Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba.

"Mahfus yana zaune a shagonshi nasir yashigo bayan sun sake gaisawa nasir yake tambayar zunnurai.

"Mahfus yace yau kwanansu biyu kenan bansan inda sukaje ba, shida mmnshi.

"nasir yace what?????

"Mahfus kasan abinda kake fadi kuwa?

"cikin nuna halin ko inkula Mahfus yace nasir kenan amma kafi kowa sani amatullah xamata takeyi kuma tana karkashin ikona ko.

"nasir yace kwarai da gaske.

"Mahfus yace to shine xatai gaban kanta tai tafiya batare da ixini naba.

"hakan yasa nasha alwashin babu inda xanje duk inda taje xata dawo ta sameni.

"nasir yace Mahfus kenan idan kai haka baka kyauta ba, kai namijine bazaka hada tunaninta da nakaba.

"banlema nasan amatullah tana sonka haka kawai bazata gudu ba, batare da wani dalili mai karfiba.

"Mahfus yace ok dama ashe xargina kakeyi a tsakanin zamana da amatullah.

"nasir yace haba Mahfus wani irin mgn kakeyi haka?

"Mahfus yace hakane mana kwata2 idan mgn tsakanina da amatullah ne kullin nine mai laifi.

"bansan meyasa ba nasir kodai akwai abinda na tsare maka ne?

"nasir yace niko me xaka tsaremin Mahfus?

"kaidai kace kana fushi da bansamu xuwa gun bikin kaba.

"Mahfus yace wannan ba damuwata bane.

"nasir yace ni dai shawarata dakai shine koda wayane kabuga gidan su amatullah kaji ko can taje.

"Mahfus yace kai idan tadameka xaka iya tafiya kadawo da ita.

"nasir yace kaima kasan inda matata bama xakasan anyiba.

"Mahfus ko yanxu xaka iya medata matarka ai sbd naga kafini damuwa da'ita.

"da mgnr ta xafi nasir cewa yai ko xaka gwada sakin tane.

"Mahfus yace ai basai na saketa ba.

"gani ranshi xaibaci da yawo yasa nasir fita daga shagon.

"saida amatullah takai kwana bakwai snn Anty Frd taje gidan su hajiya.

"bata dade da xuwa ba yya khamis yashigo itama amatullah tafito duk suka hadu a parlour.






H.S.Z.ceπŸ–Š
πŸŒΊπŸ’¦πŸŒΊ
πŸ’¦

MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)πŸ’¦

Fasaha online writes F.O.W.

28

"suna hada ido da Anty amatullah tace Anty ina yini.

"klau kawai tace batare da ta kallenta ba.

"yya khamis ne ya juyo gun Anty Frd yace Frd ga amatullah nan taxo wai sun samu matsala da mijinta.

"babu abinda yafito bakin Anty Frd sai to ni ina ruwana, can tamatse masu.

"yya khamis yace be kamata kice haka ba, kefa babbace tamkar uwa kike a gunta.

"Anty tace ai batasan da haka ba, idan tasan da haka da bata tayi mijinta ba.

"kaga koba komai ta nuna yafini kenan a gunta.

"dan haka babu ruwana taje can su kara rata.

"Anty tace gaba da cewa wlh yya khamis bafa son Mahfus ne batayi ba, nasan wiya ne yasa ta gudo.

"idan yanxu xai kirata yai mata dadin nasan komawa xatai...

"amatullah tanajin haka tafashe da kuka tana fadin dan allah Anty kiyi hakuri wlh nagane kuskure na.

"Anty cewa tai himm da kikaji wiya ba?

"amatullah rike kafar Anty tai tana fadin dan Allah sister kiyi hakuri.

"gani irin kukan da takeyi yasa yya khamis cewa ya'isa haka amatullah karki damu babu inda zaki in allah ya yarda muna nan tare.

"a lokacin ne hajiya tace to ai ba sakinta yai ba.

"yya yace wata sabuwa.

"juyawa yai gun Anty snn yace toke Frd ta'ina kike tunani za'a bullo wa lamarin..

"Anty tace wahhhh ni himm.

"yya yace himm ba mgn bane Frd.

"yazed dake gefe cewa yai wlh Anty kotu yakamata akaishi yabata ta kardanta kawai.

"wani irin mugun kallo Anty tai masa.

"daga snn besake cewa komai ba.

"snn yace nidai a nawa shawaran komawa yakata tai.

"yya yace sbd me Frd.

"sai Anty Frd tace sbd idan har da gaske ne tagani da xama dashi ita da kanta zata nimi hanyar da zasu rabu amma ba taxo tana mana kukan karyaba.

"wlh yya idan har kasake ka kashewa amatullah aure daga baya xataxo tana kuka dakai.

"idan har mace tagaji da xama da namiji lokacin da xata kashe aure basai ta shawarci wani, duk macen da ta tsaya niman shawara to wlh akwai rayuwar soyayya a tsakaninsu.

"dan haka tashi xatai ta koma idan har ta amsa sunanta mace inaso tadawo da takardan sakinta gidan nan, batare da wani ya tayata ba.

"mgn ya gagari amatullah sai kuka.

"su hajiya da yya khamis sukace kuma mgnrki gaskiya ne Frd.

"yya khamis yace tunda yau dare yayi abari gobe idan Allah ya kaimu sai yazed yakaita har gida.

"shiru hajiya tai batace komai ba.

"saida sukai hira sosae snn yya khamis da Anty Frd suka mike yya khamis ya dauki fifty thousand yabawa amatullah itama Anty Frd twenty thousand tabawa amatullah hade da fatan ta sauka lpy.

"godiya ya gagari amatullah sai kuka.

"saida suka sallami hajiya snn kowa ya kama kansa.

"tunda nasir yakoma gida babu abinda yakeyi sai tunani mgnr Mahfus,

"sai faman juyi yakeyi akan gado hade da mmkin Mahfus yanxu ya canxo.

"washe gari da safe suna karyawa hajiya tace sufito su tafi, amatullah kuka tasa kamar karaman yarinya.

"dakar tafito hajiya tabawa zunnurai su sweet bobo chocolate har xai shiga mota hajiya tasake daukar kudi tasa masa a cikin aljihu snn ta rungumeshi.

"zunnurai yana shiga mota ya dagawa hajiya hannu yana yimata bye bye har saida mota yashige.

"itako amatullah kasa sallamar hajiya tai sbd kuka.

"zunnurai saida yaga yadai na hango hajiya snn ya sauke hannu.

"suka fara hira da uncle yazed, basu dade suna hiranba bcc ya daukeshi.

"tun wayewar gari fadi take ta Jan hankalin Mahfus hakan yasa ya kasa xuwa kasuwa 24 hour tana nan available duk lokacin da waywayeta sbd magugunar da ta bashi yasashi bayajin kasala kowani lokacin suna like da juna.

"tun bayan tafiyar amatullah mmn Junior take ta kokarin kikarinta ta waya amma bata samunta da tagaji ta hakura.

su yazed basu isa ba sai bayan azahar.

"lokacin Mahfus sunyi nisa wajan wasa shida fadi guje guje sukeyi a parlour kamar wasu yara kananu.

"gateman yana gani amatullah ne da sauri ya bude mata gate.

"suka shiga tana gaba yazed yana rike da zunnurai suna biye da'ita.

"suna isa bakin kofar falo yatsaya sallama, su Mahfus basu jiba sbd su sautin da suka sa.

"da taji shiru kai tasa tashiga, tana shiga Mahfus yaje kamo fadi karaf yai ya kamo amatullah, amatullah tana gani haka hannu tasa da karfi ta igije Mahfus da baya yaje ya fadi akan cushion.

"ko kallonsu batai ba kai tasa ta shige dakin ta yazed yana biye da'ita zunnurai yana gani bbnshi xamewa yai ya sauka a jikin yazed da gudu yaje ya rungume Mahfus.

"fadi tana gani haka shigewa tai dakinta itama, Mahfus yana gani tashige da sauri ya dauke zunnurai yabita.

"tana shiga gefen fado ta xauna hade da xabga uban tagumi sbd har cikin xuciyarta bataso dawowar amatullah gidan ba.

"Mahfus yana shigowa rungumarta yai yana fadin haba baby menene abin damuwa kinfi kowa sani bafa ninace tadawo ba, idan haka babu ruwana da'ita.

"ke kadaice tilo a raina daya kike tamkar da goma haba matata ta kai.

"fadi najin haka wani irin murmushi tai kanta yakara kato abin nima yasamu.

"yazed dakin amatullah yashiga, yana shiga kan cushion ya xauna zunnurai ya haye masa jiki yana wasa.

"kitchen tashiga ta bubude foodplast shikafa da miya tagani dayan kular kuma farfesun nanan kaji tagani.

"plate ta dauko guda uku ta karkasa shinkafan saida taga yakare snn ta ije kular snn ta dauko na miya shima duk taxuba shiko na kaji dauka tai gaba daya takai daki.

"snn takoma ta dauko juice da ruwan sanyi a frg hade da cups takoma daki.

"sunaci suna hira har suka gama ci, suna gamawa yazed yace xaije sallah.

"itama mikewa tai tahada kayan abincin gefe guda sbd akwai raguwa snn tashiga toilet alwala.

"tana fitowa tasa key tarufe dakinta snn tafara sallah.

"zunnurai yana zaune yasa wasa.

"gani magrib yai yayi yazed bedawo ba, hakan yasa amatullah kiransa ta waya.

"a bunka da samari cewa yai Anty ki kwanta kawai saida safe, be saurari me xata ceba ya kashe wayar.

"itama batai tunani sake kiransa sbd hayaniyar jama'i da taji.

"tana ije wayar ta dauki ragowar abincin taci ita da zunnurai, suna gamawa sukai wanka suka kwanta.

"ana idar da isha fadi taje kitchen daukowa Mahfus abinci taga wayab babu komai a kula hatta farfesun kajin da tamasa shima babu.

"raita yabaci sosae, komawa tai tasanarwa Mahfus.

"a fusace yabufi dakin amatullah, koda ya murda hannu kofar gam yajita sai yakoma bugawa Mahfus yabuga har yagaji amatullah tana jinshi amma tai banxa dashi.

"da Mahfus yaga batada niyar budewa yasashi komawa dakin fadi babu yadda Mahfus beyi da fadi ba akan tasake wani girki amma taki tace saidai susha tea.

"Amatullah tana idar da sallar asuba tashiga kitchen ta hada masu abin breakfast aris da kwai tana gamawa ta kwashe xuwa dakinta.

"ashe Mahfus yana dawowa daga masallaci ya ganta a kitchen duk a nashi tunani harda ta hada kayan breakfast din shiyasa sukai kwsnciyarsa a daki.

"itama tana shiga dakinta ta medaki ta rufe kofe da key.

"zunnurai yana tashi sukai wanka suna gama shiri yazed shigo, a parlour ya xauna sai amatullah tace yashigo bedroom.

"anan ya xauna ya karya bayan yagamane sukai sallama har bakin gate amatullah ta rakashi saida yatafi snn tadawo ciki.

"lokacin da yazed yashigo Mahfus yana toilet yana wanka shiyasa fadi tasamu damar fita kallon amatullah da kanita.

"duk da taga kama a fuska amma besa tabar wa zuciyanta ba.

"komawa da daki Mahfus yana fita daga toilet fadi take fadi masa amatullah takawo wani kato har dakinta...

"da sauri Mahfus yace kinga fuskanshine?

"fadi tace eh sbd batasan ina kallansu ba saida na kare masa kallon.

"sai Mahfus yace yah subfabshi yake?

"nanda nan fadi tai described dinshi.

"murmushi Mahfus yai hade da cewa kanitane wanda yakawota.

"rai fadi yabaci sbd burinta becika ba.

"sai tasake cewa idan kanitane aina suka samu irin wannan dankareriyar motan da har za'a sakarwa yaro karami yanaja.

"murmushi kawai Mahfus yai, snn yace jeki ki hadomin abinci.

"batare da musuba taje kitchen daukar abinci taga babu komai.

"dawowa tai ta sanar dashi.

"Mikewa yai dagashi sai towel yaje dakin amatullah samuta yai zaune tana wasa da zunnurai.

"Mahfus yace amatullah ina abin breakfast dinmu.

"shiru tai babu amsa.

"Mahfus yace badake nakeyi ba.

"nan ma shiru tai.

"Mahfus da yaga bata da ninyar mgn fita yai yakoma dakin fadi yace taje ta hada masa.

"haka ta tashi tashiga kitchen akwai kawai ta soya masa hade da breed sai gasanshen nama, tana gamawa ta xuba a tire.

"ita kuma amatullah tana dakinta zaune sai zunnurai yace xaisha ruwa.

"dubawa tai taga ruwa da take ije masa a daki yakare hakan yasata fita xuwa kitchen dibo masa wani.

"ta fita har xata shiga kitchen a daidai bakin kofa sukai karo da fadi gaba daya abincin ta watse a kasa.

"da sauri amatullah ta duka tana kashewa hade da cewa kiyi hakuri bansan kina fitowa neba.

"a fusace fadi ta wuce taje ta fadiwa Mahfus, tare suka fita inda Mahfus yake shiga ba nan yake fitaba harda cewa muguwa yar bakin ciki idan kinyi haka dan kihadani da amaryata ne to wlh ta Allah ba takiba.

"dama malamai sunsha fadi akwai mata masu bakin ciki da maxajensu ashe kina daya daga ciki bansani ba.

"wlh amatullah fadi tafi karfinki wawiwa kawai dabba mara zuciya wanda ko kwanciyar aure bata iya ba.

"wlh amatullah bantaba jin dadin aure ba saida Allah ya hadani da fadi, shine nasan nayi aure.

"amma dah ina zaune da mace kamar ina zaune da jaka.

"fadi tace yau baby fadi mata tasan cewa bata da muhalli a zuciyarka.

"Mahfus yace kwantar da hankalinki honey inda tanada hankali hakan da nai mata ya'isa tagane haka.

"amma dayake jakace kinga bata gane ba...

"wani irin tsawa amatullah ta daka masu hade da cewa ya'isheka haka Mahfus,

"banxa jaki butulu wanda besan me sonsaba, matsiyacin banxa wanda be'iya cin duniya ba.

"acikin yar'iskan ma kai karamine mugu alxalumi maci amana.

"amatullah bata ankara taji daukan mari a fuskanta.

"daga hannu tai xata rama fadi taja Mahfus hade da cewa sweet xomatafi karka bata lokaci taxo tai mana asaran ciniki, kasan duk inda matsiyaci yake saiya nuna halinsa.

"rungumarsa tai har bakin mota yana shiga ya fisgi mota yafice.

"kafin tadawo amatullah tashige daki.

Zama tai abakin gado tasa kuka.

"itako fadi koda makka da madina aka biya mata iya kacin murnara da xatai kenan.

"tunda amatullah tashiga daki bata fitoba saida zunnurai yace zaici abinci.

"tana rike da hannunshi suka shiga kitchen indomie ta dora masa har ya tausa taxuba jin wayarta na ringing tacewa zunnurai yajirata ta dauko.

"dama fadi na makale a bayan kofa, amatullah tana fita fadi tashigo hannu tasa tai hurgi da tukuyan abincin kadin yarage ya xubawa zunnurai a jiki da sauri ya kauce hade da ihu.

"amatullah najin ihunsa a guje tafito gani indomie din a kasa yasata cewa zunnurai wayace kadawo tukiyar?

"cikin isa fadi tace nine nan.

"amatullah tace haba fadi menene haka?

"fadi tace ubanki ne...

"da sauri amatullah tace ubanafa kikace fadi?

"me nai miki?

"fadi tasake cewa nace ubanki ne banxa jaka wanda miji besan da xamanta ba.

"ni wlh inda nineke da tuni nafita nabar gidan.

"murmushi amatullah tai snn tace fadi kenan idan baki saniba to yau xansanar dake koda dakina Mahfus yai saidai yakwashi kayansa a gana masgo yabar gidan nan.

"kinga gida mota shagunan da yake gadara dasu rabkatakaf mallakinane.

"idan naga dama yau xankaishi kotu kuma dole yabani kayana...

"cikin kaukausan murya fadi tace karyane yar matsiyata.

"amatullah tace gakunan babban matsiyata daga ke harshi wanda basusan mutunciba.

"hannu fadi tadaga xata wankawa amatullah mari, da sauri amatullah tarike mata hannu hade da juya wa.

"daga nan danbe yatashi danbe sukai sosae, garin danbe duk sun wargaza kayan ciki zunnurai sai faman kuka yakeyi.

"da fadi taga bazata in'ma amatullah ba wuka ta dauko ta halbawa zunnurai, a guje amatullah tasaki danbe tai kan d'anta.

"gani besameshi ba wani tasake daukowa ta halba sai hannu amatullah.

"a guje amatullah ta dauki zunnurai xuwa daki.

"tana gudu fadi na binta tana fadin saina halakaki yau ko ke ko d'anki.

"duk da uban jinin da hannu amatullah keyi besa ta tsaya ba, har saida tashiga daki tasa key snn ta dauke zunnurai.

"gani jini a hannu mmnshi yasa ihu.

"ita ko fadi tana bakin kofa tana fadin saidai in bazaki fitoba wlh yau sainaga bayanki.

"toilet amatullah tashiga ta wanke hannu gani jini be tsaya ba tsunma tasamu ta daure hannu dashi.





H.S.Z.ceπŸ–Š
πŸŒΊπŸ’¦πŸŒΊ
πŸ’¦

MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)πŸ’¦

Fasaha online writes F.o.w.

MMN USWAN
H.S.Z.


29


"da fadi taga tsayuwar bazai in mata ba, komawa parlour tai ta xauna.

"tunani takeyi kala2 ita ina xata bullo wa amatullah?

"can daga baya wani tunani yaxo mata a take wani murmushi keta tai tashi tai takoma daki.

"Itako amatullah tana daki da kar tasamu jini ya tsaya snn ta kwance tsunman.

"fadi saida tabari yamma yayi daidai lokacin Mahfus ya kusa dawowa snn ta dauki wuka ta hanke hannunta jini yana fara xuba ta gwagoga a jikinta snn taje ta kwanta duk xani gado saida ta bata da jini.

"jin shigowar Mahfus tasa wata uwar kara hade da kuka.

"Mahfus yana shigowa tun daga parlour yafara gani jini.

"salati yasa da sauri ya karisa ciki gani yai kofar amatullah kofar fadi hanyar kitchen duk jini yasashi lekawa kitchen yaga gaba daya sun warga kitchen.

"mmki ne ya kamashi komawa yai yaje yashiga dakin fadi, fadi na ganishi tasake narkewa taci gaba da kuka.

"da fadi kwance cikin jini yasa Mahfus karisawa gunta da sauri hade da tambayar lpy me yafaru?

bata tambashi amsa ba.

"gani jinin kota ko'ina yasa Mahfus cewa ta tashi sutashi asibiti.

"hannu yasa ya dagata hade da samata hijab suka tafi asibiti.

"a hanyar dawowa ne yake tambayarta abinda yafaru, fadi najin haka tasa sabon kuka.

"da kar Mahfus yasamu tai shiru, snn tace dama duk lokacin da katafi kasuwa haka takeyi tasani a gaba.

"ni bansan abinda na tsare mataba a gidan nan.

"motsi kadin nai sai ta hau xagina da gori, har cewa takeyi wai koda mutuwa kai banida gadon ka.

"sbd gaba daya kudin da kake business dashi da gida da motar da kake hawa wai duk kudin tane.

"yau ma hakane tunda katafi kasuwa take ta zage zage wai saida nafita nabar mata gidan tunda bada kudin ubana aka gina gidan ba.

"da taga bantanka mata shine ta dauko wuka wai kona fita ko takasheni.

"idan ma karya nai kashiga dakinta xakaga hannunta da ciwo garin ta sokamine ta yanke hannunta.

"kullin haka takeyi yau ma banso kasani ba, sbd banason gani bacin raika amma saida tajawo abinda xai bata maka rai.

"karisa mgnr tai da kuka tana fadin dan Allah ka taimakeni wlh Mahfus nagaji da xaman gidan ka dan Allah ka medani gidan mu.

"tun kafin ta kasheni sbd tace yau a gidan koni ko'ita.

"kuka takeyi sosae harda shasshaka.

"cikin zafin rai Mahfus yace kada kidamu fadi ni nasan kina sona shiyasa har kike gudun bacin rai na.

"amma kinga ita da bata damuba kullin niman abinda xai batamin rai takeyi.

"garama da Allah yasa tai haka kinga yau na babbata tana bakin ciki dani.

"da sauri fadi tace wani irin dakai.

"Mahfus yace eh mana fadi duk mutumi da yace baya sonki to ai nine beso, kodan bakisan yadda nake sonki bane fadi.

"Dan Allah fadi kiyi hakuri wlh bazan iya rabuwa dake ba koba second daya ne, banle na kwana.

"fadi tace nidai in har tana cikin gidan wlh bazan iya kwana a ciki ba sbd tsoro nakeji kada cikin dare taxo ta yankani.

"da sauri Mahfus yace idan mgnr amatullah karki damu tun nariga na yanke hukunci akanta.

"jin haka wani irin murmushi keta fadi tai batare da Mahfus ya gantaba, taci gaba da cewa hatta zunnurai ma idan bakanan hanashi xuwa guna takeyi.

"koda hannunsa na rike da sauri xata fisgeshi sushiga daki, idan har kaga tabarshi yaxo guna to kana gida ne.

"Mahfus cewa yai duk ki kwantar da hankalinki.

"itako amatullah jin shiru da tai ne yasata fitowa ta hadawa zunnurai tea sbd yadameta da kukan yunwa.

"kafin tafito daga kitchen din da tashiga zunnurai yaje ya kunna TV yana kallon, koda tadawo tayi2 sukoma dakin amma zunnurai yaki sbd kallon yariga ya dauke masa hankali.

"tana zaune zunnurai yana shan tea suka shigo ko daga ido batai ba banle tace tanuna tasan da shigowar su.

"kan three ster fadi ta kwanta tana jiran result.

"tsayawa Mahfus yai akan amatullah wani irin tsawa Mahfus ya daka mata yana cewa keeeee da sauri ta daga kai ta kalleshi Mahfus yace tashi kifita min daga gida.

"amatullah ko gexau idon ta yana kan zunnurai.

"Mahfus yace ko bakiji abinda nake fadi bane?

"nan ma shiru tai.

"hannu ciwon Mahfus ya kamo yafara janta xuwa waje.

"mikewa tai tana kokari fisge hannuta.

"zunnurai yana gani haka mikewa shima yai yanabin su yana kuka, garin tashi tea din yaxube.

"nan suka kama kokuwa suna danbe da Mahfus, duk da haka Mahfus be saketaba saida ya fitar da'ita waje.

"duk inda sukai zunnurai yana biye dasu, gani Mahfus ya tura mmnshi waje shima fita yai yana kuka.

"hannu Mahfus yasa ya dauki zunnurai hade da cewa xomuje ciki yarona.

"zunnurai kuka yakeyi yana fadin momi xomuje ciki, kinji momi xomuje wajan dady.

"Mahfus yace kyaleta kawai my son rabu da'ita ga mominka a ciki' kaji.

"zunnurai yace aa dady xanje momi.

"bude masa ido Mahfus yai yana cewa dan Allah kaimin shiru ko...

"kafin ya karisa amatullah fisge d'anta tai daga hannu Mahfus.

"nan suka kama kokuwa tanaja shima yanaja.

"shiko zunnurai sai faman rabka ihu yakeyi.

"duk da tokari hade da nushin da Mahfus kekaiwa amatullah besa ta saki zunnurai ba.

"saida ta kwace shi daga hannu Mahfus snn ta nunfasa.

"gama Mahfus abinda yasa ya saki zunnurai sbd irin kuka da yakeyi ne.

"bankade Mahfus tai xata shiga ciki, gani haka yasa Mahfus yai babakere a bakin kofa ya hanata shiga.

"duk inda tasakai sai Mahfus ya tare, yana cewa ina xaki?

"amatullah tace ciki xan shige.

"Mahfus yace tunda ba ubanki ne ya ginamin ba saikiyi hakuri kibarmin gida na ko.

"amatullah tace eh naji ba ubana ya gina makaba amma da kudin ubana kagina gida..

"kafin ta karisa Mahfus ya wanka mata mari a baki.

"a take bakinta a fashe, gani haka yasata ije zunnurai a gefe shakeshi tai hade da kamo gashin gemusa ta nannade tanaja.

"xafin da yaji yasashi kwashe mata kafa tafadi kasa gwiwarsa yasa ya d'anne ta yakama xuba mata nushi, amatullah na ihu amma besa ta sakeshi ba.

"duk abinda sukeyi fadi na kallansu ta window,ji take kamar ta xuba ruwa a kasa tasha sbd murna.

"gani irin dukan da Mahfus kewa amatullah yasa zunnurai yakama dukan bbnshi a baya yana kuka.

"gaba daya idanu amatullah yaci da jini sbd nushi da yake yimata kuma besa ya daina dukan ta ba.

"sbd shakan da amatullah tai masa dakar Mahfus ke numfashi.

"jin ihu yaki karewa yasa bb maigadi xuwa gani irin barnar da sukeyi yasashi banbaro Mahfus daga jikin amatullah.

"da kar Mahfus ya daga dagakan amatullah bb yarikeshi hade da yimasa fada.

"amatullah na mikewa juye juye takeyi can gefe ta hango wani katako a duje taje ta dauko batare da Mahfus ya ankara ba ta kwada masa akai.

"a take kan Mahfus ya fashe sai jini, gani haka yasa Mahfus sake rarumar amatullah yana niman shakota.

,"itama amatullah tana gani haka sake daga katakon tai xata sake buga masa, da sauri bb yashiga tsakani hade da rike katakon.

"jini ne jaci karfin Mahfus gani jira na niman daukarsa yasashi dukawa yana tallafe da kansa.

"gani haka yasa amatullah daukar d'anta a guje tashige ciki jakarta ta dauko hade da kudinta goya zunnurai tai snn ta dauki kyaleta.

"ko kalmi bata tsaya sawaba haka tabar gidan.

"shima Mahfus fadi yai sbd idanshi yarufe.

"a guje fadi tafito tana fadin muguwa da kashemi miji na shiga uku.

"bba maigadi yace ashe dama kina ciki, cewa yai tasa hannu su daukeshi akaishi ciki.

"fadi tace aa asibiti xata kaishi.

"a mota suka sashi da kanta ta tuka duk da batagama kwarewa neba.

"wani chemis takaishi akai masa treatment snn suka dawo gida.

"amatullah tana fita tarasa ina xata dosa, wani zuciya yace kije gidan su mmn junior.

"wani zuciya yace kada kije koda kinje idan har inna taji yadda kukai da Mahfus korenki xatai.

"wani zuciya yace kije gidan su nasir idan kika kwana da safe saiki kama kanki.

"hakan yasa tanufi gidan su nasir.

"ko kafin ta'isa goma yayi sun riga sun kwanta.

"tana isa taga gida a rufe ji tai kamar takoma gani gidan rufe, har tajuya sai wani zuciya yace idan kika koma ina xaki.

"shiru tai tana hawaye can dai gani kuka ba xai finsheta ba, karisawa tai tafara knocking takai ten minutes tana knocking snn gateman yatashi yafito a bakin kofa ya tsaya hade da tambayar waye?

"amatullah tace nine.

"yana kecewa?

"amatullah tace dan Allah kabude.

"yace nabude kamar yya?

"amatullah tace idan kabude xai maka bayani.

"sai yace aa basai na bude ba, kiyi bayaniki ina jinki.

"amatullah tace dan Allah ka taimakeni ka bude.

"yace waike waye kike nima?

"amatullah tace nasir nake nima, nice amatullah matan abokinsa Mahfus.

"shiru yai snn yace to bari na duba miki shi allah yasa be kwanta ba.

"koda yaje sun riga sun kwanta.

"dawowa yai ya sanar da'ita.

"amatullah najin haka wani irin kuka tasa.

"jin irin kuka da takeyi yasashi bude mata gate tashigo.

"gani jikinta duk jini yasashi cewa lpy?

"hatsari kikayi?

"amatullah bata tanka ba ci gaba da kuka tai.

"kukan da amatullah keyi yakai kunni nasir, tashi yai daga bcc yafito hade da bude kofar parlour yana tambaya malam audu kai da wayene?

"da sauri malam audu ya kariso yana cewa ranka ya dade wlh wata matane taxo cikin datenga wai gunka taxo.

"mmki ya kama nasir yace wata mata kuma?

"muje na ganta.

"suna karisawa yaga amatullah ne, da sauri ya ce amatullah lpy hatsari kukeyi?

"ina Mahfus din?





H.S.Z.ceπŸ–Š
πŸŒΊπŸ’¦πŸŒΊ
πŸ’¦

MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)πŸ’¦

Fasaha online writes f.o.w

MMN USWAN
H.S.Z.

30

"amsar zunnurai nasir yai suka shiga cikin gida.

"a parlour suka tsaya nasir yaje ya tado hajiya daga bcc.

"tare suka fito tare.

"gani amatullah da tai jini duk jini ga fuska ya canxa yas hajiya salati hade da cewa hatsari kukeyi?

"ina Mahfus din?

"nasir yace wlh hajiya nima tambayar da nake mata kenan.

"kuka ne amatullah tasa snn tafara xaiyana masu duk abinda da yafaru.

"salati hajiya tasa tana cewa a gaskiya idan Mahfus be kyauta ba.

"ni bansan Mahfus da haka ba yaro mai kirki da natsawa amma ace yai haka.

"himm kawai nasir yace.

"hajiya tace tashi kije ki kwanta.

"bayan dawowar su Mahfus asibiti fadi ta kira inna ta sanar da'ita, salati inna tasa tana fadin na shiga uku shikenan ta kasheminshi ta huta.

""jin ihu tane yasa mmn junior da bbn Junior fitowa da sauri suna tambayar lpy?

"inna tace shegiyar ta kashemin shi.

"bbn junior yace shiwa?

"inna tace Mahfus.

"ta karisa mgnr ne hade da daukar kyaleta tafita.

"suna binta sukai da sauri, mmn junior komawa daki tai ta dauko hijab snn tabisu.

"Bakin titi sukaje suka samu napap.

"Kai tsaye gidan su Mahfus suka nufa.

"lokacin Mahfus yana daki kwance kanshi ya aune halintanshi ya canxa fadi na zaune kusa dashi tana masa fifita.

"Kamar daga sama tajiyo sallamar su inna da sauri ta mike taje tai masu iso har cikin bedroom ta kaisu.

"suna gani yadda Mahfus ya canxa duk salati sukasa inna ta fashe da kuka tana fadin garin yya?

"fadi tace kumuje waje.

"parlour suka koma nan ta kwashe karya da gaskiya banlema karyan yafi yawa ta fadi masu.

"harda cewa wlh inna kullin aikinta kenan tace saitaga bayansa

Please Login or Register in order to submit comment