Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin masifa, Maimu dake zaune a daining ne tasa dariya tana binsu da kallo ko ita tana jin takaicin shigar rashin ɗa'a da Afnan keyi, Afnan kuwa ko ta juyo ta cewa Inna Jumma.
"Idan kin faɗa masa ya kasheni."
Tayi Maganar tana ficewa, Inna Jumma cike da mita ta nufi daining ɗin zama tayi tana ta famar masifa, Maimu ce tace.
"Inna Jumma, dan Allah kibar Maganar nan haka, kici abincin ki, ita kam badai ta tafi ba."
Tayi Maganar dai-dai Haidar na sauƙowa Inna Jumma ya nufo tare da rungume ta, ta baya yana cewa.
"Wai waya taɓa min amarya ta ne tun daga sama nake jiyo hayaniyarki."
"Waye kuwa zai taɓani a gidan nan idan ba wannan fitsararriyar ba Afnatu, shegiya marar ɗa'a ni nama taɓa ganin yarinya marar kunya irinta."
Murmushi Haidar yayi tare da cewa.
"Maimu wai meye Afnan ta yiwa Inna Jumma ne kam."
Maimu cewa tayi.
"Yaya Haidar kaima fa kasan akan abinda ake samun matsala da Afnan, kaya tasa sun fitar mata da halittar jikinta, shine Inna Jumma tace ta koma tasa na mutunci, taƙi, shine ta mata rashin kunya."
Carap Inna Jumma tace.
"Tamin rashin kunya ko ta zageni, Yarinyar da tace ko uwata ce ta dawo duniya bata isa ta sata ta sauya kayan jikinta ba bare kuma ni."
Daga sama sukaji muryar Al'ameen yana cewa.
"Ita Afnan ɗin ce ta faɗa miki haka."?
Juyowa Inna Jumma tayi tare da sakin kuka tace.
"Haka ta faɗa min Aminu har tana nuna min yatsa ni dai yau a cikin gidan nan anci mutunci na, ban taɓa tsammanin akwai ranar da jinina zai zageni ba."
Tayi Maganar tana mutstsike idanuwa Maimu idanu ta zaro tana yiwa Inna Jumma kallon tsoro, wai dama wannan tsohuwar haka ta iya sharri, shi kuwa Al'ameen hasala yayi cike da ɓacin rai ya dumfaro daining ɗin ya zauna tare da cewa.
"School ta tafi da waɗannan matsiyatan kayan ko.?"
Kanta Maimu ta ɗaga alamun eh.
"Yayi kyau".
ya furta yana jawo plast ba tare daya kuma cewa komai ba, Haidar shima zama yayi suka fara breakfast, suna tsaka da breakfast ɗin Rufaida ta shigo hanunta riƙe da bag ɗin ta zasu shige school da Maimu, gefen Maimu ta tsaya tare da cewa Al'ameen.
"Barka da safiya ya Al'ameen."
Ta gaishe sa tana tsaye ba tare daya amsa gaisuwar tata ba yace.
"Magani zaki bamu ne kika tsaya a kanmu kamar sa'o'inki nemi waje ki zauna ko kuma kibar kanmu."
Murmushi Haidar yasa tare da ture cup ɗin tea ɗin yana miƙewa yaja hanun Rufaida yace.
"Kai dai ka cika takura a kanka ta tsaya ne, kinga zo muje ki bani labari."
Bayansa Rufaida tabi Al'ameen ya bisu da harara, a kujerun falon suka zauna, Haidar a hankali ya raɗawa Rufaida a kunnenta.
"Ina labarin saurayin naki, kin sanar dashi kuwa."?
Rufaida haɗa ranta tayi tamau tamkar zatayi kuka bata amsa mishi tambayar tasa ba, Haidar murmushi ya kuma yace.
"Wai fushi kike ne akan abinda Haidar ya miki, to meye abun fushin, yayanki ne fa, har dukanki Yana da damar yayi bama faɗa ba."
Ɗago idanunta tayi ta zubawa Haidar cike da Soyayya ji take tamkar ta rungumesa, cewa tayi.
"To me na masa da zai hauni da faɗa, kana gani fa ina zuwa wajen nan shina fara gaidawa ga Inna Jumma itace babba amma ban gaisheta ba sai shi, kuma shikenan sai ya hauni da faɗa."
Hanunta Haidar ya kama wani irin zubawa tsikar jikin ta yayi a duk sanda ya kama hanunta sai taji jikinta ya zuba, a hankali ya ce.
"Kinga shifa Al'ameen haka yake babu mai iya sauya masa ɗabiar sa, hkr shine kawai zakuyi dole, ki amsa min tambayata kin sanar dashi jiyan."
Kallon sa tayi tare da sunkuyar da kanta ta fara magana a hankali.
"A'a ban sanar dashi ba, saboda ina tsoro karna..........."
Bata kai ƙarshe a maganar tata ba, wayarsa yayi ringin.
"Ɗan dakata ina zuwa."
Ya faɗa mata yana ɗaga wayar cikin farin ciki yace.
"Farin cikin Haidar har kin tashi da wuri haka."?
Dam ƙirjin Rufaida ya buga da ƙarfi ita wannan a rayuwarta bata tashi kiransa sai ta dai-dai ci muna tare dashi, anya kuwa zan samu yaya Haidar a matsayin miji da alamu ta gama shigewa cikin zuciyarsa, duk cikin zuciyarta take wannan maganar cikin damuwa, Nafeesa kuwa daga can tace.
"Na juma da tashi ai Duniyata, yau kewar muryar ka nake sosai, kasan bana samun nutsuwa muddun banji daddaɗan muryar *DUNIYATA* ba, da fatan kana cikin farin ciki."
Ɗan murmushi Haidar yayi yana lumshe idanunsa cike da tsantsar ƙaunar ta yace.
"A ko yaushe idan na tuna da cewa ina da ke, koda ina cikin damuwa sai naji ta yaye farin ciki sai ya zamo shine abokina a wannan ranar dalilin kenan ma dayasa na raɗa miki suna da *FARIN CIKI NA* muddun kika kasance a rayuwata bazan taɓa baƙin ciki ba, farin ciki shine zai zamo min dawamamme ina matuƙar ƙaunarki Nafeesa."
Murmushi Nafeesa ta saki tana kannewa Amnat ido tace masa.
"Mai zai hana kuwa bazan kasance a rayuwarka ba, a duniya bani da wani farin ciki daya wuce kai, nakan godewa Ubangijin daya haɗamu domin kuwa ya aiko min da hasken rayuwata, idan harna tuna da cewa wata rana zan zamo mata gareka, sai naji Duniyar tamin daɗi, dole na ambaceka da *DUNIYATA* Domin kuwa kaine haske na kuma rufin asirina a cikinta, idan babu damuwa so nake kazo da daddare akwai Maganar da nake son muyi, sannan jiya naga katin waya na gode Allah ya ƙara arziki."
Murmushi Haidar yayi maganganun ta na ƙara masa daɗi a kunnensa yace.
"Tabbas samun masoyiya ta gari ni'ima ce a rayuwa, ki tsumayi zuwana insha Allah zanzo, take care."
Yayi Maganar yana katse kiran bakinsa ɗauke da murmushi ya dubi Rufaida da kanta ke ƙasa zuciyarta na ƙuna idanunta na zubda hawaye yace.
"Ina jinki Rufaida"
Ɗago idanunta da suka kaɗa lokaci guda tayi hawaye na zuba daga idanunta Haidar idanunsa ya zaro ganin kuka take, kusa da ita ya matso tare da saka hanu ya ɗago fuskarta, hawayen yasa hanu ya share mata cike da tausayin ta yace.
"Rufaida! Soyayya kike yiwa kuka, shin wani mummunan amsa kika samu a garesa bayan kin sanar dashi."
Kanta ta girgiza cikin rawar murya mai alamun kuka tace.
"Ban sanar dashi ba ya Haidar saboda na makara na riga da na faɗi a soyayyata, nayi rashin nasara yana da wacce yake so, a duk sanda nayi ƙoƙarin tunkararsa da maganata sai naga tazo wajen ta ɗauke hankalinsa daga gareni babu buƙatar na sanar dashi domin kuwa na faɗi warwas."
Tayi Maganar hawaye na ƙara zubo mata, numfashi Ya Haidar ya saki tare da cewa.
"Faɗuwa ba ita bace take nuna rashin Nasara ka faɗi ka gagara tashi wannan shi ake kira da rashin Nasara amma muddun ka faɗi kuma ka tashi ina tabbatar miki da cewa, akwai Nasara a gabanki, baki faɗi domin kuwa zan miƙo miki hanu domin ki tashi zan tayaki yaƙi har sai kin amso Soyayyar ki, zan baki gudumowa a matsayina na yayanki, ki saurareni da kyau Rufaida ki fahimci abinda zan faɗa miki yanzu."
Tunda ya fara Maganar ta zuba masa idanu tana ji a zuciyarta ko dai ta sanar dashi cewa shine wannan wanda take son, ina tsoro bazai barni ba, Haidar cigaba da Magana yayi.
"Rufaida! a Rayuwa ana bukatar jajircewa akan abinda kake muradi, mafarki baya taɓa cika har sai ka samu jajircewa, ba'a son saurin sarewa akan muradi a ko yaushe akan fuskanci ko wani ƙalubale da wahala domin kaiwa ga nasara akan muradi, ina so ki kasance jajirtacciya wacce bazata taɓa sarewa saboda wani ba, ke macece kuma itama macece na Tabbata bazata fiki da komai ba, meyasa zaki bari tayi Nasara akanki, na Tabbata idan har kin saka hkr da addu'a a Rayuwarki kuma kika dage da nunawa muradinki kulawa na san zakiyi Nasara, bazan taɓa yadda ki faɗi ba, karki bani kunya ki jajirce ki amso Soyayyar ki ƙanwata."
"Na yadda da maganarka Ya Haidar, sai dai ina tsoron na tura mota ta tashi ta barni da ƙura gara na haƙura kawai ni na yadda na faɗi kawai, bazan ƙara maganar sa ba."
Kansa Haidar ya dafe tare da cewa.
"Idan kina kiran kin faɗi sai naji kamar na mareki, bazaki hkr ba, na miki alƙawarin cewa sai kinyi Nasara akan soyayyarki."
Zaro idanunta Rufaida tayi tare da cewa.
"Kamin alƙawari fa kace, idan har kamin alƙawari na yadda zan adana soyayyata kuma zanci gaba da nemanta, amma fa ka sani idan na kuma faɗuwa kaine wanda zanyi kuka dashi."
Murmushi Haidar yayi tare da cewa.
"Bazaki taɓa kuka dani ba Rufaida zan tsaya miki a matsayina na yayanki, idan ta kama ma, da kaina zan nemi nayi magana dashi wanda kike so ɗin zakiyi nasara domin kuwa Nasara a jininmu take.."
Murmushi Rufaida tayi dai-dai Maimu na nufosu tace.
"Muje Rufaida."
Miƙewa Rufaida tayi tana ɗaukar bag ɗinta tace.
"Ya Haidar na gode."
Murmushi kawai ya mata suka shige Inna Jumma ne ta dubi Al'ameen dake cin abincin kamar bazai ciba, tace.
"Aminu wai ya naji kayi shuru ne akan abinda Afnan tamin ko dai-dai tayi ne."
Abincin Al'ameen ya ture gefe tare da miƙewa tsaye yana ɗaukar wayarsa yace.
"Ki jira kiga idan na barta sai kiyi mitar."
Yayi Maganar yana barin daining ɗin, bakinta Inna Jumma ta taɓe tare da cewa.
"Ni ne ma mai mitar ko, ka faɗawa Uwarka to."
Murmushi kawai Al'ameen yayi bai kulata ba ya cewa Haidar, ka shiga part ɗin naku kafin nan bara naje wajen Ummi, yayi Maganar yana haurawa sama, shima Haidar part ɗinsu yayi, Al'ameen room ɗin Aunty Amarya ya shiga bata ciki sai ihsan dake bacci, fita yayi ya shiga na Ummi tare ya sameta da Aunty Amarya suna zaune, gwanin sha'awa suna hira gefen Aunty Amarya ya zauna tare da kwantar da kansa a kafaɗarta yace.
"Amarya! Yau bake kikayi girki ba, domin kuwa test ɗin baimin ba."
Murmushi Aunty Amarya ta saki tana shafa kansa tace.
"Wato dai duk sanda kaci abincin da ba nawa ba sai ka gane, Ladiyo ce ƴar aiki ta girka, kar dai har zaku fita.?"
"Ai naji sauyi zamu fita, Ummi Barka da safiya."
Murmushi Ummi tayi tace.
"Sai yanzu ka ganni kenan, tun ɗazu ai amarya kake kira."
Murmushi Al'ameen yayi tare da cewa.
"Kai Ummi, na isa na manta dake , kunga ni fita zanyi nayi let."
Duk murmushi sukayi tare da masa addu'a cike da farin ciki Al'ameen ya fito.
Tare suka fita da Haidar a mota ɗaya, sunzo dai-dai Amina kitchen Haidar yayi parking dubansa Al'ameen yayi tare da cewa.
"Me kuma ka tsaya zakayi.?"
Haidar baice masa komai ba ya fita, Amina kitchen ɗin ya shiga, ya sayi abinci na 2k take away biyu, da lemo ya fito, gidan baya wurga ledar tare da jan motar suka nufi Sj hospital, a harabar asibitin sukayi parking tare suka fito Haidar ya ɗauki ledar, suka shiga, Al'ameen a bakin Office ɗin doctor ya tsaya tare da cewa Haidar .
"Room 10 zaka shiga anan take, ni bara na shiga na sallami doctor ina zuwa na sameka."
Kansa Haidar ya ɗaga tare da shigewa shima Al'ameen ya shiga Office din doctor.


Haidar da Sallama ya shiga room ɗin tana zaune kanta a sunkuye, tayi shuru ga wani uban yunwa dake addabarta kanta ta dago tare da amsa sallamar, tana maida kanta ƙasa, Haidar zama yayi tare da cewa.
"Sannu ƴan mata ya jikin naki."
"Da sauƙi"
Ta amsa a hankali kanta na sunkuye, murmushi Haidar yayi ganin kamar tana cikin tsoro yace.
"Baki sanni ba ko.?".
Kanta ta ɗaga alamun eh, murmushi yayi yace.
"Sunana Haidar abokin Al'ameen wanda ya bigeki, kinci abinci ne jiya da dare.?"
Kanta ta kaɗa alamun a'a, zaro idanunsa Haidar yayi yace.
"Yanzu fa kinyi breakfast."
Nan ma Kanta ta ɗaga alamun a'a, Haidar cikin ransa ya furta, lallai Al'ameen bashi da imani, ashe haka yabar Yarinyar nan babu abinci sai kace ya ijiye dutse, numfashi ya sauƙe tare da miƙa mata ledar take away ɗin hanunsa yace.
"Ga abinci kici, meye sunan ki."
"Sunana *ABLAH* "
Murmushi Haidar yayi tare da cewa.
"Nice name, kici abinci Ablah."
Kanta ta kaɗa tare da buɗe ledar, take away ɗaya ta ɗauka tare da fara cin abincin a hankali kamar bazata ciba kaɗan taci ta ijiye ruwa tasha a hankali ta furta.
"Na gode."
Murmushi kawai Haidar yayi yace.
"Karki damu ya shiga wajen DOCTOR bara a sallameki sai mu kaiki gida ko."
Kanta ta ɗaga alamun to, suna nan zaune Al'ameen ya shigo ko sallama baiyi ba ya tsaya a kanta tare da zaro dubu biyar ya ijiye mata a gefen gadon yace.
"An sallameki, ga wannan ki hau adaidaita ki koma gidan ku, Haidar tashi mu tafi."
Hararar sa Haidar yayi tare da cewa.
"Naƙi na tashin yanzu kai sai ka barta ta koma gida ita kaɗai, ka bige ƴar mutane ka Kaita asibiti, ta kwana a matsayin ta na mace, kuma sai ta koma gida ita kaɗai ta cewa iyayenta meye, kaga Malam tare zamu tafi da ita a mota mu danƙata a hanun mahaifinta mu basu haƙuri tashi muje ABLAH mu sauƙeki a gida."
Tsuka Al'ameen yaja yace.
"Ta tashi muje ina, bazata shiga min mota ba, ina ruwana dame zata faɗawa iyayenta, ni na bigeta da ganganne itace fa ta min shigar tsaye ta cuceni, bazan kaita gidan nasu ba, ka tashi mu tafi ta nemi adaidaita ta koma."
Ablah ɗago idanunta tayi ta kalli Al'ameen, tana mamakin mungun halinsa, ayi mutum a rayuwarsa bashi da imani.....................






Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi Naira ɗari biyu kacal 200 guda biyu ne daga aminai biyu Wato ƙawalli da ƙawalliya.

ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN.

acikin littafinta mai taken *AHLAN*

RASHEEDAT USMAN UMMU NASMAH.

Acikin littafinta mai taken *AMINAINA KO ITA?*


Guda ɗaya zaki samu ne akan farashi Naira 200 idan kuma duka biyun kike so zaki biya Naira 300.

Turo da kuɗin ki ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank.

Ko kuma ku turo hoton katin waya na Mtn card ta ɗaya daga cikin waɗannan numbobin.
08147537180
Ko
08165550116


Please banda VTU hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan sai ku turo screen SHORT SHAIDAR BIYA ta cikin waɗannan numbobin.

Kuyi hanzarin biya domin kuwa littattafan sunzo ne da zafin su, zasu bada citta karku sake a barku a baya koda kuɗin ku sai da rabonku.



Please Share and comments.



*Ummu Nasmah ce ✍🏻*
[6/17, 8:28 PM] UMMU NASMAH🥰: 💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅



🤦🏻‍♂️🤦🏻‍♂️🤦🏻‍♂️



💔 *AMINAINA KO ITA?* 💔


🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️



🙆🏻‍♀️ *(BETRAYED LOVE!)* 🙆🏻‍♀️



*NA*


*RASHEEDAT USMAN*

*(UMMU NASMAH)*




Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.



*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*



*Page 9*



"Wai meke damunka ne Al'ameen, wani irin magana ne ta cuceka, saboda bata hankali sai ta shigo titi dan kawai a bigeta,kaga malam dole zamu mai da wannan Yarinyar hanun iyayenta da kanmu."
Haɗe fuska Al'ameen yayi tare da cewa.
"Waya sani ko bata da hankalin, idan zaka maida ita ban hanaka ba, amma dai ba'a tawa motar ba, tunda ba motarka na hau ba."
Murmushi Haidar yayi tare da miƙewa tsaye ya cewa Ablah,
" Ablah tashi muje kinji."
Kanta ta girgiza cikin sanyin murya tace.
"A'a ka bari kawai kuje zan koma da kaina akwai fahimtar juna tsakanina da iyayena zasu fahimce ni, bazan samu wata matsala ba, baya son ɗaukata karka takura masa."
Tafi Al'ameen yasa yana sakin murmushin gefen baki yace.
"Good sarkin iya tsara zance a fuska dai gaki kamar salaha amma Allah ne kaɗai yasan abinda yake cikin ki, to waye bashi da fahimtar juna da iyayensa, kinga tun sanda kika hau titi da gangan na Tabbata ke ƴar neman masifa ce, dan haka bazaki shiga motata ba, balle ki sake jawo min wata masifar."
Haidar kansa ya dafe cike da takaici yaja hanun Al'ameen suka fito, a bakin room ɗin suka tsaya Haidar hanunsa ya haɗe duka biyu alamun roƙo yace.
"Dan Allah badan niba kayi hkr mu maida Yarinyar nan gidan iyayenta, na roƙeka dan Allah badan niba."
Bakinsa Al'ameen ya taɓe tare da cewa.
"Baka tashi cuta ta, sai ka haɗani da ubangijina, nifa hankalina bai kwanta da wannan Yarinyar ba, kawai ku hau adaidaita kai ka maida ta."
Murmushi Haidar yayi tare da cewa.
"Cool down Abokina kasan me, haɗuwarka da wannan Yarinyar iya na yaune fa kawai da zarar mun Kaita gidan su, ba zaka kuma ganinta ba, Please Abokina dan Allah ka sanyawa zuciyarka salama mu tafi kayi hkr."
Numfashi Al'ameen ya saki tare da ɗaga kafaɗarsa, Haidar ciki ya koma ya saka Ablah ta fito, baya ta shiga Haidar yaja motar, suka kama hanyar unguwar Durmi, ta mirror Al'ameen yake hango ta, ta sunkuyar da kanta idanunta sai zubar da hawaye yake, idanu ya zuba mata, cike da mamakin me kuma ya sata kuka, ko munafurci ne, bakin sa ya taɓe tare da kauda kansa daga mirrorn Haidar ne dake tuƙi yace.
"Ablah ta ina gidan nakun yake.?"
Saurin share hawayen ta tayi cikin sanyin murya tace.
"Ɗan gaba kaɗan zamu ƙara."
Kansa Haidar ya ɗaga yace.
"Ki dinga lura idan munzo sai kimin Magana ko."
Da to ta amsa, suna isowa ƙofar gidan nasu tace.
"Mun iso ".
Parking Haidar yayi tare da buɗe motar ya fito buɗe mata yayi itama ta fito, Al'ameen kamar bazai fito ba, sai kuma ya fito, duban gidan da yake gabansu Haidar yayi gida ne na langa langa babu gini ko ɗaya ƙofar gidan kuma an rufesa da bugu kana ganin gidan zaka tabbatar da gidan talakawa ne futuk, shima Al'ameen gidan yake bi da kallo a ransa yana furta cewa yanzu mutum ne ke zaune a cikin wannan gidan yake rayuwa, lallai rayuwa tana yiwa wasa wahala, numfashi ya saki sai kuma yaji tausayin Ablah ya kamasa, sam Yarinyar batayi kama da wacce zatayi rayuwa a cikin wannan gidan ba, Tabbas duk mai rayuwa a wannan gidan dole damuwa da tunani su kasance tare dashi, Haidar duban Ablah yayi yace.
"Ablah nanne gidan naku.?".
Kanta ta ɗaga alamun eh, numfashi ya sauƙe tare da cewa.
"Ki shiga ki mana Magana da babanki."
Cikin sanyin murya tace.
"Bani da Baba, Babana ya juma da rasuwa, nida mamana da ƙanina kawai muke rayuwa acikin gidan, ita take ɗawainiya da rayuwarmu, bara na duba muku ita ko ta dawo daga gidan da take aikatau."
"Aikatau kuma?".
Haidar ya furta.
"Ehh aikatau, dashi take rufa mana asiri, komai dashi take mana."
Runtse idanunsa Al'ameen yayi a rayuwar sa ya tsani ganin mutum cikin ƙangin wahala, sai yanzu ya fara fahimtar lallai damuwa tasa wannan Yarinyar shigowa titi ba tare da kula ba, numfashi Haidar ya saki yace.
"Shikenan ki shiga ki duba mana ita."
Da to ta amsa tare da shigewa kanta a sunkuye.
Haidar duban Al'ameen yayi yace.
"Rayuwarta abar tausayi, da gani suna cikin matsala jagorancin gida a wajen mace akwai wahala."
Ɗan cije leɓensa na ƙasa Al'ameen yayi tare da cewa.
"Ƙwarai kuwa suna cikin matsala, kowa da yadda Allah ya tsara masa tasa rayuwar."
Yayi Maganar Ablah na fitowa daga cikin gidan, tace su shigo, bayanta sukabi, koda suka shiga cikin gidan, tsakar gidan share yake fes babu wata alamar ƙazanta, komai a shirye yake, wata dattijuwar mata suka samu zaune a baranda wacce zata kai kimanin shekaru 45 gefenta yaro ne ƙarami shima zai kai shekara 10 yana shan garin rogo, Sannu da zuwa matar ta musu fuskarta cike da fara'a tare da musu nuni da tabarmar dake shimfide, zama sukayi itama Ablah ta zauna gefen Umma, Umma cike da sakin fuska tace.
"Sannunku da zuwa maraba da hanya."
Haidar ne yace.
"Sannu Mama, mun sameki lafiya."
Da lafiya ta amsa shima Al'ameen ya gaisheta, daga nan bai kuma Magana ba, hankalinsa yana kan Abdu dake shan garin rogo sosai tausayin yaron ya kamasa miƙewa yayi, duk suka bisa da kallo gaban Abdu yaje ya sunkuya tare da ɗauke garin a gabansa yayi wurgi dashi, yaron da kallo ya bi Al'ameen kamar zaiyi kuka itama Ablah idanunta ta zaro cike da tsoron kar a gidan nasu ma ya musu rashin mutunci, Haidar ma zaro idanunsa yayi yana tsoron Al'ameen ya basa kunya Umma mamakin ta duk yafi nasu cikin zuciyarta tana ambaton wannan wani irin mutum ne, Hawaye ne ya zubo daga idanun Abdu yace.
"Yaya ka zubar min da abinci na, yanzu Umma ta bani kuɗi na sayo shine ka watsar min kuma yunwa nake ji."
Murmushi Al'ameen yayi tare da saka hanu ya shafa kan Abdu yace.
"Wannan ba abinci bane, bazai riƙeka ba, yunwa kake ji babu wani abincin ne dole sai wannan."
Abdu cewa yayi.
"Mu bamu da wani abinci shi kaɗai muke ci da rana da daddare kuma Aunty Ablah ta mana tuwo."
Numfashi Al'ameen ya saki tare da cewa.
"Kayi hkr na zubar maka da abinci ko?"
Yayi Maganar yana ciro kuɗi daga aljihun sa Naira dubu daya ya bawa Abdu tare da cewa.
"Maza kaje shago su baka madara da milo da bread kazo kasha kaji."
Dariya Abdu yasa cike da farin ciki kamar bazai mutu ba ya miƙe tare da ficewa a guje, Umma murmushi tayi domin kuwa ta juma bata ga farin cikin ɗanta haka ba, Al'ameen dawowa yayi ya zauna kansa na ƙasa ba tare da ya kalli Umma ba yace.
"Kiyi hkr Mama na bawa ɗanki kuɗi ba tare da izinin ki ba, amm nine Wanda na bige ƴarki Mama bisa kuskure na ɗauketa munje asibiti da wani dattijo, so yace min zaizo gida ya sanar daku ya dawo, tunda dai ya tafi ban kuma ganinsa ba, kiyi hkr dan Allah na miki kuskure."
Murmushi Umma tayi idanunta na cikowa da hawaye tace.
"Yaro hankalina ya tashi sosai da banga Ablah ba, nayi ta yawon nemanta amma babu labari, duk inda nasan Ablah na zuwa naje bata nan, shi wannan dattijo Tabbas yazo sawunsa Uku muna saɓani, na tafi neman Ablah, sai sha ɗaya ya kuma zuwa yake sanar dani abinda ke faruwa, naso ma naje asibitin a wannan lokacin, amma ya hanani yace dare yayi nayi hkr har zuwa Safiya ya tabbatar min da ABLAH tana hanun mutumin kirki, yadda da Baba yasa dole na hkr amma har ga Allah banyi bacci ba, yanzu haka shina tsaya jira yazo muje sai kuma gata tayi sallama, karka damu ba komai ƙaddarace ai."
Murmushi Haidar yayi cike da jin daɗin karancin matar yace.
"To mun gode mama Allah ya ƙara sauƙi mu zamu koma"
yayi Maganar suna miƙewa kusan a tare ko wannensu ya ajiyewa umma kuɗi tare da cewa ta sayi abinci, da farko Umma taƙi amsa,

Please Login or Register in order to submit comment