Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa.
"Na faɗa muku gani nayi kamar kyankyaso cikin miyar shiyasa na zubar."
"Ƙarya kikeyi domin kuwa na hango inuwar mutum sanda nake waya zubar da abincin da kikayi shine ya tabbatar min da kece hmmm! Wato kin min laɓe, yayi kyau to ki sani ke ɗin nan baki isa ki hanani abinda naga dama ba, karfa ki manta matsayinki a cikin gidan nan *ƳARKI MARAR ƳANCI* shine kawai matsayin da kike dashi, ni kuwa uwace wacce kowa keso a cikin gidan."
Numfashi Ablah ta saki tare da ɗago kanta ta kalli Aunty Amarya tace.
"Meyasa kike so ki kashe sa, nayi mamakin hakan matuƙa kefa uwace kamar yadda kike faɗa min yanzu wacce kowa ya yadda da ita acikin gidan, meyasa kikayi Amfani da yardar da suka miki kike cutar dasu.?"
Murmushi Aunty Amarya tayi tare da zama gefen Ablah tace.
"Tambaya me kyau, Tabbas ni uwace amma ba ga Al'ameen da ƴan uwansa ba, ga ƴaƴan dana haifa a ciki na, baki san cewa baka sanin yadda zaka kifar da mutum , har sai ka shiga jikinsa ka gama sanin yaya wannan mutumin yake sannan ya gama basa yardar sa, da zarar ya yadda dakai to fa kafin ya ankara ka kifar dashi, wannan shine salon yaƙi na, banyi zaton akwai wanda zaiji asirina nan kusa ba, sai dai kash tsautsayi yasa kinji sannan har hakan yasa kin dakatar min da aikina na yau hakan ba ƙaramin ciwo yamin ba, sai dai kina da zaɓi tsakanin ki dani na farko tunda kinji sirri na, na baki dama ki dawo gareni mu haɗe ki tayani aiki, zaki samu kuɗin da har ki mutu keda uwarki bazaku yi talauci ba, na biyu kuma idan kinƙi zaki shiga cikin uƙuba ta, zaki gwammaci mutuwa da rayuwa domin ni kaina nasan bani da imani, Tabbas zan ɗanɗana miki azabar da tafi mutuwa ciwo zaɓi yana gareki."
Tunda ta fara Maganar Ablah ke kallonta cike da mamaki tunda take a duniya bata taɓa ganin Mace Irin Aunty Amarya ba, murmushi Ablah tayi cikin izzar da bata san tana dashi ba tace.
"Bana buƙatar abun duniya shiyasa kuɗi basa gabana, hmmm! Rayuwar talauci wannan ai mun saba rayuwa cikin sa, domin kuwa cikin sa muka taso kuma rayuwar tafi min daɗi a haka, bana taɓa aikin zalunci bazan tayaki ɓarna ba, domin kuwa Asali ma ni zan tona miki asiri zan sanar da kowa mugun nufin ki domin su ankara dake su kare rayukansu, bana tsoron uƙubar ki domin kuwa baki isa kimin Abinda ubangiji na bai min ba."
Dariya Aunty Amarya ta saka tare da cewa.
"Au naji tsoro ko zaki tona min asiri, yaro bai san wuta ba sai ya taka, ki tashi yanzu kije ki faɗa muga ko zasu yadda, ni ce fa wacce suka fi yadda da ita fiye da kowa a cikin gidan nan duk abinda zaki faɗa bazasu taɓa yadda ba, a ƙarshe ma kece reshe zai juyewa da mujiya, kije kiyi tunani akan zaɓi na, ki zaɓi zama lafiya ko zaman baƙin cikin rayuwa."
Tayi Maganar tana ficewa daga ROOM ɗin, da kallo Ablah ta bita dashi tana hango tsantsar rashin imani ƙarara a idanunta Tabbas gaskiya ta faɗa koda ta sanar dasu Al'ameen bazasu yadda da ita ba, sannan zata iya aikata duk wani abinda ta faɗi domin kuwa babu Allah a ranta, rasa mafita Ablah tayi sai dai ko me zai faru bazata taɓa yadda ta goyawa Amarya baya ba sai ta mata duk abinda taga dama.
Tana shiga bedroom ɗin ta ta kira Hajiya Mansura ta sanar da ita abinda ke faruwa har yadda sukayi da Ablah itama Hajiya Mansura cike da tashin hankali tace.
"Ba'a raina maƙiyi amarya domin kuwa zai iya maka illar da bazaka ganu ba, karki raina shirin wannan Yarinyar, nama rasa wani hukunci zan yanke ta gigitani da yawa."
Amarya tana hucin ɓacin rai tace.
"Ni na yanke mata hukunci mafi muni a rayuwar Mace muddun bata amsa ƙudirina ba, na rantse da Allah sai na saka an aikata mata."
Hajiya Mansura cewa tayi.
"Wani irin hukunci kika yanke mata.?"
"Hajiya Mansura muddun bata amince da buƙatata ba, to zansa a mata *FYAƊE* kuma na rashin imani wallahi alƙawari na ɗauka............ ........."





Wannan shine ƙarshen Free page daga shi bazaki kuma ganin wannan Book ɗin yana yawo ba, idan har kina son CIGABA da karatun sa, to kiyi maza kizo ki biya kuɗinki ta hanyar nuna min soyayya, siyan wannan Book shi zai nuna min masoyana na gaskiya masu bina da kuɗi ko ba kuɗi sai na jiki, amma ku shaƙata da wannan tallar 👇🏻



*TALLAH TALLAH TALLAH TALLAH*




*AMINAINA KO ITA?*






" Me kike tunanin zai faru *NAFEESAT* Idan har Aminina *HAIDAR* yasan da wannan maganar so kike ki shiga tsakanina da Aminina, to baki da wannan zarrar, ni *AL'AMEEN* nafi ƙarfin kaidinki wallahi, duk tsiyarki da makircin ki, haka zakiyi ki barni nonsense, marar lissafi da kamun kai, idan banda jakar ƙwaƙwalwa irin taki a ina kika taɓa ganin an haɗa kunu da shayi, to bari kiji idan ke ƙwaƙwalwar ki, toshashshiya CE ta kifi, to ni tawa a buɗe take ki fita a hanyata kafin na tozarta rayuwar ki, bana son kisan *KONI WAYE* shiyasa nake binki ta ruwan sanyi idan kika sake fushi na ya fara aiki akanki wallahi sai na saka miki tsoron fitowa waje sai zuciyarki ta tsinke a duk sanda kikaji sunana, bake kaɗai bace ƴar isar da ta iya makirci, ni UBANKI NE a wannan fagen 👉🏻 ki kiyayeni kafin na koyawa rayuwarki darasi, banza wacce bata gaji mutunci ba koda yake na miki uzuri da alamu baki samu tarbiyya bane daga wajen iyayenki wawiya jaka."

Dariya tasa domin kuwa duk wannan maganar da yake gasa mata ko kaɗan babu wacce ta mata zafi a ranta ita dai burinta shine ta mallakesa mai makon ranta ya ɓaci sai ma murmushi da tayi tare da cewa.

" Da zaka daina, Aibata ni da zaifi maka sauƙi, wallahi *AL'AMEEN* tunda nasa raina a kanka sai na Sameka, ina tunanin har yanzu baka gama sanin Kaidi na bane, abu mafi sauƙi a gareka shine kawai ka ajiye wannan shegen girman kan naka, ka dawo gareni, zaifi maka sauƙi, ka daina haɗa *HATSABIBANCI* na da naka domin kuwa nawa ya girmi naka, ni da ka gani wallahi zan iya rabaka da iyayenka, rabuwa kuma ta har abada, bare kuma wani Abokinka *HAIDAR* shi HAIDAR ɗin ƙanin ubanka ne da zaka dinga shayinsa, tsoron me zakaji *AMININE* fa kawai a gareka, akan me ni zaka cuceni saboda da shi, Ko sanda na soshi a lokacin ban sanka bane, shiyasa nayi kuskuren fara Soyayya dashi amma yanzu da na ganka sai naji shi sam ba Soyayya nake masa ba, kaine wanda ka dace da rayuwata ba shiba, dan haka dole sai ka soni."



****************


Faɗa sosai Momma take cike da tsanar yarinyar da kuma kyamarta da take neman tarwatsa musu zumunci.

"Ita kaɗai ce mace a duniya da zaka ce dole sai ita, *HAIDAR* Ka rabu da yarinyar nan domin kuwa ba yarinyar kirki bace."

Cije bakinsa yayi tare da runtse idanunsa yana jin wani ƙuna mai haɗe da ɗaci na taso masa a ƙirjinsa.

" Momma bazan iya rabuwa da ita ba, ina sonta Momma itace rayuwata ta yaya kike tunanin mutum zai iya rayuwa babu numfashi, bazan iya Rabuwa da *NAFEESAT* ba rayuwata tana hanunta ne, dole sai da ita rayuwata zata tafi daidai, muddun ta rabu dani mutuwa zanyi Momma nasan kuma bazaki jure rashina ba, Please Momy ki barni da numfashi na."

Mari Momma ta ɗauke sa dashi tana nuna sa da yatsa tace.

" Ƙarya kake dan ubanka rayuwarka ba a hanunta take ba, rayuwarka tana hanun Ubangiji domin kuwa shine ya busa maka numfashi, ba ita ba, ka rabu da wannan ƴar barinki HAIDAR kona tsine maka Albarka, sannan na ɗaga maka nono ka biya ni wanda ka sha, tunda kai ɗan iska ne marar zuciya, barikaji wallahi muddun nice uwar da na haifeka sai ka rabu da wannan yarinyar NAFEESA."

Hawaye ne masu zafi suka sauƙo daga idanun HAIDAR cike da tashin hankali ya dubi Momma yace.

" Kina nufin na rabu da NAFEESAT, haka kike nufi Momma hakan yana nufin nukushewar Rayuwata ne fa Momy.?"

Cikin tsawar daya rikitar da HAIDAR wanda tunda yake dashi bata taɓa masa ba, tace.

" Ƙwarai kuwa, koda hakan yana nufin mutuwar kane, dole sai ka rabu da ita, idan aje a binneka kowa ma ya huta ka buɗe kunnenka da kyau kaji, ina daf da Rabuwa da kai muddun baka fita a hanyar yarinyar nan ba kasan halina dai idan na yanke hukunci"


Momma tana gama faɗin haka ta shige Bedroom ɗinta a zuciye, HAIDAR wani irin tashin hankali ya shiga, sosai hawaye yake gudu a saman fuskarsa, Tabbas yana cikin tsaka mai wuya, wa zai zaɓa MOMMA KO NAFEESAT?.



****************


*AL'AMEEN* ashe dama kai butulu ne ɗan akuya ban sani ba, wanda baka san mutuncin aminta ba, duk ABOTAR dake tsakanin mu, da shaƙuwa, ashe zaka iya cin amanata, lallai ka cika Ɗan kunama wanda ya kasa gadon mutunci, ko ba aminta a tsakanin mu, jini ɗaya yana gudu a jikin mu, karka manta da naka mahaifin da nawa uwa ɗaya uba ɗaya suke, sannan tsabar Dabbar zuciyarka makahuwa ce ka rasa wa zaka nema duk matan da suke cikin garin nan sai WACCE nake so na aura, wani irin cin amana ce wannan."

Ya isa haka HAIDAR, wani irin mummunar Magana kake faɗa masa, akan Mace, AMININKA ne fa kuma ɗan uwan ka, meyasa bazaka yi bincike ba, sai kawai ka yanke hukunci, dan kawai ta faɗa maka son ranta, wannan ba dai-dai ban........."

Cikin tsawa da kuma zafin rai HAIDAR ya dakatar da FARUƘ.

" Ya isa haka Faruq, babu ruwan ka cikin wannan maganar, karka kuskura ka ƙara kiransa ɗan uwana ko Aminina, domin kuwa ya zubar da amintar dake tsakanin mu, da ƴan uwan taka, zaifi idan ka kirasa butulu kuma maci Amana."

Sosai idanun AL'AMEEN, suka kaɗa suka koma jajur, ko kaɗan baya ganin laifin HAIDAR soyayya ce ta makantar dashi har take sashi yin abinda ba dai-dai ba, amma Tabbas da yasan ko wacece NAFEESAT, dole ya ƙyamace komai son da yake masa, dubansa AL'AMEEN yayi tare da cewa.


" Makahuwar zuciyarka ne tasa kayi kira na da waɗannan mugayen sunan da ka kirani dasui , amma ka sani ni ban kasance koda ɓangare ɗaya daga ciki ba, amma ka gyara kalamanka a kaina a yanzu na maka uzuri saboda naga alamun kan cikin haukar Soyayya, Amma fa idan har ka kaini ƙarshe Maganar da zan faɗa maka sai tafi wacce ka faɗa min ciwo, kai kasan wata NAFEESAT har kake ɗaga jijiyar wuya a kanta ni da ka ganni nafi ƙarfin wannan yarinyar."

Yana gama faɗin haka ya juya tare da ficewa da sauri domin kuwa baya buƙatar amsar da HAIDAR zai mayar masa, FARUQ duban HAIDAR yayi dake famar huci kamar maciji kububuwa ya kasa maida martani domin kuwa wanda zai mayarwan ya fice, cewa HAIDAR yayi.

" Wai waye ne wannan NAFEESAT ɗin da take neman tarwatsa amintar ku, waye ita zanso na ganta HAIDAR."

Dafe kansa HAIDAR yayi da yake masa nauyi ba tare da yace komai ba, ya ciro wayar sa a aljihun wandon sa, screen ɗin wayar ya nunawa FARUQ, Zaro ido FARUQ yayi,yana kallon picture ɗin, gumi ne ya keto masa a matuƙar razane ya matsa baya ya furta.

" *FEENAT* itace kuke rigama a kanta innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un!!!! Budurwa tace fa, HAIDAR kana nufin itace NAFEESAT ɗinka."



Shima HAIDAR a matuƙar razane ya dubi Faruq cike da matuƙar mamaki domin kuwa ba'a ƙasar nan yake ba, ina ya haɗu da NAFEESAT har suka ƙalla soyayya, kodai kamace kawai Faruq ya gani yake zaton budurwarsa ne."






*****************


A razane AL'AMEEN ya miƙe tsaye yana kallon picture's ɗin da ta turo masa hotonsa ne yana kwance shida wata yarinya tsirara haihuwar uwarsu.

" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un allahumma ajirni fil musibati!!!!! Waye wannan yarinyar ban taɓa zina ba, taya za'a turo photo na da wata tsirara alamun muna zina sam bani bane, ban taɓa zina ba, Kuma ina roƙon Allah ya tsareni dashi."

Ya furta cike da tashin hankali, ƙarar shigowar wani text yaji da sauri ya duba.

_Idan har baka amince da Soyayyata ba, ko kaƙi ka Aure ni , Tabbas zan saki wannan picture's ɗin a ko wacce kusurwa ta social Media, kasan kuma wannan picture's ɗin suna fitowa, ba mutuncin ka kaɗai ba, har mutuncin mahaifinka da duniya ta gama sanin shi sai ya zube, wataƙil ma fitowa ta gagari ƴan gidan ku, Saboda duniyar ta tabbatar da babban ɗan *AMBASSADOR AHMAD GIWA* an tabbatar da mazinaci, wataƙil ma wasu suce waya sani ko uban naka ma haka yake, to yanzu ya ka gani, wa yafi makirci tsakanin ni da kai, ka daina kiran ka fini makirci wannan kaɗan ne daga cikin sharri na, zaɓi ya rage gareka koka Aure ni ko mutuncin gidan ku ya zube sai na jika nan da Two days kaɗai na baka idan har ka tsallake waɗannan kwanakin to ka jira kaga yanda zan yaɗaka a asibiti na barar maka da mutuncin ka_





********************


Dariya Sosai FARUQ ya saka yana tsaye gabanta ya zuba hanunsa a cikin aljihu, cikin tashin hankali NAFEESAT tace.


" Waye kai a ina na sanka da har kake ƙoƙarin shiga gonata, malam karka shiga abinda babu ruwan ka a ciki, kar na dawo kanka idan na juyo kanka sai kayi danasanin zuwanka duniya."

Dariya Faruq ya ƙara saki yana yiwa NAFEESAT kallon baki isa ba amsa ya mayar mata da cewa.

" Ai idan kikaji ganga Zaƙin ta yayi yawa to fashewa zatayi dan ubanta, domin kuwa ƙarshen makircin kine yazo, kin shiga gonata kinga kuwa ai dole na takaki, kina niyar sai kin shiga tsakanin AMINAINA, biyu HAIDAR DA AL'AMEEN, to buɗe kunenki kiji muddun ina numfashi burinki akan waɗannan AMINAI bazai taɓa cika ba, domin kuwa nine ƙalubalen ki, idan kina son burinki ya cika, to ki fara kawar dani sai mu gani ko zaki iya, bake kaɗai kika iya makircin ba, kinga wannan video kina sakin wannan picture's ɗin AL'AMEEN wallahi nima sai na sake sa, sai muga dake dashi mutuncin waye zai zube, gara shi namiji ne duk abinda yayi sai ya iya zama kwalliya a garesa, kefa Ballagaza, babu namijin da zai kalleki, bare kiyi tunanin auruwa muza mu gani ni dake shege ka fasa, muddun ina numfashi to Tabbas bazaki taɓa cin Nasara ba."

" Nasara a jinina yake, baka isa ka tare min hanya ba, Al'ameen nawa ne kuma sai na mallakesa, kai kuma nine zanga bayanka kamar yadda ka faɗa na fara ganin bayanka tukunna, to kuwa Tabbas zanga bayanka ka saka a ranka nine ƙalubalenka mu zuba mu gani wake da Nasara zamu gani kai ko ni."








Kuma masu karatu zaku sani idan kuka kasance dani a cikin wannan littafin mai matuƙar rikitarwa tare da makirci tausayi Makahuwar Soyayyar tare da cakwakiya mai wuyar sha'ani, son duniya tsantsar ƙiyayya mai ɗauke da mummunan gaba.


Shi ya kuke tunanin zata kasance Aunty Amarya zatayi nasara kuwa akan Ummi da ƴaƴanta ko zatayi Nasara akan Ablah, shin wacce makoma Rufaida zata fuskanta a wajen Haidar shin zai sota kuwa, ya zata kasance Al'ameen zai amshi Soyayyar Nafeesa kuwa idan ya amsa ina makomar abotar su da zumuncin su da Haidar.


Sai kun kasance dani kafin ku samo wannan amsar.






Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi Naira ɗari biyu kacal 200 guda biyu ne daga aminai biyu Wato ƙawalli da ƙawalliya.

ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN.

acikin littafinta mai taken *AHLAN*

RASHEEDAT USMAN UMMU NASMAH.

Acikin littafinta mai taken *AMINAINA KO ITA?*


Guda ɗaya zaki samu ne akan farashi Naira 200 idan kuma duka biyun kike so zaki biya Naira 300.

Turo da kuɗin ki ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank.

Ko kuma ku turo hoton katin waya na Mtn card ta ɗaya daga cikin waɗannan numbobin.
08147537180
Ko
08165550116


Please banda VTU hoton katin zaki ɗauka ki turo.


Sannan sai ku turo screen SHORT SHAIDAR BIYA ta cikin waɗannan numbobin.

Kuyi hanzarin biya domin kuwa littattafan sunzo ne da zafin su, zasu bada citta karku sake a barku a baya koda kuɗin ku sai da rabonku.



Please Share and comments.



*Ummu Nasmah ce ✍🏻

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment