Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kowa a cikin sa Daddy ta duba sannan ta fara magana.
"Aminu jiya Hajiya maimuna take sanar dani cewa tare da Faruqu zaka tafi, zaije ya tayaka aiki harna tsawon shekara ɗaya wanda Ni baka sanar dani hakan ba, da ka sanar dani Aminu bazan barka ka raba Faruqu da ƴan uwansa ba saboda sun shaƙu, basu kuma taɓa rabuwa da junansu ba, sai yanzu rana tsaka zaka rabasu meyasa kayi haka.?"
Nisawa Daddy yayi tare da gyara zamansa yace.
" Inna nasan ko na faɗa miki ba zaki barni na tafi dashi ba, kuma dole ina buƙatar matashi mai jini a jiki a cikin aikina saboda ni tsufa ya fara cimin ina buƙatar magajin da zai gajeni ta fuskar siyasa, bana son nabar wannan gomnatin ba tare da nabar magaji ba, dalilin ds yasa zan ɗauki Faruq naje na nuna masa yadda muke harkokin mu, Al'ameen da Haidar bazasu iya siyasa ba shiyasa ban ɗauki ɗaya a cikin su, Faruq ya fisu iya mu'amala da jama'a da kuma sakewar fuska wanda wadannan ɗabiun shine ɗabi'un ƴan siyasa, Inna ina ji a jiki na muddun faruq ya iya siyasa zai zamo babban ƙusa a gomnati , dalilin kenan da yasa nake son tafiya dashi, Kuma Inna ai rabuwa tsakanin su wannan dole ne koda tafiya bai rabasu ba akwai mutuwa Inna dole ne ana tare wata rana za'a rabu."
Duk da Inna Jumma taji daɗin zancen Daddy akan Faruq domin kuwa niyarsa mai kyau ne akan sa sam bashi da mugunta da ace son kai zaiyi Al'ameen zai ɗauka ba faruq ba, amma sai Inna Jumma tace.
" Wannan ba hujja bace da zaka rabasa da ƴan uwansa, ina jin dadin yanda nake ganin kan jikokina a haɗe sam bana son abinda zai taɓa rayuwarsu, domin kuwa da wani abu na ɓacin rai ya samesu na gwammaci ni ya sameni, Kafin yanke hukuncin tafiya dashi ya kamata ka tuntuɓesa kaji meye ra'ayinsa shin yana da burin siyasa, domin kuwa yana da ƴancin da zai zaɓawa rayuwarsa abinda ya dace dashi siyasa ana shigarsa ne da zuciya da kuma ra'ayin mutum ba wai ra'ayin wani ba, a yanzu ka yanke hukunci akansa kuma kun gama shirya tafiyarku bazan dakatar daku ba, ina fatan alheri da samun cikakkiyar nasara, amma ina son Idan kunje ka tattauna dashi akan ra'ayinsa kafin ku fara aikin hakan yana da kyau ka bawa mutum damarsa."
Murmushi Daddy yayi cike da jin daɗi domin kuwa yayi zaton Inna Jumma zata hanasa tafiyar ne da Faruq cike da ladabi yace.
" Insha Allah zan fara magana dashi kafin aiwatar da komai naji daɗi da kika bani wannan damar baki hanani tafiya dashi, insha Allah Inna zakiyi alfahari da siyasar Faruq, ina jin a jikina wata rana zai zamo babba a wannan ƙasar."
Kafin Inna Jumma tayi Magana Al'ameen cike murmushi ba tare da ƙyashi ko nuna Hassada ba, ya miƙe tsaye tare da dawowa kusa da Inna Jumma ya zauna yana dafa kafaɗar ta kamar dai yadda ya saba Magana cikin iko da taƙama ya kalli Daddy tare da cewa.
" Daddy waya faɗa maka Inna Jumma ce kawai zatayi alfahari da kasancewar ɗan uwanmu cikin siyasa, gaba ɗaya wannan ƙasar sai tayi alfahari dashi, zuciyamu ɗaya idan ɗayan mu yana son abu haka take a zuciyar ɗaya shima zaiso, muna son Wannan siyasar nasan kuma shima Faruq yana so, zai kuma yi Nasara da yaddar Ubangiji sai ya zamo tamkar kai kuma ina da tabbacin cewa al'ummar wannan jihar zata karɓi jinin *AHMAD GIWA* bazasu butulcewa alkairan daka musu ba"
Haidar shima murmushi ya yi ya miƙe ya zauna a ɗayan gefen Inna Jumma suka sanyata a tsakiya tare da cewa.
" Kayi gaskiya Daddy Faruq ya fimu da abubuwa masu yawa MUSSAMAN ta fuskar Al'umma mutum ne mai son jama'a da ganin ya kyautata musu taimako kuma wannan a jininsa yake, tabbas ya fimu wasa da dariya da kuma mu'amala da mutane wannan halin shi ake so a samu daga zakwaƙurin ɗan siyasa, sai dai Daddy ga wata tambayar da nake bukatar amsar su.?"
Ya ƙarisa Maganar yana murmushi, Faruq duk da kallo yabi ƴan uwansa domin kuwa yana jin daɗin yadda suke yawan ƙarfafa masa gwiwwa, kullum cikin son cigaban sa suke, duk da bayi da ra'ayin siyasa, sai dai bazai bawa Maganar ƴan uwansa kuma *AMINANSA* kunya ba dole zai karɓi wannan al'amari da zuciyarsu maimaita kalmar Al'ameen yayi a zuciyarsa " zuciyar mu ɗaya ce idan ɗayan mu yana son abu to haka take a zuciyar ɗaya shima zaiso muna son wannan siyasar nasan kuma shima Faruq zaiso" numfashi ya sauƙe yana jin Soyayyar ƴan uwansa har cikin ransa zai iya komai domin kare rayuwarsu ciki harda bada rayuwarsa, muryar Daddy yaji yana cewa.
" Ina jikinka Haidar yi tambayarka ni kuwa zan amsa maka."
Murmushi Haidar yayi tare da cewa.
" Hausawa suna cewa da rarrafe akan tashi har a fara tafiya, amma kai sai naga kamar so kake Faruq ya Fara da gudu, a Nigeria Faruq ya kamata ya zauna ya koyi siyasar sa amma kai kuma kana shirin kaisa American ko meyasa Daddy."
Numfashi Daddy ya sauƙe tare da yin murmushi na manya tare da cewa.
" A harkar siyasa ba'a taɓa tashi da rarrafe domin kuwa kace da rarrafe zaka tashi to fa zaka daɗe baka fara koda tsayuwa bane bare kuma tafiya, ita siyasa tana buƙatar Babban ubangida ne wanda zai maka jagora ya tsayar dakai ga al'umma wanda nasararka zata fara ne da ga wannan ubangidan, kamar dai yadda nake son ɗaga Faruq yayi gudu bama tafiya ba, bima'ana ina son na fara gabatar da Faruq ga shugaban kasar American Jolieurs Abom Wanda yake shaƙiƙi ga shugaban kasar Nigeriya Olusegun Asom Faruq zai zauna tare da Jolieurs Abom na wannan shekara ɗayan domin shaƙuwa dashi ta hakan zamu fara gabatar da son shigar dashi siyasa bisa samun babban kujerar ministan Jiha daga nan nida Jolieurs sai mu tunkari Olusegun da wannan buƙatar wanda hakan bazai bamu matsala ba wajen samun cikakkiyar nasara yanzu ka fahimci ni."
Aunty ne tayi murmushi tare jin daɗin yadda kowa a wajen ke buƙatar cigaban ɗanta ba tare da Hassada ba Haidar dariya yayi tare da duban agogon hanunsa ya ce.
" Yes Daddy na fahimta, time is over."
Ɗan dariya Daddy yayi tare da miƙewa yana miƙawa ɗan uwansa hanu Abi hanu tare da cewa.
" Ka kula da Al'ameen da Haidar kasa ido sosai a kansu, kaine ubansu mai kula da lamuransu a yanzu nida Alh Kabeer ba mazauna ƙasar nan bane kaine kake cikin ƙasar KULLUM haƙƙin kula dasu ya rataya ne a wuyan ka, zamu iya tafiya."
Gabaki ɗayan su miƙewa sukayi, kowa na rungumar Faruq cike da Soyayya sukayi sallama, Abi Haidar Al'ameen, sai Rufaida Da Sai Maimu sune suka rakasu har airport, sun juma zaune kafin jirgin ya tashi, sosai sukayi alhinin rabuwa da Faruq jikinsu duk a sanyaye, Suna tsaye har jirgin su Faruq ya tashi, kasancewar mota biyu suka fito da ita yasa Abi cewa Al'ameen yazo ya jasa zuwa unguwa, shi kuma Haidar ya maida su Rufaida gida.
Haidar yazo zai buɗe motar sa ya shige idanunsa suka sauƙa a kanta tana tsaye sanye da dogon hijabi, fuskarta cike da murmushi bakinta taji jan janbaki suna tsaye da wata budurwa wacce bazata wuce shekarunta ba, da kallo Haidar ya bita tare da furta.
" Me kuma ya kawota nan, idanunsa ya lumshe tare da kuma cewa kyakkyawa ce, tana da kyan kallo, kowa ta rako.?"
Ya furta yana murmushi tare da shigewa cikin motar yaja, yana binta da kallo, yana jin wani abu a zuciyarsa game da ita, Rufaida lura da wajen da Haidar yake kallo ya sata duban wajen, Nafeesa ta sunkuya sai ƙawarta kawai ta hango a zaton ta ƙawar Nafeesa yake kallo, cike da haushi da kuma kishi kasancewar Rufaida ta juma tana son ɗan uwanna ta wanda shi kwatakwata ya gagara gane hakan, kafaɗarsa ta dafa tare da cewa.
" Mister Love, ja muje ko kuma na fita na maka Magana da ita."
Juyowa Haidar yayi ya kalli Rufaida yana dariya tare da jan motar yace.
" Kai dai Yarinyar baki da kunya ina matsayin yayanki kike kira na da Mister Love ko, Yarinyar tana da kyau ya kika ganta ta dace da zama cikin FAMILY mu ko.?"
Kawar da kanta gefe Rufaida tayi tana jin wani baƙin ciki na taso mata, a hankali tayi murmushin yaƙe tare da cewa.
" Ni ban ganta ba, na dai hango bayanta amma banga fuskarta ba."
Girgiza kanta Maimu tayi tana sakin murmushi tace.
" Yaya Haidar ai ita mace ba kyawunta ake dubawa ba ɗabiun ta sune abin duba nasabar ta da addinin ta, idan har tana da waɗannan to ta dace da zama cikin zuri'ar mu."
Murmushi Haidar yayi yana harbawa titi yace.
" Bansan komai a kanta ba amma dai naji zuciyata na sonta, zan gwada auna matsayin addinin ta da kuma tarbiyyar ta."
Runtse idanunta Rufaida tayi ranta na mata ƙuna harta ƙagu su sauƙa domin kuwa zuciyarta bazata jure jin wannan zancen nasu ba.

Ita kuwa Nafeesa dariya tasa bayan sun shiga cikin motar Amnat, hijabin ta cire take ɗamammun kayan dake jikinta suka bayyana rigar jikinta ta kamata tamkar ƙirjinta zai tsage rabin nonon ta duk a waje, siket ɗin jikinta ma a ɗame yake tamkar bom ɗinta zai tsage, kallon Amnat tayi tare da cewa.
" Da alamu dai bai manta dani ba a yanayin yadda yake bina da kallo, naso ace yazo ya samemu amma tsabar MISKILANCI ya share yayi tafiyar sa, ina da buri na samun manyan kuɗaɗe fa a wajen wannan gaye ɗin, amma da alamu bana gabansa, sai dai fa dole ne sai na juyo da hankalin sa gareni dole na shiga zuciyarsa domin kuwa ina buƙatar cikar burina."





Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi Naira ɗari biyu kacal 200 guda biyu ne daga aminai biyu Wato ƙawalli da ƙawalliya.

ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN.

acikin littafinta mai taken *AHLAN*

RASHEEDAT USMAN UMMU NASMAH.

Acikin littafinta mai taken *AMINAINA KO ITA?*


Guda ɗaya zaki samu ne akan farashi Naira 200 idan kuma duka biyun kike so zaki biya Naira 300.

Turo da kuɗin ki ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank.

Ko kuma ku turo hoton katin waya na Mtn card ta ɗaya daga cikin waɗannan numbobin.
08147537180
Ko
08165550116


Sannan sai ku turo screen SHORT SHAIDAR BIYA ta cikin waɗannan numbobin.

Kuyi hanzarin biya domin kuwa littattafan sunzo ne da zafin su, zasu bada citta karku sake a barku a baya koda kuɗin ku sai da rabonku.



Please Share and comments.



*Ummu Nasmah ce ✍🏻*
[6/6, 10:19 PM] UMMU NASMAH🥰: 💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅



🤦🏻‍♂️🤦🏻‍♂️🤦🏻‍♂️



💔 *AMINAINA KO ITA?* 💔


🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️



🙆🏻‍♀️ *(BETRAYED LOVE!)* 🙆🏻‍♀️



*NA*


*RASHEEDAT USMAN*

*(UMMU NASMAH)*




Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.



*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*




*Page* 3



Amnat duban Nafeesa tayi tare da cewa.
"Gayen ya haɗu iya haɗuwa ga kuɗi ga wanka ga kuma class, yanzu ke Nafeesa wannan gayen bazaki sosa so na gaskiya ba, idan har kika samu kika auri wannan to wallahi kin dace, amma abun mamaki sai naga kuɗinsa kawai kike so ba shiba, baki taɓa saurayi mai kyau da ajin wannan ba, ƙawata idan zan baki shawara ki ɗauka, wannan gayen gara ki auresa ki huta, Mama ma ta huta, rayuwar barikin nan ba daɗi ne da ita ba, Nafeesa da ace nine na samu wannan damar taki bazanyi wasa da ita ba wajen rufawa kaina asiri, wallahi Auren sa zanyi muyi zaman mu na har abada domin kuwa nasan komai na rayuwa zan samesa."
Nafeesa taɓe bakinta tayi tare da cewa.
"Ke kike hango wannan kyau da wankan ni ko kaɗan basa gabana, ke nifa babu son Wannan gayen ko kaɗan a zuciyata asali ma bana hango kyawunsa, kuɗin kawai nake son na kwasa, idan na gama samun abinda nake so, yasar da banza zanyi nayi gaba, ke koma ban gama samun abinda nake so a garesa ba, naga wanda ya fisa zan yasar dashi na ɗauki wannan dan haka daina min zancen Aure babu wannan batun baya gabana."
"Yo amma Nafeesa kina gan......."
"Bar zancen dan Allah ja mota mu tafi kaina ya fara ciwo ga wannan nacaccen Alh Atiku Naira yana jirana."
Tayi Maganar tana ɗagawa Amnat hanu, Amnat taɓe bakinta tayi tare da jan motar suka bar wajen ba tare da ta kuma cewa komai ba.

Yana parking Rufaida ta fita cikin sauri ta nufi part ɗinsu ranta a cunkushe, Maimu kanta ta girgiza tare da cewa Ya Haidar.
"Ya Haidar bara na shiga part ɗin Aunty."
Kansa ya ɗaga mata alamun to yana tafiya, Maimu part ɗin Aunty ta shiga da sallama tana zaune ita da Atine Aunty Kanta ta ɗago tare da cewa.
"Maimu lafiya kuwa naga Rufaida ta shigo cikin damuwa.?"
Ɗan murmushi Maimu tayi tace.
"Lafiya Aunty wai kanta ke ciwo yanzu ma wayarta na shigo bata, bara na haura na sameta."
Ta yiwa Aunty ƙarya tana haura bedroom ɗin Rufaida akwance ruf da ciki ta sameta sai kuka take numfashi Maimu ta saki tare da zama gefenta tace.
"Kina bani mamaki Rufaida yanzu meye abin kuka anan bayan kece kike wasa da dukkanin damarki ki tashi muyi magana."
Miƙewa Rufaida tayi ta zauna tana goge hawayenta tace.
"Wace dama na samu a garesa da har nayi wasa da ita, gani nayi baima san inayi ba, bare kuma har yabani damar da zanyi wasa da ita, ni kaɗai nake dakon sonsa shi baisan inayi ba Maimu anya rayuwa zata yiwu min babu yaya Haidar mtsss!!! Bansan yadda zanyi ya fahimci girman son da nake masa ba zuciyata har nauyi take min wani lokacin."
"Hmmm!!! Shiyasa nace laifinki ne, kefa macece kuma kina da kyau da diri gami da ajin da namiji zai soki baki da makusa ko kaɗan, to meyasa zaki gagara shawo kan namiji ƙwaya ɗaya ki amshe Soyayyar sa, damar da kikayi wasa da ita, itace Yaya Haidar dai ɗan uwanki ne, kinfi ko wacce mace kusa dashi, wannan babbar dama ce da zakiyi Amfani dashi wajen juyo da hankalinsa gareki, ina fatan kin fahimci abinda nake nufi."?
"Na fahimta amma meyasa kike basa ƙwarin gwiwwa akan wata mace, kina nuna masa yaso waccar Yarinyar idan tana da nasaba da addini, hakan yamin ciwo a zuciyata mussaman da naji daga bakinki Maganar ta fito."
Murmushi mai sauti Maimu ta saki har haƙwaranta ya bayyana duban Rufaida tayi tace.
"Ina sane nayi hakan saboda na zaburar dake ki gane cewa muddun baki tashi kin tsaya akan yaya Haidar ba, zaki iya rasashi ya kufce miki, kinga karki tsaya kallon ruwa kwaɗo ya miki ƙafa gara ki fara lalubo Soyayyarki a zuciyarsa tun kafin lokaci ya ƙure miki domin kuwa da alamu hankalinsa ya fara tafiya ga wannan Yarinyar."
"Maimu da alamu kin fini gogewa a wannan fagen, ki sani a hanya domin ƙwato Soyayyata."
Murmushi Maimu ta saki tare da cewa.
"Angama ƴar Uwata, insha Allah sai Yaya Haidar ya dawo hanunki zai soki Soyayya mai tsanani zai kalli dukkan wasu mata tamkar maza kece kawai zaki kasance mace a idanunsa."
"Na yarda dake Maimu nasan zaki iya."
Murmushi Maimu tayi tare da miƙewa tana cewa.
"Bara na ƙarisa part ɗin mu, nasan yanzu Ummi na jirana akwai aiki sai kin shigo."
Har falo Rufaida ta rako Maimu ta wuce sannan ta koma.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Hajiya Mansura na faɗa miki hankalina bazai taɓa kwanciya ba muddun ina kallon Ummin Al'ameen da waɗannan yaran nata shida reras, wallahi zuciyata tamkar zata buga haka nake ji, mtsss ya kamata musan abun yi na gaji da zura idanu ina kallo wata rana tazo ta ƙwace dukiyar Daddyn Al'ameen ni a barni da ɗan kaɗan, domin kuwa ko yau Daddyn Al'ameen ya faɗi ya mutu Ni ce na shiga Uku bazan mori komai ba, yara mata biyu fa kawai nake da, ita kuwa maza biyu mata huɗu, shikenan ta ƙwace dukiyar ni ta barni a wulaƙance, Hajiya Mansura ya zanyi da wannan Ƙaddararriyar matar."
Aunty Amarya ce mai wannan maganar cikin matsanancin tashin hankali, Hajiya Mansura Numfashi ta sauƙe tare da nisawa tace.
"Ki kwantar da hankalinki Amarya kin san dai bana taɓa rasa mafita, kefa Amarya ki godewa Allah domin kuwa kece mai nasara akan Hajiya Gaji, domin kuwa zaki zame mata macijin sari ka noƙe ne, karki manta da cewa zuwa yanzu Hajiya Gaji ta gama yarda dake, bazata taɓa tunanin cewa zaki cuceta ba, kinga ko dama abinda muke buƙata kenan ta yarda dake, aikin mu zai fara ne daga yanzu, ni na gama yanke hukunci, yawan yaran nata zamu rage mata, gara ku dawo dai-dai."
Cike da rashin fahimta Aunty Amarya tace.
"Mu rage yawan ƴaƴanta kuma, ban gane abinda kike nufi ba.?"
Murmushi Hajiya Mansura ta saki tare da miƙewa tsaye ta goya hanunta a bayanta tare da cewa.
"Bamu da wata mafitar da ta wuce muyi kisan kai, zamu saka a kashe ƴaƴanta huɗu abar mata biyu, kinga kunya Drow."
"To amma Hajiya Mansura anya wannan shawarace wacce zata yiwu kuwa, akwai hatsari fa sosai cikin wannan aikin, sannan idan asirin mu ya tonu mun shiga Uku"
"hmmm to ƙarya kike hankalinki baya tashi idan kingan su domin kuwa da hankalinki yana tashi bazaki kawo tsoro cikin ranki ba, kinga Amarya muddun kina neman biyan buƙatar ki, dole ne sai munyi kisan kai, idan kuma kika saka tsoro cikin zuciyarki kina kallo ALH AHMAD zai faɗi ya mutu, ki tashi da tumulin takaba kawai kinyi zaman iska, sai dai kiga Hajiya Gaji ta kwashe dukiyar."
Shuru Aunty Amarya tayi cike da nazarin maganganun Hajiya Mansura Tabbas idan ta tsaya kallon ruwa tofa kwaɗo zai jefa mata ƙafa to ma tsoron me zataji ita da kowa ya gama amincewa da ita a cikin gidan, murmushi ta saki mai sauti tare da cewa Hajiya Mansura.
"Kina da gaskiya muddun nayi wasa to fa zanga wasa, shata min layi kawai na hau hanya, idan ta kama ko Ummin Al'ameen ɗinne itama sai mu aikata"
Dariya Hajiya Mansura ta saki mai sauti tare da cewa.
"Good Ƙawata, yanzu abinda zai faru bari muga tana da yara shida Al'ameen Maimu Khalifa ashfat Samira And Khairi, shi Khalifa da ashfat suna London karatu ba, ita kuma Samira tana boarding school, zamu fara da Khairi ita zamu fara kashewa, da ita zamu fara musu Sallama na Tabbata kuma babu mai zarginki, domin akwai Amana da yarda tsakanin ku, Isah Alolo zamu saka yayi kisan, ki turo min pictures ɗin ta da zan basa sannan ki saka mana ido akan fitarta da kuma wajen da zataje ta, shi kuma zaiyi amfani da wannan Detail ɗin wajen iske ta, naji alart na dubu ɗari huɗu, mu basa na aiki, sannan........."
"Aunty Amarya!!! Aunty Amarya!!! Aunty Amarya!!!"
Muryar Maimu ya dakatar da Hajiya Mansura da Maganar da take jiyo sautin kiran da take yiwa Amarya, Aunty Amarya amsawa tayi, Maimu ta shigo cikin nutsuwa, Murmushi tayi ganin Hajiya Mansura, tace.
"Momy Mansura, sannu da zuwa ashe kina ciki."
Hajiya Mansura murmushi ta saki cikin sakewar fuska tace.
"Ina ciki yanzu ai nake tambayar Amarya ku, ya karatu."
"Karatu Alhamdulillah!! Amm Aunty Amarya key ɗin motar ki zaki ara min zanje gidan su Safara'u zan amso assignment ɗina, tawa motar tayar ta samu matsala sai an sauya wata, kuma babu wata tayar, Ummi kuma ta hanani nata, nasan kekam bazaki hanani ba Aunty Amarya."
Murmushi Aunty Amarya ta saki tare da cewa.
"Oh Ummin Al'ameen sai kace wanda zaki cinye motar, ai kuwa bazan hanaki ba, kije falo na, tana kan desk ki ɗauka."
Da to Maimu ta amsa tare da ficewa tana dariya, Hajiya Mansura bakinta ta taɓe suka cigaba da ƙulla ƙullar su, ta juma sosai cikin room ɗin Aunty Amarya kafin ta tafi.


"Oh ni jikar mutum Huɗu, Amarya kizo ki rabani da wannan ja'irar Yarinyar taki, tabi ta isheni, sai famar ɓuruntu take min"
Ummi dake zaune gefe tare da Aunty Amarya ne tayi dariya tare da cewa.
"To fa yau kuma Minal da Inna ne ake faɗa, Amarya sai ki tashi kije rabiya kafin a kaure da kokawa"
Dariya Aunty Amarya tayi tace.
"A'a Ummin Al'ameen ni babu ruwana kece zakije wannan rabiyar faɗan."
Ummi murmushi tayi tare da ƙwalawa Minal kira, tana cewa.
"Meena ta, mazo zoki amsa rabu da Inna kizo wajen Ummin ki."
Minal baki ta tura tare da miƙewa tana tura bakin ta taho, Khairi ce ta shigo hanunta riƙe da school bag tayi matuƙar gajiya jikin Aunty Amarya ta faɗa kasancewar tayi sabo sosai da ita tamkar Ummi haka takejin Aunty Amarya.
"Aunty Amarya yunwa nakeji, yau Ummi ƙwai kawai ta soya min Allah duk ban ƙoshi ba yunwa nakeji."
Girgiza kanta Ummi tare da cewa.
"Ina kuwa zaki ƙoshi aike bakya ƙoshi Khairi cikin ki zurfi garesa komai kikaci anjuma babu, ke gaki uwar ci."
Aunty Amarya ce tace.
"Ummin Al'ameen babu ruwanki cikin wannan lamarin, bafa dake take Magana ba, Auntyn ta take faɗawa, dan haka karki shiga tsakanin ƴa da Uwa, tashi muje Khairi na, na haɗa miki abinci ko."
Khairi gwalo ta yiwa Ummi tare da miƙewa tabi bayan Aunty Amarya, Ummi murmushi tayi sosai take jin daɗin yadda Aunty Amarya ta ɗauki yaranta tamkar nata ƴaƴan babu wani banbanci.


Hancin motarsa ya danno cikin Companyn, a parking space yayi parking tare da fitowa fuskarsa sam babu alamun dariya, tunda ya fito ma'aikatan suke risinawa suna gaishesa, amma tsabar MISKILANCI irin na Al'ameen hanu kawai yake ɗaga musu babu wanda ya amsawa gaisuwar, harya shige Office ɗinsa, Ibrahim ne ya taɓa Salihu tare da cewa.
"Wallahi na tsani gaishe da mutumin, ya cika girman kan tsiya, mutum shi kullum babu rahama a fuskarsa, gaisuwa ma ya amsa yana ganin asara ne mtsss Allah ji nake kamar nabar aiki a Companyn nan saboda mutumin nan."
Salihu dariya yasa tare da cewa.
"Ko kaima ka faɗa, amma ni sai nake ganin kamar ba baƙin hali bane, haka yanayin sa, yake, idan ka lura shifa koda ma'aikata masu office bai cika magana ba, saɓanin Oga Haidar dashi babu ruwansa kowa nasa ne."
"Hmmm koma yaya ne shi dai ya sani bara naje na sanar da Oga Haidar ya shigo yace idan ya shigo nazo na sanar dashi."
Da to Salihu ya amsa kowa yayi wucewar sa harkar sa."
Office ɗinsa ya shiga ya zauna yana jawo takaddun dake ajiye saman table ɗin, ya fara dubawa, ya ɗan juma cikin Office ɗin Haidar ya shigo zama yayi tare da fuskantar sa, yace.
"Wai kunyi waya da Faruq kuwa zuwa yanzu yaci ace sun isa just 9 hours fa, na kira layin nasa baya tafiya."
Ɗagowa Al'ameen yayi tare da ajiye biro dake hanunsa yace.
"Numbern sa bazai shiga ba ai dole sai ya sauya layi, maybe zuwa dare zai kira."
Yau naga mood ɗinka ya sauya meke faruwa da alamu kana cikin farin ciki.
Murmushi Haidar ya saki yana lumshe idanunsa tare da dafe ƙirjinsa yace.
"Nayi kyakkyawan kamu ne Al'ameen.?"
"Kyakkyawan kamu kuma to faɗi muji na tayaka farin cikin."
Ɗan dariya Haidar ya saki tare da cewa.
"Budurwa nayi kuma dai da alamu

Please Login or Register in order to submit comment