Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fi damuwa da sanin abin da ya sa ki ke zaune gida."

Tallabo fuskarta ya yi yasa idonta cikin na shi yace "Khadija me nai mi ki da zafi haka?"

Kamar za ta fashe da kuka tace "Mun samu sab'ani ne da kai akan amaryar ka, sab'anin da ya sa ka yi abin da ba ka tab'a yi ba a rayuwar ka, shine ni kuma na dawo gida gaba d'aya a lokacin ba ka buk'ata ta a gidan ka."

Da tsantsar mamaki yace "Sab'ani? Amma me na yi to?"

"Duka, duka na ka yi." Ta k'arashe da sunkuyar da kan ta k'asa tana hawaye, dafe kan shi ya yi yace "Duka? Ni da hannu na?"

Tsaye ya mik'e jiki a sanyaye ya sake sunkuyawa gabanta ya d'ago fuskarta yace "Ki yi hak'uri Khadija, wallahi Allah bansan na yi ba sai yanzu da ki ke fad'a min, ki gafarce ni dan Allah kar ki hukuntani da laifin da bansan na aikata ba, yanzu haka kunyar had'a ido na ke da ke da ahalin ki."

Ya na fad'a ya tashi ya fita ko juyowa baiyi ba, Mama ya samu a in da ya barta da alama kan ta ya d'au zafi, sunkuyawa ya yi yace "Mama, Khadija ta fad'a min abin da ya faru, Mama ina mai baku hak'uri da gaba d'aya zuciya ta, ku yafe min dan Allah, ba dagangan na yi ba, kuma banyi dan cin zarafin ku ba, hasalima abu ne da sam banyi tsammani ko tunanin faruwar shi ba."

Mik'ewa ya yi tare da cewa "Saida safe Mama." Ya fad'a ya na barin falon ba tare da jiran me za ta ce ba, Mama kam sai taji tausayin shi ya kamata sosai, watak'ila har ya yi anfani da maganin da Garba ya kawo cewar Mama a zuciyar ta, Khadija ma tausayin mijin ta ne ya sa ko fitowa ba ta yi ba ta kwanta daga nan kuma bacci ma ya d'auke ta.

Kai tsaye gida ya sake komawa ya samu malam zaune k'ofar gida sai Bilal gefen shi da wayar shi a hannu, zaune ya yi akan tabarmar ganin haka ya sa malam cewa "Fodio lafiya dai na gan ka haka?"

Idon shi cikin na malam yace "Ba lafiya Baba, Baba ka fad'a min dan Allah me ya faru da ni ne? Sannan me na aikata a lokacin da na rasa tunani na? Kawai ganin abubuwa na ke kamar sabi kuma kamar a almara."

Tank'washe k'afafu malam ya yi yace "Fodio, abubuwa sun faru da dama, idan da ka nutsu kai da kan ka za ka iya tuna komai, amma ka kasa kwantar da hankalin ka ma bare har ka samu nutsuwar."

Cike da damuwa yace "Baba ina maganar nutsuwa ga wanda ya na kallo rayuwar shi ke barazanar fita daga gangar jikin shi, a yanzu haka fa Khadija na gidan iyauen ta zaune da kuma ciki na a jikin ta, Baba ban ma san tsawon lokacin da ta d'auka acan d'in ba."

Murmushi sosai malam ya yi yace "Watan ta uku yanzu."

"Wata uku?" Ya fad'a da k'arfi da zaro ido kafin ya d'ora da "Baba da sakin ta na yi fa da yanzu ta kammala idda kenan? Kutumar bala'i, Allah ya ceceni."

Dariya malam ya yi kafin yace "Ai kam dai, dan ni dai ka ganni nan ba zan tashi zuwa yi ma ka biko ba da girman ka da komai."

"Yanzu dai malam ku fad'a min abin da ke faruwa da ni, ina so na sani."

Gyara zama malam ya sake yi bayan dogon tunani da ya yi kafin yace "Abin da ya faru da kai ba zamu dangana shi da kowa ba, dan har yanzu ba mu san mai wannan alhakin ba, dan haka kai ma ba na so ka d'auki laifin ka d'ora kan wani ko wata, ka barwa Allah kawai shine zai ma ka sakayya." Jinjina kai Usman ya yi alamar gamsuwa kafin malam ya ci gaba da bashi labarin iya abin da ya sani kawai daga barin Khadija gida zuwa yau d'in nan, sosai al'amarin ya girgiza Usman tare da bashi mamaki, to shi kam waye abokin gabar shi da har zai mi shi haka? Kasa tunawa ya yi sai kuma zuciyar shi tafi ta'allak'a mi shi komai da Haseenah, dan a ganin shi ita ce za ta iya sawa ya manta da Khadija dan ta bar gidan ita ta zauna, to amma kuma malam yace kar ya d'orawa kowa laifi, ya barwa Allah zai ma sa sakayya dan haka ya ja baki ya yi shiru, amma kuma abin da ya ji yanzun ya sa ya tuna da abubuwa dayawa da su ka faru, sai dai ba duka ba, saida safe ya mi shi dan lokacin har bacci ya d'auki Bilal daga nan, ganin zai shiga mota ya sa malam cewa "To matar ta ka fa wa ka barwa ita anan? Ko nan za ta kwana ne?"

Zaune ya yi cikin motar ya kira ta a waya yace ta fito, ba wani jimawa ta fito cikin takun k'asaita da izza dan dama zaman gidan ya isheta, kafe fuskata ya yi da ido har ta k'araso, tabbas ba munin fuska ba ko munin halitta, sai dai wani abun al'ajabi wani irin haushin ta ne yake ji na taso mi shi, wanda ko farko duk da ba wani son ta yake sosai ba amma dai ba ya mata irin wannan k'iyayyar, zagayawa ta yi ta shiga suka d'auki hanya ba tare da sunwa juna magana ba, jin shirun ya yi yawa kuma ya d'auki hanyar gida ya sa tace "Kasan fa ba mu da abin da za mu ci a gida, ka siya mana kafin mu wuce ko."

Cikin isa da gadara ya juyo ya kalle ta, a hankali kuma ya d'auke kan shi daga kallon ta cikin mak'oshi yace "Uhum."

Saida ya tsaya ya siya mata iya cikin ta kafin suka wuce gida, suna shiga ya nufi k'ofar na shi falon, da sauri tace "Beby, ina kuma za ka je?"

Juyowa ya yi yace "...


*Gidan uban da ki ka aike shi mana.*πŸ™ŠπŸ™ˆ
04/03/2020 Γ  19:43 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘


_SAMIRA HAROUNA_


*Litattafan marubuciyar*


*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._

*SADAUKARWA GA*

_MATAN FARKO_ πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)*


πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

```Fatan alkairi masoya```


_Bismillahir rahamanir rahim_


*35*


"Zan d'an shiga ciki na kwanta ne saboda na gaji, ki ci abincin kawai dama ni na k'oshi."

Sake juyawa ya yi zai wuce tace "Amma yau d'akin ka za ka kwana ne?"

"Eh." Ya fad'a a hassale tare da juyowa ya na kallon ta ya ci gaba da cewa "Kuma ke ma ina so ki kwanta d'akin ki dan ba na son takura."

Da mamaki tace "Takura kuma? Ni ce ma zan zama takura a gare ka? Babban mutum wai lafiyar ka k'alau."

Ajiyar zuciya ya sauke irin ta takura masa d'in nan kafin yace "Lafiya k'alau, na yau kawai na ke so ki bar ni na kwanta ni kad'ai, ki yi hak'uri." Ya fad'a ya na wucewa ciki ya barta nan, mamaki ne ya kama ta sosai da tunanin ko lafiyar shi? Ita dai a saninta lafiya lau suka je gida, amma daga lokacin da ya shiga d'akin malam ba ta ma san da tafiyar shi ba sai da taji kamar su na waya da Hajia duk da dai ba ta da tabbacin da shi su ka yi wayar, ita ma d'akin ta ta nufa ta cire kaya ta yi wanka kafin ta ci abinci ta kwanta, sam ba ta samu wata damuwa ba wajen baccin ta, dan kuwa ba jimawa baccin ya d'auke ta.

A wajen Usman kuma kasa bacci ya yi ya na tunanin abin duniya, da farko dai da kunya ce ke neman sa shi yin k'asa a gwiwa, amma kuma saiya duba ya ga ai ba a sanin shi bane komai ya faru, sannan bai saki matar shi ba bugu da k'ari ta na d'auke da cikin shi, da haka kuma sai ya ji ya ma k'agu gari ya waye ko ya sake komawa wajen Dije, ba kuma zai gushe ba har sai ta dawo gare shi, saboda fatan dacewa ya sa ya d'auro alwala ya shiga fad'awa Allah kukan shi tare da neman taimakon ubangiji.

*Washe gari* da safe d'aurin aure, sammako sosai Usman ya yi ya hallara d'aurin auren bayan yace wa Haseenah ta yi k'ok'ari taje da wuri ita ma, haka ya fita kamar shine angon cikin babbar riga da 'yar ciki farare, ya na isa a k'ofar gida ya tsaya saboda mutanen da ya samu a wajen, nan su ka shiga gaisawa da mutane har lokacin da motar Naseer ta kutso cikin taron jama'ar, mazauni aka samarwa da motar kafin Mama ta bud'e ta fito daga ciki, Usman na ganinta ya tafi da azama dan kwasar gaisuwa sai ya ga Khadija ta fito a matsayin dreban da ta tuk'o motar, tsaye ya yi ya kasa k'arasawa saboda haushi, tabbas yasan ta na fita da gyale sai dai yau ne ya fara jin haushin haka, domin kuwa ta na fitowa gyalen ma a kafad'ar ta yake, duk da doguwar rigar shadda ce jikinta wacce ta fito da d'an cikin ta na wata biyar, amma dai baiji dad'i ba duk da ya ga sai gyara gyalen take, har saida su ka zo daf da shi kafin ya sunkuya ya gaishe da Mama ta amsa cikin sakin fuska, wucewa Mama ta yi shi kuma ya mayar da kallon sa kan Khadija da ita ma shi take kallo yace "Ke ba ka iya gaisuwa ba ne ko me?"

Cikin tsiwa tace "Um ban iya ba, ko ka koya min ne?"

Gyara tsayuwa ya yi ya na k'ara sab'a rigar shi a kafad'a yace "Uwar yarima wai yaushe ki ka raina ni ne haka?"

Ta na kallon idon shi tace "Tun ranar da ka fara wulak'anta ni saboda ka yi amarya."

Wani kallo ya mata kafin ya d'an saci kallon mutanen da ke wajen yace "Yanzu ko albarkacin mutanen nan ba zan ci ba na ga murmushin nan na ki mai saka ni bacci."

'Yar siririyar dariya ta yi tace "Toh fa Alhaji mai babbar riga, kai da za ka je d'aurin aure kuma me ya had'a ka da bacci? To ka farka idan mafarki ka ke, kai da sake ganin murmushin Nana Khadija kuma sai dai ko a lahira, a lokacin da aka min umarni da na shiga aljanna, to zan iya juyowa na kalle ka dan na ma ka bye bye, to fa zai iya yiwuwa a lokacin ne za ka ga murmushin."

Shi maganar ta dariya ma ta bashi, da sauri ya rik'o hannunta ya matso daf da ita yace "Ki na so ki ce ni kuma zan zauna har sai kin riga ni shiga? Ko kuma nufin ki ni ba ma zan shiga ba?, ai k'afar ki k'afa ta insha Allahu, in kuma ba haka ba to sai dai ki same ni a ciki kewaye da sabbin mata na."

Fizge hannunta ta yi tace "Ka na dukan nawa ne kuma ka ke tunanin za ka shiga aljanna."

Wucewa ta yi ta bar shi nan tsaye ya na ta dariya shi kad'ai, Murtala ne ya k'araso wajen shi yace "Mijin Khadija lafiya ka ke dariya kai kad'ai?"

Hararan shi ya yi yace "Ni kad'ai ka gani a wurin? Ba ka ga wacce na gani ba."

"Na gani kam, ince dai kun sasanta za ta koma?" Kallon shi ya yi sosai yace "Da alama fa sai ka tayani bata hak'uri, ran 'yar aljanna ya b'ace sosai."

Zaro ido Murtala ya yi yace"Wa? Ni! Sam ba dani ba, kai dai da ka mata laifi ka bata hak'uri amma banda ni."

"Au! Yanzu ka na nufin ba za ka tayani ba kenan? To nagode, ai na d'auka zan iya yin zaune gida ma kai kaje har sai ka dawo min da ita, ashe ba haka bane."

"A'a ni ba haka na ke nufi ba, kasan dai maganar nan ta manya ce ba iri na ba, kuma tsakanin ka da Khadija ma ai ba ta b'aci."

Ba jimawa da shigar Khadija mutane aka fito dan tafiya wajen d'aurin auren, daga ciki har da Mama dan dama d'aurin auren take son samu, nan aka shiga motoci aka wuce d'aurin auren, Khadija na zaune d'akin Hajia Nura ya shigo da sauri ya na kiran sunan Hajia, ya na ganin Khadija yace "Uwar gida yane, ke ba ki je d'aurin auren ba?"

Hararan shi ta yi tace "Wa? Allah ya sawak'e, me zanje na yi a d'aurin auren kishiya, ai ina daga nan ina aika mu ku da addu'a."

"Yawwa hakan ma ya yi ai, addu'ar ita mu ke buk'ata ai." Cewar Nura ya na kallon Hajia da ta fito daga d'aki, cikin k'aguwa yace "Hajia takalma na da na baki jiya na ke nema."

Ledar hannun Hajia ta mik'o mi shi tace "Dama nasan su za ka nema ka ke min wannan kiran."

Bud'ewa ya yi ya saka takalman kafin ya juya zai fita yace "Hajia ku fara tausar min k'irjin ta kafin na dawo."

Haka suka wuce wajen d'aurin aure gidan waliyin Choukra, kuma ba'a b'ata lokaci ba waken yin abin da ya kai kowa wurin, nan aka d'aura auren *Nura Ali* da amaryarshi *Choukra Sabi'u*, bayan taya juya murna da farin ciki ne abokan ango su ka nufi inda za su ci su sha, manyan mutane kuma suka dawo gidan su ango dan cin abinci suma.

Bayan tafiyar 'yan d'aurin aure ne ba jimawa kuma Haseenah ta zo ita ma kamar yanda Usman yace ta zo da wuri, a d'akin Hajia suke zaune nesa da juna amma babu mai kula wani, haka suke zaune Khadija na hira da mutanen da ba su je d'aurin auren ba, Hajia ce ta fito daga uwar d'aki ta kalli Khadija tace "Nana wai kinga Bilal kuwa?"

"A'a Hajia, ya na ina ne?"

"Ai tare da malam su ka shirya su ka fita, kin ganshi kamar shine angon sai rawar k'afa ya ke, saida na gargad'e shi dai kan karya kuskura ya kalli wasu mata."

Dariya kawai ta yi ba tace komai ba har mutane su ka fara shigowa aka fara hayaniya, nan su Hassana da sauran mutane suka fara raba abinci ana kaiwa mutane.

Bilal ne ya shigo tare da malam kai tsaye wajen mahaifiyar shi ya nufa ya zauna kan k'afafun ta, wanda hakan ya yi daidai da shigowar Usman da kwalbar lemu a hannun sai malam a biye da shi, kwantar da kan Bilal ta yi a k'irjin ta tana sumbatar shi tace "Yarima na yi kewar ka fa, kwana uku ka na nesa da ni."

Bilal kenan d'an gata sai kuwa ya sake wani cakume ta kamar zai sa nonon ta a baki yace "Mummy yunwa na ke ji fa."

Lek'a fuskar shi ta yi tace "Ban gane ba, ba ka ci abinci ba ne a waje?"

Cikin shagwab'a yace "Ban ci ba, to duka fa manya ne a wajen."

Murmushi ta yi tace "To yarima na k'arami ne? Yaro ana bikin kawun ka ace ka na rasa abin da za ka ci, to ba ka had'u da Abban ka bane?"

K'ara tusa kanshi ya yi cikin jikin ta yace "Um um."

D'ago kan ta tayi za ta yi magana sai ga Usman tsaye gaban ta ya na fad'in "Yarima yanzu da girman ka za ka hau k'afafu haka?"

Da sauri Bilal ya d'ago ya na ganin Abban shi ne ya yi tsaye ya mak'ale mi shi a wuya, rumgume shi ya yi shima yace "Me ya ke faruwa ne na ga ka na ta zuba shagwab'a haka?"

Khadija ce tace "Bai ci abincin bane, amma kuma kai ga hannun ka nan har da lemu ma ka ke korawa."

Kallon ta ya yi yace "To yanzu shan lemun nawa ya zama haramun ne ko me?"

"Ya zama mana, taya za ka jefa loma bakin ka ba ka san gudan jinin ka ya ci ko bai ci ba." Yanda ta had'e fuska ne ya sa ya ga ko ya fad'a mata shi ma bai ci abinci ba ba yarda za ta yi ba, dan haka ya juya da Bilal d'auke da shi yace "Yarima muje ka zab'i abin da ka ke so ka ci, rabu da mahaifiyar nan ta ka yau tunda safiya ta waye ta tashi da masifa, can ta k'arata da masifarta."

Shiru ta yi sai kallon k'eyar shi da take, shi kam jin ta yi shiru ya sa ya juyo dan ya san ta na nan ta na kumbura, wata irin harara ta dalla masa da tasa shi b'arkewa da dariya yace "Yi hak'uri Hajia, nasan me ye matsalar ki, ki ba ni hak'uri sannan ki lallab'a ni sai na mi ki magani."

Yanda ta motsa bakin ta ya sa ya fahimci me take nufi, dan haka ya mata gwalo yace "Idan kin kamani ki mayar da gabana gabas ki yankani."

Da haka ya fita su ka bar gidan, tun lokacin ba ta sake ganin Bilal ba har biki ya yi biki ana ta bayar da zafi, Haseenah na d'akin Aziza kwance sai narkewa ta ke, sai dai kuma abin ya d'an dameta na yanda kowa baya ma kula ta, sai wanda ya ganta ne dole ya ke iya gaisawa da ita, amma har Aziza sai ta shigo d'akin ta fita ko kallon in da take ba ta yi ba, haka yamma ta yi aka raba abinci, kasancewar a d'aki take ita kad'ai ya sa aka rabe abinci ba'a ma san da ita ba, babu wanda ya damu da hakan sai ma ran su Hassana da ke k'ara b'aci.

Da dare mutane duk sun tafi gidan amarya da ango, Khadija ce d'aki ke gaggauta shirya dan tafiya tare da masu jiranta a waje tunda ta zo da mota, sai Haseenah da tun sallah magriba ta tafiyar ta gida, Hajia na zaune kan katifa gyangyad'i na neman fizgar ta Khadija tace "Hajia bacci ne?"

Kallon ta tayi tace "To tukuna dai."

Saida ta gyara jakarta a kafad'a tace "To ni zan tafi, kuma ina ga daga can gida zan wuce, sai dai gobe idan Allah ya kaimu."

"To Allah ya yarda Khadija, Allah hutar da gajiya, angode sosai Allah ya saka da alkairi, saida safe." Duk ta na maganar ne saboda Khadija har ta kai bakin k'ofa ta na amsa mata, za ta bud'a labulen d'akin Usman ya sallamo, kaucewa ta yi da tunanin ya wuce amma saiya wani tsare ta da ido yace "Hajia ke kuma wannan kwalliyar fa? Duk ta zuwa kallon ango da amaryar ce?"

Kallon Hajia ta yi sai ta ga ita ma su take kallo dan haka ta share shi kawai, hannu ya sa aljihu ya ciro da hankici (hankiciep) ya kai a bakin ta zai goge mata jan baki, da sauri ta ja baya ta na rufe bakin tace "Ya za ka goge min? Yanzu fa na saka shi, kuma ina da bak'o ne a gida."

Wani kallo ya mata yace "Bak'o kuma? Wane irin bak'o?"

Ba alamar wasa tace "Bazawari nn..." Bugun da ya kai mata a baki ne ya sa ta saki k'ara ba ta shirya ba tare da rufe bakin ta durk'ushe kan gwiwanta, Hajia da ta zabura ne ta kalle shi tace "Alhaji meye haka? Me tai ma ka?"

Zaune ya yi akan kujerar da ke iya fuskantar Khadijar ya na hararan ta, cikin d'aga murya Hajia tace "Fin k'arfi ne ko me? Dallah malam ka bata hak'uri ko."

Rai b'ace ya kalli Hajia yace "Hajia ba ki ji me yarinyar nan ta ke fad'a ba ne, ina matsayin mijin ta za tace wani wai bak'o na jiran ta, har da cewa wai bazawarinta." K'wafa ya yi hakan ya sa Hajia kallon Khadija da har yanzu ba ta motsa ba tace "Yi hak'uri kinji Khadija tashi ki tafi abinki, ba zan iya tashi bane saboda k'afafu na amma da na rama mi ki dukan ki, ki yi hak'uri kinji."

D'agowa ta yi a hankali ta sauke ido a kan shi sun mata jawur, murmushi ta yi ta kalli Hajia tace "Saida safe."

Mik'ewa ta yi ta fice daga gidan, ta yi k'ok'ari ta sauke ma su jiran ta a waje gidan amarya amma ita ba ta tsaya ba ta wuce gida.


*A gurguje*


A kwana biyu zuwa lokacin da aka kammala sabgar bikin Nura Usman ya shiga taitayin shi, dan ko wayar shi Khadija ba ta d'auka bare ta saurare shi idan ya zo, hakan ya tab'a shi sosai dan ya damu, haka ma Haseenah ta fara damuwa sosai akan lamarin na shi, dan har yanzu ba su kwana d'aki d'aya ba, gari na wayewa kuma zai buga sammako yaje gida ya na lallab'ar malam ya je ya dawo da Khadija, sam ba ya da lokacin wata Haseenah yanzun, abinci ma idan ta dafa sai dai ta ci ita kad'ai amma ban da shi, ba ya son zuwa gidan saboda ba ya son ganin Haseenah da idon shi, ya na iya k'ok'arin shi sosai wajen b'oye k'iyayyar da yake mata, ya rasa dalilin da ya sa ya ke sake jin tsanar ta a kullum idan ya ganta, ba ya son jin muryar ta ko ganin giftawarta a gidan, duk da ba ya da kokwanto akan cikin da ke jikin ta cewa na shi ne amma dai ba ya jin ya na k'aunar abin da ke cikin ta kamar yanda ya ke k'aunar wanda ke cikin Khadija, a haka har aka kwashe *sati biyu* babu abin da ya sauya.

A sati biyun nan ne Usman ya yi tattaki har k'auyen su Baba Garba mai gadi ya je ya bashi hak'uri akan abin da ya farusannan ya nemi da ya dawo bakin aikin shi, ya hak'ura ya kuma nuna masa komai ya wuce shi dama bai rik'e ba saboda ya san ba laifin shi bane, amma dai ba zai iya komawa aiki ba saboda jiki da jini, amma idan ya amince akwai d'an shi da ke neman kangarewa zai iya had'a shi da shi saiya zauna a mazaunin shi, ya amince ya taho da yaron mai sunan *Rabe*, tabbas ya fara aiki yanda ya kamata sai dai burin Usman akan yaron ba wai ya zama mai kula da pliwoyin (flawers) gidan shi bane da k'ofa, ya na so a gama wannan zagon na karatu sannan ya d'ora shi ya ci gaba da karatun shi tunda ya na yi ya dakatar saboda shirme, duk da haka kuma Usman bai daina bibiyar Khadija ba, yanzu haka har ya gaji da sawa Bilal na rok'on ta akan ta dawo, Hajia da malam dama sun ce ba ruwan su, a k'arshe ya samu da k'yar ya lallab'a Murtala ya je ya mata magana, nuna masa ta yi ba komai za ta koma, amma ya na barin gidan tace ba yanzu sai ya sake shiga hankalin sa, jin shiru shiru ya sa saida ta kai ga Usman ya turo Nura da Kabir da kuma Mannir su ka je bata hak'uri, sai lokacin Mama tasan da irin tsiyar da Khadija ke tsulawa, dan sam babu wanda ya tab'a ce mata ya zo bata hak'uri dan ta koma, Usman kuma idan ya zo ta kan basu wuri ne dan su tattauna, kuma ba ta nuna mata wasu alamu na rashin jituwa, hakan ya sa ba ta san me ke faruwa ba, shi ma Usman ya so ya b'oye mata ne dan yasan za ta iya tirsasata akan ta dawo, duk da ya na matuk'ar so ta koma amma ya fi so ta koma dan ganin damar ta, kuma har yau ba ya ganin laifin ta akan hukuncin da take masa, dan kuwa babu abin da ta rage shi da shi a rayuwa amma ya mata kishiya, sannan ya rasa meya shiga kan shi da ya dinga cin mutuncin ta, dan wasu abubuwan sai yanzu ne idan ya na rarrashin ta take iya fad'a mi shi irin abin da ya mata, bugu da k'ari kuma bata gama hucewa ba ya zo ya bugar mata baki har saida ya kumbura, wanda kullum mitar

Please Login or Register in order to submit comment