Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace" kul Duduwa kar in sakejin kin cewa wani d'an wahala, zum6uro baki tayi alamar shagwa6a tace" Umma wallahi shiya sa banason dawo wa k'auyen 'nan ,saboda wanan sunan , baki a sake Umma tace" au zaki canza sunan 'ne gyd'a kai tayi tace" ai nariga na sauya daga yanzu sunana Nancy, salati Umma tafara tace" zuwa barikin abin da ya koyar dake kenan , sawa kanki sunan arna ko ."


Dariya tayi mai sauti kana ta mik'e bata bawa Umma 'amsa ba , washe gari Umma ta 'tashi domin d'ora d'uma men tuwon jiya , Nancy na fitowa tace" gaskiya Umma wanan tuwon akai shi gidan su Delu ,Umma bata kula taba sai ma k'ara had'a wuta da takeyi , ganin haka yasa Nancy ficewa waje , sai da tafita ta 'tuna da cewar ai tabar wayar ta 'a gida , k'in komawa tayi saboda yunwa takeji ,tana son zuwa siyo risho ."


Ahmad ne yashigo yana sanye da wata kod'a d'iyar 'riga , Umma na ganin shi zuwa d'auko wayar , kasa receive dukayi dak'yar sukayi sa'a suka danna , jin wata murya yasa Ahmad cewa heeloo nine ahmadu d'an uwan Duduwa, zaro ido Khalil yayi kana yace "ban gane ba waye Duduwar?" Ahmad ne yace"me salular nan mana."



Khalil ne ya kashe wayar shi kana yafara tunanin kodai Nancy ta yarda wayar tane?"yanata zancen zuci ".



Da shigowar ta 'ta hango Umma da 'Ahmad gakuma waya 'a hanun Ahmad , zaro ido tayi tafara ruwan masifa , zuwa d'akin girkin su tayi ta 'ajiye rishon, kana ta fito tacigaba da masifa , itadai Umma batace komai ba , shikuwa Ahmadudu fecewa yayi yana tu nanin kar yaci na jaki, duba wayar tata 'tayi ganin sunan Kahlil yasa ta zaro ido, tafara salati tana sharce gumin da yafara bara zanar jik'a mata fuska."



Tana cikin k'ara duba number shine sai ga kira nan ya shigo , sauke gwauron nun fashi tayi , kana tayi amsa wayar, daga can 6an garen nashi yace" Aslamu alaikum , jin shiru yasa shi mai maita sallamar , sai saita muryar ta tayi kana tace" Khalil yakake ? wani farinciki yaji dama yayi missing d'in muryar ta , bai cemata wani ya 'amsa kiran shiba ,haka ita ma bata fara yimai maganar ba ,bayan sun gama wayar ne Umma tace" shid'in wanan daga ina kika samo shi ?"cewa tayi Umma ni wallahi yunwa nakeji, kibari 'idan naci abinci zanyi miki bayani , badan Umma taso hakan ba ,ta k'yaleta ."



Bayan tagama girkin 'ne taci ta k'oshi Umma takuma tambayar ta akan wanan saurayin wato Khalil , ajiye wayar dake hanun ta tayi kana tafara bawa Umma labarin abin da yafaru tsakanin su tun farkon had'uwar su sai dai bata bawa Umma labarin rasuwar Hajiya ba dakuma d'umbin kud'in da 'aka bata har koma warta gidan haya ,bata fad'awa Umma ba".



Hak'ik'a Umma ta yaba da Kahlil sosai sai dai tana tunanin yaza'ayi Khalil yaso yar talakawa bayan shid'in d'an masu hali ne ."


Nancy ce kwace a cinyayyar katifar Umma tana kallo a wayar ta , jin k'arar massage ya sata kashe kallon tahau duba sak'onni ganin wasu mahauka tan kud'i da Khalil ya turo mata yasata zare ido 50k tagani , wani tsalle ta buga kana tace kai Khalil dole in aure ka kodan wanan 6arin nerar dakakeyi min , amma yanzu wasan yafara ,dole in samo mafita ,cikin kwana d'aya."



Yau satin Nancy d'aya 'a village d'in su , bayan tayi wanka ta had'a musu abinci ,tazo kusa da Umma ta zauna , ganin haka Umma tace" to yau kuma nikike jin 'nauyin gayawa damuwar ki ? bayan ta k'a k'alo hawayen k'arya tace "Umma dama dama cikin k'osawa Umma tace" dama me?" Nancy ce tace"dama Umma so nakeyi mu tafi tare , zaro ido Umma tayi kana tace meyasa kikeson k'ir k'iro abin da bazai yiyu ba ? k'ara share hawaye tayi takuma cewa , wallahi Umma hardai bakizo mun tafi ba to nima bazan koma ba .....✍️✍️✍️.



_Mom Islam ce_


*Please share*👏
*Comments*
Vote✔️
💖🌷NANCY Y'AR K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._


_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 27_28


___Jikin Umma ne yayi sanyi tana tunanin to idan tabi Duduwa ita gurin wa zata zauna , kamar Nancy tasan tunanin Umma, matsowa tayi ta kama hanun Umma kana tace" indai gurin zama ne Umma baki da matsala , jikin Umma babu k'wari ta 'amince da bin 'Nancy ABUJA , aikuwa Nancy najin haka ta rungume Umma tana murna , mik'ewa tayi ta fice zuwa d'akin ta nada ta kunna wak'a jirgin so ,ta Umar m Sharif , tadinga tik'ar 'rawa , tsgai ta rawar tayi kana tafara maga tana cewa, ai tunda Umma tace zata bini angama saboda 'auran Khalil babu fashi muddin iyayen Khalil suka san 'ni y'ar talakawa ce to na shiga uku, amma yanzu tunda Umma ta 'amince no problem zan san inda zanyi , tunda inada kud'i Kuma zan d'inga tatso Khalil ,tana cikin maganar ne taji Umma na k'awala mata kira ,ficewa tayi a guje taje kiran Umma".



Umma ce ta dubi Nancy tace ki fad'amin gaskiya , mene ne dalilinki nason inbiki?"zaro ido Nancy tayi a zuciyar ta tana cewa 'ai nad'auka mun wuce gurin , Umma ce ta katse mata tunani da sabuwar tambayar da takuma jefo mata, ganin bata da mafi ta yasata fara kuka tana bawa Umma hak'uri akan abubuwan da suka faru bata fad'a mata ba ta bata labarin mutuwar Hajiya dakuma kudin da haliya tace abata , dakuma 'alkairin Khalil da momyn shi."




Salati Umma tayi tace" to yanzu a ina kike zaune ? Nancy ce tace" gidan haya nakama, shine naga zaifi kyau tuwa mukoma tare , Umma tayi na'am da shawarar Nancy, dan haka suka fara had'a kaya dan barin gari ."



Washe gari Nancy ta kwashi kayan da tasiyowa Umma dakuma wanda momyn Khalil ta bata takai gurin d'inki kayan kala bakwai ne tace" ayiwa umman ta d'inkin zamani."



Nancy ce zaune tana tinanin yanzu ta gama da fannin Umma saura, na Khalil , saboda idan har ta dawo to zai ze zo, gai da maman ta dan haka dole ta nemi mafita , number mutumin da yabata hayar gidan da take ciki , ringing d'aya ya d'aga , daga can 6an garen yace" dawa nake magana ? Nancy ce tace "nice wace take haya 'a gidanka Nancy, washe baki yayi kana yace" lafiya dai ko?eh lafiya tace" mai ,can kuma ta nisa tace dama so nakeyi ka samar min gida mai kyau tsararre me tails , washe baki yayi kana yace "akwai gidaje sosai , kinga inada wani a WUSE 2 shi price d'insa dubu d'ari biyar ne ,akwai wani a A Y A shi kuma price d'insa dubu d'ari uku , sanan akwai wani a WUSE 2 shi kuma price d'insa dubu d'ari buyu da hamsin ."



Tunanin ragowar kud'in ta tayi yanzu sau ran dubu d'ari hud'u , cemai tayi ina son 'na WUSE 2 d'in amma kasan banfi wata biyu a gidan kaba, zaka bani ragowar kud'in , mutumin ne yace" karki damu shi na WUSE 2 d'in kibada dubu d'ari biyu ,inyaso sai 'in cika da ragowar kud'in ki godiya tayi mai suka yi sallama ."



Washe gari Nancy ta kar6o kayan Umma'a gurin d'inki ,Umma tayi farinciki sosai akuma sanya mata 'albarka, Nancy ta hana Umma d'aukar kayan ta saboda bata san Umma tasa Khalil ya ganota wasu ,sababbin hijab guda uku ,tabawa Umma, sun gama had'a kayan da zasu buk'ata sabo da washe gari zasu koma 'ABUJA.....✍️✍️✍️.



_Mom Islam_


*Please share*👏
*Comments*
Vote✔️
🌷💖NANCY YAR KARYA💖🌷

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 29_30


Misalin k'arfe 8am su 'Umma sun gama shiri Nancy ce tace"wa Umma jiya kince zaki shiga mak'ota kuyi sallama , jikin Umma a sanyaye tace" eh walahi barin zo inshiga tunda kince karfe tara zamu tafi, mik'ewa Umma tayi kana ta janyo sabon hijab d'in da Nancy taba ta sanyawa tayi a jikin ta kana ta fice zuwa gidan dake mak'ota ka da nasu , da sallama ta shiga gidan matar gidan mai suna inna tace" lafiya uwar Duduwa naganki da sanyin safiyar nan? Umma ce ta nemi kujerar da tagani a gefen ta 'ta zaune ,bayan sun gaisa ne tace "wallahi zamu wuce Abuja ne , cikin tuhuma inna tace"zakije gurin su illu kenen ?eh umma tace" a tak'ai ce saboda batason kowa yasan abinda suka shirya ita da Nancy, saboda idan har mutane suka san ga dalilin tafiyar su to lallai babu makawa sai yazamo gutsuri tsoma 'shiyasa ta 'amsawa inna tambayar ta ."



Bayan tafito daga gidan inna bata gida ta koma suka fito domin tafiya tashar mota , da zuwan su sukayi sa'ar samun motar Abuja , Nancy ce tabiya kud'in motar , suna cikin tafiya ne sai ga kiran Khalil nan cikin farinciki Nancy ta d'auka tana cewa 'al bishirinka cikin k'aguwa Khalil yace"goro sai da tad'au lokaci sanan tace" ina hanya insha Allah wani tsalle ya buga kana yace "yau akwai surprise me girma 'amma burina inganki kin iso lafiya ,sallama sukayi da Khalil , juyawar dazatayi taga umma nata sharar bacci tace" tabb umma tun yanzu bacci , game tafara 'a wayar ta batayi nisa ba saiga kiran Khalil yakuma shigowa d'agawa tayi tana cewa munkusa fa big boy wata uwar dariya yasa sai kuma Nancy tafara zargin ko tayi turancin ba dai_dai bane yasa yake dariya , kawar da tunanin ta tayi kana tace"meka tanadar min idan 'na iso ?kamar jira yakeyi yace"kya kyawa kina isowa zan zo dagudu nayi hugging d'inki, rufe ido tayi can kuma tafara tunanin menene hugging? " tunawa tayi ai tanajin wanan kalmar a gurin ssu Anty humaira suna cewa runguma , Khalil jin tayi shiru ya katse shirun da cewa yanzu dai nabar komai saikin zo , to kawai tace" dan wanan kalmar tanada girma ."





Jin mota ta tsaya yasa Umma farkawa tace"Duduwa har mun iso ne? eh tacewa umma suka fara shirin sauka ,kaya'yyakin su 'suka d'iba daganan suka nemi gurin hutawa , number megidan da zasu shiga tafara gwadawa ,tayi sa'ar samun shi a waya cemata yayi ganinan kusa da tashar dama yanzu nake zancen ki a raina tun safe nafito da keys d'in , kwa tancen inda yake yayi mata babu, 6ata lokaci taje ta kar6o keys d'in tazo gurin Umma tace"mata su wuce gidan bayan sun hau mota basuyi tafiya mai tsawo ba kasancewar tashar motar ta cikin gari ne ,kud'in mota tabawa mai motar daganan suka sauka wani gida ta hango mai kyau sosai saboda gidan ta tsaru matuk'a."





Bud'e gidan tayi suka shige ita da Umma tunda suka doso layin umma tafara yimata tambayoyi amma babu wacce Nancy ta amsawa umma ' umma ta tsorata da ganin gidan saboda tunda tazo duniya bata ta6a ganin gida mai kyan wanan ba ,🤨nikuwa nace"bakiga gidan su Khalil bane da saikin tsure🤭am sorry umma🤙."



Bayan sun shige gidan 'Nancy tagama bud'e kowane d'aki na cikin gidan , gidane mu had'u a parlor mai d'akuna uku da bedroom dakuma bathroom sai kitchen sai d'akin bak'i duka 'a ciki bedroom d'in tundaga sama har k'asa tails ne hakama ko ina na gidan sai dai outside wato harabar gidan shikuma interlocks ga kuma parking spice ."


Kai gidannan yayi araha sosai 🤭anty Nancy Allah yakawo mota to gida babu kujeru babu gado babu plasma babu AC 😫kubiyo mom Islam wato Zainab Habib danjin yaya Nancy da Umma zasu kasance kuma yaushe Khalil zai kawo ziyara .....✍️✍️✍️.




Karku manta comments d'inku shine babban burina inason k'ara yawan rubutun koda Read more biyu ne to kuna sagemin gwuiwa yakamata indinga ganin shar'hi please👏.


_MOM ISLAM CE✍️_
[31/01, 6:33 pm] Mom Islam ce💃: 💖🌷NANCY YAR KARYA 💖🌷.

Story and writing

By

ZAINAB HABIB
{Mom Islam }

_Mom Islam tadawo🚴

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page 31 & 32

,,,,,,,,,Ragowar kud'inta ta d'iba tacewa umma zataje siyo kayan gado , zata fita taji wayarta na ruri ,tsayawa tayi ta 'amsa kiran ganin Khalil ne yasata mumishi tace ”ranka shidad'e dafatan kana lafiya ?lafiya Lou yace ”mata daganan yace ”to ganifa 'a hanyar zuwa gidan Ku ,zaro ido tayi tacemai wallahi yanzu bana gida ,ummace keson sauya kayan d'aki shine naje bakin titi zantafi gurin mai kayan ,Khalil ne yace ”to kibar ganinan zuwa yanzu saimu wuce ,wani tsalle ta doka ta tsaya tana jiranshi ,mintiuna kad'an sai gashi yayi parking ,saida ya matso da motar dai _dai saitin ta tukun ta shige suka wuce ,suna zuwa ,tacewa mai kayan gado nakeso da katifa nawa ne ,mai kaya ne yace ”kinsan kud'i kud'ine wanne kika za6a ,wasu masu tsadar gaske ta nuna ,gaya mata kud'in yayi zaro ido tayi, tana tunanin idan kud'inan suka k'are yazatayi ?cewa mai kayan tayi to gaskiya kud'in data bani basukai ba yanzu kabani na dai _ dai kud'ina ,Khalil ne yace ”am kabamu gadon data nuna dakuma katifa da bedside duka dai kayan dakasani harda dining chair ,zaro ido Nancy tayi tace ”walhi kud'i ne tsugugu kabar wanda yasamu ,ko kulata baiyi ba yasa 'akasa kayan a mota yasa Nancy tabasu address din gidan ,bayan tabasu shikuma Khalil yace ”to Shiga mota muje itadai binshi kawai takeyi amma hidimar tafara yawa ,gurin masu kayan kallo sukaje yasiya musu TV jibgege da sauran kayan aikuwa farinciki bai 6oyu a fuskar taba ,rungumeshi ne kawai batayi ba."



Gida suka nufa ,wasu masu yimai aiki yakira yayi musu kwatancen gidan su Nancy 'yace ”suje ankawo kaya susa komai yayi kyau ,babu damuwa sukace daganan yakashe wayar ,suna shigowa 'anguwar yayi parking motar shi ,Nancy ce tafara hawaye ,hankalin Khalil ya tashi ya dubeta yace ”Nancy meke faruwa ?please gayamin ,cikin wani salo tace ”bansan da bakin dazanyima godiya ba ,hak'ik'a ka can canci godiya to nikam ina ganin godiyar ma tayi kad'an ,murmishi Khalil yayi yace ”no karki damu, abu d'aya zakiyi ki biyani shine ki aureni ,farr tayi da ido takuma kashemai 'ido d'aya tace ”kullum ina mafarkin hakan ,nandai sukayi hirarsu ,yace ”zai shiga ya gaida su momy ,to Nancy tace ”barinje in sanar mata ,to yace ”daganan ta shige gidan samun umma tayi ta shimfid'a tabarma 'cikin azama ta isa gurin Umma tace ”umma Khalil nefa zai shigo gaisheki ,gyara hijab umma tayi tace ”to kicemai yashigo man ,Nancy ce tace ”umma ina lefin yashiga ciki ?umma ce tace ”nima fitowa nayi a cikin d'akin tunda masu gyara suka shigo ,amma 'a ina kika sami mak'udan kud'in siyayyar nan ?dariya Nancy tasa tace ”umma walh amma dai kibari zuwa 'anjima zanbaki labari barin shimfid'a masa sallahya, fita tayi tace ”ka shigo OK yace ”ya bud'e bayan booth yayi ya ciro wata k'atuwar leda ya shiga da ita ,umma da ganinshi tafara washe baki tana mai sannu da zuwa ,bayan ya zauna ne ya sunkuyar da kansa k'asa 'alamun girmamawa yace ”ina yini umma, lafiya lau tace ”yasu maman 'naka ?tana lafiya kuma tace ”a gaisheki ina 'amsawa umma tace ”Nancy ce tafito d'auke da ruwan gora dakuma cin cin ,lokacin umma na shirin mik'ewa tayi gaba tabarsu ,zama tayi nesa dashi tayi shiru ,kallonta yayi yace ”to wa kika kawowa¿kai mana ,tabashi amasa ,Khalil ne ya sha ruwan ya d'auki cin cin biyu yaci, daga nan yace ”nikam zan tafi ga wannan kibawa umma ,godiya tayimai ta rakashi har bakin mota tana d'agamai hannu."



Washe gari dadyn Khalil na hanya ,hidima momy take shirya masa sosai yau dakanta take girki ,gidan sai tashin k'amshi yakeyi , Khalil ne yashigo yake cewa momy dady fa yakusa sauka, saura 30 minutes momy ce tace ”ai nagama mutafi ,airport suka wuce ,lokacin jirgin 'na gaf da sauka ,Khalil ne yanemi guri yazauna yana cewa momy lokacin fa yayi ,bai gama rufe baki ba saiga jirgin yana sauka, jama'a ne suka tattaru kowa na jiran wanda yazo tarya ,momy sai dad'a bud'e ido takeyi ,aikwa ta bud'e a dai _dai 'idanunta sukayi tozali da dady da sauri taje ta rungumeshi ,shiko Khalil sai alokacin ya ga dadyn , dady ne yace ”ba'a girma ko ?"dariya sukasa ,wata farar yarinya ce budurwa kya kyawa tana sanye da riga da wando ,na Jens ta d'aura rigar sanyi a kwankwason ta ,rik'e take da hannun dady tana yiwa su momy murmishi...



Momy ce tace ”bak'uwa mukayi ne ?dady ne yace ”Suhailat ce ko kin mance ta ,momy ce tayi shiru alamun tunani ,Khalil yace ”please kuzo mu wuce ,shigewa motar sukayi Khalil yana driving d'insu ,Suhailat ce taketa satar kallon Khalil, shiko baisan tanayi ba ,da isarsu gida hira ta 6ark'e aka wuce dining cin abinci ,dady ne yace ”my son zoka cikawa Suhailat plet ,dariya sukasa dukkan su shikuwa Khalil jiyayi yarinyar bata kwanta masa ba...


Abincin yafara zuba mata momy kuma na zubawa dady ,Suhailat ce tace ”brother kabarshi haka ,banacin abinci over ,wanan ma tare zamuci ,zaro ido Khalil yayi ganin tana magana ko kunyarsu dady bataji ba ,wani kallo yayi mata itako murmishi ta mayar masa,dady na lura da yanayinsu itako momy hankalin ta nakan dady."


Dady ne ya kalli Khalil yace ”to da 'abar abincin ya lalace ai gara kuci tare ko ? shiru Khalil yayi ,yasa cokali suka faraci Suhailat na cikin cin yanga dubawar dazatayi taga babu komai duka ya cinye, 6ata rai tayi tace”sai kuma nace maka na k'oshi ko¿" Khalil ne yaga su momy sun tashi ,wata muguwar dariya yasa ya bud'e food flaks ya zubo mata abincin da yawa ,zaro ido Suhailat tayi tace ”kad'an fa zanci danma inason jollof mai kifi ne ,ko kulata Khalil baiyi ba ya zaro bell d'in wandonshi yace ”wallahi ko kici abincin anan kokuma na zzaneki."

Allah ya zubawa Suhailat tsoron bulala haka ta fara tura 'abincin tana tsayawa zai ce saita ci kuma yace” bayason ,nishin kuka haka taci abinci mai yawa da k'ayar take tafiya rasa wane d'aki zata shiga tayi ,parlor ta koma ta kwanta 'a kujera .


Bayan anyi sallahar la'asar ne kowa na parlor dady ne yace ”Khalil ya kasuwa ?alhamdulilah yace ”daganan dady 'yace ”banyi muku bayanin Suhailat ba ko ?amma ke momyn Khalil ai kinsanta saidai kin manta da ita, momy ce tace ”eh to ina buk'atar tuni ,dady ne yace ”kin mance brother na ABDURRAHMAN ?"shiru tayi tana kallon Suhailat can kuma tace ”yanzu itace ta zamo haka tabb lallai girman d'an mutum babu wuya ,dady ne yacewa Khalil to ga Suhailat nan tunda taganka 'a photo tace”saita biyoni zatazo ta ganka ,humaid ne yace ”to nagode ,murmishi take jifanshi dashi amma ko kawota 'a gabanshi baiyi ba .


Washe gari ta tashi da wani matsanancin ciwon kai ,momy ce tacewa Khalil yazo ya kaita hospital cikin fushi ya shigo d'akin da yazamo nata 'yace ”inkinyi ra'ayi zaki 'iya tashi munafuka kawai ,dariya ma yabata duk da ciwon kan daya matsa mata bai hanata darawa ba ,k'ufula yakuma yi ya zo kusada ita ya kaimata rank'washi a kanta jin zafin rank'washin yasata kurma ihu ,da sauri momy ta fito daga bedroom d'inta ta shigo d'akin ,ganin Khalil a tsaye yasa momy cemai to maiya faru naji kina ihu ,cikin shagwa6a tace ”momy nakasa tashi ne.....✍️✍️.

Mom Islam ce 😘


Please share👏
[31/01, 6:33 pm] Mom Islam ce💃: 💖🌷NANCY YAR KARYA 💖🌷.



_Mom Islam tadawo🚴‍♀️🚴‍♀️🚴‍♀️🚴‍♀️_.


story and writing

By

ZAINAB HABIB
{Mom Islam


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page 33 & 34

,,,,,,,,,,Kama mata momy tayi ta mik'e Khalil na jingine da jikin bango yana kallon su ,jin dady 'yakira momy 'yasata tafiya tabarsu , Khairat ce tace please my lovely brother help me dan Allah ,a razane ya d'ago kai yana yimata kallon kin rainani ma ,yana shirin ficewa ta rik'o mai hannu tana rok'onshi akan ya d'auketa ya kaita mota , zaro ido yayi ,yace ”ke bakida tarbiya ne¿ ko bakisan haramun ba? d'aga kafad'a tayi tace ”ni aganina maiya had'a d'aukata dakuma haramun ?"jin iskancin 'nata yayi over yasashi ficewa ,da gudu Suhailat ta mik'e tana kiran sunanshi ,lokacin da tafito harabar gidan ta hangoshi ,harya shige mota ,k'wala ihu tayi tace ”momyy, cikin azama momy tafito har tana shirin kifawa ,kafin momy tace maiyyafaru har Khalil yaja motarshi yayi gaba ,zama suhailat 'tayi tana kuka ,tayarwa da momy hankali takeson yi ,momy ce tace ”to maiya kuma had'aki da yayan 'naki? cikin shagwa6a tace ”momy kaina kamar zai fashe walhi ,yakaini hospital yak'i shine ya gudu, momy ce ta juya zuwa d'auko wayar ta number shi ta duba ta danna kira ,ring d'aya ya d'aga momy ce tace ”yanzu ka kyauta kenan ?da katafi kabarta tana famada ciwon kai ko¿"Khalil cikin girmamawa yace ”afuwan momy na banyi nisa ba barinzo na d'auketa ,albarka momy ta Sanya mai daganan momy tace ”tashiga ta d'auko hijab d'inta ,to kwai tace ”le k'owa tayi taga momy bata parlor ,hakan yabata damar sanya riga pink color da wando blue sun d'an kamata sosai tasa dogon hijab har k'asa ,tasami k'aramin mayafi ta d'aura 'a kanta ,fitowa tayi tacewa momy natafi ,Allah ya kiyaye momy tayi mata ,dagan ta fice tayi waje, tana bud'e gate ta hango shi a cikin mota yana waya yana dariya ....




Cikin azama ta iso jikin motar tana nocking bud'e mata yayi da hannu d'aya ,d'ayan kuma ya rik'e waya , shiga tayi ta zauna 'a back side tanason jin ko dawa yakeyin hira ,tana kuma tunanin karya ce yafasa kaita inda takeson zuwa ,gashidai ba ko ina tasani ba ,kasancewar 'rayuwar Nigeria ba damuwarta bace, jitayi yace ”kya_kyawa burina bai wuce ingani ace yau nine angonki ba ,dariya suka sa itako Suhailat tunda taji sunan daya kira zuciuarta tafara tafar fasa ,saboda tanada zafin kishi ,bud'e mirfin motar tayi ta fice ,wata shu'umar dariya Khalil yasa saboda dayaso yaje hira gurin 'Nancy da ita kuma ya kulleta 'a mota ,fitowa yayi daga cikin motar da keys a hannunshi yana waya yana cilla keys sama ,momy ce tafito tanason aikan driver ta ganshi ,murmishi tayi tace ”yaron kirki kaida wa kake waya ¿cikin fara'a yace ”momy nida y'arki ne fa ,fatan alkairi tayi musu daganan tashige ciki , 6angaren Suhailat kuwa kuka takeyi tana neman mafita saboda bazata iya bari wata mace ta 'auri Khalil ba muddun tana raye ,dabara ce ta fad'o mata ,lokaci d'aya tasa dariya tace ”good ,number momynta ta lalubo kira takeyi amma ba'a d'agaba ,a karo na biyu ne momyn ta d'aga hello tace ”Suhy how a you? fine momy _momy akwai problems fa ,gyara zama momyn tayi tace ”bangane ba dama bakince zakije kiga yaron d'an uwan dadynku ba , eh tace ”daganan tafara kuka.....




Momy ce tace ”to kigayamin mana kinsan kukanki yana iya rusa farincikin mu ?,share hawayenta tayi tace ”momy inason Khalil momy da taji dad'in faruwar hakan tace ” to yanzu shi yasani ,a'a tace , shi wata ma yakeso fa ,momyn ce tace mata to ki kwantar da hankalinki ko ta halin yaya sai Khalil yazamo mijinki ,wani farinciki ne ya lulu6e Suhailat tafara yiwa momyn 'nata kirari tana cewa kai kinyi a rayuwa momy ina alfahari dake godiya mai tarin yawa ,dagan sukayi sallama.


*LONDON*
Momy Suhailat ce kwance a ciyar dadyn Suhailat ,tana shafa mai kai cikin sigar wayewa dakuma k'warewa ,tsawa tayi dadyn 'ne ya taso da kanshi yace what happen my only ?"cikin sigar jan hankali tafara kukan kissa ,janyota yayi ya mik'e yace ”to nikuma yau kike 6oyewa damuwarki ?shafo kanshi tayi tace ”mu muna nan muna farinciki Suhailat na cikin matsala !!dady jin kalamar yayi babu dad'i saboda babu abinda Suhailat zata nema 'a duniyar nan baiyi mata shiba saidai bayan ranshi ,momy ce ta kwashe duk inda sukayi da Suhailat ta gayawa dady ,dady ne yace ”ina raye?tabb ,barin kira d'an uwan 'nawa muyi magana , number dadyn Khalil ya kirawo ring d'aya dady 'ya d'auka ,gaisawa sukayi cikin girmama juna da bisani kuma dadyn Suhailat yace ”dama inason zamuyi wata magana ne OK ina jinka dadyn Suhailat ne yace ”inababu damuwa d'an uwana mai zai hana mu had'a 'zumunci a tsakanin yaranmu saboda zumuncin mu yayi k'arfi ,farinciki ne ya lulu6e dadyn Khalil yace

Please Login or Register in order to submit comment