Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lafiyayyar fatarta fara tas data bayyana
abu'dadden bayan rigarta sbd tuni gyalenta ya zame.
Wani kiss ya manna mata atsakiyar baya dayasata
numfashinta sha'kewa tajiyo da sauri tana fidda
numfashi da sauri da sauri Bai tsaya komaiba ya kai
bakinsa cikin nata yana bata wani mahaukacin kiss daya
kashe jikinta takasa kwatace saima lafewa datayi ajikin
nasa yana cigaba da kissing dinta. Kamar wasa taji yana
shafarta harda zura hannu arigarta amma sam takasa
kwace kanta dan bakaramin kashe mata jiki yayiba. Jin
suna shirin xubewane yasa ta 'dan tattara 'karfin dabaifi
cikin cokaliba ta xame tareda fadawa daki tashige toilet
da sauri tana maida numfashi. Da daddare bayan
sunkwantama har bacci yafara 'daukarta taji yanata juyi
ta bude idanu dakyar sbd bacci saitagansa ya dafe ciki
yanata juye juye cikeda axaba ta tashi zaune da sauri
takamosa arude tana kiran sunanta Yana dude idanunsa
akanta kawai saiya fixgota tafado jikinsa yana wani irin
nishi yafara kissing dinta yana shafa arude takeso tashi
amma sai maidata yake da karfi nan take wani irin tsoro
yakamata tafara kuka tana kiran sunansa dan tasan
tunda ba hankaline dashiba komai xai iya faruwa. 'Yar
Rigar baccin dake jikinta ya 'barka da karfi yana lugwui
gwuitata tako ina tana rixgar kuka duk karfinta amma
sam kamar wani mai cikakkiyar lafiya sbd karfin dataji
yanadashi. Tanaji tana gani yakusanceta adaren Yarabata
da budurcinta ta dunkule gefe tana kuka awahalce sbd
yanda ya nuna mata rashin tausayi sbd beda hnkali gashi
ya kusance a lokacin baisan waye shiba itada taso saiya
warke idan ya yadda ya karbeta amatsayin mata tukunna
amma yanxu agaba idan yajita ba budurwaba yaki yadda
da shine yakusanceta. Duk ta tuno da hakan wani sabon
kuka take saki sbd tsoron abunda xai iya faruwa agaba.
Shikuwa wani irin baccine yadaukesa cikin kwanciyar
hankali yake sharar abunsa fuskarsa cikeda annuri..... ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰
mamuh geee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE โ˜†dedicated
toโ˜† Husnah 41โ†’45 Amai taketa she'kawa kaman ranta
zai fita sbd babu komai acikin nata Ga rashin 'karfin jiki.
Wanko bakinta tayi tana dafa bango radawo 'dakin
tazaun 'kasa bakin gadon tana tsiyayar hawaye. Motsi
taga tameer nayi ta yunkura ta tashi ta isa kansa jikinta
na rawa takira sunansa Cikin rashin tsammani taga ya
bude idanuwansa awahalce Sbd ciwo dake cinsa
Ahankali kuma taga ya fara jijjiga idanunsa na juyewa
Ihu tasaki tareda dira kansa tana kuka mai karfi tana
kiran sunansa. Jitayi ya Shaketa da karfi Idanuwanta suka
firfito tana shure shure amma baida alamar sakinta
Shidewa take batunyi taji yasaketa yakoma yaxube
kwance yana jijjiga jijiyoyin kansa duk sun fito ya ri'ke
kan da hannuwansa yafara buga kan abango da karfi
yana ihu.. Kuka tasaki tana tashi Duk da bata gama
wartsakewaba daga muguwar sha'kar dayayi mata.
Hankali tashe take kallonsa kukanta na 'karuwa sbd
ganin yana buga kan nasa sosai harya fara jiwa kansa Da
sauri ta isa ta 'kankameshi tana kiran sunansa cikin kuka
'Kokarin tureta yake daga jikinsa amma ta 'kankameshi
ta'ki sakinsa sai kuka take. Ahankali taji ya daina ya sulale
'kasa xaune idanuwansa arufe. Xamewa tayi itama
zaunen agabansa tana ta'ba fuskarsa datayi jajir tana jini
tana hawaye tace, Meer meyake damunka? Meyasa ka
chanxa sosai? Pls meer kakoma yanda kake sbd zuciyata
da kwakwalwata neman tarwatsewa suke, Bansan
yazanyiba. Bu'de idanuwansa yayi sunyi jajir kamar
bashiba ya 'dorasu akanta yana kallonta awahalce. Tana
ganin yabude ido ta mi'ke da sauri ta dauko 'dan
'karamin towel da ruwan 'dumi tafara goge masa jinin
fuskarsa tana tanajin ra'da'din ganinsa ahaka. Idonsa
akan fuskarta ko 'kyaftawa bayayi ahaka ta goge fuskar
ta mike ta maida kayan tazo tashiga toilet ta ha'da masa
ruwan zafi a bathtub ta fito takamasa takaisa har cikin
ruwan. Suna fitowa ta zaunar dashi ta goge masa jiki
tasakamai kayan shan iska tazaunar dashi ta fice zuwa
'kasa dan samo masa abinci. Abincin aikinta takarbo
takawo masa dakyar ta lallabasa yaci sbd jikinsa da yayi
xafi sosai alamar xaxxabi. Kwantar dashi tayi ta lullubesa
takoma gefe tana kallon sauran abincin tanajin yunwa
amma baxataci ba sbd kada yatashi babu abunda zaici
duk da darene. Da wuri ta tashi tayi sallah tana idarwa
shima yatashi takaisa toilet sukadawo tasashi yayi sallah
yana idarwa wani sabon xaxxabin yataso masa
tamayardashi gado ta futa zuwa aiki. โšœโšœโšœโšœโšœ Gaba 'daya
rayuwar ta juye mata Da kuka take yini, Da kuka take
kwana, Sbd komai ya lalace mata Tameer gaba 'daya
baida lafiya Ga doke doke dayake wani lokacin yayita
farfasa kaya Idan kuwa ya damketa saita kusa mutuwa
allah ke kubutar da ita. Wani lokacin har falla mata mari
yake bakinta yayita jini. Idn kuma haukar ta kwanta to
kwana yake cikin matsanancin xaxxabi.. ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰mamuh geee ๐ŸŒ•
โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE โ˜†dedicated toโ˜† Husnah
bbchoudiallo 46โ†’50 Ta rame sosai tayi wani irin haske
wanda takesa ran 'kila jinine babu ajikinta Ta fige,ta
hargitse sbd wahala da yunwa ga tashin hnkalin tameer
da yanxu gaba 'daya tsoronsa take dan yanda alamun
cikar hauka keta bayyana ataredashi. Shi kansa tameer
yayi wata irin muguwar rama sbd yanxu gaba 'daya ko
abinci baya iyaci kota basa Rayuwar ta ida birkice masa
gabaki 'daya. Aikin bawa flower ruwa taketa famanyi Sai
sauri take tagama sbd mugun jirin datakeji duk da
bawani kuzari takedashiba sbd tuni tayi hannun riga da
lafiya. Batayi auneba taji Jiri mai 'karfi ya kwasheta ta
xube abun ban ruwan dake hannunta yayi sama yadawo
mata ruwan dake cukinsa suka xube ajikinta gaba 'daya.
Sanyin ruwan yashigeta sosai ga muguwar buguwar da
kanta yayi. Goge hawayenta tayi tareda daddafawa ta
mi'ke tana kallon kayanta dasuka jike ta nufi babban
palon dan xuwa sama ta chanxo kaya. Tana shiga palon
ta du'kar da kai sbd haj xeenat na palon hakimce tana
waya. Hanyar hayewa stair ta nufa tana kakkama jikinta
sbd sanyin A.C daya ciki palon gata kuma kayanta ajike.
Wani razanannen ihu taji haj xeenat tasaki ta juyo da
sauri har jikinta na mazari. Nafisa ma dake kicin aguje ta
fito hartana zamewa a tiles. Fizgo nazli tayi da wani irin
mugun 'karfi dan yanda tashin hnkali da ki'dima sukasa
idanuwanta rufewa Wannu ta 'dora akai tana kallon rigar
yadin dake jikin nazli ta kwanta ajikinta sbd ruwa ta
nuna cikin nazli jikinta na rawa murya asar'ke tace,
Me..me..mene..ne wannan? Nazli da nafisa atare suka kai
kallonsu ga kallon cikin nazli suka ga ya'dan taso ka'dan
Nafisa data fahimci me haj xeenat ke nufi itama ta waro
idanu cikin kidima da tashin hnkali. Nazli kallon cikinta
take tanason taga abunda ya 'daga musu hankali amma
bata ganiba bayan cikinta daya kumbura kadan wanda
take tunanin yunwace ta kumburar mata dashi dan tuni
ta lura da kumburinsa. Figitaccen marin da haj xeenat
tasakar matane yadawo da ita hnklinta kafin ta wartsake
marin takuma xabga mata wani wanda ya haddasawa
hancinta 'barewa da jini. Rufeta tayi da duka kamar
mahaukaciya cikin tashin hnkli kaman zatayi kuka take
fadin, Wllh kasheki zanyi, Bazan bari wannan abun
yafaruba koda zanyi yawo a tsirara, Bazan taba bari haka
tafaru ba, Allah ya isa tsakanina dake shegiya munafukar
karuwa. Ganin haj bata hayyacinta gaba 'daya yasa
nafisa doka shahada tayi kukan kurar 'kwace nazli tana
bawa haj hakuri Zaman 'yan bori haj xeenat tayi bakinta
na kumfar fitina da masifar tashin hnkli. Dakyar taja jiki
ta tashi daga kwancen tana hawaye hancinta da bakinta
suna fidda jini Sai kakkarwa jikinta yake dan bakaramin
duka haj xeenat tayi mata ba ga mararta dataji ta 'daure
nan take ta dafe ciki tana tsiyayar wasu hawayen. Rarrafe
take kokarinyi ta haye sama tsabar wahala Haj xeenat ta
xabura tsaye tayi kanta ta shakurota tajawota kamar
kayan wanki ta dawo da ita tsakiyar palon ta wurgar
tareda rarumo wayarta jikinta na rawa takira dr tace
maza maza yazo yanxu tana son ganinsa.. ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰mamuh geee
๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE โ˜†dedicated toโ˜† Husnah
bbchoudiallo 51โ†’55 Kafin dr ya iso kasa zama tayi
tafara safa da marwa afalon tana jin xuciyarta kaman
xatayi bindiga ta fashe. Baiwar allah nazli kuwa tuni
azaba da zazzabi mai mugun 'karfi ya dirar mata jikinta
babu inda baya karkarwa sai hawaye take tsayayarwa
dan har alokacin batasan abunda haj xeenat ke nufiba.
Minti goma sha biyar saiga dr yashigo palon Haj xeenat
tayo kansa tana nuna nazli da hannu tace, Dr dubamun
yarinyarnan dan banason xargina akanta ya tabbata.
Shima cikeda mamaki yakalli nazli 'din dakyau na tsawon
lukuta Tabbas amatsayinsa na dr yaga wasu lamomin
ciki atattare da ita tunkan ya duba Amma dandai su
tabbatar yamatso gabanta ya dukusa yayi mata wasu yan
tambayoyi amma ko magana takasayi sbd matsanancin
halinda take ciki. Roba yaba nafeesa yace, Kamata kuje
toilet inason fitsarinta yanzu. Hannu biyu nafisa tasa
takamata sukaje toilet 'din 'dakin nafisa dake palon.
Suna dawowa nafisa ta mi'ka masa ya karba da
hannuwansa daje cikin hnd gloves ya fiddo da pt strip
yasaka cikin fitsarin ya dangwalo ya rike yana kallo dan
ganin abunda result zai bayar. Duk wani numfashin haj
xeenat dake fita dakyar to 'daukeda tashin hnkli da tsoro
yake fitowa Sai addua take allah yasa kada result 'din ya
nuna positive. Ko 'kyafta idanunta batayi daga kan pt
strip 'din yawuma dakyar take hadiyesu. POSITIVE shine
abunda result ya nuna Kawai sai hawaye suka gani a
fuskar haj xeenat ta mike kamar guguwa tayi 'dakinta Ta
fito da damin kudi ta xubewa dr tana cewa, Gasunan
idanma basuyiba xan 'karama koma nawane
KACIREMUN SHEGEN CIKIN JIKINTA AYAU BASAI
GOBEBA. Nazli dr nafisa atare suka mike tsaye sbd tsoro
da bazatar furucinta Hardai nazli da furucin na haj yasa
ta fahimci abunda tun farko haj ke nufi harta kira dr
kuma ya tabbatar da cikine da ita har takeson axubar.
Bata taba saran zata iya mikewaba sbd axabobin ciwon
datakeji acikin jikinta Amma ta zabura ta mike cikin
tashin hankaki biyu Dana jin tana 'daukeda ciki dakuma
jin xa'a xubar mata dashi. Magana dr xaiyi ta 'daga masa
hannu fuska adaure tace, Deal ne xakayi kona nemi
wani? Damin Kudaden yakalla yaji bazai iya bari
suwucesa suje gurin waniba Koba komai idanma baiyi ya
tabbatarda saitayi tunda tayi niyya. Tattara kudin yayi
yana xubawa ajakar kayan aikinsa dayazo da ita yana
cewa, Nafisa kamata kusameni amota muje asibiti yanxu
na wankosa waje. Ajiyar xuciya haj xeenat tasaki tana
wani shu'umin murmushi. Kamar wata rakumi da akala
takoma tanajin wani radadi daya danne zuciyarta Takasa
bude baki tayi magana sai hawaye dake gudu a fuskarta
nafisa tajata suka tafi. Bushewa xuciyarta tayi dan itama
gwara acire mata cikin dan batason ta haifosa yaxo ya
tarar da wulakantattar rayuwar dasuke ciki itada
mahaifinsa kuma batada tabbacin idan yazo duniya
ubansa xai karbesa idan ya warke. Tunani mai xurfi
nafisa tashiga tanajin bazata iya bari axubar da magajin
wannan babban familyn me tarin dukiya ba Amma tana
tsoron yiwa dr magana yakoma yafadawa haj. Har suka
kai asibitin suka 'dunguma xuwa office 'dinsa suka xauna
shikuwa kasa xama yayi yafara kai kawo yana tunanin
Tabbas idan yazubar da cikin jikan alh zaid to yaxama
cikakken maha'inci kuma butultacce sbd alh xaid ne
sanadin duk wani matsayi dayake akai yanxu Afterall yafi
kowa sanin alh zaid da tameer suna tsananin bukatar 'da
jafin duk ashiga cikin wannan halin na ciwon tameer.
Dakewa nafisa tayi ta mike taje gabansa ta tsaya takallesa
cikin ido tace, Idan xuciyarka batason yi kada kayi Kuma
ka tuna komai daren dadewa gaskia xata iya bayyana
alokacin da baka tunani. Shin me xamu samu idan muka
cutatar da rayuwar wa'inda suka taimaki rayukanmu
suka kyautata rayuwarmu. Dan allah inason kayi amfani
da shawarar da zuciyarka ke baka kadaka cutatar da
cikin nan๐Ÿ™ ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰mamuh geee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE
โ˜†dedicated toโ˜† Husnah bbchoudiallo 56โ†’60 Kallon
nafisa yayi yana nazarin kalamanta kuma sun shigesa
sosai ya zauna tareda huro iska Yace, Tabbas bazan iyaba
sbd alh da tameer bazan iya cutatar da gudan jinin suba
To amma kobanyiba haj bazata zaunaba saita tabbatarda
babu cikin nan kuma yanxu bama cikin kadaiba tunda
harta gane tameer zai iyayin ciki ayanayin dayake ciki to
tabbas zata 'dauki mummunan mataki akan hakan.
Kukan nazli ne ya tsaidasu sbd kukane take rerowa mai
ciwo daban tausayi sbd ganin yanda rayuwarta takoma
dakuma rayuwar abundake cikinta tun baizo duniyaba.
Durkusawa tayi gaban dr tana tsiyayar hawaye tace, Idan
har halaccin da daddy yayima kakeson mayarwa to Dan
allah kakiramunshi yasan halinda 'dansa yake ciki, Meer
yana cikin tsananin halinda yake bukatar taimako Amma
babu mai taimaka masa, Dan allah ka taimaka kakirasa
koxata shiga. Duk yanda sukaso su samu daddyn basu
samesaba har suka gaji. Kallonsu yayi bayan yayi
scanning 'din cikin yafara musu bayani, Yanzu zan baki
maganin karin jini saiku fadawa haj anxubar da cikin Illa
dai abu 'daya dazan fada muku shine kushirya tarbon
tashin hnklin dazai biyo baya idan cikin ya fito gaba
'daya Dan ni nanda sati mai xuwa zanbar 'kasar zuwa
wani aiki. Babu me cikakkiyar nutsuwa suka dawo gidan
sbd gudun kadata gane. Tana ganinsu tasaki murmushin
'keta dajin 'dadi tareda jinjinawa dr. Shikuwa bai tsaya
dogan zanceba yatafiyarsa dan gaskia yana shakkar haj
zeenat sbd rashin imaninta. Har 'palonsu nafisa takaita
tasauko cikin tunanin bala'in dazai nufatosu nan gaba
idan haj xeenat tagano gaskia. Kwance ta tarar dashi
idonsa biyu yabita da kallo da kyawawan idanunsa
batasan sanda taje da gudu ta fada jikinsaba tareda sakin
'dan siririn kukan tausayinsu dakuma wani jarababben
sonsa datakeji dakuma cikin jikinta daya kasance
tsotsonsane. Shima rungumeta yayi yana lumshe ido
akaro na farko taji yace mata, Shihhhhhh. Cikin farinciki
da hawaye ta 'dago tana murmushin datama manta ya
ake yinsa ta 'kara 'kankameshi tanajin sonsa. Wanka
sukayo sukayi sallah tare sukaci abincinta na aiki.
Mikewa tayi zata fita yayi saurin dawo da ita jikinsa yana
kallon 'dan bakinta Batai auneba taji nasa bakin anata
yana bata wani irin kiss me dadi. Sam batayi yunkurin
kwacewaba harya fara shafarta yana zura hannuwansa
cikin rigarta nandanan yafice hayyacinsa ya sureta sai
gado. Sosai suka raya daren wanda rabonsu da zama ma
kusada juna harta manta bare wata soyayya. Tund safe
cikin bacci taji ana 'barin kaya Ta tashi afirgice
Idanuwanta suka sauka kan 'dakin Ya fasa komai na
'dakin ya hargitsashi ta hango jini akasa da sauri ta diro
gadon jikinta na 'bari ta xari riga tasaka tayi palon a
tsorace aiko komai na palon ya fasa duk yajiwa kansa
rauni sbd hannuwansa jini suke fitarwa sosai ga
'kafafunsama haka. Juyowa yayi suna hada ido ta ha'diyi
wani yawu da 'kyar sbd gaba daya kamannunsa sun
chanxa idanuwansa sun birkice Tafara 'kokarin ja da
baya dan ganin ya nufota. Cikin rashin sa'a ta taka
kwalba cikin abubuwan daya fasa ta fadi 'kasa aiko nan
yahau jibgarta da 'kafa yana taka kanta Tun tana motsi
harta daina ta sume agurin. ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰mamuh geee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ•
Na MAMUH GEEE โ˜†dedicated toโ˜† Husnah bbchoudiallo
71โ†’75 Tapia suke ta 'kankame hannunsa tana waige
waige jikinta sai 'bari yake har lokacin ga mugun zazzabi
tanaji Shi kansa tameer ciwone ajikinsa sosai dan layi
kawai yakeyi idanuwansa a lumshe. Tafia kawai suke
batareda tasan inda suka dosaba Babban tashin
hankalinta baifi dataga dare yafara tsala musuba ga
tameer daya fara ficewa hayyacinsa yana 'kokarin xube
mataba ga jakar kayansu haka itama ta galabaitu
matuka. Wata motace ta 'dan tsaya gabansu razana tayi
tareda ja da baya tana 'kankame tameer. Wani
wurjigegen inyamuri tagani cikin motar yace, Madam do
you need a taxi? Kallonsa tayi cikin tsananin tsoro tana
hada gumi Kafin tabasa amsa sukaga tameer ya sulale
agurin. Sakin jakar hannunta tayi aki'dime ta cakumosa
tana kwala kiransa. Idansa ya'dan bude awahalce
akalleta yamaidasu ya lumshe. Da sauri ta bude motar
tana kokarin tadashi jiki na rawa Direban ganin yanda
take kiciniyar kamasa duk a rude takasa ya fito ya kama
matashi suka sakashi cikin motar yasaka musu jakarsu
tareda shiga motar yace ina zai kaisu? Shiru tayi tana
hango tashin hnkalin dazata tadda amma bayanda ta iya
dole can xata kodan ganin tun yanxu sun fara yagayyara
ga tameer na..... "Kano. Tafada murya na rawa hawaye
na silalowa daga idonta ahankali. Direban kallonta yayi ta
mirrow tareda maimaita kano cikin wawuyar hausarsa
kafin ya girgixa kai ya tada motar da nufin kaita tasha
tunda yasan shidai ba kanon zashiba. Har aka kai tashar
bata hayyacinta sbd hawayen daketa zirarowa daga
idanunta tana kallon fuskar tameer dake nuna yana cikin
tsantsar ciwo. Suna isa tashar ya suka fito ya karbi dubu
daya yatafiyarsa. Duk da darene amma akwai mutane
sosai atashar sunata sha'anin gabansu. Rabewa sukayi
bakin wata rumfa atsorace take gaba 'daya banda kuka
ba abunda take. Tana kallo ahankali bacci mara da'di
ya'dau tameer.ta cusa kanta tsakiyar gwiwowinta tana
rero kukan tausayinsa san gwara ita tasaba da wahala
amma shi baisan wata wahalar rayuwa ko 'dayaba Gashi
yanxu batasan wace irin rayuwa zasuyi ataredasu babah
ladingo. โšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœ NAZLI ADO BUBA TAKAI shine
sunanta, Mahaifinta adamu abubakar 'dan asalin takai ne
kuma maraya daya taso hannun kakarsa dan yarasa
iyayensa tun yana yaro. Yayi karatu dai dai misali dan
headmaster ne primary school 'din 'yan 'kauyen.
Matarsa 'daya ladidi wadda ake kira da babah ladingo Da
'ya'ya biyu bubah wanda yaci sunan headmaster malam
ado,sai idi. Daga ladingo har 'ya'yanta babu me hali na
kirki ko mutunci. Sam su bubah banda sace sace da
'kwaya basusan komaiba wanda ladingo ita ta lalata
abunta danko malam bai isa yayi maganaba akansu.
Raihanat budurwar buzayen nijar dasukayi gobara suka
rasa dukiyoyinsu da gidajensu ta rasa iyayenta sai
aminin mahaifinta 'dan uwan me gari dashima acan
yake kuma yayi basa rashin saiyazo da ita tareda matarsa
da 'yarsa 'daya asmah ya hadasu ya rike. Basu wani
jimaba agarin ya aurar dasu Ita raihanat ga headmaster
ado dake sonta sosai sai ita asmah acan 'kauyen gaba
dasu ga wani 'dan dagacin 'kauyen. Bayan aurensu da
wata biyar allah yakarbi ransa me 'dakinsa ta tattara ta
tafiyarta garinsu itama. Raihanat dai takoma batada
kowa sai mijinta wanda gaba 'daya rayuwar gidan sam
batada da'di ko kwanciyar hankali dan ladingo da
'ya'yanta sun saka gaba da tsangwama ga cuta iri iri gefe
'daya ga aminiyar ladingo wato iya jummai da kullum
tana gidan suna cutatar da ita. Iya jummai mijinta ya
jima da rasuwa sbd ba'kin cikinta dana 'yayanta iro da
karima. Raihanat nada hakuri da biyayya sosai shiyasa
mijinta ke tsananin sonta dan agurintane kawai yakeji
sanyi. Ahaka ta haifi 'yarta ta fari nazli mai kama da ita
sosai sak buzuwa. Haka 'yarta girma babu ranar
dazasuce sunyi farin ciki a rayuwarsu ta gidan sai gashi
garin haihuwa ta biyu su ladingo suka rufeta a'daki tana
nakuda tayita neman taimako tana rokonsu amma suka
'ki budeta saida suka tabbatar da axaba ya kasheta. ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰
mamuh geee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE โ˜†dedicated
toโ˜† Husnah bbchoudiallo 66โ†’70 Zaune take bakin
gadon dayake kwance tana shafa lallausan gashin kansa
dake kan cinyarta ahankali idonta akan fuskarshi tana
kallo shima ita yake kallo yana lumshe idanun marasa
lpia. Gabanta ke'dan faduwa akai akai dan haka takasa
tashi tabar gurinsa. Hawayene suka gangaro daga idonta
ahankali suka sauka akan fuskarsa Ya rintse ido sbd jin
afuskarsa suka xuba amma a xuciyarsa yaji zafinsu.
Hannu ya 'dago yana rawa ya shafo fuskarta tareda
girgiza mata kai alamar ta daina kuka. 'Karasa rushewa
tayi da kukan ahankali tana cewa, Meer inajin wani irin
nauyi a xuciyata dana kasa ganewa, Meer idan narasaka
bansan ya rayuwata xata komaba, Pls meer kada katafi
kabarni, Kabari na rayu dakai dan rasaka daidai yakeda
tabarbarewar rayuwata. Meyasa nakeji kamar wata rana
xaka barni? Meer pls dnt ever leave me sbd kaine
rayuwata da abunda zan haifa. Yanda take kukan ne tana
maganganun yasa ya tashi zaune dakyar tareda jawota
jikinsa ya rungume tsam. Saidata sha kuka sosai har
kukan baya fita kafin tafara sauke ajiyar zuciya ahankali
har bacci ya 'dauketa. โšœโšœโšœโšœโšœโšœ Kaida kawo take a tsakiyar
makeken 'dakinta. Xuciyarta a cunkushe take ta rasa
gasgata abunda xuciyarta da shawarar aminanta suke
bata. Ingizata xuciyarta takeyi akan tayi gaggawar
aikatarda 'kudirinta akansu. Zama tayi bakin gado tareda
'bata fuska tana cewa, To idan nakoresu ai zasu iya
dawowa wata rana hardai idan shegen balaraben yaron
nan ya warke. Zabura tayi tana cewa bazai yiyuba.
Wayarta ta 'dauka rai abace ta nemo wata number takira
tana huci. Ringin biyu wayar tayi aka 'dauka Cikin
'kosawa tace, Lilo ya alhajin yake? Lpia klau haj saidai
ciwonsa gaba yake. Kyalesa indai kuna basa abinci.
Yanxu dai akwai aiki na musamman daxakuyi a daren
yau. So nake kuzo da daddare inason ku aika
mahaukacin 'dansa barxahu tareda shegiyar aljanar
matarsa kuma banaso asamu matsala. Angama haj
kawai yanxu naji alert. 'Kokarin sakin tray 'din hannunta
take nafisa tayi saurin tarewa tana zare idanu tareda
ha'de wani wahalallen yawu tana dam'ko hannun nazli
sukabar 'kofar 'dakin sbd datayi 'barin kayan to tabbas
data jawo musu masifar datafi wadda sukaji. Kicin suka
koma ko wanne jikinsa na 'bari tsabar tashin hnkl Nazli
ta saki wani irin kuka tana sulalewa 'kasa Nafisa ma
tsabar rudu kukan take dan iya ka'duwa ta ka'du da
abunda sukaji haj na fa'da. Kuka take mara sauti sosai
kamar ranta xai fita Jikinta har karkarwa yake tana
sha'kewa. Cikin tsananin tausayi nafisa ta dafata murya
na rawa tace, Na..na..nazli inaga kija sir tameer ku gudu
wani guri nesa da inda bazata taba sanin kuna canba,
Nazli yanxu kece komaina sir tameer tunda mahaifinsa
babu labarinsa, Kodan kasancewarsa UBAN 'DAN DAKE
KWANCE ACIKINKI. 'Daki taje da sauri tadawo rikeda
kudi masu 'dan afki ta kamo hannun nazli ta dam'ka
mata su tana hawaye tace, Ki tafi dashi nazli,i trust you,
Nasan ke kadaice xaki kula dashi fiyeda kanki. Tayar da
ita tayi jiri na 'dibarta tana sheshshekar kuka suka hay
stairs 'din takaita har 'kofar palonsu ta juya. Gadon
dayake kwance yana bacci ta nufa tana toshe baki sbd
kukanta dayake tsananta Ta xube akansa tana sakin
kukan gaba 'daya. Sosai ta risga kuka cikeda tausayin ya
rayuwarsu zata koma idan sukabar gidan, Ya zatayi da
tameer daba lafiyane dashiba. Ina suka dosa? Yazatayi da
kanta,tameer dakuma abunda ke cikinta. Kiran sallar
magrib yasata ta mike tana goge hawayenta tareda
fa'dawa toilet tayo alwala tayi sallah Ta tadashi takaisa
yayo alwala yayi sallah. Kayansu ta zuba a akwati 'daya
tana danne kukanta ta kama hannunsa tana kallon 'dakin
hawaye nabin fuskarta tajasa suka fice gidan batareda
kowa yaga fitarsuba danko masu gadi suna cikin
masallacin gidan suna sallah.. ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰ mamuh geee ๐ŸŒ•
โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE โ˜†dedicated toโ˜† Husnah
bbchoudiallo 76โ†’80 Rayuwar nazli ta tagayyare danko
wanka ladingo bata iya yi mata sai idan malam da kansa
yayi mata dan ya'dauki son duniya ya 'dora ga 'yarsa
nazli. Tana isa sakawa makaranta yasakata duk zashi aiki
tare suke zuwa su dawo tare ahaka harta girma tasan
kanta tanada shekara goma sha 'daya ya rasu yabarta
cikin muguwar ukubar ladingo. Ta taso cikin wahala da
azaba. Duk wani aikin gidan ita keyinsa, Ga sana'ar
abincin ladingo itake 'dorawa duk da aikin yafi 'karfinta
kuma idan tayi ba daidaiba a aikin buba ko idi take sawa
ko iro 'dan iya jummai su laka'da mata dukan da saita
gagara motsa koda 'dan yatsanta. A mataccen 'dakin
mahaifiyarta take zama bayan duk sun kwashe tarkacen
kayan 'dakin suka barta da 'yar matacciyar tabarma ga
'kofar 'dakikn sun cire. Ahaka ta rayu ta girma acikinsu
har wannan auren 'kaddarar yahau kanta.
โšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœโšœ TAMEER ZAID OMAR Alh zaid
omar 'dan asalin jahar maidugurine. Yanada tarin dukiya
mai 'dinbin yawa wadda ya gada ga iyayensa dakuma
'karin tashi daya tara takansa. Alh zaid omar su biyu
kacal iyayensu suka haifa kafin su rasu shida yayarsa
dayafi so fiyeda komai wato HAJ NURATU. Haj nuratu
nason 'dan uwanta itama fiyeda komai wanda duk
wandake tare da ita zai sheda hakan. Haj nuratu na aure
a 'kasar cairo sbd mahaifin mijinta alh kabeer balaraben
can ne sai mahaifiyarsa yar maiduguri. Zamanta acan
yasa shima alh zaid yamaida rabin business 'dinsa acan.
'Yayan haj nurat biyu isma'il da ammar. Ganin da gaske
alh zaid baida niyyar aure yasa tasakashi agaba harda
hawayenta akan lallai sai yayi aure Hankalinsa ya tashi
sosai ganin yayarsa na hawaye Ya lallasheta tareda bata
zabin matarda taga ta dace dashi. Farin ciki tayi sosai
dan dama akwai 'yar 'kanwar surukinta datayi masa
sha'awarta balarabiyar asalin cairo 'din mai suna NYSSA.
Bawani dogon zancen suka amince da juna haka
iyayenta basuyi jaba sbd sunason nurat kuma suna yaba
halayenta dan haka sunsan 'kaninta xaiyi kirki kamarta.
Aurensu da shekara bakwai nyssa ta haifi 'danta namiji
balabe sak ga tsantsar kyawu Aka saka masa suna
tameer. Soyayya da gatan da tameer yake samu ba
ka'dan bane sbd takowane 'bangare kowa sonsa yake
bama kamar iyayensa da haj nurat dakejinsa fiyeda
'yayanta Ga 'bangaren dangin nyssa masu tashen dukiya
mai 'dibbin yawa agarin suma tsananin 'kaunarsa suke.
Haka ya girma a sangarce harsaida yayi shekara goma
sha biyar kafin mum 'dinsa takara haihuwar mace taci
sunan FANNAH. Tsabar dukiyar alh zaid yasa yayi suna
sosai ako ina wanda gidan tashar gatanmu channel dake
kaduna nigeria ta aiko da ma'aikatanta na musamman
dan samun ganawa dashi. Ranar daya gana dasu
ma'aikatan nakomawa masaukinsu xeenat takasa zama
saikai kawo take tanajin wani irin kwa'dayi da son alh
zaid yayi mata dirar bomb axuciya wanda daga 'karshe
ta 'dau mummunan 'kudiri akansa. Kodata dawo nigeria
gidan aminiyarta haj kareema ta nufa ta fesa mata aiko
nan suka 'dunguma gidan abokiyar cin mushensu haj
bilki daganan suka 'dunguma gurin boka. Bayan uwar
dukiyar dasuka kashe aikinsu yafaraci dan kuwa tana
kiran wayarsa kiran farko daya 'dauka tafara masa
bayanin kanta ya datse kiran sai gashi bayan kwana biyu
dakansa yakirata. Sannu sannu aiki yafaraci saiga alh zaid
harda zuwa nigeria gurin xeenat inda anan ne sukayi
aikinsu na 'karshe akansa wanda baikomaba saida
aurenta akansa. Dukiya da daular daya sakar matane
yasa nanda nan ta chanxa tazama hamshakiyar haj dan
dama can ba yarinya bace ta'dan kwana biyu. Dunia
tadawo musu sabuwa itada aminanta da mahaifiyarta
Haj sabuwa da itama boss ce harkar bin bokayen kafin
mijinta ya yarasu. CAIRO Sannu ahankali suka fara ganin
chanji daga alh zaid dan yanxu akai akai yake xuwa
nigeria kuma yakan jima acan. Tsananin son dayakewa
matarsa da 'dansa harma da 'yar uwarsa bai rageba
shiyasa basu kawo komaiba arai sai tunanin kila business
dinsane. ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰mamuh geee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE
โ˜†dedicated toโ˜† Husnah bbchoudiallo 81โ†’85 Ganin
daular da haj xeenat take cikine yasa suka 'kulla
'kullalliyarsu suka aika mijin haj bilki barzahu ta aure
mijin 'yayar wata 'kawarsu gurin aiki mai tarin dukiya
shima dake abuja bayan sun kore matarsa daga gidan.
Haj kareema ma wani minister ta aura bayan ta tarwatsa
matarsa da 'yayansa ya koresu ta haifi 'yarta meenah
Wadda sam batada tarbiya ko kadan. Ganin haryanxu
yanason matarsane yasa haj zeenat yanke shawarar
xuwa harcan ta tarwatsa zaman tunda anyi aikin har
angaji yakasa ciresu aransa koda da minti 'dayane. Tana
isa cairo kai tsaye gidan yayarsa tafara isa cikin iko da
takama.

Please Login or Register in order to submit comment