Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Zaunawa tayi tana murmushin 'keta saiga haj
nurat 'din tafito sbd ansanar da ita tanada bakuwa.
Kallon mamaki takebin xeenat dashi kafin tadan saki
fuska tana mata sannu suka gaisa aka kawo mata drinks.
Ruwan sanyi ta kurba tareda crossing legs tana girgixawa
tace, Sunana haj xeenat zaid omar. Kallonta haj nurat
tayi dakyau amma bataga alamun hauka atareda itaba
saita 'dan saki murmushin ya'ke tace, Allah sarki wane
zaid omar 'din? Zaid omar 'kaninki Ni matarsane tsawon
shekara uku kenan ina zaune a abuja nigeria. 'Kuri
tayiwa haj xeenat tanason tayi tunani 'kwakwalwarta
takasa dan ita takasa ma tuno me xeenat 'din tace tsabar
rudani. Kafin tace wani abu saiga alh zaid sun shigo shida
matarsa dasu tameer Tasaki ajiyar zuciya tana kallonsa
dan bakaramin dadin ganinsa tayiba alokacin.
Idanunwansa na sauka kan xeenat ya washe baki duk da
ya razana sosai da ganinta. Ganin yanda yasaki fara'a be
yasa suka kalli juna cikeda mamaki. Haj nurat ta'dan
ha'de fuska tace, Zauna ka fadama wacece ita. Zama yayi
yana kallon fuskar nyssa dan makaramin so yake mataba
Yamaida kallonsa ga yayarsa murya a'dan tsarge yace,
Kuyi hakuri naso na bayyana mukune yanda xaku
fahinta amma kuma sai abun yazo ahaka Xeenat matata
ce, Munyi aure shekara uku yanxu. Kallonsa suke dakyau
ba alamar wasa axancensa bari makamancin hakan. Iya
'kuluwa sun 'kulu Nyssa ta mike tareda sa'ba fannah
akafada ta fice afalon batareda ko gefensa ta sake
kalloba. Haj nurat ma mikewa tayi tashigewarta tabarsu.
Mikewa yayi yabi bayanta ta dakata da tafiya ta juyo ba
'bata lkc tace, Tabbas bani bakai idan har kana tareda
waccar matar. Zaro ido haj zeenat tayi dan tana labe
tana jinsu. Lallai zanyi maganin wannan matar tafada
tana 'kafa. Tashin hnkli akayi sosai amma aikin asiri yaki
bari yasaketa ga nyssa tuni tafara ciwo sbd mugun 'kullin
da haj xeenat tazo dashi ta barbada mata a palo sbd
'karfi da yaji suke zaune gida 'daya. Tameer bayanan
yana paris karatu Kwanciyar hankali ta 'kauracewa
familyn dan nyssa ciwo ya munana ga xeenat taki
komawa Shikansa alh ya susuce gaba 'daya ganin
masoyiyarsa kwance rigis. Mahaifiyar nyssa ita takarbi
fannah tadawo hannunta kafin nyssa ta warke. Shekara
'daya tana jinya allah yakarbi ranta wanda kuma gurin
xuwa gaisuwar munafincine su haj bilki suka zomata da
wani mugun aikin daya haddasa fitina gaba 'daya a
familyn dan kuwa 'kiyayya mai zafi ta shiga tsakanin
dangin nyssa dashi dan gani suke shine sanadi. Hakama
'yar uwarsa haj nurat tayi mummunan fushi dashi
tanajin wata irin tsanarsa shima haka yakejin duk
tsanarsu dansun tsani matarsa haj zeenat. Da haka ya
tattara yabaro cairo yakoma paris gurin 'dansa dan
yanda yakejin tsanarsu ko fannah dake gurinsu bazai iya
zuwa ya kar'ba ba. Rayuwa tayiwa haj xeenat yanda
takeso dan tuni tazama haj babba ga hutu da dukiya
dasuka mufun ratsata. Matsalar farko dasuka fara samu
itace 'dansa tameer ya girma yazama saurayi yafara
'dorasa adukiyarsa sai abun yafara damunta sbd yanda
ta tsani yaron dan ya'dau son duniya dana nyssa ya
'dora masa. Tameer saurayine bamai wasu shekaruba
dan duka duka shekarsa ashirin da biyar xuwa da
bakwai, Yarone 'dan gata fiye da tsammani, Balarabene
sak dan mum 'dinsa ya 'dauko akomai. Dad 'dinsa baya
boye sonsa agaban kowa. Ganin 'kiyayya ta ginu tsakanin
haj zeenat da tameer yasa ya tattarata yamaidota nigeria
dan yanxu babu wani sauran sonta aransa kawai dai
zaman ake hakama 'kiyayyar 'yan uwansa ta ragu aransa.
Barinta 'kasar yasa tameer yakoma cairo dan kula da
kamfunan dad 'din nacan wanda wata sabuwar 'kauna
da gata yatashi acan dan kuwa dan lelensu yazama
wanda hakan ne yasa yake asangarce duk da ya girma
amma idan ka gansa a waje ya iya ha'de gira ba wasa.
Zamansa a cairo yasa komai ya cahanxa masu
rayuwarsu suke a nutse sai lokaci lokaci yakanje nigeria
gurin dad 'dinsa duk da shima bai cika zama a nigeria
'dinba. Wani zuwane dayayi meenah 'yar haj kareema
tagansa tace ita duk duniya shi takeso Shikuwa harya
koma baimasan dazamantaba. Awata dawowar ne suka
aikata masa mummunan aikin tunanan yafara 'dan
ciwon kai kafin ya tattara yakoma Aiko yana komawa
ciwo ya tabbata hauka. Sannu ahankali abu yaki sauki
'Karshe dai dad 'dinsa yazo yadau 'dansa yafara yawon
'kasa 'kasa dashi amma an tabbatar masa da
kwakwalwarsa ta juye. Nijeria ya dawo ya damka kula da
'dansa ga dr sufyan wanda ya budewa babbar asibiti
yana sakar masa dukiya. Ahakane wani malami ya
tabbatar musu da sammune. Anyi neman maganin
sammun har angaji ba wani sauki ga masu kula dashi sai
guduwa suke sbd wahalar kula dashi shinefa karshe
akayi masa aure dan asamu akula dashi dakyau kafin ya
warke ya za'bi zama da matar ko rabuwa da ita.
TOFAH..... πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE
β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 86β†’90
TASHA...... kiran sallar asuba yasa ta'dan 'dago kanta tana
kallon masallacin cikin tashar Bata gani sosai sbd
kumburin da idanuwanta sukayi dan tsabar kukan
datake sharba har asuba 'din. Maida kallonta inda
tameer ke kwance tayi tana kallon yanda sanyi ke ka'da
jikinsa yatakure yana fidda numfashi da sauri da sauri.
Duddubawa tayi taga inda ake diban ruwa taje ta 'debo
tadawo tayi alwala ta tada tameer da 'kyar tayi masa
alawa sukayi sallah. Gari na'dan fara haske taga anfara
gyar motoci zasu fara lodi ta mike tareda kamosa ta'dau
jakar kayansu suka nufi motocin. Da sauri wani yayo
gurinsu yace ina zasu murya adashe tace kano. Karbar
kayansu yayi yasaka a mota suka shiga atsorace sai
rabon idanu take sbd kallon da aketa binsu dashi dan
ganinsu kamar larabawa ita buxuwa da zuriar hausawa
shima larabe da xuriar hausawa. Tameer gaba 'daya
afirgice yake duk da baida lafiya Ganin ana kallonsu saiya
'kankame nazli yana lafewa ajikinta Mutane mezasuyi
inba dariyaba ganin 'katon saurayi dashi yana boyewa
bayan mace Gashi a fuska kamar jarumi. Dariya ake
musu sosai harda tsokanarsu aka fara tana hawaye tayi
saurin jansa suka fada motar suka xauna yana
'kankameta. Hawaye take sosai har motar tacika suka
tashi bayan ankarbi kudin motarsu. Lafewa tameer yayi
ajikinta yana kallon kyakkyawar fuskarta data kumbura
Ta'dan kallesa cikeda fargabar abunda zasu tarar atakai
dakuma tsoron kada cimar can tayi masa mummunar
illah akan wadda yake ciki. Da rana tsaka suka isa kano ta
fito rikeda hannunsa tashin hankalinta na tsananta ganin
sun kusa isa kenan. Motar 'kauyen takai suka shiga daga
cikin tashar Ga yunwa da 'kishirwa dake damunsu su
duka hardai ita me juna biyu da duk kaganta kasan
cikine da ita. Karfe hudu suka isa takai ana saukesu ta
rushe da kuka jikinta na mazari dan tun bata isaba
takejin wani irin tsoro na shigarta musamman na cikin
jikinta dabatasan yaza'ayiba. Da 'kafa suka isa 'kofar
gidan taja ta tsaya cak shikuwa tameer sai shige mata
yake sbd tsoron yaran dake biyarsu tun a hanya suna
cewa lah buxaye. Hawayen idonta suka gangaro ahankali
tasaka hannu na rawa ta shafesu tareda doka shahada
tashiga tsakar gidan. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Zaune suke a
tsakar gidan sunacin gyada suna rangada fira itada
aminiyarta ta kullum wato iya jummai sai karima 'yar iya
jummai dake 'dakin babah ladingo itada bubah suna
firar soyayya cewar su babah ladingo amma kuma
banda tumurmuxarta ba abunda yake a'dikin kuma sarai
suna jiyosu amma sai firarsu suke cikin nishadi. Ganin
larabawa a gidan yasa suka mi'ke atare suna kallonsu
Babah ladingo tayi saurin juyawa zata 'dauko tabarma
tana fadin, Sannunku ba'ki kushigo. 'Ko'karin shinfida
tabarma takeyi iya jummai data 'kurawa nazli dake
hawaye ido tana mata kallon 'kurulla ta waro ido da
'karfi tace, NAZLI Kallon iya jummai tayi murya 'kasa
'kasa tace, Jummai wace nazli kuma salon ki kore
manasu 'kila ba'kin arzikine. Da 'karfi taja bushashshen
hannun ladingo takaita gabansu tana duba kigan...... Bata
'karasaba sbd cikin jikin nazlin data gani. Tattakewa
babah ladingo tayi ta zuba ihu tana kiran jamaa suzo su
tayata ganin ankoro nazli da cikin shege datayo da
aurenta. A kidime su bubah suka fito yana gyara zaman
wandonsa suma a firgice suke kallonta sai alokacin suka
lurada balaraben dake bayanta nan take suka rufeta da
duka har ita harshi Ma'kabta suka taru ana kallo tareda
yin tir da halin nazli datayo cikin shegen aka korota
'karshema cewa sukayi mai gadin gidanne buzu irinta
yayi mata ciki aka korosu tare. Labari yakai kunnen me
gari ya aiko 'dan aike da wuri akan adaina dukansu
akawo masasu yanxu yanason ganinsu dan bazasu zauna
agarinsaba. Koda sa'ko ya isa tuni dukkaninsu sun jima
da suma tsabar duka. Ruwa aka kelaya musu suka fara
motsi Ta bude idanuwanta dakyar tanajin wani irin ciwo
tako ina ajikinta. Cikin wata irin dauriya ta daddafa ta
tashi zaune tareda jan jiki ta isa inda yake zube ko yatsa
bai iya 'dagawa bakinsa da hancinsa na jini haka itama
Kuka tafashe dashi tana kiran sunansa agalabaice.
Ciccibarsa sukayi itama su iya jummai suka jata kawar
kaya akayi fadar me gari dan ladingo ta gwammace ta
kashesu data zauna dasu. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na
MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo
91β†’95 Gaban me gari aka xubesu kamar kayan wanki
ko motsi dakyar sukeyi anyi musu raunika bakyan gani.
Kallonsu yayi saiyaji wani tausayinsu yashigesa hardai na
nazli dayasan mahaifinta sosai da mahaifiyarta kuma
yana sane da ukubar datake ciki hartayi aure. Gyara
xama yayi yana kallonsu yace, Dukan dakukayi musu
bazai bari nayi wani hukunci ayanxuba dan haka abarta
ta zauna gidan mahaifinta harta samu sauki sai adawo.
Yana fadar haka ya sallami kowa su babah ladingo kamar
zata fashe tsabar ba'kin ciki tana fadin, Ni yaushe
wannen 'bakar zuri'ar zasu barni naji da'din rayuwata.
Da taimako suka iso gidan ladingo naxabga musu harara
kamar idonta zasu fado Zuciyarta na tafarfasa kaman ta
'kone jitake kamar ya sha'kesu su mutu ta huta Ta shige
'daki da 'karfi tana huci tareda mukarabanta. Da bin
bango ta isa kofar tsohon 'dakinta daya tsufa ya mutu
duk ramukan cinnaku da 'beraye yacikashi sbd dama ba
siminti ne dashiba. Jiri na 'dibarta ta share 'dakin ta fidda
zaninta 'daya ta shimfida a'kasa takoma takamosa ta
kwantar dashi akai itama ta sulale 'kasa ko shimfida
babu Nan take suka fice hayyacinsu sbd zazzafan
zazzabin dayayi musu mummunan kamu sbd azaba.
Ruwan randa me sanyin aka antaya musu bokiti guda A
firgice ta tashi zaune duk da ba 'karfi ajikinta ko kadan
Shikuwa idanu kawai ya iya budewa awahalce dan ko
motsi baya iyayi sbd arayuwarsa baisan wahalaba,
Jikinsa banda hutu da gyara ba abunda yasani shiyasa
yake cikin azaba sosai. Baba ladingo ce tsaye karima
agefenta rikeda bokiti. Cikeda ba'kin cikinta takalli
shegen buzun ta 'karbi bokitin 'karfen hannun karima
xata buga masa akai Nazli tayi surin fadawa jikinsa
bokitin yasameta a goshi tuni jini ya 'balle amma
hakanan ta daure tana share hawaye. Shewa ladingo tayi
tana cewa lallai naga alamar akan wannnan ko'dadden
zaki 'dau komai to muzuba nidake dan wallh su buba da
iro da idi zansa su jibgarmun shege kekuma ni zanji
dake. Tashi nafasa korarku agidana aikin bauta
zakuyimun koba komai nasamu bayi Tashi maza wanki
zakimun yanxu. A ki'dime ta 'dago sbd tsakar darene
gata tana cikin wani hali na ciwo da yunwa ina taga
'karfin wanki. Kan tameer tayi da bokitin a fusace zata
rafka masa cikin sauri ta mike tana cewa xanyi wankin.
Wata dariyar 'keta suka saki suna kallon wani sabon ikon
allah. Tana kallo yana rawar sanyi kamar zai shide sbd
sanyi ake ga ruwan da aka zuba musu ga 'dakin ko 'kofa
baida Tana kallonsa ahaka ta fice tana hawayen ba'kin
ciki. Wankine kamar sunyi shekara basuyi dan harda
kayan iya jummai danasu buba dana karimar dana ita
ladingo hardana iro da idi. Jikinta na rawa ta fara wankin
ko gani batayi sosai ga hankalinta duk yanakan meer
dake can kwance cikin ruwa da sanyi. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee. πŸŒ•
⚜DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah
bbchoudiallo 96β†’100 Wankine mai yawan gaske na
dukkaninsu hardana iya jummai da 'danta iro, Gana
buba da idi hardana karima da ladingo. A wahalce take
wankin jikinta na mazari sbd zazzabin datake ciki ga
sanyi dake kadawa sosai Duk radadin datake ciki Gaba
'daya hankalinta nakan tameer data baro 'dakin kwance
yana rawar sanyi cikin ruwa ga sanyi da ciwo. Saida gari
yayi haske sosai ta gama wankin dakyar ta mi'ke a
duddu'ke tana tafiya dan bazata iya mikewaba. 'Dakin ta
nufa tana hawaye dakuma fargabar halinda zata samesa.
Kukane tareda farin ciki sukaxo mata lokaci 'daya sbd a
zaune tasamesa jingine da bango yana bude idanu
dakyar sbd azaba. Da gudu ta fada jikinsa tareda sakin
wani irin kuka mai ratsa zuciyar mai sauraro. Saidata sha
kukanta kafin ta mike tareda kamasa tana shirin canza
masa kaya sbd ajike yake har alokacin. Jakar kayansu ta
duba bataga komaiba. Ta sake dubawa da kyau ba kala
ko 'daya aciki Hayaniya tajiyo a tsakar gidan tana
saurarawa saita jiyo rabon kayane suke Da sauri ta fita
tsakar gidan aiko kayansu kaf Su idi,da bubah, da iro
suka rabe kayan tameer Nawa kuwa kaf karima aka ba.
Ahankali hawayenta suka cigaba da gangarowa ta juya
takoma 'dakin tareda zama kusada shi ta cusa kanta a
tsakiyar gwiwowinta tana rero kuka sbd. Kiran tashin
hankali ladingo tafara yo mata ta mike ahankali taje
fuskarta duk ta kumbura sbd kuka. Aikin gidan tasata
harda 'diban ruwa tana gamawa taje tasiyo tameer koko
Tana basa yafara kelayo mata amai. Hankali tashe take
kallonsa harya gama Ta goge masa jiki tareda gyare
gurin. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Rayuwa ta zame musu
u'kuba a 'kauyen Tun suna jiran kiran me gari harta
daina dan yayi watsi da zancen. Ladingo kuwa duniya
tadawo musu sabuwa dan tasamu bayi yanda takeso duk
da itake duk aikin dazasu saka tameer 'din kasancewar
yanxu agarin kowa yasan lalurarsa ta juyewar hankali.
Itake aikin gidan kaf Tayi wankinsu kaf Tayi 'dibar ruwa
da abincin saidawar ladingo komai yawansa duk da aikin
yafi 'karfinta. Tun yana mata rakin cizon cinnaku harya
daina yasaba Yunwa kuwa tasamu kyakkyawan mazauni
ajikinsu dan sunyi wata muguwar rama. Fatarsu ta dafe
ta lalace sbd sunma manta da wani sabulu ake wanka
Sunyi wani furi furi dasu. Tameer yadaina ciwo sosai
saidai haukarsa data fito muraran dan yanda idan zasu
'dibar ruwa suna tafiya yana tsince tsince Hakama idan
sukaje rafi cewa yake saiya fada ruwan yayi wanka Ga
yara da suke bibiyarsa suna masa wakar mahaukaci.
Abun nadamunta amma ba yanda ta iya. Tun ana
zaginsu da kyararsu har andaina anfara tausaya musu
sbd ukubar dasuke ciki sosai. Suturar sawama basuda ita
dan kayansu sun ko'de harsun fara yayyagewa. Ahaka
Cikinta ya tsufa sosai kuma hakan take duk wahalar Ta
bushe bayan kashi ba komai. Soyayyarta da kulawarta
kullum akan tameer 'dinta suke, shi kadai ke kawo
murmushi afiskarta dan duk takallesa takanyi murmushi
hardai idan tana aiki yana damunta da shirmensa.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Zaune take tana wanke wanke cikin sanyin jiki
sbd tun daren jiya takejin ciwo ahankali amma take
daurewa dan kota nuna ba me taimakonta. Tana
kallonsa yana wasa da ruwan wanke wanken amma
takasa hanasa hartasamu ta gama dakyar. Gyare gurin
tayi ta'dau bokiti tana rintse idanu suka fice zuwa 'dibar
ruwa. Shike rikeda bokitin itakuma tana tafiya ahankali
sbd ciwonta yafara tsananta. Wata mata data shigo
'kauyen rikeda 'yar ledarta harta giftasu saita 'dan dawo
tana kallon nazli tace, Yarinya gidan malam adamu
headmaster nake nema dan ya'dan 'bacemun. Lumshe
idanu tayi ta budesu dakyar cikin 'dan kannewa tace, Ya
rasu tunda dadewa. Salati matar tasaki cikin rawar
murya tace, 'Yarsa fa tanan? Dan allah nunamun gidan.
Cikin ciwonta daya fara fin karfinta tace, Ni..ni nice
'yarsa. 'Kara dam'ke hannun tameer tayi duk da tana
cikin ciwo dan zai iyayi wani gurin. Akidime ta 'kurawa
fuskar nazli ido Sai alokacin matar ta lura da halinda
nazli take ciki πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH
GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 101β†’105
Kamota tayi tana kiran sunanta dan 'kokarin
durkushewa take kuma har lkcin takasa sakin hannunsa
Matar takalli tameer dakeson kwace hannunsa ya hango
kara yanason yaje ya 'dauko. Kamata tace masa tana
kamo nazli 'din Kallonta yayi yana son boyewa bayan
nazli. Cikin azaba tace bashida lafiyar hnkli. Kamata tayi
suka koma gidan dakyar Kai tsaye 'dakinsu suka shiga
zuwa lkcn ciwo take sosai. Bakowa agidan dan basanan
sunje wani 'kauye bikin suna. Kwantar da ita matar tayi
dan dama itake karbar haihuwa garinsu. Cikin ikon allah
babu 'bata lokaci ta haihu lafiya 'kalau. Ruwa matar ta
'dora tayiwa yaron data kirada balarabe sbd tsantsar
kyawunsa data gani wanka. Kama nazli tayi tayi mata
wanka tas kuma allah yasa bayau su ladingo zasu
dawoba. Nade yaron sukayi axanin bakuwar dan babu
kayan daza'a saka masa. Ido ta 'kurawa yaron tana
hawaye dan tasan bazai samu rayuwar jin da'di kamar
yanda taso masaba. Kuka take rerowa harda shesheka
matar nakallonta harta gama ta matso kusada ita tace,
Sunana INNAH ASMAH Tareda mahaifiyarki nataso akayi
mana aure tare Tun rasuwar baffana data mahaifiyarki
ban 'kara xuwa garinnanba sai yanxu naxo sbd na duba
'yar rahane ashe har malam yarasu an miki aure.
Hakanan ta kwashe komai kaf tafada mata tana kuka
sosai. Ita kanta innah asmah hawaye take tana sharce
majina kafin ta mike tana cewa Nazli wahalarki insha
allah takare dan bazan barkiba dake xan tafi. Mikewa tayi
tafice afusace tana sharce hawaye. Sai alokacin tameer
yashigo 'dakin kayansa sharkaf da ruwa dan tunda suka
shigo yanacan tsakar gidan yana 'bata ruwan ladingo
allah ma yasa basanan. Da sauri yazo kusa da ita yazauna
yana kallon 'dan jaririn dake hannunta yana keta kuka ta
rasa yazatayi sai kukan take itama. Washe hakora yayi
yana 'kokarin tabashi saiga innah asmah tayi saurin
karbar yaron tareda saka masa kayan dataje tasiyo
yanxu. Duk wani abun bukata tayi musu dan kwananta
biyu kafin su ladingo suka dawo sunyi mamakin ganin na
haihu amma ganin innah asmah yasa sukayi biris damu
dan tace sai bayan sati zata koma. Tameer kuwa wawa
yakoma kan yaron dan rigima yakeyi sosai sai anbashi
jaririn Tun innah asmah najin tsoro harta daina dan
sosai yake nuna son yaron. Sati nayi suka radawa yaron
suna ZAID Nazli nakiransa da WALEED Sun 'dan walwale
cikin 'yan kwanakin sbd samun cima mai 'dan kyawu da
kula da innah asmah ke musu. Kwananta goma cif ta
ha'da kayanta zata tafi da niyyar zata dawo ta tafi dasu
wani satin. Hawaye nazli keyi sosai bayan tafiyar innah
dan tasan zasu komama wahalane Amma idan ta tuna
daxata dawo ta tafi dasu saitaji wani sanyi aranta.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Ahankali dai sai gasu sunkomawa
wahalarsu ladingo ga nauyi daya 'karar mata na waleed
allah ma yasa tameer takebawashi su zauna 'daki tayita
aikinta. Tun tana lissafin dawowar innah harta daina sbd
fiyeda wata uku kenan amma babu ita. Wahalarsu ta
yanzu hartafi tada dan tuni suka 'karmaje dukkansu
hardai ita dake shayarwa. Kullum dare kwana take kuka,
Ko aiki take hawaye takeyi sbd tausayin rayuwarsu.
Kamannin waleed sun fito sosai da tameer dan kuwa
kamar tasu hartayi yawa. Ga wata irin shakuwa dake
tsakaninsu danko ita wani xubin yafison tameer da ita.
Muguntar dasu bubah kewa waleed yasa bata bari suna
fitowa tsakar gidan kullum suna 'kunshe adaki. Akwai
ranar da waleed yayiwa ladingo 'barin gari aiko buba
yayi ball dashi Ladingo kuwa ruwan talginta ta zuba
masa ahannuwa harda sumewa yayi Ranar basuyi
bacciba kwana sukayi zaune suka kuka harda tameer
'din sbd yanda yaron hannuwansa suka sale ga wani irin
kuka dayake sbd zazzabi da azaba. Komai ya ida jagule
musu wuya tayi wuya Ga waleed yagirma sosai harya iya
magana Sunkoma suturama saida fadar mai gari taji
tausayinsu aka basu kala biyu biyu wanda daga gani
kayan sun jima da mutuwa amma haka suka karba suna
sawa. Babbar damuwarta baifi waleed da bayajiba gasu
sukuma sukamasa suyi masa dukan tsiya kamar wani
'kato 'dan uwansu. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Zaune take tana bawa
tameer ruwa sbd ciwo dayake fama dashi tun daren jiya.
Waleed ya shigo 'dakin da gudu yana haki yace, Anty
kinga wata tana nemanki gatanan xuwa. Zaunar dashi
tayi tana cewa, Waleed bana hanaka yawoba. Allah anty
banje yawoba ina 'kofar gidafa. Sallamar innah asmah ya
hanata yin magana ta mike da gudu ta rungumeta tareda
fashewa da kuka. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH
GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 111β†’115
Wani wawan haushin kare yaji daga nesa baisan sanda
ya juyo da gudu ya fa'da gonar wani wawan jiri da
sarawar kai ya ziyarcesa amma baitsayaba saidaya kai
tsakiyar titin wanda yayi daidai dakawowar wata mota
aguje tayi sama dashi ya zube cikin jin. Akidime nacikin
motar yafito yayo kansa yana salati sbd ganinsa cikin jini
Juyosa yayi da sauri dan 'daukarsa yakaisa asibiti tunda
shi likitane abun zaixo da sauki insha allah. Zabura yayi
da 'karfi ya ware murya yace TAMEER Jikinsa har rawa
yake yadaukesa yasa amotar ya figeta da wani irin speed
sai kano. Asibiti ya wuce dashi kai tsaye aka shige dashi
emrgency. Waya dr ibraheem ahmad ya fiddo wayarsa
jiki na rawa ya lalubo wata number ya danna kira.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ ABUJA Zaune yake cikin tangamemen
palonsa Idanunsa sanyeda farin medicated glass Yayi
xurfi cikin tunani da damuwa Yau tsawon wata shida
kenan da allah yabasa sa'ar kubutowa daga 'yan
ta'addan dasuka sacesa suka rufe Tunda yadawo yasamu
bayanin 'bacewar 'dansa da nazli abakin matarsa
datayita kukan munafuncin cewar ba'asan inda sukayiba
anyi nema har angaji. Wannan mugun labarin saidaya
haddasa masa kwanciya asibiti tsawon wata biyu a
newyork kafin yadawo aka baza bincike tako ina.
Wayarsace tayi ringin harta katse bai dubi inda takeba.
Haj xeenat data shigo palon cikin ado tana she'ka
'kamshi takalli wayar dan ansake kira tamaida kallonta
garesa tana zama kusa dashi tareda 'daukar wayar sbd
sunan dr ibrhm data gani dan sam tana kasa nutsuwa a
duk lkcn dataji yakira alh zaid sbd tsoron yafada masa
komai gameda abunda yafaru. Arikece yake fadin,
Alh...alh tameer....gashi nnan asibiti Wat ta fa'da da 'karfi
tana mikewa cikin wani irin tashin hankali Jikinta nan
take ya'dau rawa. Alh zaid kuwa wayar ya warta da 'karfi
yana sauraron bayanin dr ibrhm aibai tsaya jin sauranba
yafice palon baikobi takan haj xeenat dake daskare
agurin tana aman xufa. Motoci uku na alh zaid da
securites suka 'dau hanyar airport adaren dan xuwa
kano. Wuraren asuba suka sauka kano kai tsaye asibitin
suka wuce Alh zaid naganin yanda tilon 'dansa yakoma
ya yanke jiki yafadi. Yana farfadowa ba'a tsaya komaiba
ya ha'da 'dansa da dr ibrhm suka bar 'kasar zuwa
germany. ******** Jinyarsa ake ana kula dashi sosai a
garmany 'din dan tuni su haj nurat suka isa germany
'din suma. Watansa 'daya akwance kuma anasa ran
farfa'dowarsa ko wane lokaci. Haj nurat ce da fannah
zaune a'dakin. Haj nurat waya takeda ammah mahaifiyar
nyssa tana fada mata yanayin jikin nasa Fannah kuwa
chattin takeyi da tsadaddiyar wayarta. Ahankali yafara
bu'de idanunwansa dasukayi masa nauyi sosai yana gani
dishi dishi harsuka bu'de. UMMEE ya fa'da muryarsa
bata fita amma cikin sa'a kuwa haj nurat taji hakama
fannah. Rige rigen isa gurinsa suke cikin tsananin farin
ciki wanda yayi daidai dashigowar alh zaid Farin cikin
dasuke ciki baya misaltuwa dan kuwa tameer ya warke
ras yadawo cikin cikakken hankalinsa kamar kowa. An
sanar da 'yan cairo dabasu sabu xuwa kowa murna
yakeyi anata farin cikin. HMMMMMNN WATA SABUWA
KENAN. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE
β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo 106β†’110
Zaunawa sukayi tana lallashinta tace, Nazli kiyi hkr rashin
lafiya nayi sosai kuma maigidana ya rasu shiyasa ban
dawoba amma yanxu gani nazo kuma ayau zamu wuce
basai gobeba. Sharce hawaye tayi gabanta na faduwa
hakanan taji gabanta yafa'di da tafiyar. Kallon tameer
tayi kafin tamaida kallonta ga inna tace, Inna meer
bashida lafiya yazamu iya tafiya dashi. Kadaki damu
tunda zai iya tafiya muje damun shiga mota zai
aishikenan. Ha'da 'yan tsummansu tayi tana share
hawaye dan sam ta rasa nutsuwa batasan dalili ba. Kamo
tameer tayi inna ta riko hannun waleed dake murnar
zasuje yawo. A tsakar gida suka samu ladingo da iya
jummai suna she'ka firarsu Suna ganinmu suka 'daure
fuska suna harare harare. Inna ce tayi musu bayanin
xata tafi damu har xuwa samun saukin tameer. Harara
iya jummai ta watsowa inna tana fadin, Dan wa'innan
dangin buxayen masu kama da figaggun kaji to tafi dasu
ko aminiyata da 'yayanta sa huta da ba'kin iri. Ladingo
kuwa ko kallo basu isheta ba sai ka'da kafarta take.
Ficewa sukayi jiki asanyaye. Dakyar suka samu motar
'kauyensu inna. Tunda suka baro gida takasa tsaida
hawayenta tana tunanin yaushene zata samu
kyakkyawar rayuwa? Itakenan kullum garari yanxuma
batasan wace rayuwa zasuyi acanba. Da maraice suka isa
'kauyen da 'kafa suka isa gidan inna. 'Dan 'karamin gidan
'kasane mai tsakar gida da 'dakuna biyu sai 'dan
'karamin ban'daki atsakar gidan. 'Daki 'daya tabasu suka
share tsaf tabasu tabarma suka shimfida tareda aje 'yan
kayansu. Sanwar abinci inna ta 'dora musu tana gamawa
tabasu sukaci suka 'koshi nan waleed yafara wasarsa
itakuwa share gidan tayi tas Ana kiran sallah sukayi
sallarsu har lkcn kwanciya yayi suka kwanta. Washe
garima da kanta ta gyare gidan tayi duk aikin gidan inna
na yaba mata sosai sbd tayi 'kokari. Chanjin rayuwa yazo
musu sosai sbd yanxu harsuna dariya su 'kyakyata Ga
yunwa tuni ta gudu ajikinsu Sunyi 'danyi kyawun gani
dan yanzuma kamannin tameer da waleed ke 'kara fita
abun har tsoro yake bata Ga muguwar sha'kuwar dake
tsakaninsu sbd waleed yasan tameer shine babansa.
Hankalinsu yanxu akwance yake basuda matsala sbd
inna asmah nada rufin asiri sosai sbd tanada dabbobi da
yawa ga sanaar saida kayan 'kulle 'kulle datakeyi.
⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ 4 month later Tun jiya takejin
jikinta asanyaye da faduwar gaba har saida inna ta
tambayeta lafiyarta 'kalau kuwa Tace lafiyarta 'kalau.
Zaune suke tsakar gidan inna na 'daura kuka datake
saidawa nikuma ina wanke wanke. Waleed da tameer ke
wasarsu suna dariya sai waleed ya 'dale bayan tameer ya
goyasa yazagaya tsakar gidan dashi ya saukesa saiya juya
waleed yana 'kokarin shima wai waleed 'din ya goyasa.
Daria muka saki duk mu duka waleed ya gudo bayan
inna yana cewa, Inna dubi wai saina goyasa babba dashi
fa. Daria inna tayi tana cewa, Aini bana shiga tsakaninka
da babanka nazo naji kunya anjima dan nasan shiryawa
zakuyi. Da gudu waleed yabar bayan inna yana daria
shima tameer dariyar yake Nazli ta 'kura masa ido sbd
kyawun dataga yayi mata sosai wanda rabon datayi
masa irin kallon harta manta Wani sabon sonsa takeji
yana sake tsima azuciyarta. Waje sukayi dukkansu suna
daria itakuwa taci gaba da aikinta inna ma hankali ta
mayar anata aikin. 'Boyewa waleed yayi bayan bishiyar
'kofar gidan tameer yawucesa batareda yagansa ba
Shikuwa yana ganin ya wuce fito ya zauna 'kafar gida
yana wasar 'kasarsa. Tafiya yaketa famanyi shi ala dole
saiya kamo waleed haryayi nisa sosai. 'Karyen 'kauyen
yakai ammai bai tsayaba sai kawai yaci gaba da tafiya tun
yana gani har duhun mangariba yasawo kai nan take
tsoro yafara kamasa Yafara waiwaye yana tafiya da sauri
sauri. Har duhu yayi sosai gudu yake ketawa adajin
kamar

Please Login or Register in order to submit comment