Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba mutumba. Daidai wata gona yakai ya tsaya cak
kamar an tsaidashi. Gonar wani bawan allah ce dayayiwa
wani kyakkyawan asiri sbd 'barayi duk wanda yashiga
gonar indai yanada asiri ajikinsa to zai karye ko wane
irine. Soyake ya keta gonar ya wuce yakasa dan tsananin
tsoro sbd titin daya hanga motoci na wucewa da mugun
gudu dazarar ka wuce gonar. Juyawa yayi da sauri dan
komawa inda yafito. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na
MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo
116β†’120 Gab da magrib ta le'ka 'kofar gidan taga
waleed ka'dai tace, Waleed kudawo gida lkcn sallah yayi
Ina meer 'din yake? Kwaso kayansa wasansa yayi yana
cewa, Tun tuni fa yatafiyarsa yawo nika'dai nake wasana.
Dam. Gabanta ya buga tareda ha'de wani yawu da'kyar
tafito wajen gaba 'daya ko hijab babu ta riko waleed ta
jijjigasa da 'karfi tace, Waleed ina yatafi? Kuma tun
yaushe? Anty tunda muka fito baiko tsayaba fa yawuce
yabi can. Yayi mata nuni da hanyarda tameer 'din yabi.
Cikin gidan takoma a ki'dime jikinta na zuba wani irin
'bari tajawo hijab tasaka a birkice tana 'kokarin ficewa
inna tayi saurin kiranta tana cewa, Lafiyarki kuwa inata
tambayarki kina 'kokarin ficewa hijab ajuye? Hawaye
suka tsinke mata cikin rudewa tace, Inna meer bayanan
wai wai baya 'kofar gida ya..ya..y sai kawai ta juya ta fice
da sauri Hijab inna tasaka tabi bayanta da sauri sukabi
inda waleed yake nuna musu yabi. Yawon nemansa suka
fara suna tambayar duk wanda suka hadu dashi har
akayi magrib babu wata alamar ganinsa. Kuka take
wanda ya gagara tsayawa jikinta Sai mazari yake saida
inna ta ri'keta sbd ganin yanda take neman xubewa dan
gaba 'daya a ki'dime take Waleed ma dayaga halinda
antyn tasa take ciki saiya fara kuka. Har 'karfe goman
dare suna yawo saida suka zagaye 'kauyen tas amma
babu alamarsa. Da'kyar inna takamota dajan 'kafa suka
dawo gidan suna shiga ta sulale 'kasa tareda sakin kuka
da 'karfi tana kiran sunansa. Kuka sosai take tana kiran
sunansa cikin wani irin ra'da'di da ciwo a xuciya, Yanda
take kukan ne kamar ranta xai fita cikin wani irin hali
yasa hawaye tsinkewa inna na tausayinta dakuma
tunanin wane hali tameer 'din yake. Kamata inna tayi
tana 'kokarin tadata sai kawai taga ta zube idanuwanta
arufe. Salati tasaki tana yayyafa mata ruwa cikin ru'dewa
dan yanda take ganin wani irin tashin hankali daga nazli
'din dan tasan tameer ya 'bata amma tasan nazli zata
shiga mummunan halinda yafi wanda zaije yashiga sbd
ganin idonta taga yanda naxli ke masifar sonsa fiyeda
komai. Tana farfadowa tasaki siririn kuka ahankali inna
takaita 'daki tana bata 'karin gwiwar zaa gansa insha
allah. A daren ranar basuyi bacciba sbd halinda nazli
tashiga dan kuka take babu alamar tsayawa har shi'dewa
take Inna hankalinta ya tashi sosai dan tsoron kada wani
abun yasamu nazli acikin wannan halin ga waleed ma
saidaya sha kukan akaisa gurin tameer kafin inna ta
lallabasa da'kyar yayi bacci wanda hakan ya 'kara 'daga
hankalin nazli. ********* Duk iya yanda inna ta
tsammaci abun ya wuce nan dan saida 'yarta tilo guda
sa'adah dake aure a kano tazo dan taimakawa halinda
ake ciki Dan ciwo rigis nazli ta kwanta bayan sun share
kusan sati biyu kullum suna yawon nemansa har
'kauyukan kusa dasu sunje amma ba wani alamarsa. Tayi
wata muguwar rama,kuka da tunaninsa sun zama
abincinta, Inna tayi iya yinta amma babu wani sauki har
ciwo yayi mata mugun kamu. Inna da sa'adah sosai suke
kula da ita har saida tayi wasu sati biyun akwance kafin
taji sauki amma ba'a zuciyaba dan kuwa batajin zata
ta'ba iya cire tunaninsa aranta. Duk lokacin data tuna
cewar bashida kowa ayanxu sai ita gashi tayi sakaci
tabari ya 'bata. Al'kawarin datayi na kula dashi yatafi
abanxa yakasa kula da tameer 'dinta, Tameer 'dinta
datakejin rayuwa babusa batada amfani agareta. Duk
wani so da 'kauna ta tattara ta 'dorawa waleed, Shikansa
waleed kullum saiya musu rigimar abbansa saisun
lallabasa. Ahaka har wata biyu suka shu'de musu kuma
tana 'dan sakewa wani lokacin amma shikam kuka
kullum daren allah saita sha'ki abinta. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•
⚜DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah
bbchoudiallo 121β†’125 TAMEERβ˜† Yaji sauki sosai ya
warware kamar bashiba Kowa ji yake dashi kamarsu
ha'desa. Cairo yayi zamansa dad kuwa suka koma tareda
haj xeenat datazo dubasa itama. Dad dakansa yasa ayi
masa binciken inda nazli take bayan yadawo sbd tameer
sam baisan komai gameda ciwonsaba hasalima sun
'boye masa hauka yayi sun fada masa cewar kawai
yasamu accident ne. Duk iya yadda dad yaso asamo
masa inda nazli take ba'a samu ba haka ya hkr yana
adduar allah ya bayyanota kodan auren 'dansa dake
kanta. Watansa biyu a cairo yakoma asalin balarabensa
yayi wani irin jajir dashi, Yakoma asalin tameer 'dinsa
'dan gaye da tsafta ga class ga nera tuni 'yar tsohuwa
ammah(kakarsa mmn nyssa)tafara masa maganar ita
aure takeso yayi. Hutawa yakesonyi sosai kafin ya koma
office dan haka ya shirya ya wuce 'kasar america.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ 5month ltr Watansa biyar cif a
america yana cikin kwanciyar hankali da hutu Ya xabga
wani irin kyawu na ha'kika, Fatarsa ta 'kara kyawu na
musamman sai she'ki take alamar hutu ya ratsata sosai.
Duk wanda yagansa zai 'dauka mawa'kin nanne na
larabawa me suna tameer housny. Wani kwarjini da
annuri ke fita afuskarsa da duk wadda takallesa saita
'kara kallonsa komai haduwarta da ajinta. Jirgin cairo
yabi yana sauka motocin kamfaninsu nanan akaxo
'daukarsa. Sanye yake cikin black jins da red shirt data
maseefar yimasa kyawu,sai wasu ha'daddun takarma
ba'kake da agogon diamond rolex dake 'daure
ahannunsa. Fuskarnan sanye da gogls baki sai hakan
yasa kyawun jajayen lips 'dinsa suka 'kara fitowa ga
gashinsa dayasha gyara sai she'ki yake. Wani irin 'kamshi
ke tashi ajikinsa na turaren signature designer na maza.
Kai tsaye gida aka nufa dashi saidaya huta yayi wanka
kafin yashirya ya tafi gidan umminsa wato haj nurat.
Tana ganinsa farin ciki ya bayyana afuskarta yazo ya
rungumeta yana cewa, I miss you so much my ummi. I
miss you too tameer ta fada tana jan kumatunsa.
Fannah ce ta fito 'daki rikeda waya tana magana da
daddynsu aitana ganinsa ta katse kiran tareda fadawa
jikinsa tana nurnar ganinsa. Rungumeta yayi shima yana
murmushi ya 'dago fuskarta yaja dogon hancinta irin
nasa yana cewa, My fannah has grown up but still acting
like a bby. Turo baki tayi tana cewa, Pls B. Tafada cikin
shagwaba. Ammi kallonsu take cikin tsananin 'kauna
tana 'karajin sonsu aranta. Nandanan aka gyare dining
cikeda abinci kala kala sbd shi kawai. Sam bai wani ci
abincinba dan bayason abinci da yawa. Yana gamawa
shida fannah suka fita zuwa gurinsu ammah. Dakansa
yake tukin cikin nishadi sbd ganun 'yar little 'kanwarsa
dayakeso fiyeda komai tana taredashi. A gidansu ammah
suka kwana dan yanda tsohuwar ta rikice masa akan
lallai aurensa takeson gani Dakyar ya lalla'bata hardai
saida suka kwana agidan. Satinsa 'daya a cairo ya shirya
yadawo nigeria dan sam ji yake kamar komai nasa farin
cikinsa,ruhinsa,rayuwarsa duk jiyake kamar suna can.
Tareda fannah suka taho dan hakanan yanxu bayajin zai
iya rabuwa da 'yar 'kanwarshi bare yanxu dazai zauna
nigeria gaba 'daya. Dad da kansa yazo 'daukarsu tareda
direbansa Yana ganin 'yayan nasa ya rungumesu cikin
farin ciki da tsananin 'kaunarsu. Kai tsaye sabon 'katon
gidansa mai kamada mention dake asokoro. Babban
gidane mai 'daukeda sashe biyu 'Daya na dad da haj
xeenat sai 'dayan na sir tameer. GODIA ME TARIN YAWA
DA RASHIN IYAKA GAREKU MASOYAN DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngπŸ™πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜ πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰
mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated
toβ˜† Husnah bbchoudiallo 126β†’130 Haj xeenat nacikin
tashin hankali sosai sbd dawowar tameer harda 'karin
'kanwarsa fannah wadda ta gani 'baro 'baro daga dad
'din har tameer ji suke da ita kamarsu ha'diyeta. Babban
tashin hankalinta baifi boka dayace aiki bazai 'kara kama
'daya daga cikinsu Sannan gasu liloh sun gudu sunbar
'kasar sbd alh zaid yasansu su suka kamasa dan haka
itadasu haj bilki sun basu kudi masu yawa sunbar nan
sbd kada akamasu su fa'di sunayensu amatsayin wa'inda
ke sasu aiki. Yanxu batada wata sauran dabara data wuce
tayi amfani da kissa tasamu yanda takeso dan ta
tabbatar da baxata hutaba saitaga bayan tsinannun
dangin larabawan. Gate biyune da gidan Na farko
securitys ne xube agurin kuma anan duk wasu masu aiki
ke tsayawa. Saina biyu idanka shege na farkon shikuma
motar masu gidanne kawai keshiga dan duk ba'ki da
sauran motacin tsaronsu duk a harabar gate 'din farko
ake barinsu. Harabar gate na biyu kuwa duk
motocinsune na musamman jere agurin parkin space.
Fa'dar tsaruwar gidan tabbas zaicinye page 'din gaba
'daya amma ku kwatanta irin yadda gurin zai tsaru.
Flowers ne masu kyau da tsada a harabar gurin ga fitilu
masu ban sha'awa rufi da pentin gidan kawai abin
kallone. Babbar 'kofar palon shiga palon gidance agurin
sai 'kofar garden 'din gidan. Steps uku zaka taka kashiga
ha'daddiyar babbar 'kofar palon. Palon ya hadu ya tsaru
sosai da royal kushins brown sai komai na palon shima
brown tun daga kan cuttons 'din da center crpt,dasu
manyan frames daduk wani abun dake palon dan hatta
splite a.c guda biyarne a palon. Opposite da dining area
dake palon matattakar benene guda biyu suna kallon
juna 'daya na hayewa palon tameer da two bedroms
dinsa aciki, Sai 'dayan na hayewa 'bangarensu dad suma
amma nasu palo da tree bedroms. Palon 'kasa 'din akwai
wani palo ha'dadden palo da bedroom 'dinsa aciki
wanda aka gyaresa tsaf da komai mai kyau da tsada sbd
fannah. Kwanansu biyu da dawowa tameer yafara fita
office Hakama haj xeenat ta maida hankali sosai gurin
nuna musu so da kulawa na munafinci wanda ba 'bata
lokaci ta siye xuciyar fannah tuni dan wani gata da ririta
take nunawa fannah Itakuwa fannah dama 'yar tagace
sai kawai rasaki jiki tana shagwabarta son ranta Kafin
kace me tameer sbd son dayakewa fannarsa saiya fara
girmama haj xeenat sosai hardai idan ana dining cin
abinci ta kulawa kamar tabasu abaki. Hankalinsu ya
kwanta sosai sai rayuwar jin dadi suke da mum kaman
yanda suke kiran hj xeent. ********** Cikin nutsuwa
yake saukowa daga stairs 'din yana sanye cikin black suit
sai 'kamshi yake ya xuba kyawu iya kyau. Fannah tayi
saurin mikewa ta tarosa tana cewa, Gud morning b.
Morning my little, Daria tayi tana ce masa, B pls inason
xanbi mum biki xuwa kano Pls kabarni nabita. Xama yayi
kan dining table 'din yana gaida dad da haj xeenat Kafin
cikin isa da class 'dinsa yace, Little ure not goin anywhr
for now but kibari next mnth am goin there for some
work sainaje dake. Shagwa'be fuska tayi tana kallonsa
kamar xatayi kuka tace pls b. Haj xeenat tasaki
murmushi tace, Alh kasa baki b yabarta taje mana. Aa
kunfi kusa amma bari nataimaka muku. Kallon tameer
dake kur6an black tea yana duba jaridar yau yayi yace,
Son kabarta sutafi since bata ta6a zuwa kanon ba dama
and its just a matter of 5 days. Kallon agogon diamond
'din dake hannunsa yayi yace, Shikenan dad since ka
amince da tafiyar Mikewa yayi tareda kwasar wayoyinsa
yafice dan yanada meeting 9 gashi har 9 'din tayi. B what
tym xaka dawo yau sbd i wnt to spend sumtimes wit you
cox all diz days bakada tym 'dina koyaushe busy. Kafin
yabata amsa MEENAH tashigo harabar gurin cikin wani
irin ado najan hankali tana sanyeda doguwar rigar pink
lace ya kamata tasaka wasu heels masu shegen kyau sai
'kamshi ke tashi ajikinta. Tun kafin ta iso gurinsu
zuciyarta ta buga da 'karfi Tunda allah ya halicceta bata
ta'ba ganin ha'dadde,kyakkyawa,cikakke mai class
kamarsaba. Wani gigitaccen sonsane ya daki xuciyarta
nantake tayanke tasamu mijin aure. Shafo fuskar fannah
yayi yace, Take care lttle Yafada motar direba yaja suka
bar gidan. Kallon fannah meenah tayi tareda sakin
murmushi dan sai yanzu tagano sune 'yayan mijin
mummy xeenat 'kawar mummynta. Gaisawa sukayi
fuska asake kafin suka shiga palon daidai nan dad yafito
shima yabar gidan. Rungumesu haj xeenat tayi tana farin
cikin ganin meenah kafin suka 'dunguma xuwa cikin
palon. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE
β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 131β†’135
Agidan ranar meenah ta yini tanata faman jan fannah
ajikinta harsaida suka saba sosai Ta girmi fannah da
kusan shekera hudu amma haka dan tanada 24 fannah
kuma nada 19. Kamar kadasu rabu haka meenah ta tafi
da motarta Tana isa gida ta fada jikin mummynta cikin
farin ciki tace, Mummy nasamu wanda nakeso zan aura
tameer 'din gidan mummy xeenat. Wani farin ciki haj
karima taji dan dama tundata 'kyalla ido akan tameer
taga yanda dukiya da hutu tareda jin dadi suka kwanta
masa taji tanason meenarta ta auresa dan zasu samu
dukiyarda suke burin samu tuni. Kallon 'yarta tayi tana
cewa, Bby ai kuwa kinyi miji dan idan har ni haj karima
ina yawo saikin auri tameer kin haifamun larabawan
jikoki. Cikin farin ciki ta rungume mummyn tana fadin i
love you mum. Ta waya haj karima takira haj xeenat tayi
mata bayanin komai haj xeenat harta kusan fin haj
karima farin cikin hakan nan suka hure kunnan meenah
suka koya mata kissoshin dazatabi ta mallakesa wadda ta
farko itace ta siye zuciyar fannah wadda ita xata saka
tameer yaso meenah tunda yana maseefar son 'kanwar
tasa zai iya komai akanta. ************ Burin meenah
yacika dan kuwa yanxu sun 'dinke da fannah sun zama
aminan juna Kullum suna gurin yawon shopping ko
gurin shakatawa Tameer kuwa ya maida hankali sosai
akan aikinsa sai kudi dayake sakar musu dan tun yana
'daurewa meenah fuska harya 'dan fara sake mata
ka'dan sbd shakuwarta da little 'dinsa.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ 'Karfe biyar jirginsu yasauka a
airport 'din kano sbd bikin dasuka xo na 'yar 'kawarsu
mummy. Fannah,meenah,mummy karima da mummy
balki ne kawai sukaxo mummy xeenat bata samu
zuwaba sbd wani uzuri. Daga airport gidan haj karima
dake kanon suka dosa Babban gida mai kyau dashi ba
kowa sai mai gadi da matarsa dake kula da gidan.
Sa'adah 'yar inna asmah itace matar me gadin gidan
kuma 'yar aikin haj karima ita ta gyare gidan tsaf tana
musu barka da xuwa suka amsa fuska asake kafin kowa
ya wuce daki dan hutawa ita kuma ta shiga kicin tafara
ha'da musu lafiyayyen abinci. 'Kamshine yacika ko ina
agidan na girkin datake tana gamawa ta jere a dining nan
duk suka fito kowa yayo wanka yafito cikin shigar shan
iska dan sai jibine ma xa'a fara bikin. Saida kowa
yazauna dining kafin fannah ta fito daga bedroom cikin
3 quater jins pink da farar vest ta 'daure gashinta dakw
lilo har kan bayanta tana waya da b 'dinta. Saura 'kiris
sa'adah tasaki drinks 'din data dauko a tray zata kai
dining 'din sbd ganin fannah. Ido takura mata tana
ha'diye wasu yawu dakyar sbd fuskar waleed 'din nazli
'dinsu data gani sak a fuskar fannah hatta 'dan dimple
'dinsa da dariyarsu komaima sak gashinan illah hutun
dake fatarsu ya banbanta. Dakyar ta iya kai tray 'din ta
aje tana yiwa fannah data gama wayar ta zauna barka da
fitowa Cikeda fara'a ta amsa tana cewa, Lallai xanji
'dadin abincin nan dan 'kamshinsa na da'di. Daria kowa
yayi banda sa'adah data 'kara gigicewa sbd maganar da
fannah tayi ya 'kara fiddo da tsantsan kamanninta da
waleed. Suna gamawa ta tattara gurin takoma tana
cigaba da aikinta. Kano tayi musu da'di dan kuwa
shakatawarsu suke kafin afara biki sbd kullum suna
yawon gari dan yanxu ba 'karamar dukiya suke samu ta
gurin fannah ba dan kudi sosai tameer ke sakar mata. A
'bangare 'daya kuwa wata irin shakuwa tashiga tsakanin
sa'adah da fannah dan sosai takeson aikin sa'adah sbd
tsananin tsaftarta da iya girkinta ga barkwanci da saurin
sabo. Jitakeyi badan sa'dah nada aureba da da ita xata
tafi dan tanada bukatar 'yar aikin kanta acan sbd duka
duka nafeesat ce kawai me aikin mummy dan haka tana
bukatar me kula da tsaftar gurin b 'dinta dakuma nata
gurin. Fira sa'adah take mata tana yanka mata fruit
sukadai ne agidan dan su mummy sun fita meenah kuwa
tana 'daki tana bacci. Kallon sa'adah tayi tace, Maman
abdul bakida 'kanwa ko wata dakika san ta iya komai
kamar ke kikawomin ina tsananin bukatar me aiki gaskia
kuma xan bada ko nawa takeso indai har tanada tsafta
kuma ta iya aiki. Babu wadda tafadowa sa'adah arai sai
nazli dan tasan tama fita iya aiki da tsafta. To amma
yazatayi da waleed dan tasan naxli bazata iya rabuwa da
waleed ba daidai da minti 'daya bare taje har abuja
tabarshi amma xata gwada tagani. Cikin jin dadi tace,
Akwai 'kanwata kuwa tana gida ta ta'ba aure mijin ya
'bata tanada 'da 'daya kuma tanada tsafta fiye danima.
Farin ciki fal fuskar fannah tace, Yauwa maman abdul
kije gidan kijiyo idan zatayi aikin saiku taho tare sbd
saura kwana biyar mu koma. Meenah data fito 'daki
cikin wata 'bingilalliyar riga ta xauna tana tambayar firar
me sukeyi. Fannah tayi mata bayani nan itama tayi naam
da hakan tunda dan kula da 'bangaren rabin rantane
wanda tuni fannah tasan son da meenah kewa tameer
kuma tamata alkawarin ganin ya aureta insha allah. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰ πŸŒ•
⚜DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah
bbchoudiallo 136β†’140 Zaune suke atsakar gidan inna
na bubbuga 'dan redionta daya tsaya kwana biyu waleed
na kwance jikinta yana wasa da zaren tabarma Ita kuwa
tanka'den gari take ahankali tayi nisa cikin tunani.
Sallamar sa'adah tasa dukkaninsu 'dagowa suna kallonta
cikin farin ciki banda nazli datayi nisa cikin tunani.
Harsuka gaisa ta zauna inna na tambayarsu abdl data
baro nazli batasan me ake ciki ba. Cikin tausayi da
jimami sa'ada takalleta tamaido da kallonta ga inna tayi
mata bayanin aikin data samowa nazli ta 'dora da fadin,
Inna ina ganin kodan asamu ta rage wannan damuwar
datake ciki ta 'bacewar abban waleed kuma tasamu
tasaka waleed makaranta kodan yanayin rayuwa. Jinjina
kai inna tayi cikin gamsuwa da zancen sa'dah amma
kuma zaiyi wuya ita nazli ta yarda sbd baxata taba 'yarda
tabar waleed ba. Cikin jinjina kai tace, Kinsanfa nazli
waleed da tameer sune rayuwarta To tarasa tameer yaya
kike ganin xata iya barin waleed dan yanxu ko nan da
'kofar gida bata bari yafita wasa. Waleed ne yafada
jikinta da 'karfi yana cewa, Anty ki goyani. Dawowa tayi
daga dogon tunanin data fada sai kawai taga sa'adah
zaune da inna Ta saki fuska tana cewa, Anty sa'adah
yanxu kike tafe, Ya hanya? Inasu abdul? Cikin sakin fuska
ta amsa tana cewa, Nazli bazaki hakura ki fawwalawa
allah komaiba kullum sai 'karewa kike kinsa tunani
aranki fiyeda shekara nawa. Murmushin 'karfin hali
tasaki tana danne hawayenta. Inna ta gyara xama ta
zayyanewa nazli abunda yakawo sa'adah. Shiru tayi cikin
tsananin tashin hnkli amma kuma batajin zata iya
watsawa inna da anty sa'adah ido sbd sun taimaketa
fiyeda tunani To amma kuma waleed 'dinta fa? Anty
sa'dah ce ta katse mata tunani da cewa, Nazli nasan
waleed kike tunani To kadaki damu zamu dashi kanon
saiki barsa agurina asakasa mkrntar dasu abdl keyi ta
gwamnati. Shiru tayi tana 'boye hawayenta na tsananin
tausayin kanta da 'danta. Inna tace, Nazli kadaki saka
damuwa aranki wannan ba abun damuwa bane idan
bakyason zuwa baida matsala munsan halinda kikeji.
Share hawayenta tayi tareda rintse ido tace, Inna tunda
har anty ta tunada ni ta nuna kulawarta akaina ta taso
tazo bazanji dadi ba idan har nayi mata haka dan haka
inna inkinyi na'am zanje. Aa nazli kiyi tunani ba abun
takura bane. Bakomai inna aitunda aikin na 'dan
lokacine tace kuma idan naje naga ba matsala aisaina
dawo natafi da waleed 'din kuma aiba tabbata zanyi ba.
Sosai suka jinjinawa yanda ta daure tayi musu bazata
dan basuyi tunanin zata yarda haka da wuri ba. Harta
gama aikinta dare yayi suka kwanta akan gobe zasu wuce
hawaye take tanajin wani irin sabon ciwon 'batan
tameer 'dinta dakuma jin cewar abj za'a da ita Garin da
takejin tsanar shigarsa ayanxu sbd ba tameer 'dinta. Har
gari ya waye tayi sallah goge hawaye take. Saida rana
suka fito dan tafiya sai alokacin tasaki siririn kuka Inna
da itama takejin damuwar kewarsu dazasuyi ta lallasheta
suka wuce. Da maraice suka isa gidan me gidanta dake
zaune bakin gate na ganinsu yataso yana musu sannu
harsuka shige boys quatrs inda anan suke zaune. Sallah
sukayi sukaci abinci nan waleed yafara wasa dasu abdl
duk da sun girmesa. Sai bayan sallar magrib taja nazli
'din suka nufi sashen mutanen gidan dan gabatarda naxli
ga fannah. Zaune suke dukkaninsu a palon suna fira idan
kacire fannah dake 'daki tana waya dasu ammah daga
cairo. Cikin ladabi sa'adah ta gaidasu Amsawa sukayi
suna kallon nazli dake tsaye gefenta sunne dakai. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰
mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated
toβ˜† Husnah bbchoudiallo 141β†’145 Haj wanannan ita
'kanwata da haj fannah tace nasamo mata yar aiki. Kai
sunkuye nazli ta gaidasu suka amsa batareda sun 'kara
kallon gefentaba. 'Dakinda fannah take can sa'adah ta
nufa nazli na bayanta jiki duk amace. Tura 'kofar 'dakin
tayi tareda sallama tashiga suka tsaya nazli na bayanta
har lokacin kanta aduke yake. Ganinsu yasa tacewa
ammah dasuke waya, granny i will call you later inada
ba'ki. Kallon sa'adah tayi tana murmushi tace, Maman
abdul sannu da dawowa wanban itace 'kanwar taki?
Tafa'da tana kallon nazli. Eh itace gatanan nace muzo ki
ganta. 'Dagowa nazli tayi zasu gaisa wani mahaukacin
bugu xuciyarta tayi Tari mai 'karfi ya sar'keta su duka
sukayo kanta fannah tayi saurin bata ruwan swan dake
kan bedside drower. Kasa karbar ruwan tayi ta dafe
zuciyarta dake bugawa da 'karfi kamar xata faso ta
watse. Kallon tashin hankali takebin fannah dashi Saida
sa'adah ta jijjigata da 'karfi ta'dan sauke idanunta 'kasa.
Tameer,waleed dakuma wannan budurwar yarinyar
komai nasu zak babu banbanci kamar 'yan uku. Tabbas
datasan tameer 'dinta nada 'kanwa to da saitace wannan
'kanwarsace, Hakama dah ba ita ta haifi waleed ba to
dah tabbas saitace wannan itace ta haifesa. Yawu ta hade
dakyar ta gaidata Fannah tasaki ajiyar zuciya tana cewa,
Ohh wlh ni harna tsorata. Kallon nazli tayi tsaf taga
tabbas babu alamar 'kazanta atareda ita saidai talauci
daya koma'data. Gata budurwa kamarta kamar bata
haihuba dan badan sa'adah dakanta tace mata ta
haihuba da vazata yardaba. Gata Kyakkyawa sosai kamar
itama balarabiyarce duk da ta dafe ta 'kanjame hakan
hana fannah gano hakanba dan tayi mamakin sam ba
xubinsu 'daya da maman abdl ba. Shikenan maman abdl
tayi ba matsala saikuje tun anan ki kokkoya mata wasu
abubuwan kafin jibi xamu wuce kuma zan ringa bata
dubu talatin a wata. 😳zaro ido sa'adah tayi itakuwa nazli
bata wani damuba dan babu wani abu dayake burgeta
ko aikin zatayine kawai sbd zuciyarta dake ingixata
takuma rasa gane meyasa. Godiya sukayi suka fice suka
koma can gurinsu sa'adah. ********* Washe gari duk
aikin gidan tare sukayisa sa'adah na bata shawarar iya
xama da mutane. Sam su haj karima da haj bilki babu
wanda yagane nazli ko kusa sbd muguwar canxawar
datayi sannan kuma dama can ba wani cika ganinta
sukayiba tunda kullum tana sama. Sun fara hidimar
bikin daya kawosu dan gobene xaa daura aure amarya ta
tare kowa ya watse. Sosai fannah ta fara yabawa da halin
nazli sbd yarinyar akwai nutsuwa da tsafta ga wani irin
class datake dashi duk da tana 'yar aiki dan bata shiga
lamarin kowa saina ita data 'dauketa aiki. Murmushi tayi
tana cewa, B nasan zakaji dadin wannan abun danayi
mana tunda nasan sarai kana bu'katar mai kulada tsaftar
part 'dinka dan nafisat aikin yayi mata yawa da bazata
iyayinsa yanda kakesoba. Ranar dazasu wuce kuka take
wiwi akan rabuwa da waleed amma haka tayi masa wayo
suka fice. Aharabar gidan ta tarar dasu sun fito suka
shiga mota akayi airport dasu. Jirgi suka shiga babu bata
lokaci suka 'daga xuwa abuja. Da maraice suka isa motar
gidan haj bilki tazo 'daukarta Itama haj karima direbanta
yazo 'daukarta. Suma motarce tameer ya aiko 'daukarta
airport. Suna isa gidan kai tsaye 'dakinta ta wuce nazli na
biye da ita sbd babu kowa a gidan Dad baya 'kasar yayi
tafiya, Tameer ma bayanan yaje lagos meeting hakama
mum tana cikin gari sai dare zata dawo. Akwatinta da
nazli ta jawo mata tayi mata nuni data shigar dashi
bedroom. Kaiwa tayi tadawo ta tsaya gefe atsaye
bakomai hannunta dan fannah tace kada tadauko
kayanta zata siya mata kaya idan sunzo nan 'din dan idan
b 'dinta yaganta a yamutse zai iya cewa bayason aikinta
dan bayason 'kazanta ko ka'dan. Nafisa fannah takira da
landline 'din palonta tace tazo yanxu tana nemanta.
MUCH LOVE😍😍😍😍😍😘😘😘😘😘 πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH
GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 146β†’150
Turo 'kofar palon fannah 'din tayi tareda sallama ta
'karaso kusada nazli ta tsaya tareda cewa, Gani.
Hankalinta nakan wayarta Tana 'kakarin kiran b 'dinta
tace, Nafisa wannan wadda zata ringa kula da tsaftar
dakina da palona dana b ce kuma ni takewa aiki ba kowa
ba atakaice komai nawa dana b Is her responsibility ta
kula dashi. Daidai nan tameer yadau wayar ta mike tayi
'daki tana waya dashi. Atsanake suka juyo dan gaisawa
da juna Lokaci 'daya kamar wa inda wutar lantarki taja
kowanne yaja baya da sauri cikin mugun tsananin
ki'dima. Nafisa ce tayi 'karfin halin 'daga hannu tana
nunin nazli 'din tana cewa, Nazli kece? Ko kuwa idanuna
ne? Nazli datafi firgita sosai dan nan take tafara tunanin
kaddai fannah 'yar uwar tameer ce takawota gidan aiki?
Idan kuwa hakane kiketa zasuyi saita kaisu gurin tameer
Tameer 'din dabatasan inda yakeba Yanacan 'kilama
cikin mugun garari. Girgixata nafisa tayi da 'karfi jikinta
na rawa ganin sai zubar hawaye take ba magana. Murya
na rawa cikeda damuwa da tsoro tace, Nafisa inane nan?
Ina haj xeenat? Wacece wannan fannah 'din? Wane
gidane nan? Duk arude take watsowa nafisa tambayoyin
Itama nafisar arude take Kawai saita damki hannun nazli
tajata sukabar palon. 'Dakinta dake gurin 'kofar kicin
tajata ciki ta dannawa 'kofar key har alokacin duka
hankalinsu atashe yake su duka. Jiyowa nafisa tayi a
kidime take cewa, Nazli nan ba gidan kowa bane face
gidan alh zaid da iyalansa, Haj zeenat nanan acikin gidan,
Sun baro can gidan sun dawo nan ne tun bayan da alh
zaid yadawo yatarar da 'bacewarku yakasa zama
awancen gidan, Fannah 'kanwar sir tameer ce daya
dawo da ita nan tun bayan dawowarsa daya samu lapiya.
Tunda nafisa tafara koro mata bayanan hankalinta da
nutsuwarta suka fara barin jikinta amma Kalmar nafisa
ta 'karshe ita tafi dukan zuciyarta ta razanar da ita fiyeda
tunani. Kamar bebiya tafara nuni da hannu tana cewa,
Meer...meer...a..a...ina Meer...ya...ya... Ganin takasa
'karasawa dan a birkice take yasa nafisa ta gya'da kai
tace, Tabbas nazli sir tameer ya warke yanzu yana cikin
cikiakkiyar nutsuwarsa. Dr ibrhm yakira alhaji yace ya
bugesa da mota can hanyar wani 'kauye a kano Akayi
kasar waje dashi kuma yana farfadowa cikin hankalinsa
yatashi wanda kowa yayi mamakin hakan. Nazli babban
abun ba'kin cikin dazan fada miki yanxu shine SIR
TAMEER BAISAN KOMAI DAYA FARU LOKACIN RASHIN
LAFIYARSA

Please Login or Register in order to submit comment