Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya cin tuwo a lokacin da ke kad'ai ce cikin gidan, yanzu kuma Haseenah ta shigo, dan haka ki barni na yi rayuwa ta mana, ki barni ni ma na kafa salon nawa tarihin a gidan nan kuma a zuciyar miji na, amma ba ki dinga min shishigi ba, ba lallai dan kin saba mi shi da saka kalar fari ba ki ce nima wannan kalar ki ke so na saka mi shi, ki barni na yi abin da ya dace, nan gidan miji na ne."

Wani warrr Khadija ta yi da manyan idon ta kafin ta sa hannun ta tana fifita da shi tana fad'in "Wash Allah, zafi."

Kallon Haseenah ta yi da murmushi tace "Sannu mai miji, Allah ya bar k'auna."

"Ameen." Ta fad'a har da zaburowa, fita Khadija ta yi, tsaf Haseenah ta gama tuwonta ta mulmule, da kan ta ta kawowa Khadija na su tuwon, ko k'ala ita ma ba tace da ita ba har ta fita, Uwani ce ta tashi tafiya tace "Uwani d'auko wani kwano a d'akin can ki tafi da abincin nan."

D'aya d'akin ta shiga da ke da tarkacai abubuwan buk'ata ta fito, juye tuwon ta yi ta tafi da shi bayan sun yi sallama, Bilal ne ya shigo gida shi kad'ai da takarda a hannun shi, rumgume maman shi ya yi ita kuma tace "Wa ya dawo da kai ne?"

" *Bilyaminu* ne Abba ya tura ya d'auko ni, Mummy karb'i wannan." Ya fad'a bata takardar, ta na dubawa tace "Har wata ya k'are kenan?"

Kai kaxai ya d'aga mata, ba shi ta yi tace "To ka aje wurinka idan Abbanka ya dawo sai ka ba shi, amma ni zan iya mantawa."

A tare su ka tashi ita ta shiga d'akin ta saboda magriba ta gabato sosai, kaya kawai Bilal ya canza ya wuce masallaci, Khadija ma na idar da sallah ta shiga wanka, shiryawa ta yi sosai kafin ta lalabi gilashin ta na jiya da Usman ya cilla kan gadon, dan tun jiya bata waiwaye shi, shi ta saka dan ya fi mata kyau sannan ta fito, zaune suke ita da Bilal su na kallo su na hirar su, bayan sallah isha'i ko da su ka yi sallah abincin ranar da Uwani ta kwashe mata a kula ta d'auko ta zuba, tare su ka ci hankali kwance su ka k'oshi, hamdala su ka yi kafin su ka tashi kamar ba su ci ba.

Kamar yanda ya yi alk'awarin komawa gida haka ya wuce, ya kuma samu su Kabir Mannir da Nura, hakan ya sa suka bud'a babin hira su ka dinga yi, Haseenah da ke jiran shigowar shi taga shiru sai da ta kai ga kira, amma sai ya d'aga yace ya na gida zai zo ba da jimawa ba, amma fa bai zo d'in ba saboda suna tattaunawa da ahalin shi, sai wajen *22:20* ya baro gidan ya nufi gida, Khadija har sun kwanta ita da Bilal ya shigo, ko da ya ga babu wuta a falon sai ya wuce falon shi kai tsaye, Haseenah na ganin shi ta d'ago kai ta kalle shi, ba fara'a ko sakin fuska tace "Sannu da zuwa."

Sai da ya kamo hannun ta tayi tsaye ya rumgume ta yace "Sannu da gida."

Kamar ba ta son magana ta amsa da "Yawwa."

Kallon fuskarta ya yi yace "Ki yi hak'uri na barki ke kad'ai ko? Ina can gida tare da yaran nan su na ta min shirme."

Cikin shagwab'a tace "Na ji to, yanzu dai mu je ka yi wanka sai ka zo ka ci abinci."

Rimgume ta ya yi yace "Wallahi kamar kinsan kam na d'ebo yunwa, muje ki kintsani yanda ya kamata."

D'akin shi su ka nufa, bayan ta taya shi wanka ya canza kaya su ka fito, ya na jan kujera ya kalle ta yace "Da alama su Bilal har sun kwanta ko?"

Kallon shi ta yi tace "Eh to ban sani ba dai, amma tun da na ji shiru babu hayaniyar tv na ke tunanin haka."

Ba tare da ya kalle ta ba yace "Haseenah me zai hana idan ba na nan ki dinga zuwa wajen su ki na zama ku na hira? Ina ga hakan ai zaifi ko? Tunda daga ke sai sune a gidan, kuma sune abokan rayuwar ki a yanzun."

Ta na aza marar tuwo a farantin ya kalle ta, bai kai ga jin amsarta ba yace "Haseenah tuwo ki ka dafa?"

Kallon shi ta yi tace "Eh, da matsala ne?"

Ya na ci gaba da kallonta yace "Khadija ta ga ki na aikin nan?"

Sam Haseenah ta ma manta da abin da Khadija ta fad'a mata, sai kawai tace "Eh, me ya faru?"

Da wani irin kallo yace "Kuma ba ta fad'a mi ki komai a game da hakan?"

"A'a, wai me ya faru ne?" Ta fad'a cike da k'aguwa, a hankali yace "Shikenan kawai, zo zauna nan."

Janyota ya yi ya zaunar da ita akan cinyar shi ya na kallon fuskarta yace "Haseenah, ki yi hak'uri kinji, ina ganin laifi na ne da har mu ka yi soyayya da kai ba tare da kinsan abubuwa da dama a kai na ba, kuma hakan ya samo asaline saboda ba mu jima tare ba, sannan ni mutum ne da bai cika fad'an abin da ya shafe shi ba, amma a gaskiya ni ba na cin tuwo da dare, ba kuma shi kad'ai ba, akwai abin da ma kwata-kwata ba na cinsu kamar wake da nasan sa, sannan kinga shinkafa ma ban cika son ta ba haka, sannan kifi ma ba na cin shi da dare, wannan shine."

Bushewa ta yi da dariya ta sauka daga cinyar shi taja kujera mai fuskantar shi, da k'yar ta tsayar da dariyar tace "Miji na, ka na d'an africa, a africar ma a niger, kuma ka ce ba ka son shinkafa, lallai ka na jin dad'in ka."

Ganin ta mayar da abun kamar wasa ya sa ya d'an gimtse fuska yace "Ni dai ban son ta, na fad'a mi ki ne dan ki kiyaye."

Ita ma had'e fuska ta yi tace "To yanzu tuwon nan fa ya zanyi da shi?"

Shima dariya ya yi yace "Ku ba kun ci ba? Kawai ki samar min wani abu na ci."

Cike da kasala tace "Kamar me fa?"

"Ko taliyarku ta yara ki d'ora min." Yanda ya yi maganar da zolaya ya sa ta taso ta na dariya ta rumgume shi ta baya ta na fad'in "Yanzu ni yarinya ce a wurin ka?"

"Sosai ma." Ya fad'a ya na dariya, cikin kunne ta rad'a ma sa "Ni kam banyi tsammanin za ka iya kira na da yarinya ba."

D'ago kai ya yi ya kalle ta yace "Shekarar ki nawa ne wai dan Allah?"

Saida ta waina idon ta tace "Sha takwas."

Da sauri ya mik'e tsaye ya na k'are mata kallo, har zagayata ya ke ya na kallonta, tab'e baki ya yi yace "Lallai ina da sa'a, gani tsoho amma sai Allah ya dinga had'a ni da yara yan sha takwas shakaf."

Juyawa ta yi ta nufi madafar, d'ora tukunya ta yi duk da ba wani sanin kan indomie ta yi ba, amma dai wani lokaci ta d'an dafawa yayan ta *Mubarak*, yanzun ma yanda take yi a gida haka ta dafa, sai dai da ta zuba a faranti sai ta ga abun bai birge ta ba, dan indomien duk ta dahu sosai kamar za ta narke, to amma ya ta iya haka ta d'auko ta kawo mi shi, dakewa kawai ya yi tamaza ya d'ura indomien nan, amma bai ci sosai ba, ya na gamawa ya mik'e yace "Zan lek'a na ga su Bilal."

Kallon shi ta hi ta kalli farantin indomien, k'ala ba tace masa ba ta tashi ita ma ta wuce d'akin ta dan shirin bacci, shi ma ficewa ya yi bai kula ta ba, d'akin Bilal ya fara shiga, sai da ya k'arewa yaron kallo ya shafi kansa kafin ya fito, da sallama ya shiga d'akin amma shiru, kujerar gaban madubi ya janyo ya zauna bayan ta ya daddab'a ta, bud'a ido ta yi ta tashi zaune ta janyo gilashin ta ta sanya, kallon shi ta yi shi kuma yace "Hajia Khadija ki na lokaci, yanzu har an daina sona ta yanda ba'a jira aga na shigo lafiya ko akasin haka."

Murmushi ta yi tace "Abban Bilal ma ya na lokaci, tun da har zai shigo gidan nan amma ya kasa neman mu."

Da mamaki ya bita da kallo ita kuma tace "K'warai, na ji shigowarka ai."

"Hum." Ya fad'a ya yi shiru, ita kuma tace "Ka daina mantawa, yanzu mu biyu ne da hakk'in kula da kai, in da lokacin kwana na ne zan iya jiran ka har gari ya waye."

"Amma in ba kwananki bane kuma ko oho ko?"

"Kai ma kasan dole zan damu da kai, sai dai ba na son shiga hurumin da ba nawa bane."

Mik'ewa ya yi ya nufi frije d'in ta ya bud'a, wani k'aton cake ya d'auko mai suffar zuciya tare da yagourt mai kauri da sanyi, komawa ya yi ya zauna ya fara ci ya na shan madarar, Khadija dai kallon shi take har ya sai da ya cinye duka kafin ya mik'e, ban d'akin ta ya shiga ya wanko bakin shi ya dawo, kallon ta ya yi yace "Umman Bilal ya yarinyar can ta fad'a min kinga lokacin da take tuwo ko?"

Gyara zama ta yi akan gadon tace "Eh, na gani."

"To amma me ya sa ba ki fad'a mata ba na cin tuwo ba? Tunda ke kin sani."

Da mamaki ta kalle shi tace "Au! Wai dama duk soyayyar da ku ka yi ba ka tab'a fad'a mata abin da ka ke so ba da wanda ba ka so? Dole sai ni ce zan dinga fad'a mata?"

Matsowa ya yi kusanta yace "A gani na ya zama dole tunda ke ce gaba da ita, me ya sa ba za ki d'ora ta a hanya ba a matsayinki na babba?"

Da k'arfi ta zaburo daga kan gadon ta sauko ta na fad'in "Oho, wato babba juji ko? Komai tunda ke ce babba ke ce babba, to daga yau na bar mata girman ta d'auka, kuma ka je ka tambaya ta idan ban fad'a mata ba ka cin tuwo ba, amma sai tace a dole ita ma sai ta d'ora ka a tsarin da ya mata, saboda ita ma matarka ce, haka kawai za ka zo ka d'ora min laifi ka cika ni da surutu."

Komawa ta yi kan gadon ta kwanta ta ja zani ta rufa, shi kam baki bud'e ya ke kallonta har ta kwanta, sunkuyawa ya yi ya sumbaci kumatun ta ya d'ago yace "Saida safe masifata."

Zunbur ta tashi tace "Masifar ka kuma? Abban Bilal ni ce ma masifar yanzu? Lallai ka kyauta."

Gimtse dariyar shi ya yi yace "To in ba tawa ba ta wacece? Ai Khadija sai Usman, Usman kuma sai Khadija, kinga dole na kiraki da masifa ta tunda na ga kin fara koyon masifar."

Cinno baki ta yi gaba ta bishi da kallo har ya kai k'ofa, sai da ya bud'e ya fita ya juyo yace "Allahya huci zuciyar Umman Bilal, ta Usman bada kanka a sare kaje gida ka ce ya fad'i, na Khadija ba ni shan furataba nono, hakan ya yi ko? Saida safe, ina son ki."

Dariya ce ta kubce mata, sumba ta aika masa tare da fad'in "Ina son ka ni ma, saida safe."


_Ni ma dai saida safen nan gaskiya._πŸ˜‰


*Washe gari* ta kama alhamis, hakan kuma ya sa duk yan islamiyya na hutu ba karatu, k'awayen Haseenah na su ka zo gidan tun misalin *11:00* bayan fitar Usman ba jimawa, in da Bilal ma ke gida ya na wasan shi, dan ya so ya je gidan su maman Khadija amma ta hana, a madafa suka tare su na ta hira abinsu, kasancewar *Zeinab* na da k'ok'arin aiki ya sa yau ita taja ragamar girkin gidan, abinci su ka had'a kala har uku da kuma abin sha, bayan sun gama su ka dawo falon Haseenah dan cin abinci, kiran Usman ta yi ya aiko a d'aukar mi shi abinci ta na da bak'i a gida, ba d'aukar lokaci ya aiko da yaron shi Bilyamin ya d'auka, su na ci su na kwamtsa hirarsu sai ga Mariya, sai da suka gama ta shiga da ita ciki inda ta kwashe komai ta fad'a mata, bud'ar bakin Mariya cewa ta yi "Lallai Haseenah ina tausaya miki, dan wallahi kishiyar nan ta ki ba k'aramar muguwa bace, kawai ki hak'ura ki bita sau da k'afa, domin kuwa ita da d'an ta ne da gidan nan wallahi."

Cike da damuwa Hassenah tace "Ni ma na fahimci hakan, kar ki tona raina ki ji me na ji ranar, ita ce da laifi amma ya rufe ido ya d'ora min laifin, wai shi ya san matan shi."

"Ai kad'an ma ki ka gani in dai ba ki tashi tsaye ba, yanzu dai ina magani da na baki? Kinyi aiki da shi?"

"Duka na yi, kuma ya ci abincin? Amma ni banga wani sabon abu ba."

Gyara zama ta d'anyi tace "Kinsan me zai faru, ki sake kawo kud'i a kaiwa malam ya sake mi ki wani maganin, ko da na bakali ne da kuma samun soyayyar shi."

"Kamar nawa?" Ta fad'a ta na kallonta, ita ma kallonta ta yi tace "Eh to, iya kud'in ki ai iya shagalinki."

Da alamar tambaya Haseenah tace "Ki na nufin idan na bayar da kud'i dayawa zaifi kyau aikin?"

"Sosai ma."

Mik'ewa ta yi ta bud'a jakarta da take zuba kud'in da yake bata tun da ta zo, yan biyar biyar ko karyawa babu guda hud'u ta bata, aifa baki har waje ta karb'a suka fito daga d'akin, sallama su ka yi ta tafi ta barta da k'awayen ta, yamma ta yi suka sake tashi kama mata aiki, sai dai suna buk'atar bredi dan soya shi da k'wai, babu yaron da za'a bawa ya siyo sai Bilal ta kira dake farfajiyar gida tare da mai gadi, kud'i ta bashi ya siyo mata bredi, cikin sanyin jiki yace "Aunty nan ba'a siyar da bredi sai can nesa tsallaken titi, kuma Abba ya hana ni fita har can wajen."

A gadarance tace "Kenan ba ka da wani anfani cikin gidan? Sai dai a dafa a baka ka ci? To k'arya ka ke, maza wuce ka d'auko wannan shegen moton na ka da baida anfani sai dai ka yi yawo da shi cikin gida ko k'ofar gida ka je ka siyo ka kawo min yanzun nan."

Cikin sanyi ya juyo ya nufo wajen uwatai, d'akin da ya ke aje moton ya fito da shi, Khadija na gani tace "To, to ina kuma zuwa da wannan tuk'a-tuk'ar?"

Sai da ya zo gabanta cikin turo baki yace "Ba aunty amarya ce ta aike ni siyan bredi ba."

Da mamaki ta kalle shi tace "Bredi fa? Amma ba ka fad'a mata ba ka tab'a zuwa ko bakin titi kai kad'ai ba bare gaban shi?"

"Na fad'a mata, amma tace wai ni ban da anfani a gidan sai dai na ci abinci, kuma wai dole na je na siyo."

Wata shegiyar dariya Khadija ta bushe da ita ta kalle shi ta kalli Uwani, mik'ewa ta yi tace "Ku biyo ni har da ke Uwani."

Fita su ka yi har madafar ta same su, sai shewa da hira su ke, suna ganin ta kowa ya yi shiru sai wani kallo ake mata, ko ta kan su bata bi ba ta kalli Haseenah tace "...


*Ku yi hak'uri da wannan.*
29/01/2020 Γ  13:36 - πŸ’‹πŸ˜˜πŸ’‹: πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘πŸ’‘



_SAMIRA HAROUNA_


*Littatafan marubuciyar*


*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._


*SADAUKARWA GA*

_MATAN FARKO_πŸ§•πŸΌ *(UWAYEN GIDA)*


πŸ‡ΈπŸ‡¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_πŸ€œπŸ€›


```Fatan alkairi masoya```




_INA K'ARA TAYA 'YAR UWARMU KUMA D'AYA DAGA CIKIN 'YAR GIDAN AMANA WATO MEMBER'S D'IN K'UNGIYAR *πŸ‡ΈπŸ‡¦ZAMAN AMANA* MAI SUNA *MARYARHMAH UMMISIDDIQUE* MARUBUCIYAR *MINTI KARU'NYI YE* DA KUMA *NAGA TA KAINA* TA'AZIYYAR RASHIN UWA MAHAIFIYA DA TAYI, INA ADDU'A GA UWAR KIRKI HAR KULLUM ALLAH YAKAI RAHMA K'ABARINTA, ALLAH YA K'ARA MANA HAK'URIN RASHINTA, MUNYI RASHIN UWAR K'WARAI😰_




_Bismillahir rahamanir rahim_


*17*


"Haseenah, ga Uwani ki bata kud'in ta siyo mi ki bredin, amma Bilal mahaifin shi ya hana a aike shi ko kusa da titi."

Sai lokacin ta juyo ta kalle ta tace "Yanzu kamar Bilal ne za ace ba'a aikin shi, shi kad'ai ne yaro cikin gidan nan, kuma ace ba'a aikin shi, to me ya sa? Me ye anfanin haihuwar shi kena..."

Ba ta sauka daga abin da za ta fad'a ba Khadija ta ji ba za ta iya d'auka ba, zuciya ce kawai ta d'ebe ta ta kife ta da mari, kafin ta ankara ta shak'o wuyan rigar ta cikin d'aga murya tace "In ke ba ki san zafin haihuwa ba ni na sani, in ba ki san darajar 'yaya' ba ni na sani tunda na haifa, idan ba ki san anfanin haihuwa ba, to ki bari har ki bari ki haifi na ki sai ki zuba cikin shara, dama ya fad'a min kin ce wai sai dai a dafa a bashi ya ci, to ki sani Bilal ba jinin matsiyata bane, ko gidan uban shi babu abinci ba zai rasa abincin da zai ci ba daga dangin uwar shi, ki kiyaye ni, sannan ki fita ido na."

Sakin ta tayi ta juya ta fice, Zeinab ce ta yi saurin kallon Haseenah tace "Wai k'yale ta za ki yi? Jar uban nan, ai wallahi babu macen da ta isa."

Wannan magana ce ta sa Haseenah d'aukar k'aramar tab'aryar da ke madafar ta fita, su na ganin haka su ka tashi da sauri su ka bi bayan ta, Khadija na daf da shiga falon ta Haseenah ta sauke mata tab'aryar nan a kai, dafe kai ta yi ta juyo ta na fad'in "Kai kai kai kai."

Ta na ganin Haseenah ce sai kuwa ta cakume ta da kokawa,πŸ˜‚ (Allah ya kyauta, mata mu na bawa kan mu wahala wallahi, wata sai ki ga ma mijin da su ke fad'a akai kamar kalangu, amma haka za su yi ta bala'i a kan shi maimakon kwantar mi shi da hankali), k'awayen Haseenah na ganin haka su ka shigarwa k'awar su saboda tuni aka aza Haseenah ga k'asa ana shirgarta, Uwani na ganin haka ta fita da gudu zuwa gidan mak'wabtan da Khadija ke abun arzik'i da su, Bilal kam wayar shi ya d'auka k'arama ya kira mahaifin shi ya fad'a mi shi, mai gadi na daga gefe ya na dan Allah ayi hak'uri amma ko jin shi ba su yi, jin zafin dukan da k'awayen ta ke mata ne ya sa Khadija finciko wata daga cikin k'awayen ta had'a su ta taushe, wuri fa ya kaure ana ta bawa hammata iska sai ga mak'wabtan sun shigo, da gudu su ka k'arasa su ka d'aga Khadija daga kan Haseenah da *Farida*, anyi jina jina sosai kamar filin yak'i, cecekuce aka shiga yi tare da aikawa juna ashar, Khadija na k'ok'arin k'wacewa ta koma ga Haseenah amma an rik'e ta, su na haka fa gida ya kaure Usman ya baro mota waje ya kutso ciki, ganin su duk a yamutse ya sa ya tsaya ya sa hannu ya rufe fuskar shi, ya d'an jima a haka kafin ya k'araso wajen, k'awayen Haseenah ya fara kallo yace "Yamma ta yi, za ku iya tafiya."

Cikin sanyin jiki duka aka watse aka bar shi da matan shi, har Uwani ma ba ta tsaya ba tafiyar ta ta yi gida, falon shi ya nufa ya na fad'in "Ku same ni a falo na."

πŸ˜‚ *Aiki ya samu Usmanu, yanzu ma ka fara cewa a biyo ka falo ai*

Su na shiga daga zaman da Khadija ta yi zai tabbatar maka ba arzik'i, cikin b'acin rai ya yi tsaye yace "Me ku ka zama? Me ku ke son mayar min da gida? Wannan wane irin dabbanci ne?"

Tsaye Khadija ta mik'e tace "Dakata malam, dakata min, a sani na irin haka ba ta tab'a faruwa ba, to akan me sai yanzu haka za ta faru? Akan me ye amaryar ka za ta nemi ta raina ni? Ni sa'ar ta ce? Ko kai ka ce ta raina ni? Saboda rashin sanin darajar mutane har ta bud'e baki tace min wai mi ye anfanin Bilal a gidan nan, bayan kin fad'a ma sa bai da anfanin komai sai dai a dafa a ba shi ya ci, to uwar ki ce ke dafa mi shi ya na ci? To ki kama bakin ki ki dinga sanin me za ki fad'a."

Mayar da kallon ta ta yi ga Usman tace "Kai kuma dan Allah idan kun shiga ciki ka yi k'ok'ari ka sanar da ita mahimmancin d'an ka gare ka da anfanin shi gare ka, ni ba buk'atar sai na fad'a mata anfanin d'ana gare ni, amma ka fad'a mata shi kad'ai gare ni, dan haka bana had'a yaro na da kowa da kuma komai a duniya, a matsayi na na uwa kuma zan iya yin komai saboda shi."

Ta na gama fad'a ta fice ta bar su, juyowa Usman ya yi ya na kallon Haseenah, a hankali ya furta "Haseenah, ki na tambayar anfanin haihuwar Bilal a gidan nan? Ni fa uban sa ne, duk fafutukar da na ke yi saboda shine na ke yi, amma ki bud'e baki ki ce me ye anfanin haihuwar shi."

Girgiza kai ya yi cike da damuwa ya dafe k'ugu da hannu d'aya yace "Maganar gaskiya Haseenah ba na so na nuna mi ki b'acin rai na, amma ki sani ko Khadija ba na buran b'acin ran ta bare kuma Bilal da ya fito daga tsatso na, ina k'aunar iyalin nan nawa matuk'a, su ne ni, su suka mayar da ni mutum da har ki ka so ni a haka, ki kiyaye furta abin da zai iya ja mi ki matsala, sannan k'awayen nan naki in har kinsan zuwan su gidan nan ba alkairi bane, to zaifi kyau ki fad'awa kowace ba na son sake ganin k'afar su a gidan nan."

Ya na gama fad'a shima ya fita ya barta, kallon shi ta yi a matuk'ar hassale ta mik'e ta nufi madafa, kashe wutar ta yi ta gyara abin da ya sawak'a ta koma d'akin ta, wayar ta ta d'auka ta kira Mariya ta fad'a mata duk abin da ya faru, nan dai ta girmama abin tare da k'ara tunzurata sannan tace ta bar komai a hannun ta, da haka su ka yi sallama ta yi wanka ta shirya, sai dai ba wata kwalliya ta yi ba dan duk jikin ta ma ciwo ya ke na tsinannan dukan da ta sha.

***************

Bayan sallah isha'i Khadija na zaune tare da Bilal a falo Nura ya shigo gidan da rahar shi kamar yanda ya saba, tun daga bakin k'ofa ya ke fad'in "Dije, Dije ba ta jina ne? Na shigo amma ki kasa tarba ta tun daga k'ofar gida."

Ganin Khadija zaune ta yi shiru sai kallon shi take ya sa yace "Ah lallai ma matar nan, ashe ki na jina na ke ta kwaroronton nan amma ki ka share ni? Ko dan yau ban baki kud'in cefanai ba?"

Khadija da har yanzu ran ta a b'ace ya ke k'ala ba tace mi shi ba, Bilal ne ya tarbe shi da murna sosai, tare su ka zauna ya na kallon Khadija ya kalli Bilal yace "Yaro waya tab'a min maman ka ne haka ta ke ta kumbura?"

Shiru Bilal ya yi ya na kallon ta, a hankali ta maido kallon ta gare shi tace "Sannu ko."

"Ai na ba za ki yi magana ba, da na tabbatar mi ki mijin gaske ne ni."

"Ya su Hajia?" Ta fad'a ba yabo ba fallasa, saida ya sauke ajiyar zuciya yace "Lafiyar su k'alau, kai kawo min lemu mai sanyi na sha." Ya k'arashe da kallon Bilal.

D'auko masa ya yi ya kawo ya ba shi ya amsa, sai da ya fara sha ya kalli Bilal yace "Ina auntyn ka take?"

"Ta na d'akin ta." Cewar Bilal ya na kallon k'ofar falon mahaifin shi, tura shi Nura ya yi yace "Je ka ce ina kiran ta, ka ce ta

Please Login or Register in order to submit comment