Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana tsiyayar hawaye kusan
3mins sannnan ya yafito ta da hannu, yace xo
nan! Da sauri ta isa gunsa, ta fada jikinsa ta kara
fashe da kuka. A'a, kinga ni fa kukan ne bana so.
Yanxu menene damuwarki? Ta goge hawaye,
tace kullum in rinka samun kulawarka, hakan shi
xai tabbatar min da kana sona kana son abinda
ke cikina. Yayi dan murmushin nan nasa, ya kara
janyo ta jikinsa, yace, kin samu bebi, karewa ma
da kewarki na dawo. Kin ci abinci? Ta kada kai,
saboda me? Bana iyawa ne, jikina gaba daya ya
canza, sai amai kamar xai kasheni. Yace ayya
sorry ko? Amma duk da haka ba za a rasa abinda
kike sha-awa ba, gaya min in nemo shi, na kosa
in kore kishirwata. Ta mako masa harara, ya
kyalkyale da dariya, meye na harara ta? Ko ke
ma xaki min BAKIN CIKI ne, irin na 'yan sa ido?
Masu shiga tsakanin masoya suna son suga
bayansu. Haushi su nake ji wlh. Tace ai ko ni din
ma haushin su nake ji, ah haba? Wlh kaji na
rantse. Ya cacume ta tana dariya tana fadin, ban
da lfya Danliti, bai saurare ta balle ya tuna ya
nemo mata abinda take son ci. Karfe 8 ya fito ya
barta can kwance tana murkukusun ciwon ciki,
ya wuce waje wani mai suyan nama, ya karbi
danyan naman da yasa ya aje masa. Ya dawo ya
bade shi da magani, ya maida cikin leda ya
nade. Yana xaune bakin shgo bisa benci, yana
tunanin tafiya yayi wanka ko ya samu yayi
sallah. Mama ta fito tana yafa mayafinta, ya bita
da kallo yana murmushin keta, ya cikin? Tace
yayi sauki ni xan koma gida sai gobe. Haba haka
da wuri? Yanxun fa 8 ta wuce? Kar a neme ni ne.
Wa xai neme ki? Don Allah xaumna muyi hira, ba
wanda xai nemeki, bayan sun san kina nan. Bata
da xabi, don haka ta xauna kusa dashi, ya shiga
bata labaran banxa. Jimawa kadan wani kare ya
xo gilmawa nan take ya hau kiransa, tace me
xakayi da kare kake kiransa. Kasan karen
okundiri fada gareshi ko?
Yace bai sami nama bane don ubansa
okundiiri, ya kece da dariya, okundirin ne ubansa?
Lallai ka samo shi. Yacee to da waye ubansa?
Kinga bude ledar nan nama aciki dauko ki ba shi.
Yana magana yana shafar kan karen. Tace, taf
ya cafke min hannu? Kai dai ka bashi kai da ka
siyo masa,don raka asara. Yace karki bani kunya
mana, me xai sa ya cije ki, bayan yasan ke
bebina ce, ko kare? Ai ka santa ko? Sweetheart
dina ce kar ka cije min ita. Tuni kanta ya fasu,
ya jawo leda ya bude ta dauko katon yanka ta
mika masa tana fadin, abin har da yaji? Sangarta!
Ya kwashe da dariya, yace ina ruwanki? Ke dai
mika masa gudan. Ta dauko ta mika masa, ya
cafke, Dan liti ya runtse ido yace yes! Ya xarce
da dairya. Ta xuba masa ido tace, menene abin
dariya har da wani cije labe? Yace ji nayi kamar
ya hade da hannunki ya gartse. Takai masa bugu
a kirji tace amma kai mugu ne! Yace sosai ma
ashe baki sani ba yarinya, to tashi kije gida an
gama hirar, kinga karen yayi tafiyarsa. Ka gaida
okundiri kaji? Ta ci da kyakyata dariya. Yace, ah!
Tashi karki sa yarona ya fito yana fito yana
kyakyatawa kamar dolo. Ta shi kije gida sai safe.
Don Allah kiyi hkr, so nake nayi wanka inyi
sallah. Ta fido lah nima har ka tuna min banyi ko
magriba ba. Ta juya da sauri tana cewa, sai da
safe! Yace Allah ya kaimu. Ya bita da kallo, yace
yarinya kin gama yawo kin shiga 3 kin lalace, ya
daga murya ki fa sami abinci ki ci. Ta juyo ta
amsa, kar ka damu xanci. Suka ja hankalin
mutane, don haka yama didi ya biyo baya, masu
tsinuwa nayi, masu addu'ae shiriya nayi. A tsakar
gida ta iske su Abba na jiran dawowar ta, shi da
su Alh. Basiru. Tana shigowa tasha jinin jikinta,
ta shiga bin bango, tana so ta shige falo. Alh.
Basiru ya daka mata tsawa, ke dawo nan! Simi
simi ta matso gun su ta durkusa guiwa 2, batayi
aune ba, taji saukar wani wawan mari. Gaba
daya ya ratsa kanta, ya gigita ta, ta dunkule ta
fasa kuka. A cikin ba tace ga wanda ya xabga
mata wannan marin mai tsanannin xafi ba. Sai
dai taji muryar Abba na fadin wannan shine
gargadi na karshe da xanyi miki, shi ya sa na
tara kowa su xama shaida! Idan har ba xaki bi
umarni na, ki xauna a gida ba, to wlh sai dai ki
xaba, ko mu ko Danliti! BAKIN CIKIn nan ya ishe
mu mama. Gara in sallama ki, in tabbatar da kinfi
karfina xaman kanki kikeyi. Saboda haka daga
yau kika kara sa kafarki kika fita kikaje gun yaron
nan, to kar ki dawo, ki yi zaman ki can wajensa
ku sha shagalinku yadda kuke so. Duniya ce
Mama, mai dauke da axuxuwa babu adadi! Ina
fatan kinji kuma kowa ya shaida! Alh. Basir ya
karbe karuwa kike so ki xama ko? To Allah ya
baki sa'a, mu dai ba xa mu hana shi ba, duk
ranar da koreki. Alh. Adamu yace dama saboda
me xamu hana shi? Cikin shege ne fah ajikinki,
amma bai sa kinyi nadama ba, to me xai sanya ki
kuwa? Karkiji da wai, mun tsame hannun a kanki,
haka xuri'ar gidan nan kaf! Kar ki ce kin san daya
daga cikinsu, duk ranar da wuya ta koro ki! Ta
shi ki bace mana da gani shashasha sakarya. Ta
mike da gudu ta fada dakinta, ta dasa kukanta, a
fusace abba ya bar wajen kowa ya kama
gabanmsa, suka cigaba da yada xancan a sasan
su. Daren nan su ma Umma basuyi barci ba,
musamman Umma da tabbatar wa kanta ciwon
xuciya ya kamata. Da safe ta atashi xuru-xuru
baki daya idanuwanta sun xurma, shi kansa Abba
ya rame ta maxa kawai yakeyi yana wa Umma
fada kar ta salwantar da rayuwarta akan Mama.
Ita Mama ba wannan ta aje ranta ba, kawau
burinta kasance tare da Danliti, don haka take
ganin kowa ya tsangwame ta saboda kiyayya.
Kafin safiya ma ta mance duk kalaman su Abba
da kawunninta. Allah Allah takyi ta sami saukin
laulayin safe dake damunta ta lababa taje ta
gano Danlitin ta. Xuwa 12noon ta iya shiga kicin,
ta dan tsiyayi ruwan lipton, ta dawo ta shanye.
Xufa ta keto mata, danji dadi ajikinta, kana ta
shiga bayi tayi wanka da sabulun wanki maras
kamshi. Ta kimtsa, tsaf, duk da tayi haske sosai,
ta kuma rame kwarai, kana iya gane kyanta na
asali mai daukar hankali. Ta koma ta kwanta
yana kllon agogo 1:00 ta tashi tayo alwala tayi
sallah, ta dauko gyalemnta ta xura takalma ta
leko falo bataji motsin kowa ba, ta kwahi sauri ta
fice abinta. Yara suna ce mata sai kin dawo
aunty Mama! Jin haka yasa Umma yanke sallah,
ta fito da sauri ta tambayi yaran ina maman?
Sukace yanxun ta fita. Tabi xauran, yaran suka
biyota ta tura su tace, ku kira min ita. Yara suka
fice da gudu suna kwala mata kira, Aunty Mama,
ki zo Umma na kira! Haka suke ta gudu suna fadi
har suka isketa, ta dube su tace, sai na ci
ubanku in kuna kwala min kira haka! Ni sa'ar
kuce don Ubanku? Ku tafi ku ban wuri kafin in
fallawa yaro mari! Mts..... Taja tsaki, ta wuce
abinta, yara suka dawo a guje suka iske Umma a
xaure sukace, wai sai ta ci ubanmu idan muka
sake kiranta! Ta dafe kirji tace, ta kyauta, kuje
wasan ku. Ta dawo cikin gida a salube tare da
mamakin taurin kai irin na Mama, me take nufi
kenan? Ta xauna a falo tana juyayi. Da kyar ta
sake mikewa ta shiga dakin Abba, ta tashe shi
barcin ramakon da yakeyi. Ya farka yana
kallonta......
Yace, azahar tayi ko? Tace tayi alhaji.
Ya yankura ya tashi yace menene na ganki a
salube? Tace tasake fita, wa? Mama mana. Cike
da mamaki yace ta fita? Yanxun nan kuwa,
kamar fako na takeyi, har yaran nasa su kirata,
ta dinga kunduma musu xagi, taki dawowa. Ita
Maman ta zage su? Tayi murmushin takaici, tace
kana mamaki ne? Bai kamata kayi ba alhji. Ta
kuwa tafi kenan, kinsa Allah ba zata dawo ckin
gidan nan ba. Kiyi hkr, duk abinda ke ranki na so
da kaunar Mama, ki cire ki dangana da ita, nima
na hkr da ita. Umma ta fasa kuka, ta tashi da
asauri ta bar dakin. Hankalin Abba ya kara tashi,
ya taso ya biyota dakinta, tana xaune bakin gado
kukan kawai takeyi. Ya tsaya kanta, yace saboda
Allah ya kike so nayi Halima? Ta cira kai murya
na rawa. Tace har ga Allah ba korar Mama ke
sanya ni kuka ba, tausayin rayuwarta ke bani,
yadda ta ka sa gane cewar mu ba tsangwamarta
mukeyi ba, saboda tana son Danliti. Yanxun
shikenan ba xata gane cewar alabarkar mu itace
kwanciyar hankalinta ba, duk tsananin son da
Danliti ke mata, shikenan ta xabi cigaba da
xaman shashanci akan ta nutsu, dn tym kankani
a daura masu aure? Wannan rayuawar tana cike
da tausayi da ban Mamaki, kamar Ya asirce
Mama? Ta kada kai ta ciga, ba haka Mamar mu
take ba alhji, ta sauya saboda soyayya, kenan ta
fi son shi a kanmu? Ina xan samo amsoshin nan
Alhji? Ina xan..... Ya rufe bakin da sauri, ya ace
ya isa haka! Kar ki jefa kanki damuwar da xata
tada miki ciwo, ki kauda kanki ki akan komai,
sannan ki nisanta xuciyarki ga irin wadannan
tambayoyin da kike wa kanki. Xaki xautu saboda
yarinyar da bata damu da lfyarki ba, xamani ne
Allah ya kawo mu da yara ke rufe idanuwan su
akan abinda suke so. Suyi ta fada da iyeyensu
har xuciyoyin iyayen su fara xargin asirce su
akayi. Xan ji dadi da farin ciki idan xa'a ce, duk
wannan abubuwan da suke faruwa, ki dauke shi
amatsayin mafarki mai wucewa, tamkar baki
taba haihuwar wata mai suna sakeena ba. Ta
dube shi xai yuwu ko? Mai hana? Idan har zaki
dage da adduoi, ubangiji ba xai barki haka ba, ta
goge hawayenta ta sauke gwauran numfashi
tace, xan yi iya kokarina Alhji. Ya jinjina kai.
Yace haka nafiso sadiya, kin san ina jin dadin
xama dake, kuma tun ina saurayi ban taba son
wat 'ya mace ba sai ke. Ban fatan abinda xai
salwantar min da rayuwarki, ya kasance wata
kaddara tasa kin fara barina cikin duniyar nan.
Kullum nayi sallah, sai na roki Allah ya fara
daukar raina saboda ba xan iya ganin gawarki ba
halima. Idanuwanta suka kara tara hawaye. Tace
ka daina fadar maganar nan Alhji..... Ya katse ta,
ni ma ba ason raina na fadi ba, domin sirri nane
wanda nake xaton shi kdai ne ban taba gaya miki
ba, sai yau, dole ce ta sanyani, don ina son ki
sami nutsuwa sadiya. Ta matse ido kwallatana
suka kwararo ya mika hannu ya goge mata yace,
sha kurkuminki Maman abdul 3, gwarazan
samarin nan masu takama da baiwar Allah. Ta
numfasa tace, Allah yayi masu albarka baki
dayansu. Kina nufin har da sakeena ko? Ta amsa
da kai, kafin tace, ai mu na mata fatan shiriya
ko? Yace haka ne, toh Allah ya shiryta. Amin ta
amsa. Haka yayi ta rarrashinta, ta samu
nutsuwa, sannan sukayi sallah suma mika kukan
su ga Allah. Na san kilan kuyi musu ko mamaki
idan nagaya muku Mama bata dawo gida ba, sai
bayan sallar magriba. Abu na farko da ta fara cin
karo da shi a kofar sasansu dake kulle, shine
akwatin kayanta. Taja cak! Ta tsya ta xura masa
ido tsawon tym, kana ta matsa ta tura kofar taji
ga,! A kulle. Ta tabe baki tare da jan tsaki, ta figi
akwatin ta juya tana fadin a ranta, sai aga na
kwana a titi. Kai tsaye Danliti ta dosa, yana
xaune kofar shagonsa, inda ta basa. Yana
hangota da akwati, ya mike ya shige daga ciki
yana gayawa Ayuba ga mutuniyar can tafe da
akwati, ko maganarta tace ta tabbata? Ayuba ya
murtuke fuska yace ni xaka tambaya? Au haushi
kaji? Amma dai kana ji na gaya mata kar ta
kuskura ta bari su koreta, don bani da wurin
ajeta, ko ban gaya mata ba? Yace oho! Wai kai
wani irin banxa ne? Yace Ni banxa bane, ai rainin
wayau yasa ka gaya mata hakan. Wa ke jan
ragamar rayuawarta, in ba kai ba? Ai sanin bata
da xabi shi yasa ka raina mata hankali. To ya isa
malam, sai gata tsaye gaban kanta, tana kokarin
dagawa, duk suka xubo mata ido, ta karasa
shigowa, ido waje ya dubi shirgegen akwatin, ya
ce ya dai? Bata saurare shi ba, kofar dakin ta
tasarmawa xata shige. Yayi azama ya shawo
gabanta, magana fa nake yi, kona kokarin
shigewa kamar gidanku? Ta xubo masa ido a
marairaice tace, me na gaya maka? Ni kuma me
na gaya miki? To yaya xanyi? Ina komawa na
iske akwatina akofar gida sun kulle gidansu. Ya
gayara tsayuwa, da yake kuma ke sakarya ce sai
kaka kamo hanya kika taho baki tsaya kika nemi
sulhu ba! Yanxun menene nufinki? Anan xaki
xauna? Cikin shago? Lallai kin cika dakikiya,
Jaka! Kuka sosai ya kwace mata, ta tsugunna ta
rungumi kafafwansa, murya na rawa tana fadin,
karkayi min Haka Danliti! Saboda kai suka koreni,
ina kake so naje, idan ba nan ba?
[12/01 21:58] ‪+234 818 701 7363‬: BAKIN CIKI 2***15
Ayuba ya daga kanta, ya fice
hankalinsa tashe, shi kuwa ko gezau beji ba
ajikinsa, a dage yake kallonta, tsawan tym
sannan ya fizge kafarsa ya kama hanya xai fita,
da sauri ta mike ta cukuikuyo rigarsa, fadi take,
kayi hrk don girman Allah. Wasu samari 2 suka
iso wajen siyen taba sigari, ai sai suka buge da
shari'a, kaya-kaya hayaniya har waje Danliti na
daga murya shi ba xai aje ta cikin shagonwa ba,
ta koma ta nemi sulhu da iayeynta. Kan ka ce
kwabo jama'a sun cika makil a gun. Kai Mama ta
sha zagi da la'anta, Allah shi kara kwando-
kwando. Kalilan ke cewa Allah ya shiryeta, Dan
liti ya gacciye banci kofar shagoin ya xauna yace
yaga uban da ya tsaya mata agarin nan, wnada
xai sashi ya ajeta. Baiwar Allah kuwa na tsugene
gaban akwatinta, tana ruasar kuka har karfe
10pm. 'yan ganin kwakwaf suka gaji suka koma
gidajen su dauke da labari mai ban al'ajabi. Wasu
suna ganin bai kamata Uban dawaki ya koreta ba
a matsayin sa na Uba, kuma babban mutum mai
sarauta, wasu kuwa suna ganin hakan shine
daidai, imna xai sa BAKIN CIKI? Idan bai sallame
ta ba, tunda ta tara masa, ya cika masa xuciya,
tana neman fashewa ta hallakashi? Ai gara da ya
sallamata duniya ta koya mata hankali. Ga darasi
na farko nan ta fara gani, duk iskancin Danlitim
yace baxai aje taba. Alhalin saboda shi aka
koreta. Wannnan ya nuna a fili ita ta nace masa
kamar sauran 'yan mata marasa xuciya. Mutane
na mamaki abinda Danliti yake da shi wanda
yake tsonewa 'yan Mata ido. Su mutu cikin
soyayyar sa. In bata ga kyau me yake da shi? Shi
babu hali babu kwakkwaran asali. Amma duk
wacce ta fada tarkonsa sai gagari iyayenta. Ko
don kudi da ya ke kashe mus ne? Shiya sa suka
dauki laifi kacokan suka dorawa 'yan Matan masu
biye masa don kwadayi da kyalekyalen jikinsa.
Wayyi, kai bai san dawan garin ba, dai bai yi
tunanin kutsa kansa ciki ba. Tun ciki dare surutai
kala-kala suka fara baza gari. Shi kuwa gogan da
ya ga kowa ya watse sai ya matso ya xunguri
Mama da kafa, ta dago kai da sauri ta dube shi,
matso mana nan kiji, ta matsa gareshi, tana
hawaye. Ya dubeta da kyau yace, ke banxa ce
wlh, shi ya sa kika bani haushi. Nace ba xaki
xauna anan ba. In banda hauka irin naki, ya
xa'ayi ki xauna tare da mu cikin shago? To ina
sane da abinda nakeyi, kin gane? Saboda haka ki
koma ki nemi wani wurin ki xauna, ki bani nan da
sati xan san abinyi. Murya dushe tace, ni bansan
inda xani ba, a'a ko gidan 'yanwanku ba xaki je
ba? Ko baku da su ne? Sai dai inje gidan su
Baraka, yace ko gidan su Mubarak xaki, sai kinm
dawo matsalar kice. Amma ba xaki kwana
shagon nan ba. Yauwa, tashi ki sungumi
akwatinki, ki wace kar su kulle gidansu. Tace to
nagode, sai da safe, Allah ya kaimu 'ya bebine.
Muyi fada mu shirya ko? Kar ki damu xan ganki
goben. Tayi murmushi, dadi ya rufeta, ta mike
tana kara masa godiya, taja akwatinta ta nufi
gidansu Baraka. Ya mike janye da benci yana
kyalkyala dariya, ya shige shago. Kai mugu dan
gidan buzu mai shayi! Yayi wa kansa kirari ya
shige daki. Ayuba na kallonsa yana kada kai.
Gidan su Bara akulle yake, saboda sha dayan
dare tayi ma. Ta shiga bugawa har aka xo aka
bude mahaifin Baraka ke tsaye cikin xauran, ya
dubeta da kyau yace, Mama ce? Daga ina haka?
Ta fara kuka yace shigo shigo ciki! Ta wuce da
uban akwati ya maida kofa ya rufe. Tana gaba
yana biye da ita yana fadin, subhanalillahi! Dakin
Inna saude suka shiga tana tsaye tsakar daki,
lfya? Ta xube sharaf! Cikin kuka tace, abba ne ya
koreni..... Ina saude ta nemi waje ta xauna, yayin
da malam kasim ke fadin, me ya sa Uban dawaki
xaiyi hak? Inna saude tace BAKIN CIKIN ta ne ya
ishesu. Ace kamar Mama ta gagari kowa duk
abinda ya sameta da abinda ake gaya mata ba
su isheta nadama ba, idan ba su koreta ba me
kike so suyi miki? Ba shashanci kike sha'awar yi
ba? To sun baki hanya, meye kuma na kuka?
Mal. Kasim yace hakan ba hujja bace, duk abinda
xatayi, gara tana gabansu suna tsawata mata,
yau da gobe ana hada mata da addu'a, sai Allah
ya taimaketa ta gane illar abinda take aikatawa.
Saboda haka ta xauna, gobe Allah ya kaimu lfya,
xanje in ganshi. Ke kuma je ki kwanta kiyi tunani,
meye amfanin lalata rayuwarki da kikeyi? Har
jikokinki sai an yi musu gori, wannnan abinda
kika aikata! Kina da babban laifi mama, sai kin
tuba kin bi Allah kin bi iyayenki sannnan xaki ga
daidai a rayuwarki, kinji ni? Ta amsa da kai, yace
ta shi ki shiga wajen 'yar uwarji kafin Allah ya
kaimu goben. Ta mike simi-simi ta ja akwatinta,
inna saude ta xuba mata ido tana mamakinta. Ta
kada kai, taca baka ce xata aikata ba, yarinya
kyakkyawa, ta lalata rayuwarta. Allah ya shirya
mana, yace amin albarkar annabi. Atsakar gida
taga Baraka tsaye tana share hwaye, ta matso ta
kama mata akwatin suka shiga dakin, kowacce ta
nemi wuri ta xauna bakin katifa. Baraka ta
dubeta.........
Tace anya mama abubuwa da kike yi
kanki kalau? Ke bakijin kinya? Baki tunanin gaba
daya idanuwan garin nan sun dawo bisa kanki?
Baki da martaba da darajar Abba agarin nan?
Haba Mama, kamar ba tare muka taso ba?
Tarbiyarmu iri daya, nutsuwa da kamun kai, kowa
na yabon mu. Mutane na rububin mu, da son
hada xuri'a tagari. Ta daga kai sama, idanuwa
cike da hawaye ta cigaba, Allah ya isa
tsakaninmu da Danliti! Ta dube ta sukayi ma juna
xuru kafin Mama tace kar ki sake xagin Danliti
Baraka, alhakin sa xai kamaki, laifin mune? Tun
tym din da mukace muna son juna, ya kamata su
Abba su rungume mu hannu 2 amma suka ki,
suka gwammace in kwashe kayana in bishi. A
tunanin ki wane sakamako ya kamata su gani?
Bayan wannan dake jikina? Baki sake take
kallonta, kafin tace, maganar Banza ce, idan duka
jina kunnuwa ne xai taba sauraronki ba, wa kika
burge don kin aikiata wannnan sakarcin? Shi
kansa Danlitin adage yke kallonki. Kin dawo an yi
miki afuwa, cikin nman ya bayyana, duk sun hkr,
sun shanye, amma ki ntsu xuwa tym din da xaki
haihu, a daura maki aure, kar fa ki manta xaman
nan naki agida ibadane tunda Allah ya shifida
hakan, sai ki ga dalilin xaman, duk xunubunku
sun kankare, auran ku yayi karko tare da xuria
masu albarka. Ki kwanta kiyi tunani mama, ko
asiri Dan liti yayi miki, xakewar taki tayi yawa. Ta
sualala kafita ta kwanta, tace, na kwanta shekiya
Baraka, sai da safe ko? Ta bita da kallo ta
numfasa, tace Allah ya sa ki gane. Amin, ta
amsa da gatse ta juya baya abinta. Baraka ta
mike ta rufe daki ta dawo ta kwnta. Ta jima bata
sami barci ba, saboda juyayin halin da 'yar
uwarta ta shiga. Da farar safiya M.kasim ya usa
gidan Ubban dawaki yasa aka yi masa sallama da
shi, jin cewa shine ke sallam ya sa yace ya shigo
cikin gida. Bayan su gaisa. Umma ta fito suka
gaisa. Sannan ya maida jawabinsa, a karshe
yace, alhaji kar bacin rai yasa ka yanke wannan
hukunci, ni ina ganin gara yarinyar nan ta xauna
agaban ku, kuna tsawata mata, sai Allah ya
taimakemu ya shiryar da ita. Don girman Allah ka
yafe mata dawo gida, tunda tayi tunani taxo
wajenmu, ta kawo mana kukanta. Abba ya gyara
xama yace, a tunanin ka a kashin kanta, ta yanke
shawara taje wajen ku? To ba haka xancen yake
ba, kila ba xaka sani ba ne, saboda kuan cikin
lungu. Amma ni tun jiya na sami labarin
wulakancin da yaron nan yayi mata, ya tara mata
jama'a, ya tozarta ta, ya kuma ce ba xata xauna
masa a shago ba, kaji dalilin nemanku, amma ba
nadama tayi ba. Yace, duk da haka ina son ka
duba girman da martabar ka agarin nan. Kayi hkri
ka amshi rokona, ba don ni ba, sai don girman
Allah da darajar iyaye. Ya sunkuar da kai yana
kadawa, kafin yace, M.kasim ban ki ta taka ba,
amma ba xan iya xama da yarinyar da ban isa in
bata umarni ta bi ba. Ta fita tayo shashancinta,
ta dawo min gida ta wanke najasa ta kwanta.
Mts! Ban jin idanuwana xa su iya jure gainin
wannan kaxanta. Gara ta tafu su cikashe. Wlh na
hkr da ita, kuma ina rokon Allah ya sanya mana
dangani nida Mahaifiyarta, ba kuma xamu gaza
ba wajen yi mata addu-ar shiriya. Watakila wata
rana taga uwar bari, ta dawo da kanta ta neme
mu. Kaga a tym din xan tabbatar da tayi nadama.
M. Kasim yayi shiru, jawabin Uban dawaki na
cike da tausayi, ya numfasa, yace, na yarda da
kai Alh. Sai dai har yanxun ina rokonka, da ka
sake bata dama ta karshe, mu gani.idan bata
daina ba, to muma sai mu tsame hannayen mu.
M. Kasim ya cikwa Abba ido kwarai da gaske, ya
jima kafin ya numfasa, yace, shikenan ba komai
nagode. Yace nima nagode, Hajiya akara hkr, a
bata damar karshe, tace babu komai M. Kasim,
Allah saka da alkhairi. Yace amin, barin in koma
in turo saude ta dawo ita. Tace to ka tsaya kaga
abin kari akawo maka mana, ya mike cike da
fara'a, yana fadin alhmdlh, kar ki damu nagode,
to nabr ku lfya, Allah ya shige mana gaba, suka
amsa amin. Yaka hanya fice. Bayan tafiyarsa
kamar da hadin baki, jama'a sukayi ta xuwa suna
ba uban dawaki hrk tare da rokonsa ya daure ya
maida 'yarda gabasa xai fi kyau agareshi. A cikin
su har da abokansa da yaron gidansa, watau
kalla. Duk ya karbi rokonsu, kuma yaji dadin
kulawar jama'a gareshi tare da tausaya masa
akan kaddarar da ta fada wa iyalinsa. Karfe Tara
saura, Inna saude ta taso Mama xuwa gida. Bata
ma biyo da ita ta shagon Danliti ba, balle ya
gansu, haka suka taru da matan gidan kamar
zasu cinye ta danya, sannan matza suka shigo
suka dasa nasu. A gaban kowa suka tilasta, ta
dauki alkawarin ba xata sake xuwa ko ina ba,
kidan kuwa ta saba, to a yanke mata hkunci da
yafi wannan. Kwana 2 hatsaniyar nan ta kwnata,
mama na xaune cikin gida bata fita daidai da
tsakar gidan sasansu. Muna iya cewa Danliti bai
murda kambunsa bane haka? Saboda haka
xuciyar Mama ta sami 'ya nutsuwa. Bata ita
kadai ba, su abba ma sun sami 'ya nutsuwa har
tana debo 'ya'yan itatuwan da Abba ya ka siyo ta
kawo mata, tace ta sha saboda rashin cin abinci
da take fama da shi.....
***************** A wannan
asabar din ma abdulkrm ya xo daiyalinsa duka.
Su ameera nata murnar ganin auntynsum domin
sun jima basu ganta ba. Dr. Na ta dabo, yana son
ya taka, sai 'yar banxar kuiyam shi ya sa yaki
yarda Mama ta daukeshi. Aunty Rabi ta tasa ta
da nasihohi, ayoyi, hadisan Manxo SAW akan ta
dage ta yaki xuciyarta ta dawo kan kanya,
sannan ta nuna mata wannan ba shine soyayya
ba, duka saurayin da ya nemi lalacewa da
yarinyar da yake so, a hakikanin gaskiyya ba son
gaskiyya yake mata ba. Sha'awar sassan jikinta
kawai yakeyi. Haka yayanta ta tsatsagge mata
gaskiyya, har yayi mata alkawarin idan ta nutsu
ta xauna gida kamar yadda aka umarceta, to
bayan ta haohu za'ayi bikinta, duk abinda take
so, shi xai sayo mata. Mama ta wani kuka tana
ba su ameera tausayi. Anann suka kwana,
washegari lhadi karfe 12noon suka juya. Su
ameera nata tambayar antyn su yaushe xata xo?
Tace kar su damu tana nan xuwa nan bada
dadewa ba, suna isa gida, yayan ya kira 'yan
uwansa, ya labarta musu abinda ya gani game
da Mama, idan har ya dore a hakan, alhmdlh! Ana
iya cewa an fara samun nasara. Kowa yayi farin
ciki jin wannan labarin da fatan Allah ya shige
mus gaba. Allah, da ikonsa a yammacin yau din,
tun bayan sallar la'asar mama ke cike da kewar
Danliti, kafin 5pm ra mance kaf! Da alkawuran da
dauka, babu abinda take so face gain Danliti,
kewarsa ta gigita kwakwalwarta, ta birkita ta.
Kamar an tsikare, kawai ta tashi ta suri gyale da
takalmi ta fito kanta tsaye ta fice abinta. Dan
gogan ta samun cikin dakin barcinsu, tana
shigowa yana xubawa wani kaskon rushi ruwa,
ya dago ido ya dubeta, yace ba xan miki sannu
da xuwa ba. Ta xaune gefensa tana murmushi,
saboda me? Ya xubo mata harara, yace kwanaki
nawa rabon ki da nan? Sabo da nayi miki fada
ko? Ta rungomoshi tana dariya, ayya nawan ba
haka bane, kowa yasa min ido, sai surutai sukeyi
kamar ni kadai na fara soyayya agarin nan.
Amma kana cikin raina, kaima ka sani, bani da
burin da wuce in kasanxe tare da kai, ta bae baki
yace tsarani, au baka yarda ba? T yanxun ba ni
na xo ba? Dana kiraki ba? Ka kirani? Kamar ya?
Ya ture kaskon ba xaki gane. Sai dai na yarda
kina sona, tunda kika amsa kiran. Ta xura masa
ido tace

Please Login or Register in order to submit comment