Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dole tasa ta amsa ganin sun fita sun barta da kuɗin, sanda suka fita Umma ta dubi kuɗin tace.
"Sannu Ablah, ya kike jin jikin."?
Murmushi Ablah tayi tace.
"Bana jin komai yanzu Umma, dama nayi tunanin hankalinki zai tashi."
"Ba dole hankalina ya tashi ba, alhamdulillah tunda Allah yasa kina hanun na gari"
Kuɗin Umma ta kalla ɗagawa tayi taga wanda Al'ameen ya ijiye mata 200k shi kuma Haidar 50k numfashi Umma ta saki ta cigaba da cewa.
"Alhamdulillah! Mun sami kuɗin registration ɗinki Ablah idan kace ya zakayi ka manta da Allah, gobe da sassafe zanyi sammako naje na biya kuɗin nan dubu hamsin kuma sai mu sayi kayan abinci."
Tayi Maganar cike da farin ciki, a da harta fitar da ran cewa ƴarta zata yi karatun likita, saboda bata da kuɗaɗen registration dana littatafai, sai gashi yau Allah ya mata, itama Ablah murmushi ta saki tace.
"Umma bara naje na kwanta."
Da to ta amsa Ablah ta shige ƙaramin ɗakin nasu, bata juma da shiga ba Abdu ya shigo da gudu hanunsa riƙe da leda ya sayo kayan shayi a gaban Umma ya zauna yana dariya da kanta Umma ta haɗa masa tea ɗin kafin ta tashi ta ɗauki hijabin ta tare da leƙawa ta cewa Ablah ta shige gidan aikinta.
Da adawo lafiya Ablah ta amsa mata tare da maida kanta ta kwanta gidan su ƙawarta Hafsa take son shiga sai dai bazata iya sakamakon ƙafarta dake ɗaure.



Tunda ya zauna a Office ɗinsa jikinsa duk yayi sanyi, bai taɓa zaton cewa akwai waɗanda suke cikin ƙuncin rayuwa ba haka, ace abincin da zakaci ya gagareka, wai garin rogo shine abinci.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! "
Ya furta yana tuno kukan da yaga Yarinyar tanayi a cikin mota, gata kyakkyawa amma sam ba jin daɗin rayuwa, ga rashin mahaifi, Tabbas suna buƙatar taimako, amma duk da haka sai yake ganin Yarinyar kamar munafuka ce.
Yayi Maganar cikin ransa, ya juma yana jinjinawa lamarin wunin ranar dai haka yayi aikin cike da tunani.

Koda suka tashi a aiki tare suka dawo gida da Haidar sai dai basu kuma Magana akan gidan su ABLAH ba har suka shigo gida, Haidar part ɗinsu ya shige shima Al'ameen ya shige nasu, Ummi ya samu ita da Inna Jumma suna zaune a falon sun zubawa tv idanu da Sallama ya shiga jikinsa duk a sanyaye ya zauna kusa da Ummi tare da kwantar da kansa a cinyarta idanunsa ya lumshe yana sakin ajiyar zuciya aduk sanda ya kwanta jikin mahaifiyar sa sai yaji nutsuwa da sanyi na ratsa jikinsa damuwar dake damunsa sai ta kau, Inna Jumma ce tace.
"Yau naga wani sabon salo, dan Allah dubeka goɗai goɗai dakai ka kwanta mata a cinya kalan ka karyata, ke kuwa Gaji kin zuba masa idanu tsabar jarabar son ƴaƴa, dallah ɗagata Malam."
Murmushi Al'ameen yayi idanunsa na rufe a hankali tamkar baya son Maganar yace.
"Ai ke matsalarki kenan shishshigi da saka idanu meye matsalarki dan ɗa ya kwanta a jikin Maman sa, Please karki dameni nutsuwa nake nema."
Tsulum Inna Jumma ta miƙe Ummi na dariya ba tare da tace komai ba, zuwa tayi ta ɗakawa Al'ameen duka tare da cewa.
"Allah sai ka tashi, baka isa ka nakasa min ƴa ba."
Dariya Al'ameen yasa tare da miƙewa ya cewa Inna Jumma.
"Oh Wannan tsohuwa kin isheni, yauwa Inna Afnan ta dawo ne.?"
Murmushi Inna Jumma tayi cike da salon mugunta tace.
"Ɗan albarka ta dawo tana can Uwar ɗaka yanzu ta gama min dariya kamar taga mahaukaciya."
Miƙewa Al'ameen yayi ba tare da yace komai ba ya haura, Ummi da kallo ta bisa domin kuwa ita bata san neman me Al'ameen yake yiwa Afnan ba, bedroom ɗinsa ya shiga tare da ijiye jakar sa, belt ya ɗauka ya fito ROOM ɗin su Afnan ɗin ya shiga tana zaune ta ƙure digin daga ita sai best da legis, kallonta yayi gaba ɗaya hankalinta naga waƙar bata ma lura dashi ba, hanu yasa ya dannawa ROOM ɗin key ya tako har gabanta sai da yazo gabanta Afnan ta kula dashi cike da tsoro taja baya tana zaro idanunta ganinsa da belt, hanu yasa ya kashe waƙar yana dubanta tace.
"Me kika cewa Inna Jumma da safe, wato a gidan nan kin zamo fitsararriya ko, kina ganin kin isa kinfi ƙarfin kowa, to ko Daddy bazai zageta ba bare kuma ke, ban hanaki kiyi wannan shigar banzan ki fita dashi ba.?"
Cikin in.ina Afnan tace.
"Ni..ni.. fa ban zageta ba walla......."
Tsawa ya daka mata tare da cewa.
"Rufe min baki dan ubanki sharri zata miki."
Yayi Maganar yana zuga mata belt ɗin wani irin ƙara tasa na azaba, shi kuwa sai zuba mata yake tana ihu Ummi dake zaune ne ta jiyo kamar sautin kukan Afnan ne ta tashi da sauri ta haura wato neman da yake mata kenan room ɗin ta nufa tare da turawa rufe gam taji sa, ga kuma Afnan na zunduma ihu, Ummi ƙofar ta buga tana cewa.
"Al'ameen ka buɗe min ƙofar nace!"
Yana jinta yaƙi amsawa bai kuma fasa dukanta ba, muryar Ummi da yaji cikin tsawa ya sashi dakatawa.
"Ina maka gana dan ubanka bazaka buɗe ba! Idan ka kuma saka hanu jikinta wallahi sai na saɓa maka."
Runtse idanunsa yayi domin kuwa a duk sanda zai hukunta Afnan Ummi ke dakatar da shi, belt ɗin ya sake tare fitowa a fusace ya buɗe ƙofar bai kula Ummi dake tsaye bakin room ɗin ba, ya shige ROOM ɗinsa cikin ɓacin rai, Ummi shiga tayi tana kamo Afnan jikinta duk ya tashi yayi ja abinka da farin mutum, sosai Ummi ke faɗa, shi kuwa tollet ya shige yaje ya sakarwa kansa ruwa ya juma sosai cikin tollet ɗin kafin ya fito, wayarsa ce tayi ringin tare da dubawa *BROTHER KHALIFA* ɗan murmushi ya saki tare da ɗaga kiran yana cewa.
"Ya akayi ne mutanen Egypt."
Daga can Khalifa yayi dariya tare da cewa.
"Kaga sauri nake jirgin mu yanzu zai tashi, nan da 8 kazo ka ɗauke mu a airport."
Murmushi Al'ameen yayi tare da cewa.
"Au wato ma bazata ka mana, har kun gana exam ɗin kenan, to Allah ya kawo ku lafiya."
Da ameen Khalifa ya amsa suka katse kiran, Al'ameen Aunty Amarya ya kira, duk yasan ta fita unguwa amma dai yasan itace kawai zatayi wa su Khalifa abinci mai kyau, tana zaune gaban Hajiya Mansura ya kirata bayan ta daga ne ya sanar da ita cewa su Khalifa suna hanya ta dawo ta haɗa musu abinci, murmushi ta saki ta amsa da to tare da kashe wayar.


Dariya Aunty Amarya ta saki tare da cewa Hajiya Mansura.
"Albishir!"
Murmushi Mansura tayi ta amsa da
"Goro!"
"Ƙaramin marar kunyan yana hanya shida Ashfat, zasu iso nan da 8.".
Guɗa Hajiya Mansura ta saki tare da cewa.
"Ta faɗi ƙasa gasassa,dama ta samu, Amarya zamuyi amfani da wannan damar mu aikasu lahira kafin ma su iso gidan, kuma cikin hanya mai sauƙi zamu haɗamu musu accident Wanda babu wanda za'a zarga a cikin mutuwar sai a ɗauketa a hatsari."
Dariya amarya tasa suka tafa tace.
"Bani da ja acikin zancen ki, bara ma kiga na tashi naje, ki tsara komai kimin text zan miki transfer ɗin kuɗi sannan zan sanar dake da zarar an tafi ɗaukosu sai kubi bayan su."
"Ki tabbatar fa kin sanar damu akan lokaci yanzu zan nemi Isah Alolo."
Murmushi amarya tayi tare da cewa.
"Baki da matsala dani ƙawata."
Tayi Maganar tana dariya cike da farin ciki suka rabu.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Kallon Amnat tayi tare da sakin dariya tace.
"Ko tsarin nawa bai miki bane, idan akwai shawara gara ki bani time na ƙurewa, gida nake son na samu yau a wajen sa koda ƙarami ne."
"Nafeesa sai naga kamar kina nuna haɗamarki da wuri yaushe ma kuka haɗu dashi da har zakiyi plan ɗin samun gida, mtss! Karki kuskura ki bari ya fahimceki da wuri domin kuwa duk son da yake miki wallahi zai watsar dake, yanzu abinda zakiyi maimakon kiyi ƙaryar cewa sister ɗinki tana cikin matsala an koreta a gidan haya ya taimaka musu ya basu inda zasu zauna, to gara ki sauya da cewa ya taimaka musu da kuɗin haya, idan kika bi a hankali gidan ma zai saya miki wata rana, amma ni ga wani shawara mai zai hana ki kai sunan Haidar wajen Malam ya miki aiki akansa duk abinda kika tambaya ya baki babu musu bare bincike ni ina ga zaki samu idan kin kaisa wajen Malam......................."





Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi Naira ɗari biyu kacal 200 guda biyu ne daga aminai biyu Wato ƙawalli da ƙawalliya.

ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN.

acikin littafinta mai taken *AHLAN*

RASHEEDAT USMAN UMMU NASMAH.

Acikin littafinta mai taken *AMINAINA KO ITA?*


Guda ɗaya zaki samu ne akan farashi Naira 200 idan kuma duka biyun kike so zaki biya Naira 300.

Turo da kuɗin ki ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank.

Ko kuma ku turo hoton katin waya na Mtn card ta ɗaya daga cikin waɗannan numbobin.
08147537180
Ko
08165550116



Please Banda VTU hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan sai ku turo screen SHORT SHAIDAR BIYA ta cikin waɗannan numbobin.

Kuyi hanzarin biya domin kuwa littattafan sunzo ne da zafin su, zasu bada citta karku sake a barku a baya koda kuɗin ku sai da rabonku.



Please Share and comments.



*Ummu Nasmah ce ✍🏻*
[6/19, 11:09 AM] UMMU NASMAH🥰: 💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅



🤦🏻‍♂️🤦🏻‍♂️🤦🏻‍♂️



💔 *AMINAINA KO ITA?* 💔


🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️



🙆🏻‍♀️ *(BETRAYED LOVE!)* 🙆🏻‍♀️



*NA*


*RASHEEDAT USMAN*

*(UMMU NASMAH)*




Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.



*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*




*Page 10*




"mtss! Ina ga hakan zamuyi insha Allah gobe zamu fasa, dan wallahi ba ƙananan kuɗi nake buƙata ba, a hanunsa, jiya wannan ɗan iskan ALH Atiku Naira ya kirani wai mu haɗu a hotel."
Murmushi Amnat ta saki tare da cewa.
"Za kuma ki samu domin kuwa ko duka dukiyar sa kikace ya kawo miki zai kawo babu musu, ai kinsan aikin malam, kinje hotel ɗin ne.?"
Kanta Nafeesa ta ɗaga alamun eh.
"Naje ina ga ban dawo gida ba ma sai 10:30pm kinsan dawowata har Baba ya dawo, da sanɗa kamar munafuka haka na shige room ɗin mu, dama Allah ya rufa min asiri bai ganni ba, dana shiga Uku da mita."
Dariya Amnat ta saka tace.
"Kai ƙawata kice kin tsallake rijiya ta baya, da ya kamaki wallahi da kin shiga Uku, dan babu abinda zai hana bai jibgeki ba, dan wannan tsohon naku ba dai bala'i."
Bakinta Nafeesa ta taɓe tare da cewa.
"Babu kuma abinda yake iya tsinana mana sai, sai iko da gadara, ke nifa yanzu Allah ko kallon fuskar wannan tsohon bana sonyi, balle na tuno cewa ubana ne."
Dariya Amnat ta saka tare da miƙewa tace.
"Time na ƙurewa, nasan yanzu haka yana can mu yake jira, ƙawata nafa faɗa miki karkiyi Maganar sayan gidan nan yanzu."
Miƙewa tayi ta ɗauki jakarta ta saka hijabinta har ƙasa suka fita, bata ma yiwa Mama Sallama ba, a ƙofar gidan nasu suka gansa tsaye jikin motar sa, tunda suka fito yake sakin murmushi cike da ƙaunar Nafeesa.
"Assalamu alaikum Duniyata Barka da isowa."
Tayi Maganar tana kashe murya tare da murmushi mai shiga rai, shima murmushin yayi tare da amsawa da.
"Amin wa'alaiku mussalam Farin ciki na, ya naga sai walwali kike kinyi kyau fa sosai farin ciki na."
Murmushi Nafeesa tayi tare da cewa.
"Duk walwali na ban kaika ba Duniyata, domin kuwa a ko wani lokaci kyawu kake ƙara min fiye da kullum, idanuna ko yaushe a cikin begen ganinka yake, zuciyata kuwa bata da aiki ko yaushe zai tunaninka, hanci na bashi da muradin daya wuce jiyo ƙanshinka, idan har na wuni guda ba tare da naji muryarka ba, sai naji kunnuwa tamkar sun kurmance, Soyayya ni'ima ce musamman idan ka haɗu da masoyi na gari mai addini ilimi tarbiyya sanin darajar manya mai riƙon Amana to Tabbas ubangiji ya gama maka ni'imar duniya, shiyasa nake jina yanzu bani da wata damuwa saboda na sameka, kasan meye kuwa.?"
Sosai sonta yaƙe ƙara shiga zuciyarsa domin kuwa macece ita wacce ta gama fahimtar yadda ake kula da masoyi wanda shine burin ko wani namiji ya samu mai kula dashi, ji yake bazai taɓa iya rayuwa ba tare da Nafeesa ba, tamkar numfashin sa haka yake jinta a zuciyarsa, kansa ya kaɗa alamun a'a yana lumshe idanunsa.
Murmushi tayi tare da jan numfashi kafin ta cigaba da cewa.
"Kana da kyawawan ɗabi'u sannan ka fito daga gidan mutunci, ga ka kuma da tausayi, wannan dalilin yasa nakejin bazan taɓa iya rayuwa babu kai ba, ina sonka Duniyata kuma zan cigaba da sonka har ƙarshen rayuwata I love You."
Wani lumshe idanunsa yayi cike da jin daɗin maganganunta, dariya yayi tare da cewa.
"Bansan wacce irin Soyayya nake miki ba, Nafeesa Soyayyar ta wuce ma'auni a zuciyata, na dai san bazan iya rayuwa babu keba, koda zan rayu to Tabbas zanyi rayuwa ne cikin wahala, bazan iya rabuwa dake ba komai tsanani ko mai wahala bazan gujeki, kimin alƙawari bazaki gujeni a ko wanni irin yanayi domin kuwa ji nake tamkar na shekara goma tare dake mantawa nake da bamufi kwanaki tare ba, shekaru nake ɗauka munyi."
Murmushi mai cike da salon yaudara Nafeesa ta saki kafin tace.
"Ka daina kiran cewa zan gujeka, babu macen da zata sameka a matsayin miji kuma taji ta gujeka abune da bazai yiwu ba, har abada ina tare da kai."
Tayi Maganar tare da ƙin amsa masa cewa tayi alƙawari, Amnat ne tayi gyaran murya cike da zolaya tace.
"Au sannunku romio, wato ma kun manta dani shanye ko."
Dariya Haidar yasa tare da cewa.
"Ni ɗinne idan tana gabana bana kallon komai sai ita, ta haske min kene ya kk."
Yayi Maganar yana dariya, sun ɗan juma suna zance har aka fara kiraye kirayen sallar magaruba, numfashi Haidar ya saki tare da cewa Nafeesa.
"Kince akwai Magana gashi anfara kiran sallah ya kamata na koma gida, ina jinki menene.?"
Kanta Nafeesa ta sunkuyar alamun kunya tare da cewa.
"Dama akwai ƴar sister ɗin Mama mijinta an koresu a gidan haya to suna cikin matsala yanzu haka tana gida sun rasa inda zasu zauna, shine Mama tace a maka Magana ko zaka taimaka musu."
Ɗan murmushi Haidar yayi tare da cewa.
"Ikey ba damuwa dama akwai wacce itama muke da burin a taimaka musu so insha Allah zansa da ita a ciki babu damuwa zan miki Magana idan komai ya kammala."
Murmushi Nafeesa tayi tare da masa godiya, Sallama sukayi yaja motar sa ya tafi, Nafeesa tafa sukayi da Amnat suna dariya, sannan suka shige cikin gida.


Bayan sallar magaruba, kusan isha'i Aunty Amarya ta gama haɗa komai girki mai rai da lafiya tayi musu yau zuciyarta wasai take jinta domin kuwa gani take burinta zai cika zasu dawo dai-dai da Ummi a cikin gidan, ita kuwa Ummi babu komai a cikin zuciyarta Tamkar ƙanwa haka ta ɗauketa, Ummi zoɓo ta haɗa musu sosai take farin ciki da zuwan yaran nata shekara biyu rabon da su dawo gida hutu sai yau ga Ambassador ya hanata zuwa tagansu, Al'ameen da kansa ya kira Haidar cewa yazo su tafi ɗauko Khalifa da ashfat airport, ƙarfe bakwai da rabi, Al'ameen ya fito, numbern Haidar ya kira baya tafiya, da kamar zai shige sai kuma ya shiga part ɗin nasu babu kowa a falon sai ƴar aikinsu Azumi, cikin girmamawa Azumi ta gaishe da Al'ameen, a daƙile ya amsa mata tare da tambayarta "Haidar fa" Azumi sanin cewa Haidar baya nan ya sata sanar daahi ya fita, bai kuma cewa KOMAI ba yayi fitarsa, bai kuma nemi sabon drevern da suka samu ba, yaja motarsa ya tafi duk shige da ficen Al'ameen Aunty Amarya idanunta yana kansa, sanda ta tabbatar da cewa shine da kansa ya tafi ɗaukosu ya sata kiran Hajiya Mansura ta sanar da ita, wayar ta kashe tare da komawa cikin su Ummi da Inna Jumma, dama ita Maimu tana part ɗin Aunty tare da Madina da Rufaida.

Hankalinsa kwance yake dreving ɗin, yayi nisa da tafiya harma ya kusa shiga airport ɗin yaji wayarsa na ringin dubansa ya kai ga wayar, Bros Haidar, amsa kiran yayi tare da cewa.
"Ina jinka"
Daga can Haidar yace.
"Sorry Company na koma yanzu Abdul ya kirani game da ɓatan kuɗaɗen nan, amma insha Allah yanzu zanzo airport ɗin sai mu haɗu."
"Okay sai ka iso"
Abinda ya faɗa kenan ya katse kiran, ya cigaba da dreving ɗinsa, harya shiga airport ɗin, parking yayi tare da fitowa, can gefe ya hango kujeru Uku babu kowa a wajen da alamu dai wajen bazaiyi hayaniya ba, hakanne ya basa sha'awar zuwa ya zauna yana jiran isowar jirgin su Khalifa, tunda ta zauna ya maida hankalin sa ga wayarsa a yayin da Isah Alolo ke haƙonsa, sai da suka tabbatar cewa hankalinsa baya ga motar sannan suka samu suka sunce tayar motar cikin hanzari suka bar wajen, cike da saɓani suna fita Haidar kuma na shigowa, shima hango motar Al'ameen ya sashi yin parking gefenta, tare da kiransa ya faɗa masa inda zai samesa, sun ɗan juma kusan 8:15pm jirgin nasu ya sauƙa, miƙewa sukayi dukkan su tare da nufar jirgin suka tsaya, yayin da fasinja suke ta ƙoƙarin fitowa, a hankali yake jawo jakarsa fuskarsa cike da murmushi bayansa wata budurwa ce, wacce take mungun kama da Marigayiya khairat, hango su yasa Al'ameen sakin murmushi shima, ashfat da gudu ta faɗa jikin Al'ameen tana dariya Shima murmushi yayi tare da buga bayanta yana cewa.
"Welcome my sweet sister"
Kasancewar duk cikin ƴan uwansa Al'ameen yafi jituwa da ashfat sosai yakan iya zama da ita yayi hira, shi kuwa Khalifa Haidar ya rungume cike da farin ciki suke yiwa juna sannu, Haidar ne cikin zolaya yace.
"Oh wato dai ashfat kin manta dani Al'ameen kawai kika gani, daɗin abun ma dai nima ga nawa ɗan uwan ya zo gareni."
Murmushi ashfat tayi tace.
"Kai yaya Haidar, wayace na manta da kai, babu ta yadda zan manta da ya Haidar ɗina, ina yaya Faruq."
Murmushi Haidar yayi tare da cewa.
"Au baki san yana can American tare da Daddy ba."
"American kuma"?
Khalifa yayi Maganar cike da mamaki, Al'ameen ne yaja hanun ashfat tare da cewa.
"Kunga nan fa ba wajen hira bane, ku bari mu ƙarisa gida kuyi zancen, kai Khalifa shiga motar Haidar ke kuma ashfat muje."
Yayi Maganar yana buɗe motar itama ashfat zagawa tayi ta shiga, bai tsaya jiran shigansu Haidar ba yaja motar yayi gaba, kafin suma Haidar suka bi bayansa.
Tunda suka ɗau titin ashafat ke famar bawa Al'ameen labari wani ya bata amsa wani kuma yayi dariya kasancewar ta mutum mai shegen surutu.
"Ya Al'ameen Allah kuwa da Bro khalifa yace na shirya jibi zamu dawo gida Nigeria sai naji zuciyata ta cinke, kawai naji bana son tafiyar, amma fa a raina ina son ganinku Nigeria ne kawai bana son d............"
Bata ƙarisa ba birkin motar ta ƙwace daga hanunsa take motar ta fara juyi a tsakiyar titi, taya ɗaya ta fice, karo motar ta dinga ci da motocin dake gabanta, accident ya dinga haɗuwa, ashfat kanta ne ya dinga gwaruwa da ƙarfen motar yayin da Al'ameen yake ƙoƙarin dakatar da motar a gigice amma ya kasa aiwatar da hakan, Haidar dake bayansa ne yayi parking suka fito a gigice suna salati, wani mai mashin Al'ameen ya daka da ƙarfi take mutumin yayi gefe shida mashin ɗinsa, ƙara dukan wata mota tayi da ƙarfin gaske furfin motar ne ya buɗe da ƙarfi, tamkar wacce aka wulllo ashfat haka ta faɗo daga cikin motar ta bigi ƙarfen mashin, fitt ƙafarta guda ɗaya ta fita tamkar an saka wuƙa an dashe, wani irin mungun ƙara ta saki mai shiga har cikin ƙwaƙwalwa jin ƙararta yasa Al'ameen runtse idanunsa, daga wannan ƙarar koda motsi ashfat bata kuma yiba, bayan motar Al'ameen ta daki wannan motar ne sai ta tsaya, cikin ikon ubangiji da buwayarsa Al'ameen ko ƙwarzane baijiba a jikinsa a matuƙar gigice ya fito daga cikin motar ya nufo ashfat da gudu yayin tuni har Haidar da khalifa sun isa, Haidar runtse idanunsa yayi cikin wani irin tashin hankali mai wuyar fassarawa, ya ɗago kanta yana jijjigata alamun ta tashi shi kuwa Khalifa kuka yasa tamkar ƙaramin yaro, Al'ameen yana isowa yaga jini har gudu yake dubansa ya kai ga inda jinin ke zuba, ƙafar ashfat ne da ta fita saurin kawar da kansa yayi tare da rufe idanunsa yana ambaton innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!! Wani irin nauyi yaji zuciyarsa ta masa, wannan wata irin munguwar ƙaddara ce, ya furta cikin zuciyarsa yana jin kansa na sara masa da ƙarfi, Khalifa ne ya tashi da sauri tare da faɗawa jikin Al'ameen ya kuma sakin kuka, cikin kukan yake cewa.
"Bata son zuwa, nine na tilasta mata lallai mu taho ashe ƙaddara take gujewa, ni kuma nake jawo mata, duk wannan laifi nane dana sata zuwa dole nine na jawo mata tayi asarar ƙafarta, na cucet..........."
Saurin toshe masa baki Al'ameen yayi da idanunsa yayi jajur yatsarsa yasa a bakinsa tare da cewa.
"Shish!! "
Gidan wata mata aka shiga da sauri aka karɓo fallen zani ƙafar dake bulbular jinin Haidar ya kama ya ɗaure idanunsa sai gudun hawayen tausayi yake, shi kuwa Al'ameen ƴan sanda ya kira tare da kiran Papa ya sanar dashi ba'a juma ba kuwa sai ga police ɗin tare da ambulance, Al'ameen Haidar khalifa duk ambulance ɗin suka shiga suka nufi asibiti, darect emargency aka shige da ita cikin gaggawa, tunda aka shiga da ita Al'ameen ya zauna tare da dafe kansa dake famar sara masa idanunsa sunyi jajur maganganunta da take masa a cikin mota sune suke yawo a zuciyarsa, (Ya Al'ameen Allah kuwa da Bros khalifa yace na shirya jibi zamu dawo gida Nigeria, sai naji zuciyata ta tsinke, kawai naji bana son tafiyar amma fa a raina ina son ganinku Nigeria ne dai kawai bana son.......) Runtse idanunsa yayi, a hankali yake jin jiri yana ɗibarsa tunda yake a tsawon rayuwarsa bai taɓa jin tashin hankali irin wannan ba, shin wannan wacce irin masifa ce, Haidar ya gagara zama waje ɗaya sai famar kaiwa yake da komowa, ya rasa nutsuwar zama, sosai hankalinsa yake tashe, sun kai kusa 40minute sai kuwa gasu Ummi da Inna Jumma har Aunty Amarya, Momma ma ita da Aunty sunzo, Maimu Sosai take kuka tamkar za'a zare mata rai yayin da kuka yake zuwa da sauƙi a zuciya shi wanda zuciyarsa ta cunkushe da baƙin ciki kukan ma gagararsa take haka take a wajen Ummi da Al'ameen tashin hankali da baƙin ciki ya kanasu kuka sai ajiyar zuciya kawai da Ummi ke sauƙewa, babu wanda bai tausayawa Ummi halin da take ciki ba, Aunty Amarya cike da makirci ta riƙo Al'ameen tana kuka tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!! Lallai yau munga baƙar ƙaddara, yanzu ina ashfat take, ta mutu ko, sun kaita mutuware ne,

Please Login or Register in order to submit comment