Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan Rayuwar sannan nasan dole zaki samu wani darasin a wannan gida na masu kuɗin sai kinje zaki fahimci zance na, domin kuwa yanzu a ɗaure na baki Maganar zaiyi wuya ki fahimta, sai dai abinda nake so dake Ablah karki taɓa bani kunya a rayuwa, na baki tarbiyya dan Allah ki riƙe tarbiyyar ki, bana son ki kasance mai kwaɗayi akan abunsu, ki dinga kawar da kanki daga shiga harkar da bai shafeki ba, ki kasance mai haƙuri akan komai, karkiyi wasa da ibadarki Ablah, sannan ina ƙara jaddada miki cewa karki yadda ki cuci wani da ki cuci mutum gara shi ya cuceki, sannan karkiga abinda zai cutar da wani kiyi shuru idan har kina da halin dakatarwa to ki dakatar, ki taimaki duk wanda yake bukatar taimako muddun kina da abinda zaki taimaka Allah ya miki albarka, insha Allah rayuwarki zata haska."
Kanta Ablah ta kaɗa tace.
"Shikenan Umma Allah yasa hakan shi yafi alkairi, kuma insha Allah bazan baki kunya ba, duk abinda kika umarce ni shine abinda zanyi a rayuwata, baki da matsala dani Umma bazan taɓa watsar da tarbiyyar ki ba har abada."
"Allah ya miki albarka, ki ƙarasa karatun ni bara nayi gyaran ɗakin."
Da to ta amsa tare da ɗaukar ƙur'aninta ta cigaba da karatu.

Washegari da safe, Umma bataje wajen aiki ba, ta taya Ablah haɗa kayayyakin ta, sanda ta tabbatar sun haɗa dukkan abinda zata buƙata Ita dai Ablah jikinta duk da sanyi haka kawai take jin bata son tafiyar, haka ta wuni sukuku jikin ba daɗi, ko da azhar kamar yadda Inna Jumma ta umurci Faruq haka akayi ƙarfe biyu bayan sun idar da Sallar azhar, daga Companyn ya taho unguwar Durmi a ƙofar gidan nasu yayi parking yaro ya samu ya aika yace yaje yace wai Faruq yazo, babu jumawa kuwa Umma suka fito da Ablah tare da akwatin ta, Abdu sai kuka yake baya son rabuwa da ƴar uwarsa Faruq cikin girmamawa ya gaishe da Umma, tare da karɓar kayan Ablah yasa amota, ɗan murmushi Ya saki tare da cewa Abdu.
"Abokina, kana kukan rabuwa da Aunty ko?"
Kansa Abdu ya ɗaga idanunsa cike da hawaye, sunkuyawa Faruq yayi a gabansa tare da cewa.
"Share hawayen ka daina kuka Aunty tana nan ba nisa zatayi ba, zan dinga zuwa na ɗauke ka, ina kaika wajenta kaji, ka daina kuka ka yiwa Aunty fatan alheri, ko so kake itama Aunty tayi kuka."
Still kansa Abdu ya girgiza alamun a'a yace.
"Ni dai bana son Aunty na tayi kuka, Aunty tace min zata saya min keke ina zuwa makaranta idan ta samu kuɗi, kuma itace take bani kuɗin break kullum, nima idan nayi kuɗi zan sayawa Aunty mota irin taka nan fara mai kyau, to kuma shine yanzu Aunty zata tafi ta barni."
Murmushi Faruq ya saki hanunsa ya riƙe tare da miƙewa mota ya buɗe ya ɗauko kuɗi, dubu arba'in ya danƙawa Abdu a hanunsa tare da cewa.
"To ga kuɗin keken naka, ka bawa Umma ta saya maka ko, sannan Aunty ma zatana zuwa."
Cike da farin ciki, Abdu ya rungume ƙafar Faruq, Umma murmushi tayi domin kuwa Faruq ya birgeta Sosai tana son mutum mai ƙaunar yara, motar sa ya shiga yana ɗagawa Abdu hanu, Ablah Umma ta rungume idanunta na cikowa da hawaye tace.
"Umma zan tafi ki cigaba da min addu'a, ki kuma yafe min idan akwai laifin dana miki."
Hawayen da Umma ke ɓoyewa ne suka gangaro, Faruq cike da ƙaunar familyn yake hangosu ta cikin motar basu dashi amma suna da wadatar zuci da ƙaunar junansu, Umma cewa tayi.
"Na yafe miki Ablah babu abinda kika min, Allah ya rabaki da sharrin Mutum da aljan Allah ya zamo gatanki a duk inda kika tsinci kanki."
Sake Umma tayi ta kama hanun Abdu.
"Zan tafi Abdu, zan dinga zuwa ina dubaka, karkayi wasa da karatunka kaji, ka kula."
Kansa ya ɗaga, Ablah ta juya ta shiga motar, tana ɗagawa su Umma hanu, idanunta na hawaye har ta daina ganinsu, sunyi nisa da tafiya ita da Faruq babu wanda ya yiwa wani Magana.
Sunyi nisa da tafiya Faruq yace.
"Ablah baki son tafiya ko?"
Ɗago daradaran idanunta tayi tare da kallon Faruq, hawayen ta ta goge tare da girgiza masa kai alamun a'a.
"To meyasa kike kuka, tunda naga ai ba nisa kukayi ba, ina nan ina *AMBASSADOR AHMAD GIWA ESTATE* "
Still dai shuru tayi bata tanka masa ba, murmushi Faruq yayi tare da cigaba da dreving ɗinsa har suka iso first get ɗin Estate ɗin idanunta ta ɗaga jin Faruq na danna hon hon, ta kalli get, *AMBASSADOR AHMAD GIWA FAMILY ESTATE* taga an rubuta da manyan baƙi wani irin tsinkewa taji zuciyarta tayi, idanunta ta runtse tare da ambaton LA'ILAHAILLAH ANTA SUBAHANAKA INNI KUNTU MINAZZALUMIN, har aka buɗe get ɗin suka shiga bata bar furta wannan kalmar ba domin kuwa har yanzu zuciyarta bata daina tsinkewa ba, ji take tamkar zata haɗu da mungun Abu a cikin gidan, jin yanda ƙirjinta ke bugawa sai taji tamkar tace Faruq ya mai data gida, da kallo take bin Estate ɗin, gidane na kerewa sa'a gidan masu kuɗin ma irin wanda suka kai suka kawo manyan masu kuɗi, haka ta yiwa gidan kallo, komai a tsare yake ga wasu shimfiɗaɗɗun fulawowi, numfashi ta saki, get ɗin da zai sadaka da part ɗin su Al'ameen Faruq ya nufa nanma sanda ya danna hon sannan aka buɗe musu gadin get ɗin farko security ke gadi amma taga wannan kuma ba security bane, sai dai duk tsaruwar da taga can ya mata, sai kuma taga inda suka shigo yanzu yafi kyau nesa ba kusa ba, a parking space yayi parking tare da buɗe motar ya fito ya zaga itama ya buɗe mata, fitowa tayi a nutse tana bin part ɗin da kallo, mai bawa flowers ruwa Faruq ya kira tare da basa kayan Ablah yace ya kai wajen Inna Jumma, sannan ya cewa Ablah muje, gaba yayi ta bisa a baya cikin babban falon suka shiga babu kowa kasancewar su Maimu da Afnan suna school, ihsan kuma ta dawo tana bedroom ɗin Ummi Aunty Amarya da Ummi kuma duk suna bedroom ɗinsu, duk da kayan more rayuwa da ƙawatuwa da falon yayi baisa Ablah ta masa kallon ƙauyanci ba, bedroom ɗin Inna Jumma suka shiga har yanzu tana kan darduma tana lazimi, Faruq sanin cewa muddun Inna Jumma tana laziminta ba magana takeyi ba, ya sashi juyawa tare da cewa Ablah shiya koma office.
A hankali ta furta.
"A dawo lafiya Allah ya tsare."
Murmushi Faruq yayi ya amsa da ameen yana ficewa, Inna Jumma ta kai wajen miti talatin tana lazimi, kafin ta idar tare da murmushi tana kallon Ablah.
"Shalelena har kun iso, sannu da zuwa, ina miki barka da shigowa cikin mu."
Murmushi Ablah tayi tare da zamewa har ƙasa ta gaishe da Inna Jumma, ta amsa cike da sakin fuskar jin Ablah take tamkar jininta numfashi ta saki tace.
"Jirani Ablah bara na watsa ruwa na fito ko."
To Ablah tace Inna Jumma ta shige tollet koda ta fito sosai ta dinga jan Ablah da hira har ta ɗan saki jiki kaɗan, ƙarfe Uku dai-dai falon ya fara cika da mutanen gidan, kasancewar duk wanda suka tafi school sun dawo, khalipa shima yana kwance a doguwar kujera, Ashfat ma tana gefen sa, sai Maimu dake zaune ita da ihsan tana mata assignment, dama ita Afnan Uwar baƙin hali bata cika zama cikin mutane ba, tana can bedroom ɗinsu, Aunty Amarya da Ummi suma suna zaune suna taɗi, kasancewar yau Ladiyo ce take girki, Inna Jumma ce ta fito tare da ABLAH, Ashfat kallon sani ta yiwa Ablah domin kuwa bazata manta da ranar da Al'ameen ya wurgota a asibiti ba, Aunty Amarya ma da kallon mamaki tabi Ablah, Maimu idanunta ta ɗago ta kalli Ablah tare da Inna Jumma, tana bin Ablah da kallon rashin sani, khalipa ne ya kasa hkr yace.
"Ke tsohuwar nan a ina kuma ki ka sato Wannan kyakkyawar halittar."?
Yayi Maganar yana nuna Ablah da yatsa.
"A gidan ubanka"
Inna Jumma ta basa amsa tana jawo hanun Ablah, Maimu dariya tasa tare da ijiye pencil ɗin dake hanunta tana duban Ablah tace.
"Ke dai tsohuwar nan ba'a rabaki da rikici koma daga ina kika satota idan tayi tsami zamuji."
Harara Inna Jumma ta jefawa Maimu tare da cewa.
"Bani da lokacinki, ina wannan shegiyar kura Uwar baƙin halin."?
Sanin da wanda Inna Jumma take yasa Khalifa sheƙewa da dariya ya mata nuni da sama, taɓe bakinta Inna Jumma tayi tana zama cikin ɗaya daga cikin kujerun falon, Ablah cike da girmamawa ta ƙarisa wajen su Ummi da Aunty Amarya, sunkuyawa tayi har ƙasa a hankali ta furta.
"Sannunku da hutawa, ina wuni."
Tayi Maganar cikin tsoro domin kuwa haka kawai take jin gidan bai mata ba, murmushi Ummi tayi tare da dafa kanta ta amsa da.
"Lafiya lau ƴata, sannu da zuwa."
Kallon Maimu tayi tare da ce mata.
"Maimu jeki nemo mata abinda zataci."
Murmushi Maimu ta saki tana miƙewa ta nufi kitchen, Aunty Amarya kuwa randa a haɗe ta amsawa Ablah gaisuwar ta, domin kuwa tun haɗuwar da tayi da ita a asibiti taji sam bata yarda da Yarinyar ba, asali ma ta tsaneta, Ablah miƙewa tayi tare da komawa gefen Inna Jumma zata zauna a ƙasa Inna Jumma ta hanata tare da mata nuni da ta zauna a kujera gefenta, cikin ɗari ɗari ta zauna.
"Kai Usmanu, maza jeka ka cewa ubanka yazo ina kiransa."
"Oh Inna Jumma waike a rayuwarki kowa sai kin ɓata masa sunane, wai Usmanu sunan ko daɗin ji babu, idan bazaki ce Khalifa ba, sai ki barni a Usman ɗin bai sai kin wani saka *Nu* a gaba ba, shi kuwa wanda kike kiran baya nan ya fita da BARRISTER IBRAHIM suna da meeting."
"Okay Allah ya dawo dashi lafiya sannan nace Usmanun dashi ai ubanka ya yanka maka suna ko.?"
Murmushi Khalifa yayi tare da miƙewa yana haurawa sama yace.
" Sai kuma kiyi."
Maimu ce ta fito hanunta riƙe da plat ɗin soyayyiyar doya fara tare da ƙwai sama ta haura ta ijiye sannan ta dawo, kusa da Ablah tazo tace mata.
"Sister kizo muje bedroom ɗin mu kici abinci."
Kanta Ablah ta girgiza a hankali tace.
"Ya isheni naci abinci a gida kafin na taho."
Ummi ce tace.
"Ki tashi kije kici mana, ai na rana kika ci yanzu Kuma yamma ne."
"Allah bana jin yunwa ya isheni."
Aunty Amarya ce ta taɓe bakinta tare da cewa Maimu.
"Tace ya isheta sai ki ƙyaleta ba'a dole ai."
Kanta Maimu ta kaɗa tare da komawa ta ƙyale Ablah, Hajiya Mansura ce ta shigo gidan da sallama, Ummi ne ta amsa fuskarta cike da murmushi ƙarasowa tayi ya sunkuya gaban Inna Jumma tamkar mutumiyar arziki.
"Barka Inna."
Murmushi Inna Jumma tayi tare da amsawa Hajiya Mansura.
"Mansura kece tafe, kwana biyu shuru baki ziyartan mu, ni yaushe ne, Abbati yazo shi nake ce masa na sama masa bazawara, kinga shi matar sa ta mutu kema mijinki ya rasu, shi kenan sai ku rufawa juna asiri."
Dariya Hajiya Mansura tayi tare da cewa.
"Inna ina ni ina Alhaji Abba, ai yafi ƙarfi na, amma dai zanzo mu saka labule."
"To shikenan, ina jiranki."
Zama Hajiya Mansura tayi gefen Ummi tace.
"Ina wuni Hajiya Gaji ya jikin Ashfat."
"Jiki alhamdulillah! Gata nan jiki yayi sauƙi next week ma ina ga zasu koma Egypt akwai likitan da Daddyn su yayi magana dashi, za'aje ya duba ƙafar idan da yiwuwar za'a saka mata wata ƙafar wacce ake amfani da ita ga wanda ya rasa ƙafarsa."
"Masha Allah, zamani kenan da dai idan ka rasa ƙafa shikenan ka rasa, amma yanzu na'ura tazo da abubuwa iri iri to Allah yasa a dace, sannu kinji Ashfat kin gamu da ƙaddara kema rayuwa kenan kana tafiya akan ƙaddarar ka baka sani ba, Allah dai yasa mu dace muyi kyakkyawar ƙarshe."
Da ameen Ummi ta amsa Aunty Amarya miƙewa tayi tace.
"Mu ƙarisa ciki Hajiya Mansura."
Tashi tayi suka haura bedroom ɗinta, Ablah jin ta takura a falon ya sata tashi ta shige bedroom ɗin Inna Jumma.


Numfashi Aunty Amarya ta saki tana kallon Hajiya Mansura tace.
"Ƙawata kwana biyu na jiki shuru babu wani labari, ni fa na fara gajiya da tura mota Wallahi."
"Haba Amarya gajiya fa kike kira, hmmm! Ai bari kiji ba'a taɓa gajiyawa ga naiman cikar buri, kinga yanzu ne ma fa zamu saka ɗanban neman Nasara, yanzu ma aka fara wasa farin girki, karki manta ɗaya kawai muka samu muka rage nan gaba akwai sauran huɗu da muke neman rayuwarsu."
"Hajiya Mansura, yanzu fa kina ji take sanar dake Monday zasu koma Egypt, sai yaushe kenan zamu ta jiransu, ni fa burina idan na gama dasu shima Uban nasu na dawo kansa, amma abubuwa a wannan karon sun gagara."
"Babu abubuwan da suka gagara, su tafi mana so what, kinga ba dole sai akansu zamuyi aiki ba, karki manta a yanzu kina tare da Uku, Al'ameen Maimu da kuma Uwar tasu, domin kuwa idan ta gagara sai mu turata lahira a madadin ƴaƴanta biyu, dan haka daina damuwa, wannan karon bada Isa Alolo zamuyi aiki ba, da guba zamuyi aiki."
"Da guba! Taya zamuyi amfani da guba a wannan gidan sannan waye za'a fara sawa gubar.?"
"Tambaya mai kyau, *AL'AMEEN* shi zamu fara sakawa domin kuwa gani nake kamar shine matsalar mu, idan mun aikasa sauran aikin zaizo mana da sauƙi dan haka ki ijiye girki a cikin gidan nan ki barwa ƴan aiki domin gujewa zargi, kisan yadda zakiyi kice kin daina girki dole ki ƙirƙiri wata matsalar da zata sakaki ijiye girki"





Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi Naira ɗari biyu kacal 200 guda biyu ne daga aminai biyu Wato ƙawalli da ƙawalliya.

ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN.

acikin littafinta mai taken *AHLAN*

RASHEEDAT USMAN UMMU NASMAH.

Acikin littafinta mai taken *AMINAINA KO ITA?*


Guda ɗaya zaki samu ne akan farashi Naira 200 idan kuma duka biyun kike so zaki biya Naira 300.

Turo da kuɗin ki ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank.

Ko kuma ku turo hoton katin waya na Mtn card ta ɗaya daga cikin waɗannan numbobin.
08147537180
Ko
08165550116


Please banda VTU hoton katin zaki ɗauka ki turo.


Sannan sai ku turo screen SHORT SHAIDAR BIYA ta cikin waɗannan numbobin.

Kuyi hanzarin biya domin kuwa littattafan sunzo ne da zafin su, zasu bada citta karku sake a barku a baya koda kuɗin ku sai da rabonku.



Please Share and comments.



*Ummu Nasmah ce ✍🏻
[6/30, 8:52 PM] UMMU NASMAH🥰: 💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅



🤦🏻‍♂️🤦🏻‍♂️🤦🏻‍♂️



💔 *AMINAINA KO ITA?* 💔


🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️



🙆🏻‍♀️ *(BETRAYED LOVE!)* 🙆🏻‍♀️



*NA*


*RASHEEDAT USMAN*

*(UMMU NASMAH)*




Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.



*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*





*Free page 15*



"Na fahimta amma Hajiya Mansura kina ganin babu wata matsalar da za'a samu idan sukaci gubar bana son bincike ya biyo kaina ne ko zargi."
"Ta yaya bincike zai biyo kanki, haba Amarya wai kin manta yardar dake tsakanin kune, wallahi ko kusa bazasu taɓa tunanin zarginki ba, domin kuwa sunyi imani da cewa bazaki taɓa bari wani ya cucesu ba bare kuma ke, zargin su zai ƙare ne kawai iya kan ƴan aiki, wanda mu kuma bamu da matsala da hakan muddun burin mu ya cika."
"Hakane nasan bazasu zargeni ba, amma dole tsoro da waswasi zai shiga zuciyar kowa daga nan zasu ankara su fara saka idanu akan lamuran gidan, kinga kuwa hakan zaisa su fara ƙoƙarin gano Ni, wanda ni kuma bana buƙatar su san asalin koni wacece nafi so mu rabu da kowa a cikin su yana min kallon ta kirki."
"Hmmm amarya kenan farar kura uwar tsoro, ba dai kin yadda da ni ba, haka kuma ban taɓa baki kunya ba."
Ɗaga kanta Aunty Amarya tayi alamun eh, murmushi Hajiya Mansura tayi tare da cewa.
"Good to ki amince da wannan ma, domin kuwa zata miki kyau."
Murmushi Aunty Amarya tayi tare da ɗago hanunta suka tafa da Hajiya Mansura, amarya cewa tayi.
"Na yarda dake ƙawata kuma na amince da shawararki."
"Ko ke fa, abu ne zamuyi shi na nutsuwa da taka tsantsan, yanzu dai ki bari a kwana biyu kafin mu fara aikin, amm jiya Goggo Hali ta kirani wai ta kira layinki baya tafiya, kuɗi take so 30k wai Zainab ta haihu zatayi mata kayan fitar suna, abinda ma ya kawo ni kenan yanzu."
"Okay ba damuwa zan karɓi account numbern Zainab ɗin zan tura mata, nima ina so insha Allah zanje na mata barka."
"Eh to ya kamata kam gaskiya, ni kinga bara naje yanzu ma haka zanje gidan Hajiya mariya ne zamu fita."
Tayi Maganar tana miƙewa tare suka fito da Aunty Amarya, Inna Jumma bata nan ta shige bedroom ɗinta sai Ummi da Ashfat kawai ke zaune, Hajiya Mansura cewa Ummi tayi.
"Hajiya gaji bara na gudu, ina Inna, mu ƙarisa zancen Inna tana son nayi Aure bata san kuma Alhaji Abba yafi ƙarfi na ba."
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
"Mace ai bata fin ƙarfin NAMIJI Hajiya Mansura, ke dai sai dai idan baki sonsa, amma dai kika faɗawa Inna haka zaki sha faɗa."
"Ai kuwa tunda bata kusa guduwa zan idan na tafi na kira ta anjuma nace tayi hkr na manta."
Tayi Maganar tana shigewa da sauri cikin dariya, murmushi Ummi tayi Aunty Amarya tabi bayan ta.


Yau tun fitar Al'ameen daga gidan tun safe bai samu ya dawo ba sai 8:30 na dare kasancewar aiki daya masa yawa a Office, koda ya dawo bedroom ɗinsa ya shige a gajiye tollet ya shige tare da sakewa kansa ruwan ɗumi ya juma sosai tsaye ruwan yana ratsa jikinsa kafin yayi wankan ya fito ɗaure da towel tsabar gajiyar da ta damesa, body spray kawai ya fesawa jikinsa tare da sanya wando boxer da tshed ya faɗa saman makeken gadonsa yana lumshe idanunsa, wani irin ganda ne yake jin yana ratsa gaɓoɓin jikinsa, shuru yayi tare da lumshe idanunsa, can ya jawo wayarsa numbern Afnan ya kira tana ɗagawa yace ta kawo masa lipton, ya katse kiran, babu jumawa kuwa sai ga Afnan da lipton ɗin, ta ijiye masa a table ɗin dake gefen bed ɗin kwalin sugar ta ɗauko ta jefa masa guda biyu kasancewar tasan yadda yake so.
"Ga lipton ɗin Ya Al'ameen."
Kansa ya ɗaga mata alamun to ba tare daya mata Magana ba, ta fice abinta, tashi yayi ya ɗauki lipton yana sha a hankali.
Inna Jumma da Ablah kuwa har sun ɗan saba tun da sukayi sallar isha'i suke fira, sai tara Inna Jumma ta fita falo, Aunty Amarya bata nan tana bedroom ɗin Daddy kasancewar itace take dashi, Ummi da Maimu ne sai ihsan kawai suke zaune, duban ihsan Inna Jumma tayi tare da cewa.
"Ke ihsan jeki cewa Daddyn ku ina kiransa maza."
Tashi ihsan tayi ta haura sama da gudu, duban Ummi tayi tare da cewa.
"Idan ya fito ina ɗakina kuzo dukkan ku har amarya da yaran naku ku sameni."
"To shikenan Inna"
Ummi ya amsa Inna Jumma ta koma room ɗin nata, haka kuwa akayi Daddy jin kiran mahaifiyarsa ya sashi tashi cikin gaggawa ya nufi bedroom Inna Jumma, ya taradda ita a falon ta, suna zaune a tsakiyar kafet ita da Ablah, gefe Daddy ya samu ya zauna tare da cewa.
"Barka da hutawa Inna."
"Yawwa barka Amadu, ina iyalan naka da nace kuzo tare.?"
"Suna zuwa yanzu insha Allah."
Ablah ce ta rusuna kanta tare da cewa Daddy.
"Ina wuni."
Murmushi Daddy yayi tare da amsawa da.
"Lafiya Alhamdulillah! Yarinya."
Ya amsa mata yana kallon ta cike da yabawa da tarbiyyar Yarinyar, su Ummi ne suka shigo tare da Aunty Amarya da su Maimu har Khalipa da Afnan, zama sukayi gefen iyayen su, Inna Jumma ne tayi gyaran murya tare da cewa Daddy.
"Amadu ga yarinya na ɗaukota daga gidan iyayen ta, Saboda yabawa da nayi da tarbiyyar ta, zata dinga mana ƙaramin aiki, zan haɗata da Ladiyo sai su dinga girki tare, ko kuma su dinga shiften ɗin girkin na kuma yanke shawarar cewa zaka dinga biyanta 50k a wata."
Numfashi Daddy ya saki tare da cewa Inna Jumma.
"Inna duk abinda kika yanke a cikin gidan nan bani da ja dashi, ba damuwa Allah ya bamu ikon riƙeta."
Da ameen Inna Jumma ta amsa tana saka masa albarka kafin ta maida dubanta gasu Ummi tace.
"Gaji ke da Amarya kun daiji abinda nace duk da bani da shakku daku, sai dai ke Afnan kece zanyiwa karariya domin kuwa kece baki da mutunci, kin dai ga wannan Yarinyar Magana ma bata dameta ba, to wallahi karki kuskura kice zaki sakata a gaba a cikin gidan idan kika sata a gaba to wallahi nima zan saki a gaba, domin kuwa zan iya ɓatawa da kowa a cikin gidan nan akan wannan baiwar Allah, ina shima babban shegen yake Aminu na masa kashedi domin kuwa nasan dashi zamu samu matsala."
Tura bakinta Afnan tayi tare da cewa Inna Jumma.
"Harkar waye kikaga ina shiga a cikin gidan da zaki zageni, ko ƴan uwana Kinga ina shiga harkar su ne bare kuma wata can ƴar aiki."
Tayi Maganar tana miƙewa tabar wajen, Ummi murmushi tayi kasancewar dama tasan Afnan da Inna Jumma sun saba tace.
"Al'ameen yana bedroom ɗinsa da alamu baya jin daɗi ne maybe shiyasa bai fito ba, dan ko abinci bai ciba."
"Zai fito ne ya sameni dan wallahi dole na masa gargaɗi, sannan Aminu wancan bedroom ɗin na gefen nawa anan wannan Yarinyar zata zauna bazata boss cutter ba."
"Nifa Inna duk abinda kikace dai-dai ne bani da ja akai."
"Okay shikenan zaka iya tafiya, kuma zaku iya naku tafiyar dama abinda yasa na tara ku kenan."
Ummi da Aunty Amarya da take jefawa Ablah mungun kallo ne suka tashi tare da ficewa, Daddy da ihsan ne suka tsaya, Daddy ya ɗan juma tare da Inna Jumma suna hira har kusan goma sannan ya tafi, a ranar tare Inna Jumma suka kwana da Ablah a room ɗinta da niyyar da safe sai a sharewa Ablah nata room ɗin ta koma.

Washegari da sassafe Aunty Amarya ta shigo room ɗin Inna Jumma,bata nan tana tollet sai Ablah dake zaune tana karatun Alkur'ani, taɓe bakinta Aunty Amarya tayi tare da cewa.
"Keee!"
Ɗago kanta Ablah tayi ta kalli Aunty Amarya cikin girmamawa tace.
"Ina kwana Aunty."
Aunty Amarya bata amsa gaisuwar ta ba, tace.
"Zaman me kike har yanzu baki fito kin fara aikin ki, ba, ko kin manta da aikin aka kawo ki, to

Please Login or Register in order to submit comment