Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wani abu da ku ke buk'ata."

Murmushi kawai ta yi tace "Allah huci zuciyar ka ranka shi dad'e, ai akwai hikima sosai a cikin hallitar kowane bawa da iyaye biyu, naga ba ka gari ne kuma kullum cikin aiki ka ke, ba ka da lokacin waya dani bare har mu yi magana da ta shafi d'an ka, shi ya sa ni kuma na mi shi duk wani abin da zai buk'ata, har kud'in makarantar ma na biya."

Duk da ya ji wani abu a zuciyar shi a game da ita, amma basarwa ya yi yace "Uhum." Kashe wayar kawai ya yi, take ya durmiya cikin tunani, Khadija kud'in da ya bata babu abin da za su mata, amma da su take buk'atunta har ta biyawa yaro kud'in makaranta, amma kuma Haseenah daya lodawa masu yawa yanzu haka zaije ya tura mata kud'i ne dan tace suna buk'atar kud'i, dan haka ya kasa nutsuwa ya kira Aziza ya tambaye ta da gaske Haseenah ta na bata kud'in adaidaita, bud'ar bakin ta cewa ta yi "Eh yah Fodio, ta na bani na zuwa da dawowa, har da ma d'an na kashewa, kuma kullum fa sai mun siyi abinci in dai ranar girkin Khadija ne, kuma jiya masu karb'ar kud'in ruwa sun zo dole sai aunty Haseenah ce ta basu."

Duk da ya yarda da Aziza dan abu d'aya suka fad'a amma Haseenah ba ta fad'a mi shi suna siyen abinci ba, haka dai ya sa Nura ya kawo mata kud'in sannan ya kira ya tambaye ta K'arin haske akan abin da Aziza ta fad'a, cikin marairaicewa tace "Kawai ba na so ne wani abu ya faru kuma ace ni ce sila."

"Shikenan to ya yi kyau." Ya fad'a ya na kashe wayar, wayar Khadija ya kira dan jin dalili, amma suna gama waya ta farko Aishatu ta kira ta tace ga ta k'ofar gida mai gadi na mata iskanci, dariya Khadija ta yi kafin tace ta na zuwa, Bilal ta aika sai gasu sun shigo tare, Aishatu budurwace da ke da larura ta iska, hakan ya sa komai nata daban ne, fad'a da masifa kamar shan ruwa ne a wajen ta, tunda su ka shigo tare da Bilal ta ke zagin mai adaidaitar da ya kawota wai yace sai dai ta bashi arba'in ita kuma ishirin ta bashi, hakan ne ma ya sa sam Khadija ba ta ji kiran Usman ba saboda wayar na (vibration) ne, aifa nan hira ta b'arke suna ta yi kamar wanda aka jonawa lantarki, tunda wuri kamar yanda ta saba suka shiga girkin yamma, kuma yau ta yi niyyar yin waina dan akwai wa abokanan mahaifin ta, saboda sabo ya sa ba wani wahala tasha ba musamman kuma ga mai kamawa, sai salade da shima aka siyo mata suka gyara abinsu, Bilyamin ta kira ya kai wainar in da ta zubawa Haseenah na su tace ya kaii, da sauri Aishatu tace ya jirata su tafi tare ta ga amarya, nan fa gaban Khadija ya shiga dukan uku uku, dan ba lallai ta shiga lafiya ta fito lafiya ba, k'aramin aikinta ne ta k'arewa Haseenah kallo tace au dama wannan ce amaryar? Saida Khadija ta rik'e hannunta tace "Dan Allah idan ki ka je ku gaisa kawai ki juyo ki dawo, ba na son tashin hankali ko kad'an."

"Wai amaryar 'yar akuya ce kenan? To ai sai ki fad'a mata ki na da irin mu 'ya'yan busurai, mu za ta wa iskanci?" Cewar Aishatu har tana gaggawar tafiya, rik'e ta Khadija tayi tace "Ni fa ban fad'a mi ki haka ba, kawai dai ku gaisa ki juyo ki dawo, kar ki ce za ki tsaya wani abun da bai shafe ki ba."

Saida ta fizge hannunta tace "Naji dallah."

"Kinyi alk'awari?" Cewar Khadija ta na binta da kallo, k'ala ba tace ba ta bi bayan Bilal su ka shiga, Bilal ne ya yi sallama amma shiru, bubbuga k'ofar ya yi ya sake jin shiru, sai Aziza ce ta lek'o daga sama ta hangeshi tace "Bilal ga auntyn ka nan sama."

Daga nan yace "Abinci ne na kawo mu ku."

"Kawo nan." Cewar Aziza, kallon Aishatu ya yi tace "Muje saman na ganta, ai ko saman bakwai take sai na ganta yau."

Can suka nufa, Bilal na isa ya aje abincin sai aishatu da ke k'arewa Haseenah kallo ta hakimce akan kujera ta na latsa waya, kallon Aziza ta yi tace "Ke na ganeki k'anwar Usman ce ko?"

"Eh, ina wuni." Cewar Aziza wacce ba tun yau ba tasan Aishatu farin sani, mayar da kallonta ta yi ga Haseenah ta na wani murmushi tace "...


*Allah fidda A'i daga rogo.*
15/02/2020 Γ  13:58 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘


_SAMIRA HAROUNA_


*Litattafan marubuciyar*


*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._

*SADAUKARWA GA*

_MATAN FARKO_ πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)*


πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

```Fatan alkairi masoya```


_Bismillahir rahamanir rahim_


*26*


"Wai ke ce dama amaryar da ya yi? Kai, amma dai wallahi maza ba su da tabbas, yanzu shi dan Allah rufe mi shi ido ki ke kayi? Ko kuma tallarki aka mi shi?"

Bilal ne ya kalle ta yace "Aunty Aishatu mu tafi ko."

Bushewa ta yi da dariya tace "Bilal barni na k'are kallon amaryar Baban ka, wannan mace haka sai kace kaza ta ga wuk'ar yankanta."

Wata dariyar ta saka mik'ewa Haseenah ta yi da nufin magana sai Aziza ta rik'e hannun ta, girgiza mata kai ta yi alamar a'a ta rabu da ita, ganin hakane ya sa Aishatu cewa "Da kin barta ta fad'i abin da ke ran ta ai kar ta zama ajalin ta, ni ma saboda ba zan iya yin gulmarki bane ya sa na fad'i abin da ke raina tun a gaban ki."

Iza k'eyar Bilal ta yi tace "Mu tafi kai yaro ka ji, Allah ya tsigewa Babanka rigar wahala, wannan mata kafin ya sa k'asusuwanta su cika ai sai mai kampanin gidan shinkafa na *oriba* ya san da zaman shi."

Ta na wucewa Haseenah tace "Ita kuma wannan mahaukaciyar fa? Wacece ita?"

Ajiyar zuciya Aziza ta sauke tace "Hum! Cousine d'in Khadija ce, mahaukaciya ta sawa a gidan gaba, wallahi da kin biye mata ina tabbatar mi ki yau a gidan nan sai kinga motar masu kashe gobara."

Tab'e baki ta yi tace "Kin dai gani Aziza da idon ki, duk wanda ya zo gidan nan wajen ta sai ya zo ya ci mutumci na, ba na shiga sabgarta amma ita sai ta san yanda ta yi ta tsokane ni, yanzu wannan da me ya yi kama?"

"Ki yi hak'uri dan Allah ki rabu da ita, can aniyarta ta koma mata." Cewar Aziza, Haseenah ce tace "Mu sauka k'asa kawai dan magriba ta gabato."

"Gaskiya kam." Aziza ta fad'a ta na d'aukar kwanon abinci ta na fad'in "Ta mayar da mu mabarata k'arfi da yaji, in dai ta yi abinci ran alhamis da juma'a to ranar za mu samu abinci, saboda ta na yin abincin da take rabawa mutanen ta, shi ma fa ba kullum ba sai taga dama."

Kallon ta Haseenah ta yi ta wutsiyar ido a zuciyar ta tace "To ai saboda ki na gidan a wannan ranakun shi ya sa ba na iya zubar da shi, sai kin fita kad'ai na ke samun wannan damar."

Tunda Aishatu ta koma take mita akan amaryar Usman, har akayi sallah magrib da isha'i su ka ci abinci, anan take tambayar Khadija za ta je bikin *Saratu* (kamar jikanya take ga mahaifiyar Khadija), zaro ido ta yi tace "Wai yaushe ne bikin Saratu?"

"Jibi mana." Cewar Aishatu tana shirgar wainar ta, cike da mamaki Khadija tace "Wallahi na manta, kuma Mama ba ta sake tuna min ba, amma dai bara na kira Abban Bilal na fad'a mi shi yanzun nan, dan zan iya mantawa, kuma tafiya ce da ba nan cikin gari ba akwai buk'atar ya sani da wuri."

Saida ta d'auki wayar ta ga kiran shi har uku ba ta d'aga ba, maida kiran ta yi kamar kuma jira ya ke sai kuwa ya d'auka dan ya zazzage kwandon bala'i, cikin sa'a sai Aishatu ta d'aga murya tace "Gaida min shi, ki ce na ga amaryar shi ina taya shi murna."

Dariya Khadija ta yi tace " bara na baki sai ki fad'a mi shi." Bata wayar ta yi, kasancewar akwai fahimtar juna tsakaninsu ya sa su ka dinga hira ta na tsokanar shi shima haka kafin Khadija ta karb'i wayar, ta na d'orawa a kunne tace "An wuni lafiya saraki."

"Lafiya lau, anga damar d'aukar wayar?"

Murmushi ta yi tace "Ka yi hak'uri, ina aiki ne a lokacin ban lura ba, yanzu ma na d'auko wayar ne zan nemi izinin ka sai na ga kiran."

"Izinin me kuma?"

"In ba ka manta ba wata biyu da ya wuce na baka goron Saratu? To bikin ne ya taso yanzu ni har na manta ma saida Aishatu ta tuna min."

"Yaushe ne?"

Ta na wasa da yatsunta tace "Jibi, ranar da su Bilal za su koma makaranta."

"Amma ai ba cikin gari bane?"

"Eh hakane."

"Shikenan, Allah ya tsare, zan kira Mama na tambaye ta shirye shiryen tafiyar." Ya na fad'in haka ya datse kiran, ita kam bata wani damu ba tunda dai ya barta, sai wajen tara na dare Khadija ta ma Aishatu kyautar fitar hankali kafin ta bar gidan.


B'angaren Haseenah kam tunda ta ci wainar nan dayawa sai ta tayar mata da zuciya ta dinga kelaya amai, sosai ta galabaita har Aziza ta tashi hankalin ta, dare na sake yi kuma sai zazzab'i da ciwon kai, Hajia su ka kira aka fad'a mata tace su shirya su fad'awa Khadija tunda ita ta iya mota saita kai ta asibiti, ira kuma za ta same su asibitin yanzu, har Aziza za ta tafi wajen Khadija kawai Haseenah ta rik'e hannunta tace kar taje, "Me ya sa to?" Ita ce tambayar da ta mata.

Cikin galabaita tace "Kawai ba na so tasan halin da na ke ciki, ko ta taimaka min ba dan Allah bane, dan ta samu mafakar da za ta yak'eni ne."

Da mamaki tace "Amma Haseenah dan ta kai mu asibiti miye a ciki?"

Kallonta ta yi tace "Aziza in za ki samo mai adaidaita ki samo, in ba za ki sami ba ki bar shi, yanzu haka da yan uwa na za su san ina cin abincin ta wallahi da sun tofa min yawu, mutum fa ba abun yarda bane, kuma ke kinfi kowa sanin ta ai."

"Gaskiya ne kuma." Cewar Aziza jiki a sanyaye, haka suka shirya suka fita a hanya suka yi sa'ar samun adaidaita su ka hau, asibitin kud'i aka kai da ke nan kusa da su ta *Clinique Alheri*, tun kafin su ka likitan Hajia ta k'araso ta na waya da Usman da ta sa aka kira shi take fad'a mi shi, aifa kamar ya taso ya zo ya ke ji ance amarsu ba lafiya, ko da su ka ga likita ya mu su albishir da ta na da ciki amma k'arami, nan dai aka mata allura tare da bata magunguna, bayan sun biya kud'i tsagaga su ka dawo gida da rankiyar Hajia, kwance Haseenah ta yi Hajia ta kalli Aziza tace "Da na ce ku fad'awa Khadija ta kai ku me ya sa ba ku mata magana ba ku ka hau adaidaita?"

Aziza ce "Hajia zan..." Da sauri Haseenah ta mata alama da hannu kan ta yi shiru, duk da Hajia ta gani amma da tace "Me ye ta yi shiru?"

Cike da tausayi tace "Hajia kawai ku bar maganar, tunda dai gashi mun tafi kuma mun dawo lafiya."

Shiru Hajia ta yi da mamaki, kallon ta tayi tace "Kun ci abinci?"

Kallon juna su ka yi sai Haseenah ce tace "Wallahi wata waina ce aunty Khadija ta aiko mana, ko gama ci banyi ba zuciyata ta tashi sai amai."

"Yanzu ta na aiko mu ku da abincin kenan?" Cewar Hajia ta na kafesu da ido, Aziza ce tace "Hajia bata aikowa fa, sai kamar irin wannan ranakun alhamis ko juma'a, shi ma sai in ya na girkin ta ne."

Kallon Haseenah ta yi tace "Ki fad'awa Aziza idan za ki ci wani abu mai sauk'i saita d'ora mi ki kafin ki sha magani, ni yanzu gida zan tafi dare ya yi."

"To." Ta fad'a ta na yamutsa fuska, Hajia na fita tasa Aziza ta d'ora mata zallar shayi tasha kafin tasha magana, kiran ta Usman ya yi suka dinga hira har saida tace za ta yi bacci, Hajia kuma na fita ko kallon b'angaren Khadija ba ta yi ba saboda ran ta ya sake b'acewa a game da ita, adaidaita ta hau ta koma gida, ba ta yi nauyin baki ba wajen fad'awa malam abin da ake ciki, sai dai shi baiji komai ba a zuciyar shi, sai dai yafi mayar da hankalin shi kan Usman da ya ke d'an ganin canji a tare da shi yanzun, da haka suka kwanta da fatan ganin wayewar gari lafiya.


Tunda safe Hajia ta had'a abin kari ta bawa Nura ya tafi ya kai ma su Haseenah, a lokacin Khadija na madafa da doguwar rigar bacci a jikinta Nura ya shigo, da kallo ta bishi har ya wuce b'angaren Haseenah kai tsaye kamar yanda Hajia ta fad'a mi shi, amma bai jima ba ya dawo dan gaisawa kad'ai ya yi da Haseenah ko jiki bai tambaye ta, falon Khadija ya lek'a sai Bilal kwance akan kujera, baisan da shigowar shi ba yace "Yarima barka da safiya."

Juyowa ya yi yace "Tonton Nura, ina kwana?"

"Lafiya lau, ka tashi lafiya?"

"Lafiya lau."

Ba tare da ya shigo ba daga k'ofar yace "Ina maman ka?"

"Ta na madafa." Ya fad'a da ma sa nuni da yatsarshi, hannu ya d'aga ma sa yace "Ina zuwa to." Madafar ya nufa da sallama, ya na ganin Khadija yace "Uwar gida ran gida, uwar gida sarautar mata, kowa ya shigo gida ke ya tarar, ko mai gida sai kin lamunce ya shigo, sannu da aiki."

Da wuk'ar hannunta ta nuna shi tace "Bansan dad'in baki, fad'i abin da ka ke so na ma ka."

Cikin had'e rai yace "Kamar ya? Ban gane me ki ke nufi ba?"

Kallon shi ta yi tace "Ai dana gan ka gidan ka to da dalili, bugu da k'ari kuma gashi har da min wani kirari kamar marok'i."

Dariya ya yi yace "Lallai uwar gida daban ki ke da kowace mace, cikin sakan biyar har kin fahimci akwai abin da na ke buk'ata ki min ko?"

Hararan wasa ta mi shi tace "Yau da gobe ai bata bar komai ba, karfa ka manta a hannu na ka k'arasa girma."

B'ata rai ya yi yace "Haba kema, basar mana."

"To naji, me ka ke so."

Saida ya matso kusan ta yasa hannu ya na cakurar dankalin da take soyawa ya na jefawa baki yace "Aunty Khadija maganar fa mai mahimmanci ce."

"Uhum, ina jinka."

Saida ya saci kallon ta yace "Aure na ke so."

Da sauri ta dakata daga abin da take ta kalle shi tace "Me? Aure fa ka ce Nura?"

"Eh mana, ko ban isa ba?"

Zaro ido ta yi tace "Ni bance ba, amma dai me zai hana ka bari kad'an k'ara mallakar hankalin kan ka, Nura aure fa ba iya abin da kawai ka ke tunani bane."

Kamar zaiyi kuka yace "To ni me na ce mi ki ina tunani?"

Mirmushin gefen labb'a ta yi tace "Ba ma irin wannan hirar da kai, amma na tabbatar ba zai wuce wutar balaga ce ke fizgarka ba."

"Kinsan me?" Ya fad'a ya na rik'e k'ugu, "A'a sai ka fad'a."

"Mijin ki ma haka yace da na masa magana, wai na bari har nan da ko shekara biyu, a gaskiya kuma ni ba zan iya ba, aunty Khadija wallahi gaskiya na ke fad'a mi ki, na fad'awa su Baba sunce ba ruwansu na fad'awa Usman tunda shine zai min auren, shi kuma yace ba yanzu ba."

Ajiyar zuciya ta sauke tace "Yanzu me ka ke so na ma ka?"

Cikin sigar rarrashi yace "Ki daure dan Allah ki taimaka min ki ma sa magana, wallahi nasan zai saurare ki, ni fa har mun gama magana da iyayen yarinyar ma, sunce kawai na turo manya na."

"Babbar magana." Cewar Khadija, "Haba wannan k'arama ce, yanda na san ki da Abban yarima ai sha yanzu mgani yanzu ne."

"Sanin da ka yi mana ada ne wannan." Cewar Khadija a zuciyar ta.

Basarwa ta yi tace "Shikenan kar ka damu, zan jaraba na gani, amma ba lallai ya amince ba tunda har ya nuna bai yarda ba tun farko."

"Zai ma amince in dai ki ka masa magana wallahi." Da haka ya bar gidan ita kuma ta shiga tunanin yanda za ta fara tunkarar sabon Usman d'in ta da maganar nan, ba ma lallai ya saurare ta ba bare har ya amince da abin da Nura ke tsammani.

Ta na gama abin karin ta bawa Bilal na su Haseenah ya kai mu su, suma ko da su ka kammala suka fito farfajiyar gida, Bilal na yawo da moton shi a tsakar gidan Khadija zaune da waya ta na tunanin ta kira ko karta kira, ta na haka sai kiran shiya shigo wayar ta, yau ma mamaki ta yi ganin kiran shi, hakan ya sa ta d'auka ta aza a kunne, ba sallama bare gaisawa yace "Na kira Hajia akan maganar tafiyar nan, sai ki shirya da wuri ki same su can gida dan sun ce Naseer ne zai kai su."

"H...hello." Ta fad'a da sauri saboda jin zai katse kiran, cike da k'aguwa yace "Ina ji? Lafiya?"

Cikin fad'uwar gaba tace "Lafiya lau, dama ina son yin magana da kai ne."

"Magana akan me kuma?"

Murya k'asan mak'oshi tace "Nura ne dama ya same ni akan maganar aure da ya ke so, amma yace ka ce ba yanzu ba, shine..."

"Shine za ki sani na yarda na mi shi auren ko me?" Ya fad'a cike gatsali, kamar ta kashe wayar sai kuma ta daure tace "A'a ba haka bane, ya fad'a min ne saboda shi a tunanin shi Khadija tafi k'arfin komai a gurin Abban Bilal, ya zo da buk'atar shine gare ni saboda sanin da ya mana ina iya shawartarka akan al'amura har na cikin gida ma kuma ka yi aiki da ita, ya fad'a min ne ba dan tunanin zan saka ka dole ba, sai dan cewa kamar ina da mahimmanci da kima a wajen ka da zan iya nemawa wani alfarma a wajen ka, sannan ni a gani na ba wani abu bane idan an mi shi auren, matashi kamar Nura ya kalli iyayen shi yace ya na son aure, ina ga a mi shi auren shi yafi kwanciyar hankali."

Har k'asan zuciyar shi maganganunta sun ratsashi, amma saiya dake yace "Me Nura ya sani a game da aure da za ayi mi shi? dan ya na da abinyi ba shi ke nuna zai iya rik'e mace ba."

"Amma ai ko neman auren ya tafi daga cikin tambayoyin da za'a masa akwai son sanin abin da yake, hakan kuma nasara ga d'an uwan mu da ya zamana ya na da aikin yi, ko ba komai zai ciyar da ita, zai shayar da ita da tufatar da ita, sannan ina da yak'inin zai kula da ilimin ta ko wane iri ne, sannan zai iya biya mata buk'atar ta."

Saida taji sautin sauke ajiyar zuciyar shi a kunnenta kafin yace "Bansan me ya fad'a mi ki haka ba da ki ka yarda da shi, gashi har kinsa nima na ji banda wata hujjar hana shi auren, ki fad'a ma sa na amince, amma dole ya jira ni na dawo sai ayi duk wacce za ayi, idan kuma ba zai iya jira ba sai ya turaki ki nemo masa auren."

Ya na fad'a ya kashe wayar, ita kam dad'i ne ya sata bushewa da dariya saboda abin da ya fad'a a k'arshe, wayar Nura ta kira ta fad'a ma sa yanda su ka yi da shi, sosai ya yi murna tare da binta da addu'a Allah ya barta da yayan su, suna gama waya ta ji wayar Bilal na k'ara, hannu ya sa a aljihu ya fito da ita ya d'auka, take ta fahimci Abban shi ne ya kira shi, suna nan zaune Hajia ta shigo gidan da sallama saboda ganin su, da farin ciki Khadija ta mik'e ta tarbe ta tana mata sannu da zuwa su na gaisawa, Bilal ma saida su ka tab'a hira irin ta kaka da jika kafin ta kalli Khadija tace "Ina yer uwar ta ki ta na ciki?"

"Eh Hajia su na ciki."

Nufa b'angaren ta yi ta na fad'in "Bara mu gaisa."

"A fito lafiya." Cewar Khadija, ta na shiga su ka gaisa kafin ta tambaye ta sun ci abinci ai? Eh, shine amsa da su ka bata, kallon Aziza ta yi tace "Ke ki zauna gidan to, ke sai ki tashi mu koma asibitin."

Dama a shirye take, hijabi kawai ta saka suka fito tare da Hajia da ke rik'e da katin likita a hannu, "Hajia har kun fito? Gida za ku tafi ne?"

"A'a." Ta fad'a kai tsaye, ganin Haseenah tare da ita ya bata mamaki, musamman da taga ta na gaba ta na binta, "Hajia lafiya kuwa? Ko ba ta da lafiya ne?"

Sai kawai Hajia ta ji haushin wannan tambayar, bud'ar bakinta cewa ta yi "A'a lafiyar ta k'alau, akwai in da za mu ne."

Da ido kawai ta bisu ta na mamakin kamuwar Hajia ita ma da wannan cuta ta 'ya'yan ta, ido kawai ta zuba mu su har suka dawo lokacin ta na madafa ta na girki, lokacin ne kuma 'yan uwan Haseenah da ma 'yan uwan Usman d'in suka fara zuwa ganin ta, ita dai ta na kammala girki ta fitar mu su ta bayar aka kai, sai dai ta yi niyyar ko ciwon ajali ne Haseenah keyi ba za ta je ta duba ta cikin mutane, tunda ta lura b'oyewa ake ba asa ta sani saboda tunanin wani abu.

Da yamma Haseenah ta karb'i girki, amma 'yan uwan ta ne suka shigar madafar suka yi yanda su ke so, sai dare su ka bar gidan Khadija ta shiga dan samun abin da za su ci, yanda ta ga madafar abin ya bata mamaki da dariya, saida ta gyara ta sosai kafin ta samu abin da za su ci, ko da su ka kammala suka kwanta abin su.


*Hummmmmmmmmm.*

Tunda asuba Khadija ta shirya tare da Bilal suka yi karin kumallo, sai da ta kira Usman tace ta na si ta aje Bilal a gida, amma sai yace "Me ye haka Khadija? Gidan nan fa akwai mutane, ya ki ke so ki nunawa yaron banbanci a zahirance."

"Shikenan ka yi hak'uri." Ta na fad'a ta kashe wayar ita ma, zuwa k'arfe *07:15* suka fito, saida su ka shiga d'akin Haseenah da sallama suna falo ita da Aziza ita ma ta na shiri, "Antashi lafiya?"

"K'alau." Cewar Haseenah, Aziza ce tace "Ina kwana."

"Lau." Cewar Khadija, kallon su ta yi tace "Dama zan tafi Tessaoua ne wajen biki, na kulle d'aki na, ga kayan Bilal idan an dawo da shi sai ya canza wannan, sai na dawo."

Hannun shi ta kama su ka fita, Aziza kam cewa ta yi "Ka ji matar nan sai ka ce akwai bawanta anan d'in."

"Ke kuwa miye a ciki? Bilal ai d'an mu duka, Allah dai ya kaita lafiya."

Saida ta gama shiri suka karya tace"Idan na tafi zan tsaya gida na wuni, na san dai saida dare ko na dawo gida."

Da haka su ka yi sallama ita ma ta tafi makaranta, Khadija ma ko da suka isa Ashir ne ya kai su makarantar duka, su kuma zuwa tara Naseer ya d'auke su suka tunkari *Tessaoua*.


*Me kuma zai faru yanzun?*
16/02/2020 Γ  13:20 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘


_SAMIRA HAROUNA_


*Litattafan marubuciyar*


*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._

*SADAUKARWA GA*

_MATAN FARKO_ πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)*


πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

```Fatan alkairi masoya```


_Bismillahir rahamanir rahim_




Please Login or Register in order to submit comment