Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yauma hakane tunda ta tashi daga bcc take nimansa da masifa amma Mahfus be kulata ba.

"da yace na hada masa tea har nahada ina fitowa kenan taxo ya bankade yaxobe haka Mahfus yafita be karyaba.

'"bayan fitarsa ne nake mata mgnr abinda tai bata kyauta ba nan ma ta hauni da xagi ban ankara ba ta dauki wuka ta yankeni.

"kinga ma gun.

"nuna masu hannu tai.

"a lokacin ne bbn Junior yai mgn yace kama mahaukaciya?

"da sauri fadi tace eh dama kullin sai tace saitaga bayanmu nida Mahfus.

"wlh da kar na kwaci kaina a gun ta.

"ta karisa mgn hade da nuna masu hannu.

"Allah ya kyauta kawai bbn Junior yace sbd kwata kwata be yarda da mgnr ta shiyasa tunda tafara mgn ya xuba mata ido.

"itama kan ta mmn junior jinta kawai tai.

"gani dare yayi sukace mudai xamu tafi.

"inna tace kutafi kawai sbd be kamata a barta ita kadai da jinya ba.

"bayan fitarsu ne fadi taci gaba da cewa wlh inna narasa abinda Mahfus yaiwa amatullah gashi yana iya kokarinsa a kanmu amma bata gani.

"Kullin cikin cin mutunci da toxarta take masa.

"idan kina gun saiya baki tausayi.

"Hatta zunnurai ma ta hanashi xuwa guna.

"idan nai mgn sai tace nabari na haifi nawa.

"karisa mgn fadi tai da kuka.

"inna tace kiyi hakuri ki daina kuka in Allah ya yarda kema xaki samu naki.

"in banda rashin kai irin na amatullah ina aka taba yiwa budurwa gorin haihuwa.

"yanxu ina take?

"fadi tace tunda ta aikata hakan tafita har yanxu bata dawo ba.

"ina tace Allah ya raka taki gona.

"mikewa fadi tai takoma daki.

"gaba daya maganin da akabawa Mahfus ta dauko rabashi biyu tai taje toilet tai puloshing din magani saura kuma ta meda ta ije.

"bbn junior suna hanyane yace mmn junior tace naam.

"yace wlh nidai banyarda da mgnr fadi ba.

"mmn junior tace sabodame?

"bbn junior yace kinfi kowa sanin yadda amatullah keso Mahfus wlh bazata iya aikata masa haka ba.

"idan ma kinga ta aikata hakan to tabbas akwai abinda ya hadasu dan ruwa baya tsami banxa.

"da haka sukai ta hira har suka isa gida.

"da safe bayan su amatullah suyi wanka sun shirya hajiya tacewa nasir yafara kaita asibiti dsga nan ya karisa da ita gida.

"komawa daki amatullah tai ta dauko jakarta da kyaleta.

"shikuma nasir ya dauki zunnurai har xasu fita sai hajiya tace su tsaya mayafinta ta dauko tace suje tare.

"saida sukaje asibiti doctor ya dubata ya bata magani snn suka karisa gidan su Mahfus.

"har ciki suka shiga nasir ne a gaba sai hajiya follow by amatullah.

"da sallama suka shiga inna da fadi da suke parlour suka taresu da murnarsu.

"nasir yafara shiga sai hajiya amatullah nasa kafa da sauri inna taxo ta igijeta waje.

"tana fadin ina xaki?

"batare da ta tanka ba sake ta kafa tai.

"inna tasake tureta waje.

"gani sufara kokuwa da inna yasa hajiya shiga tsakani.

"jin muryan hajiya ne yasa Mahfus fitowa daga daki.

"hajiya tace dan Allah Dan annabi inna kibarta tashiga.

"inna tace babu inda xata shiga tunda ba gidan ubanta bane.

"gani hajiya ne a gun yasa Mahfus cewa inna kyaleta ta shigo.

"snn inna ta barta ta shigo.

"bayan sun gaisane hajiya tai masa allah ya kyauta.

"Mahfus yace amin.

"snn hajiya ta juya gun inna tace dan Allah inna kada kisake kokuwa da amatullah wlh ba girmanki bane.

"idan kince batada kunya ne yanxu yaxama ruwan dare.

"in kuma ana biye na haka muma yar'yar'mu suna wani gida bamusan abinda suke aikatawa ba.

"dan Allah inna kada kikara amatullah amanace a gun ku batada kowa a garin nan saiku.

"dan Allah ya kiyaye.

"kai Mahfus kaine shugaba a gidan nan dan Allah banda daukar jita jitan mata.

"amatullah amanace Allah ya baka idan kaci amanarta Allah ba xai barka ba.

"Mahfus harda dukawa yace kwarai da gaske hajiya nagode.

"snn hajiya tace kuma inaso taci albarkacina ka kyaleta ta xauna a dakin ta..

"da sauri Mahfus yace amma hajiya..

"Hajiya tace banason jin komai daga gareka.

"nidai alfarma nake nima.

"kunyane yakama hajiya yace to shikenan babu damuwa.

"hajiya tace nagode.

"snn tajiya snn amatullah itama fadi tai mata sosae.

"fadi kuwa tunda Mahfus yace amatullah yashigo shine tabar gun sbd bakin ciki.

"hajiya tace to mu xamu tafi.

"duk mikewa sukai suka rakasu Mahfus ya duka har kasa yai mata godiya.

"bayan su hajiya sun tafine amatullah takoma parlour ta xauna.

"Mahfus yana shigowa yacewa amatullah tunda ba ubanki bane ya ganamin gida tashi kifita.

"amatullah tace badai ubana na wlh.

"Mahfus yace sai ubanwa?

"amatullah tace kai kasani..

"kafin ta karisa ya wanka mata mari a baki.

"kafin tace xata mike Mahfus ya shaketa.

"itama tana gani haka kamo masa gaba tai tana murdawa.

"jin zafin murdawan da takeyi yasa Mahfus xuba mata nushi.

"itama kara murdawa takeyi hade da ja.

"wiya yasa jikin Mahfus ya hau rawa hade da xufa.

"ihu sai fama ihu takeyi tana kuka.

"da Mahfus yaga tanada ninyar hallakashi, wani irin nushi ya xuba mata.

"wani irin ihu tasa batasan lokacin da tasskeshi ba, jin ta sakeshi dagawa yai yana gyara wando.

"komawa tai gun TV taja ta tsaya, Mahfus yace xokifita dan ubanki.

"amatullah tace ba ubanaba saidai ubsnka kuma babu inda xani.

"Mahfus yace good saina nuna maki kuskurenki kuwa yau dinna.

"saida ya cire jallabiyarsa snn yafara tunkarota.

"amatullah na gani haka tukuyar flowers dake gefen TV ta dauko ta halba masa tai.

"tsalle Mahfus yai da sauri.

"sake dauko wani tai tasake halba masa.

"gani haka yasa inna daukar zunnurai a guje suka shige daki.

"duk da haka Mahfus kokarin kamota yakeyi.

"speaker na woofer ta dauka tana fadin wlh idan kamatso saina buga maka.

"ok kawai yace.

"gani haka yasata kwadawa TV dake bango atake TV yafado yafashe.

"kananu kwalaben da akai dressing dashi a bango amatullah ta duga banlowa tana halbawa Mahfus.

"duk inda ya kyauce saita binshi dashi.

"kamar mahaukaciya ta koma, a guje Mahfus ya shige daki hade da rufe kofa.




H.S.ZceπŸ–Š
πŸŒΊπŸ’¦πŸŒΊ
πŸ’¦

MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)πŸ’¦

Fasaha online writes F.o.w.

MMN USWAN
H.S.Z

31

"tunda inna suka shiga daki da zunnurai sai faman ihu yakeyi xaije gun mmnshi.

"amatullah naji ihu zunnurai da sauri taje bakin kofar dakin inna tana bugawa.

"inna taki budewa kuma tanajin bugun da amatullah keyi.

"zunnurai yanajin muryan mmnshi ya kara sautin kuka.

"amatullah sai faman kiran inna takeyi ta bude amma inna taki.

"jin muryar zunnurai yafara canxawa da sauri ta shiga kitchen taje ta dauko tabarya tafara buga kofar.

"inna najin bugun bana hannu bane tasa ihu tana kiran Mahfus.

"shima Mahfus yanajin ihu inna da sauri yanufo bakin kofa.

"fadi na gani haka rikeshi tai tana fadin dan Allah karka fita taxo ta illataka.

"Mahfus yace babu damuwa kedai ki tsaya a daki kawai.

"a hankali ya bude kofar ta daga kenan yarike ta baya.

"yana cewa haba amatullah kanki daya kuwa meye kikeyi haka kamar mahaukaciya.

"amatullah tace kace mata ta fitomin da yaro.

"Mahfus yace yanxu duk akan zunnurai kike haka amatullah?

"nimafa d'anna ne inada iko dashi.

"baxan dashi amatullah tai, gani xai bata mata lokaci fisgo tabaryan tai xata cigaba da buga kofar.

"da sauri amatullah yace dan Allah ki tsaya idan akan zunnurai ne, bugawa inna kofar yai yana cewa kibude inna nine Mahfus.

"duk yana yine hannunshi a rike da tabaryan.

"Inna na budewa a guje zunnurai ya fito ya rungume mmnshi.

"daukarsa amatullah tai hade da kokarin shiga dakinta.

"da sauri Mahfus ya tare hade da cewa ina xaki?

"bata tanka masa ba sai faman kokarin shigewa takeyi.

"amatullah tace kabani hanya na shiga daki mana.

"Mahfus yace wani dakin?

"ai nariga na haramta miki wannan dakin, ke ba dakiba gaba daya cikin gidan na haramta miki.

"da sauri inna tace kaimin daidai, rubutawa shegiya takarda ta tafi ta bamu waje shegiya jini masifa duk yadda akai a nono suka sha.

"karaf amatullah tace ni inda ma xai sakeni wlh dana huta da wannan auren lalura.

"da sauri inna tace kajiko rubutawa shegiya ta karda muhuta da bala'i.

"Mahfus yace inna ki barni da'ita basai na saketa ba amma da kaina xan hukutata.

"amatullah tace kinji kenan banxa mara zuciya, wlh idan har kaga nabar gidan nan kabani takardata.

"a lokacin ne fadi dake makale tace ina xai iya bata takarda inna tunda ta shanyeshi.

"Mahfus yace fita.

"amatullah tace babu inda xani.

"Mahfus yace fita tun kafin na illataki.

"wani irin mugun kallon amatullah tai masa hade da jan tsaki, sakai tai kadan yarage ta buge inna da sauri inna takoma bayan Mahfus.

"shegewa dakin tai da sauri Mahfus yabinta yana fadin xokifita.

"xani ta dauka ta goya zunnurai snn ta kwashe xani gado duk mgnr da Mahfus keyi idan ta tanka kasa ya tanka.

"tana gama gyara gado saida ta daidaici Mahfus yana kusa da bakin kofa batare da ya ankara ba tana xuwa kusa dashi ingijeshi tai yana fita da sauri tasa key ta rufe kofa.

"Mahfus yaso ya kamata da kokuwa gani tana goye da zunnurai ne yasashi kyaleta kai kawai ya kada.

"gefe ya koma yana kallon ikon Allah inna dake zaune a kan cushion dake parlour tana gani amatullah ta tunkarota da sauri ta mike.

"jakarta ta dauka da kyaleta snn takoma daki.

"tana shiga ta rufe kofa da key snn ta sauke zunnurai saida tai masa wanka snn itama tai nata.

"tun daga lokacin kowa na gidan ya kiyayeta, itama bata shige masu.

"yaran shagon Mahfus dukkansu sukaxo gida gaidashi, lokacin amatullah tana wanka zunnurai bude kofa yai yafita har parlour.

"suna ganinshi daya daga cikinsu yace oga amma wannan yaranka neko?

"murmushi kawai Mahfus yai.

"fadi dake zaune kusa da Mahfus ji take kamar ta hadiyi zuciya ta mutu takeji.

"suko sai faman daukarsa sukeyi suna cewa oga ai wannan shine photocopy din ka.

"dariya Mahfus yai yakara kallon zunnurai da kyau.

"fadi na gani haka tsaki tai hade da mikewa tabar gun.

"da sauran xasu fita kyauta sukai tabawa zunnurai mai 500 mai 1000 haka sukai ta bashi zunnurai sai faman godiya yakeyi.

"dama haka amatullah ta koya masa koda bbnsa ne idan yabashi abu saitace saiyayi godiya hakan yasa ya saba.

"hannu zunnurai cike da kudi yadawo jikin bbnshi ya xauna.

"mutani biyu suka rage sbd cinikin da aikai a kasuwa suka kawo masa daga nan kuma xasuyi lissafi.

"da manager da assistant manager suka rage.

"amatullah na fitowa wanka bataga zunnurai ba da sauri taleko gani bakine yasata komawa saida ta sanyo doguwar riga ta jallabiya hade da hijab snn ta fito.

"tana isa parlour gun tasamu ta xauna snn tace ina yiniku.

"duk suka amsa cike da fara'arsu amatullah tace ya kasuwa?

"sukace kasuwa alhdumll hajiya, ya kuma me jiki?

"amatullah tace jiki da sauri.

"sukace Allah ya kara sauki.

"amin tace hade da mikewa tace bari a kawo maku ruwa ko.

"murmushi kawai sukai hade da nuna jin dadin tarban da tai masu, sabanin irin wanda fadi tai masu.

"ita jirama tai su gaisheta, koda suka gaidata babu amsawar arxiki.

"kitchen ta shiga ta bude frg ta dauko ruwan swan hade da 5life duk ta xuba a babban tire har ta dauka can gefe ta hango gasanshiyar kaza.

"ije tire din tai ta dauki kazar tasa wuka ta yayyake su snn ta dauko plate ta zuba duk ta hada ta kaimasu.

"tana ijewa sukace hajiya sannu da kokari.

"murmushi kawai tai snn ta juya gun Mahfus tace kawoshi naga kuna aiki kada yasaku ku rinka bata.

"hannu tasa ta dauki zunnurai snn tasa kai.

"tunda amatullah ta tsaya a gaban Mahfus yake kallonta hade da yimata murmushi na nuna jin dadin kulawar da tabawa yaran aikinsa.

"itako amatullah ko'a jikinta dauke kanta tai kamar bataga abinda yakeyi ba.

"suma yaran shagon cin namar sukai sosae hade da juice din, saida suka gama tass snn suka fara lissafi.

"kasa kunni fadi tai sbd taji abinda sukeyi.

"itako amatullah suna shiga daki tasa key ta rufe kofa snn ta dauke zunnurai fadi tai masa sosae akan fitar da yai snn tace idan yasake fita sai tasa wuka ta yankeshi.

"gani yadda take masa yasa zunnurai xaiyi kuka.

"kara bude masa ido tai hade da hanashi kukan.

"kama baki yai besake kukan ba.

"amsar kudin hannushi tai taxubasu a gefe.

"suna gama lissafi suka bawa Mahfus kudin, amsa yai hade da godiya snn yacire wani abu daga ciki yai masu insani.

"suma godiya sukai sosae har bakin gate yai masu rakiya.

"yana dawowa ya dauki kudin yashiga dakin fadi.

"dayake tasan kudi ne a hannushi sakin fuska tai sabani daxu da da daure fuska.

"durowar dake gefe ya bude yasa kudi snn yasa key ya rufe.

"gani ya xauna sai fadi yah dai ply?

"Mahfus yace me kika gani.

"fadi tace gani nai ka xauna shiru ko kana bukatar wani abune?

"murmushi kawai yai yace dibomi juice.

"da sauri ta mike ta nufi kitchen.

"fadi kawai yai amma har acikin xuciyarsa ba haka bane tunani abinda amatullah tai masa kawai yakeyi.

"dubi duk irin abinda yai mata na ranshi kyautatawa amma dubi yadda ta daga masa daraja a gun yaran aikin shi.

"fadi ma da yake kyautata mata amma dubi abinda tai masu gaisuwa ma kawai ya gagara, su gaishetan ma bata amsa ba.

"fadi ne ta katse masa tunani hade da cewa gashi.

"amsa yai ya ije a gefe.

"sai fadi tace kayi hakuri kaga na dade ko?

"wlh kaza ne na gasa maka amma yanxu naje dauka bangani ba.

"Mahfus yace maybe shine amatullah tabawa baki...

"da sauri fadi tace kazan nawa?

"ta karisa mgnr ne hade da mikewa ta kami hanyar kofa.

"Mahfus yace ina xaki?

"tace xanje na same ta.

"Mahfus yace dawo ki xauna.

"tace mai?

"yace forget about that.

"xama tai tana makosune.

"shima Mahfus ko kulata beyiba be kuma sha juice din ba, ya xabga uban tagumi hannu bibbiyu.

"tunda Anty Frd taji shiru take cewa hajiya, hajiya kingani ko?

"dama amatullah tanaso mijinta inda a lokacin wani ya kashe mata aure da tananan tana kuka dashi.

"dariya hajiya tai snn tace gaskiya ne.

"nan dai sukai ta hiransu.

"lokacin da kabari yakai kunni alhji Ibrahim yai fada sosae akan koranta da akai.

"hakan yasashi kiranta bayan sun gaisa alhji Ibrahim yake cewa naji abinda yafaru meyasa lokacin da kikaxo baki kariso guna ba?

"shiru amatullah tai.

"sai yace amma yanxu babu komai ko?

"idan kinsan akwai matsala ki sanar dani, ni nasan yadda xan bulowa al'amarin.

"amma yanxu komai yai daidaita ko?

"shiru amatullah tai..

"amatullah tace babu komai abba.

"alhji yace alhdumll haka akeso, dan Allah amatullah duk abinda kike bukata ki sanar dani kada kiji kunya ko nawin.

"amatullah tace to naji abba nagode.

"suna sallama alhji Ibrahim yai mata transfer na dubu dari.

"tana gani alert yashigo murna tai sosae kiranshi tai tai masa godiya.

"barin kudi tai a cikin account dinta sbd akwai kudi da tadawo dashi daga gida a hannunta kuma babu abinda tasiye dashi.

"cikin dare lokacin bcc yaiwa fadi dadi Mahfus ya tashi ya raba kudin biyu ya canxa masa ma xauni.

"da safe bayan su karya sai fadi tace xataje unguwa gaida wata Anty bataji dadiba kwana biyu.

"Mahfus yace bari na kaiki mana...

"da sauri fadi tace aa kai da bakada lpy, nima fitan yakamani dolene shiyasa.

"inba haka ba ta yaya xanfita nabar mijina babu lpy.

"dariya inna tai hade da cewa gaskiya ne.

"shima Mahfus murmushi yai snn yace nagode saikin dawo.

"fadi tana fita gun areas boys dinta tanufa kai tsaye.

"suna ganinta sukace yahh dai hajiya ehhhhh yana, wata ta samune?

"murmushi fadi tai snn tace tunda har kunkaga nazo ai kunsan tasamune.

"ba'a taba samu matsala ba wannan ma banaso asamu matsala.

"idan kuka shigo duk wanga yanimi kawo maku yawa kuci ubanshi ko wayene bance ku ragawa kowa ba.

"dauko address din gidan tabasu snn ta bar gun.

"tana komawa gida inna tace har kindawo?

"fadi tace nadawo inna bansameta bane shiyasa amma xuba jibi xankoma.

"inna tace Allah ya kaimu.

"tana ije kyale kitchen ta shiga ta hadawa inna ferfensun kaji.

"har parlour takawo wa inna, inna taci tana santi, Mahfus yani to ni baxa'a baniba.

"fadi tace aa sbd inna nai.

"inna naci fadi namata tausa.

"duk abinda sukeyi amatullah tana daki tana jinsu.

"sukai shadaya suna hira snn suka kwanta.

"misalin karfe biyun dare saiga barayi abu na farko da sukai shine kashe light din gida.

"snn suka kama bbn maigadi suka daure hade da cusa masa abu a baki.

"suka karisa cikin gida master key sukasa suka bude kofa, suna shiga sukai karo da inna rike da touch light tana kokarin haska masu ido.

"babban cikinsu ne ya watsa mata mari, a gigice inna tasa wata uwar ihu.

"da sauri suka danneta a kasa igija sukasa suka daureta item rufe mata baki sukai da abu.

"amatullah naji haka tashi tai takara rufe kofarta da kyau snn ta xauna bakin gado tana addu'a.

"kai tsaye dakin su fadi suka shiga, suna shiga suka karawa Mahfus bindigar karya a kunni.

"janshi sukai xuwa parlour a tsaye Mahfus ya tsaya daya daga cikinshi ne ya kwashe masa kafa Mahfus ya duka.

"ita kuma fadi wuka suka samata a wiya.

"sukace ina ka ije kudi?

"Mahfus yace ni banida kudi.

"sukace karya kakeyi aina suke.

"Mahfus yasake cewa banida kudi.

"dayan su yace kashirya wa mutuwa kenan.

"banxa dasu, daya daga cikinsu wuka ya dauko zai cakawa Mahfus kenan fadi tasa ihu.

"tana cewa aa Mahfus kabasu kawai dan Allah karsuxo su kasheka a banxa.

"wanda yake kan fadi yace tashi muje ki dauko mana.

"sata a gaba yai suna shiga ta kwashe ta basu.

"Mahfus can gefe ya hango inna tana murkusu2 hawaye ne yake xubo masa.

"su fadi suna fitowa a guje barayi sukabar gidan.

"suna fita a guje Mahfus yaje kan inna yana kuka yana kwanceta.

"fadi na gani haka ihu tasa harda suman karya.

"itama amatullah fitowa tai daga daki.






H.S.Z.ceπŸ–Š
πŸŒΊπŸ’¦πŸŒΊ
πŸ’¦

MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)πŸ’¦


Fasaha online writes F.o.w.


MMN USWAN
H.S.Z.


32

"saida Mahfus ya gama kwance inna.

"snn ya juya kan fadi gani bata numfashi aguje aje ya dibo ruwa ya kwara mata.

"amatullah gefe ta koma ta tsaya tana kallansu.

"a burkice fadi ta falka snn taci gaba da kuka tana fadin a sanarwa police tunkafin su nisa.

"a guje taje daki dauko waya tana fitowa tafara danne2 karya acewarta tana kiran police ne.

"da sauri Mahfus ya karbi wayar hade da cewa kibari kada ki sanar masu.

"fadi na kuka tana cewa yanxu shikenan Mahfus.

"be tanka bata ba kan inna ya koma kamota yai ta hau kan cushion.

"Shima kan cushion ya xauna hade da xabga uban tagumi hawaye ne wani kebin wani.

"kusa dashi fadi ta dawo ta xauna itama kukan taci gaba dayi.

"ita ko inna kukan ma yaki xuwa kurum baka kawai tai.

"amatullah na kare masu kallon tace Allah ya kyauta dakinta ta koma.

"da safe Mahfus ya sanarwa bbn Junior dasu suwaiba da nasir.

"yana sanar dasu duk suka hadu sukaxo, basu dade da xuwa ba bbn Junior da mmn junior suma sukaxo.

"duk a parlour suka hadu bayan su gaigaisa hade da Allah ya kyauta.

"Fatima take tambayar amatullah.

"Mahfus ne yace tana ciki.

"ita da suwauba da mmn junior suka bita har daki lokacin tana kwance.

"nata ganinsu ta tashi da fara'arta suka gaisa sukai mata Allah ya kyauta, tace amin.

"saida dasu dan xauna snn suka fito amma beda mmn junior, bayan fitan sune mmn junior take tambayar amatullah meyasa ta xauna a daki ita kadai?

"amatullah tana kuka ta sanar mata irin rashin mutunci da Mahfus yai mata harda inna.

"shiru mmn junior tai tana jijina lamarin.

"amatullah tace shiyasa ma na daina fita parlour idan kinga nafita kitchen ne kawai kuma ina gama abinda xanyi nake dawowa daki.

"mmn junior tace to abinci fa?

"amatullah tace tunda ya daina kwana a dakina nima na dauke yimasu abinci.

"idan kinga nai abinci daga ni sai zunnurai.

"mmn junior tace kinyi daidai amma dan Allah kikara hakuri wataran sai kabari.

"abinda yasa kikaga sun dade haka sbd bata haihu bane amma tana haihuwa komai xai daidai ta.

"babu abinda amatullah keyi sai hawaye.

"hakuri mmn junior tai ta bata, shigowar Zainab ce ya katsesu.

"batare da ta gaida amatullah ba tacewa mmn junior wai kixo inji yya kutafi.

"bayan ta fitane sukai sallama, mmn junior tana fita amatullah ta koma ta kwanta.

"gani bbn Junior xasu tafi inna tace itama gida xata koma.

"babu yadda ba ai da itaba akan ta tsaya amma taki, da taga suna niman matsa mata kuka tasa masu.

"Hakan yasa suka hada mata kaya suka tafi tare.

"su inna basu dade da tafiya ba su suwaiba suka tafi.

"suna fita hajiya ta kira amatullah sun dade suna hira.

"shiko Mahfus daki suka shiga da matarsa suka kwanta.

"duk da dadewar da sukai da hajiya suna hira amma amatullah bata sanarwar hajiya ba.

"nasir besamu xuwa ba saida ya tashi daga kasuwa snn yaxo bayan sun gaisa ne Mahfus yace su fita waje.

"suna fita can gefe suka koma suka xauna.

"ashe fadi tana makale taji abinda da xasuce gani sun fitane itama tabi ta kitchen tafita ta sito din abinci taje ta makale cikin flower sbd taji abinda mgnr da xasuyi.

"bayan sun xauna ne nasir kecewa Mahfus kaima Mahfus in dan bandakai wake ije kudi masu yawa haka a gida.

"Mahfus yace kaima nasir kafi kowa sani halin yaran shagon baka sani cikinsu shiyasa nace duk cinikin da akai su rika kawomin idan muyi lissafin abinda yashiga da wanda yafita da safe sai akai bank.

"nasir yace hakane amma daga yanxu kada sukara kawo maka kudin gida.

"daga manager har mataimakinsa su rika hada duk cinikin da akai susa a bank duk bayan wata shidda ko karken shekara sai kuyi lissafi kaga abinda kasamu da kuma abinda da karasa.

"Mahfus yace hakama xaifi.

"mikewa Mahfus yai hade da cewa ina xuwa.

"ciki ya koma ya dauko kudin da yaraba biyu ya kawowa nasir.

"nasir yace menene wannan?

"saida Mahfus ya rage murya kayar yasa fadi na makale tana jinsu, snn yace dama da suka kawomin kudin rabawa biyu ne nai na boye rabi kadan din ne na barshi a durowa shine suka dauka.

"Ga me yawan nan kaje dasu.

"fadi tayi iya kokarin dan taji mgnr da sukeyi daga karke amma batayi ba hakan yasa ta ciji yatsa ta koma ciki.

"suma sukai sallama nasir ya tafi gida.

"washe gari fadi tace xataje gidan Anty ta ta gaidata.

"Mahfus be musa ba yace Allah ya kiyaye hanya.

"tana fita gun abokanin tafiyarta taje.

"fadi na fita Mahfus yaje yana bugawa amatullah kofa.

"amatullah tana jinshi amma tai banxa dashi, sai Mahfus yace pls idan baxaki budemin na shigo ba,to dan Allah kituromin yarona inajin ganinshi.

"Mahfus yai mgn har yagaji amma amatullah bata bude ba, saida taji Mahfus yabar gun snn ta budewa zunnurai.

"Mahfus najin fitowar zunnurai da sauri ya bude hannu yana cewa oyoyo my son.

"a guje zunnurai yaxo ya rungume bbnshi, shima Mahfus daukarsu yai yana yimasa kiss.

"sashi a cinyarsa yai hade da kunna masa game a wayarsa suna bugawa tare.

"fadi tana isa gun su suka fito da kudin suka mika mata.

"fadi na budewa bayan ta kirga taga eight hundred thousand ne bude bakin fadi tace har kincire naku kasone?

"Tana mgnr ne fuska a daure.

"hada baki sukai sukace wani irin mucire namu?

"fadi tace nidai kudin da nasani yafi haka ta yaya xaku dauko wannan kudin kubani kamar bansan abinda nakeyi ba.

"daya daga cikinsu yace dan Allah malam idan xaki bamu kasonmu kibamu, idan kuma baxaki bamuba mudibi uwar watsi uban kowama yarasa.

"fadi ta yarasa mana kai ne sabon shiga a harkan, wlh sisi baxan bakuba.

"babban cikinsu yace ku rabu da'ita tasan koni waye dauki kudin kitafi tashi.

"amma kisani wlh binlahi aximu in har kika tafi dashi a yau din nan saina sami maigidanki na sanar dashi ke kika turomu, kuma na sanar da auran wani akanki xarra kikai masa.

"da sauri fadi tace to saime?

"dan tonan asiri dama nasan bakada mutunci.

"dariya yai hade da cewa rashin mutunci ya kare a gunki tunda har kika iya turowa mijinki barayi.

"dariya fadi tai hade da cewa kaidai bakada dama.

"to yanxu ya xa'ayi kasan dai inada bukatar kudi ko.

"tabawa tai ta dauki 75% su kuma tabasu 25% da kar suka amsa, tace karku damu wata aikin tananan xuwa wanda tafi wannan.

"sukace Allah.

"tace Allah kuwa.

"duk kansu dariya sukasa snn takami hanya.

"banki ta nufa direct.

"gani shabiyu tayi kuma tasan yanxu zunnurai xai iya jin yunwa yasa amatullah shiga kitchen ta dafa jollof rice.

"Mahfus na gani amatullah tashiga cikin dauke zunnurai yai daga kafarsa ya barsa da wayan a hannu yana game a hankali yake sanda yana kaiwa dab da kitchen din a guje yaje ya rungume amatullah ta baya.

"amatullah najin haka tasan ba kowa bane sai Mahfus sake spoon din hannunta tai tana kici kicin kwace kanta amma takasa sbd da karfi ya riketa.

"ya jin haka kara riketa yai hade da kwantar da kansa a bayan ta yana shafeta.

"kyaleshi amatullah tai yaci gaba da abinda yakeso sbd ta riga da dora spoon din akan tukuyar da kan wuta saida tabari Mahfus yai nisa wajan shafeta snn ta dauki spoon din dake kan wuta ta nana masa a hannu.

"da sauri ya cire hannun hade da ihu hade da cewa muguwa kawai.

"fadi na shiga bank taga layi yai yawa, kamar ta juya ta koma gida sbd kada Mahfus yaga ta dade.

"amma kuma idan ta koma gida da kudi Mahfus ya ganta da kudi tace masa wa yabata?

"dole yasata ta tsaya bin layi.

"amatullah tana gamawa ta kwashe duk abincin a kula ta xubawa zunnurai nashi a plate ta kai dakinta.

"saida ta wanke duk abinda da ta bata snn taje parlour daukar zunnurai.

"har tasa hannu xata daukeshi da sauri Mahfus ya rike mata hannu

Please Login or Register in order to submit comment