Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

🌕⚜DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ng⚜🌕 Na MAMUH GEEE☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo 203→204 No
dad i'm feeling sumtin abt him, I jst have this feeling dat
hes my waleed my boy my little me. Dafasa umminsa
tayi sbd ganin yana neman rikice musu tace, My boy
kwantar da hankalinka dr zaiyi mana dna test 'din just
relax okey? Kallon dr dad yayi yace yayi musu test 'din.
Zama sukayi cikin dan tsurewa dan hakanan suke
fargabar jin result 'din badan komai ba sai dan gudun
ace ba waleed 'dinsu bane ba tameer ya birkice musu
dan yanxu yakoma kamar yaro. Fannah ce zaune bakin
gadon tana qure kallonta ga waleed tanajin maseefar
sonsa tun kafin ace shine. Dad da haj nurat a xaune suke
a kujerun 'dakin Yayinda shikuwa yakasa koda zama
jinsa yake cikin wani sabon tashin hankali haryaje aka
'dibi jininsa ya dawo. Zaman shiru sukayi nakusan rabin
awa Kamar a mafarki saiga yaron yafara motsi ahankali
harya bu'de idanunsa ya saukesu kan fannah dake kusa
dashi. Qura mata ido yayi sbd ganin kamar yasanta sbd
fuskarta da kamanninta. Ita quri tayi masa gabanta na
tsananta bugawa sbd qwayar idanunsa zak na tameer
sbd sun 'dan fita manyan ido kadan. Tashi yayi da sauri
sbd tsoro daya kamasa lokaci 'daya ganin kansa a inda
yake 'din. Saurin miqewa tayi taja da baya ganin ya
firgita sai alokacin kowa ya lura da abinda ke faruwa.
Hankalinsune ya qara tashi ganin qarin kamannin dasuka
bayyana. Shikuwa da kallon tsoro yake binsu 'daya
bayan 'daya har idanunsa suka sauka kan tameer dayayi
wujiga wujiga tsabar tashin hankali. Qara kallonsa yake
dakyau ya murza ido ya sake kallonsa Duk sukayi tsit
suna kallon ikon allah Ai basu gama tunaniba Waleed ya
diro gadon da wani irin qarfi ya fa'da jikin tameer ya
qanqamesa sai kawai yasaki kuka yana cewa, Abbanah,
Abbanah ka tafi ka barni nayita kuka anty ma tayita kuka
harda inna tayi kuka, Ka tafi ka barni a makaranta su
abdul suna fadawa 'yan ajinmu banida baba, Abbah
kadaka tafi ka barni kuma ka tafi dani mu ringa
wasanmu na doki, Kada ka tafi anty kullum kuka takeyi
ka tafi. Ai sai kawai sukaga tameer ya fashe da wani irin
kuka yana qanqame waleed kamar zai maidasa cikin
cikinsa. Da gudu fannah ta fada kansu tana sakin nata
kuka itama. Haj nurat na hawayen take gogewa Dad
qarfin hali kawai yayi shima sbd ba qaramin dukan
xuciyoyinsu xancen waleed yayiba. Aha dr yashigo da
result 'din wanda yayi daidai dashigowar haj xeenat data
kira dad yafada mata suna asibiti shine itama takawo jiki.
Tsit sukayi batareda tameer yasaki waleed ba sunason
suji me dr xaice. Gyara zaman glass 'dinsa yayi tareda
gyara tsayuwa yana kallon tameer yace, Sir munyi test
'din har kusan so uku yana kuma bamu result 'daya
ma'ana dai yaronnan ba........ ehhh ehh hem ya gyara
muryarsa data 'dan sarqe yana 'dan jan neck tie 'dinsa
daya 'dan shaqesa yaci gaba dacewa, Result ya nuna
cewa hundred percent yaron nan jininkane, 'Dankane.
Sai alokacin dad ya jawo tameer da waleed jikinsa ya
qanqamesu lokaci 'daya fannah ma jikin haj nurat ta
fada tana sakin sabon kukan farin ciki itada haj nurat
'din. Hannu haj xeenat ta 'dora akai 🙆🏿 Cikin masifafen
tashin hankali tana kallon fuskar waleed wadda ba
abinda ya banban tata data tameer da fannah harma da
baqar marigayiyar uwarsu. Tabbas tayi alqawarin aika
shegen 'dan nan lahira da shegiyar uwarsa da duk ita
takawo mata matsala arayuwarta. Kafin kace me tuni
akayi waya cairo aka sanar musu da ganin waleed da
akayi. Yar tsohuwa ammah cewa tayi maza akawo
matashi saida aka lalla6ata kafin tace to aturo musu
hotunansa sunason ganinsa. Gabaki 'daya waleed
rikicewa yayi sbd ganin wanan yajasa jiinsa Wannan
yajasa jikinsa Sai rungumarsa suke kamar su lashesa
shidai abbansa ya maqalewa sbd shikadai yasani. Shiru
tameer yayi yana kallon 'dansa wanda rabin ransa ta
haifa masa. Baisan sanda wani shu'umin murmushi ya
kufce masa ba sbd hango wata fitinanniyar soyayya
daxai xubawa savior 'dinsa randa suka ha'du. 🌕🌕👉mamuh
geee 🌕⚜DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ng⚜🌕 Na MAMUH GEEE ☆dedicated to☆
Husnah bbchoudiallo 201→202 Cikin tashin hankali
yake tuqin fannah kuwa tana riqeda yaron sbd jini daya
'dan 6ata masa fuska har ba'a ganin kamanninsa. Suna
isa asibiti aka kar6esa da gaggawa aka shiga emergency
dashi. Xama sukayi bakin qofar gurin cikeda damuwa
dina jiran suga abinda allah xaiyi. Hankalinsu ne ya qara
tashi ganin anshare awanni suna zaune dr 'din ko 'daya
daga cikin nurses 'din ba wanda ya fito. Kiran
umminsane yashigo wayarsa ya 'daga asanyaye kafin tayi
magana ya fada mata halinda suke ciki. Hankalinta yadan
tashi tace gatanan xuwa asibitin yayi saurin cewa, No
umminah kadaki zo zamuyi handling komai fannah is wit
me So pls relax ummi dnt take d trouble of comin hia D
boy will b okey insha allah. No my boy hankalina
yarigada ya tashi tunda kuna cikin matsala dan haka
bazan iya xama ba ganinan tafe kawai. Duk yanda yaso
lalla6ata yaqi saurararsa ta kashe wayar. Tana fitowa
palon alh xaid shima yana fito yace, Haj ina zaki yanxu
haka kuma? My boy ne tsautsayi yasa ya ka'de 'dan wani
yaro shinefa sunkaisa asibiti amma har yanxu bai
farfado ba Shine zani can asibitin dan nasan yana can
cikin damuwa ga wadda yake ciki kafin wannan 'din. Da
ita da dad 'din driver yakaisu asibitin Koda suka isa har
lokacin ba wani bayani. Taruwa sukayi suka zauna jigum
jigum har tsawon lokaci. Dr ne yafito nurses na bayansa
ya gaida alh xaid tareda haj nurat kafin ya gyara tsayuwa
yana kallon tameer svd muguwar kamat yaron dashi
saiyayi tunanin shine mahaifin yaron yace, Well alhmdl
yaronka babu wata matsalar data samesa sai bugewa da
yayi da firgita data sumar dashi, Munyi masa dressin 'din
raunikansa dan haka yana 'dakin hutawa ankaisa nurse
zata kaiku sai kudin charges da magani da zaku biya.
Ajiyar xuciya suka saki su duka sbd jin ba abinda yasamu
yaron mutane. Ummice tace, Angode dr kuma yaron ba
dansa bane tsautsayine yasa ya kadesa. Cikeda
mamakinsa dabai 6oyuba yace, Haj ina nufin yaron da
suka kawofa? Qwarai kuwa dr ba 'dansa bane. Ikon allah
amma kuwa kamar harta 6aci dan bantaba ganin kama
irin wannanba. Tsabar ya qara tabbatarwa da kansa yace
suxo yakaisu gurin yaron. Ahankali suka tura qofar
'dakin dayake Yana kwance agado an 'daura masa 'dan
bandage kadan akai Nurse na tsaye tana 'daura masa
ruwa. Tana gamawa ta matsa gefe fuskar yaron ta
bayyana tsaf a idanunsu. Murza ido fannah, Haj nurat
'dan qyafta idanunta tayi alamar su bude da kyau ta
tabbatar da abinda suke gani, Dad kuwa gyara xaman
glass 'din adanunsa yayi sbd yagani dakyau. Oga sir
tameer kuwa quru yayiwa yaron baimasan me xaice ko
xaiyi ba. Atare dukkansu suka isa bakin gadon suna qara
yiwa yaron kallon tsoro. Haj nurat batasan sanda tace,
My son kaine kana qarami. Dr ganin suma sunga
muguwar kamar daya gani yace, Alh kaga ikon allah ko?
Kasa magana yayi sai kallon ikon allah dasuke. INASON
DNA TEST NA NAWA DA YARON NAN DR. shine abunda
tameer yafada idanunsa kafe akan yaron xuciyarsa na
bugawa da qarfi. A razane dukkansu suka kalli tameer
'din kafin suka maida kallonsu ga waleed dake kwance
sai alokacin suka gano me tameer ke nufi Yana nufin
yaron qila dansane,waleed 'dinsu su duka. Jikin kowa
mutuwa yayi sbd tsoron me result xai bayar Dad ya dafa
tameer cikin taushin murya yace, Son meyasa zakayi
haka, tunda kasan ana kama a duniya why not kabari
muga nazli nasan duk inda take tana tareda 'danka
Bazata ta6a sakacin barinsaba sbd shi jininkane and
batada abin so kamarsa. 🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ng⚜🌕 Na
MAMUH GEEE ☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo
205→206 NAZLIE A guje su abdul suka shigo gidan suna
haki murya na rawa suka tsaya gaban mamarsu dake
kicin tana aiki sukace, Mama waleed mota ta ka'desa ya
mutu yanata jini kuma turawan sun 'daukesa sun tafi
dashi. Sakin kofin hannunta tayi da qarfi cikin tsananin
firgici tayi saurin kallonsu xatayi magana amma ganin
fitar nazli a guje ko hijab bare 'dan kwali batada ajiki
yasa ta fahimci taji abunda su abdull 'din suka fada.
Mara mata baya tayi da gudunta itama dan kada ayi biyu
dan tasan nazli tsaf indai ta ha'da da abinda ya shafi
waleed da ubansa. Gudu take saadah da mijinta na binta
tana kaiwa gurin taja ta tsaya sbd ganin jini agurin.
Sarewa qafafunta sukayi ta durqushe gaban jinin jinkinta
na rawa xuciyarta na wata irin azabar da bata ta6a jiba
Tasaka hannunta duka ta shafo jinin a zabure ta miqe
kafin suyi wani yunquri ta dafe xuciyarta data buga ta
yanke jiki ta fa'di jini na futa ta bakinta. Gigitaccen ihu
saadah ta yanka wanda yayi daidai da dawowar me
gidansu yana ganin nazli ce a xube qasa a gigice cikin
mugun tashin hankali ya fito motar ko kasheta ma
beyiba bare rufe qofar yana ganin halinda take ciki cikin
ru'du ya tanbayi meya sameta Saadah na kuka ta fada
masa sai kawai ya sunkuci nazli 'din yasa mota Saadah
tashiga ya fizga suka bar su abdl da babansu tajasu
yakoma gida dasu yana namakin yanda duk wani
alamarin waleed megidansa hameed ke kula dashi sosai
sbd ya hango masifaffen son nazli 'din a tareda hameed
'din. ********* Suna isa asibiti aka kar6eta da gaggawa
akayi ciki da ita. Kaida kawo yake cikin tashin hankali.
Baisan yanawa yarinyar mugun so hakaba sai yau
dayaganta cikin wani hali, Tabbas yana mata
mahaukacin so dayakejin zai ita sadaukar da komai
akanta, Kuma bayajin ko iyayensa xasu hanasa aurenta
dan ta ta6a aure. Kuma yayi alqawarin riqeta da 'danta.
Anty saadah kuwa har alokacin sharar hawayen tausayin
yanda rayuwa takewa naxli take. Duk yanda sukayi
tsammanin abun yawuce nan dan nazli kam babu
alamar xata farfado qarshema wani 'daki na musamman
aka kaita sbd hameed 'din. Oxygen tub aka 'daura mata
sbd taimakawa numfashinta gurin fita.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Bayan kwana uku nazli ba wani
motsi ba alamar zata tashi Ga hameed sai hidimar
narkar da dukiya yakeyi Duk da anty saadah na cikin
tashin hankali bai hanata mamakin hameed 'dinba
danko innah dataxo saidata tayi tambaya akansa.
****** Kwana biyu dasukayi a asibitin fadar irin gatan
dayake samu bama zai faduba sbd kowa anan yake yini
sai dare sosai suke tafiya tameer da fannah ne suka
xama dashi. Tuni yasake dasu sbd irin soyayyar dasuke
nuna masa sai idan dare yayi yahau yimusu rigimar
akaisa gurin antynsa. Sunyi yawo a anguwar dasuka
kadesa amma sun rasa gano komai sbd duk sukaje suna
cin karo da abu maigadi yaje asibiti dubosu. Haka
sukayita yawo ba sa'a tuni tameer ya koma ruwa
tsundum dan kuwa damuwa ta dawo masa sabuwa.
Xaune yake idanunsa sun ka'da jajir ya tallafe kansa ya
qurawa su dad ido dasuka shagala akan waleed sai
riritata suke. Nan take idonsa suka tara ruwa sbd nazli
'dinsa takamata ace tana gabansa yana bata wannan
gatan. Kamar an mintsilesa ya 'dauki wayarsa 'daya ya
nemo number hameed ya danna masa kira. Shigowarsa
asibitin kenan kiran tameer yashigo masa ya dauka cikin
sanyin murya. Hey friend dan allah kayi hkr ranar kunzo
kunsama bananan wlh wife to be 'dinace ba lpia muna
asibiti ma haryanxu. Sauke ajiyar zuciya tameer yayi
cikin sanyin murya shima yace, Kadaka damu nima
ranar ban qarasoba nasamu prblm kuma nima ina
asibiti haryanxu. Wane asibiti? Hameed ya tambaya yana
rufe mota. NAZMEER SPECIALIST Tameer yafada jiki a
sanyaye. Nima muna asibitin yanxu hakama ina parking
space shigowata kenan ban isa room dinba. Ok kajira
ganinan xuwa. Yana isa gurinsa suka qara jajantawa juna
kafin suka 'dunguma zuwa 'dakin da nazli take dan
tameer ya duba jikin wife to be 'din aminin nasa.. 👉WATA
SABUWA 🌕🌕👉mamuh geee 🌕⚜DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ng⚜🌕 Na MAMUH GEEE
☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo 209→210
Ahankali idanun ke motsi sbd hawayensa dake shiga
cikinsu. Budewa suka farayi suna lumshewa har suka
bude gaba 'daya. Dishi dishi take gani sbd nauyin
dasukayi kwana biyu ba'a budesuba. Fuskarsa take kallo
tana lumshe idanu cikin ciwo Saita 'dan motsa hannunta
tanason shafo fuskarsa Anan ya lura da ta farfado Wata
irin dariya mai ha'de da kuka yafara saki yana ha'de
fuskarsu ko kalma 'daya takasa fita daga bakinsa sai
zallar farin cikinsa. Lumshe idanu tayi zata bude baki
daqyar tayi magana Bakinsa kawai ya jefa anata baiko
tsaya la'akari da kwanakin datayi a kwance ba kuma sam
bai tsaya tunanin su innah na 'dakin ba. ******** Yana
gama wayar ya juyo da nufin komawa 'dakin cikin
tsautsayi yaji yayi karo da mutum harsaida wayarsa ta
fadi qasa. Atare suka 'dago idanuwansu suka shiga cikin
na juna Ai nan take wani irin shock yashigesu hardai
fannah da ba 6ata lokaci tagane sonsane yayi mata
shigar sartse. Shima iya burgewa ta burgesa amma
kammaninta da tameer ne dakuma waleed 'din nazlie
'dinsa su sukafi 'daukar hankalinsa. Tabbas dah ba
tsananin so yakewa nazlie ba dasai yace yasamu mata to
amma zuciyarsa bazata iya barin nazli 'dinsaba. Cikin
classic voice 'dinta tace masa, Sorry i was in hurry so
wlh ban luraba. Kar6ar wayarsa yayi yana 'dan sakar
mata murmushi yace, No its ok nima ban luraba ina
sauri. Murmushi ta saki tana cewa, Shikenan tunda kowa
yace ba komai. Suna waiwayen juna suka wuce kowa da
abinda yake ayyanawa aransa game da junansu. Kai
tsaye 'dakin yashiga daidai lokacin dasu inna ke qoqarin
barin 'dakin sbd ganin abinda yafi qarfin idanunsu.
Idanunsane sukayi masa mummunan gani saida wani jiri
ya 'dan 'debesa yayi saurin dafa bango Wani
mahaukacin kishi da baqin ciki suka rufe zuciyarsa a
hasalce ya isa gaban gadon ya fixgo nazli daga jikin
tameer Amma kasancewar tameer ba qaramin riqo
yayiwa abarsaba yasa bata baro jikin nasaba. Rai ahade
tameer ya 'dago yana kallon aminin nasa cikin tsananin
6acin rai zaiyi magana hameed ya rigasa da cewa, Let go
of her b4 sayin anytin bcoz i cnt stand to see her in
sumones arms shes my wife to..... Tasss tasss sir meer ya
watsa masa wasu lafiyayyun marika a tare jikinsa na
wani irin mazari. Qoqarin sharara masa wani yake inna
tayi saurin riqesa cikin tsananin mamakin mugun kishin
datake hangowa atare dashi wadda tuni suka tsorata sbd
'yan mazan kowa jikinsa rawa ya 'dauka fannah data
biyo hameed tana shigowa 'dakin taga b 'dinta ga nazli a
kwance tana nishi sannan ga hameed a tsaye suna
mazuran 6acin rai. Da gudu tashiga tsakaninsu tana
kallon yayanta da idanunsa suka ka'da xuwa ja. A fusace
hameed ya nufi nazli xai 'dauketa subar asibitinma
gabaki 'daya Tameer ya sha gabansa yana cewa, Duk
hannunka yasauka kan rayuwata(nazli 'dinsa) I swear i
wont hesitate to rip out ur heart. Kallon rainin wayo
hameed ya watsa masa shima rai a6ace ya wucesa zai
nufeta da sauri fannah tasha gabansa tana hawaye tana
roqonsa kada yayi Finciketa gefe yayi wanda hakan ya
qara qular da tameer Ya juyo afusace yashoqosa nan
hnkalin kowa ya tashi suka taru suna son qwatar
hameed amma sun kasa sbd yaji maza. Kuka fannah keyi
sosai haka su inna ga hameed 'din idanuwansa sun firfito
harya idanubsa sun fara juyewa. Da gudu fannah ta fita
tayi gurin dad dake gurin waleed tana kuka arude take
fadin, Dad dad b b zai kashe wani a... Arude dad ya miqe
basu tsaya wata wataba suka bar 'dakin wanda haj
xeenat dazata shigo 'dakin tayi saurin la6ewa har suka
fice tayi saurin fadawa 'dakin sbd yau tasamu damar
datake jira akan waleed. Har dad da wasu likitoci aka
taru amma ankasa 6an6are hameed daga shaqar
maxaje. Nazli dake fidda numfashi ahankali ta sauko
gadon jiri na 'dibarta tana dafa bango ko gani batayi
sosai ta nufosu. Hannu na rawa irin na marasa lpia ta
daga ta 'dara a kafadar tameer. Dukkaninsu dad dake
riqeda shi bai hanasa jin saukar hannunta ahankali
ajikinsaba. Da sairi ya juyo lokacin tayi baya zata zube
sbd jiri kafin qyaftawar ido yasaki hameed ya riqota
jikinsa aikuwa ta qanqamesa tana kiran sunansa
ahankali.. 🌕🌕👉mamuh geee Copied By HAYATU BABA
ZUBAIRU (admin Novels villa Duniyan novels Hayat
hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel,
makeup and cooking) WHATSAPP NO:
+2347039625239 🌕⚜DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ng⚜🌕 Na MAMUH GEEE
☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo 211→212 Qara
qanqameta yake yana cewa, Yes my nazli nine, Ur meer,
Pls dnt close ur eyes, Open them and see nine, Nine
agabanki. Ganin numfashinta na neman 'daukewa ne da
gaske yasa shi 'daga murya cikin ihu yana kiran sunanta
amma ina. Fannah ce da anty saadah suka fita cikin rudu
harsuna gwarewa Suka kirawo dr. Shikansa dr arude
yazo yana ganin halinda take ciki yace nurses su 'dauketa
maza amaida masa da ita emergency. Ganin nurses 'din
kamar basa sauri ne yasa ya miqe 'daukeda abarsa yayi
gaba da wani irin sauri. Rufa musu baya su dad dasu
inna sukayi hankali tashe. Hameed kuwa a fusace ya
miqe daga durqushen dayake zuciyarsa na wata irin
tafasa Ga wata muguwar shawara da zuciyarsa ke basa.
Wani shu'umin murmushi yasaki yana cizon le6e
ahankali yace, Hmmnnn tameer zaid omar u will pay for
this, Dagani har kai babu wanda zai sameta. Zaka qarasa
rayuwarka cikin baqin ciki tareda ciwon rasata aduniyar
gabaki 'daya. Ficewa yayi yana qara daukar mugayen
shawarorin da zuciyarsa ke basa. Kaida kawo yake
abakin qofar hnkali tashe danko gani bayayi sosai Dad ne
ke qoqarin yaga ya lallashesa ya kwantar masa da hnkli.
Innah da anty saadah harma da fannah na zazzaune a
gefe suma suna jiran tsammani. Haj nurat ce tashigo
asibitin kai tsaye ta nufi 'dakin dan ita batasan wainar da
ake toyawaba. Turus tayi tana kallon 'dakin ganin
bakowa aciki har waleed 'din da ake jinya. Toilet ta duba
taga ba kowa ta dawo 'dakin ta tsaya tareda fiddo
wayarta daga jakarta ta lalubo number tameer. Kira
kusan biyar tamasa amma bai 'dagaba Nan mamakinta
ya qaru ta koma kan kiran fannah ita tata wayar ko shiga
batayi Zuwa lokacin hnkalinta yafara tashi Ta kira wayar
dad Kiran farko ba'a 'daga ba saidata kuma kira ya 'daga
Hankali a 'dan tashe tace, Meya sami kowane inata kira
baku 'dagaba gani tun dazu a 'dakin waleed 'din amma
ba kowa. A kasalance ya fada mata abinda ya faru kafin
ya 'dora da fadin, Ki zauna da waleed 'din kafin nan 'din
muga yanda jikin nata zaiyi sbd tameer ya matsa sosai
zai fita da ita nace yabari ta farfado tukuna. Gyara
tsayuwa tayi tana cewa, Banfa gane wane waleed 'din
kake magana ba sbd ban samu kowa a dakin ba. Miqewa
dad yayi da qarfi yana 'dan satar kallon gefen da tameer
yake amma ga mamakinsa saiyaga shi tameer 'din ya
kafe da idanu. Sakin murmushin qarfin hali yayi yana
hada zufa ya matsa gefe tareda basu baya hankali tashe
yace, Waleed baya 'dakin? Then yana ina? Katse kiran
yayi ya nufi 'dakin a rikice yana hada gumi. 🌕🌕👉mamuh
geee ******** 🌕⚜DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ng⚜🌕 Na MAMUH GEEE
☆dedicated to☆ Husnah bbchoudiallo 213→214 Yana
isa 'dakin yafara lelleqa ko ina na 'dakin yana fadin anan
muka barsa Yana cikin dakinnan. Wasa farin girki
saigashi an dube asibitin tsaf babu waleed Likitoci da
nurses harma da securities hankalinsu tashi yayi sosai
hardai ganin shine jika 'daya tak ga alh zaid omar. Haj
nurat kuwa kuka tasa musu wiwi akan sai an nemo mata
jikinta. Shi kansa alh zaid hnkalinsa a tashe yake dan tuni
ciwonsa ya fara barazanar tashi amma yana daurewa
sbd tsoransa 'daya kada zancen yakai ga tameer sbd
damuwar dayake ciki ma yanxu tayi masa yawa bare
yaqara data 'batan waleed 'din. Lallashin haj nurat yame
amma ina kuka take bakin rai. Jami'an tsaro kuwa tuni
suka zagaye asibitin ana tsananta bincike. Dr ne yafito
daga 'dakin fuskarsa adan sake ya miqawa tameer hannu
yace, Ka kwantarda hankalinka mr romeo ur ms juliet is
ok now, So anytime zata iya farkawa lapia klau. Ajiyar
zuciya yasaki yana kallon qofar 'dakin bai tsaya komaiba
ya fa'da 'dakin. Ahankali ya isa bakin gadon ya zauna
tareda riqo hannunta ya damqe cikin nashi Baisan sanda
hawaye suka 'digo daga idanuwansaba suka 'diga a
hannunsu Murya na rawa yafara magana xuciya a karye,
In my whole life i neva tot dat sumday i wil love sumone
like this, Being wit you is my fate, Ure my life,my savior
my me. Hawayensane suka qara gudu muryarsa ta qara
karyewa yaci gaba da fadin, I try very hard to muster up
d courage to not feel defeated but it is very difficult to
deal it this. I love you, I love you so very much that i
cant even think of anytin. Su fannah dake tsaye qofar
'dakin banda hawaye ba abunda suke sbd tsananin
tausayinsa idan yaji 6atan 'dansa waleed. Ahankali
idanunta suka fara budewa Tana gani dishi dishi harsuka
bu'de. Akansa idanunta suka sauka yana riqeda
hannunta ya kifa kai akansu sai hawaye yake. Lumshe
idanu tayi ahankali tasake budesu akansa. Wani sabon
sonsane yake qara tsima azuciyarta Idanunta suka cika
da hawaye Ta 'dago 'dayan hannunta ahankali ta 'dora
akansa. 'Dagowa yayi da suka hada ido da ita yasakar
mata wani lafiyayyen murmushi yana qara qanqame
hannunta. Murmushin tasakar masa itama ahankali cikin
rashin qarfin jiki. Tasowa yayi yay manna mata kiss a
hnkli a goshinta. Lokaci 'daya suka sakarwa juna
murmushi yana kafeta da idanu. Juyar da kanta tayi tana
'dan rintse idanu sbd kallon dakuma qwayar idanun
nasa. Hakan datayi sai yaji wani sabon masifaffen sonta
ya qara shigarsa har tsikar jikinsa na tashi. Juyowa yayi
yakalli dakin saiyaga ba kowa sun fice sbd ganin abinda
ke shirin faruwa. Murmushi yasaki yana kallon qofar.
Fitowa yayi daga 'dakin yana qaqarin kiran dad a waya.
Ganin kiran tameer ya 'daga hankalinsu dad ya kalli dr
da fannah dasu innah yace suje suyi abinda yace kada
suyi kuskuren dasu tameer zasusan da 6atan 'dansu.
Yana gama fadar haka suka wuce jiki asanyaye shikuma
ya'dau wayar yana daidaita muryarsa. 🌕🌕👉mamuh geee 🌕
⚜DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ng⚜🌕 Na MAMUH GEEE ☆dedicated to☆ Husnah
bbchoudiallo 215→216 Yes son? Dad my savior is finally
o..... Arude dad ya katsesa da cewa, Alhmdllh son yanxu
kawai ka 'dauketa kutafi gida ka kula mana da ita sosai
tasamu hutawa kaman na kwanaki kaima kana buqatar
hutawa so ku huta Mukuma zamu kula da waleed. Shiru
yayi yana nazarin muryar dad 'din nashi kamar akwai
wani abu aciki amma baikawo komaiba yace Ok dad. Ya
katse wayar tareda juyawa daidai nan su dr suka iso ba
'bata lokaci dr yayi dischrgin nasu sbd cika abinda dad
'din yace. Su inna da fannah kuwa sai murnar qarfin hali
suke wanda duk aikin dad ne. Ciki suka shiga anty saadah
ta hada kaya Fannah da innah suka kama nazli 'din yana
biye dasu abaya ji yake kamar suna ja masa ita da qarfi.
Har sunkai mota yace, Ku bani 3min naje nagano my
little soldier. Arazane suka kallosa duka atare tashin
hnkali qarara bayyane afuskarsu amma babu wanda ya
iya samun bakin magana. Ganin da gaske can yayi yasa
fannah tayi saurin sakin nazli tareda 'dan sa qafa ta take
mata qafa. Ahhhhhh ta fada da 'dan qarfi aiko kaman
yanda ta tsammata a rude ya juyo tareda dawowa yana
riqo hannunta. Ajiyar xuciya fannah tasaki tana riqo
nazli 'din cikin damuwa tafara fadin, Oh am really sorry
sister inlw bansan ya akayi na takaki ba sorry.... Girgiza
mata kai nazli mamakinta na qaruwa da abubuwan
datake gani. Kamar kuwa yanda suka tsammata fasa
zuwan yayi ya kama hannunta yashigar da ita motar ya
zagaya shima yashiga. Kallonsu fannah dasuka tsaya yayi
fannah tayi saurin sakin fuska tana cewa, No b ku tafi ni
zanzo dasu inna amotana. Innah ya kalla itama ta qaqalo
fara'a tana cewa, Eh zamuxo a tata motar tunda dai duka
'dayane. Murmushi yasaki tareda jan motar sukabar
asibitin. Tuqi yake ahankali yana 'dan satar kallon
gefenta jin kansa yake cikin wani irin tsantsar farin ciki
mara misaltuwa. Itadai kanta a qasa yake sbd ita
tambayoyine fal aranta. Suna isa gidan batayi mamakiba
dan ganin sbd tasan sunada tarin dukiyar dazasuyi goma
irinsa a kanon. Yanayin parking a harabar gidan ya fito
ya zagayo gefenta ya bude qofar. Rintse idanunta tayi
sbd ganin abinda yake shirinyi. 'Daukarta yayi cak kamar
baby da qafa ya tura qofar motar yayi ciki da ita. Kallon
fuskarta yake yanajin nishadi da shauqinta. Idanunta a
rintse suke harya fara hawa stairs da ita ya isa 'dakinsa
bai tsaya ko inaba sai a bedroom 'dinsa ya kwantar da ita
a lafiyayyen gadonsa. Saurin kifewa tayi sbd kallon
dayake jifarta dashi yana firgitata sbd tasan ma'anar
kallon tun awancen lokacin. Yasoyin wani abu sai ya
rarrashi xuciyarsa ya fasa ya fada toilet yana sakin wani
shu'umin murmushi. Ruwan 'dumi sosai ya hada tareda
turaren wanka mai sanyin qamshi. Tun acan ya tu'be ya
fito 'daure da towel a qugunsa. Har alokacin idanunta
arufe suke Sai baiyi wani babban motsiba saijin tayi ya
'dagata. Toilet ya direta tareda zame hijab 'din jikinta
yana kallon fuskarta dake qara masa sonta. Qanqame
jikinta tayi hawaye nabin fuskarta sbd jin qoqarinsa
nason rabata da kayan jikinta. Jin sautin kukanta yafara
fita ahankali yasa ya tsaya da cire mata kayan. 'Dagowa
yayi tareda tallabo fiskarta yana kallon hawayen dake
gangarowa. Kan bakinta ya maida kallonsa yana matsar
da fuskarsa zuwa nata ahankali. Jin numfashinsa na
matsowa ga fiskarta yasa ta bude idanunta wanda hakan
yayi daidai da saukar bakinsa cikin nata. Kissing 'dinta
yake yana lumshe idanu alamar ba qaramin dadin hakan
yakejiba. Jikintane ya mutu gabaki 'daya har qarafunta
suka gaza mata Ya tallafota jikinsa yana cigaba da tsotsan
bakinta. Shagalar datayi yasa harya cire mata kaya bata
saniba saidaya cirata cak yana sakar mata murmushi ta
lura Tsabar kunya kawai saita sakar masa kuka. Cikin
bathtub ya ajeta tayi saurin qanqamesa sbd ganin zai
koma seti da ita dan yariqa kallonta dakyau. Murmushi
yasaki yana ra'da mata, Why? Bakyason naga savior 'dina
dakyau ne? Cusa kai tayi a qirjinsa tana qoqarin sakin
wani sabon kukan Yayi saurin tallafota yana cewa, No no
pls dnt nadaina okey. Daqyar yasamu sukayo wankan ya
na'dota a towel suka fito A kan dressin chair ya ajeta
tareda bu'de wardrope ya 'dauko mata wata fitinanniyar
sleeping dress ya aje mata. Mai yashafa tareda turare
yasaka farar jallabiyarsa ya fice da 'dan sauri sbd sallar
isha da aka tayar. Mai tashafa jiki asanyaye kafin ta 'dan
saka turare ta 'daga rigar daya aje mata tasaka Ai da
sauri ta duqe duk da ita kadaice adakin. Doguwar hijab
'din sallah daya aje mata ta dauka ta zura ta tada sallah.
Tana gama addua saigasa yashigo yace ta tashi suyi nafila
Batada baki ko qarfin musu dan haka saita tashi sukayi
nafilarsu suka gama tareda addua. Kamota jikinsa yayi
ya zame hijabinta Wasu yawu ya hade da qyar amma
afili saiya miqe tareda

Please Login or Register in order to submit comment