Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ga BAKIN CIKI Ba tamkar yadda muka
ganshi kiri kiri.amma bamuda maganinsa.kisani
duk abubuwan da kika lissafa babu wanda bamu
kwatanta akankiba.sai dai abin ya
faskara.saboda anriga an mallaki zuciyarki
mama.karki danganta laifin akan kowa.don babu
wanda yasan gaibu sai Allah.shidin kuwa mukayi
ta roko ya warware mana abunda ke boye.agame
da lamarinki.ina ganin yakamata ki kalli
uzirinmu.kiganecewar munyi iya kokarinmu.
Hargashi Allah ya shige mana gaba ya kwato
mana ke.ayanzu mukeda damar nunawa danliti
cewar lalle ya debo ruwan dafa kansa.dazai
kaisa har lahira.ki kuma sa ido kigani. Da sauri
tadawo wajensa shima ta rungumeshi murya na
rawa take cewa karka barshi da rai yaya!kasa a
masa azaba mafi radadi harya mutu.ya lafe
kanta a kirjinsa zuciyar maxa ta motsa.idanuwa
suka qara jirkita.kawai gani sukayi yasaketa ya
miqe cikin hanxari zaiyi waje,,,abba yayi azama
yace ku riqo minshi don Allah!su alh basiru suka
cafke hannayensa.dawo ciki ka zauna ya qame a
tsaye suna ganin yanda jikinsa ke rawa.namansa
na girgiza saboda fishi.alh adamu yace alh ne
zaiyi magana dakai..abba ya daga murya yace
abduqadeer dawonan ka zauna!a hankali fishin
yarinqa sauqa sannan su alh basiru suka dawo
dashi ya zauna.yayinda mama tasake baro jikin
abba tadawo gunsa ta zauna. Abba ya numfasa
dukkanmu musulmai ne,,kuma munyi imani!da
ko waccw qaddara ce.ina ganin fushin farko
banamu bane.kar zuciya tasa mu aikata aikin
nadama.yaya soja ya kasheshi babu nadama dan
an harbe azzalumi macuci.irin danliti.karka
manta muya fesa mana gubar mutuwa.mun
shaqa harta shige mana da ginshikin gidan nan
abba,!bazamu yafewa danliti ba abba.koza a
kasheni saina harbeashi.abba yace kenan bamu
godewa ubangiji ba daya nuna mana wannan
ranar?wanda yace muyi afuwa a
tsakaninmu.domin shi yanason masu yafiya.ko
bamuyi fansa a gun danliti ba.nayi rantsuwa
Allah bai gama walaqanta shiba.tunda ya
walaqanta ayoyin alqur'an.inaso mugane
wannan.ba haqqin mama kadai ke wuyansaba.
Banajin akwai hukuncin dazamu yankemasa face
mu qyaleshi da wanda yabasa ikon aikata
wannan aiki akan mama.na tabbata bazai
qyaleshiba yaci bulus!ba.ina roqonku da muyi
haquri.mu sadauqar da yafiyarmu a matsayin
godiya ga Allah daya musanya mana bakin ciki
da farin ciki.ina fatan yaya soja zaibi umarni
na? jikinsa yayi sanyi yadan kada kai..yace ya
wuce abba yayi dan murmushi. Yace nagode!
mama zonan...!ta rarrafo ta dawo jikinsa ya
jawota. Yace ki nitsu nasan kinrasa komai na
tsarin rayuwarki yanda kika shirya....saidai inaso
ki gane cewar shirin Allah shine gaba da
komai...saboda haka ki rokesa sabon rayuwa mai
albarka.muma zamu tayaki zakiga kamar
wannan abun bai faruda rayuwarki ba.ki sani har
ummanki ta rasu bata taba yi miki baki
ba.kullum addu'arta Allah shiyaki.idan zatasa
albarka tare takesa muku da sauran yayunki.don
haka tsakaninku adda'a ne kawai. Na tabbata
hasken addu'arki zaije gareta.harta gane cewa
lallai albarkar ta na tare dake kinji mama?ta
dubeshi kwalla na zuba tace naji abba.don Allah
kayafemin ya goge mata hawaye yace baki min
komaiba mamana.ayau nagane baki da laifi ko
kankani saboda haka ki saki jikinki.tace nagode
abba intambayeka abba?yace tambayeni
mamana.ta karya wuya gefe tace al'ameen fa?ya
kada kai yace allahu akbar!alkairi Allah yakai
mas duk inda yake.haqiqa bantaba ganin tashin
hankaliba irin wanda nagani a fuskar
al'ameen..saboda rashinki mama kiris yarage ya
zautu amma qarfin adda'a ya miqar da imaninsa
zuciyarsa ta daidaitu bisa shirin ubangiji.ya
rungumi qaddara yawuce da ita rasha.gaskia
bansake jin duriyarsa ba haryau din nan danake
magana dake...kuma hulda ta yanke
tsakaninmu.ni kaina bansan daliliba.watakila
iyayensa sun nisancemu don qara nesanta
rayuwar dansu ga tinaninki.hasashe nayi amma
bansan musabbabinba.
BAKIN CIKI 3***7 Tacire kai ta dubesa kwalla na
zuba tace tabbas zai iya zama hakan abba!nima
nayi alqawarin zanyi masa addu'a Allah qara
nesantamu.ya mance ya taba sanina a duniya..ko
a hanya kar Allah ya qara hadamu.abba yashafa
kanta Allah ya shige miki gaba.yayi miki jagora
a sabuwar rayuwar dazaki fuskanta nan
gaba.kowa yace ameen yace muyi addu'a.sun
raba dare a falo suna hirarrakin duniya abba yace
aje a kwanta a huta.mama ta turashi a kekensa
zuwa dakinsa wanda tuni anty amina ta dade da
gyarawa.suka kamasa yakwanta a gado.sannan
sukayi sallama takoma dakin umma!inda anty
amina da baraka suke. Kowa ya kwanta barci ya
kwasheshi.amma mama ta kasa.kawai tunanin
yanda tayi cudanya da danliti take.nan da nan ta
ji kyaman kanta ta kamata.tafara sunsuna
jikinta.hankalinta tashe batasan lokacin data
diro tashige bayiba.ruwan sanyi ne a bokiti da
anty amina ta dibo.mama ta duba ba soso ba
sabulu.haka nan tahau kwara ruwan sanyi
ajikinta.tana dirjewa da hannu hawaye na
xuba.ruwan ya qare ta dauki bokoti ta kwarara
sauran. Tadauki bokitin takwara sauran ruwan
gaba daya.haushin qarewar ruwan
yakamata.tasanya kayanta ta figi bokitin da
nufin taje tsakar gida ta debo a rijiya.su anty
amina da baraka tagani cirko cirko abakin
bayin.tawuce abinta ta doshi kofar.yayinda anty
ameena kefadin haba mama! ashe bakiyi
bacciba?yakamata kimanta komai karki zautu a
banxa da wofi.ta zuba mata ido kwalla na xuba
wari nake anty ku bakuji?babu wani warin da
kike mama!tunaninki yagaya miki
qarya.yakamata kisamu bacci ko kwakwalwarki
zata huta.ta dubi baraka taga hawaye itama
take,,,tace saboda Allah baraka bakiji warin
danake ba?sunsuna fa kiji....takara mata hannu
a hanci baraka ta goce da kuka ganin haka jikin
mama yayi sanyi ta zube qasa dabas takama
kai.wayyo Allah na!suka kamota sukayi ta
rarrashinta.tadan nutsu.amma barcin da basu
komaba kenan gabadayansu Washegari kowa ya
hallara da iyalansa.ya abdulkareem da anty rabi
kamar su hadiye mama sukeji.sun xubda hawaye
saboda murna.ta dubi girman ameer da ameera
kawai sai ta kada kai.tana tuna al'ameen
shikansa docta yazama saurayi.ta zura masa
ido,,,hannayenta bisa kafadunsa ta matse
ido.hawaye suka kwararo..jitayiyana share mata
hawayen tayi wuf! ta bishi da kallo.bakinta na
rawa tace al'ameen momy nagayama inasonka??
ta taba gayamaka? ya juya ya kalli
mominsa.yamaidoda kansa gareta ya girgiza
kai.bata gaya maka ba?amma momy bata
kyautaba.tasanfa yadda nake sonka Allah tasani
boyema tayi togayamin kana sona? yadaga kai
alamar eh.ta rungumeshi tana fadin nima
inasonka dokta. Anty rabi ta taso ta dafata.ta
dago kai ta dubeta kwalla na xuba mama!ki
kwantar da hankalinki na tabbata Allah baxai
barki hakaba.zai musanya miki mafi alheri wata
qilama fiye da al'ameen.tayadd a rayuwarki zata
daidaita tamkar da. Ta miqe a hankali ta
fuskanceta tace hakane.nasan babu abunda zai
gagari Allah.amma dokto shine farko shine
qarshe.ta wuce ta murda kofar dakinta.ta qare
masa kallo inba qarya idonta ke gayamata
ba.kamar ta taba ganin al'ameen tsugunne a
wajen data qurawa ido.dukda takasa tuna
kalaman dayake fadi.idanuwantana nuna mata
zubar kwallansa.tayi wuf!ta cafke yatsunta ta
runtse su tamau.tana tambayar kanta ina zobe
na?ina na ajeshi?ta wuce a hankali bakin gado
ta zauna tayi shiru tana tuna kalaman dayake
fadi idanunta na zubda hawaye.kai al'amarin
mama qara sukurkucewa yake dalilin dayasa
abba yace subar garin wataqila tafi samun
nutsuwa.nanda nan suka fara shiri.kafin wani
lokaci kowa ya kimtsa abba ya sallami en uwa
da abokan arziki.su hajiya hajo sunata neman
gafara wajen abba da mama.motoci suka
kwashesu kowa da iyalansa suka miqe
hanya.suka bar danliti hannun hukuma.duk
abinda yakamata su masa A kagara suka sauqe
baraka tukuna suka dau hanya.minna suka yada
zango gidan ya abdulkareem.ko anan dinma
al'amarin bai sauyaba.haka suka kwana ba barci
a idon mama.washegari suka kimtsa masu tafiya
abuja suka dau hanya.ya abdulrahman yayi
kaduna da iyalansa da malami.shikuwa
abdulkareem jirgin shabiyu sukabi zuwa
legos.yan abuja suna dira gida wanka mama
tafarayi.wannan wanka yafara damun yan
uwanta.su wanka ma kawai suke gani basusan
yanda taga dare haka take ganin ranaba!akwai
fargaban rashin bacci zai mata illa.idan ba'ayi
gaggawar daukan matakiba.towayasani bare ayi
mata magani? shiyasa kafin sati ta birkice gaba
daya.ga zama shiru ga sunsune sunsunen
jikinta.wanka kuwa ba'a maganarsa.saidai in
danliti bai fado mataba.nan da nan tafara mura
zazzabi mai zafi ya rufeta.hankalinanty amina
yatashi.data shigo dakin tasameta nade cikin
bargo sanyi na kadata.cikin sassarfa tasamu
abba.ta durqusa a hankali tace abba idan ba'a
dau matakiba mama zata kashe kanta da yawan
wankan nan. Mama zata kashe kanta da yawan
wankan nan.gatacan jikn kamar wuta sai rawar
sanyi take.yakamata asan abinyi cikin
gaggawa.nanda nan ya latsa control din kekensa
yawuce ya nufi dakin yana fadin kira yayanta a
waya.kuma fa yau dinnan naji yana fadin sun
gama magana da yan uwansa egypt zasu wuce
da ita asibitin dana kwanta. Su duba lafiyarta!
tace nima yagayamin amma duk da haka
yakamata afara kaita nan tafara samun
taimakon farko.yana kutsa kai dakin yana fadin
gaskia ne.kirashi din ki kara gaya masa.ta juya
shiya shige dakin yasamu mama sai kyarma take
cikin bargo.kwananta biyu a asibiti basu gane
ainihin matsalartaba.amma taimakon dasuke
bata yataimaka kwarai wajen sanyata bacci.tana
samun hutu.duk takardar tafiyarsu masar sun
kammala itada yayanta wato soja.a ranar basu
kwana ko inaba sai egypt .acan bincike ya
tsananta.don babu irin gwaje gwajen da bata
samuba.hoton kwakwalwa hiv aids,,ciwon sanyi
da sauran ciwuka dakan kama mutum
sakamakon shiga wahala mai tsanani.Ba a
sameta da wata matsalaba sai hawanjini da
rashin bacci.kamar dai yadda likitotin nigeria
suka ce amma su abba basu yaddaba dan gani
suke kamar hauka mama keda niyyan yi.sai dai
Allah da ikonsa likitotin masar suna kokarin
shawo kan matsalarta.da magunguna da
shawarwari.don cire mata damuwa wanda
gabadaya ita ummul aba isin komai.to muma
bari mubarta ta huta. A lokacin da mama ke
kwasar hutu damagunguna akasar masar.shi
danliti yashe yake aofishin yan sanda.yanata
hauhawa kamarfarashi.gaba daya fuskarsa ta
aune ta kumburasundum.sukansu yan sanda sun
gaji da saya masagarin rogo yanasha..babu mai
belinsa.tsawon kwana biyar dama ayuba ne yake
zaton ziyi belinsa to shimatunda yaga ayar Allah
ta sauqa.don haka yayi wakansa alqawarin tuba
daga nasa laifukan zinacezinace dayake
aikatawa.babbar mota yabi sai indamai
yaqare.wajen neman halal.to Allah ya
karbitubansa.shikuwa dan goga yarasa tudun
dafawa ga ciwo ga masifar yansanda.ranar daya
cika kwanashida.sukace zasu sakeshi yatafi
yanemilafiyarsa.idan yaga dama ya gyara
halayensa ko yacigaba da lalacewarsa..shidai
yana kuka yana roqonsusu barshi dare yayi su
sakeshi saboda kunya kunjidan iska ashe yanada
kunyan?kuma da tsoron kar jama'a suganshi su
sake rufar masa da duka,Yansanda suka amince
hakan amma baxasu bashiabinciba.h aka
yazauna da yunwa har qarfe gomandare.suka
tarkata shi suka tura waje.a hankaliyasamu ya
sulale yakoma gidansa ya kwana.yanatunan in
mafita da da hali gidansa zai sayar a darannan
yahada kudinsa yatafi neman magani.sai dai
kash takardun sun kone a shago lokacin
gobara.meyeabunyi yanxu?bai runtsa ba kamar
sauran dararendasika shude.yana wahala da
ransa.sai dole yakaudakunya ya nemi wasu
takardun yasaida gidan danbashida wata mafita
data wuce wannan.idan yanasoya tsira da sauran
mutuncinsa duk inda zashi..haka kuwa akayi da
sassafe ya lallaba gidan maianguwa.baiko dawo
masallaci ba.ya zauna yajirashi.ya gurfana
gabansa yayita roqon gafara.sannanya miqa
masa kukansa.mai anguwa bai bata lokacibaya
amince domin shima zaiyi farin ciki idan
danlitiyabar garin fandogari.saboda haka nantake
yakawo takarda da biro suka rubuta wani
takadda.dakansayanemo shaidu uku sukasa
hannu.kuma yasa akanemo dillalai sukayi wa
gidan kudi yace shi zai Saya,Gaba daya dubu
dari biyu cinikin ya kaya.danliti yasallama ya
karbi kudinsa a hannu.kafin qarfe goma nasafiya
ya tattara yabar gari.gashi nan gashinan harwani
kauye da ke tsakanin zariya zuwa kura
jaharkano.da la'asar sakaliya.kofar gidan daya
dosa cikeyafe fal!da jama'a anata alwala.a
raunane yayi musu sallama.suka amsa ya
tambaya..ko lafiya kofar gidanmalam?daya daga
ciki yabashi amsa ai malam wa'adiyayi.shirin
yimasa sutura ake.danliti ya dora hannuaka yace
ciwo yayi? yace to ciwon ajali ne.kwanansabiyu
kacal a kwance.ya nemi waje a qasa ya
zaunahankalinsa ya qara tashi..wanda ke bashi
amsa yamiko masa buta yana fadin hala kaima
cikinalmajiransane?yace aytoo harda neman
taimakoma.Allah sarki malam Allah jiqansa.yace
amin yialwala yanxu za'a fito dashi.jiki babu
kwari yafaraalwala.ya na kammalawa ana fito
dashi.daganan sukadiba zuwa makabarta..ga
kabarin malam an haqa duk abunda ake anyi
akasakasa a kabari aka maida qasaakarufe
iyalansa nata kuka harda danliti,Daga nan aka
dan jira ayi masa addu'a kawai ganingawar
malam akayi ta bulloqo waje,subhanallah!
mekefaruwa ne? tashin farko jama'ar wajen suka
watse.kafainbak iyi kibani waje musamman
danliti.daya riga kowaficewa daga wajen.daga
bisani liman yasa aka tattaromasa mutane suka
dawo.danliti nacan baya yana rarraba
idanu.liman yadaga murya yace innalillahiwainna
ilaihi rajiun.! jama'a wannan al'amari fa
banagudu bane.! wata ayace dake bukatar
bincike.matsayin malam agarin nan wannan zai
iya zama abin kuka agaremu.domin mu a zahiri
munsan malam mai iliminaddini ne,,wanda ya
koyar da almajire da yawa.wanda yake wakilta
na lokutan danake da uzuri.sai dai ahalin yanxu
wannan abun yanuna mana akwaiboyayyen laifi
agareshi!ina rokonku dan girman Allahku tsaya
muyi masa addu'a.mu roqa masa
rahamarubangiji.alfarmar annabi muhammad
(s.a.w) Yayi kabbara sau uku jama'a na
amsawa.iyalanmalam kuka da firgici yaci
qarfinsu labari kuwa tuniyabaza kauye.har
wadanda wani uxiri yahanasu xuwasun sheqo
aguje.shiyasa makabarta taqara cikamakil.liman
ya jagoranci addu'a mai tsawo.sannanaka qara
haqa kabari aka sakasa.shikansa liman kuka
yake da hawayensa saboda ganin wannantashin
hankalin.bayan anmaida qasa an rufe .sukasake
tsugunnawa dan nema masa gafara.ai sai
gagawa tayo waje.ana salatin annabi da tasbihi
daistigifari akasake mai dashi.amma ba'a gama
maidaqasar ba gawa tasake bullowa waje.liman
ya dubi babban dan malam.ya tambaya!meka
sani agame damalam wanda mu bamu sani ba?
gashi ubangiji yananuna ishara gamasu yi su
tuba su daina.ya gogekwalla yace wlh bansan
komaiba,,,bantaba lura dawani aiki na assha
atare dashiba.dana sani wlh danafadi sai dai ko
aje atambayi mata a gida, LLiman ya numfasa
duk guri yayi tsit!kawai sai ganindanliti akayi a
gaban liman ya tsugunna Allah gafartamalam ni
nasani.na kasance ina daya daga cikinmasu
zuwa gun malam.neman taimako akanabubuwan
dasuka damemu ko ince nemanduniya.bansan
irin shirin dayake wa sauranba amma nida kaina.
Nasha kawo ruwan..........ruwan maniyyinayana
rubuta ayoyin Allah dashi.yana
hadaminmagunguna danake buqata.ina bashi
maqudankudade.tahanyar malam mun cutar da
bayi Allahwadanda basujiba basu ganiba.ba
malam kadai kebuqatar addu'a ba harda ni.Allah
gafartawa malam.wuri ya kaure da sallami.wasu
sukafarazungurar dan liti suna la'antarsa.liman
yatsawatar.yace a saurara.tsarki ya tabbata ga
ubangijindukkan halittu.jama'a kunji wannan
mummunan tashinhankali?toga aya ta
tabbata.ina ganin ta ishemutsoron Allah.ta
ishemu mu gane komai ka boye wa mutane
bazaka boye wa Allah ba..kuma ko ba dadekoba
jima zaka koma gareshi.bamu da abinyi a
halinyanxu dan hukunci yakoma gunsa. Ya daga
hannunsa sama yaci gaba da fadin yaubangiji
muna tawassali da sunayenka guda casa'inda
tara,,,ka taimakemu ka amshi wannan bawa
nakadan kar warin gawansa yazama guba ga
bayinkasalahai!ya Allah ka sauqar da rahamarka
cikinkabarinsa badon halinsaba.badon
halinmuba.badon ayyukanmu ba sai don monxon
mu annabimohammad (s.a.w)suka qarasa tare
da muryoyinmutane dake cike maqil.kai tsaye
liman yace akamaa maidashi.kankace kwabo
ansakasa a rami anrufeakayi zuru! ana jiran ikon
Allah.amma tsawon mintocishabiyar. Babu
abunda yafaru.aka soma qabbara.liman kuwa
fadi yake jama'a muji tsoronAllah.muji tsoron
Allah ya al'umman musulmai.kodada nliti yaga
haka saiya fakaici idon mutane tuni yasulale ya
tsere kar yasha dukan banxa gun wadannanyan
kauyen.A gigice yashiga kano cikin dare da
kullin kudinsayanufi inda yasaba sauqa,,,,,zuwa
safiya yayi amfanida kudinsa danyin wata
sana'ar don riqekansa.washegari yashiga kasuwa
yin sari wani mutumya bangajeshi ya wuce.saida
aka hada masa kayandubu dari da hamsin.ya
laluba kudi sukace daukarmu inda ka
ajiyemu..nanda nan ya firgice.ya tubekayansa
tsundur yana dube dube....ina kudin suke?anan
fa na ajiyesu...masu shago sukayi zuru
sunakallonsa.am ma dasukaga abin nasa babu
hankali aciki sai suka turasa waje.ga ganin
wannan mugun nufine yakawo sa Allah
yakamashi.yakama haukan qarya.haka masu
shagon da jama'ar wajen ketafadi.danliti kuwa
ya rinqa bi kwararo kwararo akasuwayanata
surutai.fadi yake...wannan bala'in
yayiyawa..wata tsiyar ma sai anmutu.lalle lahira
dakallo.toni wama zan kalla?aini ne zanxama
abinkallo.da dama idan sukaji dariya suke.wasu
kuma al'amarin yabasu tausayi.ga mutum har
mutum daganiya aje iyali amma ba saiti,Bayan
watanni hudu har mutan fandogari
sunfaramantawa da abin mamakin daya
faru...wanda ya ajetarihi musamman ga yan
jarida ta yadda..suka rinqawatsa labaru.cikin
shafukansu.na abin al'ajabindayafaru a kauyen
dunduta.ba xato ba tsammanikawai sukaga
danliti ya keto titi a kafa da rana face face.yayi
bakikirin.gashi n kansa cunkus hade
daqasumba.harda furfura.dafarko basu shaida
shibasaida yayi sawu uku.nanda nan labari yayi
tambari harkunnen su abba cewa danliti ya
HAUKACE.Allah daikonsa,tunda ya iso fandogari
bai qara gaba ba.nanyaketa bilayinsa.qafafu duk
sun kumbura.wani lokacinma kasa tafiya
yakeyi.kaganshi kwance cikinrana quda na
binsa.idanyaji yinwa yayi tabin gungunmutane
yana bara.asiya masa abinci.kai jama'a
muceALLAHU AKBAR! **A watannan hudu,,ita
mama sauyi sosaitasamu.domin tasamu matuqar
kulawa a sati ukundatayi a masar.tacci gaba da
samun kulawar yanuwanta.suna nuna mata gata
fiyeda wanda tasamuada.tadawo sakeenarta.sai
dai dan qara manyanta dafuskarta tayi.ayau suke
sa ran dawowarta daga umara!inda tasami sati
biyu a saudiyya tana ziyararka'aba.tana samun
nutsuwa tare da miqa addu'ol daneman buqatu
na alheri.sai dai bata sauqa abuja ba alegos ta
yada zango.anty rabi dasu ameera sukadaukota a
filin jirgi tayi bulbul. Abinta
gwaninsha'awa.dokta yafi kowa tsaraba masu
tsada.bayan taci abinci ta huta ta kira wayan
abba.ya dauka tayimasa sallama kafin yace haba
mama na! watau dagaske kike a legos din kika
sauqa? tayi murmushitace yi haquri abba.ai
bazan dadeba zandawo kwanauku kawai
zanyi,Yace sunyi yawa mamana!kiyi kwana biyu
na tabbatasun isheki warware gajiya.akwai
magana muhimmiyadanake so muyi.tace
shikenan abba Insha Allah jibinzanbiyo jirgi
inade ya soja baiyi fishiba?yace yayiamma ya
huce tunda yayan legos din yabada
haquriinkindawo jibin kinqara wanke kanki.ta
qara murmusawa tace nima na qosa in ganka
abba dukkewarka tadamen.yayi yar
dariya,,,mamana kenan tomuna sauraronki
jibin.sai munsake waya tace toyanxuma zankira
any amina mu gaisa. Toyayikyau.ace ina gaida
halima.zangayamata.sukayisallama takashe
wayan tasake kiran yayanta.sannan ta kira anty
amina duk suka gaisa.tagaya musu inshaAllah
jibi zasu iso abuja.daganan kaduna ta bugasuma
suka gaisa.bayan tagama wayan duk indatakeson
kira ta dubi dokto.dake liqe jikinta.kanatakallona
na fiye surutu koh?yayi yar dariya yace
nibanceba anty.taja habarsa tace ai nasan
bazaka ceba.kai din waya kaika surutu?yaware
ido kamarnata yace ni anty?ko a skul gentle man
antynmu kecemen saboda banda surutu da
yawa.Ta zura masa ido fuskarta cike da
murmushi taceuhm.....yabon kai adai rage dokto
saboda gobe yacemai zan rage?tace qarya!yadan
cunno bakin takamatana dariya.toyi haquri
gettlemen ai nima nasan kaigentle ne.akwai
wasu cakulate a jakata miqominnaqara maka
sunfi ta dazu dadi.yamiqe da gudu yadauko mata
bisa madubi.ta bude ta kwasomasa.tadauki daya
ta bare tace bude bakin insanyamaka...kunya
takamasa.ya tsaya yana kallonta
yanamurmushi.lah!kunya?dan kyauye bude
mana.yakasabudewa sai rufe fuska yake ba zato
tafara fadin bahaka akeyiba...gaskia ba haka
akeyiba dokto!ka bude bakin insaka maka.anty
rabi ta kyalkyale dadariya.sannan mama tagane
tashigo dakin.tadubeta afirgigi.lah anty labe kike
mana?ni yasu mezanyi walabe a sha'anin uwada
danta?akwai dai son kai danbashi kadai bane
dan.amma ankilliceshi shikadaianabasa
gara.adai rinqa adalci...... Tayi dariya sosai tace
kaji hassada,,bude bakinkamubasu haushi.ya
bude tasanya masachocolate.suna ta masa
dariya.ta jawosa jikinta tarungume..anty rabi
tazauna gefen gadon sukaci gabada hira.da
daddare ma bayan cin abinci haka sukataru.a
falo suna kallo suna hira.da yayanta.washegari
bayan cin abincin rana.suna kebe cikin daki da
antyrabi..suna hira.mama tace anty nikuwa
tuntuni nakeson tambayanki wani abu amma
inajin nauyi.tazubamata ido menene shi? tace
don Allah ko kinadatsofaffin hutunan su ameera
da al'ameen?tayimurmushi mama kenan!inbanda
abinki waya isa yarabaki da al'ameen balle
yahanaki ganin hotonsaharda zaki rinqa jin
nauyin tambaya?ni wlh bakiji dadindanake jiba
innaga yanda kike hira da al'ameen dankisai
inrinqa ganin kaman a'ameen dinkine.yanzu
zanbinciko miki nasan dai suna nesa cikin
tsofaffinalbum. Tayi murmushi to nagode!tamiqe
tayita sauqe kaya tazakulo album din tadawo
dashi inda mama kezaune.ta miqa mata tace
gashi duba,,tafara budewatana kallon tsofaffin
hotunansu harta kawo wandaal'ameen yadauka
dasu ameera.yana tsakiyarsu duksuna dauke da
wadataccen murmushi!gabanta yafadi ta bude
ledar ta dauko hoton tazuba masa ido.dagacan
tajiyo muryar anty rabi na fadin nidai
mamatsorona daya kar ganin hoton nan yasake
jefaki waniyanayin da bama fata.kinsan abba
bazaiji dadiba.tanumfasa ta dubeta anty rabi
nayi rashi tace nasani!nakuma tabbata shima
bazai taba mantawa dakeba.tace zai manta idan
haryasamu labarin mummunan halindanake
ciki......takada kai nikuwa banjin wannanaraina
saboda shine mutum na farko dayaqi yardacewar
akan ra'ayinki kika canxa.kullum fadi yakeyasan
kina sonsa..lalle akwai rashin sani a
waniwaje.kowa yayi biris!da zancensa.dan
anaganin zautuwar sanki ne.ta gigitashi.kinga
kuwa banjinakwai wani abu dazai goge sonki
aransa. Ta goge kwallan daya zuba mata.anty
rabi tacekingani koh?gaskia bazan baki hoton
nanba.kisa inyilaifi gurin kowa.tagoge da sauri
tace bawani abu antyrabi kinsan Allah?zuciyata
adake take kanal'ameen.kuma nasan narasa sa
har abada.kuma nikaina bana fatan mu hadu.ina
mai tabbatar miki a gaban ka'aba nayi wannan
rokon wajen Allah.fatanaya amshi rokona.saboda
haka kar hankalinkiyatashi.donkinga ina hawaye
bazan iya hanasuzubowa bane..tunda sun taho
sanadin farin ciki.tacegaskia ne.to Allah zaba
mafi alheri.taceameen.intambayeki mana...waiya
kikaji da akace miki danliti ya haukace?tayi
murmushi ta kada kai tacemaizanji kuwa anty?ai
qarshen alawa qasa kuma dukwanda yataba
qur'ani.bazai shaba anty.Allah yayigaskia
dayace qurani nashi ne kuma shi zai bashikariya!
kinga kuwa danliti yadebota da zafi.wata qilada
haqqina kadai yadauka abin yazo masa da
sauqi.Allah ya shiryi zukatanmu baki daya.ta
amsa daameen tana mata kallon tausayi,80.....
.jirgin safe tabi xuwa abuja tana zaunecikin jirgi
tunanin maganan anty rabi kawaitake.tabude
jaka ta zaro hoton ta zura masaido,,,salon
soyayyar dayake mata take karantowa.tasauqe
numfashi cikin ranta tace inasonka
al'ameenamma bana fatan sake haduwarmu
dakai.tamaida hoton cikin jaka takoma ta
jingina da kujera.taci gabadayiwa Allah tasbihi
har suka iso abuja.tana fitowaharabar taran
fasinjoji ta hangi anty amina a tsaye.Suka
rungume juna zuwa inda tayi parking.suka
shigemota anty amina tajasu zuwa gida.a guje
tashigegidan cikin falo ta iske abba zaune kan
kekensa ta zube jikinsa cike da murna..abba
nah!mamana kenan! andawo lafiya? ta dago kai
tadubeshi lafiya lau.yacenayarda saudi ta
amsheki kinga kumatunki kuwa? tayidariya kai
abba harda zolaya? yace aiba zolayabacekowa
yaganki zai shaida hakan.anty amina tace
nimadai haka nagani.tace to ai hakan akeso ko?
yace kwarai kuwa bakiji dadin danajiba.toya
mutan legos?tace qalau suke suna gaidaku.ina
amsawa.anty aminatace nizan haura sama.Anty
amina tace ni zan haura sama..duk abindakikeso
naci akwai a kicin.tace to anty sai na
hayosaman.tajuya ta haye saman tabasu gu su
gana.abbayace kije kisamu abunda zakici..tace
aibanjin yunwaabba karfe 12 ne yanxu akwai
sauran lokaci.yacekodan ruwa mamana.?tayi
murmushi ta miqe barin dauko abba..ta ajiye
mayafinta tawuce kicin ta zuboabinci filet tanaci
suna yan hiransu.tana bashi labarinumara har
aka kira azahar.takaishi dakinsa
yayisallah.itama taje tayi tasawo tasamesa yana
cinabincinsa gefensa ta zauna ta qara yawan
abincinsunaci tare abba kace zamuyi
magana..amma bakace min komaiba?yace ina
sane inasone ki qaranitsuwa.tace a nitse nake
abba...kagayamin nimainada nawa
maganan.yace toki saurarenidakyau.bayan
tafiyarki umara kawunki alh basiru yabugamin
waya wai mutane sunata zuwa nemanaurenki...
..aurena?yace wlh kuwa kuma abin mamaki duk
yan fandogari ne..bangama nazarin
maganarba..saiga wata wayar tasameni aranar
dakika sauqalegos,,,ake gayamin ko yar gida
zamuyi, Domin yayanki ali yadawo da
maganarku tabaya.nace duk sumin uxiri kidawo
muji tabakinki..nanda nan fuskarta ta sauya
tashin hankaliyabayyana a fuskarta..abba ya
zura mata ido kafinyace..yanaga hankalinki
yatashi?hawaye suka gocemata tace dole
hankalina yatashi abba nah!don ka kawo min
maganar dana jingineta a
babinrayuwata.....kamar ya mamana? aini
addu'ata kenanAllah fidda miki miji nagari kuyi
aurenku.hankalinkowa yakwanta..kuma Allah ya
amsa ganin gamanema Allah ya turasu..ko baki
zabi kowaba inakyautata zaton bazaki qi zaben
dan uwankiba.domin aliyu yacika dan halas
kuma masoyi na haqiqa. aliyuna daya daga cikin
mutanen da bazanmantaba.saboda shine mutum
na biyu daya roqe ninayi afuwa a gareki duk
ranar da kika dawo gidalokacin dakika bi danliti
kuka gudu.al'ameen shine nafarko sai ali.haka
bana manta ranar daya kamo hannunki yakawo
minke.ya durqusa yanema miki,Kuma ya hana
mu daga miki murya saboda baqi
cikingidan.aliyu ya jima yana zubda hawayensa
akanBAKIN CIKIN Qaddarar data sameki.ba
qaramin maisonki bane zai nuna maka irin
wannan yardabamamana.a yanxu kinga zahiri ali
mai qaunar ki ne.donAllah mamana kar kice
bazakiyi aureba! saboda wani dalili nikam
ayanxu banida wani buri face nagankidakin
mijinki.ta kada kai tana share hawaye
wannanbashi ne burinka akaina ba abba,,,tun
banda wayaukagayamin burinka akaina amma
yarinta yasanamaka musu.na sauya maka
tunani.akan dolekadauki zabina.bansani ba
wataqila musun dana maka ne yazamemin
matsala.abba yanxu nayihankali burinka shine
nawa,,,yadda kake sha'awar yamace likita insha
Allahu Allah zai nuna maka ni amatsayin
likita.kamar yadda kake burin hakan tunasali.da
wannan tunanin nadawo umara.kuma
itacemaganar danace zamuyi.don Allah abba
kagoyamin baya akan rayuwar danake ganin
itace zaman lafiyada kwanciyar hankalina,Kuka
sosai takeyi hankalin abba yayi mugun tashiyace
saurara mamana sanin kanki ne idan na
goyamiki baya kikaqi aure,,haqiqa nabi son
raina.ni aganina ai auran bazai hanaki karatu
ba.idan banmantaba hakan kuka shirya da
al'ameen.Allah ne bainufaba inkuwa hakane
mezaisa ki fasa mamana?tace abba a fuska
faram faram,amma zuciya saiAllah.inada abin
gori ajikina wanda yazame mini adolena nesanta
kaina da kowa.don tsira damutumcina.abba na
tabbata ka gane nufina.dangirman Allah kaban
izini nakama karatu.ya kada kaicikin
damuwa.mamana ko wani zai miki gori kamar
yadda kike hasashe na tabbata aliyu dan
uwankibazai miki gori ba.ki sadauqar masa da
kanki kamaryadda ya miki halacci lokacin da
kowa yakyamaceki.tace zan iya yiwa ya ali
komai muddin inadashi har qarshen rayuwata
amma bazan iyaaurensaba.tu nda yanada
mata.kubashi haquri yaci gaba da juriya da
kulawa da iyalinsa yadda yadace.tayunqura ta
tashi tayi waje.abba yabita da kallo
yanasoyakirata amma ya kasa saboda
tausayinta. ana fitowa ta hadu da yayanta yana
shigowa.ta rugata rungume shi yace menene?
takasabashi amsa yajata suka koma dakin abban
yanazaune shiru yana juyayi,,abba meya faru ne?
sukazauna kusa da abban yace ba'ayi komaiba
akan maganar nan ne dana gaya maka masu
sonta daaure.shine tace karatu zatayi amma ban
yarda dahujjojintaba.ina ganin aurenta zai zamo
mata garkuwaaduk inda zata neman ilimin.yaya
soja yace gaskia nesai dai inbata aminceba
akwai matsala dan ita bayarinya bace.tasan
abinda take hangowa kanta,,,so pls abba..idan
bazaka damuba a madadin sauran yanuwana
muna roqonka kabar autanmu ta
nemiilimi.ahankali zata gane aurenma
yanadamuhimmanci.dakanta zata kawo maganar
cikin gidannan so please abba!please!!ya tallafe
goshi shiru jim!Ya dubesu yace.shikenan Allah
yasa hakan shine mafi alheri matsalata kawai
bansan mezan cewa aliba.inajin nauyin yaron
nan.farin ciki ya mamaye matazuciya.yayin da
ya soja ke fadin yayi haquri.Ai ali ya girma babu
wannan haukan yarinta a taredashi kamar
da.kekuma dole kiyi taka tsan tsan andaishaki
kin warke.rayuwa ta zarce duk yadda kikezatonta
saboda haka ki kiyaye.tayi murmushin farinciki
ta matsa kusa da abba nagode abba,,kuma
dayardar Allah zan kiyaye.yadafa kanta yace
Allah yayi miki albarka tace amin.yaya
nagode.yace inatsarabata?kinje kin rabeta a
legos ko?kin kai wa lazydokto.ta rufe baki hannu
biyu lah yaya me kake nufi?ya damki bayan
wuyanta yace are u askin me? aiangayamin
kayan al'ameen yafi tsada da yawa.taceok nasan
magulmaciyar ameera ce babbar kwabo batada
abokin kishi sai al'ameen.sukayi dariya
abbayace umman takice mai gulma?lalle ya ta
riqa.tacigaba da dariya tana cewa ni ummata
bata kishi dakowa.Allah ya jiqanta amin.anty
amina tayi sallama tashigo ta zauna cikinsu
abba yace mutuniyarki taqiyarda.yayanta kuma
yace abarta tayi karatu.tayi murmushi kayi
haquri akan hakan abba Allah saalherine.yace
amin haka nake fata.hira ta tsunke ananya soja
yaci abinci.
BAKIN CIKI 3***8 Ai ali ya girma babu wannan
haukan yarinta a taredashi kamar da.kekuma
dole kiyi taka tsan tsan andaishaki kin
warke.rayuwa ta zarce duk yadda kikezatonta
saboda haka ki kiyaye.tayi murmushin farinciki
ta matsa kusa da abba nagode abba,,kuma
dayardar Allah zan kiyaye.yadafa kanta yace
Allah yayi miki albarka tace amin.yaya
nagode.yace inatsarabata?kinje kin rabeta a
legos ko?kin kai wa lazydokto.ta rufe baki hannu
biyu lah yaya me kake nufi?ya damki bayan
wuyanta yace are u askin me? aiangayamin
kayan al'ameen yafi tsada da yawa.taceok nasan
magulmaciyar ameera ce babbar kwabo batada
abokin kishi sai al'ameen.sukayi dariya
abbayace umman takice mai gulma?lalle ya ta
riqa.tacigaba da dariya tana cewa ni ummata
bata kishi dakowa.Allah ya jiqanta amin.anty
amina tayi sallama tashigo ta zauna cikinsu
abba yace mutuniyarki taqiyarda.yayanta kuma
yace abarta tayi karatu.tayi murmushi kayi
haquri akan hakan abba Allah saalherine.yace
amin haka nake fata.hira ta tsunke ananya soja
yaci abinci.Basu tashiba sai la'asar kowa yaje
sallah.bayan taidar da sallah ta haye gado
tasaka (ear piece)tanasauraren karatun
qur'ani.wucewar minti talatin tanasaurare
dadinsa na ratsata.tashi guda karatun yayanke
adalilin kiran daya shigo.ta duba allon wayandan
ganin waye sunan ya ali ya bayyana.gabanta
yafadi amma ta daure ta danna ok' ta dauka
kawaitaci gaba da saurare.da sallama ta fara.ya
amsadawata muryar dabata saba jiba.tace yaya
ali dangirman Allah......ya katseta da sauri yace
karki hadanida Allah ki cuceni mama!meyasa
baki tausayina newai?ta numfasa idanu suka
kawo kwalla.tace bazaka fahimceni bane ya ali
.....yace babu abinda zanfahimta mama,,,ai
dama kin dade kina azabtardani.axatona yanxu
tunda babu al'ameen zaki iyamaye gurbinsa
dani.ashe bazaki iyaba? wannan yanatabbatar
min ko alama can zuciyarki bata
sonamama.mesa?ta kada kai tace yaya ali ba
haka bane nasan ada al'ameen kadai naso amma
ayanxu hardakai kashiga raina.saboda halaccin
dakamin.wlh dazaniya aure kai zan aura Sai dai
bazan iyaba don girman Allah kayi
haquri..yayiajiyar zuciya yace mesa mama?
kinkuwa san yandatausayinki ya ke bin jinin
jikina?bani da wani buri dayawuce kizama
matata mama don inshare mikihawaye.kimanta
rayuwar wahalar dakika sha canbaya.kiyi tunani
zanbaki lokaci karatu kuwa na miki alqawarin ko
ina kikeso zakije indai kinxama mataagareni.kai
tsaye tace bana buqatar lokaci yaya
ali.ainagama yankewa kaina hukunci..kariqe
matarka zaifima kyau yaya ali..idan kuwa qari
kake sha'awakanemi maras tabo ka aura.tabo?
ban fahimceki bamama.tace bazan jure goriba.ka
kuwa san yauda gobe sai Allah.ba daga gareka
nakejiba ina nufinkishiya da kaidinta.zan iya
mutuwa saboda BAKINCIKI.Duk ranar da matarka
ta gorantamin.wani abudaga rayuwata.kasani ba
ruwan kishiya da asiri idantaso musguna maka
zata iya maka sharri zata iyarufe komai ta
musguna maka da gangan.Yaja dogon tsaki
wannan ne hujjarki mama?ni bankarbetaba dan
nasan amina bazatayi mikihakaba.idan kuwa
harta kuskura zan nuna matabayan tsananin
sonda nake miki zan nuna mata keyar uwata ce
ta jini.saboda haka bake zatayi wagoriba ni
zatayiwa.tace nagode Allah da bakinka

Please Login or Register in order to submit comment