Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bada karfine xai amshi kudi a gun amatullah ba, cikin dabara ne da hikima.

"Anty Frd bata kira amatullah ba saida tadawo daga aiki misalin takwas da rabi snn ta dauki waya xata kira amatullah.

"itama a lokacin amatullah ta kare aikinta daukar zannurai tai ta goya sbd tasamu damar mgn kafin Mahfus ya shigo.

"Anty Frd na kokarin kira, itama amatullah na kokarin kira, hakan yasa suketa gani number busy.

"saida daya ya hakura snn daya yakira ya shiga amatullah ne takira Anty Frd na gani da sauri tai picking call hade da cewa kedawa kike waya naita kira number busy nake gani?

"amatullah take kece nake nima.

"Anty tace ok, snn amatullah tace ina yini Anty.

"anty tace lpy klau ina yarona?

"amatullah tace gashi nan a baya.

"Anty tace ki gaida minshi.

"snn tace amatullah daxu hajiya ke fadimin wata mgn da gaske ne amatullah?

"amatullah tace name Anty?

"Anty tace amatullah me kikai da kudin hannu?

"idan kin kashe na hannuki ina wanda suke cikin account?

"ko duk suma sun kare ne?

"amatullah tace aa.

"Anty tace ina suke?

"amatullah tace sunanan.

"Anty tace idan har da gaske sunanan shine recharge card kawai yake gagaranki sawa amatullah, amatullah banyarda ba.

"amatullah banaso ki boyemin komai idan kinsan akwai matsala ki sanar dani.

"ni yar'uwan kice ta jini, bakida wanda tafini.

"jin motsin shigowar Mahfus ne ya hanata mgn sai hawaye.

"Anty tace ina sauraranki amatullah.

"gani yashigo har bedroom din yasata share hawaye da sauri tace wlh Anty babu komai.

"Anty tace amatullah idan kinsan akwai matsala kifadi ni yar'uwarki ce baxanga abinda xai cuceki na kyale ba.

"gani yadda Mahfus ya tsareta da ido yasata cewa allah Anty babu komai.

"himm kawai Anty tace tana jijina mgnr.

"jin shiru da taine yasata cewa hello.

"Anty tace ina jinki.

"amatullah tace da gaske Anty.

"Anty tace amatullah nasan kina matukar son Mahfus hakan yasa bakiso a fadi laifinsa.

"wlh amatullah duk ranar da allah yakawoni garin naga mgnr hajiya gaskiya ne wlh daga ke har Mahfus din saina maku rashin mutunci tunda ba ubanshi ya nimo mana kudin ba.

"kuma daga yau babu wanda xaisake baki ko sisi tunda bakisan ciwon kankiba.

"shiru amatullah tai tana hawaye har Anty takare fadinta ko sallama bata bari suyiba ta kashe wayar.

"tana kashewa Mahfus yace lpy me yafaru?

"amatullah tace babu komai.

"kwafa kawai yai snn ya tube.

"tun daga lokacin amatullah nata kwana biyu sai takira hajiya sun gaisa.

"ita hajiya idan taga lokacin kiran amatullah yayi bata kira ba ita saita kira.

"bayan kwana biyu da amatullah taga koda ta tambayi kudi dan bukatunta Mahfus baya bata, ita kuma bazata iya kiran gida tace abata kudi ba yasa ta yanke shiwarar fita da credention d'inta xata nimi aiki.

"da dare lokacin Mahfus yadawo daga kasuwa bayan yagama cin abinci har xai kwanta sai amatullah tace tanason mgn dashi.

"jin haka yadawo ya xauna kusa da'ita hade da cewa Allah yasa dai lpy?

"murmushi tai hade da cewa lpy klau.

"snn tace dama dama dama tsayawa tai tana inda inda.

"Mahfus yace dama me kiyi mgn mana.

"sae tace dan Allah niman izini nakeyi a gunka.

"tsareta da ido Mahfus yai snn yace name fa amatullah.

"sai tace dama aiki nakeso na nima koda a pravent school ne....

"da sauri Mahfus yace aiki fa kikace amatullah?

"shiru tai tana kallonsa.

"sae Mahfus yace amatullah akwai abinda kika nima kika rasane a guna?

"ko kuma kokuma kintaba tambayata wani abu naki yimiki?

"shiru amatullah tai.

"Mahfus yace dake nike mgn.

"hannu tasa ta rufe fuskanta hade da fashewa da kuka tana cewa to meyasa idan na tambayeka abu bakami?

"da sauri Mahfus ya matso kusa da'ita ya rungumeta yana cewa haba amatullah me kika bata yambayana banmiki shiba?

"idan har kinga kin tambayeni abu banmiki ba kin tabbata naga abu bame mahimmanci bane.

"idan kuma kince kudine amatullah me xai da kudi?

"nasan duk wani abu da xaki bukata nariga na tanada mikishi.

"idan Allah amatullah inaso kicire mgnr aiki a ranki, ba lailai bane kisan irin sonda nake miki.

"wlh amatullah ina matukar kishinki sosae, ba xan'iya bari kije kina gogaiya da wasu maza a waje ba.

"nafiso duk abinda kike bukata ki sanar dani, nikuma in allah ya yarda xanmikishi.

"idan kuma business zakiyi amatullah nasan baki rasa kudin da zakiyi ba.

"cikin kuka amatullah tace ina kudin yake?

"Mahfus yace bake kikace akwai kudinki a gun alhji Ibrahim ba, kiranshi xakiyi kice yabaki kudinki zaki rinka juyawa da kanki kinga idan yabaki shago xaki bude sai a xuba kaya aciki.

"idan ma bazaki iya xamaba ni inada wanda zasu xauna miki suna kula miki da kayan duk cinikin da akai sai a xuba miki a cikin account kina gida xaki rinka gani alert.

"shiru amatullah tai kamar ta amince Mahfus yafara jin dadi can kuma tace aa kabari kawai na hakura.

"Mahfus be nuna damuwa ba yace kokefa har naji dadi nagode da kika fahimceni.

"murmushi yake tai.

"Mahfus yace xomuje mu kwanta matata ta kai na, dagake babu wata kano one but you ya karisa mgnr ne da jawaota jikinsa.

"bayan watanni amatullah taji duk gaba daya yanayinta ya canxa ga kasala komai taci sai tai amai yauma hakane tun safe take amai shiko zunnurai yana can cikin yaran mmn junior yana wasa saidai idan bakin nono ya kamashi yadawo yasha yanajin ya koshi xai koma wasanshi.

"itako amatullah tana kwance motsi mai karfima bata iyayi da haka ta yini har Mahfus yadawo.

"yana dawowa yaganta haka shikuma zunnurai yana kwance kusa da'ita mmn junior tai masa wanka yana bcc babu riga a jikinsa.

"koda Mahfus ya tambayi amatullah kasa mgn tai sai hawaye hijab Mahfus ya dauko ya samata saida sukai zunnurai dakin inna snn yaxo ya dauketa suka tafi asibiti.

"suna xuwa gwajin kofar ya nuna ciki harna wata biyu gagguna aka basu suka dawo gida

"suna dawowa Mahfus ya sanarwa inna, sai inna tace kada a yaye zunnurai sai cikin yakai wata bakwai.

"da haka taci gaba da raino cikinta, yana kaiwa wata inna ta amshi zunnurai ta yayeshi.

"tanci tashi babu wiya cikin amatullah na kaiwa tawa tara ta haifi yar'ta baby girl suna dawowa daga asibiti Mahfus ya kira hajiya ya sanar da'ita haihuwa.

"hajiya tai murna sosae.

"anty bata samu xuwaba sai ranar suna, goma Anty su isa kano itada matan yya khamis.






H.S.Z.ceπŸ–Š
πŸŒΊπŸ’¦πŸŒΊ
πŸ’¦

MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)πŸ’¦

MMN USWAN
H.S.Z.

24

"gidan su na dah Anty Frd tanufa,

"koda ta'isa tanata knocking ba'axo an bude ba.

"gani haka yasa takira amatullah a waya tasanar da'ita gata a kofar gida.

"da sauri amatullah tace wani gidan?

"Anty tace gidan ku na dah mana.

"amatullah tace Anty ai mubar nan.

"Anty tace to yaya xa'ayi yanxu?

"amatullah tace bari Mahfus yaxo ya daukeki.

"Anty tace ok amma dan allah karya batamin lokaci.

"amatullah tana kashe wayar takira Mahfus, yana dagawa ta sanar masa Anty Frd ta'iso tana can gidan.

"Mahfus yace ok bari naje na dauketa.

"Mahfus ba tsaya bata lokaci ba yaja mota yaje daukota.

"yana isa yafito saida ya gaidata snn yakoma yashiga mota nashi na gaba tana yana baya.

"suka dauki hanya, gani Mahfus yai kwanan area dinsu yasa Anty cewa matan yya khamis kardai family house suka dawo?

"matan yya khamis tace haba dai nasan amatullah bataza iya xama a gidan ba sani kankine amatullah tafi kowa tsantsami.

"himm kawai nace.

"snn tace yau ko xanga ikon Allah.

"Mahfus yana isa yai parking yafito.

"itama Anty fitowa tai hade da cewa nan ne kuka dawo?

"Mahfus da fara'arsa yace eh Anty.

"matar yya khamis nafitowa hannu tasa xata dauki jaka.

"da sauri Anty tace barshi tuku.

"duk tana mgn ne fuska a daure.

"Mahfus yana gaba sukuma suna baya.

"kyale Anty tasa ta toshe anci.

"saida Mahfus yakai bakin kofa snn yace ga dakin nan.

"amatullah da sauri tafito tana cewa Anty sannunku da xuwa.

" wani irin salati Anty Frd tasake.

"tana fadin amatullah mai xangani kece haka?

"amatullah bata nuna damuwa ba, tace Anty dan allah kishigo ciki.

"kamo hannunta tai suka shiga ciki, ko takalmi bata cireba haka tashiga dashi.

"a parlour ta tsaya matan yya khamis tashiga cikin bedroom.

"amatullah jiki na rawa taje takawo mata abinci da pure water, tace Anty ga abinci.

"cikin xafin rai Anty tace tashimin dashi gaba ko nayi hurgi dashi.

"cikin sanyi murya amatullah tace Anty menene haka kuma dan allah daga xuwanki xaki fara.

"Anty tace ga masifenfiya taxo ko?

"dama nasan baki farin cikin xuna.

"shegiya mara tausayin kanta wanda batasan ciwon kanta ba.

"kuka amatullah tana fadin dan allah ya'isa haka.

"Anty tace wlh amatullah idan ina mgn kina sami baki sainaci uban ubanki.

"in banda rashin kishin kai irin naki da kinriga kin tare a gindinshi kin like har Mahfus ya'isa ya kawo maki rainin wayo haka?

"ji inda kike zaune fa sbd allah, dan tsabar rashin mutunci da rashin imani irin na Mahfus da rashin tsoron allah.

"idan ma beda kudin biyan wancan gidan dasai yakama maku wanda bekaishi tsadaba amma ba yaxo ya'ijeki anan ba.

"dubi kwata har bakin kofa, shi bayama tsoron kada wani cuta yaxo ya kamaku?

"to wlh bazan yarda ba yau d'innan xa'ayita takare ko ya canxa maki gida ko yabaki takar danki mu tattara mutafi tare.

"dubifa yadda kika koma kwata kwata aure bewuce shekara biyu ba amma ji yadda kika koma ko suturan arxiki babu, ji wani shegen yar'kunni kamar fulanin kauye ta karisa mgnr ne hade da daka mata tsawa tana cewa dan allah kije kisa daya daga cikin sarkokinki kisa.

"shiru amatullah tai ko gexau bata da alamar tashi.

"Anty tace badake nake yiba.

"amatullah tana mgn ne cike da inda inda tana cewa Anty wannan yaban sha'awa ne kawai yasa nasashi.

"hararranta Anty tai hade da cewa ok to yah sunan baby?

"amatullah tace suna hajiya akasa.

"da sauri Anty Frd tace wahhhh allah ya sauwake hajiya taxo a irin gidan nan.

"wlh amatullah kina bani mmki kodai asiri ne Mahfus yai miki?

"dubifa yadda kika koma ko suturun arxiki baki dasu, ina kayan auranki ko duk sun karene?

"da sauri amatullah tace duk suna ciki.

"Anty tace to muje nagani yanxu ace sbd Allah ki haihu amma suturan arxiki ya gagareki sawa?

"in banda ranshi mutunci da xalinci irin na Mahfus koshi ba xansiye mikiba tunda yanxu yana business kuma yana samu.

"wlh tunda nake bantaba gani mutum mara imani irin Mahfus ba.

"mikewa tai suka shiga ciki amatullah na biye da'ita a baya.

"suna shiga Anty tanufi gun wadrop, amatullah na gani haka tana kuka tana fadin dan allah Anty kibari wlh kayan duk sunanan.

"Anty tace ai bance basunan ba so nake kawai nagani.

"cikin kuka amatullah tace dan Allah kada ki dauke akwatin idan kika sauke ba xan'iya medasu ba.

"Anty tacr eh idan nagama ni xanmeda su da kaina.

"amatullah na gani Anty ta dauko da akwati tasa kuka kamar karamar yarinya.

"matan yya khamis na gani haka sai tace to ke Anty Frd kibari mana.

"Anty bata bariba saida ta bude akwatin daya bayan daya take bude akwatin da haka har taxo kan kid kafin ta bude da sauri amatullah ta dauke tana fadin aa Anty.

"Anty amatullah me xangani kibani ko sai na karba da karfi?

"kuka amatullah taci gaba dayi hade da tura kid din a bayanta.

"hannu Anty takai xata karbi kid din da sauri amatullah taja.

"haushi ya kamata batasan lokacin da ta dauke amatullah da mariba.

"jin xafi mari yasa amatullah sakin kid din yafadi, yana fadiwa da kanshi ya bude.

"babu komai aciki sai yar kananu paper.

"da sauri Anty ta daga kid dan tagani dakyau harda juyawa tagadai tabbas empty ne salati tasa da salalami hade da cewa amatullah mai xangani?

"zama amatullah tai abakin gado tasa sabon kuka.

"kukan da amatullah keyi yasa haushi ya kama Anty Frd kukan kura tai ta shakota tana fadin dan ubanki ina kikakai sarkokinki.

"amatullah najin shaka tasa ihu tana kiran Mahfus.

"jin ihu amatullah yasa zunnurai shigowa da gudu, gani yanda Anty ta shake amatullah yasa zunnurai kuka yana bubuga hannu Anty.

"gani yasa zunnurai fita da gudu gun bbnsa yana cewa bb, mm tana kuka kazo muje.

"ko kafin Mahfus yaxo amatullah taji jiki.

"daki yacika fal da mutani suna bawa Anty hakuri amma taki hakura.

"mikewa Anty tai da tafara xaxxaga masu ba'ina gaba daya suka watsa harda mmn Mahfus.

"babu juyin da Anty batai ba amma amatullah taki fadi.

"suna cikin haka Mahfus yashigo rike da zunnurai, Mahfus yana shigowa Anty tamike tajo kanshi hade da cewa bakin axalumi mugu mara mutunci, Mahfus na tsaye yana cewa me kuma nai miki?

"Anty tace kace haka mana bakin shege wlh yau saika sakanmin kanwata tunda abin naka rashin mutuncine.

"yau kafana kafarta, kuma duk kudin da kasan kaci mata wlh saika biya.

"hannu Mahfus yasa yanajan gemusa yana dibota daga sama har kasa yana xubarwa.

"joyawa yai xai fita a dakin batare da ya tanka mata ba.

"itama kyaleta ta dauka hade da cewa kitashi mutafi.

"amatullah taki mikewa da Anty taga haka danmara tai da kyaleta snn tacewa matan yya khamis ta dauko baby, hannu tasa ta fisgo amatullah xuwa waje hade da cewa dan ubanki idan ya mallakekine ni be mallakeni ba.

"idan kina tsoron ni bana tsoron shi, ko ubanshi be'isheni yiba banle shi.

"babu abinda amatullah keyi sai kuka.

"har sun fita daga dakin karaf Zainab tace badai ubanshi ba saidai ubanki idan kin dauketa kuntafi sai mai?

"akace miki yyan namu yarasa kudin da xaiyi wani aurene?

"shegu matsiyata kawai wanda basu gaji azikiba.

"Anty najin haka sake hannu amatullah tai da ta rarumo Zainab ta hadata da bango saida bakinta ya fashe snn taje xata hau ruwan cikinta.

" aguje Fatima da suwaiba suka shiganwa Zainab.

"itako Anty cewa tai kuxo ko kafatalin danginku ne xasuxo ba zasu hanani yin abinda nai niya ba.

"sai naci ubanku naci uban yya naku.

"mmn junior da taji haka aikawa tai aka kira Mahfus dake waje, tare suka shigo da yaron.

"gani su Zainab suna medawa Anty da mgn wani irin tsawa ya daka masu. yana cewa ashe rashin kunyar naku yakai ga haka?

"tana sa'anku ne?

"ko daku akeyi?

"wlh idan baku tashi kun bani gun ba, karma ace ke Zainab nasan kinfi kowa fitsari idan baki bacemin da ganiba wlh saina miki wanda yafi wanda ita tai miki.

"sunajin haka duk barin gun sukayi suna tafe suna guguni.

"Anty tace garadai da kafadi masu gaskiya mara mutumci kawai.

"Mahfus yace gaki babban mara mutunci banxa wanda batasan ciwon kanta ba.

"banxa wanda batasan abin kunya ba.

"juya kawai ba mmki shiyasa Allah ya hanaki haihuwa sbd bala'inki.

"wani irin kara Anty tasa hade da shako wuyar Mahfus, amatullah na gani haka aguje taxo tana kokarin cirewa Anty hannu a wiyar Mahfus.

"Anty na gani haka wani irin masga takaiwa amatullah gigicewa amatullah tai kadan yarage ta fadi Mahfus ya fisgota jikinshi.

"haushi yasake kama Anty sakin Mahfus tai takoma kan amatullah tana cewa yau koshine autar maza saikin barshi.

"hannu Mahfus yasa ya bugewa Anty nata tasaki amatullah a guje taje bayan Mahfus ta boye.

"dariya Mahfus yai snn yace kingani ko, to ko haka ya'isheki babu uban da ya'isa ya rabani da matata.

"Anty tace karya kakeyi, hannu tasa tasake fisgo amatullah.

"itako amatullah kara kankame Mahfus tai tana kuka.

"Anty sai faman Jan amatullah takeyi tana fadin koda asirine yai kimi yau saina karyashi.

"duk abinda sukeyi mmn Mahfus tana daki yar'uwanta su hanata fita.

"Mahfus janyo motarshi yai xuwa daki hade da rufe kofa.

"matan yya khamis na gani haka itama ta janyo Anty fikabar gidan.

"hade da mmki amatullah matan yya khamis na cewa amma amatullah tabani mmki waya cemata ana nunawa namiji so haka?

"karki damu nasan duk dare dadewa watarai da kanta xata nimemu a lokacin muriga mumata nisa.

"babu abinda Anty keyi sai huci matan yya khamis ta amshi key din mota suka shiga suka hauki hanya.

"saida Mahfus ya tabbata sutafi snn yabude kofa.

"suko masu suna kowa na fadin albarkacin bakinsa.

"amatullah kuka tai harda xaxxabi.

"Mahfus ne yaje ya hado mata maguguna tasha snn taji daidai.

"bayan sallar isha lokacin Mahfus yana daki shida motarsa mmnshi tai sallama inda take shiga ba nan take fitaba rashin mutumci sai wanda tamance, xagi kaf babu irin wanda amatullah bata shaba.

"babu abinda Mahfus keyi sai bata hakuri.

"haka amatullah ta kwana tana kuka, Mahfus yai lailashi har yagaji.

"su Anty basu isaba sai around 12AM suka isa gida.

"sbd dare yayi gidan su hajiya suka sauka.

"tun cikin dare sukabawa hajiya labara abinda ya faru.

"hajiya tai salati ta sanarwa ubangiji hade da mmki yadda amatullah ta lallace haka.

"matan yya khamis tace wlh hajiya asiri yai mata.

"sai hajiya tace babu kowani asiri, idan son mace yafi na namiji abinda yafi hakama xatayi.

"amma tunda ta nuna Mahfus yafimu shikenan mun barta dashi.

"daga yau sisina ba xai sake ciwon kai akanta ba.

"da haka dai sukai ta hiransu har safe.

"da safe bayan Mahfus yafita kasuwa mmn junior tashigo dakin amatullah, bayan sun gaisa ne mmn junior takewa amatullah fada akan abinda tai bata kyau taba.

"tana cewa idan banda abinki amatullah har Mahfus yafi miki yar'uwanki?

"karfa ki mance xaku iya rabuwa dashi amma bazaki iya rabuwa da yar'uwanki ba.

"kuma idan kika shiga wani hali mijinki saiya gujeki amma yar'uwanki bazasu gujeki ba.

"yanxu abin Allah ya kiyaye idan kuka samu matsala da Mahfus da wani ido xaki kalli yyaki?

"gaskiya amatullah baki kyauta ba.

"kan amatullah a kasa tace nagode.

"snn ta dauki baby taje tai mata wanka ita da zunnurai.

"tunda su Anty suka tafi babu wanda yasake kiran amatullah, itama kuma bata kira ba haka taci gaba da zama.

"ana kwana hudu da suna tun dare bilkisu ke kuka, amatullah tai lallashi har tagaji sai ta tada Mahfus daga bcc shima yai irin nashi amma ina.

"dakin inna sukaje Mahfus ya buga mata kofa tana budewa ya mika mata ita.

"inna tace kodai cikine?

"ruwan xafi hade da gishiri aka bata, duk da haka bata daina kuka.

"gani batai shiru ba sukace ko kuma kunni ne?

"man zaitun amatullah ta dauko a daki hade da auduga.

"inna ta diba kadai hade da audugun aka samata shima a banxa.

"da sukaga haka ruwa Mahfus ya dibo yai addu'a a ciki inna ta bata tasha hade da shafa mata, tana gamawa inna ta guyata.

"ko minti goma basuyi inna taji tana ajiyar zuciya, inna naji haka tasa salati da sauri Mahfus yace yah dai inna?

"inna tace babu komai.

"saida inna ta tabbata bilkisu tacika snn ta saukota ta shinfidata a tabarma.

"gani haka yasa Mahfus cewa inna yaya haka kuma.

"inna tace allah yai nashi ikon.

"Mahfus yace yanxu yanxu inna?

"inna tace yanxu yanxu sai Allah ba.

"kuka amatullah tasa.

"gani haka yasa Mahfus jan amatullah xuwa dakinsu, a nan gawa takwana ita da inna da mmn junior.

"da safe amatullah takira hajiya ta sanar da'ita rasuwa, hajiya tace allah yaji kanta.

"tunda amatullah tasanarwa hajiya rasuwa, hajiya babu wanda tafadimawa.

"amatullah har akai uku akai bakwai babu wanda yaxo banle yakira cikin dare tasawa Mahfus kuka.

"hakuri kawai yabata hade da lallashi suka kwanta.

"bayan sati uku amatullah tana kwance cikin dare taji Mahfus yana shafeta.

"da sauri ta bude ido tanaso taja baya Mahfus ya riketa yana cewa haba my wife ina xaki?

"kixo mu kwanta mana.

"amatullah naji irin shafan da yake mata tasa kuka.

"Mahfus yace haka amatullah saikace yau ne farko yinmu abunan munyishi yafi a karga.

"kuka amatullah tasa tana zaiyana masa abinda yaiwa Anty bataji dadi ba.

"Mahfus tunda yana niman biyan bukatarshi be nuna damuwa ba, kara kwantar dakai yai yana bata hakuri.

"ga yaga ta matsa da kuka yace haka amatullah meyasa tun ranar baki nuna damuwa ba sai yanxu?

"kamar wanda aka xugata.

"kara jawota yai ya mannata a kirjishi yakawo bakinshi daidai kunninta yace yauwa matata ta kaina fadimi waye ke xuga minke yakeso ya shiga tsakaninmu.

"yauwa fadimin my amatullah.

"Mahfus yana mgn ne hade da yi kamar yana yimata tausa fuskanta kuma bi yake daki daki yana yimata kiss.

"cikin shagwaba amatullah tace ba mmn junior ne tace bankyau taba, wai ina kallon kanaciwa yyata mutunci.

"cikin dimauta da niman biyan bukata Mahfus yace kyaleta kawai kinfi kowa sani ina matukar sonki ba xan iya bari a daukemike ba.

"kuma inba haka naiba nasan Anty tafiya dake xatai.

"amma kiyi hakuri baxan karaba kinji.

"kai kawai tadaga masa.

"da haka har Mahfus yasamu ya biya bukatarshi.

"har safe Mahfus lallaba amatullah yakeyi, tunda yana samun biyan bukatarshi.

"da safe lokacin Mahfus yashirya fita kasuwa, yafita kenan daga daki xaije dakin inna sukai karo da mmn junior da fara'arta tace maigidan katashi lpy?

"ko kallon bata isheshi ba banxa yai da'ita yashige.

"ita kuma bata kawo komai a ranta ba taci gaba da aikinta.

"koda Mahfus yafito daki inna haka yaxo ya sakai batare da ya kulata ba.

"ita kuma cewa tai maybe yau da gobe ne.





H.S.Z.ceπŸ–Š
πŸŒΊπŸ’¦πŸŒΊ
πŸ’¦
MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)πŸ’¦

Fasaha online writes F.o.w.

MMN USWAN
H.S.Z.

25

"tana kare aikinta takira zunnurai tai masa wanka yadda tasaba.

"mmn junior tana kyautatawa amatullah ne ba sbd komai ba sbd abin hannu amatullah baya rufe mata ido.

"mafi yawanci lokacin takan taimakawa mmn junior game da kayan abinci suturu daidai abinda baza'a rasaba.

"harma kudi a lokacin da take dashi takan taimaka mata dashi ko biyawa yara kudin makaranta school feel.

"ko yanxu ma da bata da kudi still bata daina taimaka mata ba.

"tunda mijinta baya aikin komai duk wasu hidimomin gida itace.

"hakan yasa tun daga wayewar gari tana sauka daga gado bata sako komawa har dare tanan tana niman abinda xata rufawa kanta asiri da yara.

"ita kuma uwar mijinsu irin mutaninanne wanda sai kanadashi akeyi dakai.

"shiyasa da taga batadashi miji ma bedashi bata shigewa inna sbd kada ta fadi mata abinda xai dameta.

"itama amatullah da talura da haka duk kyautan da xataiwa mmn junior bata bari inna tasani.

"yawanci lokuta ma inna bataso ta gansu tare da amatullah sbd kada ta sanarwa amatullah wanene su.

"abinda yasa kenan mmn junior bata gani yar'shin yiwa amatullah aiki.

"sbd inba aiki tai mata ba bata da wani abun da zatabawa amatullah a matsayin kyautatawa.

"da yamma lokacin mmn junior tana rabawa yara abinci Mahfus yashigo kai tsaye daki yashiga batare da yai mgn ba.

"ita kuma gani tai irin abinci Mahfus yafi shiyasa ta diba a plate tabawa junior yakaiwa Mahfus.

"saida junior yai sallama amatullah ne ta amsa snn yashigo hade da cewa gashi iji mmn wai abawa uncle.

"amsa amatullah tai hade da godiya.

"da sauri Mahfus yace meda mata dashi cike bazan ciba.

"haka junior ya medawa mmnshi.

"duk da haka bata nuna damuwa ba tunda dama ba'isan su yai ba.

"cikin dare suna kwance Mahfus yake cewa amatullah daga ya hanata hulda da mmn junior, ko tsakar gida ma bece ta rinka fitaba.

"idan ma tagaji da xaman daki taje dakin inna, daga dakin inna bece tashiga kowani daki ba.

"amatullah tace to naji.

"da safe Mahfus yashirya yafito zai tafi kasuwa mmn junior tace maigida jiya na aiko maka da abinci dace bakaci.

"eh kawai Mahfus yace batare daya kallenta ba.

"tun daga lokacin amatullah ta daina fita waje, koda dama ba fita takeyi ba.

"ko wani lokacin amatullah tana daki ita da zunnurai, idan kaji hiranta mmn junior ne tashi mata ko kuma xatayi wanki shine xata fito waje tana gamawa xata koma daki.

"bayan kwana biyu inna tace su amatullah da mmn junior su shirya suje gaisuwan rasawa.

"kamar Mahfus ya hana dan dai babu yadda zaiyine.

"yana fita suma suka shirya xuwa gaisuwan, suna cikin napap mmn junior tace amatullah naji wani mgn a gun bbn junior da gaske ne?

"amatullah tace na mefa?

"mmn junior tace kwanakin baya bbn junior yake min hira ashe kudin kine Mahfus ke juyawa?

"murmushi kawai amatullah tai.

"mmn junior tace ke amatullah meya kaiki?

"meyasa kike abu babu shawara ne sbd Allah?

"wlh inda kin shawarce ni. ba zanbari ki bashi ba.

"kiba tunanin inba mutuwa akawi rabuwa?

"abu allah ya kiyaye akace yau baku tare kina gani Mahfus xai dauki kudinki ya baki,?

"kema kinsan abinda ba xaiyu neba.

"amatullah tace ba haka bane mmn junior gani nayi lokacin yana zaune babu sana'a ne shiyasa.

"mmn Junior tace dan baya sana'a sai me?

"bayai karatu ba?

"mai xaihana baxai dauki takardanshi yaje yanimi aiki ba.

"duk guri yasamu inda yaga baki dashi dole yaje ya nimi aiki ai.

"shiru amatullah tai tana sauraron mmn junior.

"mmn junior tace amatullah har yanxu bakisan waye Mahfus ba shiyasa.

"a lokacin ne amatullah tace mmn junior kenan shekaranmu biyu fa dashi, shine xakice har yanxu bansan waye Mahfus ba.

"mmn junior tace bawai nace yanada wani mugun hali bane amma inaso kisan Mahfus mutum d'an adam ne yana iya sauyawa a kowani lokaci.

"ajiyar zuciya amatullah tai hade da cewa haka ne.

"mmn junior tace wlh amatullah koni da kike gani mu haihu har yara biyar bazan iya daukar kudina nabawa bbn Junior ba, banle har miliyoyi.

"mmn Junior tace amma kiyi hakuri karkice xugaki nakeya.

"amatullah tace aa ba komai nagode.

"bayan amatullah tai arba'in tacewa Mahfus tanaso taje gida.

"Mahfus yace yafiso ya kaita da kanshi bayaso ya sata a motar kasuwa amma akwai kayan da yakesa sa rai za'a kawo masa kwanan nan tabari idan ankawo sai sutafi.

"bata nuna damuwa ba tace allah ya kaimu.

"sati biyu yaxo har yawuce shiru babu mgnr tafiya, har aka shiga sati uku shima shiru,gani anshiga na hudu amatullah tasake mgn.

"wata karyan Mahfus yasake shirya mata.

"kusan kowani lokacin amatullah tai mgn Mahfus yasan irin karyan da xai shirya mata.

"abu da yafi dagawa amatullah hankali

Please Login or Register in order to submit comment