Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, zuciya ta ba zata tabba samun natsuwa ba." ta ida maganar tana fadawa jikin Momy tana goge hawaye.



Dago da kanta Momy tayi tana share mata hawaye sannan tace ." nayi maki alkwarin daga yau ba zaki sake kuka ba akan so Jameel ,Dota keda shi duk daya kuke a wajena,karki manta da mamanki da ni uwarmu daya ubanmu daya ,mu biyu ne kawae mahaifiyarmu ta haifa a duniya farincikinki shine nawa bakincikinki shine nawa,dan haka yau dinnan Dad dinku na dawowa zan sake yi mashi maganar aurenku next two week sae ayi auren, saboda karda asa next week ba kowa zai samu damar zuwa ba amman idan akasa next two week kinga anfita hakkin kowa." murmushi tayi sannan tayi ma Momy pick a kumatu tana cewa. "Thank you Momy Ilove you with all my heart bloody." tana gama fadin haka ta sauka bisa cinyar Momy ta haye sama ranta fas, dan har ta manta da abunda J yayi mata wani dadi da annashuwa take ji na ratse ko wani shasha da lungu na jikinta .


Ita kuwa Hudah sae da ta gama kukanta ta godema Allah sannan ta goge fuskarta ta cigaba da duk abunda ya dace haka, sannu a hankali ta samu ta gama duk abunda aka bukata sannan ta jera a dinning ta gyara ko ina ranar ko daukar abincin da take daukar masu batayi ba, dan ji tayi bata jin dadin komae koda ta koma room dinsu taba taida Hafsat ba wanka kawae tayi ta sake kaya ta kwanta da yake tana fashin sallah tana kwanciya ta kama salati har bacci yayi awon gaba da ita.



&&& &&&


Tunda suka fito cikin gida ,yaki yaba Amal fuskar da har zatayi mashi wata magana, dan fuskarnan a murtuke take ba wani sausauci a cikinta ba drive ba haddata ita Amal a tsorace take dashi dan tunda take a duniya bata taba ganin rain Yaya J ya baci ba har haka ,ya zama tamkar zaki ko kallonshi bata son yi, ji take kamar ta kurma ihu ita da yazo da ita gwara yayi mata shegen duka ya rabu da ita tayi jinya haka take ji .



"Duk park din da kaga, yayi maka kaimu can." abunda sukeji yace kenan da sauri Amal ta waiga tana kallonsa ,amman bataga alamun yayi magana ba ,salati ta kamayi tana gaya ma Allah ,Allah yasa karda yayi mata fada dan da yayi mata fada gwara yayi mata shegen duka,haka take ji parking din motar da taji anyi yasa Amal ta godema Allah tana saurin bude motar ta fita da sauri ya kamo hannunta ya riketa ba tare da ko ya kalli inda take ba,hawaye suka fara zubo mata a fuska dan sosae take tsorace da yayan nata,sae da suka shafe minti goma a cikin mota sannan ya sakar mata hannu ,aikuwa yana sakar mata tana bude marfin mota ta fita sauke ajiyar zuciya tayi tana goge hawayen fuskarta,duk da yana cikin bacin rai amman ta bashi dariya ,dan ya lura da yanayin tsoran da take ciki girgiza kai kawae yayi shima ya ida fitowa tare suka jera duk suka shiga ciki,samun waje sukayi suka zauna icecream da turkey tea aka kawo masu da lemu mai sanyi.


Tura mata lemun yayi shi kuma ya dauki tea din ya dan kurbe kadan ya ajiye dan baya son shan komae ,sosae yakejin zuciyarshi nayin zafi kamar ana watsa mashi narnarkar darma haka yake ji,lumshe ido yayi yana dafe zuciyarshi gami da taune lebeshi na kasa har sae da Amal taji karar taunar da yayi, da sauri ta runtse idonta tana budewa a kanshi tana kallon yanda yake shafa zuciya gashi ya tauna bakinshi ko zafin bai damaishi ji tayi kas!dasauri ta maida kallonta wajen hannunshi jini taga yana zuba dan glass cup din gabanshi na tea ya matse a hannu da sauri ta tashi zataje wajenshi Waga mata hannu yayi, yana sauke mata jaijajen idanuwanshi dan sun tashi daga farare sun koma jaijaye kamar jini sun kwanta rufe bude bakinta tayi dasauri zatayi magana.

"shhhhh."

yace mata yana daura dayan hannun a lebenshi Murmushi yayi sanann ya nuna mata seat babu masu ta koma ta zauna bude baki yayi ya fara ce mata...


>ØúÝ=Ø%Ý>ØúÝ=Ø%Ý>ØúÝ=Ø%Ý>ØúÝ=Ø%Ý>ØúÝ=Ø%Ý>ØúÝ=Ø%Ý>ØúÝ=Ø%Ý


*HEHEHE KARO DA KARO SAI RAGO DAN AKUYA BA ZA YA IYA BA*=؃Ü<Øûß=؃Ü<Øûß=؃Ü<Øûß

*_MAMAN YUSUF YAR SOKOTO DAYA DAGA CIKIN K'UNGIYAR SHAHARARRUN MASU KAYAN MATA 'YAN SOKOTO, 08133079957 OR 07069711327 CALL OR WHATSAPP_*

_ina kuke mutanena Yan sokoto dama sauran garuruwan da suke kewaye damu ,Kai har ma da na k'asashen k'etare ,Albishirinku . Ni ce dai shahararra Kuma gogaggiyar Mai Saida zafafan kayan matan Nan masu Sanya namiji ladabin Dole wato maman yusuf likitar Mata Yar mutan sokoto ,Kamar yadda aka Saba dai duk shekara to alhamdulillah wannan karon ma nazo maku da zafafa Kuma k'asaitattun kayan Mata masu kyau da inganci domin farincinku kawai_=؃Ü<Øûß=؃Ü<Øûß=؃Ü<Øûß=Ø%Ý=Ø%Ý

_Akwai discount ga duk abunda zaku siya , ma'ana an sauke farashi daga wannan lokacin har zuwa sallah da sati d'aya , bonunza ce darajar wannan watan da muke ciki karku sake ta wuce ku_

_ina Amaren mu na bana Kuma ba'a barku a Baya ba nayi maku shiri na musamman ,da kalolin kayan da Zaki kankarowa kanki daraja a wajan Mai gida,_
_akwai sahihi Kuma ingantaccen maganin sanyi_
_Maganin gyaran nono Mai kyau da inganci_
_Maganin tado da hips da duwawu komai kankantarsu da shafewarsu shape dinki yy kyau kema ki shiga jerin Mata masu aji_
_Maganin rage k'iba da tumbi_
_zumar kiba da garin kiba Masu ciko da rama cikin kankanin lokaci don Sam Rama batayi ba Yar uwa_

_Gefe d'aya zafafan kayan gyaran HQ kala kala Wanda zasu ciko ki su matseki Gam sannan subaki ni'ima da dandano irin wanda akeso ,hmmm kedai ziyarci maman yusuf sokoto Dake marna Police station ko Kuma ta numbar wayarta Kamar Haka 08133079957 ko Kuma 07069711327 don bambance tsakanin Aya da tsakuwa , zamu aika maki da kayanmu a duk inda kike acikin fadin Nigeria da Niger harma da wasu k'asashen , cikin aminci da yardar Allah ,karku manta a Dade anayi sai gaskiya_=؃Ü<Øûß=؃Ü<Øûß=؃Ü<Øûß=Ø¥Ü=Ø¥Ü

_Hmmmmm in Ana Dara fidda uwa ake ,har Ila yau darajar wannan watan min fito maku da wani mashahurin set Wanda Zaki samu kalolin Kaya aciki masu dauke da sirrikan mallaka , gefe daya ga hatsabibin turaren mallaka ,Wanda ba namijin da zai jishi hankalinshi Bai tashi ba duk acikin wannan set namu Mai suna *MUJALLAB* wannan mashahurin set a waje biyu kawai kike da damar samunshi , Zaki iya samunshi a wajena anan sokoto kenan ko Kuma a jahar Kano wajan Mom fu'ad wadda aka fi sani da gidan k'amshi, Wanda Zaki iya nemanmu ta wannan Numbers_
=ØGÜ<Øûß=ØGÜ<Øûß=ØGÜ<Øûß=ØGÜ<Øûß
08133079957 mmn Yusuf sokoto (likitar Mata)

08132506044 Mom Fu'ad Kano (gidan k'amshi)

Zaku same MUJALLAB a farashi Mai sauk'i>ØpÝ>ØpÝ>ØpÝ>ØpÝ

_Amare zawarawa tanadinku daban ne na shirya tsab domin Yi maku hadin *sabon budurci* Wanda Zaki ciko ciki da waje ku hade Gam Gam kamar baku taba sanin wani d'a namiji ba domin kankarowa kanki mutunci da daraja a wajan oga_

_Hakama amarenmu Wanda suka samu matsalar rashin budurci sanadiyar fyade ko yaudarar d'a namiji ,naku na musamman ne ,Hadi ne da in akayi makishi da izinin Allah sai kinzo kinamun godiya , kedai nemeni ta pc don samun cikakken bayani akan hakan_

*Idan fa nace Zan zayyano maku ire iren kayan da muke dasu to fa wannnan page din bazai ishemu ba ga Maison ganin kalolin kayana yayi sarving number ta yayimun magana nayi nashi zaku dinga ganin kalolin kayana a status ngd*>ØpÝ>ØpÝ>ØpÝ>ØpÝ>ØpÝ

*Pls in ba serious kike ba don Allah ki Bari sai kin shirya siya sai muyi magana azumi ne yanzu banason mu batawa juna lokaci*=Ø
Þ=Ø
Þ=Ø
Þ

08133079957
07069711327
Mmn Yusuf likitar Mata


*œ&þ BUŠARŠIYAR SOYAYYAœ&þ*
```the naked love```


Jameey Yar'mutan kankia


*Sdeendtm*
I'm sell data to all Nigeria network

Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I'm
selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp 08066268951


_Akwai ingantaccan maganin<Ø4ß<Ø4ß gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._



_Litaffi na kudi ne sau Waya rana #300,sau biyu a rana #500 sau ukku a rana #700 sau Hudu a rana #1000 zaki turo ta wannan Account number din 0777512438 Jamila Abubakar Bello Access Bank, ko kuma katin Mtn ko airtel ta wannan numbers din_ 08160508316 07034464517.

*Note:- please yan special person da masu Vips pls banson vtu=ØOÞ*


(3E 'DDG 'D1-EF 'D1 -JE



Last free page



<Ø“Ý<ØÝþ2þã 9þã ”!þ3þã 0þã



"Amal." ya kira sunanta yana mai kara kureta da kallo,dukar da kanta kasa tayi tana ansawa,girgiza kai yayi yana cewa. "Dago da kanki ki kalleni sosae magana nike son yi dake bani son ki bata man lokaci dan inada abunda zanyi." dagowa tayi tana kallonshi cikin kirma tace. "to Yaya J." Murmushin gefen baki yayi yana cewa. "Good girl,tambayar zanyi kuma inason komae na tambayeki kibani ansa kuma gaskiya idan kika kuskura kikayi man karya LilSis bansan hukuncin da zan yake maki ba,dan haka ki natsu some question kawae zanyi maki bansan shirme Ok." daga mashi kai kawae tayi tana kallonshi kara lumshe ido yayi yana mai kara dafe zuciyarshi da ta fara rage yi mashi zafi ,dan ba kamar dazun ba kamar bansan magana dan bai cika yawan magana ba ,amman ta zama dole bude baki yayi yana cewa.


"Maiyasa kike biyema Anisha kuna shirmen banzan shirmen wofi Amal."? Girgiza kai tayi tana cewa. "Yaya J ba biye mata nike ba,kawae dai tana sonka bata iya control akan sonka Yaya J Anisha abun tausayi ce wallahi, dan tana bala'in sonka idan kaga yanda take sonka take kaunarka sae ka tausaya mata ka yarda da soyayyarta Yaya J maiye aibun Anisha da kake mata haka."?


Murmushi yayi yana kallon Amal tabbas ta fadi gaskiya daman nan yake son azo a maganar, shiyasa yayi summaring dinta yanda zasu gama maganar da wuri hannunshi mai ciwo ya kalla sannan ya kalli Amal yace ." hakane tana sona ,son yayi nisa da har ta kasa control dinshi ko"? Daga mata shi kai kawae tayi tana mai shan ice cream din gabanta cigaba da cewa yayi. " Ada bansan zafin so ba kuma bansan maiye so ba,masu yinshi mamaki suke bani dan gani nike suna wasting time dinsu a banza and yanzun nasan zafin so nasan ya akeji a so,kinsan dalilin da yasa na fasa cup din nan?and kinsan dalilin da yasa nike dafa zuciya ta."?

Gyara zamanta tayi tana kallonshi tace. "Aa Yaya J,amman inason sani dalilin da yasa duk kayi haka ,dan nayi mamaki kuma na tsorata sosae da sosae." ......"Amal duk kan sone,idan tana kuka zanji zuciyata tana zafi ,zanji zuciyata ta shiga kunci bata cikin walwala Amal koda kuwa bani kusa da ita tayi kuka sae nashiga cikin yanayin da na gaya maki ,Amal idan nayi hour banji muryarta ba to wallahi zanji duk ban lafiya ,idan kuwa ban ganta ba to zan shiga halin da ba zan iya musulta maki shi ba ,Amal duk mai ya kawo man haka inason ki bani ansa."?


"So,Yaya J Sone yaja haka,amman wacece wanann haka kakema wannan son Yaya J ? zan iya gaya maka tunda nike a rayuwata ban taba jin irin wanann son ba na kalli finafinai kala kala na karanta novels both english and hausa ban karanta irin wannan soyayyarba sae yau a wajenka."


Sauke hannunshi yayi daga zuciyarshi sanann yace. "Haka abun yake *SO NUFIN ALLAH NE* na yarda da Anisha tana sona ,amman nima ayi man adalci a tausaya ma zuciyata abar sata cikin halin zafi da kunci mana Amal ,amman kullum sae ansa man zuciya cikin kunci da radadi why Amal."?


Ya ida magana yana kafeta da ido yana sauraron Ansarta ruwan sanyi ta tura mashi alamun yasha kauda kai gefe yayi,yana goge hawayen fuskarshi dan baisan Amal taga hawayenshi akan mace dan bata taba ganinshi a yanayin ba,ruwan yasha ya ajiye sauke ajiyar zuciya tayi tana cewa.


"Yaya J ban fahimci maganarka ba,akan Anisha kakejin wannan sing din ko kuwa akan watace daban please tell me."



"Ba kan Anisha nikejin haka ba,akan *HUDAH* nike jin Amal inason Hudah ina kaunar Hudah duk ranar da tayi kuka toni a ranar zan kasance cikin halin da na gaya maki,yanzun haka bata dade da gama kuka ba,kuma kinga bani gida amman nasan akwae abunda Momy da Anisha sukayi mata har yasata kuka ,sauke hanuna da kikaga nayi to daina kukanta kenan dan naji zuciyar tawa tabar zafi da radadi ,amman Amal maiyasa kullun baku da fata da guri sae na gani kun tozartata kunci mata fuska sannan zakuji dadi a zuciyarku Amal."?


Hawaye Amal ta fara tabbas yanzun ta kara yarda da maganar Yayan nata na so nufin Allah ne ,tabbas batayi mamakin da yace mata yana son Hudah ba sae dai yanda son yazo mashi ne yasata kuka,zata kasance bayan Yaya J dan ya kasance da farincikinshi to ita Anisha fa?ita shidace ita zata iya cika litafi da irin son da Anisha take ma J ,ita kenan ansata a tsakiya ,kallon J tayi sannan tace. "Yaya J itama Hudah harda laifinta wani wajen, tunda Momy ta gaya mata dokarta sai ta manta kuma Yaya J kaima kana kara ja mata da kake nuna tausayinta a fuskarka kana nuna sonta ba tare da kasan kana nuna hakan ba,amman ita tasan kana sonta."?


Girgiza kai yayi ." ban gaya mata ba,nasan ko na gaya mata ba yarda zatayi da soyayyata ba, kodan saboda Anisha da Momy and you,tana tsoron tozarcin da zakuyi mata infact nasan ba zata taba sona ba kodan gujema matsalarku."

hawayenta Amal ta share tana cewa. "Yau ka gaya mata kana sonta ka samu ta soka ,nima zan tausashi zuciyar Momy da Anisha har su yarda da kaddara may be harda rabo ma." hararar Amal yayi sannan yace. "Ban bukatar lailashen Anisha dan ba uwata bace yarda Momy kawae nike bukata kuma ki gaya masu mudun Momy ta nemi hanani auren Bintu to zan fasa auren Anisha sae dae duk abunda zai faru ya faru." girgiza mashi kai Amal tayi tana cewa. "Yaya J dan Allah karda kayi haka mana ,kabi komae a sannu Anisha yar'uwarkace koda babu so tsakaninku dolenka ce, kuma ka auna irin son da kake ma Hudah kasa haka itama Anisha takeji akanka shin zaka iya kyaleta kaki aurenta."?


Girgiza kai yayi yana tashi tsaye gami da cewa. "Aa zan aureta amman sae da Hudah tare zan auresu kinga kowa ya samu abunda yake so Ok." duk da akwae sauran magana a bakin Amal dole yasa tayi shiru dan ta lura bai ma son magana tunda ya gama fadin abunda yayi niya cewa kawae tayi "Uhmm" tana bin bayanshi dan har ya so yayi mata nisa da sauri ta taddoshi tana cewa. "Allah ya tabbatar da alkhari."



"Amin." yace yana bude mata marfin mota ta shiga shima zagayawa yayi ya shiga dan har drive ya bude mashi,gidan su Faisal suka biya amman basu shiga ba waya kawae ya kirashi ya fito ganin Amal yasa Faisal Murmushi yana kallonta yace.


"Baby haka mukayi dake."? Murmushi kawae tayi ta kasa cewa komae saboda J da yake wajen sake cewa yayi." kuma kinsan zaki fita ba'a gaiyace ni ba."? Tsaki J yayi yana cewa. "Dallah Malam idan zaka shigo mu wuce ka shigo idan kuma baka shigowa mu tafi dan kasan muna bukatar magana dakai." harararshi Faisal yayi yana cewa. "Sorry father of love." ita dai Amal Murmushi kawae tayi ta kasa cewa komae dan a takure take da kallon da Faisal yake mata suna isowa ta kalli J tana maraice mashi fuska ,Murmushi yayi yana cewa."Uwar yansauri go."
aikuwa ta fice tana dariya ta wuce cikin .


Fitowa sukayi suka wuce apartment dinshi,sae da ya gaya ma Faisal duk abunda ya faru da maganar da sukayi da Amal nan Faisal ya kara goya mashi baya akan kawae ya gaya mata kuma ya gaya ma Momy da kanshi yana son Hudah ,amman ya jure duk abunda zai biyo baya ,sae da yayi wanka suka fita tare suka wuce part din Momy dan cin abincin dare ,Murmushi dauke a fuskar Anisha tayi masu sannu da zuwa saukowa Momy tayi tana cewa. "Laile yau ayi ruwan Faisal kaine yau da kanka rabon da ka shigo ka zauna a parlorn nan har na kusa mantawa, sae da ka leko a gaisa ka parka a wajen abokinka ko."? Dukar da kai kasa yayi yana sosa keya baida ce komae ba Murmushi kowa yayi sannan Momy ta zauna tana kallon Amal tace .

"Maza kije ki kiranman Hudah." tashi Amal tayi ta nufi wajen su Hudah nocking tayi Hudah ta tashi ta bude mata ganin Amal yasa ta durkushe kasa tana cewa. " Sannu da zuwa Hajia Amal ina wuni." Murmushi Amal tayi tana cewa. "Yauwa sannu dai Hudah ,kizo Momy na kiranki." zaro idanu tayi waje tana dafe kirji wasu hawaye ne suka zubo mata tasa hannu ta share hawaye ,sannan ta tashi da sauri tabi bayan Amal da sallama ta shiga kanta kasa tana adduar Allah yasa ba wani laifi tayi ba,tunda ta shigo J yake kallonta wani farinciki yaji yana mamaye ilahirin jikinshi dukawa tayi tana cewa.

"Hajia gani." fuska tsuke Momy tace. "Maiyasa baki hada juice ba Hudah." shiru ta danyi sae ta kalli Momy idonta cike da hawaye dan ta gaji da halin su Momy ji take kamar ta kurma ihu,cikin sarkewar murya tace. "Hajia baki ce nayi ba,tuwon shinkafa da miyar danyar kubewa kawae Hajia Anisha tace nayi." tsaki kawae Momy tana cewa. "Wallahi har nagaji da ce maki daina da kuma kiyi,maza tashi ki dauko drinks to ki kawo haka zamu ci abincin babu abun sha."? Girgiza kai kawae tayi tana tashi ta nufi kitchen ,shi dai J ba abunda yace kuma tunda Momy ta fara bai kalli inda suke ba har ta gama baiji dadi ba ,amman ba yanda zaiyi sae dae hakuri kawae ,bayan ta gama jera masu drink din ta juya ta koma room dinta tayi wanka ta cigaba da karatu quri'ani tana cikin yi Hafsat ta shigo ta cigaba da yi mata kari daga baya suka kwanta.



Daga can bangaren su J kuma sae da suka cin abinci suka dan taba fira sannan Faisal ya wuce yaso ya kirata waya amman yaga dare yayi sai ya hakura ya kwanta dakyal ya samu bacci ya kwasheshi.


Washe gari bayan sun gama breakfast yahada duka yan aikin gidan ya ba kowa salary ,amman bai ba Hudah ba koda taga bai bata ba bata damu ba daman ko ya bata babu abunda zatayi dasu,dan bata da kowa da zata ba kudin koda kuwa ya bata,komawa sukayi room Hafsat sae murna take kallonta Hudah tayi tana Murmushi tace.


"Kawata har nawa aka baki kike wannan murna har haka."? Dariya Hafsat tayi tana cewa."Hudah dubu dari ne ake bamu duk wata ,wae bai baki naki ba."? Šaga mata kai tayi tana cewa. "Allah sarki rayuwa ,dubu dari kike ma wannan murnar ,to Allah yayi ma kudin albarka." Hafsat bata fahimci maganar Hudah ba sosae saboda murnar da take ciki ko Amin bata ce ba,kwanciya kawae Hudah tayi tana tunanin rayuwa gani tayi tunanin baida wani amfani a wajenta ,ta tashi tana kallon Hafsat da take lisafin kudi ,dagowa Hafsat tayi tana mike mata dubu goma ,kallon mamaki tayi ma Hafsat tace.

"Mai zanyi da wannan kudin kuma."? Tashi zaune Hafsat tayi ta kama hannun Hudah tace. "Kyauta na baki Hudah kinyi wani abun kema dasu nima kinga na dauki 20k sauran kuma zan aika dasu gidanmu sunyi wani abun dasu." Murmushi Hudah tayi tana danke hannun Hafsat tace. "Nagode sosae da sosae ,sae dae maganar gaskiya ba zan ansar maki kudi ba,dan ba abunda zanyi da kudi wallahi ko kin bani kinga ba amfani na ansar maki kudi,ki kara dasu a aika gida." Hafsat zatayi magana kenan wayar Hudah ta fara ringing tasan J ne shiyasa taki dauka, dan tana tsoron abinda zai hadata dashi har yanzun bata manta warning din da Momy sukayi mata ba, sae da ya kira sau uku bata dauka ba a na hudun ne Hafsat ta dauka tana mai daura mata wayar a kunne gami da girgiza mata kai, amsar wayar tayi tana yin sallama ba dan rainta ya so ba,sauke ajiyar zuciya yayi yana cewa.


" Bintu."


shiru tayi bata ce komae ba sai da ya sake maimaita kiran sunanta sannan tace. "Naam." Murmushi kawae yayi yana cewa." mu hadu garden please yanzun karda kice Aa." kashe wayar yayi yana kara lumshe idonshi, sae kukan tsuntsaye da suke shawagi yake ji dasu tatalo da dawisu wajen ya hadu dan ana kiyo sosae a gidan ,dan harda su zaki da damisa ake kiwo a gidan cikin garden gasu biri dan su bari ba'a keji aka sasu ba,bude idonshi yayi yana kallon yanda jimina suke wasa ita da mijinta sae abun ya burgeshi sai yake jin ina shi da Bintu ne suke soyayya haka.


Kallon Hafsat tayi tana dirowa bisa gado tace bani himar dinta na saka naje naji abunda zai gaya man kuma." kallonta Hafsat tayi tana cewa. " kiranki yake yi ne."? Šaga mata kai tayi tana cewa. "Wallahi Hafsat tsoro nikeji sosae karki so kiji yanda dazun su Hajia Anisha sukayi man warning akan Jameel ,ni ko ganinshi ne zuciyata bata so ba,a'a ina tsoron matsalar da zan jefa kaina,kuma kinga ya kirani fatana Waya Allah yasa har naje na dawo ba wanda ya ganni dan na gaji da wannan cin mutuncin da ake mani dan kawae rayuwa ta juyaman kawae dai na tafi." tafiya tayi bata tsaya taji abunda Hafsata zata ce mata ba,tafiya take cikin natsuwa sae kace wanda kwai ya fashemawa a ciki ba yanga take ba dan haka take tafiyarta kamar da gaiya ,dan idan tana tafiya dole sae ka tsaya ka kalleta ka gaya ma Allah kayi ma Annabi Muhammad (SAW) salati ,hanyar garden ta nufa zuciyarta sae tsale take dan tsoro ,ba wai tsoran haduwarta da J take ba, dan tasan ba zai yi mata komae ba,tsoron da take karda wani ya ganta cikin masu aikin garden aje ace angansu tare da J ta shiga uku da lalace,ko ba'a mareta na anzageta ana ce mata maiya bayan ta tsani kalmar maitar da ake kiranta dashi gwara ma marin da zagin da suke mata.



Tunda ta taho yake kallonta yana kara kare mata kallon tabbas sae yanzun ya kara yarda da son da yake ma Bintu kuma zai iya jure duk wani ™alubale daga wajenta ko kuma wajen Momy idan har zata aureshi ,sallama tayi tana mai ida isowa wajenshi lumshe idanu yayi yana budewa a kanta kujerar kusa dashi ya nuna mata,babu masu taje ta zauna tana dukar da kanta da kasa tana wasa da zoben hannunta,shi kuma zuba mata ido yayi yana kallonta dan tayi mashi kyau sosae dan har ya rasa abunda zai ce mata sae da ya aro jaruntarshi sannan ya kira sunanta.


Šagowa tayi ta kalleshi sannan ta kuma kauda kanta gefe Murmushi yayi sannan ya cigaba da cewa. "Kin gama fushin dani ko kuwa dai har yanzun ba'a gama ba."? Kallonshi tayi sannan tace. "Ni zanyi fushi dakai?mai kayi man da har zanyi fushi dakai."? Ta ida maganar tana turo baki gaba ,Murmushi ya

Please Login or Register in order to submit comment