Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sunada yawa sosai ,a tsorace ta sauko ta nufi bayi kayanta tacire domin yin wanka da d'aura tawul zata wanke fuska ta hango wani abu ta cikin mirror d'in toilet d'in jikinshi duk gashi ,wayo Allah na tace ”lokacin da taga yana rikid'a izuwa halittu da ban daban ,k'ok'arin tunkarota yakeyi ta jikin mudubin tana gudu ,da sauri ta bud'e k'ofar ta fice ko kayanta bata tsaya d'auka ba ."



Khalil ne kwance a d'akin aminin nasa wato KB _KB ne yace ”mutumin na yanaga ka rame da yawa ko madam bata kula dakai ne ¿"murmishin yak'e yayi yace ”wlhi 'ina cikin tashin hankali abokina , dadyna yak'i fahimtata 'akan yarinyar nan gashi tana bala'in sona kuma nima haka , KB ne yace ”to abokina mezai hana ka rabu da ita kawai ka hak'ura da matarka , cikin fusata Khalil ya cakumo wuyan KB yace ”bakada hankali ne kana nufin yarinyar da tazamo.jinin jikina in barta kenen , wasu zafafan hawaye suka zubo a fuskar Khalil ,ya sake KB yace ”kaima bazaka fahimceni ba? ashe babu mai sona sai mahaifiya ta dakuma budurwa ta abokina ba bai damu dani ba ,wayo Allah ,yana kuka mai ban tausayi cikin tausayawa KB ya kama kafad'ar Khalil yace ”abokina karkace haka matsalarka tawace ka zamo jarumi ina tare dakai Khalil ,suka rungume juna cikin so da k'auna ."


Yau kwanan su momyn Suhailat biyu da zuwa gurin boka , komai ya kwance mata batada wal wala ko kad'an gashi k'awayen sun gudu ,duk dan bata yarda da umarnin boka ba , tagumi ta zuba tace ”my daughter kota halin k'a k'a saina kwato miki y'ancinki a gidan mijinki, lalubo number wata babbar k'awarta da rabonsu da waya zasuyi shekara biyar , dalilin rabuwarsu da momyn Suhailat kuwa shine ,ita k'awar tata mai suna Baraka ta shiga harkar karuwanci ne shiyasa momy tayi watsi da ita , amma yau gashi tana nemanta ido rufe lalubar number Bakara momyn Suhaital tashiga yi cikin sa'a kuwa ta ganta danna kira tayi , tana ring amma ba'a d'aga ba ,sake kira tayi a karo na biyu , jin muryar baraka na nishi yasa momyn Suhailat cikin tsoro tace ”lafiya kuwa baraka?" Baraka dake shek'e ayarta tace ”lafiya momyn suhyy ykk wanan tsohonne ya dameni da jaraba , momyn Suhailat ce ta kawar da zancen ta hanyar cewa dan Allah temako zakiyimin , jim Baraka tayi can kuma tace ”to kibani 6 minutes innayi wanka zan kiraki , OK momyn Suhailat tace ”sukayi sallama ."



Nussy ce kwance a k'irjin wani k'aton arne ,cemasa takeyi 'inason zuwa Nigeria fa , cikin kulawa yace ”bakuda kowa 'a Nigeria gurin wa zaki ?"Nussy ganin tambayar tayi yawa yasata cewe nifa ba kud'i na tambayeka ba , rungumota yayi yace ”to koma nawane ai zanbaki masoyiyata nawa kike buk'ata , juya masa baya tayi ,kasancewar ba tun yanzu suke tare ba yasashi fahimtar abinda takeso da wanda bataso , d'aukarta yayi yakaita toilet yai mata wanka shima yayi ,yana fitowa ya shafa musu mai , suka shirya , super market suka nufa ta sisiyo abubuwan da take buk'ata , suka dawo, shikuma ya koma inda yake da zama kasancewar Nussy tace ”yayi mata shirye _shiryen komai gobe zata d'aga zuwa Nigeria."


Washe gari misalin 2pm bayan 'Nancy ta idar da sallah taji wayarta na ruri duba number gani takeyi kamar tasan 'number amma takasa gano ko number waye , d'agawa tayi tare da sallama , jin muryar anty Humaira yasata murna suka gaisa anty Humaira take tambayarta ya k'auye ?"Nancy ce tace ”ai run rasuwar hajiya ban koma ba ummana ma tadawo nan , cikin murna anty Humaira tace ”aikuwa zan kar6i address d'in inda kuke muzo , Nancy ce tace ”kinyi aure ne ? dariya anty Humaira tayi tace ”saura one week bikina wow Nancy tace ”insha Allah baza'ayi babu mu ba anty Humaira ce tace Allah ya kawoki amma zuwa gobe zanzo in gaida Umma to Nancy tace sukayi sallama ."


KOMAI NISAN DARE GARI ZAI WAYE 🤏.


Zaune take a jirgi tana sanye cikin riga da skirt na Pakistan ba k'aramin kyau tayi ba kannan yasha adon da indiyawa sukeyi fuskarta sanye da bak'in glass k'afarta na sanye da takalmi mai tsini , kunnenta na mak'ale da eyepiece , NUSSY kenan , babu wanda yasan da zuwanta sbda bata gayawa kowa ba .


Kirane yashigo wayarta da gudu ta taho dan tasan wacce take dakon jira ce ta kirawo ta , tana zuwa taga ita d'ince ,cikin rawar jiki tace ”ya 'akayi ne ?" momyn Suhailat ce tace ” Baraka ina hatsabibin bokanki dan Allah kizo muje gurinsa inada damuwa dan Allah ki temakeni , dariya ta sheke da ita kana tace ”wata sabuwa yaukuma ? keda ko zancen boka bakyason ji to meyasa kike son zuwa gurinshi? shiru momy tayi can kuma tace ”k'addara ce kitemakeni dan Allah , Baraka ce ta ce ganinan zuwa ,amma kiyiwa securitys d'in gidanku mgna dan ba lallai subari in shigo ba , karki damu zasu barki suka katse waya
[31/01, 9:04 pm] Mom Islam ce💃: 💖🌷NANCY YAR KARYA 🌷💖.


*STORY AND WRITING*
_BY_

*ZAINAB HABIB*
(Mom Islam)

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com



_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_


Page 63_64


,,,,,,, Da sallama ya shiga gidan ,tun daga parlor yafara tsorata saboda ganin yanayin gidan inda ya koma ,k'arasawa yayi ciki har zai wuce part d'inshi saikuma ya dawo yayi part d'in Suhailat, ganinta yayi kwance a sume ko motsi batayi , salati yashiga yi cikin tsoro ."

Anty Humaira ce takira Nancy tace ”ganinan a k'ofar gidan ku , dama tagama yimata abinci mai rai da lpy ,da gudu ta janyo mayafinta ta fice ,oyoyo tayiwa anty Humaira cikin farinciki ta rungumeta suka shige ciki , Umma ce take cewa maraba da bak'i ,bayan sun gaisa ne taci abinci ta k'oshi ,Nancy taja 'anty Humaira d'akinta suka fara hirrar yaushe gamo , anty Humaira ce ta ciro wani less mai kyau rigada skirt ne ba k'aramin kyau yayi ba kasancewarsa pink ,murna gurin Nancy abin ba'a magana shine ankon bikin ?cewar Nancy ,eh shine yau saura kwana shida bikin fa ,Nancy cikin d'oki tace ”insha Allah baza'ayi babu mu ba ,misalin k'arfe biyar na yamma anty Humaira ta koma gida ."


Janyota yayi kamar gawa yasata a mota suka nufi hospital , emergency room aka kaita suka fara bata kulawa ,doctors sun duk'ufa 'a kanta dan ceto rayuwarta , Khalil ne ya kira momy 'ya shaida mata Suhailat babu lafiya , cikin sauri momy ta janyo hijab tasa driver ya kawota hospital d'in kasancewar anan suke komai nasu sunada family doctor , da zuwan momy ido na zubarda hawaye ta hango Khalil a zaune a benci ,k'arasawa tayi cikin muryar kuka tace ”ina Suhailat?" Khalil ne yace ”momy basu bari kowa ya shiga room din , gurin zama momy tasamu suka cigaba da jira kowane doctor fitowa yakeyi fuskarsa babu wal_walah ,da sauri Khalil ya tari wani doctor yace ”meyake faruwa ne naga kuna fitowa ranku a 6ace , babu komai yace ”ya wuce ,tun k'arfe 2:pm sune har 6pm a hospital basusan halinda Suhailat take ciki ba ...


Yau saura kwana hud'u bikin anty Humaira Nancy tagama shirye shiryan biki saidai , rabonta da jin muryar Khalil kwana biyu kenan 'number shima a kashe ."

Hostel Nussy ta kama mai tsada bata kula kowa kuma bata cika fita ba yau da shigowarta Nigeria kwana uku tana san saitayi sati sanan tafara aikin da yakawo ta ."

Momyn Suhailat ce zaune itada Baraka ,labarin damuwar da take ciki tabata dariya Baraka tayi tace ”kwantar da hankalinki sister tunda kika sameni ai angama komai yanzu kisa mana rana , momyn Suhailat tace ”ko gobe OK to nizan tafi cewar Baraka ,kud'i masu yawa momyn Suhailat ta bata ta wuce ."

Dady da momy da Khalil hankalinsu ya tashi ganin har yau kwana biyu doctors basuce komai a kan ciwon Suhailat ba , cikin 6acin rai Khalil ya nufi office d'in babban doctor , bayan anbashi 'izinin shiga ya nemi guri ya zauna , duban doctor yayi yace ”ina ganin bai kamata kudinga 6oye mana abinda ke faruwa ba , akan wacce muka kawo , doctor ne yace ”kai menene a gurinta ?" Khalil ne yace ”ni mijinta ne sunkiyar da kai doctor yayi yace ...




******************

Kayan sawarshi ya ciro a drowa shadda ce mai ruwan k'asa tasha aiki ,hula ya sanya fuskarshi cike da fara'a ,turare ya fesa ya d'auki wayarshi ya fice , direct gidansu ya nufa , samun Nussy da momy yayi a parlor suna kallo cikin fara'a momy tace ”harka dawo ?eh momy dama ba wani guri naje ba , Nussy ce tace ”brother ya aikin ,momy na dariya tace ai rago ne da yasaba dadynshi ya d'auko ya bashi yanzu kuwa yakoma kasuwanci Nussy ce tayi dariya ta mik'e zuwa kitchen ta d'auko masa abinci takai dining ...✍️.


Kuyi hakuri da wanan 🤙.

Nasan kanku zai daure fan's kudai kubiyoni zaku fahimci komai takuce maison zaku nishadi mom Islam ✍️🥰.


Only comments 08141799224💃
[31/01, 9:04 pm] Mom Islam ce💃: 💖🌷NANCY YAR KARYA 🌷💖.



*STORY AND WRITING*
_BY_

*ZAINAB HABIB*
(Mom Islam).


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_


Page 65_66



,,,,,,,Mik'ewa yayi cikin farinciki sabda fuskar ta wani haske take yimasa baya iya yimata musu ,momy ce ta mik'e tayi d'akinta tabarsu a wajen ,k'arasowa Nussy tayi ta zauna a d'aya daga cikin kujerun dake zagaye a gurin kusa da Khalil ta zauna , jikinsu na gogar na juna , abincin ta zuba masa tafara bashi a baki , wanan hali na Nussy kaf gidan babu wanda zai iya yimata magana , tanayin iskancinta iya san ranta , bayan tagama ba Khalil abincin ta goge masa baki ,ta kamo hanunsa ,shidai binta yakeyi kamar' rak'umi da akala haka suke tafiya ,bedroom d'inshi suka wuce ta cire masa kayan jikinsa anzo kan wando tana k'ok'arin zata cire Khalil ya rik'e kam a lokacinne yasami damar yin mgna yace ”haba kifita mana nayi wanka , wata uwar harara Nussy ta wurga masa da yabashi damar yin shiru da bakinsa, ya wayance da cewa baby fitomin da kayan da zansa, OK tace ”sanan yasami damar shigewa toilet ,yana fitowa ita ta shafa masa mai d'ibar kayan yayi kafin ta ankara yai toilet dasu ya sanya , yafito sbda tsoron kartace anan zaisa ,ko mai bai shafa ba ya taho zai fita hannu tasa ta tokare k'ofar d'akin dan dole ya koma ya zauna ,yana jiran umarni...✍️.


Kufayi hakuri wayata ce tasami akasi narasa komai nawa ina jiran sharhinku dafatan kunfahimci karatun🤏.
[31/01, 9:05 pm] Mom Islam ce💃: 💖🌷NANCY YAR KARYA 🌷💖.


*STORY AND WRITING*
_BY_

*ZAINAB HABIB*
(Mom Islam)

💖🌷Wanan page d'in nakine *DOCTOR MARYAM (Autar mata)kiyi inda kikeso dashi 🤙💖🌷*


_💃_kubiyoni yaukam zaku gane inda na dosa 🥰page din jiya ya rikirkita mutane sosai 🤣 ku kwantar da hankalinku yau zan k'ara yawan page zaku fahimta kubiyoni_✍️.




_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_




*~Wai waye adon tafiya~*😗


Page 67_68

,,,,,,,,,Yau kwanan Suhailat hud'u a hospital , doctors sun yi 'iya k'ok'arinsu na ganin sun shawo kan ciwon amma ina abin yaci tura , samun Khalil baban doctorn yayi, tunda shine mijinta , tambayoyi yafara yiwa Khalil akan ciwon Suhailat doctor yace ” yarinyar nan tana cikin wani hali amma baka ta6a sex da ita ta bayanta ba ,kuma gabanta na fitarda wani ruwa mai wari ,to jiya nurses sun kirani harda tsutsa , zaro ido Khalil yayi yace ”innalilahi wayo Allah na , doctor ne yak'ara da cewa gaskiya zaka fad'a mana ,munyi iya bakin k'ok'arinmu mugano ko menene ya janyo hakan mun kasa 'amma inka sanar damu gaskiya wata k'ila musamo bakin zaren , gumi ne ke tsatsafowa Khalil jin furucin doctor, ya girgiza matuk'a gyara zama Khalil yayi jiki a sanyaye yace ”doctor walhi Allah watanmu biyar da 'aure amma sau d'aya nata6a kusantar ta kasancewar ba son auran nakeyi ba ,kuma a ranar ta inda Allah ya halatta na kusanceta , doctor ne ya zare farin gilashin dake sanye a idanunshi yace ”yanzu tashi muje ka ganta k'ila ka fad'a mana gaskiya, mik'ewa sukayi izuwa d'akin da aka kwantar da Suhailat ta rame sosai tayi bak'i ,zanin da aka rufe ilahirin jikinta doctor ya cire , abinda Khalil yagani ne yai matuk'ar firgita shi...........hango gabanta yayi duk tsutso tsi suna yawo ga wani uban wari da yake fitarwa , wasu zafafan hawaye suka zubo daga fuskar Khalil , ganin tabud'e ido yasa Khalil da doctor maida hankali gurin ,Suhailat , tausayinta ne Yakama Khalil yace ”mata sannu Suhailat ya jikin ?" muryarta bata fitowa sosai tace ”da sauk'i , doctor ne ya dubeta yace ”munzo yimiki tambayoyi ne akan ciwon dake jikinki ,kuka Suhailat tafara tana girgiza kai , doctor ne yace ”kiyi mana bayani ko kinta6a had'uwa da y'an lesbian ne ?a'a a'a Suhailat tafad'a tana kuka , to gaya mana ,cewa tayi ”kafin nayi aure na had'u da wata k'awa tana sona nima ina sonta to itace ke saduwa dani ta cigaba da kuka , tari ne ya sark'eta babu k'ak'autawa ga wasu yawu masu kumfa hancinta kuma na fitarda jini , duk k'yan k'ya minta da Khalil takeyi ya mance ,da sauri yayo kanta yana kuka , cikin sark'ewar murya Suhailat tace Khalil ka ,ka ya, ya femin , wani uban ihu Khalil ya kurma ganin tunda Suhailat tafad'i kalmar k'arshe idanunta suka rufe jikinta ya saki , momy da tagama jin komai ta taho jiki babu k'wari ta tallafo kan Khalil tana kuka tajashi suka fito harabar hospital din ."

Bayan anyiwa Suhailat sutura 'aka kaita makwancinta , labari ya isa London , momyn Suhailat tayi kuka sosai tana fad'i tashi a kanta gashi tabar duniyar ,amma k'awayenta sunbari a kan k'awar Suhailat ce ta kasheta hmm ,musamman Hajiya Zinat da take zuga momyn Suhailat akan karta yarda ta k'yale wlhi garata d'au fansa, wanan mutuwar ba k'aramin girgiza momyn Suhailat tayi ba ,amma ta godewa Allah da bai bata sa'ar yin amfani da sharud'an bokaye ba , k'awayenta kuma duk tayi watsi dasu ."



Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah har anti bakwai d'in Suhailat dady da baya gari akayi raduwar shima ya girgiza lokacin da Suhailat tayi sati uku da rasuwa , ana gobe d'aurin auran anty Humaira , Khalil ne yaje gidansu Nancy suna cikin hira take gayamasa tanada zuwa bikin wata sistern ta , Nancy na kiran sunan layin Khalil yace ”ai mijin ma abokina ne ayya Nancy tace ”kaima zakazo kenan? insha Allah Khalil yace ”ai inbabu ni to ina tunanin bikinan za'a iya fasashi ,gashidai a school muka had'u amma munzamo y'an uwan juna nida angon , Nancy ce ta katse zancen ta hanyar cewa dan Allah kayi hak'uri ko ya k'arin hak'uri banceba , Khalil ne yace ”to kina zumud'in biki rau_rau tayi tace ”Allah sarki Suhailat Allah yakai haske k'abarinki , Khalil yaji dad'in wanan adu'ar cikin fara'a yace ”amen ,yanzu zan koma gida gobe ki shirya misalin 12:pm zanzo mu wuce ,insha Allah kafinnanma nagama komai , dahaka sukayi sallama ya wuce gida."


Washe gari ,Nancy tad'au makeup tayi kyau sosai sbda gwana ce gurin iya kwaliya ankon da za'asa ranar d'aurin aure tasa cot less mai ruwan toka sai gyalenta fari siriri dakuma takalminta mai tsini ga faskekiyar wayarta data dauka ,taci sark'a da d'an kunne da war waro wani d'auri da tayi kaikace zuwa tayi aka yimata shi komai nata yayi kyau ,Umma ce kecewa walhi wanan takalmin kiyi a hankali karki tako y'a y'an mutane , Nancy na dariya tace ”Umma ayi mana 'adu'a bayan tagama komai ne ta d'auki jakarta ta fice ,kasancewar wayarta tana ruri Kuma Khalil ne mai kiran, tafiya takeyi cikin yanga tun daga nesa Khalil ya hangota masha Allah yace ”wai gaskiya na iya za6e Allah ya mallakamin ke beauty na , tana isowa ta hangoshi yayi wani bala'in kyau raina tata kwaliyar tayi amma karta bada mata yasata waskewa ta shige , motar tare da sallama , amsawa Khalil yayi yace ” beauty ai zakiyi rawa ko kinga kyan da kikayi kuwa ?" dama hijab kikasa dakinfi haka kyau , Nancy ce ta shagwa6e fuska tace ”hijab kuma kamar matar ustaz uhm , dariya Khalil yayi yace ”inmun dawo zankaiki ki gaida momyna zaki? maize hana cikin farinciki Nancy tace ”inason momy sosai dariya Khalil yayi yace ”itama tana sonki sosai Nancy , cikin hirarsu duka iso gidan bikin lokacin ana shirin d'aurin aure , Nancy ce ta wuce inda humaira take , misalin k'arfe hud'u aka wuce reception Nancy a motar Khalil suka tayi , guri ba k'aramin tsaruwa yayi ba , gurin zama kowa ya nema Khalil kusada ango ita kuma Nancy kusada anty Humaira , Nancy ce t gaisheda ango, cikin fara'a ya amsa anty Humaira ce tace ”ka ganne Nancy kuwa , a'a angon yace ”anty Humaira tayi dariya tace ”toke Nancy kin ganeshi kuwa ? Nancy ce take tunanin a ina tasan wanan bawan Allahn takuna kasa tunowa , ango ne yace ”na ganeta koba itace ta zauna a gidanku ba , yar aikin hajiya , what!!!! cikin tashin hankali Khalil yace ”me kunnuwana suke jiyomin yar aiki fa kukace ? ina Nancy batayi kama da yar aiki ba cewar Khalil, banda hawaye babu abinda ke fita a idon Nancy ,sai a lokacin anty Humaira ta tuna cewar batayiwa Nancy adalci ba ,tana tsaka da tunani ne taji saukar tagwayen maruka har biyu , tashi d'aya guri ya kaure da fad'a abin babu dad'i ,Khalil ne yakai dubansa ga inda Nancy take a zaune yaga babu ita babu alamarta ,fitowa yayi daga hall din yanata waige_waige amma baiganta ba , wani jiri ne ke d'ibarshi, yana tuno kalaman Humaira mota ya shige yabar gurin rasa inda zai Sosa yayi dan haka ya zarce gidanshi , ikon Allah ne yakaishi ,zuciyarshi sai zafi take yimasa ,a fili yace ”to wai shin gaskiya ne Humaira ta fad'a ko k'arya ?"

Shikad'ai yake tambayar kanshi, no Nancy ba y'ar aiki bace Allah yasa mafarki nakeyi ba gaskiya bane ,shikad'ai yaketa surutunshi kamar zararre ."


Da isarta gida ta shige da gudu fuskarta sha6e _sha6e da hawaye ,Umma da ta sauke abinci tana zubawa a kula ta taho tana cewa , DUDUWA maiyafaru ?"Nancy ce taji kamar Umma ta caka mata kifiya takuma tsala ihu ,tana cewa na shiga uku na lalace wayo Allah na wayo Allah na, ta shige d'akin tazube a k'asa tana kuka , Umma dai tayi iya yinta na ganin Nancy ta fad'a mata 'abinda ke faruwa amma tak'i, kujera mai zaman mutum uku ta hau bacci mai nauyi ya d'auketa da mafarkai kala _kala dakuma na ban tsoro ,sada akayi akayi sallahr isha'i sanan ta tashi sbda umma tasan tana fashin sallah , wanke baki tayi ta nufi kitchen batayiwa Umma magana ba taje ta zubo jollof d'in taliya ta d'auko ruwan leda🤣 tana cikin cin abincinne tafara tunanin inhar Khalil ya gane gaskiyar lamari to babu makawa saiya gujeta , ta juya ruwan ledar dake hannunta tace ”shikenan yanzu bama ruwan leda ba har komai ma zaifi k'arfinmu , nashiga uku hatta kayan makeup d'ina wayo Allah na ,yanzu yazanyi da Khalil ? umma ce tazo ta zauna tafara yimata fad'a tana cewa”wato ni banida matsayin da zaki gayamin damuwarki ko?to shikenan kije da damuwar taki intai wari maji , Nancy ce tace ”ba haka bane Umma wata gagarumar matsala ce ta taso sbda wlh tashafemu dukkanmu , ta fashe da kuka , Umma da tashiga rud'u tace ”niwai bangane ba wace ”matsala ce ?"kuma kin hau kuka Nancy ce tace ”Umma Humaira ta tonamin asiri wlhi ta gayawa Khalil cewar ni y'ar aikin gidansu ce a gaban dubban jama'a ,jikin Umma yayi sanyi sosai sbda itama tafara tunanin yadda rayuwarsu zata kasance✍️.


Mom Islam ce 💃.
[01/02, 10:29 am] Mom Islam ce💃: 💖🌷NANCY YAR KARYA 🌷💖.


*STORY AND WRITING*
_BY_

*ZAINAB HABIB*
(Mom Islam)





_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_



69_70

,,,,,,,,,Umma ce tace ”karki damu insha Allah _Allah zai kawo mana d'auki , dagan an suka fara jajanta lamarin ."

Washe gari Khalil yatashi da wani matsanancin ciwonkai ,wanka yayi ya zarce gidansu da sallama ya shiga ya sami momy a parlor tana karanta wani litrafin adu'oi ,durk'usawa yai ya gaisheta cikin fara'a ta 'amsa tare da sanya masa albarka ,ganin idanun sa sunyi ja yasa momy tambayarshi ,cemata yayi ciwon kai ne kawai , momy da tabi ta damu tace ”yakamata kaje hospital to kawai Khalil yace dan shiyasan halinda yake ciki ."


Tun had'uwarsu a gurin bikin Humaira yau kwana bakwai kenan bai k'ara kiranta a waya ba , rayuwa tayimai k'unci babban abinda yafi 6ata masa rai shine k'aryar da Nancy ta zuga masa ,in dadynshi yaji wanan zancen da wuya yabari ayi auranan ,mik'ewa yayi yace ”momy ayimin farfesun kifi anjima zan dawo ,da kallon tausayi momy tabi Khalil a tunaninta duk matsalar auran Nancy ne ya sashi rama ."


Muk'araban momyn Suhailat ne suka wai_wayo ta , rabonsu da gidan tun gaisuwar rasuwar Suhailat ,ganinsu da Momyn Suhailat tayi saida gabanta ya fad'i , Hajiya Zinat na taunar chingom tace ”oh mm Suhailat yanz zumuncin mu yaja baya , momy dake jera musu kayan ciye_ciye tace ”ba haka bane wlh ni yanzu fitar cema take yimin wahala , d'ayar ce tace ”to karkiyi tunanin zuwa gurin boka ya k'are dole muje mu d'aukarwa daughter fansa , girgiza kai momyn Suhailat tayi tace ”inma wani abinne nidai nabarwa Allah ita kuma Allah ya gafarta mata Allah yakai haske kabarinta , ta6e baki sukayi dukkansu kana sukace , to mekike nufi kina nufin yanzu bakya tare damu ne ?a'a momy Suhailat tace ”muna tare mgnar zuwa gurin boka ce gaskiya yanzu nadena but kuma ina nema muku gafara gurin Allah , eyeee y'ar iyayi ke harkin isa kice wai ga zance ga magana ,to tunda kince haka komai ya wargatse babu mu babu ke ko wata matsala ta taso miki to kimagan ceta da kanki karki nemi d'aya daga cikinmu , idanun momyn Suhailat na fitarda hawaye tace ”nifa ba haka nake nufi ba kunyimin wata fahimta ta daban , zata kuma magana suka mik'e suka fice ,kuka ne yakuma ku6ce mata seda tayi mai 'isarta sanan ta koma wani tunanin da daban."


Yau kwanan Nussy takwas tana k'arewa garin kallo tunda tazo bata kula kowa ba ,hijabai ta shiga kasuwa ta siyo manya ,yaune take shirin zuwa gidansu Khalil , bokanta takira a waya take gaya masa tagama duk wani shiri da yabata ,yanzu tanason ya rufewa mutanen gidan baki kuma kar Khalil yadinga yimata musu , komai tasashi tadinga yimata kuma yasawa mahaifinshi da mahaifiyarshi soyayyarta a cikin zuciyarsu , bokane yace ”angama karki damu buk'a tarki ta biya angama ,ya kashe waya , fitowa tayi ta tari mashin zuwan anguwarsu Khalil ,da isarta ta bawa mai mashin kud'insa tasauka tafara bubuga get d'in ,maigadi ne yazo cikin sauri zaiyi mgna yaga ta suri kayanta ta shige kasa yiwa Nussy magana yayi har lokacin da ta 6ace masa baya angota kasancewar kafin mutum ya isa cikin gidan da tafiya , samun k'ofar a bud'e ne yabata damar yin sallama ta shige da kayanta , momy ta samu a parlor tana kallo , da ganinta momy taso ganeta amma inna ta 6ace mata , Nussy ce ta gaida momy cikin fara'a ta 'amsa Nussy tace ”momy nazo gaisuwar rasuwa ne na Suhailat ,oh momy tace ”kece k'awar tanan ko eh nice amma ba wacce take London ba ni iyauena sun rasu ta sanadiyar hatsarin mota , Allah sarki momy tace ”cikin tausayawa , nan suka fara hira da Nussy jefi_jefi, dady na shigowa yasamesu ita da momy a zaune bayan sungaisa ne yake tambayar Nussy ya k'arin hak'urin iyayenta ?tana kukan gulma tace ”alhamdulilh , misalin k'arfe 8pm Khalil ya shigo momy ce

Please Login or Register in order to submit comment