Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

juna fatan sake had'uwa , daganan Duduwa ta tattara akwatin ta zuwa anguwar da takama haya , bayan ta biya wanan mutumi dubu hamsin ,

Da shigar ta gidan taci karo da wata datijuwar mata da 'a shekaru zatakai sittin a duniya , gaisheta Duduwa tayi kana ta nemi d'akin da 'ya zamo nata ,

Tunda tazo birni bata tunanin komawa k'auye saboda wahala zatasha 'a can ,


Tana zaune tana tunani , taji wayar ta na neman agaji , duba number tayi ganin Khalil yasata sauke gwau ran nunfashi , daga can 6an garen shi yace", kya kyawa yakike yasu momy ?cikin sanyin jiki tace lafiyan su lau , daganan yafara janta da hira , bata wani sake sosai ba , ganin haka Khalil yace"kodai baki da lafiya ne ?eh tace "daganan yayi mata fatan samun sauk'i sukayi ssallama,


Washe gari ta 'tashi da wani matsa nancin ciwon kai , saboda kukan data sha jiya da daddare , ganin wata jaka mai kwalin lifton har , uku yasata duba sauran kayan dake ciki suga na da bonvita dakuma biskit na shan shayi, in bazata manta ba Anty Humaira ce tabata leledar....✍️✍️✍️.

_mom Islam ce_

*please share*🤝
*Comments*
Vote✔️
💖🌷NANCY Y'AR K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._


_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.
________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 13_14

____ Hajiya ce tace" akwai wasu kud'a d'e da take bina sunkai , dubi d'ari uku , zaro ido Duduwa tayi, saboda har tafara tunanin kalar gidan dazata siya bayan an biya ta kud'inta,


Hajiya ce tafara wani 'irin tari kana wani , miyau _wato yau mai kumfa yafara biyo baya , tana gamawa rai yayi halin sa, kowa na hospital d'in saida ya tausaya mata bare yaran da Hajiya tabari , wani 'ihu Duduwa ta kurma tana cewa, na shiga uku bani da gata sai Allah, ganin kukan 'nata yayi yawa ne yasa doctors d'in sukayi waje da ita,




Anty Humaira ce tadin ga kiran waya tana gayawa y'an uwa rasuwar Hajiya , hak'ika mutuwar ta ta6a kowa saboda Hajiya bata da son duniya ,


😭Allah kasa muyi k'ya k'yawan k'arshe amen 🤲.



Bayan rasuwar Hajiya da kwana biyu, y'an uwan Hajiya suka ce zasu tafi da su Humaira garin su,
Duduwa bata gama tabbatar da , rasuwar Hajiya ba sai lokacin da wani dattijo wato d'an uwan Hajiya ya kira ta, yana cema ta yanzu kulle gida zasuyi saboda , umarnin Hajiya zasu bi,

Wasu hawaye ne masu zafin gaske suka zubo mata , duk da kud'in da take ganin kamar inta samu zata warke , amma yanzu jikin ta yayi sanyi sosai,

Washe gari ta tattara kayan ta tana neman gidan haya , cikin ikon Allah tasamu wani mutumi da yake kusa da gidan su yana dashi a can wata anguwa ta' talakawa ana kiran anguwar Riga y'ar kasuwa ,


Tambayar shi kud'in hayar tayi , cemata yayi dubu hamsin shekara d'aya , bayan sunje gidan tagani tace" mai yama ta uzuri saboda ba'a bata kud'in taba , cikin 'nuna rashin yarda yace" sai dai tabari 'in aka biyata sai ta koma ,


Gidan da mutumin ya kaita gidane mai kyau ma'ana 'akwai siminti kuma akwai bayi a ciki ga kitchen a waje bayi a d'aki ,

Mata biyu ne a cikin gidan kuma duk zasu girme ta d'aya tana da miji d'ayar kuma karatu ne ya kawo ta saboda bazata iya zaman hostel ba,

A yau ne akayi bakwai d'in Hajiya, an sallami Duduwa kud'in da Hajiya ta buk'ata 'a bata, alhamdulilah uncle yabata dubu d'ari uku da hamsin , kuka Duduwa takeyi sosai saboda 'a ganin ta sunyi mata hallacci,


*Wayoo kud'i 😫 Anty Nancy bani aron two thousands🤨*


Bayan sun su Anty Humaira sun k'ara bata kaya sabba bi dakuma gyale da hijab , sosai suka yiwa juna fatan sake had'uwa , daganan Duduwa ta tattara akwatin ta zuwa anguwar da takama haya , bayan ta biya wanan mutumi dubu hamsin ,

Da shigar ta gidan taci karo da wata datijuwar mata da 'a shekaru zatakai sittin a duniya , gaisheta Duduwa tayi kana ta nemi d'akin da 'ya zamo nata ,

Tunda tazo birni bata tunanin komawa k'auye saboda wahala zatasha 'a can ,


Tana zaune tana tunani , taji wayar ta na neman agaji , duba number tayi ganin Khalil yasata sauke gwau ran nunfashi , daga can 6an garen shi yace", kya kyawa yakike yasu momy ?cikin sanyin jiki tace lafiyan su lau , daganan yafara janta da hira , bata wani sake sosai ba , ganin haka Khalil yace"kodai baki da lafiya ne ?eh tace "daganan yayi mata fatan samun sauk'i sukayi ssallama,


Washe gari ta 'tashi da wani matsa nancin ciwon kai , saboda kukan data sha jiya da daddare , ganin wata jaka mai kwalin lifton har , uku yasata duba sauran kayan dake ciki suga na da bonvita dakuma biskit na shan shayi, in bazata manta ba Anty Humaira ce tabata leledar....✍️✍️✍️.

_mom Islam ce_

*please share*🤝
*Comments*
Vote✔️
💖🌷NANCY Y'AR K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._


_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{Mom islam}

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 15_16

____Dauko su tayi kana tarasa inda zata dafa ruwan zafi, bayan tayi wanka da ruwan sanyi tayi kwaliya tana gamawa , ta d'auko , wani less mai ruwan ganye wow kuzo kuga kyan da , Nancy tayi , wani takal minta marar tudu ta d'auko kana ta yafo farin gyale ta fito , rik'e da mukullin d'akinta bayan ta d'ibo kud'i marasa masu d'an yawa ,
Tafiya takeyi cikin yanga , inka ganta zaka rantse y'ar shugaban k'asa ce saboda iya taku irin'na Duduwa , mai adai_daita ta gani yana tahowa , hannu tasamai ya tsaya, cemai tayi ya kaita kasuwa , maraba ya kaita , wani shago ta hango na kayan shafe_shafe , shine ya d'auki hankalin ta tayi wajen ,
Da shigar ta shagon wasu samari dabaza su wuce 27yrs ba suka fara cewa maraba hajiya mai kikeso ?" cikin yanga Duduwa tafara magana tana fari da ido , powder ta d'auka , mai kayanne yace" dubu d'aya , ko tayi batayi ba tafito da kud'in tabashi ,

Wani saurayi da naji suna kira da Usman ya k'araso gaban Duduwa ,itako ganin had'uwa irinta bawan Allah yasata rud'ewa , magana yafara yimata cikin wata da sanyar murya , saida ta lumshe ido kana tace ina lafiya tayi hanyar waje ,
Binta yayi cikin k'aware wa saikuma yaga taje gurin masu siyar da electri tana tayawa , mutumin ne yace " dubu 'uku zata bashi , sai wanan saurayi ya ciro kudin yabada , batasan yana bin ta ba ,

Godiya tayimai kana tafara tarar motar dazata kai ta gida , k'ara sowa yayi da sauri yace"please kibari 'in kaiki gida 'a mota ta 'a'a tace"kana tacigaba da tafiya , saida ya rok'ota yanata had'ata da 'Allah tukun tabari ya kaita a mota,



Suna cikin tafiya suna hira kad'an kad'an , yake tambayar ta inane anguwar su ?" saida tayi jimm kafin tace (A.Y .A),

*Wato cikin abuja kusada su baba buhari🤣*


Tamabayar ta number gidan yayi , bata nuna mai ba saidai tace"mai yabari 'idan sukazo zata nunamai gidan ,
Wani tsararen gida ta hango , fad'in tsaruwar gidan ma 6ata lokaci ne amma , my Fan's kuyimin afuwa , gidan kamar a k'asar waje,

Usman 'ne ya kalle ta kana yace nanne gidan Ku ?cikin gadara tace " eh nanne , yace to barin in shigo mu gaisa da momy , kasa magana tayi ,
Suna shiga na hango wata budurwa da bazata gaza shekara goma sha biyar ba , tana ganin su tafara bro, alamar tayi shiru yayi mata kana ta gimtse dariyar ta saboda ta d'auka yazo da budurwar sa ne,


Da shigar su cikin gidan sukaci karo da wata mata fara doguwa ba can can ba , ganin Usman yasata ,fad'a d'a fara'arta tace"Usman har kuntashi a shagon 'ne? Duduwa ce tazaro ido tana tunanin wai'inama tazo ne, murmushi Usman yayi kana ya dubi , momyn shi yace"momy wanan itace budurwa ta, cikin farin ciki momy tafara yiwa Duduwa tsiya 'akan tak'i sakin jikinta suyi hira , momy na fita , Usman ya cewa Duduwa yana zuwa, to tace mai saboda jitakeyi kamar k'asa ta tsage ta shige dan kunya , yana fitowa rik'e da zam6a leliyar bulala ya zuba mata biyu lafiyai yyau , ganin yana neman jimata ciwo ne yasata rugawa ta fice da uban gudu daga gidan...✍️✍️✍️


_Masoyana nifa burina baya wuce ganin comments &shar'hi indai kunaso in k'ara yawan Page to kudage💪nikuma zan sambad'o muku shi 💃_


_mom Islam ce_

*please share*🤝
*Comments*
Vote✔️
💖🌷NANCY Y'AR K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._


_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 17_18


____Bayan ta fice ne daga gidan taci karo da wani mutum , a wata galle liyar mota mai nunfashi, ganin mutumin yasata saita tuna nutsuwar ta , cikin isa mutumin yace"Hajiya ina zuwa ne ? gyara muryar ta tafara yi kana tace ba da nisa zani ba , gidan mu yana can gaba , hango wani katafaren gidan da Duduwa ta nuna yayi , a iya sanin shi wanan gidan gidan k'anwar momyn shi ce amma baisan ko tayi bak'uwa ba , cewa yayi to inba damuwa ki shiga in k'arasa dake , k'in shiga motar tayi , shikuma ganin haka, yasa shi yadinga binta a hankali har sukazo dai' dai gidan , ganin bata shiga gidan ba yasa shi tsayawa, da motar shi yafara dogon tunani".




Ita ko Duduwa burin ta tagan ta 'a cikin d'akin ta , seda tayi nisa sanan taga wani mai adai daita , hannu tasamai ya tsaya , tace "mai RUGAN JULI cemata yayi d'ari biyu babu musu yace" tashiga suka wuce".



Da isar ta gida ta tuna da electri d'in ta da powdern da tasiya duk ta man cesu gidan su Usman,kamar zatayi kuka , sai yanzu takejin yunwa ta dawo mata sabuwa , k'ara fita tayi anan ta hango wani shago na siyar da kayan ci k'arasawa tayi kana tayi siyayar abin da take buk'ata , tana hanyar dawowa ne taga wani saurayi ,mai kamada Kalil , dad'a ware ido tayi kana tace" kamar Khalil ko?
Kashe mata ido d'aya yayi kana yace"nine kya kyawa nadawo jiya, amma mai kikeyi a nan anguwar ? gyara mayafin ta tayi kana tace"nazo duba wata yarin yar abokin dady na ne amma kai maikazo yi? dariya yayi mata kana yace"najiyo bugun zuciyar ki ne shiyasa nayo nan anguwar,
Amma inba damuwa maizai hana ki zo muje ki gaida momy na , wallahi kullum saina bata labarin ki , murmushi Duduwa tayi kana tace"to ai kaga ban sanar dasu Hajiya ta ba , 😓(Allah sarki kidena yiwa hajiya karya saboda taci yalo😫)".



Cikin ta ttausan kalamin shi yace "please kya kyawa kokuma Nancy kizo muje a mota ta Allah bazaki dad'e ba , to tace " mai kana suka shige motar , ammafa tabar kayan da tasiya gurin mai shagon anguwar su,
Suna cikin tafiya yana bata labarin irin missing d'in ganin kya kyawar fuskar ta dayayi , cikin shgwa6a tace" ai na fika wallahi ,


Seda sukayi tafiya mai nisa sannan suka shigo anguwar su Khalil wato (WUSE TWO , G.R.A),


Tunda take bata ta6a ganin kyau da tsari kamar na gidan su Khalil ba , ko gidan su 'Usman baikai kyan'nasu Khalil ba , horn yayi wani dattijon mai gadi ne ya bude musu gate , bayan sun fito daga motar ne yaciro wata k'atuwar leda a bayan , motar shi".


Dama ya sanar wa da momyn shi babu musu suka shige yana rik'e da hannun ta , bataso rik'e hannun da yayi mata ba amma saboda karta kwafsa yasata biye mai,

da sallama suka shiga cikin parlorn , ganin k'awatuwar d'akin'ne yasa Duduwa tsayawa tana kallon kowani ,ado na d'akin ,

Allah yasa babu kowa da kinbamu kunya anty nancy🤣".

da bayan sun zauna ne saiga wata mata mai kamada ,Khalil amma saidai ,Khalil yafita haske, tunda ta k'araso momy tana ta fara'a da 'alamun farinciki a shimfid'e a fuskar tta,

Bayan ta zauna ne Duduwa ta , sauko daga kan kujerar da take zaune , ta durk'usa tana gaida momy , bayan momyn ta 'amsa ne tace"ai munzama d'aya yarinya taso zonan , cikin farinciki Khalil yace"Nancy kije momy na kiranki.....✍️✍️✍️.


Masu cewa bana typing da yawa kuyi hakuri wlh jikinne sai a hankali🤦‍♀️, fatan alkairi sisters and antys

_mom Islam ce_


*Please share🤝*
*comments*
Vote✔️
💖🌷NANCY Y'AR K'ARYA💖🌷.




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 19_20


_____K'arasawa tayi kusa da momyn Khalil , bayan ta zauna 'a kusa da k'afarta momyn tace" a'a kitashi."

Kin tashi Duduwa tayi , yin hakan da Duduwa tayi yasa momy k'ara jin sonta 'acikin zuciyar ta, y'ar aikin gidan ce ta shigo da tire d'auke da kayan mar mari a ciki , a gaban Duduwa ta 'ajiye , sunkuyar da kai Duduwa tayi ,kuma 'acikin zuciyar ta tana son ta d'auka amma tana kunya , momy ce tace" Nancy ki d'auka kici mana , batayi magana ba sai ma mur mushi datayi, Khalil ne yace"Momy please kibamu guri wlh kunyar ki takeji , cikin shagwa6a yayi maganar , dayake Khalil d'in gwani ne gurin iya shagwa6a ".

Dariya momy tasa mai sauti ,kana ta mik'e tace kai ma taso muje saboda zaka iya hanata , jeka kiramin Ummi tazo ta kawo mata abincin inta gama had'awa , shima dariyar yakeyi , ya mik'e ya rufawa momy baya, amma har yabar gurin idon shi na kan gimbiyar tashi wato Nancy, bayan sun tafi ne ta gyara lulu6in ta, kana gyara zaman ta 'tafara cin ayaba tsabar yunwar da takeji saida taci ayaba uku lemu biyu kan kana yanka hud'u sai tuffa guda d'aya,

,(oh🤦‍♀️Anty Nancy kinbani kunya daga cewa abaki guri , shine kika cinye abincin Allah yasa ma tiren a cike yake da kayan mar marin😫".


Ummi ce wato y'ar aikin gidan tafe da kulla abinci da jug na lemu mai sanyi wata kulla na hango cike take da farfesun kaji ,bayan ummi tagama 'ajiyewa ne ta wuce tabar gurin ".

Cikin wanan abincin da 'aka kawo abu d'aya Nancy taci shine naman kazan kuma guda d'aya ta d'auka ta mayar ta 'ajiye".

Burin ta kawai tagan ta 'a gida saboda 'a yanzu hankalin ta yafara tashi , Khalil ne yashigo da 'alamu wanka ya kuma yi saboda ba kayan d'azu bane a jikin shi, kashe mata ido yayi kana ya matso kusa da ita ya zauna 'a k'asa yace" Nancy mai yasa kika k'i sakewa da momyna ? cikin jin kunya tace"dan Allah ka maidani gida , dariya yayi sosai kana yace"ai anan zaki kwana yarinya, cikin murya kamar zatayi kuka tace "shikenan nagode babu komai ,dayaga 'alamun ranta ya 6aci sosai ya durk'usa ya rik'e kunnen shi kana yace " am sorry kya kyawa , murmushi tayi kana tace" to muje ka maida ni saboda yanzu wata k'anwar momy na ta kirani wai kakarmu babu lafiya🤭 , azama yayi yace"Allah sarki barinzo mu tafi".


Komawa ciki yayi kana yafa k'iran momynshi , bayan sun d'auki lokaci saiga momyn ,d'auke da wata k'atuwar leda ta mik'owa Khalil tace" yabawa Duduwa , dur kusawa tayi har k'asa tana yiwa momy godiya , hak'ika momy ta yaba da hankalin Duduwa k'awarai ".




Bayan sunyi sallama suka fice momy na d'aga musu hannu , har suka fice daga gidan, suna shikin tafiya ne Khalil yake tambayar Duduwa , shin kina sona? jin kalmar tayi kamar saukar aradu , daurewa tayi tace" ai mutum baya k'in mutum d'an uwan shi ,😴wallahi bacci nakeji , kila dasafe in k'arasa 😴,

Itako tanada dalilai masu yawa na k'in auran Khalil , cema tayi wace anguwa zan kaiki ? cikin yanayin damuwa tace" kaini RUGAR JULI saboda dazu da 'aka kirani ance wai sun wuce asibiti , Khalil ne yace "har ina sako manyan kaya saboda inshiga mu gaisa, murmushin yak'e tayi kana tace" ai suna 'asibiti , Khalil ne yace "to inba damuwa kizo mu wuce asibitin mana , kallon jikin ta tayi kana tace gaskiya nayi datti da yawa saina shiga nayi wanka ,k'arewa gidan da yake gabansu kallo Khalil yayi , gidan kewaye yake da fenti sai k'ofa itama da fanti a jikin ta , to gidan dai za'a iya kiran su da masu rufin asiri".


Bud'e murfin motar tayi kana tayi mai bye bye, kiran ta yayi cikin sanyin jiki ta k'araso mik'a mata ledar da momy ta bata yayi, kanta 'a sunkuye tayi mai godiya ta wuce....✍️✍️✍️.


_mom Islam CE_

*Please share*
*Comments*
Vote ✍️
💖🌷NANCY Y'AR K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._


_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 21_22


____Bayan ta wuce cikin gidan tasami muta nen gidan a zaune suna hira,da wanan tsohuwar matar dakuma wanan budurwar, bayan tayi sallama sun amsaata sannu tayi musu ta shige cikin d'akin ta , kamar jira sukeyi ta shige suka fara gulmar ta , wanan tsohuwa da 'ake kira da baba Dije tafara cewa kinga yarinyar nan duk lokacin da zata fita saita dawo da leda k'atuwa , to wai ma ina iyayen ta ne? ita dai wanan budurwa mai suna Nafisa batace komai ba saboda yawan magana ko gulma bai dame taba, baba Dija data gama surutanta ta wuce d'aki ."


Nancy ce zaune a d'aki tana sak'a da war wara , saboda 'a yanzu ne lokacin da take buk'atar iyaye acikin al'amuran ta, 'amma gashi tazo tayi watsi da iyayen ta , tana cikin tunani ne taji wayar ta na ruri, d'auka tayi had'i dayin sallama , cikin sa'ssanyar murya tace" Khalil nazo gida lafiya kaifa? ka koma gidanne¿".


A kasalan ce yace" kya kyawa bazan iya bacci ba muddun bansaki a idona ba , zaro ido tayi kamar yana ganin ta cikin sigar lallashi tafara magana , kamar mai shirin yin kuka tace"dan Allah ka huta mana nifa ina cikin kwanciyar hankali, k'ara marai raicewa yayi kana yace kodai baki san zuwana ne , da sauri ta katse shi tana cewa ina ai ban isaba 'amma please kabari sai zuwa gobe,
Babu inda ya iya haka ya hak'ura 'amma badan yaso ba, ita ko Nancy tunani ne yayi mata yawa tarasa wanne zata kama, washe gari tayi shawarar bude account saboda 'ajiyar kud'in ta 'a halin yanzu tanada dubu dari hud'u saboda ranar dasukaje gidan su momyn Khalil ta zuba mata kud'i a cikin ledar dakuma 'atamfofi da kayan makeup."




Washe gari ta shirya bayan tagama breakfast , tad'au hand bag d'inta tanufi bank ,saboda akwai masu bayani bata sha wuyar fahimtar komi ba, da dubu hamsin tadawo gida , bayan tayi sallahar azhar ne ta kwnta a madai daiciyar katifar ta' takuma fad'awa kogin tunani ."




Gashi Khalil yace zai zo gidan su yau ,to ita bata san yaya zatayi da rayuwar taba, wata dabara ce tafad'o mata ,shiryawa tayi ta nufi gurin kayan ta akwati k'arami ta d'auka dayake cin kaya kala goma ."



Azama tayi ta nufi gurin da ragowar kud'inta suke ta sasu a hand bag d'in ta 'ta fito bayan ta kulle d'akin ta nufi gurin, mutanen gidan tayi musu sallama , Nafisa ce tace" Nancy kibani number ki mana ko madinga gaisawa , amma dai ba dad'e wa zakiba? Nancy tace"eh gaskiya bazanfi two weeks ba ."



Da isar ta bakin titi ta nufa ,tayi sa'ar samun mota da wuri bayan ta isa tashar motoci ne taji ana cewa saminaka ,saura mutum biyu motar ta cika ,
Bayan tabiya kud'in motar ne , tana shirin zama taji wayar ta na ruri , amsawa tayi had'e da sallama bayan sun gaisa ne yake tambayar ta 'akan tayimai kwa tancen anguwar su, cikin yanayin damuwa tace gani a tashar mota zani garin su kakar mu ,saboda jikin 'nata yak'i ankoma da ita gida, cikin sauri yace kina wacce tasha ne?".


Ina tashar saminaka tabashi amsa , cemata yayi to kijira ni ganin'an zuwa yanzu , to kawai tace mai , bayan wasu lokuta saiga Khalil nan ya iso ......✍️✍️✍️.


_Afuwan👏kunsan dai banida lafiya shiyasa kukaji ni shiru love yau all my fan's_


_Mom Islam ce_


*Please share*
*Comments*
Vote✔️
💖🌷NANCY Y'AR K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._


_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.





*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 23_24

____DA isowar sa yafara dube dube, ganin bai san motar data shiga ba, yasa shi ciro wayar shi a cikin aljihu, number ta ya danna ,yana cikin kiran 'ne ya hango ta cikin wata mota dake kusa dashi, lokaci d'aya ida nuwan su had'e ."




Sakkowa tayi daga cikin motar jiki a sanyaye tazo kusa dashi , kana tace" barka dazuwa ,yauwwa yace" mata 'a tak'ai ce , bayan shirun daya wanzu tsaka ninsu , Khalil ne ya katse musu shirun ta hanyar 'ruk'o hannun ta , jin wani yanayi a tare dasu yasa ko wannen su idanun su 'sukawo ruwa 'alamar hawaye ,
K'ok'arin janye hannun ta tayi daga na Khalil shikuwa kamar jira yakeyi wasu hawaye masu zafi suka zubo daga kuncin sa , bazata iya jure ganin kukan saba yasata juya baya ."


Jitakeyi 'inama 'ace mijin tane data nuna mai soyayya marar misaltuwa , ganin tsayuwa tana neman ga gararsu ne yasa Khalil juyo da ita tana fuskan tar shi , ganin idanun shi sun koma launin ja yasata cemai kaga mota tacika ni ake jira zan tafi saimun sake had'uwa, a san yaye yace" Nancy menayi miki dahar zaki gujeni ?gashi kin d'auki k'atuwar jaka , mir mishin yak'e tayi kana tace" soyayyar ka tana cikin zuciyata karka damu bazan dad'e ba insha Allah."



Murfin d'in motar ya bud'e kana ya d'ibo wasu ledoji manya guda biyu , mik'owa Nancy yayi , cikin farinciki ta k'ar6a tana yimai godiya sabuwa waya 'ya mik'a mata , zaro ido tayi tana cewa"to wanan ta hannuna inyi yaya da ita? ranshi a 6ace yace"oho nidai nasiyo kuma dole kiyi using da ita, cikin zuciyar ta tafara tunanin menene using ? ganin kar asami matsala yasata cewa to nagode Allah yak'ara bud'i ."



Amin yace"kana yace " please karki dad'e bata iya sake kallon shiba ta shige mota ".


Khalil sai da yaga tashin su sanan ya shiga motar shi jiki a sanyaye , tana cikin mota yakira ta yakai sau goma duk saboda yaji muryar ta , bayan ta sauka ne ta 'tari mai adai daita yakai ta 'anguwar su ,bayan yafad'a mata kud'in tahau suka wuce , suna cikin tafiya ne wani yaro mai suna Ahmad lokacin tana k'auye shine abokin wasan ta , yana ganin ta yafara cewa" oyoyo DUDUWA tadawo ."



Runtse idanun ta tayi kana tafara cewa wallahi dana sani daban dawo wanan k'auyen ba kowa yahau samaka ido , a haka dai tak'arasa zuwa gida ".



Da shigar ta suka had'a ido da umma , wani farinciki ne ya ziyarci zuciyar Nancy , dagudu ta rungume Umma tana cewa oyoyo umma na , k'arasawa d'aki sukayi daganan , suka shiga hirar yaushe gamo."


Nancy ce take cewa Umma nikam ina Dillaliya ne? nisawa umma tayi kana tace "Allah yayiwa dillaliya rasuwa!!!.



Cikin yanayin kid'ima Duduwa tace" yaushe kenan umma? bayan umma ta share hawayen da suka zubo mata tace" bayan kun dawo babu jimawa tafara ciwo sai dai tace "min zaki kasance cikin kwanciyar hankali a gidan da kike , Duduwa tayi kuka sosai , umma batayi yun k'urin hanata kukan ba , sai da tayi mai 'isar ta kana tayi shiru."


Bayan sunyi sallah ne taci farfesun da umma tayi mata , ta d'auko kayan tsarabar da tazo dasu , atamfofi ne guda biyar dakuma takalma biyu da hijab ,umma tayi murna sosai harda hawaye, kayan da Khalil ya siya mata ta d'auko dan batasan meye a ciki ba ."


Madara ce ta gwan gwani guda biyu manya sai millo dakuma biscuit da butter babbar roba , d'ayar ledar kuma kayan makeup ne dasu English wear riga da skirt dogo har k'asa sai riguna musu tsada sai kuma atamfa guda biyu."


Mik'awa umma tayi ,Umma na ganin haka tace" waye yabaki wanan ?"....✍️✍️✍️.



_Mom Islam ce_

*Please share👏*
*Comments*
Vote✔️
💖🌷NANCY Y'AR K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._


_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 25_26


____Bayan taja gwauron nunfashi tace" wani d'an wahala ne wallahi , zaro ido Umma tayi kana

Please Login or Register in order to submit comment