Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

itama ta
huta da baqin ciki da wahalar rayuwa. Kuka ta rushe
dashi har tana shi'dewa hannu na rawa ta karbi robar
batareda ta 'dagoba dan bata fatar sake ganin fuskarsa.
'Dagawa tayi ta 'dora abaki xatasha aka fixge robar da
qarfi Atare suka kai kallonsu gareta nafisace tsaye cikin
tsantsar takaici tamaida kallonta ga nazli datake faman
sheshshekar kuka ahankali kamar ranta zai fita Cikin
babbar murya tace, Nazli lokaci yayi dazan daina kallon
wannan masifar, Me kike tunani xai faru idan kikasha
wannan gubar kika mutu? Me kike tunanin wa inda
kikayi shekaru kina wahala sbd su zasuyi da rayuwarsu
bayan sun gano ko ke wacece arayuwarsu? Bakya
tunanin ya rayuwar waleed xata kasance bayan kin mutu
baki ha'dasa da mahaifinsaba. Shin nazli meyasa bazaki
daina wahala akan wa'inda basusan kinayiba? Nazli
lokaci yayi da sir ta...... Da sauri ta miqe da gudu ta nufi
qofa tana wani irin jan numfashi sbd tsabar kukan
datake. Caraf ya riko hannunta batareda yakalletaba
idanunsa nakan nafisa dake watso kalaman dasuka
kusan tarwatsa masa tunani da qwaqwalwa. Kukanta ke
qara sauti kuma ahakan nafisa taci gaba da zancenta
batareda ta tsayaba. Nazli idan har kinasonsa kinason
kare rayuwarsa to tabbas lokaci yayi dazaisan koke
wacece. Fixge hannunta tayi da gudu tana kuka sosai ta
fice. Jiri ya xubar dashi a kujera kansa na juyawa. Qara
hargitsewa tunaninsa yayi sbd bai gane komai na xancen
nafisa ba amma ya gane abu 'daya shine zancensu nada
alaqa dashi. Duk yanda yaso tashi yabi bayansu jiri
hanasa yayi sbd tashin hankali. Da gudu ta isa 'dakin ta
'dibi kudin albashinta ka'dan ta fice gidan da gudu tana
wani irin kuka mai tsima rai. Tana fita tasamu taxi ta
fa'da sai tasha kuma cikin sa'a mutun 'daya ake jira tana
shiga suka tashi suka wuce har alokacin kuka take kamar
ranta zai fita sbd ta rabu da tameer rabuwa tahar abada.
Tana shiga taga bata 'dakin ta duba toilet bata gantaba.
Fitowa tayi tafara dudduba ko ina amma babu nazli Nan
take hankalnta ya tashi tuni hawayen takaicin tameer da
tausayin nazli ya tsinke mata sbd tana hango tsantsan
masifa agaba muddin nazli tace ta tafi kenan kuma itama
wallahi tafiyarta xatayi. A ru'de ya sauko zashi 'dakinsu
dan gaba 'daya yau idan basan komaiba komai xai iya
faruwa dashi dan wata irin rashin nutsuwa yakeji kamar
xaiyi hauka. A firgice ta fito 'dakin tana hawaye suka
ha'de bakin qofar ya wuceta xai shige cikin muryar kuka
da takaici tace batanan ta gudu ta tafiyarta sbd kai, Kaine
sanadin komai na wahalarta arayuwa, Meyasa ka kasa
tsayawa ka fahimceta kayi mata wannan hukuncin harda
baraxanar shayar da ita guba, Shin ko kasan sbd kaine
xatasha gubar tabar duniya duk dan sbd kai uban
'dan..... Kasa qarasawa tayi sbd kukan dayaci qarfinta
tace nima nasan koban tafiba xamana ya qare a
gidannan dan haka tafiya xanyi. Ido rufe ya daka mata
wata mahaukaciyar tsawar dabaimasan yayiba ya bu'de
ido jajir yace, Har abada bazaki bar gidan nanba
harsaikin fadamun abunda yake faruwa sbd xuciyata na
gab da tarwatsewa sbd ru'du. Cikin rashin tsoro tana
sharce hawaye tace, Ni 'yar aikice banida dama ko
matsayin dazan fadi wani abu amma alh da haj da
aminanta sunada dama harmada dr ibrhm. Tana fadar
haka ta shige 'dakinta ta sulale qasa tana kuka amma
tasan allah bazai bari su cutatar da itaba tunda qarshen
wahalar alamarin ne takawo idan har tameer yasan
komai. A zafafe yake kaida kawo apalon, Banda sarawa
ba abunda kansa keyi ga fuskarnan tayi ja abinka ga farin
mutum. Zama yayi a 'daya daga cikin kujerun palon
yana jiran dawowar kowa daga gurin event 'din dan
ayau yakeson jin komai basai gobe ba. Sallamar dad ne
da driver 'dinsa janye da 'yar jakarsa yasashi miqewa
tsaye cikin godewa allah da dad 'din ya iso yau kuma a
daidai lokacin dayake buqatarsa. Kallon mamaki dad
yake masa sbd ganinsa a yamutse hankali duk atashe
idanunsa jajir. Subhanallah tameer meyene naganka
haka hnkli atashe? Fitowarsu haj xeenat da aminan
natane yayi daidai da fa'dar maganar dake bakinsa... πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰
mamuh geee [8:55pm, 15/01/2017] β“‚amuh geee: πŸŒ•
⚜DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah
bbchoudiallo 181β†’185 WACECE NAZLI A RAYUWAR
NAN GIDAN? alokaci 'daya jakunkunan hannuwansu su
duka ukun suka kufce musu cikin wani irin mugun
tashin hankali. Kallonsu yayi yakaranto tashin hankalinsu
tsaf a fili kafin ya maido kallonsa ga dad 'dinsa dashi
kuma mamakine xalla afuskarsa na yanda akayi tameer
yasan sunan nazli. Murya a sanyaye yace, My son ina kaji
sunan nan? 'Yar aikin gidan nance me sunan...fannah ta
fa'di haka tana shigowa palon dan dawowarta kenan taji
abunda ake fada. Mamakin dad ya qaru muryarsa har
rawa take yace, Me aiki anan gidan? Akiramun ita yanxu
nan inason ganinta. Wata wawar murdawa cikin haj
xeenat yayi ta diro tsakiyarsu da qarfi tana rawar murya
tace, Alh ba nazli 'dinsa bace wannan watace dabam. 😳😳
zaro ido su haj kareema sukayi sbd jin 6arin bakin datayi
na cewa nazli 'dinsa. Gogan kuwa qara 'daukar zafi kansa
yayi jin ta danganta nazli dacewa tasa. Fannah kallon
rashin fahimtar komai take musu Dad kuwa rashin
gaskiya ya hango tsantsa a tattare da haj xeenat wadda
ita sai daga baya ta gane ru'du yasa tasaki layi saita fara
kame kame amma ina tuni alh zaid ya nufi hanyar kicin
da kansa sbd shi ka'dai yasan irin qaunar dayakewa nazli.
Cikin wata wahalalliyar murya yace, dad ta tafiyarta
tabar gidan sbd nakamata zata kashe fannah ta hanyar
xuba mata guba tasha. Ai mutanen naku najin haka ko
wacce saidata kusan tsirgo fitsari suka fice palon da
mugun sauri suka bar gidan dan yau qila rana ta 6atar
musu. Fannah jikin yayan nata ta isa da sauri ta jirgixashi
tace, B pls dnt say that nazli baxatayi hakaba i knw her
for sum month amma na karanci halayenta she cant d....
Da qarfi yana tureta daga jikinsa yace, Just shut up. I saw
her and she...... Shut up. Shima dad ya katsesa da qarfi
sbd ganin abunfa da gaskene akwai gagarumar matsala
dabai sanda ita a gidansaba. A fusace yakalli haj xeenat
yakalli tameer 'din yace, Weda nazli 'din ce ko kuma
wata daban inason tabbas ku nemota sbd koma meyene
kune kukasa ta tafi. And as for u dakakeson sanin komai
to zan fada maka amma saika nemota duk inda ta tafi.
Fadar halinda yashiga abune mai wuya dan kuwa
idanunsa har wasu ruwa suka tara Shima cikin mazewa
yace, Nikuma na fasa auren meenah saina san ko
wacece nazli. A razane dukkaninsu suka maida kallonsu
kansa dad kuwa hayewa samansa yayi cikin wani irin
yanayi. Da rawar jiki haj xeenat ta juyo xata fara
roqonsa ya juya rai abace da sauri ya haywarsa
samansa. Juyowa tayi gurin fannah dake hawayen ganin
abundake shirin faruwa dasu yau harb 'dinta na tureta
da gudu tabar palon tana kuka tayi 'dakinta ta rufe.
Gumi ta sharce kafin ta ruga 'daki tadauki wayarta jiki na
rawa tana qara hada wani gumin takira kareema ta fada
mata wata sabuwar masifar fasa auren meenah da
tameer yace yayi. Kaf 'dinsu a daren babu wanda ya
rintsa sbd kowa nacikin nasa kalar tashin hankalin bama
kamar SIR TAMEER. Washe gari kowa da damuwa yatashi
fal danko breakfast babu wanda yayi. Haka take agidansu
haj kareema dan kuwa aure dai ya fasu sai ranar dayace
iya tashin hankali kam suna ciki. Hardai meenah da haj
kareema ta zayyane mata komai hankalinta yayi
mummunan tashi jin cewar nazli matar tameer ce. Wata
muguwar tsanar nazli ta mamayeta nan take ta'dau waya
takira megadi mijin sa'adah tace ta koresu maza maza
subar gidan ayau basai gobeba. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ Da
asuba suka isa kano Idanunta sun kumbura sunyi jajir
ko gani batayi sosai tsabar kuka ga ciwon kai kamar
kanta da zuciyarta xasu tarwatse. Mashin yakaita har
qofar gate 'din gidan ta qwanqwasa kofa abu mai gadi
mijin sa'adah ya bu'de gate 'din yana ganinta ya saki fara
yana mata sannu da hanya duk da fara'ar qarfin halice
yakeyi sbd ya lura da yanayinta. Tana shiga suka ha'da
ido da sa'adah data tashi sallar asuba. Kawai saita saki
wani sabon kuka tana shesheka kamar me asma tsabar
kukan yacita. A rude sa'ada ta rungumeta tana lallashinta
har suka samu daqyar sukayi sallah. Har gari ya waye
yayi ras suna zaune takasa magana sai kuka takeyi.
Waleed natashi daga bacci yaga antynsa da gudu yafada
jikinta ta qanqameshi tanajin maseefar sonsa sbd tayiwa
kanta alqawarin ta rabu da tameer da rayuwarsa har
abada. Sunan xaune ne saiga kiran meenah ta koresu
nan wani sabon tashin hnkali ya samesu wanda nazli
kukanta ta qaru sbd ta dangana hakan da itace sanadi
dan haka zata 'dauki 'danta su tafiyarsu. Nasiha abu yayi
mata sisai kafin ta tsaya suka tattara 'yan kayansu
sukabar gidan Sai wata babbar unguwar masu ku'di a
wani babban gida da aka 'dade da ba abu cigiyar yasamo
musu me gadi sai kawai yakai kansa babu 'bata lokaci
kuwa aka basu 'dan qaramin boys quaters 'din gidan duk
da gidan gidane babba. ********** Duk yanda kowa ya
tsammaci abun yawuce nan dan sosai gidan yakoma
kamar gidan mutuwa sbd kowa nacikin muguwar
damuwa bama kamarsa da tunani da damuwa sufara yi
masa yawa har ciwo nason yashigo ciki. Ku'di yasakarwa
p'a 'dinsa sosai ana nemanta amma ba wani lbr. Kwance
yake apalonsa idanuwansa a lumshe yayi nisa cikin
tunani. 'Dayar wayarsace tayi ringin ya bu'de idanu
ahankali sai yaga p.a ne akasalance ya 'daga wayar sai
yaji yace, Sir dama alh ne yasani 'dauko masa wasu
takardunsa acan tsohon gida gashi yanxu nakawo amma
bayanan ya fita kuma naga takardun nada
mahimmancin da bazan iyaba kowaba saikai. Siririn tsaki
yaja tareda kashe wayar ya miqe yasauka palon qasa
saiyaga takardun da 'dan yawa ya watsawa p.a kallon
wane irin takardune wa'inan. Yayi saurin cewa, Eh dama
takardun gidan yace mu 'dauko ta sai muka samesu da
wasu sauran takardun daban sai kawai na kwaso masa
gaba 'daya. Hannu yasa ya kar6ba tareda hayewa saman.
Fannah dake tsaye qofar 'dakinta tana kallon yayanta
taga muguwar damuwa tattare dashi ta share hawayen
dasuka gangaro mata takira nafisa tace taje takaiwa
tameer abinci yanxu ita xata yanka masa fruit tazo dasu.
Yana shiga palon yayi wurgi da takardun a kujera suka
watse kansa na sarawa yajuya zai shige 'daki ya tsaya cak
tareda juyowa da mugun qarfi sbd hotunan dasuka
watse daga cikin takardun. Raruma yakaiwa hotunan
nan take jikinsa ya 'dau rawa sakamon kansa daya gani
tareda wata kyakkawar yarinya kamar balaraba daya
sake dubawa saiyaga tabbas nazli ce. Hotunane birjik
duk suna dariya da wasa ta daukesu hotunan ga tsantsar
so da qaunar junansu dayake bayyane afuskarsu
Hotunane datake daukarsu awaya lokacin tana turawa
dad sune yasa aka wanko masa tun da dadewa.
Baraxanar 'daukewa numfashinsa yayi lokacin daya
'dago hoto na qarshe wanda ashe ba hoto bane katin
'daurin aurene na TAMEER ZAID OMAR DA NAZLI ADO
TAKAI. Da akayi shekaru biyar dasuka gabata. A haukace
ya 'daga takardar qarshe ta gidace da dad yasaka sunan
nazli yabata gidansa dasuka taso. Qoqarin xubewa yake
nafisa tashigo tayi saurin aje tray tayo kansa da sauri..
TO FAH YANXU AKE. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na
MAMUH GEEE β˜†dedicated toβ˜† Husnah bbchoudiallo
186β†’190 Da gudu ta iso gurinsa tana kiran sunansa. A
kujerar ya zube yana dafe kansa dake neman bugawa,
Hotunan da katin ya qanqame cikin tashin hnkli yanajin
zuciyarsa na wata irin bugawa da qarfi. Manyan
idanuwansa dasuka koma jajir ya warowa nafisa
saidatayi saurin ja da baya cikin tsananin tsoro sbd gaba
'daya ya birkice yakoma kamar wani jan xaki. Jada baya
tafara ganin ya miqe yana jefa mata wani mugun kallo
da jajayen idanunsa. Cak ta tsaya tana ha'de yawu a dan
tsorace. Gabanta ya tsaya yana mata kallon dayake qara
razanata. Hotunan hannunsa da katin 'daurin auren ya
'daga da qarfi ya watsa mata da qarfi jikinsa har rawa
yake yace, Waye nazli aguna? Wannan auren, Wannan
hotunan, Da wannan.... Just tell me everytin now I want
to know every single thing akan auren nan. Zufa ya fara
fesowa nafisa tako ina jikinta na 'dan rawa. Wata
mahaukaciyar tsawa ya daka mata data mugun razanata
batasan sanda tace, KANA CIKIN HAUKA AKAYI AUREN.
hawayen dake cikin idanunsa na 6acin rai suka gangaro
ya qura mata ido kamar bai fahimci mai tace ba sbd
qwaqwalwarsa ta gaza 'daukar xancen. Hauka? Ni? Nayi
hauka? Har akayimin aure Dakuma harkar? Sanyi
muryarsa tayi sosai kamar yaro yafara roqonta kamar
itace boss 'din. Nafisa pls am begging you ki fadamun
abunda nakeson ji kada kiyi wasa da tunani ki fadamun
gaskia. Ka kamu da lalurar ciwon juyewar qwaqwalwa
shekara biyar dasuka wuce, A farkon ciwon alh yayita
yawo dakai a qasashe amma babu Wani cigaba saima
tsanani da abun yake, Bayan andawo dakai nan ne
akayita 'daukar masu kula dakai amma dasun zauna
kwana biyu saisu gudu daga qarshe aka kira malami yazo
ya tabbatarda aikin sihirine malam yabada shawarar ayi
maka aure dan zakafi samun kulawa daga matar datasan
kai mijintane. Nazli marainiyace bata uwa batada uba ita
aka auro maka. Fa'dar irin baqar wuyar datasha kafi
gurin kula dakai zaiyi wuya, Ahaka ta samu..... Shiru tayi
tana ha'de wasu yawu sbd tsoron fa'da. Jikinsa ya mutu
iya mutuwa saiya bude baki daqyar yace, Kada kiji tsoro
fadamun komai pls. Naz....naz..nazli ta...ta samu ci.. Ciki
alokacin. Saurin dafa bango yayi sbd wawan jirin daya
kwashesa. Sannu ahankali tafara fayyace masa komai na
irin baqar wuyar da naxli tasha akansa harda rayuwarsu
a takai da kuma gidan innah asmah da waleed da aka
haifa masa. Komai bata 6oyeba saidata bayyana masa
illah abu 'daya shine mugayen ayyukan da haj xeenat ke
aikatawa.... πŸŒ•βšœAM REALLY SORRY FANS DAJINA SHIRU DA
KUKAYI TWO DAYS I WAS VERY BUSY NE AMMA INSHA
ALLAH YANXU XAKU RIQA JINA. πŸŒ•βšœ LUV U ALL😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘 πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰
mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated
toβ˜† Husnah bbchoudiallo 191β†’195 Luu ya tafi xai kife
fannah dake tsaye bayansu tana wasu irin axababbin
hawaye sbd tun fara zancensu tazo kuma taji komai.
Wurgi tayi da tray 'din hannunta tayi kansa da mugun
gudu yana ganinta ya sulale zaune itama ta zauna yayi
saurin fa'dawa jikinta tareda sakin wani irin kuka mai
ciwo kamar qaramin yaro. Rungumesa tayi tana gargiza
masa kai tana cewa, No b pls dnt cry Kada kayi kuka, Ure
breaking my heart. Cikin kuka yake fadin, Fannah i have
a son Who is out there yana wulaqantacciyar rayuwa,
And she's my wife,my sons mother but babu wanda
yadamu da afadamun qarshema a me aiki take acikin
gidanta gidan mijinta. Meyasa aka bari matata tazama
me aiki anan gidan aftr knowing d fact shes my wife the
mother of my son. Why why. I even try to kill her wit my
own hands ta hanyar bata poison tasha. Fannah i wnt to
see her i wnt to see my son I wnt them both.... Fan
fannah i..i..i..... Toshe masa baki tayi tana kuka mai
tsanani sbd tsananin tausayin halinda yake ciki dan kuka
yake sosai yana sambatun kamar ma ciwon nasa na
haukane yataso. Nafisa duqe take agefe tana nata kukan
ahankali sbd ganin yanda tameer 'din ya birkice sai
sambatu yake cikin kuka fanna na jawasa jiknta tana
goge masa hawaye amma sam kamar zugasa sukeyi. Abu
kamar wasa tameer ya birkice sosai fannah tun tana
kuka kamar ranta zai fita tadawo itama kamar wata
zararra gurin lallashinsa amma sam shi ba abunda
yakeso sai ganin matarsa da 'dansa. Nafisa tadataga abin
yayi tsanani saita 'daga wayar fannah jiki na qyarma
takira dad. Yana 'dauka cikin tsabar ru'dewa sai kawai
tace masa Daddy sir tameer ya qara hauka..... Bata
qarasa fadaba yayi wurgi da wayarsa yayo saman tameer
'din dan yadawo ko minti goma baiyiba da dawowarba
saiga kiran. A gigice yashigo palon saiya tsaya turus
ciwon xuciyarsa na neman tashi sbd ganin 'ya'yansa
zaune a qasa tameer na risgar kuka fannah ta rungume
kansa itama kukan tausayin 'dan uwanta take duk sunyi
wani iri dasu. Fannah na ganin dad ta 'dan rage kukanta
Ya qaraso cikin fargabar idan da gaske 'dan nasa ya qara
haukacewa. A tsorace yace, Fannah fadamun abinda
yasamu 'dana tun ciwona bai tashiba. Saidata 'dan goge
hawayen fuskarta Tace, Dad nazli da ciki ta tafi and.....
Kuka yaxo mata Dad ma baisan sanda yajawo tameer
jikinsaba yana fadin, Kufadamun ta haihu kadaku cemun
na rasa rasa grandson. Lafewa tameer yayi jikin dad
murya a dashe yace, Dad ta haifamun 'dana Ur
grandson, And natashi da 'dana tun yana jariri, Nayi
wasa da 'dana infact he was my friend alokacin, We
played as frnds Dad inason ganina tareda shi da nazli,
Dad do sumtin I wnt to see them now pls. My heart is
beatin faster dad ta6a kaji i cnt breath pls dad i want to
see th..... Bai qarasaba yafara wani irin tari Ai nan suka
qara rikicewa dad yakira dr da sauri. Dr ibrhm nazuwa
yaga halinda yake ciki bai tsaya wata wataba yayi masa
allura nan take ya xube yana baccin wahala. 'Daki dad da
dr suka kaisa suka kwantar fannah ta lullubesa tana
hawaye tareda shafa gashin kansa da ku'din gyaransa
dabanne amma yau tashin hankali yasa duk ya hargitse.
Bayan fitar dr da dad ta qura masa idanu tana tunano
fuskar nazli. 'Dan naxli dataxo dashi suna kano kafin
sudawo was her own son amma rashin sani yasa
batamayi tunanin dasukazo tace tanason ganinsaba
qilama datun anan zata ga wani alamar cewa shi'din
jininsune. Allah sarki my b yanada 'da, Ni aunt ce
bansaniba. Wani mugun son yaron yashigeta tun bata
gansaba tana tunanin irin gatan dazai samu daga gareta
kawai kafinsu dad da ubansa gaba 'daya wato b 'dinta
sbd ta hango wani irin tsananin son nazli atake dayayiwa
b muguwar shiga LOVE AT FIRST SIGHT, To bare abunda
ta haifamasa,jininsa,me sunan dad 'dinsu. Data tuno irin
baqar wuyar da akace sunsha sai hawaye suka sake 'balle
mata. ********* Bai farkaba sai washe gari da allurar
data sakesa Kowa gidan cikin tashin hnkali yake banda
haj xeenat da itama sam saura ka'dan ta haukace sbd jin
nazli ta haihu kuma namiji. Yanda tashin hankalunta
yafito filine yasa dad qura mata ido amma sai baice
komaiba. Qarshe dai itama allurar akayi mata sbd jininta
daya hau lokaci 'daya. Qarfe tara ya farka amma da
tashin hnkali dan kuwa wani irin jijjiga yakeyi datasa
akayi asibiti dashi hankali tashe. Kwantar dashi akayi
asibitin sbd dr ya tabbatar musuda zancen daki xuciyar
sosai wanda yaso taba qwaqwalwarsa amma bai ta6a
'din ba saidai kuma fa dole anemo masa matarsa da 'dan
nasa. shiru sukayi cikin damuwa hardai fannah da
kullum saita kira wayar data siyawa nazli amma
batashiga abunda bata saniba shine agidan nazli tabar
wayar yashe akashe tun lokacin da tameer ya damqeta
da guba ahannu. Kano suka shirya ta jirgi sukaje amma
cikin rashin sa'a koda sukaje babusu sa'adah a gidan an
koresu. Hankalinsu bai tashiba saida suka kwana biyu
akano ana xagayen nemansu harda hotunan nazli ake
nunawa a gidan talabijin dakuma kyautar maqudan kudi
amma babu wani alamun za'a samesu. Komawa sukayi
jiki asalube da damuwa. Sannu ahankali ciwo ke cinsa
amma sbd yanason yaje nemansu da kansa yasa ya nuna
ya warke dan yanda yakeji aransa idan babusu
arayuwarsa xuciyarsa bugawa zatayi ya mutu dan ko
ayanxu 'din daurewa kawai yake amma yana cikin
tsananin tafasar xuciya. Tunda yadawo gida da hotonta
yake kwana wanda fannah tasaka masa a 'dan frame ta
dora masa kan bedside drower dake gefen gadonsa. Duk
iya yanda yaso sakewa kasawa yayi dan gabaki 'daya
farin ciki yabar gidan kowa cijin damuwa yake sbd
damuwar son aga su nazli 'din dakuma uwar damuwar
da tameer 'din yake ciki. Abinci ma dainaci yayi sai
ruwan lipton kawai yakesha shima kullum sai fannah tayi
masa kuka tace "B nazli 'dinka babu abinda takeso
kaman tameer 'dinta dan haka duk inda take xataji
ajikinta meer 'dinta yaqi cin abinci so zata shiga damu...
Bata qarasawa yake shanyewa ya miqa mata cup. πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰
mamuh geee πŸŒ•βšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngβšœπŸŒ• Na MAMUH GEEE β˜†dedicated
toβ˜† Husnah bbchoudiallo 196β†’200 Haj xeenat
al'amura sun tsananta gareta sbd tana cikin
tsananintashin hnkli na neman nazli da 'danta da akeyi
kullum sai dukiya alh zaid ke sakarwa jamian tsaro gashi
ta fara samun matsala da haj kareema sbd auren
meenah da tameer 'din da'aka fasa kuma haj bilki bayan
kareema tabi abun yana ca6e musu. Hankalinta bai qara
tashiba saida taji alh zaid yace angama zuba komai a
katafaren gidansa na kano daya maida sunan waleed
akan takardun gidan zasu koma kano harsai yaga
surukarsa da grandson 'dinsa da tuni an maida sunansa
ga wasu daga cikin takardun dukiyarsa. *********
KANO Yau sun tare a gidansu na kanon wansa yake
babba sosai shima kuma tsarinsa 'daya dana abj dan
haka kamar abj kowa irin 'dakinsa nacan ya 'dauka.
Tunda suka iso bai zaunaba kullum yana tareda manyan
jami'an tsaron gari ana masa bayani akan binciken. Yau
tun safe yayi order 'din masu gyara sukazo 'dakinsa
'daya dake cikin palonsa aka cire komai aka zuna kayan
wasan yara kamar hauka da gado da komai na 'dakin na
yara ne gar stickers 'din bango na spiders da ben10
komaidai mota,mashin da sauran tarkace. Wardrop 'din
'dakin kuwa kayan da aka xuba sunfi kala hamsin duka
masu shegiyar tsada hatta takalmi saidana gaji da
qirgawa. Duk na waleed ne his own son and his bst
friend.kaman yanda take cewa kenan. A 'dakinsa ma
abun haka yake domin kaya na fitar hankali ya siya
yacika wardrope 'dinsa dasu duk na nazli 'dinsa dayake
cewa she is his savior. Duk abunda yake su dad na lure
dashi sbd mugun tausayinsa sukeji dan gaba 'daya
kamar a 'dan xauce yake ga ciwo dayake dannewa tsabar
qarfin hali. ******** Satin su uku agarin ya 'daga
hankalin dad akan saiya kaisa gurin wa'inda aka nemi
auran nazli tun farko. Sai alokacin dad yama tuna dasu
suka kwasa sukaje su duka har haj xeenat daketa
shiryeshiryen cimma burinta dan tayi alqawarin kobata
aikasu duka lahiraba ta wlh saita aika koda 'daya
tsakanin TAMEER,NAZLI,WALEED,FANNAH KO DAD.
(readers wa kuke tsammanin xata kashe batareda
xuciyoyinmu sun karayaba ) Koda suka isa gidan haj
salamatu tana ganin haj xeenat tahau rawar jiki ba 6ata
tym sukace gidansu nazli na takai sukeson akaisu. Mijin
haj salamatu yanajin haka yasan kudi zasu samu yace
aiba matsala haj salamatu ta tashi suje. Suna isa qofar
gidansu nazli na takai nan take guri yacika ana kallonsu
sbd anga larabawa. Qofar gidan ya qurawa ido xuciyarsa
na harbawa sbd muguwar tausayin wainda ke rayuwa
acikin gidan. Savior 'dina anan tayi rayuwa taredani cikin
so harta haifi bbynah anan.hw i wish zanganki my savior
dazan xa6i rayuwa a inda yafinan muni idan har tareda
kene. Hw i wish kin haifamun babys da yawa ba waleed
ka'daiba. Fannah ta katse tunaninsa ta hanyar dafasa sbd
ta lurada yayi nisa tunani. Su haj xeenat ne suka fito
tareda ladingo da jummai sai wani rawar jiki suke har
qasa suka xube kamar zasu kwanta suka gaida alhaji
zaid. Tameer kuwa kallonsu yake kamar wasu halittu sbd
a koma'de suke sai tsami ke tashi tunda suka fito. Suma
kallonsa suke ko qyaftawa basayi sbd tunanin kamarsa
da shegen mahaukacin nan mijin nazli. Haj xeenat ta
katse musu tunaninsu ta hanyar miqa musu bandir 'din
dubu ashirin tace su wuce an gode. Kallon rashin
fahimta suka aika mata tace, Alh sunce nazli tun 'danta
na jinjiri tabar garin tareda tameer kuma basusan
qauyen da innah asma take bare su fada. Cikin 6acin rai
tameer yace, Dad zai iya yiyuwa qarya suke tunda basa
santa ni xan saka police su kamaminsu ayita horonsu
saisun fadamin inda my savior take. Da sauri dad ya
dafasa yana fadin, Calm down son bazasuyi qaryaba sbd
sunga kudi dan dasun san inda take dasun fada sbd kudi.
Muje my son ka qara hkr ankusa ganinsu. Jiki asanyaye
suka koma kano bayan sun sallami haj salamatu da
'dubu hamsin. ********** CAIRO lokacin da dad yayi
waya da haj nurat ya zyyane mata komai itama kukan
tasa masa tana fadin a kashe konawa xa'a kashe koma
duka dukiyarne a nemo mata nazli da jikanta 'dan
tameer 'dinta. Su ammah ma dasukaji 'yar tsohuwar
rikice musu tayi jin cewar harda 'da a alamarin kuma ba
abunda takeson gani kamar yarinyar dataso tameer
'dinsu alokacin hauka lkcn da bashida kowa. Saurin
dangi kuwa banda waleed ba abunda sukeson gani daji.
Qarshe dai haj nurat kasa xama tayi ta tarraro tayo
nigeria dan sam hnklinta yakasa kwanciya idan basu aka
ganiba. Lokacin data iso taga yanda tameer 'dinta
yakoma rungumesa tayi tana hawaye shima lafewa yayi
ajikin umminsa yanajin wani sabon radadin rashin
matarsa da magajinsa. ⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜ NAZLI(mai
fans da yawaπŸ˜ƒ) Rayuwa a sabon gidan da mijin anty
sa'adah take aiki ba laifi saidai kam ita tuni tayi
bankwana da farin ciki sbd rashin meer 'dinta ba
qaramar illace ba. Ciwon datake fama dashi a zuciyarta
shiya tabbatar mata da ciwon xuciyane yakamata sbd
azaba takeji sosai amma haka take rayuwarta sbd bata
tunanin akwai ciwon dayakai mata rayuwa babu meer
'dinta. Waleed kuwa ya sake suna zuwa wata makarantar
gwamnati dake 'dan kusa dasu kullum mijin sa'adah ke
kaisu da qafa yadawo. Ta rame sosai kullum cikin yimata
nasiha anty saadah take harta gaji ta bari ta zura mata
ido saidai addua. ******* Wayarsace tayi qara yana
kwance 'dakin umminsa kansa nakan qafarta tana
shafawa ahankali alamar rarrashi kamar shine waleed
'din😑. Ganin yaqi ko kallon wayar yasa haj nurat kallonsa
cikin muryar lallashi tace, My boy ka 'daga wayar mana
tunda kasan a nema muke zai iya zama cikin masu
neman ne wani yagan..... Bata qarasaba ya 'daga da sauri
kamar ance masa nazli 'din ce. Hey mr tameer ne kuwa?
Yes,yes nine. Hahhhhhhh tameer hameed lamido ne.
Duk da yana cikin damuwa hakan bai hanasa farin cikiba
sbd jin babban aminsa 'dan govnr din kano dasuka 'dibi
shekaru basu haduba sbd kasancewarsu basa zama su
duka. Hameed yace 'dazu naga p.a 'dinka a bank
yacemun kuna kano ku duka dasu dad. Ajiyar xuciya
yasaki tareda cewa Hameed matana da only son 'din sun
6ata anan kano. Wat. Hameed yafada da qarfi cikin
shock Tameer ur wife and ur son? To mekayi akan hakan
kaga muhadu yanxu kawai dan nima ina kanon. Ok
hameed send me ur address xanxo yanxu. Bayan
hameed ya turo masa address din ya miqe yafita dan
xuwa. Dakansa yake tuqin fannah data biyosa
tanagefensa xaune tana waya ammah tana kwantar mata
da hankali. Sun shigo anguwar gidan hameed 'din dai dai
saura qadan su isa qofar gida wani yaro yafito aguje da
'yar ball 'dinsa kadin tameer yayi wani motsi tuni ya
ka'desa. A gigice suka fito motar basu tsaya wata wataba
suka 'daukesa sai asibiti. Kunasn waye fans? WALEED NE.
πŸŒ•πŸŒ•πŸ‘‰mamuh geee

Please Login or Register in order to submit comment