Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

”aikwa danafi kowa farinciki sosai ma ,
Daganan sukayi maganar tsayar da rana two months sukasa bikin saboda tsaro."



Washe gari ne dadyn Khalil ya kirawo shi bayan yazo yake cemai abin farinciki fa yasamu ,Khalil ne ya dubi fuskar dady kamar anyimai albishir da shiga 'aljanna yace ”dady wani abinne yafaru ¿momy dake gefe tace ”oh kanata jamai rai koni 'in gayamai ne ?"cikin zolaya momy take maganar ,dady kuwa sai fara'a yakeyi ,yadubi Khalil yace ”dama mun yanke shawarar had'aka 'aure da Suhailat ,firgici tashin hankali duka suka dirar mai lokaci d'aya ,momy na karantar yanayinshi amma bata nunawa dady ba 'dady na gama fad'a ya tashi domin amsa kira 'a waya ,Khalil ne yaje ya rik'e k'afar momy ,idanunshi sunyi ja lokaci guda ,momy ce tace ”kayi hak'uri da za6in dadynka dan Allah ,Khalil ne yace ”kema momy bazakice komai ba ,dady fa ko tambayata inada wacce nakeso baiyi ba ya zartar da hukunci ,momy da tausayin Khalil ya kamata ,tace ”to yana tunanin ya isa da kaine shiyasa 'amma ka daure kayimai biyayya ,mik'ewa yayi jiki babu k'wari ya koma d'akinshi ya kwanta kallon sama yakeyi amma zuciyar shi na kitsamai kodai Suhailat ce ta had'a wanan lamarin cije Lip's d'inshi yayi yace”to walhi indai kuwa hakane saitayi dana sani a rayuwarta ."



Momy ce ta shigo cikin tausayawa tace ”karka nunawa dadynka baka yarda da za6insa ba dan Allah kayimai biyayya ,gashi bikinma saura wata biyu naji suna magana jiya to kawai Khalil yace ”batare daya kalli momy ba ya cusa kanshi cikin filo yana kuka kamar yaro ,tunanin alk'awarin da yayiwa Nancy yayi saboda zataga kamar harda sa hannunshi a maganar auran ,Suhailat ce ta shigo d'ago kai yayi ya kalleta can kuma ya maida kai ya rufe fuskarshi ,tana sanye cikin wata doguwar riga bak'a ta matseta sosai duk surarta 'zaka iya gani ,zama tayi kusa da Khalil tana murmishi tace ”mijin Suhailat yadai ?ko bakayi fatinciki da batun auranmu ba ,tana gama fad'a ya sauke mata wani wawan mari ,juyi taga d'akin yake yimata lokaci d'aya kuma tasa kuka mai cin rai ,wata sanda ya zaro ya hau turata da shi yana cewa koki fita wallahi kokuwa na nakasaki inga mai tsaya miki banza jaka wacce batasan yaya zatayi mutum ya sota ba
[31/01, 6:33 pm] Mom Islam ce💃: 💖🌷NANCY YAR KARYA 💖🌷.



_Mom Islam tadawo🚴‍♀️🚴‍♀️🚴‍♀️🚴‍♀️_.


story and writing

By

ZAINAB HABIB
{Mom Islam


________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page 35_36


,,,,,,,,,Ta fice ko waigowa bata sake yiba ,Khalil yarasa mai ke yimai dad'i ,kwantar da kujera yai ya kwanta yana sak'a da warwara ,ya dad'e a unguwar daga baya ya tada motarshi ya fice daga unguwar, da gudu ta shigo ta fad'a kan cinyar Umma tana kuka ,hankalin Umma a tashe ta d'ago mata kai tace ”mai ya faru ne kike wanan kukan ko wani abinne yasami Khalil d'in?" a'a Umma k'alau yake Umma yaci amana ta Umma bazan auri Khalil ba ,wani mari Umma ta tsinka mata ,hannunta a kumatunta ta d'ago jajayen idanuwanta tana cewa Umma mari kuma akan Khalil ¿"Umma ce ta dubeta tace ”dan bakida kunya da mutunci da hankali har zaki iya cewa bakyason Khalil ¿"kukane ya ku6ce mata tace ”umma aurefa zaiyi wai dadynsa ya yimasa matar aure shikuma baya sonta kuma yace dole saiya aureta ,Umma ce ta dubeta irin kallon yarinya kenan tace ”to ai bazaki tozarta ba tunda yana sonki ina ni walhi umma na dena sonsa ,wani marin Umma zata kuma kai mata ta mik'e da gudu tana kkuka."






Bikin Khalil da Suhailat saura sati biyu ,yaune momynta tace ”ta hayo jirgi ta dawo gida Khalil ba k'aramin murnar tafiyarta yayi ba saidai kuma ta d'aya 6angaren inya tuna da abinda iyayensu keson k'ulla mai yake k'ona masa zuciya ,dady ne ya umarceshi akan ya kaita airport ,babu musu ta shige suna cikin tafiya ne ta shagwa6e fuska tana cewa my sweetheart wlh zanyi missing d'in wanan lallausan jikin dakuma turaren mai k'amshi ,wata harara ya galla mata yace ”to munafuka ubanwa yabaki lokaci da damar da zaki ta6a jikinsa ¿" farr da ido tayi tana cewa karfa kadamu saura 2 weeks bikinmu bazamu dinga gajiya da juna ba ,wani uban burki yataka ji kake k'iiiii ,a tsorace ta ruk'o gefen rigarshi tana cewa kayi a hankali karkayimin asara ,nuyowa yai ya wanketa da wani mari yana cewa ku acan kuna tunanin iskancin da kukeyi muma shi mukeyi to ba haka mukeba."




Murmishin takaici tayi cikin ranta kuwa cewa takeyi walhi da badan so hana ganin laifi ba da kayi danasanin marina amma ai naci gari tunda har nasa zamuyi aure ,dagan an ya sauketa ko jiran ta shiga jirgi baiyiba ya juya da motarshi.

Shi yanzu damuwarshi Nancy ya zaiyi ta fahimceshi gashi wayarshi ma bata d'auka,
Gidan su Nancy ya nufa Horn yakeyi amma duk a banza ga kuma kiranta da yaketa yi amma bata kula ba ,Umma ce ta dubeta tace ”naga kamar Khalil ne yazo ko?"eh Umma dan Allah ki k'yaleshi ,kinci gidan ku Umma tafara yimata fad'a 'akan cewar ko mata uku zaiyi har tanada bakin magana lol fita tayi tana cika tana batsewa yau ko makeup d'in da 'aka sabayi ba'ayi ba sbda ran a jagule yake tana zuwa ta juya masa baya ,bayason fushin ta sbda 'a ganinshi fushi baya yimata kyau cewa yai am sorry ya had'e hanuwan shi biyu yana bata hak'uri , yace ”nace miki soyayyarki tayi nisa cikin zuciyata inbaki yarda ba zokiji bugun zuciyata ,nanma ko kallonshi batayi ba ,juyawa tayi ta koma gida sbda yanzu bama kishi ba tsana tayiwa Khalil ,sosai takejin zafi a zuciyarta kuma bata nadamar hukuncin da tayanke a kanshi ohh🤦‍♀️ my fans a ganina hukuncin yai tsauri hmm."

Da shigarshi mota gidan wani abokin shi ya zarce, hira sukeyi jefi_jefi amma rabin hirar ta y'an matan su ne ,Khalil da yarasa ya zaiyi kowane second tuno Nancy dakuma dariyata yakeyi amma ynz lokaci k'alilan ya tarwatsa soyayyar su oh Allah help me lokacin da wasu zafafan hawaye ke kwaranyowa daga idanun Khalil abokin 'nashi ne yace ”what happen my friend ¿" share guntun hawayen yai yace ”uhm karka damu inkaji matsalar ma bazaka iya temaka min ba ,KB ne yace ”amma dai 'inbaka mance ba tare muke magance duk wata damuwa tamu ko ¿"eh hakane cewar Khalil ,labarin soyayyar su da Nancy ya bashi sai dai bai fad'i hidimar da yayi musu ba sbda dan Allah yayi , KB ne yasa dariya ,Khalil ko kallon shi yakeyi yana cewa to kaga irinta ko ,dafashi KB yai yace ”com down abokina gaskiya kana sonta over ,amma ga shawara kuma kai da kanka zaka bani lbr ,juyowa Khalil yai ya fuskanci abokin nashi yace ”ina jinka ."

KB ne yace ”wato shawarata itace kadena kiranta 'a waya nabiyu kuma ka rage tunaninta wlhi zakayi nasara gani datakeyi kana nuna damuwa dakuma ywan zuwa kowane time shiya bata damar yimaka haka ynz dai ka gwada hakan ,godiya Khalil yayi wa KB ya fito sbda komawa gida.


Driving yakeyi amma hankalin shi ya kasu kashi_kashi 'ikon Allah ne ya kaishi gida ,da shigar shi dady 'yafara fad'a tunda katafi sai yanzu ka dawo karka manta yaufa weekend ne ko hutawa bakayi ba hak'uri yabawa dady ,Khalil na shirin shigewa bedroom yaji dady na cewa Suhailat harta sauka wai takira wayarka bata tafiya ,Khalil da bayason ko jin sunan Suhailat yace ”dady innayi wanka zankirata farinciki fall zuciyar dady dan gani yakeyi sun shirya kansu lol , momy dake gefe tana shan kankana tace ” Allah yayi mana za6i nagari ,dady ne ya 'amsa da 'amen y Allah.


Yau kwana uku kenan babu text babu kira 'wata zuciyar ce tace ”anya Khalil yana lafiya kuwa Kodai na kirashi ne ?"no tace ”zan zubar da 'ajina yasha zamansa ,shikuwa Khalil dauriya ce kawai sbda 'kullum yanason kasan cewa da zazzak'ar muryar Nancy amma yanzu bari yabi shawarar KB ."


Umma ce ta lura da Khalil fa baya zuwa hira ,kiran Nancy tayi dake kwance a gadon Umma ,maiya faru naga yaronnan baya zuwa hira ? Nancy ce tabawa Umma 'amsa cewar nima dai bansani ba.


Dan Allah kuyi hak'uri naga mutane da dama masu cigiyar book d'inan to kuyimin afuwa insha Allah munkusa komawa post kullum dominku masoyan Nancy tace ”in gaishe ku .


Page d'in dai babu yawwa wasu sunata cewa inkara ywan page gaskiya inaso in kara saidai abu guda ☝️wlhi rashin shar'hi banajin dad'i gani nakeyi bama 'a karanta book d'in amma inayin kwana biyu ko sama banyi ba zanga ana tambaya please kudingayi my fan's👏sbda kuga page mai ywa love you all 💞👍.
[31/01, 6:33 pm] Mom Islam ce💃: 💖🌷NANCY YAR KARYA 💖🌷.

_Labari mai d'auke dasa nishad'i tare da fad'a karwa_

*~ALKALAMIN DA BAYA RUBUTA SHIRME~*✍️.


_________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



Page 37_38

,,,,,,,,,Zaune take ta zuba uban tagumi ,oh na shiga uku ni Nancy kayan makeup d'ina sun k'are gashi bani da kud'i ,nakwashe duka kud'in 'nayimana siyayyar kayan abinci ,jitayi duniyar tayi mata zafi sosai ,shawarar ta kalaci man shafawarta da ragowar powder ta shafa ta fice tunda tanada kud'in hawa mota ,kawai ta nufi kasuwa , tofa wanka tayi tazo tafara tsara kwaliya ,ragowar turarenta mai gigita samari tasa , ta fito da wata tsadaddiyar shadda pink mayafinta fari hakama takalminta ,inka ganta zaka rantse yar wani mai kud'inne ,fitowa tayi da gabjejiyar wayar da Khalil ya siya mata ,tana gogeta ,cewa umma tai natafi zani gidan su wata yar ajinmu lokacin ina gidan su hajiya, Umma ce tace ”kidai rik'e mutuncin ki Allah ya dawo dake lafiya ,amen umma Nancy tace lokacin da ta sanya farin glass a fuskarta ."


Tana zuwa bakin titi babu napep hakan yasata duba agogon hannunta tana tsaki ,wata tsaleliyar mota ce ta tsaya 'a gabanta ,matsawa tayi tana yatsina fuska ,zuge glass d'in motar akayi tare da cewa ”dafatan gimbiya kuma sarauniyar mata ta tashi lpy ,juyowar da Nancy zatayi taga ko waye yake magana murya 'a mak'ale oho .


Tunda Suhailt ta sauka Momy tafara yimata gyara da kayan gyran jiki ,kama daga fata har gashin kai dakuma gyaran magunguna acewarta wai sotakeyi taga yarinyar tata tafi shauran mata lol,
Tun Suhailat na shan 'na marmari har tazo ta dena kasancewar maganin ya had'u sosai ,momy ta kashe kud'i.

Abu sai matsowa yakeyi yau bikin Khalil da Suhailat saura kwana biyar hidima 'akeyi ta kowane 6angare dady da momy basuda lokaci sbda hidin dimu sunyi musu yawa ,y'an uwan momy harsun fara zuwa kasancewar bikin na y'a 'yan manya ne , wanki lafiyayyen gida dady 'yabashi ,gidan ya tsaru komai na ciki tsarre ne baki bazai iya fad'an kyaun gidan ba .

Yau ta kama Monday yau akayi Indian day ,washe gari talata Suhailat takira Khalil akan cewar yakamata yazo fa akwai wani wasa da k'awayenta suka shirya mata ,Humaid da 'abubuwa suka taru suka cunkushe masa guri d'aya yace ”waike wacce irin marar lissafi ce wlhi kika sake kirana zanyi maganinki ,da haka Suhailat ta kashe waya haka sukayita gudanar da 'al'adunsu babu ango ."

Yau alhamis yaune dady 'ya dawo da furniture's d'in Suhailat wow abin sai wanda yagani bama 'a London aka siyo ba wata k'asar aka tafi kashe kud'i sukeyi kamar basu san zafinsu ba 'a cewar momyn Suhailat y'a d'aya tilo ce dole a tsara mata komai na rayuwa ."

Yau juma'a da fitowar Suhailat wata k'warta mai suna Nussy tazo ,momy take cemata bana hanaki fitowa ba ,kushiga ciki ,da shigarsu suka fara hira sosai kuma hirar dukta inda za'a maida Khalil masoyi akeyi Nussy da 'a shekaru batafi 23 ba amma batayi aure ba 'sai dai shu'umanci irin nata sai _ita, wani turare ta ciro cikin wandon ta tace ”kinga gudunmawata nan banason tarkace wlhi kikayi wasa da tirarennan to Humaid zai 'iya ku6ce miki ,matsowa Suhailat tayi ta ruk'o Hanun Nussy tace ”nifa indai Khalil zai zamo nawa ni kad'ai to ina murna ,dariya Nussy tasa tace ”bakida dama gaskiya kin shige da yawa , to yazanyi da turaren ,cewar Suhailat ,Nussy ce ta kashe mata ido tace ”inason kibani tukwaici ,zaro ido Suhailat tayi sai dai wani abu da mai karatu bai sani ba ,shine duk wanda Nussy tabawa umarni to kwarjinin ta shikesa ba'ayi mata musu ,kasancewar bokaye kuma yare kala kala take amfani dasu yanzu haka ma bata gaban iyayenta a makaranta suka had'u da Suhailat, gaskiya Suhailat bata ta6a aikata wani iskanci ko akasin hakan ba itadai barta da rashin kunya.


To My Nussy tukwaicin mai zanbaki ?✍️.

Nasan kun matsu kuji ko ?dafarko dai kunason jin dawa Nancy ta had'u?"

Na biyu kuma wane tukwaici Suhailat zata bawa Nussy ?".

Karku damu muje zuwa innaga sharhi to anjima zan sambad'o muku wani inko bangani ba sai gobe ko jibi love you all💖.

[31/01, 6:33 pm] Mom Islam ce💃: 💖🌷NANCY YAR KARYA💖🌷.

_Labari mai d'auke dasa nishad'i tare da fad'a karwa_
_________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Page 39_40


,,,,,,,,,Sanye yake cikin bak'in yadi mai laushi ga shek'i ,fuskar sa na sanye da bak'in glass wanda ya rufe kyawa wan idanunsa,gyara tsayuwar ta tayi tace ”Khalil !!! lumshe murmishi yai tare da ”cewa mai kyau kin manta dani ko?" hawayen da take k'ok'arin tarewa ne sukayi nasarar zubo mata ,ya ilahi yafad'a lokacin da ya bud'e murfin motar yana shirin fitowa ,ji yakeyi kamar ya rungume ta ko zuciyar sa zata yimai dad'i ,juya masa baya tayi tana share hawayen fuskar ta ."

Takowa yakeyi cikin tak'ama ya iso gurin ta ya sunkuceta tana k'ok'arin sauka 'amma babu hali sbda Khalil d'in ba rago bane , yasata a mota key yai wa motar suka bar wajen ,sunyi tafiya mai nisa babu mai magana sai sanyin AC dake kad'awa had'e da had'a d'en turare mai k'amshi , guraren da Khalil ke shiga tunda tazo Abuja bata ta6a shiga ba ganin yana shirin shiga wani katafaren guri mai kamada Zoo yasata ware ido bata daiyi mgna ba ,da shigarsu gurin aka Khalil yaciro kud'i yabada 'aka basu wani kati ,yana tafe tana binsa 'a baya ,mutane ta hango iri _iri har dasu turawa da sauransu kowa kagani a gurin tafe take da saurayin ta wasu na d'aukar hoto wasu kuma na wasa da flowers wasu kuma na gurin cin abinci , wani guri taga Khalil ya shige yana yimata nuni da tayi sauri, da shigarsu ta hango kayan ciye ciye wanda tasani da wanda bata sani ba ,Khalil ne yace ”zoki za6i abinda ranki keso ,shiru tayi tana kallon shi ,k'arar wayar shi ce yasata kuma maida hankali gurin kallon shi ,tsaki yayi yace ”ke wace irin dak'i k'iya ce menace miki jiya don't worry zanbaki mamaki ba lefinki bane ,ya kashe wayar ,kuka Nancy tafara ,ta fice a guje tana kuka ,Khalil ne yasami guri ya zauna yana cewa wlhi Suhailat karkiyi tunanin farinciki zaki tarar a gidana lol."


Wasu y'an mata ta hango sanye suke da dogayen wanduna na jeans dasuka kama jikinsu ,d'ayar ce tace ”dan Allah sis zoki rakani gurin wacan beautiful d'in inason muzama k'awaye ,tashi sukayi suka nufi gurin da Nancy ke zaune tana kuka tana ganin mutane sun doso gurin ta tafara share hawayen fuskar ta, sallama sukayi ,bayan ta amsa musu ne suka fara janta da hira kasancewar sunga bata cikin walwala , tad'an sake dasu sosi d'ayar ce tace ”ni sunana Jamila ita kuma lil sis sunanta Karima ,masha Allah Nancy tace ”tana k'are musu kallo sbda tasan dukkansu ba 'ajinta bane jikinsu ma ya nuna daga inda suka fito ,Karima ce tace ”to baki fad'a mana sunanki ba ,murmishi Nancy tayi tace ”sunana Nancy nice name Karima tace lokacin da take ruk'o hannun Nancy ,amma Nancy naga kamar kina cikin damuwa ko ,eh tace ”can k'asan zuciyarta batason susan halinda take ciki ,amma lokaci guda taji ta yarda dasu ,kwashe labrin soyyayar su da Khalil tayi dakuma labarin Suhailat tabasu babu abinda ta 6oye musu , murmishi sukayi suna cewa to yanz ai kece da laifi because dayace dadynsa ya....hango Khalil tayi yana shirin tahowa gurinsu .....✍️.


Zanyi typing anjima 'amma innaga sharhi 🥰.

Banga sharhi sosai ba shiyasa kukaga rubutun kad'an👌kudaure ku sanbad'o sharshi nima in daure in sanbad'o muku typing da yawa.
[31/01, 8:42 pm] Mom Islam ce💃: 💖🌷NANCY YAR KARYA💖🌷.

_Labari mai d'auke dasa nishad'i tare da fad'a karwa_


________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Page 41_42


,,,,,,,,,, Yasa Nancy cewa to yanzu dai kubani number ku ma k'arasa mgna inna koma gida, Khalil na k'arasowa yace ”sweetheart zomutafi ,karima ce ta kashe mata ido d'aya alamar tamik'e ."

Gaishe shi Karima da Jamila sukayi, cikin sakin fuska ya 'amsa daganan sukayi sallama da Nancy bayan sunyi musayar number, sun d'an yi nisa kad'an ,Khalil yace ”daga had'uwa har kina basu number ko?" Nancy da dama jira takeyi yayi mata mgna ta sanyaya muryar ta tace ”to bagashi sun sani dariya ba tayi farr da ido tana "cewar har sunsa na mance da fushin da nakeyi dakai, wata tsadaddiyar dariya ce ta ku6cewa Khalil har yana rawa, tsabar farinciki har k'ok'arin rungumota yakeyi ,ja da baya Nancy tayi tace ”haba mijina what!!! yace ” Allahu Akbar ya d'aga Nancy sama yana juyi da ita ,Nancy na k'ok'arin sauka sbda lokaci_lokaci tana tuna nasihar umma, rik'eta yai kamar baby ,yana k'arewa fuskarta kallo, wani kyau yaga ta k'arayi , mai makon tayi hanyar mota su wuce ina ai saita ruga da gudu ta shige cikin wasu flawoyi masu ban sha'awa ,binta yayi da gudu sunata dariya, Karima ce ta hangosu ta ta6o Jamila see this lover's ehem kamar ba itace mai kuka ba ,kinga yanzu 4:pm zomu tafi kar dady yai mana fad'a ,tafiya sukeyi suna waigen su Nancy."

Wayo Allah koni wanan page d'in yasani nishad'i 🥰 tofa ta mance da umma a gida 🤣.

Duba agogon dake d'aure a hanunta tayi 4:20 zaro ido tayi tana cewa mijina zomu tafi lokaci ya tafi da ywwa ,Khalil ne yace ” beauty kinason katsemin jin dad'i ko ,Nancy ce ta marai raice fuska tace ”nikuma kanaso umma tayimin fad'a ko?"dariya sukasa daganan sukayi mota ,driving yakeyi cike da annashwa yana kallonta itako ta kashemai ido lol."



Da isowarsu anguwarsu Nancy ya mik'a mata leda mai kyau yace ”nace ki za6i duk abinda yai miki to kinki za6a nigashi na za6a miki ,murmishi tayi tace ”Allah ya k'ara bud'i ,wani farinciki ne yakuma ziyartar zuciyar shi yace ”amen sweetheart ,to ki gaida umma 'anjima zamuyi waya ,hannu ta d'aga masa tana cewa dan Allah ka gaida momy ta had'e hannuwan ta biyu please, ok aikuwa zan isar da sak'o ,to bye ka kulamin da kanka ,ta shige gida da gudu, girgiza kai Khalil yayi yace ”oh Nancy bata girma ."



Yau asabar yaune dubban jama'a suka sheda d'aurin auran *IBRAHIM KHALIL* da Amaryarsa *SUHAILAT*
Akan sadaki mafi albarka dubu d'ari kowa kagani fuskarsa cike da annuri ,dady ranar juma'a suka tafi yau zasu koma gida ,ango ko abokanshi bai gayyata ba bare susan da labarin bikin ,ana d'aura aure ya zarce airport sbda komawa gida."

zaune take da k'awayen ta sirruka suke bata na musaman kama daga ranar da Khalil ya shigo d'akinta har style na kwanciya hmm rayuwa kenan...✍️.

Kuyi hakuri da wanan kun cikamin alkawari nima banason sa6awa nawa alkawarin gawanan babu yawa,
A gaskiya yau naji dad'in sharhi sunanku sunyi yawa Allah yakaro soyayya 🥰mom Islam tana yinku .
[31/01, 9:00 pm] Mom Islam ce💃: 💖🌷NANCY YAR KARYA💖🌷.

_Labari mai d'auke dasa nishad'i tare da fad'a karwa_



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Page 43_44


,,,,,,,,Da sallama ta shige gidan zaune ta tarar da Umma ta zuba uban tagumi , ajiye jakar hanunta tayi tana cewa umma lafiya?" Umma ce ta dubeta tace ”yanzu kin kyauta kenan cemin kikayi bazaki dad'e ba 'amma maiyasa yanzu fa k'arfe hud'u da arba'inne 4:40 fa ,kiyi hak'uri Umma Khalil ne ya ganni a hanya wai sai dai muje anguwa shinefa yakaimu gurin shak'atawa ,murmishi Umma tayi tace ”Khalil d'an albarka ne Umma kinga 'abinda yabani ,bude ledar Nancy tayi ganinsu chocolate dasu snacks da sauransu ,bandir d'in yan d'ari _d'ari sababbi tagani , zaro ido tayi tana "Cewa Umma kinga haarda kud'i ,albarka Umma tadinga sanyawa Khalil daganan Nancy ta shige danyin alwalah."

Misalin k'arfe 5:pm jirgin su suhailat ya sauka 'a Abuja ,mutane y'an biki sunzo airport taryar su cike da farinciki ,da isarsu gidan su Khalil aka wuce da ita saida momy da dady sukayi mata nasiha sanan aka wuce da ita gidan ta itada k'wayenta, da Nussy da Rukky ,k'arewa gidan kallo sukeyi ,duk iyayinsu basu isa suce gidan baiyi ba kasancewar komai na more ratuwa ansa babu abinda babu kuma komai ya tsaru , d'akinta aka wuce ta ita ,bayan sun zauna ne suka fara hirarsu ta y'an duniya ,Nussy ce ta dubi Suhailat 'tace ”beb bamu k'arasa shirinnan bafa sbda daga yau anyi finale ,nidai fitowa nayi ko mezasuce oho.

Muje zuwa


Khalil ne kwance shida KB suna hirar bikin shi ,KB ya bugi kafad'ar Khalil yace ”ango tashi 'in raka ka kar dare yayi nisa fa ,harara ya gallawa KB wanda yasashi rufe baki ,juyi yakeyi amma yarasa maike yimasa dad'i wayo Allah na ,yace ”lokacin da yatuno da cewar wai aure aka yimasa , number Nancy ya lalubo ,kana ya danna kira ,Ring biyu ta d'aga tare da cewa"Aslamu Alaikum mijina ,cikin kasan zuciyarshi yanajin sanyi yace ”inama kece matar da aka d'aura mana aure yau wlhi dan a koyar dake makarantar soyayya wayo momyna , wayo fans ashe maganar Khalil ta fito fili🤣, a zabure Nancy ta mik'e had'e da cewa kutumar uuba...ka..ka ,takasa magana sai wasu zafafan hawaye dake ambaliya a fuskarta , a firgice Khalil ya mik'e cikin tashin hankali KB ko daman yasan hakan zata iya faruwa sbda Khalil bai iya 6acin raiba ."


Washe gari su Nussy da Rukky suka wuce Landon jirgin safe suka bi bayan sunkammala shawar warinsu .

*MISALIN KARFE BAKWAI NA DARE*.


Zaune yake a d'akin momy kanshi a k'asa yayinda kunnuwansa ke saurarar maganar ta ,Khalil ni kaina ba 'ason raina dadynka yai ma wanan za6in ba sbda naso ace ka 'auri wacce kakeso, amma haryanzu lokaci bai k'ure ba ,sai dai shawarar da zanbaka karka wulak'anta y'ar mutane ,kasani yanzu amana ce a gurinka ,kayi k'ok'ari ka sauke hakkinta daya rataya 'a wuyanka dan Allah Khalil, karka zamo silar 6atawar zumuncin ku, ruk'o hannun momy yayi yana share mata hawayen da suka zubo mata yace ”momy kinsan bana yimiki k'arya ,to gaskiya wlhi bazata sami duka abinda kikace ba amma zata sami kad'an ,albarka momy ta sanya masa tare da had'a masa shayi mai kayan k'amshi ,Saida yayi sallahr isha'i sanan ya nufi gidan Amarya lol, jin alamun shigowar motarshi yasata k'ara bud'e skirt d'inta ta shafa wanan turaren a mara dakuma k'asanta , gakuma wasu rikitattun humra da momynta ta bata, tunda Khalil ya doso palorn ya shak'i kamshin turaren da Suhailat tasa ,jiyayi lokaci d'aya mood d'insa ya sauya sha'awa ce kokuma mutuwar jiki ...✍️.


Dan Allah kuyi hakuri yau aiyuka sunyimin ywwa ana tare🤝gaskiya sharhin ku yana birgeni 💃.
[31/01, 9:00 pm] Mom Islam ce💃: 💖🌷NANCY YAR KARYA💖🌷.

_Labari mai d'auke dasa nishad'i tare da fad'a karwa_



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Page 45_46


,,,,,,,Kwnce take zazza6i mai zafi ya kamata ,hankalin Umma yai matuk'ar tashi sosai gashi batasan ina zata samo magani ba, kasancewar sunada nisa da shaguna , k'ullin kayanta ta dubo hayaki na zazza6i tazo tayi mata."


Momy ce zaune kan sallaya tana jerowa Khalil adu'oi ,shigowar dady 'yasata shafawa takai dubanta ga inda ya zauna, momyn dady ne. yace ”momyn Khalil hak'ik'a wanan had'in yayi armashi tabbas auran zumunci akwai dad'i, murmishi momy tayi tana cewa Allah ya zaunar dasu lafiya ."

Tunda Umma tayiwa Nancy hayak'i Allah ya temaka ta sami lafiya ,zama Umma tayi a gefen nata ta ce ”mai yake damunki dan naga yanayinki ya sauya ? sunkuyar da kai k'asa tayi tace ”Umma Khalil tayi aure ,Umma ce ta sanyaya murya dan yanzu sai dai ta kwantar mata da hankali, "wato Ummi bazaki iya hak'uri da

Please Login or Register in order to submit comment