Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sallama.

"harkan gado tahau a hankali take mgn hade da shafe masa gefen fuskanta.

"a hankali Mahfus yake juyowa hade da bude idonsa.

"gani amatullah yai a gabansa tasha kwalliya duk da ba shafe2 tai ba amma saida tai kyau.

"amatullah tai kwalliya ne cikin English wear, hannu Mahfus yasa ya jawota jikinsa yana shafeta hade da cewa baby kinyi kyau fa.

"Murmushi amatullah tai tace nagode, kokarin xare jikinta tai hade da kamo masa tace baby tashi muje kai wanka.

"shiru Mahfus yai kamar beji abinda take fadi ba.

"Mahfus kara bin jikin amatullah yai ya kwanta hade da dora mata kanshi a kirjinta yanayi kamar mesha nono, duk da akwai riga a jikinta amma behanashi shafe taba da haka har yasamu ya binya bukatar sa snn mike itama tashi tai suka nufi toilet tare sukai wanka suna gamawa Mahfus yaje dakinsa ya shirya cikin English wear snn yafito dinner.

"itama wanka tasake yi batare da tatsaya wani kwalliya ba doguwar rigar jallabiyarta tasa hade da daura dankwalin da sauri tafito dinner ta hada masa brekf dinsa.

"yanaci suna hira har yagama, yana gamawa daki yanufa ya dauko jakarsa.

"zai fita kenan ruwan sama ya banlo kamar da bakin kwarya.

"dole yasa Mahfus dawowa parlour ya xauna yana jiran ruwa ya tsaya, gani har seven thirty yayi ruwa be tsaya ba yasa rai Mahfus yafara baci koda amatullah tai masa mgn ba sosae yake amsawa ba.

"gani takwas saura yasa Mahfus yace amatullah ta tasamu masa leda ya rufe kansa dashi, xaitafi haka.

"amatullah tace bakagani ruwa akeyi ne?

"Mahfus yace to ya xanyi amatullah kina gani lokaci na tafiya.

"mikewa amatullah tai batare da mgn ba, dakinta dakinta ta koma taje ta dauko key din motar ta snn tadawo.

"lokacin yariga ya mike ita yake jira ta dawo, tana dawowa tamika masa key din motar.

"da sauri Mahfus yace me xanyi dashi?

"amatullah tace karinka amfani dashi idan xaka aiki.

"amsa kawai yai yafita sbd yariga yai late cewa kawai yai baby idan na dawo xamuyi mgn.

"murmushi kawai tai hade da cewa adawo lpy, Allah ya tsare.

"Mahfus yace amin nagode.

"duk da ruwan da akeyi behana amatullah yiwa mijinta rakiya ba, rungumeshi tai, tai masa rakiya har bakin motar.

"har Mahfus xai shiga mota amatullah tace one minute please.

"tsayawa Mahfus yai yana kallonta.

"wani irin runguma tai masa hade da d'an na masa yimasa hoon kiss.

"Mahfus najin yanayinsa yafara canxawa da sauri ya babbaro amatullah daga jikinshi yana cewa please my baby let me go, kinga nayi lete ko.

"murmushi amatullah tai hade da daga masa hannu, amatullah bata koma ciki ba saida taga tafiyar mijinta snn takoma ciki.

" Mahfus yana dawowa ya dauki key din mota ya medawa amatullah.

"kin amsa tai sai tace karike mana.

"kyaleta yai be tanka mana ba ya meda cikin aljihunsa.


"saida yabari dare yayi misalin karfe goma na dare har amatullah ta tafara bcc sai Mahfus yace ta tashi xasuyi mgn.

"da kar ta'iya mashi sbd bata dade da kwanciya ba.

"dole yasa ta tashi zaune sai Mahfus yace amatullah meyasa kikaki amsar key din motar?

"murmushi kawai amatullah tai snn tace babu komai.

"Mahfus yace mgn nakeso kiyi ba murmushi ba.

"cikin ido bcc amatullah tace haba Mahfus menene a cikin mota dani da motar duk muta karkashi ikon kane fa.

"saida Mahfus ya gyara xama snn yace amatullah kenan meyasa baki gudun surutun mutane?

"da rauri amatullah tace wa nasani a garin kodama nasani ina ruwana da abinda mutane xasuce.

"murmushi Mahfus yai snn yace amatullah kenan hakama ya nakare da surutun mutane banle sungani da mota.

"Cewafa suke sbd kudine na aureki banle yanxu kuma suga ina fita da mota.

"mikewa amatullah tai tahaye jikinsa suna fuskantar juna hade da wasa da gemun dake habansa tana wasa dashi.

"tace Mahfus.

"Mahfus yace na'am.

"amatullah tace dan Allah dan annabi inaso a xaman takewar da xamuyi dakai,dan Allah inaso mu toshe kunnimu murabu da yar' kinji2 masu kanana mgn.

"idan har bamuyi haka ba tabbas aurenmu ba xaikai ko'ina ba.

"murmushi Mahfus yai snn yace haka ne amma kinsan halin mutani...

"da sauri amatullah tace ina ruwanka da mutani badai kana sona ina sonka ba?

"Mahfus yace haka ne.

"amatullah tace to banaso mgnr mutane ya daga maka hankali, fatana Allah yabaka ikon rike amanata da Allah yabaka...

"da sauri Mahfus yace amin amatullah.

" kamo gemosa tai tana kitsawa hade da ja masa dan taji abinda xaice.

" murmushi kawai yai ya kyaleta.

"da yaga batasan ido ba, hannu yasa ya kamo kan nononta ya murxa da sauri ta sakar masa gemo tana ihu.

"Shima Mahfus kin sakewa yai duk da ihu da takeyi.

"da taga bashida niyar sakewa sauka tai daga kansa tana kokarin gudu.

"kamo nonuwar Mahfus yai da karfi ya jawota jikinshi, amatullah ihu take sosae tana cewa da xafi kabari.

"gani ihun da takeyi alama xafi takeji da gaske jawota yai cikin bargo sukaci gaba da wasa.

"ranar wata asabar da yamma Mahfus yace amatullah tashirya xasu fita.

"amatullah tai murna sosae sbd tunda taxo garin bata taba fita ko'ina ba.

"cikin doki amatullah ta shirya cikin riga da sket, shikuma yai nashi shirin cikin wado da riga na shadda.

"bakarami kyau sukai ba, kyale amatullah ta yafa.

"Gani irin kyau da tai yasa Mahfus yace saida tasa hijab.

"babu yadda amatullah batai ba amma Mahfus yaki yarda,wani karamin hijab wanda be wuce yadi uku ba tasa.

"Mahfus yace bemasa ba, babba wanda yakai yadi uku da rabi ya ciro daga wadrop yace shine yakeso tasa.

"haka ta amsa tasa, tana sawa taga ya rufe mata duk jikinta har kasa yake ja amatullah tace bazata sashi ba.

"shiko Mahfus yace saida afasa xuwa uguwar.

"kan cushion takoma ta kwanta.

"da dai taga da gaske yakeyi xai tafi ya barta a guje tabishi, suka fita tare.

"dariya ne Mahfus yai hade da cewa na dauka kinfasa xuwa ne ai.

"banxa amatullah tai dashi taje ta samu gaban motar ta zauna.

"Mahfus na shiga mota kai tsaye gidan su nasir ya kaita, suna isa Mahfus yakira nasir ta waya.

"nasir na gani number Mahfus da sauri ya daga yana cewa ango mijin amarya.

"murmushi Mahfus yai snn yace kana gida ne?

"nasir yace ina gida ne, gani zaune da hajiya.

"Mahfus yace ok to gamu a kofar gida.

"da sauri nasir yamike hade da cewa wani kofar gidan?

"Mahfus yace kofar gidan Ku mana.

"fita nasir yai,yai masu iso zuwa ciki.

"parlour ya kaisu, suna shiga har kasa suka duka suka gaida hajiya mmn nasir.

"cikin mututawa da fara'arta ta amsa.

"mai aikin sune takawo masu abinda da lemu.

"dukkansu babu wanda yaci, a tunani hajiya kunyarta sukeji haka yasata barin gun.

"tana tafiya nasir da Mahfus suka kama hira.

"itako amatullah kallon gidan kawai takeyi sbd yanayin tsarin gidan iri daya da na gidansu.

"babbancin su kadan ne.

"kwalla suka cika mata ido, shiru tai tana faman tunni Kala2.

"gani shirun da amatullah tai ne yasa nasir cewa amarya yadai?

"kinyi shiru kamar baki a gun kodai mudameki da surutune?

"murmushi kawai amatullah tai kanta a kasa, gani hawaye zasu xubo mata da sauri tasa hijab ta goge hawayen.

"Mahfus ne kawai yalura da haka, mikewa yai hade da cewa nasir xamu tafi dama kwana biyu najika shiru ne yasa nace bari na duboka.

"dariya nasir yai snn yace kasan yanxu ba lokacin xuwa gidan ka bane sbdπŸ˜‹

"dariya Mahfus yai hade da kai masa nushi.

"da sauri nasir ya kauce, duk sukasa dariya.

"da sauri nasir yashiga ciki ya sanarwa hajiya.

"tare suka fita sukai sallama ta dauki 5000 tabawa amatullah.

"har kasa ta duka tai mata godiya, snn nasir yai rakiya har bakin mota.

"amatullah kafin ta shiga mota ta goge fuskanta tsaf kamar ba ita ba.

"suna fita Mahfus yake tambayar ta meya sameta?

"tace babu komai.

"babu irin tambayar da bemata amma taki fadi, haka yagaji ya kyaleta.

"nasir na komawa ciki hajiya take cewa itace matar abokin kadin?

"nasir yace eh wlh hajiya.

"Hajiya tace Allah sarki daga ganinta yar'babban gida ne.

"nasir yace wlh hajiya saima kinga family dinta.

"hajya tace Allah mai ikon dama haka Allah yake hadinsa, Allah yabashi ikon rike amana.

"nasir yace amin hajiya, nima addu'ar da nake tayi kenan.

"Mahfus gidan iyayensa suka nufa darect dakin mmnshi suka shiga har kasa amatullah ta duka ta gaida ta.

"da fara'arta ta amsa.

"Mahfus yasamu bakin gado ya xauna, itako amatullah kasa ta xauna.

"gani dakin babu ko ledar kasa yasa Mahfus cewa dawonan ki xauna mana.

"kai kawai ta kada masa.

"alama aa.

"shima Mahfus gaida innarsa yai snn sukaci gaba da hira, itako amatullah a sace take karewa dakin kallo,hade da kallon gadan da Mahfus ke zaune gado ne gado bono mai inches 12 ko katifar arxiki babu a gadon duk juyin da Mahfus yai sai gadon yai kara.

"da taga alamar sunaso suyi mgn na tsakani d'a da mahaifi yasata fita takoma dakin mmn junior.

"basu bar gidan ba sai misalin 11PM snn suka koma gida.

"jikin amatullah yai sanyi sosae, tunda suka shiga mota har suka koma gida amatullah ko kallon Mahfus batayi ba.

"yai mgn har yagaji da yaga batada niyar amsawa yasashi kyaleta.

"koda sukaxo kwanciya Mahfus yaso biyan bukatar sa amma bega ido ba, agun amatullah hakan yasa ya hakura.

"itama kanta tarasa me kemata dadi a duniya.

"da safe suna zaune a parlour tai recharge through bank yar'uwanta take ta kira daya bayan daya.

"duk wanda takira sai sun dade suna hira.

"maza da mata duk saida suka gaisa dasu.

"kallota kawai Mahfus yakeyi duk abinda takeyi be tanka mata ba.

"sbd kusan duk mgnr da sukeyi yana jinsu, duk wanda xata kira babu wanda xai tambayeshi.

"a karshene takira mmnta itama sun dade suna hira, har abba yashigo,

"gani yadda take fara'a yasa abba cewa dawa kike mgn ne haka?

"gu yasamu kusa da'ita ya xauna.

"hajiya tace nida amatullah ne, gata ku gaisa.

"da sauri abba yace aa basai mun gaisa ba, naki gaisuwar ma ya'isheta.

"jikin hajiya yai sanyi sosae kashe wayar tai batare da sallama ba.

"duk abinda sukeyi amatullah na jinsu harda Mahfus din dake zaune, kuka amatullah tasa hade da mikewa a guje taina dakinta.

"Kokafin Mahfus yaxo tasa key ta ciki ta rufe, Mahfus ya buga har yagaji haka ya hakura yakoma parlour.

"fadawa kan gado tai taci gaba da kuka, tai kuka har tagaji bcc ne ya dauke ta.

"koda ta tashi Mahfus be tambayeta ba sbd yariga yaji duk abinda yafaru, iya kaci maganganu yai mata masu kwantar da hankali.

"result din matar kamarudee yana fitowa cikin sa'a yai kyau, duk da cikin da take dashi behana abba nima mata makaranta ba.

"sbd yaiwa iyayenta alkawari hakan a makarantar da amatullah takare anan ne yasaman wa na'ima gwurbi.

"bada bata lokacin ba tafara xuwa lecture.

"drave abba ya samanwa na'ima shiyake kaita idan ta tashi yaje ya dauko ta.

"tunda daga lokacin hankalin amatullah ya tashi,shi kanshi Mahfus yakasa gane kan amatullah kullin cikin kuka take.

"hakan yasa ta yanke shawarar xuwa gani gida, babu yanda batai ba amma Mahfus yahana.

"acewarshi sai takai wata biyar snn taje gani gida, hakan yasa amatullah takara shiga damuwa sosae.

"gani yanda tashiga damuwa sosae cikin kankani lokacin amatullah duk tarame da kode, kamar ba'ita ba.

"duk da cikin da take dashi besa tarame haka ba.

"gani yadda tarame ta lalace yasa Mahfus cewa tabari idan tasamu salary karke tawa saitaje.

"amatullah tace idan dan kudine tanadashi.

"Hakan yasa ranar asabar suna sallar asuba suka dauki hanyan Niger.




H.S.Z.ceπŸ–Š
πŸŒΊπŸ’¦πŸŒΊ
πŸ’¦

MATAR FARI
( THE FIRST WIFE)πŸ’¦


Fasaha online writes F.o.w.


MMN USWAN
H.S.Z.

16

" su Mahfus basu isa Niger ba sai bayan axahar.

"suna isa gidan su amatullah taiwa gateman mgn ya bude.

"tun kafin Mahfus ya karisa parlour amatullah tafita a guje.

"Mahfus yana kiranta amma ina aguje tashige ciki.

"lokacin hajiya na zaune a parlour bata ankara ba ji kawai tai anfado mata a jiki.

"a tsorace tace waye?

"snn amatullah ta dago ido.

"amatullah murna harda kuka.

"da mmki hajiya tace amatullah lpy?

"tafiya bako sanarwa?

"amatullah bata tanka ba saima kara shigewa jikin mmnta da tai.

"hajiya tace kedawa kikaxo...

"kafin takarisa mgn saiga Mahfus yai sallama yashigo.

"hajya da murnarta ta amsa sallama hade da yimasa bismllh.

"har kasa Mahfus yaduka ya gaida hajiya snn ya xauna.

"hajiya tacewa amatullah tashi kije kitchen ki dibowa mijinki abinci.

"batare da musuba amatullah tamike taje ta dibo masa abinci da juice da ruwa, snn takawo masa.

"ruwa kawai Mahfus yasha snn yace xaitafi sallah.

"hajiya tasake cewa amatullah taje ta dibowa mijinta ruwa a buta.

"mikewa Mahfus yai yatafi waje yana jiranta.

"amatullah na dibowa ta kaimasa waje.

"Mahfus yana amsa alwala yai yashige masallaci.

"tunda amatullah tashigo gidan hajiya ke kallonta gani yadda amatullah duk tai sanyi sosae kamar ba'ita ba.

"duk abinda takeyi jiki a sanyaye takeyi.

"gashi duk takara fari ta fada.

"Mahfus yana shiga masallaci besake shigowa ba har saida yai sallar isha snn ya ciro waya daga aljihunshi yakira amatullah.

"tana gani number Mahfus da sauri tadaga hade da sallama.

"bayan ya amsa ne Mahfus yace abba yadawo ne?

"amatullah tace eh yana parlour.

"kashe wayar kawai yai hade da mikewa.

"koda Mahfus yanufi hanyar parlour yaji gabansa na fadi, kamar karya yaje.

"matsewa kawai yai yashiga da sallama har yace ina yini abba.

"lpy klau abba yace batare daya kalli Mahfus ba.

"Mahfus yace musameku lpy?

"shiru abba yai be tanka ba.

"yani haka Mahfus ya mike yabar parlour, yana fita hotel yanufa kai tsaye, yana xuwa yabiya kudin daki aka bashi key yana shiga daki yai mgn aka yomasa order abinci.

"yana faraci saiga kiran amatullah yashigo.

"Mahfus yana gani number amatullah ne da sauri ya daga.

"Amatullah najin ya daga tace hello Mahfus kana ina?

"murmushi kawai yai snn yace yah aikai ne?

"amatullah tace dama abinci ne.

"Mahfus yace kibarshi kawai.

"amatullah tace banga ne ba?

"yanxu dai kana ina sai nabiyoka..

"da sauri Mahfus yace kibiyoni ina?

"ki kwanta kawai saida safe.

"kafin tasake mgn Mahfus yakashe wayar.

"shiru amatullah tai tana kallon wayar.

"gani haka hajiya tace lpy?

"amatullah ta xaiyana mata yadda sukai da Mahfus.

"shiru tai snn tace Allah ya kyau ta.

"jin muryan su abba a parlour yasa hajiya tacewa amatullah taxo suje parlour.

"zama sukai anata hira, harda yazed kani amatullah.

"itadai amatullah shiru tai tana kallansu.

"saidai idan anyi abin dariya tayi murmushi.

"me amatullah tagani oho mikewa tai tabar gun daki takoma ta kwanta amma ba bcc takeyi ba.

"shima Mahfus kwanciya yai yana tunani irin amsawar gaisuwar da abba yai masa.

"sai faman juyi yakeyi akan gado.

"da hajiya taji shiru amatullah bata fitoba mikewa tai tabita dakin.

"ganinta tai kwance ta kwashi hannayeta ta xuba a kirjinta da alama tunani takeyi.

"hajiya ne ta tadata hade da tambayarta lpy?

"murmushi kawai amatullah tai hade da cewa babu komai.

"zama hajiya tai kusa da'ita a hankali take janta da hira har tasaki jiki sukayi hira sosae.

"basu kwanta ba sai 1AM snn suka kwanta.

"karfe biyan asuba saiga kiran Mahfus hajiya ne ta falka gani number Mahfus ne yasa ta tada amatullah hade da mika mata wayar.

"amatullah na karba Mahfus yace tashi kiyi sallah.

"to kawai tace snn tamike.

"da safe amatullah ta hadawa Mahfus abin karyawa.

"shiru2 bata ganshiba waya ta dauka tanata niman number amma yaki shiga.

"Mahfus bexoba sai kusan shabiyu snn yaxo, koda yashigo gidan a bakin gate yatsaya snn yakira amatullah ta waya.

"tana dagawa yace kifita gani a kofar gida.

"dama lokacin tana parlour ne fita kawai tai batare da daukar mayafiba tafita.

"Mahfus yana ganinta haka daure fuska yai snn yace koma kisa hijab.

"tanaso tai mgn, Mahfus yai mata wani mugun kallo da sauri takoma ta dauko hijab tasa snn tadawo.

"suka shigo parlour tare, yana shiga amatullah tace bari nakawo maka abin karyawa.

"Mahfus yace kibarshi nakoshi.

"Mahfus yace xuwa nai muyi sallama tafiya xanyi.

"hannu yasa acikin aljihunsa ya ciro key din mota ya mika mata hade da mikewa.

amatullah tace idan kabar motan anan kaikuma da wanne xaka koma?

"Mahfus yace xanbi na kasuwa.

"meda masa key din tai amma Mahfus yaki amsa, babu yadda batai ba amma yaki haka tagaji ta rike key din.

"Mahfus yace nina tafi..

"da sauri amatullah tace yaushe xaka dawo?

"murmushi Mahfus yai snn yace bayan sati biyu xanxo na daukeki.

"cikin shagwaba tace sati biyu fa kace ina laifin uku.

"murmushi yai snn yace sati biyun ma daurewa kawai xanyi my amatullah.

"jawota yai ya rungumeta hade da yimata rada a kunni.

"dukkansu dariya sukasa hade da yimata kiss snn yace xantafi dan Allah kikulami da kanki da kuma baby mu.

"hannu tasa tarufe fuskanta alamar kunya.

"cire mata hannu yai snn yarike yace muje kimin rakiya.

"saida sukakai bakin kofar parlour snn yace koma haka nagode.

"gani xaifita amatullah tasake rungumarsa, shima rungumarta yai saida sukakai kusan five minutes a haka snn Mahfus yaxare jikinsa yace tawa natafi.

"hannu amatullah ta daga masa tana masa bye bye har saida yashige snn takoma ciki.

"duk abinda sukeyi basusan hajiya na kallansu ba murmushi kawai tai hade da girgixa kai.

"Kamar ciwo yana jiran Mahfus yatafi, cikin dare amatullah sai amai hade da xanxabi mai karfi.

"sbd amai amatullah bata iya tashi. saidai idan tai hajiya taxubar.

"da hajiya taga haka cikin daren ta sanarwa abba halin da amatullah ke ciki.

"mikewa yai sukaxo tare da hajiya gani yadda takeyi yasashi tambayar dama batada lpy ne?

"hajiya tace lpy klau sukaxo.

"abba yace to sutashi atafi asibiti.

"cikin dare suka nufi asibiti, suna shiga aka bata taimakon gaggawa ruwa aka samata nurse din tasa babban number sbd yai sauri.

"koda sukai mata test ciki suka gani na wata daya da kwanaki.

"cikin murna da doki hajiya tace alhji kaga rabo ko?

"wani irin mugun kallo yai mata, haka yasa takasa karisa mgnr.

"tunda abba yabar asibiti bedawo ba, su hajiyan Abdul da motarsa dana kamarudee duk suxo sun gaida maijiki.

"kwanan amatullah uku aka sallameta suka dawo gida.

"da dare bayan sallar isha abba yaje dakin hajiya yasamesu suna hira, ita amatullah tana kwance a kafar hajiya.

"abba yace ya jikin naki?

"tace da sauki.

"sai abba yace dama gani gida kikazo, kuma kinga gidan ya'isa haka inaso ki sanarwa mijinki yau dinnan gobe yaxo ya daukeki.

"amatullah sai kuka tana fadin Allah abba kayi hakuri sati biyu yace naji.

"wani irin tsawa abba ya daka mata hade da cewa maza kikirashi yanxu ki sanar dashi.

"amatullah na kuka ta dauki waya ta kirashi.

"jin yace hello da sauri abba ya kwace wayar.

"Mahfus yajin muryan abba da sauri yace abba ina yini.

"lpy klau yace snn yace gobe kaxo ka dauki matarka idan kuma bakaxo ba to wlh koranta xanyi saidai tasamu wani gun ta xauna amma ba nan ba snn yakashe wayar.

"jikin Mahfus yai sanyi sosae.

"itako amatullah inba kukaba babu abinda takeyi hajiya tai lailashi har tagaji.

"bayan 30 minutes Mahfus yakira, amatullah na daga wayar tasa kuka Mahfus yace ya'isa haka gobe in Allah ya kaimu inanan xuwa na daukeki dan Allah kidaina kuka haka.

maganganu masu kwantar da hankali Mahfus yaita fadiwa amatullah har saida ta numfasa.

"da safe Mahfus yana idar da sallar asuba ya dauko hanya, kafin gomn safe Mahfus ya'isa gidan su amatullah.

"ko kafin ya'isa hajiya tariga ta hada mata kaya tsaf Mahfus yana shiga suka gaisa da hade da cewa ina abba?

"hajiya tace tunda yafita da safe bedawo ba.

"shiru Mahfus yai sbd yasan sbd shine abba yaki dawowa gidan.

" sai Mahfus yace amatullah tafito sutafi.

"hajiya ta dauko mata jaka tamikawa Mahfus, Mahfus yana amsa yarikewa amatullah hannu xuwa mota.

"amatullah kuka take sosae Mahfus ya duka ya sallami hajiya snn yashiga mota yaja suka dauki hanya.

"cikin fushi Mahfus ke tuki gudu yake xubawa kamar mahaukaci.

"yana draving yana tambayar kanshi meyaiwa bbn amatullah daya tsaneshi haka.

"yasan sbd shine yasashi Koran amatullah.




H.S.Z.ceπŸ–Š
πŸŒΊπŸ’¦πŸŒΊ
πŸ’¦

MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)πŸ’¦

Fasaha online writes F.o.w.

MMN USWAN
H.S.Z.

18

"Mahfus na rike da hannu Zainab yana janta.

"ita ko kokari take ta kwace takoma ciki, tana fadi dan Allah yya kabarni da'ita shegiya mara mutunci.

"tsawa Mahfus yaiwa zainab daga bata sake mgn ba.

"har bakin titi ya kaita ya damu mata napap tatafi snn yadawo.

"dakinshi ya shiga yanasa kaya sbd dama daga wanka yafito beriga ya shirya ba.

"duk a lokacin Anty Frd bata daina bala'i ba.

"cikin kayan data dikawa amatullah taciro wata shadda bugun senigal wanda tasha aiki tabawa amatullah tasa.

"kin amsa tai tana kuka ta duka ta dauki wanda Mahfus ya dinka mata ta kakkabe xatasa.

"fisgewa Anty Frd tasake tana fadi yaushe kika lalace haka amatullah yanxu har wani banxa yafimu duk abinda nakeyi sbd kecefa shine xaki watsami kasa a ido wata Mahfus yafini kenan ko?

"banxa amatullah tai da'ita.

"Anty Frd tace to wlh idan yamiki asiri ya kamaki, ni be'isa ya kamani ba.

"kuma wlh in har kisan wnn kayan saidai in nabar gidan nan.

"shegiya mara zuciya wanda zata kari rayuwa cikin wahala, kedai Allah ya dauke miki amatullah bansan uban da kika gani ajikin Mahfus da har kika makale masa ba.

"to wlh bari kiji dagake harshi baku isheni yiba.

"juyowa Anty Frd tai gun matan yya khamis tana cewa ashedai abba yai gaskiya daya ce sisishi bazaiyi ciwon kaiba akan shegiya yarinya nan, har muna gani laifinsa.

"wlh daga yanxu na daina gani laifinsa kuma idan nakoma duk yadda mukai saina sanar masa.

"rai Mahfus yabaci sosae, kiran mmn junior yai tawaya.

"tana xuwa yace takira masa amatullah yana nan yana jiranta.

"Mmn junior tana shiga dakin amatullah Anty Frd tadibeta daga sama har kasa ta xubar.

"a tunani Anty Frd itama yar'uwan Mahfus ne.

"itako bedameta gun amatullah taje tace Mahfus yana kiranki.

"da sauri amatullah tamike suka fita tare.

"Anty Frd tace dan Allah dubi yar'wahala har wani rawan jiki takeyi akan namiji.

"murmushi matan yya khamis tai hade da cewa kyaleta kawai dan batasan waye na miji bane shiyasa.

"duk Mahfus yana jinsu kawai ya kada.

"da sallama amatullah tashiga duk ido'ta ya dirje sbd kuka.

"suna hada ido da Mahfus tasake xubo da wani hawayen.

"da sauri Mahfus ya rungumeta yana fadin menene abin kuka kuma.

"dan Allah kibar kuka haka, hannu yasa yana goge mata hawaye hade da cewa is ok my baby.

"murmushi kawai tai sbd yanda yake mata kamar wata karamar yarinya.

"saida yaga ta daina kuka snn yace amatullah.

"kai tadaga tana kallon sa.

"Mahfus yace dan Allah kije ki amshi kayanda Anty Frd takawo miki kisa....

"da sauri amatullah tace amma.....

"Mahfus yace amma me? idan har kina sona da gaske ne, kuma na'isa dake kije kisa kinjiko?

"kai kawai ta daga masa, Mahfus yace yauwa ko kefa.

" Mahfus yace ina kika ijemi yarona?

"murmushi amatullah tai snn tace yana gun Anty Frd ko na naso shine?

"da sauri Mahfus yace aa kibarshi kawai, bari naje nasir yana waje yana jirana.

"tare suka fita Mahfus yasawa dakinshi key yafice.

"itama komawa tai daki, tana shiga ta dauki kayan tasa batare da tai mgn ba.

"Anty Frd da matan yya khamis sukai shewa hade da tafawa.

"ta window dakin amatullah Mahfus yaga yadda suke shewa ranshi yasake baci.

"yana isa gun nasir yace dan Allah xomutafi.

"da sauri nasir yace mutafi ina?

"batare daya tankaba motan nasir kawai yashiga, gani haka shima nasir shiga yai sukabar gidan.

"suna barin gidan Mahfus ya fadiwa nasir duk abinda Anty Frd taiwa amatullah.

"kai kawai nasir ya kada snn yace hakuri fa xakuyi daga kai har matanka.

"kasan tunani ne kuma kowa da irin tasa.

"kallon nasir kawai Mahfus yai hade da kwifa.

"tunda Mahfus yabar gidan besake dawowa gidan ba har yar'suna suka watse.

"gani har goma yai Mahfus bedawo ba yasa amatullah daukar waya tafita waje snn takirashi.

"Mahfus yana kwance a dakin nasir kiran amatullah yashigo, Mahfus yana gani number amatullah ne da sauri yadaga da hello.

"amatullah tace Mahfus meya hanaka dawowa gida? gashi har goma yawuce.

"Mahfus yace karki damu ina gidan nasir ne, anan xan kwana saida safe kikulamin da kanki da baby na.

"bejira yaji abinda xatace ba yakashe wayar.

"shiru amatullah tai snn takoma ciki.

"tana shiga Anty Frd ta hauta da fada tana cewa dan ubanki waya cemiki mai jego na fata da dare?

"baki tsoron wani abu ya sameki, idan ma wani abu kike bukata baxaki mgn a dauko mikiba sai kifita.

"shiru amatullah tai bata tankaba har suka kare.

"xama amatullah tai suka ta hira hade da yimata fadi yadda xata xauna da mijinta ba komai ne xata dauka ta bashi ba, saidai in taga abinda xasu amfana dashine.

"amatullah tace taji.

"snn Anty Frd ta jawo jakan da taxo dashi kayane sosae sukai mata ita da hajiya harda xinari hajiya ta siyewa amatullah tai tayi fitan suna dashi.

"akwatin baby ma daban shima yar'kanti ne masu tsadan gaske aka siyewa zunnurai.

"matar yya khamis ta xabe masu wanda xatayi amfani dasu yanxu saura kuma aka medasu cikin akwati aka rufe.

"Anty ta dau kudi 100000 thousand tabawa amatullah tace iji yya khamis yace abata.

"itama Anty fifty thousand tabawa amatullah hade da cewa wlh idan kika dauki kudina kikabawa mijinki da kaina xanxo na kwace kayana.

"ta karisa mgnr da dariya, itama amatullah murmushi kawai tai.

"matan yya khamis tabawa amatullah 20000 thousand tace tasiyowa baby riga.

"duk godiya sukai.

"cikin dare suka gyara mata ko'ina kayan da kuma baxasui amfani dashi yanxu ba, nata dana baby suka cikin akwati suka rufe snn suka dora kan wadrop.

"wanda kuma xasuyi amfani dashi yanxu cikin wadrop suka jere mata, saida suka fitar tsofaffi wanda suka fara kodewa snn akasa sabbabi.

"Anty Frd tace tai sadaka da tsofaffin.

"basu kwanta ba sai karfe biyun dare.

"asalatun fari Anty Frd ta mike saida tasa ruwan wanka snn tai sallah. tana idarwa tajuyewa amatullah ta kaimata toilet snn tasheta taje tai wanka.

"amatullah

Please Login or Register in order to submit comment