Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*27*


Sha biyu Ashir ya d'auko su Bilal, suna hanya Khadija ta kira shi su ka gaisa, gida aka aje shi kafin suka wuce, k'ofa mai gadi ya bud'e masa ya na fad'in "K'aramin Alhaji har an taso?"

"Eh, ya aiki?" Ya fad'a da fara'a, shi ma da fara'a ya mayar masa da "Alhamdulillah."

Ciki ya shiga kai tsaye kuma b'angaren Haseenah ya wuce tunda yau ita ce maman shi, sallama ya dinga rabkawa amma ya ji shiru, saida ya bud'a k'ofar falon ya shiga kad'ai ya ga takalma alamar bak'i amma kuma ba kowa a falon, kujera ya samu ya zauna ya ciro wayar shi ya na dannawa da chocolat a hannu ya na sha, minti talatin ya d'auka a falon sai dariya da shewar su Haseenah ita da Zeinab wacce daga makaranta take ita ma ta ratse nan, tashi ta yi ya nufi d'akin na ta ya k'wank'wasa k'ofa duk da bud'e take, shiru su ka yi kafin tace "Waye?"

A hankali ya yaye labulen ya kalle ta yace "Aunty sannu, ni ne."

Fuska a d'aure tace "To, yaushe ka shigo gidan?"

"Na jima zaune a falo, yanzu ma dan na ce ku bani kaya na ne zan canza wannan."

"Ka je idan na fito zan baka kayan." Ta fad'a ta na mayar da hankalin ta kan Zeinab, har ya juya zai fita tace "Kai zo nan."

Dawowa ya yi jiki a sanyaye ya tsaya gaban ta, kud'i ta mik'o mi shi tace "Ka wuce maza kaje ka siyo min katin waya na airtel."

"To." Ya fad'a ya na karb'ar kud'in ya fice, ta k'aramar k'ofa ya bi zai fice mai gadi yace "K'aramin Alhaji fita za ayi?"

"Eh." Kawai ya fad'a a tak'aice ya na zura duka hannayen shi biyu cikin aljihun doguwar rigar shaddar shi wacce ka na gani kasan ta ji kud'i, a k'afa ya taka har ya iso bakin titi, ya jima tsaye kafin ya samu ya tsallaka saboda akwai ababen hawa sosai a wajen musamman da ya zama ranar farko ta komawa makaranta, siyowa ya yi ya dawo gidan ya kawo mata, falo ya dawo ya zauna amma bai jima ba aka fara kiran sallah, tashi ya yi ya fita a panpo na daf da shigowa gidan ya yi alwala ya tafi masallaci, daya dawo wajen mai gadi ya zauna shi ya na sauraren redio shi kuma ya na kallon hanya, tsawon lokaci ya d'auka nan zaune kafin ya ji cikin shi na neman agaji, cikin gidan ya koma ya samu su Haseenah har yanzu a d'aki amma su na cin soyayyen k'wai da indomie, ga lemu a gefe suna korawa mai sanyi, cikin muryar tausayi yace "Aunty abi..."

Kallon da ta ma sa ne ya sa ya yi shiru, Bilal yaro ne miskili da bai cika magana ba, in kaji yawan maganar sa to da iyayen sa ne idan suka had'u, jin ya yi shiru ya sa tace "Me ye kuma? Kayan ka na ce ka jira ni na tashi sai na d'auko ma ka, ka gansu can gefen gado, banyi niyyar tashi ba yanzun."

Juyowa ya yi ya sake fitowa daga d'akin, Zeinab ce tace "Kin bashi abincin shi?"

"Wannan d'in?" Ta nuna Bilal da ya fita da yatsa, d'orawa ta yi da "Ai munafiki ne da ki ke ganin shi kamar uwar shi, ba sa cin abinci na fa, yanzu in d'auka in bashi wani abu ya faru ace ni ce, yanda duk na ke k'ok'arin jingina mata laifukan nan ai kinga kashina ya bushe, kuma wallahi ni har ga Allah ma na manta da ya na gidan."

Da haka su ka ci gaba da hirar su Bilal kuma na fita ya samu mai gadi shi ma ya gaji da jira ya siyo wake da shinkafa, a hallitar Bilal bai tab'a cin wake da shinkafa ba, amma yau da ya ke jin yunwa sosai kuma mai gadi yace su ci, sai kawai ya sa hannu su ka ci abincin tare, saida su ka gama su ka sha ruwa, sun d'an fara tab'a hira Bilal ya ji cikin shi ya fara k'ullewa, a hankali ya fara dafe ciki ya na d'an matsa shi, amma sai abun ya fara k'amari sosai, mik'ewa ya yi kawai ya koma cikin gida kai tsaye madafa ya nufa, jar kanwa ya samu ya samu kofi ya sa ruwa ya jik'a yasha kamar yanda wani lokacin idan cikin shi na ciwo maman shi ke bashi, har zai fito sai ya ji ciwon ya fi na baya ma, dafe ciki ya yi sosai ya na murd'awa har ya sulale k'asa, jin azabar ciwon na k'aruwa ya sa shi tafiya wajen Haseenah, falo ya same su wannan karan su na kallo ana hira, a dafe da ciki ya tsaya gaban ta yace "Aunty ciki na ke ciwo, dan Allah ki bani magani idan ki na da?"

A wulak'ance ta kalle shi tace "Cikin ka kuma? To miye a ciki ya wuce kayan zak'in da kullum uwayen ka ke siyo ma ka ne ka na had'iya, sune kawai za su tambaye ka, ni ba na da magani."

Ganin idon shi cike da hawaye ne ya sa ta d'auki kud'i ta mik'a mi shi tace "Je ka siyo maganin bakin titi sai ka sha."

Karb'a ya yi ya fita ya na duk'e-duk'e, mai gadi na ganin haka yace "K'aramin Alhaji lafiya ka ke, ya na ga ka na dafe ciki? Ko ciwo ya ke ma ka."

Cike da k'aguwa yace "Ba komai." Ya wuce abinshi, da k'yar ya kai kan shi shago ya siyo maganin ya juyo ya dawo, madafa ya zarce ya samu ya sha maganin sannan ya wuce d'akin Haseenah, kwance ya yi bawan Allah akan kujera sai Haseenah tace ai ya sauko daga kan kujera ko ubanshi bai tab'a kwance anan ba, k'asa ya kwanta babu ko tapi (carpet) shinfid'e in da ya ke.

Ko dare Haseenah ba ta yi girki ba ta na hutawar ta, Bilal na gefen ta kwance ya galabaita dan babu abin da ya yi sauk'i daga ciwon cikin, sai ma kumbura da cikin shi ya yi kamar zai fashe, hakan ya sa zazzab'i sauko mi shi mai zafin gaske, yamma lis ta kalli Bilal da ke ta rawar d'ari tace "Kai zo amshi nan ka karb'o mana salade wajen mutumin can na tsallaken titi."

Da k'yar ma ya iya bud'a idon shi ya kalle ta sunyi jawur, rarrafawa ya yi ya zura mata hannu ya karb'i kud'in da take mik'o mi shi, da wuya ya iya mik'ewa tsaye ya fita sai rangaji ya ke, k'wafa ta yi tace "Munafiki, ciwon k'arya ne ka ke k'irk'irowa saboda kawai ka jaza min masifa."

An fara kiran sallah magriba kenan sai ga Khadija ta sallamo gidan, daga jakar ta sai ledar da tayowa d'an gudaliyar ta tsaraba, kai tsaye b'angaren ta ta fara bud'awa ta shiga, uwar d'aki ta shige ta cire kayan jikin ta ta saka doguwar riga ta atamfa, lokacin kuma Aziza ita ma ta sallamo gidan dan Hajia tace ta zo ko aiki ta kama ma Haseenah, zaune ma ta same ta tace ba ta d'ora komai ba, amma ta bada a siyo mu su salade su ci, Khadija kuma jin shiru ba motsin d'an gudaliya ya sa ta sallamo falon Haseenah, "Sannun ku da hutawa."

Haseenah da gabanta ya shiga fad'uwa dan ta d'auka ma can za ta kwana, Aziza ce kad'ai tace "Sannu aunty Khadija, har kin dawo?"

"Na dawo yanzun nan, ya gida?" Ta tambaya ta na kai kallon ta kowace kusurwa na falon, kallon Aziza ta yi tace "Wai ina Bilal? Ko ba'a dawo da shi ba."

Cikin rashin sani Aziza tace "Eh...to, ban dai..."

Jin kakarin amai a k'ofar d'akin ne ya sa Aziza yin shiru yayin da Khadija ta fita da sauri dan ta gane ko muryar waye, da sauri ta rumgumo shi jikin ta duk da aman da ya ke bulalowa, take idon ta suka kawo ruwa ta kalle shi tace "Bilal, me ya same ka? Me ka ci ka ke amai haka? Lafiya?"

Da k'yar ya iya kallon ta da ido dishi-dishi cikin muryar galabaita yace "Mummy, ke ce? Ki kai ni likita Mummy, ciki na ciwo ya ke."

Kuka ta fashe da shi ta manna kan shi a k'irji kamar za ta bashi nono tace "Bilal me ya same ka? Halan ka ci wani abu da ya b'ata ma ka ciki?"

Shiru ya yi sai numfashi da ya ke saukewa na wahala, fitowar su Aziza da Haseenah ne ya sa ta kalle su tace "Na d'auka za ku kula da shi ba sai na ce na bar amanarshi a hannun ku ba, amma shine ku na kallon shi a wannan halin, ya yi kyau, ki bani makullin mota na kai shi asibiti." Ta fad'a ta na kallon Haseenah.

Cike da gadara Haseenah tace "Ki yi hak'uri, gaskiya ba zan iya baki makulli ba, ko da ya bar shi a hannu na baice na ba ki ba, cewa ya yi idan buk'atar aiki ta tashi da mota sai ayi, kuma akwai wanda zai dinga fita da su."

D'auke kan Bilal ta yi daga k'irjin ta cikin hushi ta mik'e tsaye tace "Ina tunanin na jima da fad'a mi ki ba na so ana min wasa da d'ana, wallahi ba ke ba ko Usman ne ba zan lamunci ya min wasa da lafiyar shi ba bare ke, domin kuwa har yanzu shine kad'ai gare ni, shi kad'ai na mallaka a duniya sab'anin Usman da zai iya haifar wasu yaran da wasu mata, misali ke, dan haka ki ban makullin mota yanzun nan kafin kisa hankali na ya bar jiki na miki dukan mutuwa a gidan nan, kinga sai ayi biyu kenan dan na fahimci so ki ke ki kashe min d'an nawa."

Jin haka ya sa Haseenah juyawa ta koma falo, da sauri Khadija ta biyo bayan ta tasha gabanta ta shak'i wuyan rigar ta, janta ta yi har saida ta kai ta d'akin ta ta wurga ta kan gado tace "Maza tashi ki d'auko makullin ki bani."

Haseenah da ta ji mararta ta d'aure kasa tashi ta yi sai dafe mara, hakan ne ya sa Khadija cire d'an kwalin atamfar dake kan ta ta d'aure k'ugu da shi tace "Na rantse mi ki da Allah idan ba ki tashi kin d'auko min ba ko, wallahi gidan nan sai dai ya kama da wuta amma banga wanda ya isa ya shiga tsakani na da ke ba, Haseenah yaro na ne fa kwance babu lafiya, ga abin hawa a cikin gida kuma na iya sarrafa shi amma ki ce ba za'a hau ba, ba dan larura ce ba ma ni ko kallon motar na sake yi bare har na yi sha'awar hawan ta, dallah ki tashi ki d'auko min."

Jiki na rawa Haseenah ta mik'e da k'yar saboda sosai ta ke jin ciwo a marar ta, d'aukowa ta yi ta mik'a mata ta fizga ta juya za ta fita tace "Lokaci zai zo da za ki gane mahimmancin d'a da kuma zafin haihuwa."

Ta na fitowa k'ofar d'akin ta yi karo da Aziza da ta k'i shiga saboda tsoro, saida ta kwance d'an kwalin ta ta d'aura akai ta kalli Aziza da kyau tace "Aziza ba ni ki ka cutar ba, kan ki kika cutar, ba ni ki ka azabtar ba, d'an ki kika azabtar, hak'ik'a na ji ba dad'i a zuciya ta, amma ki sani bai kai wanda d'an d'an uwan ki ya ji ba, wannan yaron ko d'an mak'wabta ne ina tunanin zai iya samun tausayin ku a matsayin ku na 'yan adam kuma mata masu d'aukar ciki da haihuwa, amma kash an rasa wannan tausayin daga gare ku ba dan komai ba sai dan kawai ku na so wai ala dole sai kun cuzguna min, to bari na tuna mi ki wani abu, Bilal d'an ki ne domin kuwa ciki d'aya ku ka fito ke da mahaifin shi, Aziza rayuwa ba ta da tabbas, watak'ila wannan yaron da ki ke nunawa k'iyayya yanzun sai kin fini cin moriyar shi ni da na haife shi, idan ki na ganin kamar zanji zafi saboda kun cuta mi shi, to ki sani fa ku sai kun fini cutuwa, domin wannan yaron d'an uwanku ya na son shi fiye da komai a rayuwar shi, sannan abu d'aya da ku ka manta shine, ko a makaranta ana kiran shine da sunan *Bilal Usman Ali* ba wai *Bilal Khadija*, da yau mahaifin shi zai fad'i ya mutu, to ko shakka babu ke d'in nan Aziza zaki fini iko da shi ta wani b'angaren, da ace yau zanje nemawa Bilal aure a wani gidan, daga cikin tambayar da za'a mana ita ce *ina dangin mahaifin shi*? Domin kuwa kune shak'ik'an shi, kuma wallahi ina tabbatar mi ki ke d'in nan kawai idan na nuna a matsayin k'anwar mahaifin shi zai iya sawa a bamu aure, dan haka ku farka daga baccin da ku ke, duk abin da kukawa Bilal zai koma kan ku ne da d'an uwanku, ke ma kuma mace ce, nan da wani lokaci za ki yi aure kije gidan miji, ba zan mi ki fatan samun matsala a gidan auren ki ba, amma zan so ko na wuni d'aya ne ki fuskanci irin rayuwar da na fuskanta a dalilin ku, kinsan me Aziza? Na fi jin zafin juyawar bayan ki a kai na fiye da sauren 'yan uwan ki, kinsan me ya sa? Saboda ke ba baya kad'ai ki ka juya min ba, har da cin amana da yaudara, Allah ya ganar da ku gaskiya, za ku gane waye ya mallake d'an uwan ku."

Da sauri ta juya ta koma kan Bilal da ke kwance k'asa har yanzu, da gudu ta d'auko mayafin ta ta d'auke shi tasa mota suka bar gidan, asibitin da aka kai Haseenah ta kai shi, saida suka ciri tikitin ganin likita kafin suka samu aiki, bawan Allah saida aka saka mi shi k'arin ruwa sannan ya sabu bacci, kan shi na kan k'afafun Khadija ta na shafa kan shi, hawaye ta ke saboda tunanin irin halin da d'an ta ya shiga saboda wata tsinanniya a cewar ta, Habeeb dake ta faman kiran wayar Bilal dan su gaisa ne amma ba'a d'agawa, hakan ya sa ya kira Khadija sai lokacin suka san abin da ke faruwa, kafin ki ce kwabo asibitin ta samu hallarar 'yan biyar da mahaifiyar su, iya abin da ta sani kawai ta fad'a mu su, saida Bilal ya farka a bacci ne ya kora mu su jawabin duk abin da ya faru tun daga zuwan shi gidan har wannan lokacin, kuka Khadija ta yi sai Mama ke bata hak'uri, haka dai dare ya yi ko da ruwan suka k'are aka sallame su suka koma gida.

*Bayan fitar* Khadija sosai Aziza taji ba dad'i tare da jin nadama, amma bata gama gane halin da take ciki ba taji ihun Haseenah daga d'aki, sosai Haseenah ke murk'ususu tana kiran cikin da marar ta, waya Aziza ta d'auka ta kira Hajia ta fad'a mata, ana sallah isha'i Hajia ta zo gidan dan ganin lafiya, amma ganin irin azabar da take sha ya sa ta tambayi dalilin abun, Aziza ba ta yi magana ba sai Haseenah ce tace Khadija ce ta yi niyyar kashe ta yau a gidan, saboda kawai tace ta bata makullin mota tace Usman bai yarda ba haka kawai, ran Hajia ne ya b'ace saida Aziza tace " Amma fa likita tace za ta kai Bilal da ba shi da lafiya."

Cikin b'acin rai Hajia tace "Daga haka kuma sai tace saita nemi kashe ta, yanzu dubi ta'asar da take shirin yi."

Kama Haseenah ta yi suka tashi aka tafi asibiti, adaidaita na aje su suka shiga ciki, Aziza kad'ai ta lura da motar Khadija a k'ofar shiga amma banda su da basa hankalin su, saida akawa Haseenah Γ©co aka duba cikin na ta, a cewar likitan "Cikin ta lafiyar shi k'alau, amma fa a kiyaye dan yanzu haka jijjiga ce ta sa take jin wannan ciwon, ayi hankali sosai in ba haka ba cikin biyu za ayi d'aya, ko dai cikin ya zube ko kuma ya bar mahaifarta ya koma bayan mahaifa, dan haka a kiyaye sosai."

Nan aka rubuta mu su magani za su koma gida Aziza tace "Hajia kinga motar aunty Khadija har yanzu su na nan, mu shiga mu ga jikin Bilal mana."

A tak'aice Hajia tace "In ke za ki shiga ban hana ki ba, ni ma ai marar lafiyar na kawo."

Ba dan ta ji dad'i ba suka wuce gida bayan sun siye maganin a pharmacie, Hajia da kan ta ta fad'awa Usman halin da ake ciki, kuma yanda take magana zai nuna ma ka cikin hushi take, shi ma dai tunzura ya yi har yace "Zan shigo garin gobe, ba zan yarda da wannan iskancin ba dan naga abun nata rashin mutumci ne."

"Ai kam dai gwara ka yi ka dawo, dan nima na fara gajiya da wannan al'amarin." Aziza da jikin ta ya yi laushi ce ta kalli Hajia tace "Amma Hajia fa makullin mota kawai ta amsa ta kai yaro asibiti, me ye laifi a ciki?"

"Yarinya ce ke Aziza, ba wai makullin kawai ta amsa ba, ta so ace tsotsayi ya gifta cikin jikin ta ya zube, dan haka gwara ya zo ya wa tubkar hanci."

Saida su Ashir suka rankosu har gida, canzawa Bilal kaya ta yi sannan ta kwantar da shi akan gadon ta, ita ma shirin baccin ta yi su ka kwanta bayan ta jima tana tofesu da addu'a.

*Washe gari da safe* Gidan kamar ana wani sabga, dangin Khadija sun hallara dan ganin jikin Bilal, dangin Haseenah ma da dangin Usman sun hallara dan ganin jikin ta, duk da kowa na b'angaren da ya kawo shi amma ka kan iya jiyo hayaniya ta ko ina, a lokacin ne kuma Usman ya diro garin ba dan ya shirya zuwa ba sai dan amaryar shi na wani hali.

*Allah kare k'aramin yak'i.*
17/02/2020 Γ  21:31 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘


_SAMIRA HAROUNA_


*Litattafan marubuciyar*


*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._

*SADAUKARWA GA*

_MATAN FARKO_ πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)*


πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›

```Fatan alkairi masoya```


_Bismillahir rahamanir rahim_


*28*


Saida ya fara ganin Haseenah ya tabbatar komai lafiya kafin ya nufo wajen Khadija da nufin bala'i, ya na shigowa falon sai ya yi sanyi ganin mutanen dake d'akin, a hankali yake takawa ya na kallon Bilal dake k'afafun Mama ta na bashi magani, Khadija ma da mamaki take kallon shi kamar ba ta tab'a ganin shi ba, da sauri ya k'arasa ya zauna gefen Khadija ya na fad'in "Yarima, bashi da lafiya ne? Me ya same shi?"

Shiru Khadija ta yi sai Mama ce tace "Bashi da lafiya ai tun jiya, amma da sauk'i sosai."

Hannu ya zura ya kamo shi kamar d'an shekara biyar haka ya rumgume shi a k'afafun shi ya na shafa shi yace "Yarima ba ka da lafiya? Ya jikin na ka da sauk'i ko?"

Da kai kawai ya ma sa alamar eh, rumgume shi ya yi a jikin shi ya kalli Khadija yace "Amma ya akayi ba ki kira ni kin fad'a min ba?"

Cikin hushi tace "Saboda kai ne silar shigarshi wannan halin, kuma ma naga me za ki yi mana idan na fad'a ma ka? Tunda ba damuwa ka yi damu..." Da sauri Mama ta kalle ta tace "Khadija."

Kallon Mama ta yi ta na kumburo baki, Mama ce ta d'ora da "Subhanallah, Khadija haka ki ka koma magana da mijin ki? Ki na hauka ne?"

Shiru ta yi sai Usman da ke murmushi ya kalle ta yace "Me ya sa ki ka yi tunanin haka? Taya zan zama sila baya bana nan."

Shiru kawai ta yi saboda Mama ta mata magana, mik'ewa Mama ta yi ta d'auki gyalenta ta yafa ta d'auki jaka ta kalli su Naseer dake gefe kamar sun zo neman aure tace "To sai ku tashi mu tafi ko, ko kuma nan za ku tabbata?"

Mik'ewa su ka yi a tare da d'ai d'ai suka bawa Usman hannu su ka yi sallama kafin su ka fita, ta na ganin fitar su ta kalle shi tace "Dama na bar Bilal gida ne saboda umarnin ka, amma ka sani ba zan sake wannan kuskuren ba wallahi, tunda dai na gama lura matarka ba imani ne da ita ba, sannan daga yau wallahi ba zan sake d'agawa kowa k'afa ba, duk wanda yace zai min kan kara to tabbas sai nai masa na itace."

Mik'ewa ta yi saida ta zo gaban shi ta karb'i Bilal ta d'ora a kafad'a saboda k'arfin halin kafin ta nuna shi da yatsa tace "Da nace kowa ina nufin kowa ma, ba sauk'i a al'amarin."

Za ta juya ne taji sallamar su Hajia da sauren yaranta mata biye da ita, tsaye ta yi ta na kallon su har su ka k'araso su ka zauna, Hajia ce ta kalli Bilal da ke kafad'ar ta tace "Kai namijin duniya ya jikin na ka?"

Wani irin mamaki ne ya bayyana a fuskar Khadija ta sunkuya ta aje Bilal ta kalle ta da kyau tace "Hajia, ya jikin shi fa ki ke tambaya? Hakan na nufin dama kinsan ba ya da lafiya amma shine bai samu kimar da za ku zo ku duba shi ba tunda ku ka shigo gidan nan, tunda rana fa na ke iya jiyo hayaniyar ku a gidan nan, amma sai yanzu za ku zo ku tambaye ni lafiyar shi, hum, to ba ni ku ka wa ba, kan ku kuka wa."

Juyowa ta yi ta d'auki Bilal za ta wuce d'aki Aziza tace "Aunty Khadija ga kayan shi in ji Haseenah."

Juyowa ta yi fuska a had'e tace "Bilal na da kayan da a shekara baya saka su, ku mayar mata ta mayarwa da bokan nata tace ba ma so."

"Khadija, wai baki da hankali ne? Ke kad'ai ki ka fi kowa baki anan da za ki zaunar da mu ki na fad'a mana magana, so ko ke kice dole ke ce akawa laifi kenan bayan duk abin da ki ka aikata, me ki ka d'auke ni ne da har za ki tsaya ki na fad'awa 'yan uwa na magana kuma daga ciki har da mahaifiya ta, ko kinsan da hushin ki na dawo garin nan? Amma shine za ki nuna ke ce ma akawa laifi, to ya isheki haka, maza wuce ciki zan zo na same ki."

Yanda ya ke maganar ne ya sa ta yi dariya tace "To ka had'iye ni mana kaga shikenan sai ka huta."

Ta na fad'a ba ta tsaya sauraren shi ba ta shige ciki da Bilal a hannu, tana shigewa Hajia tace "Haka kuma abin nata ya zama? Lallai mutum bashi da kama, yanzu waye zai iya cewa Khadija za ta yi abin da ta yi."

Rabi'a ce tace "Hum, dama ai sai anyi yunwa halin kowa ke fitowa."

"Gaskiya ne, yau na tabbatar da hakan." Cewar Hajia, Usman ne ya kalle su yace "Hajia ku yi hak'uri dan Allah, kar ku damu da abin da ya faru."

"Ya kar a damu, ba ka ji maganganun da ta fad'a mana bane, nan gaba mu ka san me za ta fad'a ko ta yi mana, za ta iya cewa ma Bilal d'an ta ne ita kad'ai."

Mik'ewa su ka yi su na fad'in "Sai anjiman ku."

Tafiya su ka yi Aziza ta koma wajen Haseenah, shi kuma d'akin Khadija ya koma, ya na zuwa ta kwantar da Bilal yace "Ya kamata kisan ina d'aga mi ki k'afa ne saboda abubuwa dayawa, amma naga sam kin kasa fahimta sai ma son wuce gona da iri, Khadija wannan fa mahaifiya ta da ki ka tsaya ki ka fad'a mata magana son ran ki, me ki ke ji da shi? Rashin kunya ko fitsara?"

Tsaye ta mik'e tace "Kalle ni da kyau kaga da me ya kamata ka kira ni."

Da yatsa ya nuna ta yace "Na zo ne dan na fad'a mi ki wani abu, wannan ya

Please Login or Register in order to submit comment