Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga yau daga kinyi sallar asuba zaki fito kitchen ki fara haɗawa ihsan breakfast da zata shige dashi school, sannan kizo kiyi na gida duka, maza ki tashi kije ki samu Ladiyo ta nuna miki tsarin aikin."
Kanta Ablah ta sunkuyar ƙasa tare da cewa.
"To Aunty, bansan Ladiyon ba amma."
"Ladiyo tana kitchen muje na nuna miki kitchen ɗin ki sameta.
Da to Ablah ta amsa tare da rufe ƙur'anin ta ijiye miƙewa tayi tabi bayan Aunty Amarya, har kitchen Ladiyo suka samu tana fere dankali, cikin rusunawa ta gaishe da Aunty Amarya, Aunty Amarya cewa Ladiyo tayi.
"Ladiyo maza ijiye firar nan, ki bawa wannan tayi, duk wani aiki da zakiyi yau wannan itace zatayi, ban yadda ki ɗaga koda tsinke bane, daga nan har sati biyu, itace zatayi aiki, abinda zakiyi kawai shine ki dinga nuna mata yanda abubuwan suke, saboda karta mana shirme da alamu daga gidan matsiyatan talakawa ta fito, bata iya amfani da gas ba, kibi a hankali karta tayar mana da wuta."
Kanta Ladiyo ta ɗaga ta amsa da to, ita kuwa Ablah runtse idanunta tayi cike da jin zafin maganganun Aunty , kallon Ablah Aunty Amarya tayi ta ce.
"Ke kuma ki tabbatar kinyi komai da kula idan ba haka ba, zaman ki gajere zai kasance a cikin gidan nan."
Tayi Maganar tana ficewa, Ladiyo hanun Ablah ta jawo tare da cewa.
"Kiyi hkr da maganganunta, bansan meyasa take miki Magana da zafi ba, domin kuwa tana da kirki amma ke naga kamar jininku baizo ɗaya ba, yanzu ki fere dankalin kafin muje aiki na gaba."
Murmushi Ablah ta saki ba tare da tayi Magana ba haka ko a fuska bata nunawa Ladiyo tamkar bataji zafin abinda Aunty Amarya ta mata ba, ta hau fere da dankalin cike da rashin nuna damuwa, cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala breakfast ɗin, dankali da ƙwai suka soya sai dafaffen ƙwai guda biyu na Al'ameen wanda ya zamo masa al'ada duk wayewar gari sai yaci dafaffen ƙwai, kunun gyaɗa mai kyau suka damawa Inna Jumma tare da soya mata ƙosai sai kuma ruwan lipton da suka dafa wanda yaji citta da kanunfari da na'ana'a, a daining suka jere shaf Ablah ta mata da wannan ƙwai guda biyu da ta dafa na Al'ameen a kitchen ɗin, a cikin kitchen ɗin suka ci nasu abincin ita da Ladiyo sannan ta koma bedroom ɗin Inna Jumma, tana zaune ta sameta, gaisheta Ablah tayi, Inna Jumma ta ce ta shige tollet tayi wanka, haka kuma akayi ta shiga tayi wanka ta.
Misalin sha ɗaya dai-dai kowa ya hallara a daining ɗin kasancewar yau babu aiki asabar sai Al'ameen kawai da bai sauko ba, Maimu ne tayi seving ɗin kowa itama Inna Jumma ta fito, yayin da tabar Ablah a bedroom ɗinta, Inna Jumma da Daddy Sosai kunu da ƙosan da Ablah ta musu ya tafi dasu Daddy gagara haƙuri yayi sai da ya dubi Aunty Amarya yace.
"Amarya, amma kece da kanki kika dama wannan kunun, na juma bansha kunun daya min daɗi irin wannan ba."
Tuno da Ablah ce tayi yasa Aunty Amarya haɗa fuska tare da jin baƙin cikin yabon kunun da Daddy yayi taso ace Ablah tayi kuskure, waskewa tayi tare da sakin murmushi cikin kissa da makirci tace.
"A'a Daddyn Al'ameen bani bace nayi, Ablah ce Yarinyar da Inna ta kawo, gaskiya dai Inna ta iya zaɓe yanda Yarinyar take da hankali haka kuma ta iya komai a rayuwarta."
Afnan ce tace
"Daddy ai da kasha wannan tea ɗin to fa da kaji banbanci da na ko wanne rana, yayi daɗi sosai ba'a taɓa haɗa tea mai daɗinsa a cikin gidan nan ba, gaskiya girkinta na mussaman ne."
Murmushi Daddy yayi tare da cewa.
"Lallai kuwa ƴar Inna ta amshi yabo yau, dama waya faɗa muku mamana zatayi zaɓen tumun dare."
Dukkan su dariya sukayi har Ummi, Inna Jumma ce tace.
"To an faɗa muku niɗin ta wasa ce, Wai ko dai ma a saka muku waiji ne, domin kuwa da alamu dukkan ku, kun tafi santi."
Ummi ce tayi dariya tare da cewa.
"Gaskiya dai kam Inna mussaman ma ni Yanda kunu da ƙosan nan ya tafi dani idan babu waiji gaskiya za'a samu matsala."
Tayi Maganar suna dariya, cike da raha cikin farin ciki suka kammala breakfast ɗin nasu, Daddy bai juma ba a wajen ya fice, itama dai Ummi bedroom ɗinta ta koma, haka Inna Jumma, ya saura a falon daga Aunty Amarya sai su Afnan da Maimu da kuma ihsan.
Misalin 12:00am dai-dai Al'ameen ya fito daga bedroom ɗinsa, sanye da baƙar jallabiya wacce ta amshi fatar jikinsa, ba tare daya nufi Aunty Amarya ba ya shige daining kasancewar da yunwa ya kwana, dankali da ƙwai ɗin ya jawo ya buɗe yamutsa fuska domin kuwa bai fiye son da ƙwai haɗe ba, yafi gane chiefs ɗinsa ƙwai ɗin dabam, ture kular gefe yayi yana tsuka tare da sake jawo ɗayar, ƙosai ya gani, murmushi ya saki tare da ɗiba a plat lipton ɗin ya tsiyaya a cup, a hankali ya kai ƙosan bakinsa idanunsa ya lumshe jin daɗin ƙosan yana ratsa kansa, cike da nishaɗi yake cin ƙosan, lipton ɗin ya kurɓa, idanunsa ya lumshe domin kuwa tea ɗin yayi mungun daɗi, sosai yaci ya ƙoshi rabon da yayi breakfast haka harya manta, dube dube ya fara ta ina zaiga dafaffen ƙwai ɗinsa, babu shi babu alamun sa, Aunty Amarya ya kira.
"Aunty! Aunty! "
Amsawa Aunty Amarya dake zaune tayi tare da cewa.
"Lafiya kuwa Al'ameen.?"
"Ina ƙwai na yake.?"
"Ka duba baya wajen ne.?"
"Indai ba idanuna bane suka samu matsala to gaskiya babu."
Tashi Aunty Amarya tayi tana murmushi, dama kuwa nema take Ablah tayi kuskure, daining tazo tare da dubawa bata gani ba.
"Aunty anya kuwa yau an dafa ƙwai ɗin nan."
Dafa kanta Aunty Amarya tayi tare da cewa.
"Sorry sabuwar ƴar aiki Inna ta kawo itace tayi breakfast yau, ina ga bata dafa ƙwai ɗin ba, amma kuma ai nace Ladiyo ta nuna mata komai, wannan yarinya bata kyauta ba."
Ɗago idanunsa yayi cike da ɓacin rai ya furta.
"What sabuwar ƴar aiki kuma? Aunty yanzu kina nufin ba abincin Ladiyo naci ba, amma dai an cuceni sanin kanki ne bana cin abincin wani idan ba naki kona Ummi ko Ladiyo ba, shine zaku barni naci abincin wata, wataƙil ma ƙazama ce, wama yace ana buƙatar wata ƴar aiki a cikin gidan nan, koma wayece a kira min ita dole tabar gidan nan yanzu."
Yayi Maganar a fusace, murmushi Aunty Amarya ta saki, cikin zuciyarta tana furta (dai-dai kenan, ai kuwa yanzu zansa ayi kiranta.) Tayi Maganar zucin tana ƙwalawa ihsan kira da gudu ihsan ta taho, cewa tayi taje ta kira baƙuwar dake bedroom ɗin Inna Jumma, da gudu ihsan ta tafi aikan.
Ba'a juma ba kuwa sai ga Ablah da ihsan sun fito tare, daining ɗin ta iso tare da risinawa tace wa Aunty Amarya.
"Gani Aunty."
Muryarta ta doki dodon kunnensa, ras zuciyarsa ta tsinke, kamar yasan muryar, kafin Aunty Amarya ta yi Magana Al'ameen ya juyo tare da sauƙe idanunsa a fuskarta ido biyu suka haɗa, cike da munguwar mamaki Al'ameen ya nuna ta da yatsa.
"Dama kece?"
Idanunta ta sunkuyar ƙasa cike da jin haushin sa domin kuwa tun zagin daya mata take jin zafinsa, murmushi Al'ameen ya saki tare da cewa.
"Kin biyoni har gidan mu kenan, yayi kyau na yabawa nacinki wato dai ke a rayuwarki baki ƙaunar ganina cikin farin ciki, ai kuwa ke bazan koreki ba, ina miki barka da shigowa *AMBASSADOR AHMAD GIWA ESTATE)* "
Yayi Maganar yana sakin murmushin mugunta tare da miƙewa ba tare daya kuma yin zancen ƙwai ɗin ba, ya ɗauki wayarsa yabar falon gabaki ɗaya.
Aunty Amarya wani irin baƙin ciki taji domin kuwa bata so haka ba, taso ace Al'ameen ya wulaƙanta Ablah tsuka taja itama tare da barin wajen, Ablah da kanta ke sunkuye ne, ta juya cike da zullumin Rayuwar wannan gidan, (anya kuwa zamanta zai yiwu da waɗannan mutanen, bata san me ta yiwa Aunty Amarya ba ta jefa mata karar tsana gefe guda kuma ga wannan baƙin azzalumin.) Numfashi ta saki ta shige ROOM ɗin Inna Jumma.




✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨



Tagumi Rufaida ta zuba cike da damuwa da tunani, ita dai Soyayya ta zame mata ƙaddara a rayuwarta, soyayyar ɗan uwanta na shirin zame mata ciwo shin meyasa bazata sanar dashi gaskiya ba idan yaso ayita kawai ta kare domin kuwa bata hango Ya Haidar zai rabu da wannan Nafeesan wannan wacce irin masifa ce.
Tayi Maganar zucin tana sakin tsuka hawayen da bata san dashi bane ya gangaro daga idanunta, Haidar daya juma tsaye a kanta ne bata san yana tsaye a kanta ba, ya zauna gefenta tare da saka hanu ya dafa kafaɗar ta, a firgice Rufaida ta ɗago idanunta ta sauƙe su akansa, numfashi ta saki tana dafe ƙirjinta.
"Rufaida! Wani irin tunani kike haka, ki duba kiga yanda kike cikin damuwa ga tunani, kuma kina zuci, so kike ki kashe kanki, wai meye matsalarki ne ma yanzu.?"
Idanunta ta zuba masa cikin zuciyarta tana furta kaine matsalata, anya kuwa bazata faɗa masa gaskiya ba yanzu, mtss! Kai gara kawai ta faɗa masa ko zaiji tausayinta.....................




Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi Naira ɗari biyu kacal 200 guda biyu ne daga aminai biyu Wato ƙawalli da ƙawalliya.

ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN.

acikin littafinta mai taken *AHLAN*

RASHEEDAT USMAN UMMU NASMAH.

Acikin littafinta mai taken *AMINAINA KO ITA?*


Guda ɗaya zaki samu ne akan farashi Naira 200 idan kuma duka biyun kike so zaki biya Naira 300.

Turo da kuɗin ki ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank.

Ko kuma ku turo hoton katin waya na Mtn card ta ɗaya daga cikin waɗannan numbobin.
08147537180
Ko
08165550116


Please banda VTU hoton katin zaki ɗauka ki turo.


Sannan sai ku turo screen SHORT SHAIDAR BIYA ta cikin waɗannan numbobin.

Kuyi hanzarin biya domin kuwa littattafan sunzo ne da zafin su, zasu bada citta karku sake a barku a baya koda kuɗin ku sai da rabonku.



Please Share and comments.



*Ummu Nasmah ce ✍🏻*
[6/30, 8:52 PM] UMMU NASMAH🥰: 💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅



🤦🏻‍♂️🤦🏻‍♂️🤦🏻‍♂️



💔 *AMINAINA KO ITA?* 💔


🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️



🙆🏻‍♀️ *(BETRAYED LOVE!)* 🙆🏻‍♀️



*NA*


*RASHEEDAT USMAN*

*(UMMU NASMAH)*




Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.



*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*





*Free page 16*




Kanta ta sunkuyar ƙasa, wata zuciyar na cewa ta sanar dashi wata zuciyar kuma na hanata idanunta ta runtse zuciyarta na mata zafi, cikin sanyin jiki ta ɗago ta zuba masa idanu still dai hawayen ne ya fara gudu saman fuskarta, cikin sanyin murya mai ban tausayi Rufaida ta buɗe baki zatayi Magana, Al'ameen ya yi Sallama, juyawa Haidar yayi yana amsa sallamar, Rufaida sosai taji haushin katse mata hanzari da Al'ameen yayi, zama yayi gefe dasu yana kallon Rufaida bakinsa ya taɓe tare da cewa.
"Ita kuma wannan meya sameta, naga tana cuna baki kamar shantu."?
Ya jefawa Haidar tambaya, Rufaida takaicin baƙar Magana da Al'ameen ya faɗa mata ne yasa ta kuma jin zafi cikin zuciyarta ƙara tura bakinta tayi , sai kuma kamar wacce zuciyarta ke jira a ƙara ɓata mata rai ta saki kuka mai cin rai, zaro idanunsa Al'ameen yayi yana kallon ta, sosai ya fuskanceta cikin tsawa yace.
"Kee! Dakata haka bana son iskancin banza, da rainin wayo kukan Uban me kike, zaginki akayi ko dukanki akayi yau naga mahaukaciya, dallah tashi kibar nan, karki sa kaina yayi ciwo."
Rufaida sautin kukan ta ƙara cike da jin haushin Al'ameen, da yayi mungun takurawa rayuwarsu, mutum kullum yana nan Kamar kububuwan maciji kowa tsoronsa yake ji, jin sauƙar sautin muryar sa a kunnenta ne ya sanyata miƙewa a firgice.
"I say get out! Ko bakiji bane sai na miƙe na ɓallaki shasha."
Cikin sauri Rufaida ta bar wajen, tana cigaba da kukanta, Haidar dubansa yayi tare da cewa.
"Al'ameen wai meye hakane kam, ina ruwanka da ita kasan meye damuwarta baka rarrasheta ba, shine zaka dinga mata wannan ihun kana zaginta babu laifin tsaye bare kuma na zaune, Yarinyar nan tana cikin matsala na ijiye ta domin naji damuwarta, kazo ka korata tare da ƙara mata damuwa akan wanda take dashi, wannan ba dai-dai bane wallahi, ya kamata ka dinga saussautawa yaran nan."
"To ubana tashi ka dakeni sai nafi jin maganar taka, kaga ni fa ba wannan shashancin bane ya kawo ni, jiya naje gaishe da Daddy, kasan kuwa Maganar da Daddy yamin.?"
Girgiza kansa Haidar yayi tare da cewa.
"A'a meya ce maka, Allah dai yasa ba laifi mukayi ba."?
"Ai ni da wannan maganar da ya min gara ma ace laifin mukayi, wai Daddy cewa yake muje mu nemo Mata, Aure yake son muyi nan da wasu kwanaki kaɗan mtsss! Kuma da alamu Daddy serious yake wannan maganar."
Dariya Haidar yasa harda riƙe ciki yana nuna Al'ameen da yatsa, Al'ameen buɗe baki yayi yana masa kallon mamaki, cike da haushin dariyar da Haidar ke masa yace.
"Kai dariya ma kake min, Oh ga mahaukaci ko yayi kyau."
Sassauta dariyar Haidar yayi tare da cewa.
"To ai dole nayi dariya Al'ameen Saboda abun dariya ne, Al'ameen kaine fa a ruwa domin kuwa ni na samu matar Auren ko yau tace na fito a shirye nake, shi kuma Faruq baida matsala domin kuwa yana da niyyar Neman matar Aure, kaine dai baka da bukatar Mace, kaga kuwa kaine a ruwa kusa da kada ma.''
"Mtsss! Kaga ni fa yanzu dan Allah ba wannan maganar bace ta kawo, ni zuwa nayi na roƙeka ka rufa min asiri idan Daddy ya kira ka kan wannan maganar dan Allah karka ce masa ka samu matar Aure, wallahi muddun kace masa ka samu, to fa na shiga Uku domin kuwa ko zan mutu Daddy sai ya sani nemo mata dole, idan naƙi kuwa yamin Auren dole, ka taimakeni ɗan uwana dan Allah."
Dariya Haidar ya kuma sheƙewa dashi, cikin dariyar yace.
"Babu wannan alfarmar bazan iya maka ba, babu karya domin kuwa ni Aure nake so na gaji da zaman gauranci, kawai malam nemo Mata idan kuma baka da idon kallon mata, sai mu mu nemo maka."
Yayi Maganar cikin dariya da tsokanar Al'ameen, haɗa fuska Al'ameen yayi domin kuwa yaga Haidar kamar ya maida Maganar wasa,.
"Haidar Please stop funny! Magana fa nake maka na gaskiya amma naga kana maida abin na wasa, dan Allah na roƙi alfarma gareka."
Numfashi Haidar ya saki tare da ɗaga kafaɗarsa yace.
"Okay amma dai, gaskiya ya kamata ka maida hankali domin kuwa Aure shine cikar mutum, sai kana nuna kai baka ma ƙaunar Auren kwatakwata, gask..........."
"Dan Allah dakata da wannan maganar ni kaga tafiyata ma abinda ya kawoni kenan, idan momma ta fito kace ina miƙa gaisuwa."
Yayi Maganar yana miƙewa tare da ficewa daga part ɗin, da kallo Haidar ya bisa tare da girgiza kansa.



Kwana biyu da dawowar Ablah gidan *AMBASSADOR AHMAD GIWA* ta gama fuskantar halin kowa a cikin gidan, sosai jininsu yazo ɗaya da Maimu, sosai take son Ablah tsakani da Allah, inda yanzu Ablah tabar bedroom ɗin Inna Jumma ta koma nata dake gefen room ɗin Inna Jumma, sai dai kuma cikin ikon Allah a cikin wannan kwana biyun Allah bai haɗa fuskarta dana Al'ameen ba, saɓani suke, sosai taji daɗin hakan domin kuwa bata ƙaunar haɗuwa dashi.
Yau tunda sassafe Ablah da Ladiyo suka gama haɗa breakfast saboda akwai yau Monday ihsan zata school, ganin yayi Safiya sosai yasa Ablah bata ci nata abincin ba, ta koma bedroom ɗin ta ta kwanta, Ladiyo ce ta yiwa ihsan komai ta wuce school, shima yau Al'ameen da wuri ya tashi ya yi shirin Office saboda yana da general meeting, koda ya sauƙo ƙasa babu kowa bedroom ɗin Ummi ya shiga, ya samu ta fito daga wanka murmushi ya saki tare da zama gefen bed ɗinta yana murmushi yace.
"Ummi Barka da tashi kin tashi lafiya."
Zama Ummi tayi tana murmushi cike da ƙaunar ɗan nata tace.
"Lafiya Alhamdulillah! Har ka fito kenan, kayi sammako yau.?"
"Ehh Ummi muna da general meeting ne da Companyn Ahmad St rice, sun buƙaci na saka hanun jari a Companyn nasu, na duba na gani idan har na saka hanun jarin, za'a samu ribar da takai 5.2b so shine yanzu zamuje da Haidar mu tattauna sannan mu bada hanun jarin."
"Masha Allah, indai har za'a samu wannan ribar to ai yana da kyau ku saka hanun jarin, sannan naji kana cewa sun buƙaci ka saka hanun jari, it means kaine kenan zaka saka ba tare dasu Haidar ba.?"
"Ehh Ummi nine zan saka Banda su ciki, saboda munyi Magana da Haidar akan cewa ko zasu saka suma, to sai yake nuna min cewa, bashi da kuɗaɗen da suke buƙata, ribar da yake samu cikin Companyn mu bai kai ya saka hanun jari ba, dalilin da yasa zansa ni kaɗai."
Numfashi Ummi ta saki tare da kama hanun ɗannata tace .
"Baza'ayi haka ba Al'ameen, tunda basu dashi mai zai hana kai ka saka musu tunda kai kana dashi, ribar da za'a dinga samu sai suke rabawa shida Faruq amma a matsayin Uwar kuɗin naka ne suna ajiye, kaga kenan kamar ka basu aro ne, idan kayi haka ka taimakawa ƴan uwanka kuma zasuji daɗi sosai zamunci kuma zai ƙara danƙo ka duba maganata da kyau, karka yadda kai ka ta samu su suna baya indai da halin da zaka tallafawa rayuwarsu tafi wadda suke yanzu to kayi domin kuwa ƴan uwanka ne, komai ka musu baka faɗi ba."
"Hakane Ummi, gaskiya banyi wannan tunanin ba, baizo min ba, kuma naji dadi da kika kawo min wannan shawarar insha Allah idan munje zan saka musu."
"Da ka kyauta kuwa, jiya munyi Magana da Daddyn ku akan Ashfat yace insha Allah gobe zasu tafi Egypt ɗin zasubi jirgin 11am yace zasuje tare da Auntyn Faruq ta kula da ita idan an mata aikin da tare da amarya zasu sai Abi yace suje da Auntyn."
"Eh Daddy ya sanar dani, hakan yayi sosai Allah yasa ayi cikin Nasara bara naje nayi breakfast sai na shige Daddy bai tashi ba, zan shiga room Aunty Amarya kafin na shige."
"Amarya ai tana bedroom ɗin Daddyn ku, kaje kayi breakfast ɗinka kawai ka shige Allah ya bada Sa'a."
Da ameen ya amsa yana fita, daining yaje tare da jawo kujera ya zauna, Tuwon doya ya ɗiba tare da tea, loma daya ya kai bakinsa daƙyar ya haɗiye saboda azabar yaji da miyar tayi, shi kuwa a rayuwarsa ya tsani yaji a abinci, ai kuwa cikin ɓacin rai ya ture abincin gefe, yana huci, Tabbas yasan babu mai wannan muguntar idan ba Ablah ba, domin kuwa Ladiyo ta juma cikin gidan nan bata taɓa wannan muguntar ba, tea ya haɗa mai kauri yasha, yana tsaka da shan tea ɗin ya hango Maimu tana sauƙowa, kiranta yayi tare da cewa taje ta kira masa Ablah.
Babu jumawa kuwa sai ga Ablah yayin da Maimu tayi shigewarta bedroom ɗin Inna Jumma, Ablah daining ɗin ta nufa cikin sanyin jiki ta tsaya a kansa tace.
"Maimu tace kana kirana."
"Waye yayi wannan girkin kece ko Soloɓiyo?"
Ya jefa mata tambaya, shuru Ablah tayi cike da mamakin meyasa ya mata wannan tambayar kuma ko dai wani laifin aka masa duk da ita tayi duka girkin ba, ta dai dama kunu ta kuma daka doya sannan ta dafa lipton, to amma koma meye gara ta amsa cikin sanyin muryarta tace.
"Ehh ni ce."
Murmushin mugunta ya saki tare da juyowa ya kalleta, ɗaya daga cikin kujerun dake daining ɗin ya mata nuni dashi tare da cewa.
"Zauna anan."
Zaro idanunta Ablah tayi tare da furta.
"Na zauna kuma, ai nan ba wajen zamana bane, kawai koma meye ne ka faɗa min basai na zauna ba."
Tayi Maganar cike da tsoro Al'ameen tsawa ya daka mata wanda sai da hantar cikinta ya haɗa.
"Umarni nake baki! Nace kiiii zaunaaa!! Ko bazaki zauna ba sai na tashi na jideki kin faɗa banza wawiya, aini nayi mamaki jiya ace kece kikayi wannan abincin."
Cikin rawar jiki gami da tsoro Ablah ta zauna jikinta na rawa, kular miyar Al'ameen ya turo mata gabanta tare da cewa.
"Ki ɗauki wannan miyar ki kafa kanki ki shanyeta tass, sannan ki suɗe kular."
Yayi Maganar yana zaro mata idanunsa fuskar sa haɗe tamau tamkar hadari, da kallo Ablah tabi kular sai kuma ta ɗago ta kalli Al'ameen idanunta sunyi raurau tace.
"Kayi hkr bazan iya shan miya ba dan Allah koma me na maka kayi hkr bazan sake ba."
"Hmmm! Ashe kin iya bada haƙuri to bana yafewa mungu dan haka dole sai kin shanye miyar nan, ki zaɓi ɗaya a cikin biyu domin kuwa wallahi dole ne sai ɗaya ta Faru kinji na rantse, ko kishanye miyar nan kona ɗauka na watsa miki a fuska sannan na gwale waɗannan idanunnaki mai kama dana mujiya na tsiyaya miyar ciki, ki makance kowa ma ya huta, zaɓi wanda ya fi miki sauƙi kafin na ƙirga Uku."
Yayi Maganar yana fara ƙirge.
"1....................2................"
Sanin halin sa sarai zai iya abinda ya furta yasa Ablah saurin ɗaga miyar ta kai bakinta ta kurɓa wani irin azababben yaji ne da raɗaɗi taji ya gwauraye mata baki cike da azaba ta runtse idanunta ta gagara maida miyar bakinta sai famar shishita take tare da ijiye kular murmushin mugunta Al'ameen ya saki tare haɗe fuska yace.
"Ki ɗauka ki shanye nace wallahi kona watsa miki a idanunki."
Cikowa idanunta yayi da hawaye ta ƙara ɗauka ta kafa kai hawaye na zuba a idanunta idanunta sunyi jajur tamkar gauta, azaba iya azaba ta jisa bakinta duk ya mele, ganin azabar da tasha yasa Al'ameen ƙwace kular yana sakin dariya tare da miƙewa tsaye ya buga teburin yana sakin murmushin mugunta yace.
"Wannan shine hukuncin ki, gobe ma ki kuma mana abinci da yaji, hukuncinki sai yafi na yau tsauri wawiya."
Yayi Maganar yana kwasar wayoyinsa da key ɗinsa ya fice, da kuka Ablah ta fashe bakinta duk ya mele azaba take ji har cikin kwaƙwalwarta, miƙewa tayi ta shige cikin bedroom ɗinta prich ta buɗe ta ɗauko ruwa mai sanyi ta kafa a bakinta, sosai tasha ruwan, kafin ta ijiye robar ruwan ta zauna a bakin bed ta saki kuka mai cin rai, Tabbas rashin Uwa a kusa babbar masifa ce, rayuwa ƙasan wani akwai ƙasƙanci da wulaƙanci, meyasa Umma ta yadda aka turo ta gidan nan, gashi tun ba'a je

Please Login or Register in order to submit comment