Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yunwar da yakeji amma abinci ya gagareshi ci, juice kawai ya i'ya kurba shi dinma kadan ne kawai sai faman juyi yakeyi da spoon a hannu.

"yana juyayin ta ina xaifara.

"gani hakan yasa amatullah tace bissmllh mana.

"murmushi yai snn yafara ci yakai cokali daya biyu gani abinci taki tafiya yasashi ije cikalin, ido kawai ya xuba mata.

"gani yanayin sa ya canxa ya amatullah cewa yadai Mahfus kodai baka da lpy ne?

"murmushi karfin hali yai snn yace amatullah ni xantafi dama xuwa nai mu gaisa, tunda mun gaisa ni xantafi ya karisa mgnr ne da mikewa.

"itama mikewa tai, tana masa rakiya har yafita babu wanda ya tankawa wani.

"gani sukai bakin gate amatullah taja ta tsaya, anan sukai sallama yatafi itama kuma takoma ciki.




H.S.Z.ceπŸ–Š
πŸŒΊπŸ’¦πŸŒΊ
πŸ’¦
MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)πŸ’¦

Fasaha online writes f.o.w.

MMN USWAN
H.S.Z.

5

"Mahfus saida yai nisa da gidan su amatullah snn yasamu gun ya zauna tunina kala2 yakeyi meyasa yakasa aiwatar da abinda ya kawoshi gun amatullah?

"meyasa take cika masa ido da yawa ne?

"tsoranta nakeji ko kwarjini ne taimi da yawa da har nakasa fadi mata abinda ke zuciya ta?

"know i'tcan possible.

"duk yadda za'ayi saidai ayi amma yau d'in nan nayi alkawarin sanarwa amatullah abinda ke zuciya ta.

"bari namike zama began ni ba.

"mikewa yai yaci gaba da tafiya har yakai gun da xaisamu napap, yana yashiga sai uguwar da yake zaune.

"itama gun da suka zauna da Mahfus takoma ta xauna, tunani kala2 takeyi meya kawo Mahfus ne gida?

"da'alama akwai abinda ke damushi amma kuma yakasa fadi mata.

"to menene wnn?
kodai shima yanajin abinda nake jine a zuciya ta?

"can kuma tace to koma menene Allah yasa alkairi ne.

"mikewa tai hade da kwashe kayan abinci takai ciki.

"kafin Mahfus ya'isa gida lokacin sallar magrib yayi masallaci uguwarsu ya tsaya yai sallar magrib da isha, saida ya idar snn yakarisa ciki.

"ana idar da sallar isha misalin 8-30 saiga kamarudee yaxo gidan su amatullah kai tsaye ciki yashiga har parlour daidai lokacin akwai hajiya da abba yya khamis da ita kanta amatullah din.

"har kasa ya duka cikin girmamawa ya gaida su abba da hajiya, duk suka amsa hade da tambayar nashi iyayen yace suna lpy suce a gaidaku.

"tare sukace suna amsawa.

"yya khamis yace ina mutumina? wato yya kamarudee kenan.

"kamarudee yace yana gida.

"abdulshakur shine yyan kamarudee tare sukai makaranta tun suna yara har girmansu har aure ma lokacin daya sukai.

"tun suna yara sun shaku sosae bcc kawai ke rabasu sai yanxu da sukai aure, yau da gobe yafi karfin wasan yaro.

"bayan sun gama gaisawa ne duk suka watse, yarage dagashi sai amatullah.

"tashi yai yadawo kusa da'ita gani haka yasa amatullah kara dauke fuska.

"kamarudee da yaga haka sai yakara saki nashi fuskan hade da cewa hajiya amatullah kenan, kina lafiya?

"tace klau.

"gani yadda ta kara daure fuska da kuma amsa masa gaisuwa ciki isgili.

"yasashi cewa haba amatullah idan wani laifi nai miki nafiso ki fadimi amma bskikama fushi daniba.

"dariya tai masa me kama da yage hade da cewa babu komai kamarudee...

"bata rufe bakiba saiga kiran Mahfus yashigo wayarta.

"jin wayar amatullah tafara ringing da sauri kamarudee ya kafawa screen din ido, itama amatullah din wayar take kallon gani number Mahfus ne yasa jikinta wani iri, takasa daga wayar.

"gani haka sai kamarudee yace ki daga mana.

"shiru tai batare da ta tankaba.

"har wayar takatse.

"murmushi kawai kamarudee yai hade da cewa da kin dauka kawai.

"wayar na katsewa da sauri ta kashe gaba daya.

"shima Mahfus gani har wayar ta katse bata daga ba yasa besake kira ba.

"kamarudee yace amatullah.

"tace na'am.

"kamarudee yace amatullah xuwa nai da kaina sbd muyi mgn ta fahimta dake, mgnr waya bazata gamsar d'ani ba shiyasa nazo muyishi gani gaki.

"da sauri amatullah tace mgnr me kuma?

"gani yadda tai tuni yariga yagano inda ta dosa.

"amma be nuna mata ba, yaci gaba da cewa amatullah indai a gaskiya aure nakeso kuma a yadda nakeso banaso shekararga takare banyi aure b.

"saidai kinsan al'amarin ubangiji kana naka Allah yana nashi, nashi din kuma shine gaskiya.

"shiyasa nazo mu tsaida mgn daya, ko yah kika gani?

"shiru amatullah tai kanta a kasa.

"kamarudee yace ba shiru zakin ba, mgn zakiyi.

"a lokacin ne amatullah tace a gaskiya akwai abinda nake shiryawa, idan xaka iya hakuri har na kammala to.

"da sauri kamarudee yace menene abinda kike shiryawa wanda ba zaki'iya fadin shiba?

"tun da rana nake tambayar ki idan anyi mgn saiki ce akwai abinda kike dhiryawa.

"amatullah inaso kisan duk abinda zakiyi ya zama gaskiya kinsa gaskiya aciki.

"ita rayuwa da kike gani d'an taka sannu ne.

"idan kikabi rayuwa da sauki komai zaixo miki da sauki.

"ni ba takura miki xanyi ki aureni dole ba.

"idan Allah yayi ke matata ce wlh duk yadda kikakai ga dojewa sai anyi.

"idan kuma wani kike hange amatullah wlh ina me tabbatar miki ba zaikai abinda iyayenki suka hango miki ba.

"ni a matsayin yya nake a gareki ba xanga abinda zai cutar dake nabari ba.

"amatullah ina me tabbatar miki tattara hankalinki waje daya kisan abinda kikeyi.

"ni xantafi idan abinda na fadi miki yai miki xafi to kiyi hakuri.

"jiki a sanyaye amatullah tace aa babu komai nagode.

"mikawa yai hade da cewa idan na isa gida xamuyi waya.

"amatullah tace to ka sauka lpy.

"yace amin nagode.

"har bakin motarsa tai masa rakiya, gani fitowa yya khamis ne yasata komawa cikin gida.

"bayan shigan amatullah cikin ne yya khamis yake tambayar yadda sukai da'ita.

"babu abinda kamarudee ya boyewa yya khamis duk yadda sukai da amatullah kamarudee ya fadiwa yya khamis.

"yya khamis yace babu damuwa xansa abinyi kuma in Allah ya yarda xansa mata ido naga abinda take shiryawa.

"kamarudee yace to yya nagode sosae, dan Allah katai makami wlh inaso amatullah sosae.

"tun kafin su abba su mgnr hadamu nake son amatullah, sai kuma gashi iyaye suma sun yanke shawar hada mu.

"shiyasa yya tun kafin ta kare makaranta naso ayi auren idan yaso ta karisa a gida na, su abba sukaka bin nawa yanxu ga abinda ya biyo baya.

"yya khamis yace my brother karkaji komai in Allah ya yarda komai xai daidai ta.

"kamarudee yana mgn ne cikin rauni, yace amin yya nagode.

"yya khamis yace babu damuwa idan kaje ka gaidamin su hajiya da abba.

"kamarudee yace zasuji.

"snn sukai sallama yashiga motarshi yai gida.

"amatullah na shiga ciki dakinta ta shige kai tsaye, bayab ta shiga ne sai ta kunna wayar ta snn takira Mahfus.

"lokacin wayar tana hannushi yana gani kiranta da sauri yai receiving hade da sallama.

"cikin fara'a ta amsa bayan sun gaisa ne amatullah tace dan Allah kai hakuri naga kiranka lokacin ina tare da bakone shiyasa.

"Mahfus yace babu damuwa amma yanxu bakon yatafi ko yana nan?

"amatullah tace yatafi.

"snn taci gaba da cewa daxu kazo sai naga kamar kana cikin damuwa ko?

"murmushi yai hade da cewa amatullah kenan bana cikin damuwa saidai.....

"da sauri tace saidai me?

"yai shiru.

"tace hello Mahfus kana jina kuwa?

"Mahfus yace ina jinki amatullah.

"sai tace to kodai baka da lpy ne?

"Mahfus yace aa lpy ta klau.

"to kodai wani abu kake bukata a gun?

"murmushi yai hade da cewa kamar su me kenan amatullah?

"amatullah tace yau ake yinta Mahfus inda nasani ai bazan tsaya tambayar kaba.

"Mahfus yace hakane amatullah.

"Mahfus yace wlh amatullah tun ranar da muka fara haduwa Allah yasami kaunarki.

"tunaninki ya dameni har kusan hanani bcc yakeyi wlh amatullah ina matukar kaunarki, amma bansan yadda xaki dauki abin ba.

"wani irin sanyi amatullah taji a xuciyarta.

"da kanta take tambayar zuciyarta ashe Mahfus yanajin abinda nakeji a zuciya ta?

"shiru da yaji yasashi cewa hello amatullah kina jina kuwa?

"wani irin dadi ne ya xiyarci zuciyan amatullah da kuma kunya bashi amsa hakan yasa ta kashe wayar.

"mmki ya kama Mahfus hade da cewa to kodai banyi mata bane yasata kashe wayar?

"nadai nasan banda mummunar halinta saidai kudi ne bandashi.

"tunda yanxu wata irin rayuwa ne muke cikin duk kyaun ka da kyaun halinka idan bakada kudi aikin banxa ne.




H.S.Z.ceπŸ–Š
πŸŒΊπŸ’¦πŸŒΊ
πŸ’¦

Fasaha online writes F.o.w.

MMN USWAN
H.S.Z.

6

"amatullah na kashe wayar wani irin tsanle tai hade da cewa Allah na gode maka.

"ashe Mahfus yana sona? ashe ba nikadai nakejin haka a zuciya ba.

"lailai ni amatullah ba karamin dace nai ba, idan har nasamu Mahfus a matsayin mijin aurena ba.

"to amma ba nan gixo ke sakar ba yy xanyi da abba?

"da wani ido xan tunkari abba da cewa banaso kamarudee?

"shi kanshi kamarudee din ya xanyi dashi?

"gashi da fushi da kuma naci.

"ba lailai bane ya fahimce ni.

"a gaskiya ba xan'iya auren kamarudee ba.

"ba xan'iya rayuwa dashi ba, rayuwa kuma ta har abada.

"shiru tai sai can daga baya tai wani tunani da sauri tace kai kamarudee sai dai kayi hakuri, Mahfus shine yafi dacewa dani.

" tana cikin hakan saiga text din Mahfus yashigo da sauri ta bude text din.

"ga abinda ta gani kamar haka.

"( Assam amatullah na bugone sbd naji makomata muna cikin mgn kika kashe waya shiyasa na bugo sbd naji aina aka ijeni? idan har banyi makiba dan Allah banaso ki boyemi nafiso ki sanar dani. Kuma idan har haka ya kasance d'an Allah inaso muci gaba da zumucin mu kamar yadda muka saba.

"ina sauraran amsarki.)

"tana gama karantawa tai wani ajiyar zuciya, itama rubuta masa tai kamar haka.

(Assam Mahfus naga sakoka babu damuwa kasan hausawa sunce matar mutum kabarinsa dan haka karka damu Allah yai mana jagora)

"snn tai sanding.

"Mahfus yace gani shigowar text din ya bude.

"bayan ya karanta ya gama babu abinda ya fito daga bakinsa sai alhamdllh.

"kamarudee ya'isa gida ne cikin bacin rai kwata2 babu abinda fuskanshi ke nunawa sai alama damuwa.

"yana parlour dakin shi ya shige kai tsaye, ko kayan jikinshi be cireba haka ya haye gado ya kwata a rigigine hade da rufe ido amma ba bcc yake yiba.

"lokacin da kamarudee yashigo parlour akwai hajiya a gun, kuma ita kanta hajiya tasan idan har yafiya ne kamarudee ba xai shige be tsaya ya gaida taba.

"hakan yasata mikewa da sauri tanufi dakinshi, tana shiga ganinshi tai a rigigine kamar me bcc amma tasan ba bcc yakeyi ba damuwa ce kawai.

"karisowa tai tasamu bakin gado ta zauna hade da kiran sunanshi kamarudee kamarudee sai a na uku snn yace na'am.

"hajiya tace lpy kuwa meke damuka?

"idanshi a rufe batare da ya tubeba yace babu komai.

"hajiya tace kamarudee tashi ka xauna kaji.

"dagowa yai ya jingina da bango, snn hajiya taci gaba da cewa kamarudee lpy?

"yace ba komai.

"tace wani abune ya sameka?

"yace aa.

"wani ne ya bata maka rai?

"shima yace aa.

"hajiya tace kamarudee inaso kasan cewa nine mahaifiyarka wanda a rayuwar ka ta duniya baka da wance ta fini, idan baka fadimi damuwar kaba kanada wanda zaka fadi matane?

"kamarudee yace aa.

"hajiya tace to ina sauraranka.

"Shiru yai snn yace hajiya akwai wani abu da nake matukar so a rayuwata inaso a matsayinki na mshaifiyata kitayani da addu'a idan rabonane Allah ya bani, in kuma ba rabona banane ba Allah yamin musanya da abinda yafi maza alkairi.

"da sauri hajiya tace amatullah ne ko?

"murmushi kawai yai hade da cewa aa.

"sai tace to shikenan in Allah ya yarda duk lokacin da nai sallah xantayaka da addu'a koma menene Allah yai maka zabin alkairi.

"Kamarudee yace amin nagode.

"snn hajiya tace tashi kaje kayi alwala kayi nafila koda raka'a biyu ne, ka fadiwa ubangiji kukanka xakaji saukin damuwar ka kajiko.

"kamarudee yace naji nagode.

"hajiya tace to mike.

"mikewa yai yashiga toilet yai alwala saida taga yafara sallah snn tafita.

"sai da kamarudee yai raka'a goma sha biyu a sujudan shi na karkene ya tsaya sosae yana fadiwa ubangiji damuwarshi da niman zadin alkairi gun ubangiji.

"snn ya daga ya zauna yai taihiya hade da sallama ya dade sosae ya lazumi har saidai bcc yaci karfinsa snn ya shafa ya kwanta.

"Mahfus yana gani text yashigo wayarsa da sauri ya bude yana gama karartawa rungumar wayar yai yana hamdala.

"tun daga lokacin soyayya mai karfi ta kankama tsani Mahfus amatullah.

"shiko yya khamis tun daga lokacin yasawa amatullah ido.

"duk juyin da xatai yana nan biye da'ita.

" kowa weekends Mahfus yake xuwa gun amatullah.

"idan yana da isanshe kudi sai ya biya yai mata siyayya iya karfinsa snn ya karisa gidan su.

"duk lokacin da bazai samu xuwa ba saidai sue ko takira ko kuma shi yakira.

"tunda kamarudee yaga haka yarage kiran amatullah, sbd koda yakira ba xata daga ba.

"wata weekend bayan sallar isha Mahfus yaxo suna hira shida amatullah, kamar daga sama saiga kamarudee yaxo.

"tun kafin ya parking ya hango amatullah ita da Mahfus tsaye da alama hira sukeyi sbd yadda yaga amatullah ke fara'a.

"saida ya karewa Mahfus kallon snn yafito kai tsaye gun su yanufa yana isa gun hannu ya mikewa Mahfus suka gaisa.

"kamarudee saida ya daidaici amatullah na kallanshi snn yaiwa Mahfus wani irin kallon rainin wayo.

"snn yace bari nashiga daga ciki.

"amatullah kasa amsawa tai saidai dariyan yage.

"yana shiga sukai karo da yya khamis da sauri kamarudee ya gaidashi, baya ya amsa snn yace bari na turo maka ita.

"kamarudee yace ai naganta a waje....

"da sauri yya khamis yace a waje kace ita dawa?

"murmushi kawai yai hade da cewa da wani.

"a fusace yya khamis ya nufi gun da su amatullah suke hira, Mahfus yana ganinshi da sauri yace yya ina yini.

"hannu khamis ya mike masa suka gaisa amma babu alamar walwala a fuskansa.

"bayan su gama gaisa wane yya khamis yace dan Allah kai hakuri abbanmu ne yakeson ganinta amma xuwa gobe kadawo.

"Mahfus yace babu damuwa, a take sukai sallama ya fita.

"yana fita yya khamis yafara xaginta har suka shiga cikin parlour.

"gani bakinta na motsi tanada ninyar xaginsa ko meda masa da mgn a fusace ya dauketa da tokari kadan yarage ta fadi kamarudee ne ya tareta da sauri.

"wani irin ihu tasa,wanda yasa abba da hajiya fitowa da sauri.

"tana gani fitowarsu taci gaba da kuka sosae, abba ne yake tambayar abinda yake faruwa.

"yya khamis ya kwashe komai ya fadiwa abba, mmki ya kama abba sosae sai yace amatullah wai da gaske ne.

"shiru tai hade da sunkuyar dakai kasa.

"abba yace amatullah kiyi mgn.

"shima shiru tasake yi.

"yya khamis yace abba kaga abinda nake fadi ko.

"abba yace aa khamis kabita a hankali.

"gani shiru da tai yasa abba yace kamarudee idan kaje gida kacewa alhji inaso ganisa.

"kajiko gara kawai ayi bikin ne kowa ya huta.

"da sauri amatullah ta mike hade da cewa wlh abba bana sonshi.

"gigice abba yace amatullah me kika ce?



H.S.Z.ceπŸ–Š
πŸŒΊπŸ’¦πŸŒΊ
πŸ’¦

MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)πŸ’¦

Fasaha online writes F.o.w.

MMN USWAN
H.S.Z.

INA MAI BAKU HAKURI MASU KARATU DA MUNTUWAR DA NAYI, NA RASHIN SA SUNA DA BANYI BA A PAGE 6.

WASAU AL'AMURA NE SUKA SHAMIN KAI A'M SORRY PLEASEπŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»

7

"da gudu amatullah ta karisa daki kan gado ta fada tasa wani sabon kuka.

"jikin kamarudee yai yarasa yanda zaiyi mikewa yai hade da cewa ni xantafi gida yya khamis.

"shima kanshi jikinshi yai sanyi hade da cewa to kamarudee ka sauka lpy.

"tafiya yakeyi kamar wanda beda lalka a jiki da haka yaja motarsa xuwa gida.

"yana isa yasami su abbanshi da hajiya a parlour suna zaune, shima gun yasamu ya zauna tagumi ya zabga hannu bibbiyu.

"gani haka abba yace kamarudee lpya kuwa meke faruwa.

"kamarudee ya kwashe duk abinda ya faru ya sanarwa iyayensa.

"gani yadda ya nuna damuwa abbanshi ya matso kusa dashi hade da dafe kafadarsa yace kamarudee.

"kamarudee yace na'am abba.

"abba yace ni mahaifinka ne kasa bazanso na ganka cikin damuwa naji dadi ba ko.

"kamarudee yace haka ne abba.

"abba yace to inaso ja kwantar da hankalin ka kacire duk wata damuwa dake rai ka.

"idan kaga baka auri amatullah ba dama Allah beyi matarka bane, sbd ninasan waye alhji Muhammad,alhji Muhammad tsayayene akan iyalansa.

"dan wata dalili ta banxa da xata bujuro dashi daga baya, bayan ga yadda aka tsaida mgn da'ita tace kuma ta amince shine yanxu zata kawo wata dalili ta banxa, ninasan bata isa bane alhji Muhammad bazan kyaleta ba.

"duk da munada ninyar hadaku kafin muyi maku mgn ku kuka fara hada kanku, koda kabari yaxo mana muji dadi sosae.

"bamu yanke shawara ba saida muka tambayeku kukace kuma kun amince.

"dan me yanxu xata kawo mana wani mgnr banxa.

"kamarudee kodai wani abu kai mata?

"da sauri kamarudee yace abba niko me xanmata?

"abba yace kodai tuna.

"kamarudee yace nidai nasan wani tasamu.

"hajiya tace aa kamarudee samu wani bashi xansa ta juya maka baya haka ba.

"kamarudee yace wlh kuwa abba.

"alhji yace wanene wannan kudi yafika nasaba ko kamala komai?

"da har xaisa tajuya maka baya haka?

"ni nasan Muhammad besani bane idan ma yasani nasan ba xai kyaleta.

"hajiya tace kwarai da gaske.

"haka dai sukai ta tattanawa a tsakaninsu.

"har daki abba yabi amatullah shida yya khamis da hajiya, suka sameta kwance tana kuka.

"hajiya ce ta xuba mata mari da sauri ta mike zaune hajiya tace kukan uban me kikeyi?

"amatullah tai shiru.

"abba yace amatullah ban fahimci abinda kike nufi ba, shiyasa na biyoki har daki inaso ki fahimtar dani.

"wani sabo kuka amatullah tasa.

"abba yace ba kuka na tambsyeki ba, bayani nakeso kinmi dan na fahimta.

"amatullah taci gaba da kuka.

"yya khamis ya fusata kafa yasa xai tokareta da sauri abba ya tsaidashi.

"abba yace amatullah kimi bayani idan kuma kinfiso na barki da yyanki ne to shikenan...

"da ssuri amatullah tace aa.

"abba yace to ina sauraranki.

"dukawa tai gwiwa bibbiyu tafa da cewa dan Allah abb kayi hakuri wlh banaso kamarudee.

"hajiya najin haka tasa salati.

"hannu abba ya dagawa hajiya alama tai shiru.

"snn ya yajuya gun amatullah yace ko xansan dalili.

"amatullah tace wlh abba son shine kawai banayi.

"abba yace to meyasa da kika amince xaki aureshi, bayan kinsan baki sonshi?

"shiru amatullah tai.

"abba yace dake nakeyi amatullah.

"shiru tasake yi.

"abba yace amma meyasa da kikasan baki sonshi baki fadi masaba tun farko saida kika bari yai xurfi a sonki shine daga baya xakice xaki sonshi?

"amatullah tace eh lokacin na amince ne sbd bani da xabi a lokacin.

"abba yace amma kinsan haka yana daga cikin yaudara ko?

"idan har kinsan xaki canxa ra'ayi meyasa tun farko da yace yana sonki bakice aa ba?

"kinsan abinda kike ninyar aikatawa xai xubar maki da mutunci a idon jama'a ko?

"amatullah a nawa tunani koda ace baku kuka hada kanku ba, rana tsaka na dauki kamarudee na baki a matsayin mijinki banyi tunani xaki kiba banle ma Ku kuka hada kanku.

"amma kinsan idan har kikaki amincewa da auren kamarudee ba xanji dadi ba ko?

"amatullah tace abba kayi hakuri wlh ba xan'iya zama da kamarudee a matsayin miji nane ba.

"abba yace amatullah shi wanda kikeso yanxu kudi ko nasaba ko kamala yafi kamarudee?

"amatullah tai shiru.

"abba yace amma kinsan lokacin dana yanke miki bazan daga ba ko?

"wlh amatullah koya shirya ko be shirya ba lokacin dana samiki babu fashi, idan kuma be shirya ba kowaye nasamu xanbakishi idan kuma har kikace bakiso to wlh saidai ki barmi gida na.

"abba yac gaba da cewa shikenan idan Allah ya kaimu gobe inaso ganinshi.

"shiru amatullah tai tana kuka.

"a fusace abba yafita shida yya khamis.

"suna fita hajiya ta xanzage amatullah hade da cewa wawiyar bazan kawai wanda batasan me sonta ba.

"inaso ki fadimi dame Allah ya ragi kamarudee kyau ko kudi?

"kamarudee yarone kyankyawa saidai kice baki.

"lalla amatullah yanxu nakara yarda bakisan ciwon kanki ba.

"wani sabon kuka amatullah tasa tana cewa dan Allah hajiya kiyi hakuri wlh inaso Mahfus......

"Kafin ta karisa hannu hajiya tasa ta bigewa amatullah baki hade da cewa sainaci ubanki idan nakarajin sunashin a bakinki.

"su abba suna fita parlour suka koma shida yya khamis abba yaci gaba da fada yana cewa yarinyar banxa so take ta medani mutumi banxa wlh uwarta xataci, daga ita harshi baridai Allah ya kaimu gobe yaxo.

"yya khamis yace kawarai da gaske idan yaxo gobe tsaya xamui masa mumasa koran kare yadda koda kofar gidan ga baxai sake tunani yasani ba banle yai tunani xuwa.

"abba yace barni dasu kawai.

**** **** ****
WAYE MUHAMMAD DA IBRAHIM?
Muhammad da Ibrahim abokan juna ne tun suna yara, dare sukai primary da secondary har degree d'insu.

"bayan kammala karatun su Ibrahim be tsaya jiran aikin gwamnati ba yafara business ciki sa'a Allah yasa masa albarka aciki.

"shiko Muhammad aiki company yasamu a kaduna, gani harkokin basu garawa sosae yasa Ibrahim ya jawo Muhammad jikinshi kudin dayasamu na sallama dashi shida Ibrahim suka kara sbd harkan tafi habaka sosae.

"Allah majikan bawasan yasa masu hannu har ka ta kankama sosae a lokacin ne iyayensu sukace saidai suyi aure.

"matan Muhammad yar' asalin garin Jos ne, mai suna Bara'atu.

"matar Ibrahim kuma yar'asalin garin bauchi ne.

"Muhammad yanada yara hudu, yya khamis da anty Khadijat sai amatullah da kaninta yazed.

"yya khamis yai aure har da d'ansu guda mai sunan abba wato Muhammad, tare suke business da abba.

"Sai kuma anty Khadijat itama tai aure saidai bata haihu ba, tana aiki ne a teaching hospital dake cikin garin minna.

"sai amatullah da kuma kanita yazed.

"Shikoma Ibrahim yara uku Allah ya azurtashi dashi abdulshakur shine babba sai Rukaiyya da kamarudee.

"tun akan rukaiyya su abba sukaso hadasu da yya khamis amma Allah be yarda ba, wani d'an majalinsan taraiya take aure anan cikin garin minna amma suna zaune ne a abuja.

"saida tai aure snn yya khamis yai nashi, kusan lokacin daya sukayi dare da abdulshakur.

"duk suna zaune ne a anan minna din.

"shiyasa suka kai kokarin hada amatullah da kamarudee, tun kafin suyi mgnr hakan sai Allah yasa a lokacin sun daidai ta kansu shiyasa da kabari yakai kunni iyayensu ba karamin murna sukai ba.

***** ***** *****
CIGABAN LABARIN
"tunda Mahfus yabar gidan su amatullah zuciyarsa take fadi masa akwai matsala shiyasa yake ta juyayin kiranta.

"Itama shiru bata kiraba yasa Mahfus kiranta lokacin tana zaune da iyayenta a parlour.

"gani kiran Mahfus yashigo wayarta da sauri tamike xataje daki.

"da sauri abba yace ina zaki?

"shiru amatullah tai tana kallon wayar.

"Abba yace waye ke kiranki?

"nan ma tai shiru.

"yya khamis yace waye zai kirata inba Mahfus ba.

"da sauri abba yace mikomin wayar.

"jiki a sanyaye ta mika wayar.

"abba na amsa yai receiving call din hade da karawa a kunni.

"Mahfus yace hello baby kwana biyu da fatan kina lpy.

"abba yace ba ita bane mahaifinta ne.

"da sauri Mahfus ya gyara murya hade da sallama.

"bayan abba ya amsa.

"Mahfus yace ina yini abba.

"abba yace lpy klau.

"Mahfus yace dan Allah abba kai hakuri bansan kai bane.

"abba yace babu damuwa idan kasamu lokacin zuwa yamma inaso ganika.

"Mahfus jikin na rawa yace Allah ya kaimu.

"abba betsaya sunyi sallama ba, ya kashe wayar cikin aljihunshi yasa.

"itako amatullah gabanta sai faman bugawa yakeyi.

"Mahfus yanajin abba ya kashe wayar gun yasamu ya zauna tunani kala2 yakeyi shida kanshi yake tambayar kanshi kuma yabawa kanshi amsa.

"da yamma bayan sallar la'asar hajiya da abba da kamarudee da da abdulshakur suka shirya xuwa gidan su amatullah.

"daidai lokacin abba na zaune yana jinran xuwan Mahfus.

"kamar daga sama suka jiyo sallama abba beda ninyar tashi jin muryar aminisa ne yasashi mikewa da sauri ya fita ya taresu hada da cewa kune haka?

"murmushi abba Ibrahim yai hade da shan hannu, abba yai masu iso xuwa ciki.

"a parlour suka zaizana hajiya da sauran yaran gidan suka fito, duk aka gaigaisa cikin mutunci da girmamawa.

"amatullah tun suka gama gaisawa takoma gefe ta xauna kanta a kasa, kasa dago kai tai duk irin hirar da akeyi ana wasa da dariya amma banda ita.

"shiko kamarudee tunda amatullah tafito daga daki idonshi ke kanta ko kibtawa bayayi.

"tunda tagano haka kara daure fuska tai.

"suna cikin hirane saiga gateman yai sallama yya khamis ne ya amsa hade da mikewa ya leka gani gateman ne yasashi cewa lpy?

"gateman yace mutumin dake xuwa gun amatullah ne yaxo yace nasanarwa alhji yana waje.

"Jiyawa yya khamis yai yasanarwa abba.

"abba yace kace yashigo.

"juyawa gateman yai yaje ya sanarwa Mahfus, Mahfus shida wani abokin sane sukaxo me suna adam sun hadune a school din da yake service kuma suna good time dashi hakan yasa suka hada daki daya.

"karisawa sukai ciki sun shiga ne cikin girmamawa hade da sallama.

"su abba suka amsa.

"har kasa suka duka suka gaida su abba da hajiya.

"Bayan su gama gaisawa ne hajiyan amatullah dana kamarudee suka mike xuwa cikin daki.

"abba Muhammad ne yace waye Mahfus daga cikinku?

"Adam ya nuna Mahfus.

"snn abba yace bata sanar dakai kamar nayi mata mjin bane?

"da sauri Mahfus yace aa.

"abba yace to daga yau banaso sake ganinka a kofar gidan nan, nariga naiwa yar'ta miji nanda sati biyu zan daura mata aure.

"jin haka amatullah tasa kuka tana fadin Dan Allah abba kayi hakuri wlh b...

"kafin ta karisa yya khamis ya tokareta a baki.

"shikuma abba dakawa su Mahfus tsawa yai hade da cewa me kuke jira?

"da sauri suka mike zasu fita.

"amatullah tasa wani irin kuka tana fadin nashiga uku d'an Allah abba kayi hakuri.

"da haushi ya kama yya khamis besan lokacin da ya rufeta da duka ba.

"gani haka abba kamarudee ya dakatar dasu Mahfus, suka dawo suka zauna abba Ibrahim ya juyo kan Mahfus yace kai da aure kake sonta koyaya?

"Mahfus yace eh abba.

"abba yace to inaso kaje ka turo iyayenka suxo ayi mgn...

"da sauri abba yace

Please Login or Register in order to submit comment