ya fada hanya ya
kara dago mata hannu ya
wuce cike da begenta
tamkar yadda takeji a
ranta. Tana shiga cikin
gida muryar Ya Ali kawai ke
tashi yana
bambamin fada "ai dama
haka rayuwa take
kiri'kiri jininka saiya
wulakantaka don baka da
kudi! Muma muna kan
hanya indai arzikine abuna
Allah! (Kana da gsky
Baffaba!) Mama tayi tsaye
jikin kofar sassansu tana
saurare haj Hajjo tace
nace dai kayi shiru haka ko?
To kaci gaba idan
hakan shi zai sa a baka ita.
Mama dai ba
saurana mata tafi ba ga
yanmata nan bila adadin
duk wacce ka zaba sonka
zatayi idan ita ma ba
kwadayi tasa wa ranta ba.
Sbd haka kar in sake
jin wata magana ta fito
daga bakinka akan wata
Mama!
[11/01 12:51] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 1****5
H. Gaje ta cafe, "ki kyale shi ya amayar da bacin
ransa, kar ya zame masa ciwo! Da wanne zai ji?"
yace, "ai inna ba zata gane ba mama gaje,
wannan rainin arziki ne a ckn gida. Uwa daya uba
daya? Haba! Ya kamata a duba!". H. Hajo tace,
"wa zai duba? Lallai ranka zai fita idan har zaka
kwallafa wa kanka wannan maganar!"
Tana sa aya daidai da sallamar uban dawaki,
yayi tsaye yana kalln mama na zubda kwalla,
yaynda yaji muryar h. Gaje na fadin, "babu wnda
zai duba wannan al'amari, tnda dai shi da kansa
alh. Babban ya ya yamutsa al'amarin!".
Kalaman da suka fada kunnuwan uban dawaki
tare da bugun zcy, ya zurawa mama ido tamkar
ynda take kallnsa, "me ke faruwa?".
Bai gama rufe baki ba yaga Ali ya fito a fusace,
idanuwnsa na tsatso kwalla. Shi kansa gabnsa
yayi mugun faduwa, kasala ta kama shi, ya rage
sauri, "kai ali lfy?". Ya gnge fuska, ya dan
rankwafa yace, "sannu abba!" "nace me ya faru?"
"babu komai" "ina wasa da kai ne? Kake gaya
min babu komai!".
Mama tace, "abba tun jiya gidan nan a yamutse
yake, ana ta habaici tare da yada magana akan
zancen al'ameen. Umma taki gaya maka ne sbd
gudun fitina. Amma kowa gani yake yi sbd kudi
ne yasa ka amince inyi aure, bayn ka hana kowa
kace karatu zanyi. Me yasa za'ayi mana mugun
zato?"
Nan da nan ransa ya baci, yayi fushi sosai, ya
kwalawa umma kira. Ta fito ta samesu ransa
bace. Ckn fushi yace, "kira min matan gidan
nan!" "lfya alh?" yace, "ban son jin wata
magana". Tace, "alh ka kwntar da hnkalnka kayi
hakuri har zuwa lokcn da mazajnsu zasu dawo.
Zai fi kyau duk abnda zaka fadi ka fada a
gabnsu. Ina rokn wannan alfarmar don girmn
Allah!". Alh. yayi jim! Shiru yana kalln umma,
kafn ya dubi mama yace, "kin shirya kayanki?"
tace, "eh" "to kwaso ki zuba a mota maza mu
tafi".
Ya wuce da sauri daknsa, kowa ya kama gabnsa,
har da ali ba tare da wani ya kara cewa komai
ba. Kayn jiknsa kawai uban dawaki ya canza,
yayi rawani kamar ynda ya saba, ya fito lokacn
mama na tsakar gida da jakar kaynta tare da
tsarabar da umma ta bayar a kaiwa yara.
"Baki kai kayan motar ba?" inji abba. Tace, "ai
basu da yawa, su kenan" "wuce muje". Umma
tace, "Allah ya tsare, a sauka lfya". Ya amsa da
amin, yayi waje. Mama ta biyo baynsa.
Ali na zaune bisa dakali tmkar yayi bindiga sbd
tsabar fushi da kishi, domin sosai yake son
mama. Kuma yayi wa ransa alkawari zai ci gaba
da farautarta, sai yaga abnda ya turewa buzu
nad'i. Shi yasa ya aje wa ransa zai iya jiran ta
gama karatnta. Shi kuma zai ci gaba da gina
kansa da duk wani tanadi wnda zaizo daidai da
jin dadin rayuwr aurnsu. Ina zai sa ransa yau yaji
dadi?
Yana ganin mama ta shige mota idanuwnsa suka
yo tam! da hawaye. Musamman wannan zuwan
ita yazo gani, sanin cewa sunyi hutu. Kamar ya
kwarma ihu. Ya mike ya sake fadawa ckn gida.
Alh. Ya bude mota, kalla ya matso, "ranka ya
dade tfya za kuyi?" yace, "ai tare zamu tafi da
kai, taso ka shiga mota. Minna zan kai mama na"
yace, "to shi kenan". Ya mika masa makulli, "ka
tuka motar kalla, bana jin dadin jiki na". Ya amsa
yana fadin, "assha! Allah ya sauwake" "amin". Ya
bude gidan baya inda mama take, shima ya
shiga. Jikn mama ya kara sanyi, tasan abbanta
ya kanso suyi tfya su 2 kacal! Suna tafe yana
bata labarin duniya. Ta tabbata bacin rai ne yasa
ya gayyato kalla ya tuka su, gudun afkuwar wani
abu.
Sun mika tfya shi babu mai magana, shirun sam
baya mata dadi, sbd haka tace, "Abbana kayi
hakuri don girman Allah, kar hnkalnka ya tashi
akan wannan maganar". Ya dubeta sosai yace,
"dole raina ya baci, sbd an zarge ni akan abnda
ba shine a ckn zcyata ba. 'Yan uwana basu yi
min adalci ba, na tabbatar da saninsu mataynsu
ke yada habaici da kananan maganganu. Amma
zanyi wa tufkar hanci. Tnda babu wnda ya haifa
min ke".
"kara kayi fada dasu abba....." yace, "ya za'ayi in
tsaya ina fada da kannina? Umarni kawai zan
bayar, kuma dole kowa yabi idan ana son zaman
lfya. A iya sanina na basu hakknsu, na zauna da
su na gaya musu uzuri na. Amma duk da haka
basu gane cewar komai na Allah bane. Ke dai
abnda nake soki dashi, ki rike yarn nan amana,
sannan ki kara kula da kanki, don tsare martabar
gidan nan" tace, "Allah ya taimaki mai martaba.
Mamanka na tare da albarkar umma da abbanta,
da yardar Allah ba zata basu kunya ba".
Yayi dan murmushi yace, "Allah ya kara yi miki
albarka". Tare da kalla suka amsa, "Amin abba
Sun iso minna la'asar sakaliya, shi yasa ruwan
alwala kawai alh. Ya fara tambaya. Yayi sallah a
babban falon gidan, yaynda jerin kayan abincnsa
ke jiransa. 'yan jikoknsa kuwa sai safa da marwa
suke yi. Ya idar da sallar, suna jiran su
tumurmushe shi. Ilai kuwa yana idarwa suka
zube a jiknsa, yana drya ya soma tsokanarsu"
"ameera tsohuwa mai majina" tace, "Allah ameer
ne mai majina" ameer yace, "karya ne abba,
kullum wa ake ba tishu in zamu skul?". Abba
yace, "kyaleta Uwair, waye bai san halima
tsohuwa bace? Mai majina kawai".
Ai nan da nan tayi fushi ta tashi fuu.... Zata
fice,suna mata drya. Sai ga sallamar anti Rabi.
"momy kin gansu ko? Wai nice mai majina". Ita
ma dryar tayi ta wuce ta zube gabn abba ta
kwashi gaisuwa, sannan ta tambayi mutan gida.
Yace, "duk lfyrsu kalau"
Kuka ameera ke yi, yaynda mama ta shigo da ita
falon, "ynzu don Allah wa ya taba min umma
na?" yace, "kyale ta mai majina ce, ni bana
auranta!". Ta kara kware baki, mama ta rungume
ta, "kiyi shiru ki kyale shi, ke ma baki auran. Me
zaki yi da shi tsoho?" ameer sai drya yake mata.
Da yaga kukan da gaske take ynsa sai ya jawota
jiknsa, "wanene ya taba min madam dita? Manta
da ameer, tsoho ne shima. Ina dady bai dawo
bane?" ta amsa da kai tana murzar ido.
Anti rabi tace, "bai shigo gida ba tukuna, amma
yana bisa hnya". Yace, "To Allah ya dawo dashi
lfya" suka ce amin..anti rabi da mama suka bashi
wuri yaci abinci tare da jikoknsa.
Yan minticoci bayan kammalawarsa motar Ya
Abdulkareem tayi fakin a harabar gidan, ganin
motar Abbansu yasa ya fito da sauri kalla ya
tarbe shi ya karbi jakarsa yayi masa sannu da
zuwa suka gaisa, tare suka shigo falon ya zube
gaban Alh yana fadin oyoyo abbanmu! Yace
Abdulkareem dan Abba sadauki! Ya kara fadada
dariyarsa domin yana jin dadin kirarin da Abba
yake masa tun yana yaro sbd tsananin kokarinsa
wajen neman duk abnd yake so musamman ilimi.
A yaran gidan kaf! Babu wanda ya fara sauke
Qur'ani da karancin shekaru sai shi, yana 14yrs
yayi sauka kuma yasan littattafai dayawa.
Daka dubeshi kaga Mama illa dara daran
idanuwanta ne kadai suka banbantasu. Kazo lfy
Abba? Yasu Umma? Yace lfy lau Mamana na
kawo maka hutu.....Mama? Yanzu haka tana ciki?
Sai gata ta shigo falon ta karaso gunsa da gudu
ta zube jikinsa Yayana!. Ya kamo kunnenta ba
wani yayankitashi zakiyi ki koma inda kika fito!
Tace Allah sarki yayana dan Abba sadauki! Ya
dada mata duka suna ta dariya "maras kunya ba
Abj kika fiso ba? Ai dama nace duk randa kikazo
yan kafafuwan zan karya..
Tace, "tuba nake yayana, daga yau duk hutu anan
zan yi shi" yace, "naji amma ban yarda ba, ke da
soja ai sai Allah, watakila kema sojan zaki aura".
Ta kada kai ckn shagwaba, "a'a!" Abba yace, "ai
baka ma sani ba? To karkade kunnenka kasha
labari". "ko abba? To bani insha".
Abba na bashi labari, ita kuma mama na boye a
bayn yayn nata. Tas! Ya zayyane masa abnda ke
faruwa.
Abdul-kareem ya cika da mamaki, "to menene
abn tashn hnkali a nan?" yace, "nima shi na gani,
har ga Allah zcya ta bata da wani nufi akan
wannan al'amari, amma tnda haka suka dauko
zamu tafi a hakan, kuma mama zata auri wnda
take so".
Ya dan kada kai yace, "kayi hakuri abba, kasan
shi mutm a kullm yakan fi son kansa maimakn
neman zabn Allah. Abu kankani sai a ruruta shi
yayi girman da zai rarraba kan zumunci. Abba ka
dauki girma kamar ynda ka saba, ka dauke kai ga
tsegunguman mata". Ya zura masa ido yana
murmushi, "dan abba sadauki! Duk abnda ka fadi
gskiya ne, shi yasa ma bazan gaya wa yaynku
ba, don nasan halnsa, daga ali har mutn gidan
babu wnda zai kyale idan hauknsa ta tashi".
Yace, "haka ne, kuma nasan ali yana son mama,
dole yaji zafi a rnsa, amma su a matsaynsu na
manya ai bai kamata su rika tnzira shi ba. Abnda
ya dace shine su nuna masa komai na Allah ne.
Amma muna musu fatan Allah ya ganas da su.
Ke kuma mama ki rike amana, domin duk garin
nan babu wnda bai san familn marafan lafai ba.
Babban gida ne masu mutnci. So u hv 2 b very
carefl, ke ma ki nuna wa duniya kin fito daga
babban gida mai cike da tarbiyya, OK?"
Tace, "insha Allahu yaya zanyi iya kokari na".
Yace, "to da kyau likita matar likita. Abba kasan
wani abu? Ai mu juma munyi bye-bye da rashn
lfya". Suna ta drya, anti rabi ta shigo itama. Sun
jima suna hira, sannan uban dawaki ya bar garin
minna tare da yarnsa kalla.!
Anyi sallar magriba lokacn da suka shigo
Fandogari, don haka a guje uban dawaki ya nemi
bada farali. Bai wani ci abnci sosai ba, sbd
abncn da ya ci da yammacin dazu a minna.
Umma ya aika ta tattaro masa kaf kannensa da
'ya'yan gidan tare da ali.
Duk suka hallara a falnsa, ya dubesu ya fara
magana ckn rashn jin dadi, "abnda yasa nace a
kira min ku, a gskya abnda ya biyo baya
sakamakn maganar da muka yi da ku jiya, sam
banji dadnsa ba. Basiru da amamu kar ku manta
gaba daynmu ciki daya muka fito, babu bare. Kar
ku bari tsegunguman mata su raba kawunan mu,
domin da halima da hajo da gaje tare suka same
mu. Bai kamata in gaya muku uzuri na ba, ku
kuma ku koma kuna min yankn baya wajn
mataynku, har su sami damar yada maganganu
marasa dadi akai ba. Ko ban haifi daya daga
cknku ba, ina zatn ni uba ne a gareku, kuma
daidai gwargwado ban shiga hakkn kowa ba.
Ali da sa'eed a wancn lokaci sun yunkuro,
kowannensu yana son auren mama, a gabnku
yaran nan suka rika rigima a junansu, gaba ta
kullu, babu mai kalln dan uwnsa. Sbd Allah idan
ban ynke wancan hukunci ba me ya kamata inyi?
Shi za'a tsaga mama gida 2 ne, ali ya auri rabi
sa'eed ya auri rabi? A gani na idn aka hana kowa
zai fi mana alkhairi. Ko da bani da ra'ayn mama
tayi zurfn karatu, ballantana ina da shi.
Wlh bani da wani buri akan mama da ya wuce
tayi zurfn karatu ta zama likita gabana. Amma da
Allah ya sauya al'amarinsa, ba zan iya jayayya
ba. Sai dai a cknku laf din nan na bar muku zabi,
idn akwai mai iya yin wani abu bayn wnda Allah
ya zartar bismilla, ina saurarnsa. Ni kam na
yarda nayi gmanin al'ameen Allah ne ya turo shi,
ban isa in koreshi ba.
Kuna iya kirana kuda sbd kwadayi, ba zai sauya
komai a jikina ba, don nasan har ga Allah bana
bukatar sisin kwabo daga al'ameen ko
mahaifnsa. Na kare maganata, idan akwai mai
abin cewa yana da damar fadi".
Gaba daya ka rasa mai yin koda motsi, sbd dogn
jawabn uban dawaki ya tattaro musu kunya ckn
idanuwnsu, musamman matan. Jin sunyi shiru,
uban dawaki ya kara da cewa, "idan babu mai
magana kuna iya tfya, shikenan magana ta kare"
Har matan sun mike, alh. Basiru yace, "ku zauna.
A gskya munyi kuskure, amma ynzu mun gane
bamu kyauta ba ko kadan. Kayi hakuri alh. Da
yardar Allah wata magana ba zata sake bullowa
akan mama ba. Ku kuma hajo da gaje ku ba alh.
hakuri, har ma da h. Halima"
Da ganin fuskoknsu kowacce ba akan son ranta
take magana ba. Sun dai bada hakurin, kuma
abba da umma sun yafe, sun maida komai ba
komai ba, a matsaynsu na manyan gida, sun
nada gammo sun dauki girman kamar ynda
hausawa ke fadin Babba juji ne. Aik. Adamu ma
yayi nasa dan guntun jawabin na neman afuwa.
Kowa ya tashi aka bar Ali a zaune, ba tare da
yace wani abu ba. Abba ya dube shi yace, "akwai
magana ne ali?" ya karkada kansa da ke
sunkuye, sai hawaye shar-shar! Suka hau zuba.
Uban dawaki ya sauke numfashi, gaba daya
jiknsa ya mutu. Harga Allah bai taba tunanin
soyayyar mama tayi zurfi ckn zcyar ali haka ba,
wa ke ganin hawayn ali? Da yarntarsa ma ba
karamar azaba ke sanyashi kuka ba, shi yasa
yaci sunansa Gadanga! Domin kaf tsaransa babu
mai nuna masa yatsa.
"zo nan ali!" yayi kirnsa yana nuna masa waje
bisa kujera kusa da shi, "zauna kaji". Ya zauna
yana goge kwalla. "abnda nake sonka dashi ali
kayi wa girman Allah ka dauki imani ckn ranka.
Wlh a zatona tuni kun share maganar mama a
zuktnku, ganin na jima da soke maganar. Amma
kayi hakuri, ka dauki dangana kasa wa ranka, duk
abnda Allah ya hukunta daidai ne"
Ya dan gnge kwalla ya dube shi, "abba sa'eed ne
ya hakura, amma ni burina inyi ta jiran mama har
zuwa lokacn da zata gama karatnta. Kullum
addu'a nake yi Allah yasa a tsayn shekarun nan
zcyr mama ta aminta da ni".
Ya numfasa ya kada kai, sannan ya ci gaba,
"bansan yanda zanyi ba abba". Abba ya rungumo
kafadarsa, "hakuri magani ne ali, ban son ka
tashi hnkalnka. Mama 'yar uwarka ce, ka taimaka
ka bata goyn baya tare da addu'ar fatan alkhairi,
kaji? Ka kwntar da hnkalnka, nayi rantsuwa da
mama tana da kanwa da na baka ita. Amma tnda
babu, ina son kasa natsuwa ckn ranka, ka ji ni?"
Yace, "naji abba, kuma na gode". Umma tace,
"nima dai hakurn nan shi zan baka ali, gaba daya
hawaynka sun kashe min jiki. Amma babu abnda
zamu iya yi, sai dai ince Allah ya musnya maka
da alkhairi" yace, "amin umma". Abba yace, "to
tashi kaje ka kwnta, ka ci gaba da addu'a, komai
zai wuce". Ya mike babu kuzari ya bar falon.
Shiru su umma suka yi tsawn lokaci, kafn abba
yace, "Allah ya kyauta!". Ta cire tagumi tace,
"amin. Da gaske ali yake yi" "mtsw!" yayi dan
tsaki ya tashi ya shige daknsa dauke da tausayn
ali, ya bar umma zugum! Tana tunanin iska.
Gidan yayi tsit! Ko da tasa damuwar. Washe gari
da wuri ali ya koma birnin gwari don kara samun
natsuwa.
Idan bakwa comments sai inga kamar littafin ne
baiyi muku dadi ba, na kuma sai inji bana son
turowa din.
[11/01 12:54] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 1***6
Karfe bakwai da rabi na safiya wayar
tebur ke ta
bugawa a babban faln. Dawowar anti rabi
kenan
daga rakiyar mai gidan da yara da zai aje makrnta,
kfn ya wuce wajn aiki. Can gefn
wayar
ta nufa ta dauka tare da sallama. Bai
mance
muryar da ya fara ji jiya tawaya ba, don
haka ya zarce da fadn, "ina kwana anti?" tace,
"lfya kalau,
wa ke magana?" "al'ameen ne'. Take ta
fara
fara'a, "au Allah sarki, ya aiki?" "Alhamdu
lillahi" "madalla, bari in kira ta" "to na gode".
Ta aje kan wayar gefe ta wuce da sauri
tana kira,
"mama! Mama ki aje girkn nan kizo,
mutumin
naki ya bugo!". Ta fito daga kicn da sauri, suka
hade a kofa. "wannan likita naki da naci
yake"
"kai anti!" ta fadi cike da fara'a. "ke dai
jeki da
sauri". Ta wuce tana drya, ta dauki wayar, daddadar
muryarta a sanyaye tace,
"hello!". Ya
runtse ido yace, "hello 'yan mata ya aka
yi?" tace,
"kalau, an kwana lfya?" "sosai ma, har da
miyan barci". Tayi 'yar drya, "kaji dadnka" yace,
"har na
kai ki? Nasan barci kike yi aka taso ki".
"haba,
kamar wata raguwa?" "ita ce mana. Kowa
ya ganki ai yaga kalalatu" "kai kuma kalala
ba"
Yayi drya yace, "tun asuba nake tsaye ina
shirn
ofis. Na rataya neck tie, shine nace bari
in kira madam ta daura min"
Ta dan rufe fuska da hannu daya tana
murmushi.
Yace, "baki ce komai ba" tace, "to me
zance?"
"au ba zaki daura min ba?" tace, "na daura!"
yace, "ga abu a wuyana yana lilo kice kin
daura,
don Allah ki daura min" Ya fada a
shagwabe.
Tace, "yau na bani! To rufe idnka". Ya kuwa
runtse yace "na rufe" "me ka gani?". Ya
danne
kan wayar a gefn wuynsa ckn tunaninsa
yake
magana ido ruee, hannaynsa na aikin daura neck
tie din. Yace, "ga ki nan kin fito daga
dakn barci,
kin zuba kwalliya da wani farin less, kin yi
kyau
bebyna. Sai murmushi kike min, kin kama neck
tie din kina daura min........
"Wash!" ya bude ido firgigi, jin ya shake
wuyansa. "menene?" Ta tambaya ido
waje, ji tayi
ya shagwabe, "Gaskiya ba haka ake yi ba, ba
haka ake yi ba sakeena. Ai dai ba'a shake
wuya".
Drya sosai ta kubce mata, "ni na shake
ka?".
Yana sassauta daurn wuyn yana fadin, "da kyar
fa nake numfashi, so kike in suma?" tace,
"kaga
zaka makara wlh, idan suka ma bulala
babu
ruwana". Yace, "ya zaki ce in tafi? Kin bani
brkfst ne? Ga kofn tea nan a gabana, yi
sauri ki
ban insha in wuce". Tace, "oya, dauki kofi
kayi
bismilla". Ya dauka ya rufe ido yana kurba, yana
ganinta
ckn idanuwnsa, itace ke bashi. "ka
shnye?" "minti
daya, na kusa saura kadan". Ya
kwalkwale ya aje kofn, "yauwa, na koshi". Tace,
"good boy.
To sai
ka dawo ko?" "to me zan cewa zobenki?"
"ina
gaishe shi". Ya zura wa zoben ido,
sannan ya sumbace shi yace, "wai yana amsawa".
Tayi murmushi, "shikenan, tek care, ok?".
Murya
sanyaye ya amsa, "i will......." yayi dan jim,
tace,
"ina jinka!" ya rada mata, "I love u!". Ta dan
numfasa tace, "me too!". Tayi saurn kife
kan
wayar.
Da baya da baya ta tafi har ta jingina da
kujera,

Please Login or Register in order to submit comment