Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matar Aure na samu, gay zan rigaka Aure fa, kyakkyawa ce ta ajin farko, har yanzu sunanta yana ajiye a zuciyata Nafeesa, sai dai fa na kasa tunkararta da alamu bata ma san ina sonta ba."
Tsuka mai ƙarfi Al'ameen yaja tare da haɗa fuskarsa tamau yace.
"Mtsss!!!! Aikin banza ni nayi zaton wata magana mai mahimmanci zaka faɗa min ashe wannan shirmen banzan ne, yanzu kai Haidar akan mace kake wannan dariyar haka, to kabi a sannu domin kuwa mata sheɗanune mafi yawansu ba ko wacce mace bace zata soka saboda Allah, mafi akasarin su, sunfi son mutum dan kuɗin sa ko saboda kyawunsa, dan haka ka kiyaye kasan irin macen da zaka kula."
Murmushi Haidar ya saki tare da cewa.
"Hmmm!!!! Ba dukkan mata bane suke da fuskar daka ambata zato zunubine koda ya kasance gaskiya, idan zakayi mu'amala da mutum ka kyautata masa zato, ni dai ina sonta kuma ina ji a jikina ta gari ce, ina sonta sosai Al'ameen ya kamata ka tayani son abinda nake so."
"Haidar kenan, duk da bansan wacce kake Magana a kanta ba, sai dai zuciyata bata kwanta da ita ba, sai nakeji a jikina kamar bata dace da rayuwarka ba, kana da right ɗin da zakayi rayuwa da abinda kaso, amma ina ƙara tuna maka, kafin ka amince da Mutum ka fara zurfafa tunani da bincike akansa domin gano ainihin wayeshi."
"Hmmm!!! Al'ameen.............."
Hanu Al'ameen ya ɗaga masa tare da cewa.
"Basai kace komai ina maka fatan alheri Allah yasa ta gari ce."
Da ameen Haidar ya amsa kafin suka koma magana akan Companyn su, sune basu tashi ba sai 5:30pm kowa motarsa ya hau suka taho tare.


Da misalin goma na dare Al'ameen ya sauƙo falo hanunsa riƙe da wayarsa, kusa da Aunty Amarya ya zauna yana cewa Maimu.
"Ke Maimu jeki kawo min abinci na nan"
Da to Maimu ta amsa ta je ɗauko masa, Aunty Amarya ce tace.
"Al'ameen ɗazu Khairi take cemin wai kace gobe bazaka kaita school, kuma dai ka sani bata yadda kowa ya kaita school idan ba kai ba."
Al'ameen duban Aunty Amarya yayi tare da cewa.
"Aunty drever ya kaita ni ina da meeting da ma'aikata 7:30am bazai yiwu na Kaita school ba, gaskiya sai dai tayi hkr kawai drever ya Kaita."
Aunty Amarya cike da nuna ta isa da Al'ameen tace.
"Dole fa kai zaka kaita, idan yaso idan ka sauƙeta sai ka shige Companyn, tunda akwai Haidar sai ya wakilce ka kafin ka iso."
"Amma Aunty Amarya wannan meeting ƊIN fa yana da............"
"Kaga ban tambayeka hujja ko dalili ba, umarni kawai nake baka ka kaita school idan kuma bazaka bi umarnin nawa ba, sai naji."
Numfashi Al'ameen ya saki dai-dai Maimu ta kawo masa, dakakkiyar doya wacce tasha jar miya, gabaki ɗaya rabin miyar nama ne, table ɗin tsakiyar falon ta jawo ta ajiye masa a gabansa tare da ɗaura abincin a kan table ɗin ta juya kawo masa ruwa, duban Aunty yayi tare da cewa.
"Ni na isa naja da umarninki Aunty Amarya, amma dai ki sani Allah muddun bata shirya da wuri ba, tafiya ta zanyi sai dai ta hkr da zuwa school ɗin."
Yayi Maganar cike da biyayya tamkar da ummi yake Magana domin kuwa duka ɗaya ya ɗauke su babu bambanci yanda yake yiwa Momy biyayya itama haka yake mata, murmushi Aunty Amarya tayi tare da cewa.
"Yauwa ko kaifa, bara ma tayi latti ba, ni da kaina zan tashi na shiryata da wuri saboda karma ka mana mita."
Murmushi Al'ameen yayi tare da saka spon da Bismillah ya fara cin abincin, Afnan ce ta sauƙo daga sama jikinta sanye da three cutter ɗin wanda da kuma best fara sol mai shara shara duk ana hango rigar mamanta, ko a jikinta ta nufosu kasancewar Afnan bata da kunya ko kaɗan idanun Al'ameen ne ya sauƙa a kanta da take nufo su, ajiye spon ɗin yayi cikin ɓacin rai, cike da tsanar Afnan domin kuwa ba Yarinyar ya tsana ba, munguwar ɗabiarta da rashin kunyarta ya tsana, a kaf ƙannansa yafi jin haushinta, cikin tsawa mai rikitarwa yace.
"Keee!!!!!! Mahaukaciya, baki da hankali ne, ko jaka ce ke, juya ki koma ki cire waɗannan matsiyatan kayan, karki kuskura ki iso nan, domin kuwa kina isowa zan karyaki, wawiya wanda bata san darajar kanta ba."
Ai kuwa kaf wajen sanda kowa ya tsorata da jin tsawar Al'ameen gabaki ɗayansu da kallo suka bita, girgiza kanta Ummi tayi cikin takaicin halin Afnan ta hauta da faɗa.
"Haba Afnan, bakya gani ne zaki fito da wannan best ɗin cikin mutane ko kin manta idan mu iyayenki ne, Haidar da ma'aikata suna shigowa cikin falon nan, mutunci ne su ganki a haka, meyasa ke kike da taurin kai ne baki jin Magana, ki koma kije ki sako rigar mutunci ki dawo."
Wani irin haushi Aunty Amarya taji jin zagin da Al'ameen da Ummi suka yiwa ƴarta Afnan, amma tsabar iya makirci na Aunty Amarya sai itama ta hau Afnan da nata faɗan amma cikin zuciyarta tana cike da haushin Ummi da Al'ameen.
"Ba magana ake miki bane Afnan kike tsaye, ki juya kije ki sauyo wasu kayan, shasha marar jin magana."
Afnan bakinta ta tura cikin ɓacin rai da rashin kunya tana ƙunƙuni ta haura tana cewa.
"Ni a gidan nan duk abinda nayi ba dai-dai bane saboda kawai an tsaneni."
Tayi Maganar tana haurawa, Aunty Amarya miƙewa tayi tare da cewa Ummi.
"Bara dai nabi Yarinyar nan naci ubanta."
Tayi Maganar tana haurawa da sauri Ummi bata ce komai ba ta cigaba da kallon tv, shi kuwa Al'ameen ji yake a ransa wata rana sai ya karya Afnan Tabbas.


Koda Aunty Amarya ta haura bata kalli room ɗin su Afnan ba, ta shige nata bedroom ɗin zama tayi tare da cewa.
"Aikin banza aikin wofi, matsiyata, sun saka min yarinya a gaba duk neman su cinye min ita, kuma wallahi aniyarku sai ya biku dole ne ma na nemawa Afnan maganin baki, ɗan iska mai jajayen kunnuwa sai famar zazzaga mata zagi kake, to uwarka ce ka faɗawa jakar, kafin kuwa kuga bayan Afnan duk sai naga ƙarshen ku."
Tayi Maganar a fusace tana ɗago wayarta ta dannawa Hajiya Mansura kira ringin ɗaya ta ɗaga Aunty Amarya ce tace.
"Ɗazu na miki transfer ɗin kuɗin da kikace zasuyi aikin, gobe nake son a kashe Khairi, zataje school da misalin 7:39am su tashi 2:15pm ki sanar da Isah Alolo cewa zan ɓatawa drevern da zai ɗaukota lokaci, har sai wajen 4 idan ta gaji da jira zatace zata fito ta tari adaidaita ta dawo gida, shi kuma sai yayi amfani da wannan damar yaje ya ɗauketa gawarta kawai nake buƙatar ya dawo gidan ba tare da ruhi ba ba kuma na son kuskure cikin aikin yayi komai cikin kula."
Dariya Hajiya Mansura ta saka tare da cewa.
"Baki da matsala ki saka a ranki Khairi ta zamo gawa, kinsanni bana kuskure cikin aiki na komai zai tafi dai-dai."
Aunty Amarya Numfashi ta saki tare da katse kiran ta buɗe data hoton Khairi ta tura mata, sannan ta ajiye wayar tana sakin murmushi mai sauti tare da cewa.
"Duk ɗan da ya hana uwarsa bacci, shima kuwa bazai runtsa ba, nine nan zanga bayanki Hajiya gaji."



Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi Naira ɗari biyu kacal 200 guda biyu ne daga aminai biyu Wato ƙawalli da ƙawalliya.

ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN.

acikin littafinta mai taken *AHLAN*

RASHEEDAT USMAN UMMU NASMAH.

Acikin littafinta mai taken *AMINAINA KO ITA?*


Guda ɗaya zaki samu ne akan farashi Naira 200 idan kuma duka biyun kike so zaki biya Naira 300.

Turo da kuɗin ki ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank.

Ko kuma ku turo hoton katin waya na Mtn card ta ɗaya daga cikin waɗannan numbobin.
08147537180
Ko
08165550116


Sannan sai ku turo screen SHORT SHAIDAR BIYA ta cikin waɗannan numbobin.

Kuyi hanzarin biya domin kuwa littattafan sunzo ne da zafin su, zasu bada citta karku sake a barku a baya koda kuɗin ku sai da rabonku.



Please Share and comments.



*Ummu Nasmah ce ✍🏻*
[6/10, 9:47 PM] UMMU NASMAH🥰: 💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅



🤦🏻‍♂️🤦🏻‍♂️🤦🏻‍♂️



💔 *AMINAINA KO ITA?* 💔


🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️



🙆🏻‍♀️ *(BETRAYED LOVE!)* 🙆🏻‍♀️



*NA*


*RASHEEDAT USMAN*

*(UMMU NASMAH)*




Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.



*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*




*Page 4*



Hajiya Mansura murmushi mai sauti ta saki tare da ɗaga wayarta tana duban hoton Khairi still dai murmushin ta kuma tare da dannawa Isah Alolo kira bayan ya ɗaga ne ta fara magana.
"Na maka transfer na 200k ga pictures ɗin Yarinyar na turo maka idan ka gama aikin zan ciko maka sauran, ka tabbatar kayi komai cikin sirri, ka kuma kula saboda tsaro bana son a samu kuskure duk da na yadda da aikinka, gawarta muke son mu gani, ka tabbatar bata numfashi kafin ka wurgar da ita."
Dariya Isah Alolo yasa cikin ƙatuwar muryar sa yace.
"Kema kin sani babu kuskure a cikin aikina, ki zuba ido ki kuma saurari mummunan labari akan wannan Yarinyar."
Yana gama faɗin haka ya katse kiran ba tare daya tsaya ya saurari mai Hajiya Mansura zatace ba.
Hajiya Mansura miƙewa tayi tsaye tare da saka dariya tace.
"Yanzu wasan zai fara, hmmm!!! Amarya zan dage domin ganin burinki ya cika saboda cikar nawa burin, Mansura bata yiwa wani bauta sai ta tabbatar da cewa itace zata more dukkan abinda za'a samu, ni kura ce zanci rabona kuma naci na wani, a gama aikin ni kuma na ɗaura nawa akanki amarya muje zuwa kiga yanda reshe zai juya da mujiya dole kiyi danasanin sanina a rayuwa, domin kuwa dukiyar da kike ƙoƙarin mallakewa su zamo naki ke ɗaya, bazai yiwu ba, wannan dukiyar tawa ce ki gama min aiki da kuɗinki ni kuma zanyiwa kaina da jikina wallahi!! Wallahi!!! Wallahi!! Wannan dukiyar tawa ce sai na mallakesu ko ta halin yaya bazan yadda na mutu a matsiyaciya ba."
Tayi Maganar tana kuma sheƙewa da dariya ta samu waje ta zauna still dai dariyar take.
"Haba Amarya taya zan tsaya na zuba idanu ki zamo hamshaƙiyar mai arziki, ina sam baki dace da wannan matsayin ba, kamar dai yadda na saki kika zamo saliha mai tausayi da jin ƙan Hajiya Gaji da ƴaƴanta kuma mace ta gari a wajen mijinta surka ta gari a wajen Uwar mijinta salihar fuska, alhalin a ƙasan zuciyarki ke munguwa ce, to haka zan kasance saliha mai ƙaunarki a fuska, yayin da ni kaɗai nasan meke ƙarƙashin zuciyata, kinyi kuskuren amincewa dani Amarya, wani ma yayi rawa bare ɗan makaɗi."
Dariya ta kuma tana tashi ta shige tollet.


Ƙarar wayar sa daya jiyo ya sashi juyawa yana cewa Madina ƙanwarsa.
"Ɗauko min wayata a daining Madina."
Da to Madina ta amsa tare da miƙewa, Haidar momma ya duba tare da cewa.
"To amma momma jiya fa munyi waya dashi Salim ɗin, bai sanar dani cewa yana buƙatar kuɗi, sannan kwatakwata kwana nawa ne dana tura masa 80k just one month fa, ace har kuɗin sun ƙare sai kace wanda yake ciyar da gida, gaskiya momma bazan tura masa kuɗi ba, na fara gajiya da almobazarancin Salim saboda shi baisan wahalar neman kuɗi ba shiyasa yake kashe su a banza."
Numfashi momma ta saki cike da rarrashi ta cewa Haidar
"Na sani Salim yana wasa da kuɗi, ko jiya sai da na masa faɗa, ya kuma cemin bazai sake ba, Papan ku, yace bazai tura masa ba saboda yana wasa da kuɗi, to amma kai a matsayinka na ɗan uwansa idan baka basa ba waye zai basa kayi hkr ka tura masa dan Allah kuma danni badan salim ba."
Shuru yayi cike da sanyin jiki domin kuwa bazai iya bijirewa Maganar mahaifiyarsa ba, dole tasa ya amsa, dai-dai Madina na kawo masa wayarsa, karɓa yayi kiran na ƙara shigowa, numbern American ne hakanne ya tabbatar masa da Faruq ne, yana murmushi ya ɗaga tare da cewa.
"Mutanen American."
Daga can Faruq yayi dariya tare da cewa.
"Gamu cikin American amma harna fara jin kewarku, da alamu ƙasar nan bazata min daɗi ba, kana kusa da Al'ameen ne.?"
"No yana can part ɗin su, nima ina namu, kaga dan Allah karka nunawa Daddy baka jin daɗin ƙasar, zaiga kamar ya takuraka, ka daure karka basa kunya, karka manta rayuwarka Daddy yake so ya taimaka ƙarfin gwiwwa ya kamata ka basa."
Kansa Faruq ya jinjina tare da cewa.
"Insha Allah, komai zai tafi dai-dai wai ina labarin Helina kuwa."
Tsuka Haidar yaja tare da cewa.
"Kai nifa na gaji da wannan Yarinyar nayi blocking numbern ta, na kuma hana mu haɗu ka manta da ita kawai, kaga katse kiran nan ka kira Al'ameen tun ɗazu yake maganarka."
Dariya Faruq ya saka yana katse kiran.
Dai-dai Rufaida na shigowa hanunta riƙe da akwati, da Sallama, momma ce ta amsa tana murmushi.
"Rufaida ya na ganki da akwati?"
Madina ce tace.
"Ai kuwa momma dole ki tambaya tafiya zakiyi ne da wannan tsohon daren malama."
Hararar Madina Rufaida tayi tana karasowa ta zauna gefen Ya Haidar tana murmushi tace.
"Momma ni fa gajiya nayi da zama ni kaɗai babu abokin hira, shine nace kawai gara na dawo nan mu zauna da Madina zanfi jin daɗi."
Murmushi Haidar yayi yana zungure mata kai yace.
"Cewa zakiyi kin gaji da zama babu surutu, aku sarkin Magana, to gaki ga Madinan, sai dai fa momma ki ja musu kunne idan suka kuskura suka takura min a gidan nan, zan karya miki yara."
Yayi Maganar yana dariya, Rufaida ma dariya tayi tana tuno shawarar Maimu.
(Part ɗinsu zaki koma da zama domin ƙara samun kusanci dashi, ki san duk yanda zakiyi ki zauna sosai a zuciyar momma ki kuma yi ƙoƙarin ta gane cewa lallai kina son Ya Haidar na Tabbata zata zamo miki jigo kuma makami, sannan shi kuma Ya Haidar kiyi ƙoƙari shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin ku, idan kinyi hakan, daga nan zamu ɗaura a inda muka tsaya.)
Murmushi Rufaida tayi muryar momma taji tana cewa.
"Ai kuwa baka isa ba, yarana dole su wala a gidan nan, kinga Rufaida ku rabu dashi ki tashi kije ku ajiye kayan ki bedroom ɗin Madina dare yayi sai da safe."
Da to Madina ta amsa suka miƙe suka shige itama momma nata bedroom ɗin ta shige, Haidar system ɗinsa ya jawo shine bai shiga ya kwanta ba sai 11:00pm .


✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Washegari da safe, Nafeesa bayan sunyi breakfast ne ta koma bedroom ɗinsu shuru tayi tare da tagumi, Haidar ne kawai a zuciyarta.
"Ya cika miskilancin tsiya, duk yanda zanyi domin ya nemeni, yaƙi fahimta, mtss!!!"
Taja tsuka tare da jawo wayarta, katinsa daya bata ta ɗauka, tana tunanin ta kira ne ko kuma ta haƙura ta gani ko zai nemeta, zuciyarta ne tace mata (Gara ki kirasa kawai karki tsaya garin jan aji ajin ya tsinke) idanunta ta lumshe zuciyarta na bugawa da ƙarfi ta saka numbern cikin wayarta tana tunanin bazai ma ɗaga kiranta ba, danna masa kira tayi kusan sau Uku tana kira yana tsinkewa bai ɗaga ba, cike da damuwa ta dafe ƙirjinta Tabbas tasa burin mallakar kadarori daga garesa, ba kuma zata yadda mafarkinta ya tafi a banza ba, lallai ne dole yau sai tai waya dashi ko ta haɗu dashi dole a cikin biyu sai ɗaya ta faru, ajiye wayar tayi tare da miƙewa ta fito falo, Nazifa da Baba ne kawai zaune Mama bata wajen, ranta ta haɗa ta juya zata koma bedroom ɗinsu taji muryar Baba.
"Nafi!"
Tsayawa tayi tare da juyowa ta amsa, da hanu ya mata alamar tazo babu musu kuwa ta ƙaraso tare da zama gefen Nazifa.
"Nafi! Yanzu ƴar Uwar ki Nazifa take tambayata na baku kuɗi zaku sayi kayan kwalliya da kuma dogayen riguna, kece kika kisata ko tazo ta tambayeni."
Ɗago kanta Nafisa tayi ta kalli Nazifa cike da mamaki domin kuwa ita bata ma san maganar ba, shuru tayi tare da sunkuyar da kanta.
"Magana fa nake miki Nafi! Kin min shuru kece kika sakata ta tambayeni kuɗi, baku da suturar sawa ne, ko dole ne sai kunyi kwalliya kyan fuskar da Allah ya baku bai isheku ba, har sai kun ƙara da wani fenti saboda rashin godiyar Allah, ko ban muku ɗinki a Sallah bane, to bani dashi bazan bayar ba, domin naga alama so kuke na dinga almobazaranci da kuɗi, ina zubar dashi a banza, to baza'ayi wannan shirmen dani ba, ku tashi ku tafi ku bani waje ko sisi bazan baku ba."
Ai kuwa Nafeesa kamar jira take ya gama Maganar ta miƙe ba tare da tace komai ba sai dai har cikin zuciyarta tana cike da baƙin cikin mahaifin nasu, Nazifa ma bayan Nafeesa tabi cikin sanyin jiki, suna shiga bedroom ɗin Nafeesa ta ɗauke Nazifa da wawan mari tana nunata da yatsa cikin huci tace.
"Dan ubanki nine nace miki kije ki tambayesa kuɗi, ko kinga ina saka raina da abun hanunsa, shima yaushe ya saka suturar arziki bare ya sawa ƴaƴansa, ina ruwana da kuɗinsa ina da zuciya na kaina nake nema ban dogara dashi ba, sai dai ke da baki da zuciyar da kare ya cinye zuciyarki ki ta bibiyar sa yana wulaƙantaki amma banda dai nikam, daga yau Nazifa idan kika kuma zuwa neman abu wajen Baba kika saka sunana aciki na rantse da Allah sai nai miki walaƙanci marar zuciya."
Ta ƙarisa Maganar tana jawo jakarta kuɗi ta ɗauko dubu hamsin ta miƙa wa Nazifa.
"Gashi kije ki sai kayan kwalliyar tunda malalacin uban naki ya kasa baki, ke kuma baki da zuciyar nema."
Nazifa idanunta ne sukayi jajur tabi hanun Nafeesa da kallo wanda take miƙo mata kuɗin, kanta Nazifa ta kaɗa tare da cewa.
"Bana buƙatar kuɗin hanunki Aunty, domin kuwa ba daga halak suka fito ba, ta hanyar Haram ne, ni kuwa bazan taɓa cin Haram ba a rayuwata, kema da kike ci ina miki fatan Allah ya shiryeki, Aunty na roƙeki ki daina aibata Baba domin kuwa komai tsiya ya haifeki, kuma ba uban banza bane, raina yana ƙuna a duk sanda kika kira Baba da munguwar kalma, na sani Baba baya bamu kuɗi, amma ya mana gata tunda harya samu a makaranta Arabic da boko kuma ya biya mana, ya bamu ci dasha mai kyau, sannan duk shekara yana mana ɗinki, ki faɗa min me uba zaiyiwa yaransa bayan wannan, Aunty............"
Cikin tsawa mai ƙarfi Nafeesa ta ɗagawa Nazifa hanu.
"Ya isa haka!!!! Ya isa!!! Ba iya karatu da ciyarwa bane kawai haƙƙin mu akan Baba, idanunki sun rufe ba kuma kya da wayo shiyasa bakya fahimtar abubuwa da dama, to amma ki sani, ni dai Baba baya bani haƙƙina na ƴarsa, kuma bazan fasa kalamaina a kansa ba, zaifi miki alkairi ki gimtse bakinki ki daina min wannan wa'axin domin kuwa bazanji ba, kuɗi kuma karki karɓa kanki kika yiwa asara bani ba."
Nazifa kanta ta kaɗa tare da zama tayi shuru duk abinda Baba ya musu bataji zafinsa ba, sai dai tafi jin zafin maganganun Nafeesa akan Baba, gabaki ɗayan su babu wanda ya kuma yiwa wani Magana a cikin su, Nafeesa wayarta ta kuma ɗauka tare da ƙara kiran numbern Haidar.

Haidar dake zaune a Office yana fama da aiki a system ɗinsa yana lissafin kuɗaɗen da kayan zasu kawo musu yaji ringin ɗin wayarsa dubansa ya kai kan wayar, baƙuwar number, hanu yasa ya ɗaga tare da yin shuru, jin an ɗaga anyi shuru yasa Nafeesa itama tayi shuru kuzan 15 minute babu wanda ya yiwa ɗan uwansa Magana cike da hasala Haidar yace.
"Duk wanda ya kira idan bashi da abin cewa zan katse wayar ni ina da aikin yi."
Murmushi Nafeesa ta saki cikin kashe murya tace.
"Sorry Ya Haidar nayi zaton bakai ka ɗaga wayar bane shiyasa nayi shuru, ko ka gane mai Magana.?"
Shuru Haidar yayi yana tunanin ina ya taɓa jin muryar nan, Tabbas yasan muryar sai dai ya manta inda ya santa.
"No ban gane mai Magana ba."
Nafeesa taɓe bakinta tayi tare da cewa.
"Nafeesa ce wacce ka taimaka ka taɓa kawota unguwar mai tama sakamakon ciwon ciki daya turketa a hanya."
Lumshe idanunsa Haidar yayi tare da sakin ajiyar zuciya, dama yana buƙatar numbern ta, a hankali cikin nutsuwa yace.
"Oh sorry nafeesat, Ni kaina na kwana biyu ina buƙatar numbern ki, ya jikin naki."
Murmushi Nafeesa ta saki tace.
"A'a Ya Haidar baka neman domin kuwa daka damu da Number na, na Tabbata zaka samu, ko ka manta jiya ka ganni a airport kaƙi kulani sannan kuma kace ka kwana biyu kana buƙatar number na."
Sosa kansa Haidar yayi cike da kunya kafin yace.
"Eh Tabbas na ganki, akwai uzuri ne da yawa a gabana shiyasa ban samu na miki Magana ba, sorry, Jikin naki da sauƙi dai ko.?"
"Ehh da sauƙi sosai, fatan kana lafiya ya kuma aiki.?"
"Aiki dai ba daɗi domin kuwa baya barin mu mu sami lokaci, ya akayi Nafeesa dama kina ajiye da Number nane.?"
"Ba dole na ijiye numbern ka ba, Ya Haidar kana da mahimmanci a rayuwata, shi kuma abu mai mahimmanci ko yaushe killace sa ake, tun ranar daka taimakeni nake jinka a raina, harta mamana tana son ganinka domin ta maka godiya."
Murmushi Haidar yayi tare da ajiye biron hanunsa yana ture system ɗinsa gefe, jingina yayi jikin kujerar yana jin muryarta har cikin zuciyarsa
"Babu buƙatar Uwa ta yiwa ɗanta godiya, meyasa kika sanar da Mama nine na taimakeki, banso idan nayi abin alkairi a sanar da wani."
Murmushi Nafeesa tayi tare da kwanciya ta jawo filo, domin kuwa da alama tarkon ta ya fara harbawa inda ake bukata, Nazifa bakinta ta taɓe cike da takaicin rayuwar da ƴar uwarta keyi, Nafeesa ce masa tayi.
"Kaima kasan abinda bazai yiwu bane ƙin yabon gwani a lokacin da ya dace, ko ka manta da zancen bahaushe ne da yake cewa, yabon gwani ya zama dole, ita dai Mama tana son ganinka Allah yasa zakazo."
"Amsa kiran Uwa ai dole ne akan ɗanta, ki cewa Mama insha Allah gobe ina zuwa, amm ina cikin uzurin aiki yanzu insha Allah zamuyi waya zuwa dare."
Yayi Maganar dai-dai Al'ameen yana shigowa office ɗin domin kuwa meeting zasu shiga, zama yayi tare da harɗe ƙafarsa yana kallon Haidar.
Lumshe idanunta Nafeesa tayi tare da cewa.
"Okay ka kula da kanka."
Murmushi yayi yace.
"Okay thank."
Wayar ya katse, yana duban Al'ameen daya tsaresa da idanu.
"Da wacce zan Aura nake waya naga ka tsare ni da idanu."
Cike da izza yana taɓe baki ya ɗaga kafaɗarsa cikin ƙasa da muryar sa wanda ya zamo masa ɗabia tamkar baya son Magana yace.
"Waya tambayeka da wa kake waya.?"
"Idanunka sune suka tambayeni, wai dan Allah Al'ameen na tambayeka, me

Please Login or Register in order to submit comment