Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na fitowa Anty Frd tajuyo taiwa zunnurai.

"tana gamawa tai tasa kwalliya cikin kayan da hajiya ta siye masu aka cire daya daga ciki akasawa zunnurai.

"gani yanda yai kyau yasa Anty Frd tai ta daukarsa pict wai xata nunawa motarsa.

"murmushi kawai amatullah tai sbd ba karimin dadi tajiba gani yadda yyarta keyiwa zunnurai.

"hutuna tai masa kala2 snn ta shinfidashi.

"koda ta shinfidashi idonu kawai ta xuba masa ji takeyi kamar ta daukeshi ta tafi dashi.

"mikewa tai tashiga wanka suna gamawa suka karya hade da shiryawa.

"amatullah na gani sun dauki jaka tasa kuka,

"dariya kawai Anty Frd tai tace to menene abinda kuka kuma amatullah dan kungama wanka ba sai kuxoba.

"hawaye ne kawai ke xubowa amatullah, karasu tai har inda Anty tai parking din motar ta, matar yya khamis tafara shiga mota ita kuma Anty Frd tana rungume da zunnurai a kafadarta.

"da xata shiga mota mikawa amatullah tai yaro hade da rungumeta tana cewa dan Allah ku kulamin da yarona da kyau kinjiko.

"kai kawai amatullah ta daga tana share hawaye.

"shiga mota Anty tai, ta tada mota suna dagawa amatullah hannu har suka fita gani sunfice amatullah ta fashe da kuka.

"kan gado tahau taci gaba da kukanta ga zunnurai a hannu yana bcc. itama bcc ne ya kamata tana shinfidashi yasa kuka.

"haka ta daukeshi tana bashi nono kenan Mahfus yashigo, da sauri tacirewa zunnurai nono datake bashi taja riga tarufe nononta.

"Shikuma zunnurai yasa kuka.

"hannu Mahfus yasa ya amshi zunnurai yana lailashinsa.

"itama amatullah bata daina hawaye ba,Mahfus yace amatullah lpy meya sameki?

"shiru tai taci gaba da hawaye.

"juyawar da xaiyi yaga babu jakar su Anty, da sauri yace sun Anty suntafi ne?

"kai kawai ta daga mata.

"murmushi Mahfus yai sbd yasan tana kukan tafiyan yar'uwa tane.

"xama yai kusa da'ita yace dan Allah ki taimakeni kibashi nono idan yai shiru nima sainaji dadin lailashinki ko?

"amma ke kuka shi kuka ta'ina xanfara, a taimakeni dan Allah.

"Mahfus ya karisa mgn hade da shinfida zunnurai a ciyar amatullah snn yasa hannu yaciro mata nono yasawa zunnurai a baki.

"hannu amatullah tasa ta rikeshi da kyau.

"zunnurai yana sha ko 5 minutes bekai ba bcc ya daukeshi yana bcc ta shinfidashi. Mahfus yace yauwa ko kefa kinga yanxu sai naji dadin lailashin baby ko?

"murmushi tai masa.

"Mahfus yace to xonaji matata ta kaina kintashi lpy?

"au mantuwa nai.

"amatullah tace name fa?

"Mahfus yace kinsan yanxu muxama mu uku.

"Murmushi sa tai hade da hararrasa.

"Jawota yai jikinsa yana shafeta hade da cewa da wani lokacin ne su Anty su tafi?

"amatullah tace suna fita kashigo.

"Mahfus yace Allah ya saukesu lpy.

"tace amin, snn tace meyasa jiya baka kwana a gida ba.

"cewa yai nabaku gu ne sbd nasan xakuyi hiranku na yar'uwa kaga nazo na takura maku.

"amatullah tace haka ne.

"Mahfus yafadi hakane kawai amma a xuciyarsa ba haka bane, yaki dawowa ne sbd kada yasakejin abinda ransa xaisake baci.

"mikewa amatullah tai taje ta dauko handbag din taciro kudin da Anty tabata tabawa Mahfus.

"da sauri Mahfus yace amatullah ina kika samu kudi haka?

"gyara xama tai ta lissafa masa wanda suka bata kudin hade da xinaren da hajiya ta siye mata da kayan da aka kawo masu, harda wanda akace ta boye duk saida ta nuna masa.

"juya kayan yai ya kare masu kallon snn yace Allah ya amfana.

"amatullah tace amin.

"shaddodi guda uku wanda ba'a dikaba tabawa Mahfus da 20000 tace yakai diki.

"murmushi sosae yai hade da samata albarka.

"atanfa guda biyu kuma tace yabawa inna ta dinka itama tabata dubu biyar na dinki.

"Mahfus sai murna sbd murna daukar amatullah yai yana juyi da'ita a tsakar daki.

"ragowar kayan kuma medasu tai cikin akwati ta rufe Mahfus ne ya dora mata akan wadrop.

"kudin kuma da xinare na aurenta dana suna tabawa Mahfus tace gobe yarakata banking taje ta'ije.

"Mahfus yace Allah ya kaimu.

"su Anty Frd saida suka fara sauka a gidan su hajiya snn daga baya Anty Frd itanufi gidan ta.

"duk suna xauna a parlour Anty Frd take nunawa hajiya pitc din zunnurai.

"hajiya tace ikon Allah kenan ji yaro kama da bbnshi.

"da sauri yaxed ya amshi wayar yana gani hoton yace gaskiya hajiya yaron yana kyau.

"shima yya khamis amsa yai ya kalla yace ai wnn fuska Mahfus.

"hajiya tace wlh kuwa gashi kamar yai kaki.

"mikewa abba yai yabar gun.

"dukkansu dariya sukai sukaiwa abba.

"yya khamis ya dauki motarsa suka woce gida.

"da safe bayan sunyi wanka su karya suka shirya ita da Mahfus kaya sosae amatullah ta diba zasu kai kala goma tasa a jaka snn suka fita, ganita da jaka yasa Mahfus tambayar abibda yake ciki.

"amatullah tace kayane.

" Mahfus yace me xatai dasu?

"amatullah tace kyau xatai dasu sbd sun kide.

"daga snn besake tambaya ba.

"kai tsaye banking suka nufa Mahfus na rike da zunnurai yana jiranta a mota, cikin sa'a babu layi da yawa shiyasa bata dade ba tafito.

"tana fita tashiga mota Mahfus yajasu gidan su inna suka nufa kai tsaye.

"suna isa Mahfus ya dauki yaro ita kuma ta dauki jakar kayan suka shiga lokacin inna tana daki hakan yabawa amatullah damar jefa jakar a dakin Mmn junior snn suka karisa dakin inna.

"inna da murnarta ta taresu Mahfus ya mika mata yaro har kasa amatullah ta duka ta gaida inna.

"da sauri inna tace ta tashi akasa ta hau gado sbd jege.

"saida suka taba hira snn Mahfus ya dauki kaya da kudi yabawa inna yace iji amatullah.

"murna sosae inna tai hade da sa albarka.

"suna cikin haka Mmn junior tashigo da sauri amatullah ta kashe mata ido hade da mikewa suka tafi dakinta.

"suna shiga cikin rawar jiki mmn junior tace naga kaya nawaye?

"murmushi amatullah tai tace kena bawa.

"Mmn junior sai murna baki yakasa rufuwa sbd murna.

"hira sukai sosae da mmn junior, Mahfus ne yaleko yace taxo sukafi gida.

"bayan tafiyarsu Mmn junior ta raba kayanda gida uku tanunawa inna kaso daya afili inna tanuna bakin cikinta ko kallon kayan batai ba, banle tace kala.

" itama dayake tasan halinta abinda inna tai bedameta ba.

"komawa tai da kayanta daki.

"kwanci tashi babu wiya su amatullah har sunyi arba'in.

"tun bayan sallar isha zunnurai yake kuka amatullah tai lailaishi har tagaji Mahfus ma haka.

"da suka bashi maguguna har yafara bcc kamar wanda aka mitsila cikin dare yasake tashi yaci gaba da kuka, da amatullah taga haka itama kuka tasa Mahfus yarasa yadda xaiyi gashi shabiyun dare ne.

"bashi da yadda xaiyi haka ya daukarsu suka nufi gidan inna cikin dare suna isa Mahfus yakama buga gida a tsorace yya Mahfus yaje xaure yana tambaya waye?

"Mahfus yace nine yya.

"snn yabude suka shiga.

"gani yadda amatullah da yaro suke kuka yasa yyan Mahfus tambayar lpy?

"mmn junior ne taxo da sauri ta amshi yaron.

"kowa yai iya kokarin sa amma zunnurai yaki shiru.

"inna ta amshi zunnurai ta goya Mahfus yai lailashin amatullah har yagaji.

"yyan Mahfus yai masa addu'a acikin ruwa alabawa zunnurai yasha ragowa kuma aka shafe masa idan yai kamar yai bcc sai kuma yatashi yaci gaba da kuka.

"tun daga lokacin inna tace a kyaleshi idan kaga yaro yakatse kuka haka cikin biyu xa'ai daya ko xa'ai mutuwa ko kuma wani mumunar abu xaifaru.

"inna tace koma menene Allah yakawo da sauki.

"duk sukace amin.

"haka suka kwana a zaune babu wanda ya rumtsa zunnurai yana kafar inna kuka kawai yakeyi babu sasauci.

"karfe shidda safe Mmn junior tai mata wanka Mahfus ya dauki d'abshi xuwa asibiti.

"koda sukaje maguguna kawai aka basu su vitamin C hade da na bcc suka koma gida.

"suna dawowa a parlour suka tsaya Mahfus ne ke xubawa amatullah a spoon ita kuma tana bashi.

"yanasha sai bcc suma anan suka kwanta suka sashi a tsakiyarsu.

"hann Mahfus daya yana rike da hannu zunnurai itama amatullah haka.

"shiru2 da su inna sukaji yasasu biyosu gida, suna shiga suka samesu kwance suka rirrike d'ansu suna bcc.

"murmushi kawai inna tai hade da cewa gani shikadai ne yakawo masu haka.

"Mahfus ne yafara falkawa gani su inna yasashi tada amatullah.

"su inna sukace ya maijikin?

"sukace da sauki.

"ganishi yana bcc inna tace aa yasamu sauki tunda gashi har yana bcc, Allah yakara lpy.

"Mahfus yace amin.

"inna tace sutafi gida dama mejiki sukaxo gani tunda yasamu lpy,Allah yakara lpy.

"komawa gida sukai.

"washe gari da safe Mahfus yana xuwa aiki yaga laptop koda yai tambaya akace koran ma'aikata akayi kuma hardashi a ciki.

"jikin Mahfus yai sanyi, a lokacin ne yatuno da mgnr inna.




H.S.Z.ceπŸ–Š
πŸŒΊπŸ’¦πŸŒΊ
πŸ’¦

MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)πŸ’¦

Fasaha online writes F.o.w.

MMN USWAN
H.S.Z.

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’Masoyana abin alfaharina ina alfahari daku a duk inda kuke.Comm dinku ke karamin karfin gwiwa. Home of novel gaskiya ni yar'gata ce nagode nagode sosae da kaunarku a gareni, da kuma bibiyar novel dinna da kukeyi Allah yabar kaunaπŸ€πŸ’

Hafsat Hausa novel (H2) Facebook, Banmance da kuba nagode da nunamin kauna da kukeyi da kuma bibiyar novel dinna a duk inda nai posting kuna tare dani, thank you so much all my fansπŸ€πŸ’

🍬🍬🍬🍬🍬
Sis mardiya ka'oje (Mmn Ahmed) ban mance dake ba ina alfahari dake a duk inda kike nagode da nunamin kauna da kikeyi Allah yabar kauna da zumunci. Allah shiryar damu ya shiryar mana da xuri'a bisa tafarkin Islamic, yasa mufi karfin zukatanmu, ya kuma kare mana mazajenmu a duk inda suke. Y basu ikon nimo mana halas, ya kuma basu ikon gujewa haram amennn ya AllahπŸ‘πŸ»

Wannan page din sadaukar wane ga dukkani masoya novel din MATAR FARI
nagode Allah yabar kauna
πŸ’πŸ’πŸŒΉπŸ¬πŸ¬

20

"Mahfus na gani sun fita,a guje yai kan amatullah yana kiran sunanta.

"gani bata numfashi da sauri yashiga toilet ya dibo ruwa. kwara mata yai gaba daya jikinta.

"firgigi tai tamike a guje tai hanyar kofar hade da kwadawa Mahfus kira.

"fisgota Mahfus yai yana cewa kitsaya.

"amatullah igijeshi tai taci gaba da kwadawa Mahfus kira hade da kuka.

"Mahfus na gani haka riketa yai da karfi yana cewa amatullah kitsaya nine, nine Mahfus dinki.

"duk da haka amatullah bata dai na buga kofaba, gani haka yasa Mahfus danneta da karfi a kasa.

"amatullah naji haka wani irin ihu tasa hade da fashewa da kuka tana kiran nashiga uku xasu kashemi Mahfus din na..

"Mahfus najin haka rungume amatullah tai yai da karfi yana fadin nine Mahfus dinki babu wanda zai kashe miki Mahfus dinki.

"amatullah najin haka da sauri ta daga fuska tana kallon Mahfus da taga shidin nedai da sauri ta rungumeshi hade da tallafo fuskanshi tana masa kiss.

"jin zunnurai na kuka da sauri amatullah takoma kan da'nta ta rungume taci gaba da kuka.

"biyota Mahfus yai kan gadon yace dan Allah kidaina kuka haka is ok.

"gani taci gaba da kuka yasa Mahfus yace kodai ya tabaki ne?

"da sauri amatullah tace aa.

"Mahfus yace aa amatullah ban yarda ba.

"sa hannu yai ya ware mata kofa yana lekawa,da yaga be hango komai ba kwantar da'ita yai ya ware kafar da kyau hade da sa hannu yana shafo gaban ta.

"da yaji babu komai gaban ma a bushe yake wani irin ajiyar zuciya Mahfus yai hade da cewa alhamdllh.

"snn Mahfus yakoma kan kofa yai iya yinshi amma ina,sun riga surufe su da key.

"Mahfus yanimi abinda zai fasa kofar besamu ba.

"komawa window yai yagani ko zai samu hanya amma ina.

"suna fita da mota, mota ta tsaya sunyi iya yinsu mota taki tashi.

"daya daga cikinsu yace oga mubarshi mu tafi kawai kaga safiya ya kusanyi kada axo a kamamu.

"waje kokarin fita daga motar wayar Mahfus tafadi a cikin mota sukuma suna kokarin gudu basu luraba.

"haka suka tafi sukabar motar a bude.

"Mahfus da yaga besamu abinda xai fasa kofar dashi ba, karfe da amatullah ta kwadawa barawo ne Mahfus ya dauka kafa yasa da karfi yake juya karfe garin kokarin karya karfe yaji ciwo.

"jini sosae yake xuba amma besa Mahfus yabari ba, yana karyawa yaje yasa a gun key da karfi yasa ya juya kofar da bude.

"yana budewa fita yai kuwa parlour amatullah tana fadin ina xaka Mahfus?

"ina xuwa kawai yace.

"gani haka da sauri amatullah ta goya zunnurai hade da daukar masa jallabiyarsa ita hijab ta dauka snn tabishi parlour.

"har yasa kafa xai fita da sauri amatullah ta rike masa hannu tana cewa dan Allah karka fita.

"Mahfus yace babu komai kikoma ciki kawai.

"kuka amatullah tasa tana fadin saidai mutafi tare, Mahfus betsaya ya saurari abibda xata ceba fita yai itama amatullah da sauri tabishi kafa babu takalmi tana rike da rigansa a hannu.

"gani gate a wangale yasa Mahfus karisawa bakin gate din da sauri.

"can ya hango mota da sauri yabi motar, itama amatullah a guje tabishi.

"yana isa gun yaga mota a bude key na makale a kan sitiyari da sauri ya kunna light yana dube2 wayarsa ya hango can gefe dagawa yai yabawa amatullah itako amatullah sai faman cewa take dan Allah Mahfus kaxo matafi kada sudawo.

"Mahfus yace karki damu shigo mukoma gida.

"tana shiga Mahfus ya meda mota gida hade da rufe gate da kofar parlour.

"ruwa amatullah ta dibo ta wanke masa hannu snn tasamu kyale fari tass ta daure masa.

"a parlour suka xauna dan babu mgnr bcc kuma Mahfus na fadin yar'iska kawai, amatullah kwantar da zunnurai tai akan three ster snn tadawo gun Mahfus ta kwanta a jikinshi, shima Mahfus rungumeta yai a jikinshi.

"ba'a dade aka kira sallar asuba saida sukai sallah snn Mahfus yakira yyanshi ya sanar masa, salati yai yasanarwa ubangiji sa.

"a take yasanarwa inna da motarshi.

"suna gama mgn da yyanshi yakira nasir ya sanar dashi.

"shima salati yai ba'a dauki lokacin ba sukaji knocking da sauri Mahfus yacewa amatullah taje tacire rigar bcc tasa wani da babban hijab.

"saida yaga tashige snn Mahfus yaje ya bude kofa, nasir ne yagani.

"nasir na gani hannu Mahfus daure da duk jini ya bata tsuman salati yai hade da cewa fito mutafi asibiti.

"murmushi kawai Mahfus.

"saida suna xauna nasir yake tambayar garin yya barayi suka shigo.

"Mahfus yace wlh nasir muma bcc mukeyi sai mukaji motsin anshigo ashe barayi ne.

"shigowar amatullah parlour ne yahana nasir mgn, tana tana xama su inna da yyan Mahfus da mmn junior sukai sallama.

" su amatullah suka taresu da sannu da xuwa.

"sukace yauwa ya akaji da farga ba.

"sukace alhamdllh.

"har kasa amatullah ta duka ta gaida bbn junior su inna kuma tace suxo sushiga ciki.

"mmn junior ta dauki zunnurai suka shiga cikin bedroom bayan su gaisa ne amatullah take basu labarin abinda ya faru, tanayi tana kuka.

"inna da mmn junior sukai ta bata mgn har ta numfasa, zunnurai yatashi yana kuka mikawa amatullah sukai tabashi nono koda yasha be daina kuka sai mmn junior tace kodai wanka yake butaka?

"amatullah tace eh dama beyi wanka ba.

"amsarshi tai suka shiga toilet tai masa wanka tafito ta shiryashi tsaf snn sukace zasu tafi.

"tana rike da zunnurai suka fita parlour snn tamikawa bbn junior saida ya dinyi wasa dashi snn suka mike.

"nasir ne ya amshi zunnurai yana masa wasa sai faman wangale baki yakeyi yana dariya, kamar Mahfus ne ke dariya.

"nasir be bar gidan ba saida aka fara kiran sallar axahar snn suka fita tare xuwa masallaci bayan su idar da sallah ne suka nufi chamis akaiwa Mahfus treatment din hannunsa nasir yabiya sbd Mahfus bashi da ko sisi ajikinshi suna fita nasir gida yanufa Mahfus ma haka.

"koda Mahfus yashigo gida gani amatullah yai ta'idar da sallah tana zaune kan sallaya tana faman kuka.

da sauri Mahfus ya karisa gunta yana lailashinta share tai tace ina wayarka?

"mika mata yai.

"tana amsa tasa number hajiya takira.

"hajiya ta gani number Mahfus kamar bazata daga ba saidai ta daga muryar amatullah taji cikin kuka take gaidata.

"gaisawar da hajiya bata amsaba kenan sai faman cewa take amatullah lpy meke faruwa?

"cikin kuka take sanarwa hajiya abinda ya faru.

"da sauri hajiya tace sun tabaki ne?

"amatullah tace aa.

"hajiya tace alhamdllh yaron fa?

"hajiya tace to bawa mijin naji idan yana kusa.

"mikawa Mahfus wayar tai bayan sun gaisa hajiya tai masa Allah ya kyauta.

"suna cikin gaisawa abba yashigo hajiya ke sanar dashi abinda yasami su amatullah.

"cikin rawar jiki abba yace amma dai basu tabata ba?

"hajiya tace aa.

"da sauri abba yace bari na kirata naji yadda take, wayarsa yaciro daga aljihunsa yana niman number ta.

"hajiya tace aitace sutafi mata da waya, saidai na mijinta.

"amsar wayar hajiya abba yai yakira duk a lokacin wayar tana hannu amatullah,amatullah najin muyar abba tasake fashewa da kuka.

"abba yace dan Allah amatullah kidaina kuka tunda Allah yasa basu tabaki bama ai muyin barka in Allah ya kaimu goya xanturo hajiya ta dubaki.

"amatullah ji tai kamar ba abba yake mgn ba.

"abba yaci gaba da cewa nima dan banijin dadin jikina ne da tare xanuxo, jibi ma xantafi Cairo naga doctor din na.

"cikin kuka amatullah tace abba Allah ya kara lpy, yasa kaje lpy kadawo lpy.

"abba yace amin nagode.

"snn sukai sallama.

"suna sallama amatullah tafadiwa Mahfus cewa hajiya na xuwa gobe.

"Mahfus yace to yanxu me yakamata a shirya masu gashi banida kudi.

"amatullah tace babu damuwa, yanxu tashi xakai mutafi kasuwa.

"tashi sukai Mahfus yashiga wanka yana fitowa itama tashiga amatullah ne ta taimaka masa wanjan sa wando sbd ciwon dake hannunsa.

"itama bakar jallabiya tasa hade da mayafinsa suka fita cikin ikon Allah tanasa key mota yatashi Mahfus yana rike da zunnurai ita kuma tana draving.

saida sukaje A.TM.tacire kudi snn suka karisa kasuwa, siyayya sukai sosae snn suka dawo gida.

"suna shigowa sukaga su suwaiba sunxo suna tsaye a bakin gate.

"amatullah tana parking da sauri taje ta rungumosu hade da cewa kuxo mushiga ciki.

"wani irin kallon Zainab taiwa amatullah, duk da tagani amma bata nuna damuwa ba.

"ita ko Fatima amsar zunnurai tai a hannu yyanta.

"amatullah na cewa au ni bazaki amsheni ba sai yyanki?

"duk dariya sukai.

"gani kaya yai mata yawa yasa Mahfus rage mata kayan.

"suwaiba da sauri ta amshi yynta.

"suna shiga kitchen amatullah tashiga da kayan Mahfus ya amshi na hannu suwaiba yabita dashi saida sukasa kayan a frg snn ta dauko ruwa suka dawo parlour dukkansu hada baki sukai suka gaida Mahfus hade da yimasu Allah ya kiyaye na gaba.

"Mahfus yace amin nagode.

"snn suka gaida amatullah amma banda Zainab.

"Mahfus yace kefa ko kinfi karfin ki gaida tane?

"Zainab tace yya to bana gaida kaba....

"da sauri yakatar da'ita hade da cewa karki kawomin iskanci banxa a nan idan har bazaki gaida taba kintashi ki barmi gida na.

"murmushi kawai amatullah tai snn tacewa Mahfus dan Allah karabu da'ita waya cemaka ana shiga tsakanin mata da miji.

"duk dariya sukasa, gaisuwar da Zainab batai ba kenan.

"da haka sukai sallama suka wuce, suna fita tashiga kitchen Mahfus yana rike da zunnurai.

"zunnurai kokarin rike hannu bbnshi yakeyi, da amatullah taga haka karbanshi tai tagoya snn taci gaba da aiki.

"washe gari hajiya na idar da sallah asuba suka dauki hanya ita da yazed, yazed ne ketuki.

"sbd gudun da yakeyi shadaya suna cikin kano, kiran Mahfus sukai suka sanar dashi inda suke.

"yana jin haka shida amatullah suka fita tarosu sbd batasan hanya sosae ba Mahfus ne kenuna mata hanya har suka tarosu snn sukai masu jagora xuwa gida.

"suna parking amatullah a guje taje ta rungume hajiya da yazed yazed ya amshi zunnurai suka shiga ciki.

"suna shiga bayan sun xauna amatullah ta kawo masu ruwa da lemu sukasha snn Mahfus yaka ya gaida hajiya, hajiya ta amsa hade da yimasa Allah ya kyau.

"Mahfus yace amin nagode.

"amatullah taja hajiya xuwa daki snn ta kaimata abinci tana ijewa takai masu yazed nasu parlour.

"amatullah na fita hajiya ta karewa dakin kallon tana mmkin yanxu aciki nan yar'ta ke rayuwa.

"zunnurai yana hannunt sai faman fesheta da yawu yakeyi yana hura hakori.

"amatullah na dawowa taxubawa hajiya tana, hajiya naci suna hira, hajiya tace abbanki yace a gaida mishi ke har yabada sako nabaki.

"cikin doki da jin dadi amatullah tace da gaske hajiya.

"jaka hajiya ta jawo taciro sabuwar waya hade da note din one one thousand tabawa amatullah.

"amatullah sai murna.

" hira sukai sosae, kiran sallah ne ya katsa su tashi sukai sukayi sallah suna idarwa sukayi sallama.

"amatullah da Mahfus saida suka fitar dasu hanya snn suka dawo gida bayan su dawone amatullah take nunawa Mahfus wayar da abba ya siye mata hade da kudin daya aiki mata dashi.

"murna sosae Mahfus yai a take suka kira abba sukai masa godiya.

"amatullah raba kudin biyu tai tabawa Mahfus dubu hamsi itama tarike hamsi.

"Mahfus godiya yai sosae.

"bayan tafiyar abba Cairo jikin yaki hakan yasa suka hannashi dawowa sukaci gaba da bashi kulawa.

"satin da xai kewayo hajiya na shirin tafiya dubashi yya khamis yace ta dakata tunku dama tare sukaje da yya khamis.

"cikin dare abba yace ga garinku.

"Allah yai masa rasuwa.

"cikin daren aka sanarwa gida, kafin safe gida yacika da jama'a sai faman koke koke akeyi.

"da safe misalin karfe tara amatullah suna parlour xauna da zunnurai a hannu taga kiran Anty Frd da sauri tadaga jin murya cikin kuka yasata cewa Anty ply?

"cikin kuka Anty Frd tace abba yarasu.

"amatullah ihu tasa batasan lokacin da tai hurgi da yaroba.

"Mahfus yana daki jin kukansu ita da yaro yasashi fitowa da gudu.





H.S.Z.ceπŸ–Š
πŸŒΊπŸ’¦πŸŒΊ
πŸ’¦

MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)πŸ’¦

Fasaha online writts F.o.w.

MMN USWAN
H.S.Z.

22

"gani yanda Mahfus yakeyi yasa amatullah dariya.

"biyeshi tai sukai ta wasa bayan su gama abinda da xuyi ne Mahfus yacewa amatullah ta shirya su tafi kasuwan tare tunda shi ba sani kanshi yai ba.

"kada axo cuceshi, sbd yawanci yar' kasuwannan ba tsoron Allah ne dasu ba.

"amma idan akaje da wanda yasan kai koda xasuyi cutan xaixama da sauki.

"amatullah tace hakane.

"shiryawa sukai suka tafi kasuwan tare.

"cikin ikon Allah sunsamu yanda basuyi tsanmani ba.

"sbd a lokacin dala ya tashi.

"shiyasa shima darajan zinare ya karu.

"cash aka basu kudinsu daga bank suka tafi direct amsar kudin Mahfus yai yasa acikin account dinshi.

"na wajan amatullah shima transfer sukai xuwa cikin account din Mahfus, saida suka hada kudin gun daya snn suka dawo gida.

"da yamma bayan su alhji Ibrahim su gama cin abinci shida iyalansa, suna zaune da hajiya shine yake sanar mata yanda sukai da amatullah.

"hajiya tai salati ta sanarwa ubangiji tana mmkin amatullah.

"hajiya tace yanxu kabata kudi ne?

"alhji yace nabata amma ba dukka ba.

"million two nabata shidima sbd kukan da tasane.

"hajiya tace wlh alhji inda ka shawarceni kafin kabayar da baka bataba, yanxu da haka wannan shrgen mijinta din nanne xaisata.

"sbd yaga ubanta ya mutu kuma yasan yabar dukiya shine xai mata wayo yagama cinye mata kudin.

"to wlh daga yau ba kukaba ko kukan jini xatayi sisi baxa'a bata ba.

"alhji yace nima shawara da nayanke kenan.

"da dare Mahfus yana gama cin abinci yatafi gida su nasir, yana isa yatsaya a kofar gida ya kiranshi ta waya nanda nan nasir yafito saida suka gaisa hade da cewa ya karin hakuri?

"Mahfus yace alhdumll.

"Mahfus yace nasir gun ka naxo.

"nasir yace allah yasa dai lpy.

"Mahfus yace klau wlh, dama wasu kudi nasamu nakeso nafara business shiyasa nazo gunka sbd kai ne kasan sirrin kasuwanci.

"nasir yace hakane amma Mahfus kasan business yanxu saida isanshen kudi.

"Mahfus yace hakane nasir.

"nasir yace kamar nawa kake dashi?

"Mahfus yace xasukai million biyar yar'kai.

"cikin mmki nasir ya bude ido😳
hade da cewa Mahfus ina kasamu irin wannan kudin haka?

"Mahfus yace wlh nasir amatullah ne tabani tace naja jari dashi.

"da sauri nasir yace aa wlh Mahfus banyarda ba,haka kawai bazata dauki kudi tabaka ba.

"a nan ne Mahfus ya warwarewa nasir komai babu abinda ya boye masa.

"nasir yace gaskiya Mahfus baka kyau taba, saidai idan kuyishi da yarjejeniyar gaba daya business din nata ne kai kai kuma katsaya a matsayin manager.

"amma inba haka kai ba xaixama akwai cutarwa aciki.

"san kaine ka tursasata ta amso kudin nan, duk da haka be maka ba ka kuma sata ta saida xinarenta.

"idan da gaskiya Mahfus yau koda amatullah taso saida wata kaddararta kai mai hanawa ne, amma ace da kanka kabata shawarar haka dan kaga burinka ya ciki.

"idan harda gaske kakeyi mai xaihana baxaka fitar da takardunka kaje ka nimin aiki ba.

"na babbata idan baka samu na kwamnati ba xaka samu na campany.

"Mahfus yace haka amma wlh nasir duk yadda kake tunani ba haka bane.

"kuma idan ma wani abu kake in Allah ya yarda xanyi iya kokarin naga nakiyaye.

"hmmm kawai nasir yace snn yaci gaba da cewa idan hakane Mahfus meyasa kamaida amatullah family house dinku?

"kayi hakuri bana raina ma arxikinku bane.

"murmushi Mahfus yai snn yace ba haka bane nasir a lokacin gaskiya banida kudin da xanbiya hayane shiyasa nace mukoma gida.

"amma ko a lokacin amatullah tace xata biya nine na hanata, sbd ba hskkinta bane biyan haya.

"shiyasa nace aa idan tabiya na wannan shekara waye xaibiya na wani?

"shiyasa nace mukoma gidan mu kawai har allah ya horemin nawa.

"murmushi nasir yai hade da cewa amma kasan ka tauyeta ko?

"kaduba irin gidan da tataso Mahfus banaso kayi dubi da soyayyar da amatullah take maka yasa kayi anfani da wannan damar kayi abinda kakeso.

"wlh Allah ba xaibarka ba.

"shiru Mahfus yai besake mgn ba.

"gani yanda jikin Mahfus yai sanyi yasa nasir cewa kai a naka ra'ayin wace irin business kake sha'awa?

"a sanyaye Mahfus yace ai sha'awa xamu biba nafison nayi business din da yafi shaga wanda koda kasiye ba xata dauki lokaci bata kare.

"nasir yace haka ne, yanxu dai business din kayan masarufi yafi

Please Login or Register in order to submit comment