Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dawa?

"ba dai ni ba.

"murmushi abba Ibrahim yai snn yace eh dani xasuyi.

"karamar tadarda abba ya dauka ya rubutawa Mahfus number wayarsa abawa Mahfus.

"Mahfus ya amsa hade da godiya snn suka fita.

"kamarudee dake zaune ji yai kamar ruwa ya cinyeshi.

"abba Muhammad yace kamarudee.

"da sauri yace na'am abba.

"abba yace kaje kanimo mata ko a inane idan har kana sonta ni xan aura maka ita.

"kamarudee yace to shikenan abba.

"yya khamis da yafara dukan amatullah saida yakai ta daki.

"ihu tane sukaji yasa hajiyan kamarudee fita da sauri dakin amatullah tashiga gani irin dukan da yya khamis kewa amatullah yasata shiga tsakiyarsu.

"tana fadi saidai kadukeni.





H.S.Z.ceπŸ–Š
πŸŒΊπŸ’¦πŸŒΊ
πŸ’¦

MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)πŸ’¦

Fasaha online writes F.o.w.

MMN USWAN
H. S.Z.

8

"jin kamar da hajiya tai yasa yya khamis jifa da igijar da yake duka dashi.

"kai tsaye parlour ya nufa gun su abba.

" gani yadda abban kamarudee yashiga damuwa yasa alhji Ibrahim cewa su kamarudee da yya khamis su basu gun zasu mgn.

"mikewa sukai suka fita mota ne kamarudee yakoma ya samu ya zauna tunani irin2 yakeyi.

"bayan su fita ne alhji Ibrahim yake cewa abba, alhji Muhammad.

"Muhammad yace na'am.

"yace dan Allah banaso kasa damuwa a ranka kasan ance matan mutum kabarinsa, tunda kaga haka yafaru dama amatullah ba matar sa bane.

"abinda nakeso kasani a rayuwa wani baya auran matan wani haka kuma wani baya haihuwan d'an wani.

"abba yace himm Ibrahim kenan amma kafi kowa sani...

"da sauri alhji Ibrahim yace sanan me?

"alhji Ibrahim yace alhji Muhammad inaso kabar yarinya ta auri wanda takeso, kafi kowa sanan halin yaran xamani idan har kai kokarin hanata kafi kowa sani komai xata iya aikatawa tunda tana sonshi.

"ka godewa Allah ma tunda da aure yake sonta.

"da sauri yace nikuma banyi niyar bata shiba.

"alhji yace Muhammad idan kaga ba'ai wannan auren ba to ka tabbata mutuwa nai kafin lokacin.

"amma idan har ina raye sai amatullah ta auri wanda takeso.

"dan me yarinya gata da wanda takeso ace za'a mata fin karfi, to wlh ba zaisabu ba.

"dolene auren shi kamarudee yaje ya samu wata mata, tunda ance ba'a sonshi dole ne.

"abba yace to shikenan amma saidai tanimi wanda xai daura mata aure bani ba.

"shikuma kamarudee Allah yabashi wanda tafita.

"da sauri alhji Ibrahim yace itama Allah yabata wanda yafishi.

"duk sukasa dariya.

"su jima sosae suna hira, snn suka koma gida.

"bayan su fitane abba da hajiya suka sami amatullah a dakinta fada sukai mata sosae.

"hajiya na cewa yanxu sbd Allah kinzabi kije ki auri wani bare ba d'an uwarki ba?

"Kinxabi kibar dangikin ki da yar'uwanki da kowa naki kije can ida babu wanda kika sani?

"amatullah na kuka ta daga kai alamar eh.

"da sauri hajiya tace eh fa kikace amatullah?

"inaso ki fadimi dame Mahfus din yafi kamarudee?

"amatullah shiru tai taci gaba da kuka.

"gani yadda amatullah keyi yasa abba jin haushi cewa kawai yai kyaleta hajiya xataga tsayarta.

"suta sukai suka barta agun.

"su alhji Ibrahim suna isa gida kamarudee be tsaya ko'ina ba sai dakinshi gado ya haye hade da jingina jikin hango kanshi na kallon sama.

"tunani ne kawai yakeyi yarasa abinda yaiwa amatullah da take kinshi haka.

"a xuciyarsa yake fadin nidai nasan Mahfus befini da komai ba, kyau yafini ko wayewa ko kuma kudi da har amatullah zata bujirewa mgnr akan wani banxa.

"duk a zuciya yake tunani2 haka, ashe abba yanata sallama kamarudee bejiba yariga yai nisa a tunani.

"har abba yashigo kamarudee besani ba saida ya dafe kafadarsa a gigice ya kalli abba snn yace abba yaushe yashigo?

"abba be tanka ba gun yasamu ya zauna hade da dafe kamarudee snn yace kamarudee3 sau nawa na kiraka?

"yace sau uku.

"abba yace inaso ka cire amatullah a zuciyarka, inaso ka shafeta a tarihin rayuwarka, inaso ka mance kamar a rayuwa kuntaba soyayya da'ita.

"idan har nina haifeka umurni na baka.

"kai baka gode bama da tanuna bata sonka? inda wata ne sai anyi aure taxo ta cutar dakai.

"wlh kamarudee bana bakin ciki da haka ya kasance Allah yasa haka yafi alkairi.

"kuma banaso ka kullace ta azuciya dan tace bata sonka har gobe amatullah kanwarka ce, ko bayan rainane inaso kariketa tamkar uwa daya uba daya kana jina ko?

"Kamarudee yace inaji abba.

"in Allah ya yarda xantayaka da addu'a Allah yai maka musanya da abinda yafi alkairi.

"kamarudee yace amin nagode abba.

"hira sukai sosae snn abba yafita yaje ya kwanta, shiko kamarudee tashi yai ya dauro alwala yaxo yafara jera nafifili har saida yai raka'a goma snn yai sallama yadade yana fadiwa ubangiji kukansa snn yashafa.

"ranar juma'a ana sauka daga masallaci Mahfus ya kami hanyar kano yana sauka direct gidan kani bbnshi yanufa bayan sun gaisa gani haka yasa bb karami yace amma isowar kenan ko?

"Mahfus yai murmushi hade da cewa wlh bb.

"da sauri bb karami yacewa motarshi takawowa Mahfus abinci.

"da sauri ta mike ta kawo masa abinci, sosae Mahfus yaci yanaci suna hira.

"bayan ya gama cin abinci ne Mahfus ya sanrawa bb karami abinda ke tafe tashi.

"saida bba karami ya jijina mgnr tuku snn yace to Mahfus kadaifi kowa sani halin da muke ciki, abincin da xamucima wani lokaci gagararmu take.

"wlh Mahfus a yanxu da nake haka idan har kace mutafi ko kudin ko mota bandashi.

"murmushi kawai Mahfus yai hade da cewa bba babu damuwa, Allah xai rufa asiri.

"bb yace yarufa saidai yakara.

"saida suka kara taba hira snn Mahfus ya karisa gida gun mmnsa.

"Mahfus yana sallama Mmn Mahfus tana gani d'anta da sauri taje ta rungumeshi tana murna a parlour suka fara xama ruwa ta dibo masa hade da abinci Mahfus yace aa mm nariga naci a gidan bb karami.

"tace au kace bayanxu ka'iso ba.

"murmushi kawai Mahfus yai snn sukaci gaba da hira, Mahfus ya kwashe duk abinda ake ciki ya sanarwa mmnshi.

"murna tai sosae amma kuma jikinta yai sanyi sbd yadda yabata labarin iyayen amatullah.

"gani yadda tai yasa Mahfus yace mm lpy?

"murmushi tai hade da cewa to Mahfus dole jikina yai sanyi kafi kowa sani kafi kowa sani halin da muke ciki bamu dawata kaddara da yau xamu daga musiyar duk karatunka ya cire sai dai gidan ga da yarage.

"kuma a yadda kake mgn yar'masu kudine kana gani xata'iya zama damu?

"murmushi Mahfus yai snn yace idan gun xamane babu matsala sbd haya xankama.

"da sauri tace haya Mahfus?

"Mahfus yace eh mm kinga bekamata daga yin aure tafara xama a nan ba.

"idan kudi kike tunani Allah xairufa asiri.

"hira sukai sosae hade da tattanawa yadda xasuyi.

"da safe yaje ya sanarwa kawonshi kani mmnshi.

"ana gobe xasuxo Mahfus ya dibi kudi ya bawa mmnshi taxaman siyayya Mahfus da kawo abu da bb karami suka biyo Mahfus xuwa nima masa auran amatullah.




H.S.Z.ceπŸ–Š
πŸŒΊπŸ’¦πŸŒΊ
πŸ’¦

Fasaha online writes F.o.w.

MMN USWAN
H.S.Z.

9

"su Mahfus suna isa dakinshi ya kaisu saida sukayi sallah snn ya dibo masu abinci.

"dama tun suna hanya Mahfus yaiwa adam da suke daki daya waya da cewa yai masu abinci, gasunan a hanya.

"shiyasa kafin su iso adam yagama abincin.

"suna idar da sallah Mahfus da adam suka kawo masu abinci.

"bayan sun fara cine adam da Mahfus suka fita waje sbd suyi mgn, bayan sun fitane Mahfus yake cewa adam to adam ya kake gani za'ayi?

"adam yace abinda yafi kawai kiranshi xakai ka sanar masa cewa ga iyayen naka su iso, da wani lokacin zamuzo mu sameshi?

"Mahfus yace ko?

"idan na kiranshi ta waya na sanar masa ba xaixama rainin wayo bako?

"kasan manyan mutani sai a hankali abu kadan xakai kai kuskure.

"adam yace babu komai kiranshi ma yanxu.

"Mahfus yace yanxu fa kace?

"adam yace eh mana.

"fisge wayar Mahfus adam yai hade da searching number alhji Ibrahim yana gani dealing number yai, alhji na dagawa adam yabawa Mahfus wayar.

"cikin girmamawa Mahfus ya gaida alhji Ibrahim snn yace dama na kirane na sanar dakai cewa ga iyayena din sunzo.

"da sauri alhji Ibrahim yace madalla abu yai kyau, ina masu snn da xuwa.

"murmushi Mahfus yai snn yace suna amsawa hade da cewa alhji da wani lokaci ne xasuxo su sameka?

"alhji Ibrahim yace idan nine ko yanxu xasu iya xuwa.

"murmushi Mahfus yai hade da cewa alhji idan sukaxo da safe fa yayi?

"alhji yace Allah ya kaimu, sai kunzo.

"Mahfus yace to alhji nagode sosae Allah ya kara girma.

"alhji yace amin.

"snn sukai sallama.

"Mahfus yana koshe wayar da sauri ya juya suka hada ido da adam, adam yace kagani ko.

"Mahfus yace wlh kuwa.

"zama sukai suna tattana yadda zasuyi, suna cikin hada saiga kiran amatullah ya shigo.

"gani number amatullah ne yasa Mahfus receiving call din da sauri hade da cewa hello my baby.

"wani dadi ne yakama amatullah sbd jin muryar abin kaunar ta, shiru kawai tai tana sauraron baitocin da Mahfus yake rera mata.

"jin shiru da tai yasa Mahfus yace hello my baby kina jina kuwa?

"amatullah tace ina raurarenka.

"saida yagama jera mata baiti snn yace my baby albishirinki.

"amatullah tace goro.

"Mahfus yace nakawo su bbna, yanxu da haka ma suna daki suna cin abinci.

"amatullah tace da gaske?

"Mahfus yace wlh kuwa, harma nai waya da alhji Ibrahim yace gobe mutafi yana jiranmu da safe.

"amatullah tace Allah ya kaimu.

"nan sukaci gaba da suransu,adam ne ya katsesu da cewa sukoma daki maybe su bba sun gama.

"Mahfus ya kashe wayar suka shiga cikin daki, su bba har sugama hira kawai sukeyi.

"su Mahfus suma zama sukai sukaci gaba da hira.

"da safe bayan su karya duk sukai wanka duk suka shirya snn Mahfus yakira alhji Ibrahim yake tambayar shi ina ne xasuje?

"shine alhji Ibrahim yace su hadu a gidan su alhji Muhammad.

"suna gama mgn da Mahfus ya kira alhji Muhammad ya sanar masa ya nanan xuwa amma sanar masa da iyayen Mahfus xasuxo ba.

"suna gama mgn alhji Ibrahim ya shirya sai gidan su alhji Muhammad, sbd yasan idan har be igasu xuwa sune suka rigashi xuwa gidan ba lailai bane alhji Muhammad ya barsu su shiga gidan.

"be dade da isa ba saiga su Mahfus da iyayen sa harda adam, a parlour akai masu ma sauki bayan su gaisa ne alhji Ibrahim yake sanarwa alhji Muhammad ga iyayen Mahfus sun isa.

"saida suka sake gaisawa snn alhji Muhammad yacewa alhji Ibrahim kaine da mgn ai.

"nan alhji Ibrahim yace ina fatan yaronku ya sheda maku dalilin niman da muke maku ko?

"duk sukace kwarai da gaske.

"sai yace dama d'anku ne yaga yarinyar guna yake so, shiyasa nace idan har da gaske yakeyi yaturo manyanshi asan inda aka tsaya.

"suka eh duk yai mana bayani.

"alhji Ibrahim yace alhamdllh.

"snn ya juya kallonsa gun alhji Muhammad suka hada ido.

"a lokacin ne alhji Muhammad yace tunda har su riga susan da mgnr me za'a jira ko yanxu ma za'a iya daura auren ya dauke ta sutafi.

"murmushi kawai alhji Ibrahim yai snn yace baza'ai haka ba, anan suka shirya aka yanke masa sadaki hade da sa ranar nan da wata uku me xuwa.

"godiya sukai sosae snn sukai sallama daga nan basu tsaya ko'ina ba sai tashar mota saida ya sasu a mota hade da biya masu kudin motar, mota na tashi suka juyo kai xuwa gida.

"bayan su Mahfus sun fita ne alhji Ibrahim da yya khamis suke kara tattanawa yadda za'a tsara bikin, shiko alhji Muhammad idan ya tanka kasa ya tanka har suka kare mgnr su besa bakin ba.

"bayan su gama mgn ne alhji Ibrahim yamike zai fita sai alhji Muhammad yace dan Allah idan ka'isa gida kace inaso gani kamarudee.

"cikin wasa alhji Ibrahim yace baza'a fadi ba, waye d'an aikenka?

"ashe babu dadi ina mgn akan yar'ta amma kokasa baki.

"da sauri alhji Muhammad yace au tanan kafito Allah ya baka hakuri.

"duk sukasa dariya harda yya khamis dake gun saida yai dariya.

"snn alhji Muhammad yace kabari ma kawai xantura yynshi ya kira minshi.

"cikin wasa alhji Ibrahim yace da dai yafi maka.

"duk sukasa dariya hade da tafawa.

"bayan alhji Ibrahim ya fita sai alhji Muhammad yacewa yya khamis yabashi number kamarudee, a take agun yana amsa ya kira.

"kamarudee yana gani number alhji Muhammad da sauri ya daga cikin girmamawa d ya gaidashi bayan su gaisa ne alhji Muhammad yace yanaso ganishi.

"kamarudee yace in Allah ya yarda da yamma zanxo.

"alhji yace Allah yasa mikai.

"su Mahfus suna isa gida yakira mmnshi ya sheda mata duk yadda aikai hade da mgnr sa rana.

"nan dai sukai ta tattana yadda za'ayi.

"suna gama mgn ya kira abokinshi nasir ya sanar dashi duk abinda ake ciki hade da mgnr sa rana.

"nasir yace babu damuwa xaisamu sauran abokansu ya sanar dasu duk abinda ake ciki.

"nasir abokin Mahfus ne tun suna yara tare suka taso, saidai basuyi makaranta daya da Mahfus ba sakamakon shi nasir iyayensa masu haline shiyasa yai pravent school amma kuma duk da haka besa abotansu ya rabuba.

"kuma yana tai makawa Mahfus sosae babu me jin kansu.

"da yamma bayan sallar isha kamarudee yaje gidan su alhji Muhammad, yana isa ya samesu duk suna zaune a parlour amma banda amatullah.

"bayan su gaisa ne alhji Muhammad yake tambayar kamarudee har yanxu besamu yarinyar da tai masa bane?

"sai kamarudee yace yasamu amma besanar da iyayen taba sbd tana zana exma din kammala secondary ne shiyasa.

"amma din ta kare sai natura manyana.

"alhji Muhammad yace aa ba haka za'ai ba, gara muje akan lokaci sbd kada wani ya rigamu.

"yace kasanar dani yar'gidan waye? kuma aina ne gidansu yake?

"kamarudee yace yar'gidan tsohon d'an majalisan taraiyane, dake zaune a (Bosso Lowcost).

"alhji yace babu damuwa idan Allah ya kaimu gobe da safe kazo muje gidan.

"kamarudee yace Allah yasa mukai.

"nan sukai sallama.

"washe gari da safe misalin karfe goma na safe kamarudee ya shirya cikin shiga ta alfarma yaxo daukar alhji Muhammad.

"alhji Muhammad shima haka yai nashi shigan abin sai wanda yagani, abba yace kamarudee yaxo sutafi a nashi motar ne.

"kamarudee da abba suna baya direba yana jansu.

"a hankali suke tafiya ga sanyi A.C dake dukansu turarewa kamar wanda aikai bari a jikinsu.

"suna isa security dake gadin gidan yaki budewa, karamin card abba yacire daga aljihunshi yabawa security din ya kaiwa alhjin ciki.

"ana kai masa ya karanta yace maza aje a bude masu gate, duk da besan su waye ba amma yasan ba kananan mutane bane.

"suna shiga da kanshi yafito yai masu iso xuwa parlour.

"suna shiga suka gaisa snn masu aiki suka kawo masu su fruit hade da su abinci da ruwan sanyi.

"kadan kawai sukaci sbd karma ace basuci bane.

"snn suka sake gaisawa, alhji tasi'u yace alhji bangane kaba.

"murmushi yai snn yace eh balailai bane ka ganeni sbd yai ne farkon haduwarmu, yaro nane yaga yar'ka na'ima yakeso kaji dalili xuwanmu.

"murmushi alhji tasi'u yai snn yace gaskiya a yadda naso nafiso sai tai karatu sosae snn tai aure.

"abba yace idan karatu ne nayi maka alkairi bayan aure ni da kaina zansaman mata makaranta taci gaba da karatu.

"shiru alhji tasi'u yai snn yace to yanxu ya kakeso aiyi?

"murmushi abba snn yace alhji duk yadda kai daidai ne.

"murmushi shima yai snn yace yanxu kamar wani lokacin kukeso?

"abba yace idan d'an mune ko yau akabamu so muke sbd a shirye muke.

"alhji yace shikenan yanxu abar takare exma sauran mata paper two takare idan takare da sati daya sai a daura masu auren ko beyiba?

"abba yace zaikai kamar wata nawa kenan?

"alhji yace wata daya kenan.

"abba yace madalla mugode sosae Allah yabar zumunci.

"anan kasa masu kudin sadaki atake abba yabiya komai.

"snn sukai sallama.

"gidan alhji Ibrahim suka nufa direct alhji Muhammad ya zaiyanawa alhji Ibrahim duk yadda sukai.

"godiya alhji Ibrahim yai sosae hade da cewa watodai kanaso d'anka ya riga yar'ta kenan.

"duk sukasa dariya.

"sun jima suna hira snn alhji Muhammad yaje gida.

"da yamma bayan sun gama cin abinci ne alhji Muhammad yake zaiyanawa su hajiya da yya khamis abinda ake ciki.

"duk murna sukai hade da fatan alkairi.

"itako amatullah ko ta tanka, karshenta ma tashi tai tabar gun.

"gani haka hajiya ta bita har dakin ta hauta da fada inda take shiga banan take fita ba.

"sauran sati biyu bikin kamarudee alhji Muhammad ya aiki yya khamis DUBAI siyayyan kayan lefen kamarudee.




H.S.Z.ceπŸ–Š
πŸŒΊπŸ’¦πŸŒΊ
πŸ’¦

MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)πŸ’¦

Fasaha online writes F.o.w.

MMN USWAN
H.S.Z.

10

"kwana biyu da tafiyar yya khamis DUBAI yadawo kaya kam sai son barka abin ba'a cewa komai.

"washe da dawowar yya khamis hajiya mmn su amatullah da kawayen mmn kamarudee suka kai kayan lefe gidan su na'ima.

"duk wanda sukaga kaya basu cewa komai sai san barka.

"hakan yasa aka basu tukwici me yawa.

"Mahfus kuwa sai faman shirya2 yakeyi gashi saura sati yakare service dinshi, yanxu haka shirin komawa kano yakeyi.

"ana saura kwana uku bikin kamarudee Mahfus yaxo sallamar amatullah zai kama kano.

"amatullah najin haka tasa kuka tana fadin yanxu tafiya xakai kabarni?

"gani babu wanda ke ganisu yasa Mahfus rungumarta yana fadin please stop crying my baby kwata2 kwana nawa yarage mu kasance tare na har abada?

"dan Allah kidaina kuka kinji amatullah.

"amatullah tace to idan katafi bayan kwana biyu zakaxo?

"Mahfus yace haba amatullah ki tausayamin mana bakisan ba'aso ango yarinka yawo akan hanya sbd tsautsayi ba.

"kidaiyi hakuri kinji my amatullah.

"gani taci gaba da kuka hannu yasa yana goge mata hawaye hade da kissing dinta.

"gani yadda yake kissing d'inta kamai xai cinyota a take taji wani iri yana yinta yafara canxawa da sauri ta fisge jikinta daga nashi.

"shima kanshi Mahfus din haka yaji amma sai yamatse hade da cewa ya dai?

"kai kawai ta girgiza.

"Mahfus na rike da hannunt yace ni xantafi sbd banaso nayi tafiyar dare.

"shiru amatullah tai tana kallonshi.

"Mahfus yace haba amatullah kiji mgn mana.

"amatullah sai hawaye.

"Mahfus sake rungumeta yai yana yimata rada a kunni har saida tasaki jiki tai dariya snn Mahfus yace baby xantafi.

"amatullah tace to Mahfus Allah ya kaika lpy.

"Mahfus yace yauwa matata kokefa.

"murmushi kawai amatullah tai.

"cikin gida ta koma ta dauko hijab dinta wanda ya sauka mata har kasa snn tadawo, tana fitowa tace suje.

"da sauri Mahfus yace muje ina?

"murmushi tai snn tace rakiya ne xanyi maka.

"Mahfus yace aa kikoma kawai kada ai maki fada.

"da sauri amatullah tace babu damuwa mutafi kawai.

"Mahfus yace idan abba ya ganki fa, mexaki ce masa?

"amatullah wlh banaso kijawo abinda za'ai maki fada.

"murmushi tasake yi snn tace babu matsala tunda kai ne.

"Mahfus yace to shikenan mutafi.

"haka suka fita suna tafe suna hira har saida suka kusa barin layinsu snn Mahfus yace ya'isa haka tsayawa sukai suna sallama, mani Mahfus xaitafi amatullah tasake sa wani kuka.

"dole yasa Mahfus tsayuwa yana rarrashinta har saida tai shiru snn yace xaitafi, har Mahfus yajuya xaitafi komai ya tuno oho dawowa yai yace muje nakai ki gida.

"batare da musuba amatullah ta juya har kofan gida ya kaita kuma saida ya tabbata tashiga ciki snn shima ya dauki hanya.

"batare da bata lokaci ba yana isa gida jakarsa ya dauka xuwa tasha.

"adam ne yai masa rakiya har tasha saida adam yaga tashin su Mahfus snn yajuyo xuwa gida.

"sun rabune akan shima gobe xaitafi garinsu gwambe sai kuma idan Allah yasa yasamu xuwa biki.

"gidan su amarya na'ima biki akeyi gadan gadan yau ake arabiya day gobe kuma akwai kumbo jibi kuma sai walima washe gari kuma daura aure.

"gidan su amatullah tamkar nan ne gidan ango sbd komai anan akai yar'uwa da abokan arxiki anata shirin xuwa arabiya day kowa ya shirya cikin shiga ta alfarma amma banda amatullah babu yadda ba'ai da'ita ba amatullah taki tafiya dole yasa suka kyaleta.

"dakinta ta shige hade da daukar alkur'aninta taci gaba da karartawa.

"kamarudee ansha kyau duk da janlabiya yasa amma saida yai kyau.

"kudi kuwa ankasheta ne kamar ba'a sonta.

"Mahfus yana isa gida ya kira amatullah ya sanar da'ita.

"hira sukai sosae har saida kudin su duk yakare snn suka koma chatng su Mahfus basu kwanta ba sai misalin karfe uku na dare.

"misalin karfe goma na safe ne aka daura auren kamarudee da na'ima.

"da yamma aka kai amarya gadan ta dake G.R.A. alhji Muhammad ne ya basu gidan kusa dana yya khamis su xauna.

"alhji tasi'u ya hana kowa kwana a gidan amarya daga ita sai mijinta kamarudee.

"bayan kowa su watse aka rako ango dakinshi.

"abokai kowa yai irin nashi jawabi bayan sun kare kamarudee yaje ya rufe gida snn yadawo amatullah na zaune kan gado kanta na lulube da mayafi.

"saida yai mata sallama sau uku gani shirun da tai ne yasashi hayewa kan gadon hannu yasa ya bude mayafin dake kanta na'ima na ganin hakan da sauri tasa hannu tarufe fuskanta.

"murmushi kawai kamarudee yai snn yace haba amarya yata menene haka kuma?

"ninefa kamarudee angonki dan Allah ki budemi kyankyawar fuskarki na gani mana ko nasamu natsiwa.

"hannu yasa a hankali yake bude mata fuska yace xomuje muyi sallah ko? mununawa ubangiji godiyar mu.

"yana rike da hannunt suka shiga toilet suna shiga buta ya dauka ya mika mata tai alwala.

"bayan ta amsa gefe ya koma yana kallonta har saida takare snn shima yai nashi.

"bedroom suka dawo kamarudee ya jasu sallah raka'a biyu, suna idarwa kamarudee ya dora hannu akanta yafara addu'a ya jima yanayi snn suka shafa.

"duk tambayoyin da yai mata akan tsarki da sallah na'ima tabashi amsarsu.

"snn kamarudee ya jawo ledar kaza da juice ware ledar yai ya'ije mata agaba yace bismilh.

"da sauri na'ima tace aa nakoshi.

"murmushi kamarudee yai hannu yasa ya dibo har yakai mata baki da sauri ta kauda bakinta.

"gani haka yasa jikinshi yin sanyi juice bakwai ya diba yasha snn itama ya bata yace tasha koda kadan ne.

"Amsa tai tasha kadan snn ta'ije cup din a gefe.

"mikewa kamarudee yai hade da cemata ta tashi ga kayan bccn tasa.

"daukar nashi yai yakoma dakinshi ya canxa kaya snn yadawo ko kafin yadawo tariga ta canxa kaya gado ta hau ta kwanta.

"kamarudee na gani haka yana shigowa ya kashe light ya haye gadon shima.

"a hankali ya matso inda take na'ima najin ana shafeta ihu tasa hade da cewa na shiga uku.

"da sauri kamarudee yasa bakinshi a nata ya toshe mata nata bakin hade da hayewa kanta.😜

"cikin daren kamarudee ya wanke na'ima ya meda'ita cikankiyar mace.




H.S.Z.ceπŸ–Š
πŸŒΊπŸ’¦πŸŒΊ
πŸ’¦

MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)πŸ’¦

Fasaha online writes F.o.w.

MMN USWAN
H.S.Z.

12

"motar su nasir ne a gaba sai nasu kani bbn Mahfus na baya kuma sauran yar'uwa ne a ciki.

"suna tafiya ne suna biye da juna karfe tara suka isa kofar gidan su amatullah.

"parking sukai a gefe nasir da Mahfus suka koma gefe snn Mahfus ya kira alhji Ibrahim yake tambayarsa a ina ne za'a daura auren?

"alhji yace har kun iso ne?

"Mahfus yace eh.

"alhji yace su jiranshi a kofar gidan su amatullah.

"Mahfus yace to.

"alhji bekai minti goma ba ya'iso.

"har kasa su Mahfus da su nasir suka duka suka gaidashi.

"hannu alhji ya mika masu duk suka gaigaisa snn yai masu iso xuwa gunda za'a daura auren.

"yar'uwan Mahfus sai faman kallon gidan sukeyi hade da mmkin ta yaya akai Mahfus ya hadu da yar'manyan mutani haka?

"yarinyar da tasha tai wanka da naira.

"shiko ba d'an kowa ba, wanda dakar ake samu nacin yau na gobe sai Allah yakawo amma har ta yarda xata aureshi.

"lailai kab akwai lauje cikin nadi.

"manya manyan tabarma aka shinfida malaman da xasu daura auren duk su hanlara amma banda alhji Muhammad.

"gani alhji Muhammad be fitoba yasa alhji Ibrahim binshi har dakinshi, koda yashiga samunshi yai zaune kan cushion.

"cikin fushi alhji Ibrahim yake mgn hade da cewa haba alhji meyasa kake abu kamar ba musulmi ba?

"meyasa a rayuwa baxaka yarda da kaddara ba?

"dolene abinda kakeso a rayuwa kace saika samu?

"alhji kada kabari rabo yakashe ka bakasan abinda Allah yake nufi da wnn auren ba.

"gani beda ninyar tashi yasashi cewa alhji ko xakai jayayya da ubangiji ne?

"da sauri alhji yace aa.

"alhji Ibrahim yace to katashi mutafi.

"sashi a gaba alhji Ibrahim yai suka nufi gun daurin auren.

"suna isa gun suka xauxauna aka fara daurin daure,

"tunda alhji Muhammad yanufo suka hada ido da Mahfus, gaban Mahfus yake ta fadi.

"hankalin Mahfus be kwanta ba saida yaji an shafa snn yai ajiyar zuciya.

"ana shafawa alhji Muhammad yamike ya koma ciki, ko tsayawa a gaisa beyiba.

"alhji Ibrahim ne da su yya khamis yya Abdul da kamarudee sune suka kula bakin da sukaxo daura aure.

"hira sosae kamarudee da Mahfus harda nasir sukai kamar dama sun taba sani juna.

"karfe biyu alhji Ibrahim yace a fito da amatullah sutafi sbd kada suyi tafiyar dare.

"hajiya mmn kamarudee ne tashiga dakin da amatullah take takamo mata hannu xuwa dakin da abba yake, lokacin yana tare da hajiya.

"har kasa ta duka a gaban su hajiya kanta na kasa.

"hajiya tace to alhji ga amatullah taxo kuyi sallama yau za'a kaita dakin mijinta.

"jin haka yasa amatullah fashewa da kuka.

"alhji ko kallon inda amatullah take beyiba mikewa yai xaifita yabar masu dakin.

"da sauri amatullah ta rike masa kafa tana fadin dan Allah abba kayi hakuri ka yafemin dan Allah abba.

"kukan da takeyi ne yasa mmnta fashewa da kuka.

"da karfi abba ya fisge kafarsa ya fice daga gidan.

"hajiya mmn Abdul na gani haka da sauri takira mijinta ta sanar dashi ga alhji yafita be tsaya suyi sallama da amatullah ba.

"abba yana fita hanyar fadukwoi ya dauka direct yana gudu kamar wanda xaibar kasan.

"yya Abdul ne ya

Please Login or Register in order to submit comment