Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fara biyowa ta hancin shi yana
xubowa a jikin shi.
.
.
ALLAH SARKI AMIR, MALLAMIN SOYAYYA. JARUMIN
JARUMAI A DA'IRAR SOYAYYA."
.
.
Yana nan a saman bishiyar sai ya ga mutane suna xuwa
cikin qauyen ana ta hayaniyar sha'ani da ake yi. Amir ya
dago kan shi daqyar ya bude idanun shi ya hango mutane
a cikin qauyen sun yi dandaxo ana daurin aure a qofar
gidan su Sadiya.
.
Ya san cewar Sadiya ce ake daurawa aure da mutumin da
aka bashi labari. Amir ya koma ya kwanta ya dafe qirjin
shi da hannun shi a ynx xuciyar shi tafi komai damun shi
da radadi.
.
.
Lp=36
>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 36
.
.
A ynx xuciyar shi tafi komai damun shi da radadi a jikin
shi. Ya dade a haka kafin ya sake bude idanun nashi. A
lkcn har mutane sun fara fitowa daga qauyen suna ta
dararraku, wadansu a qasa wadansu kuma akan kekun da
babura. Har an daura auren Sadiya da Alh. Mamuda
Sarkin noma.
.
Bayan mutane sun watse sun bar qauyen, can da yamma
tayi sai ya hango motoci uku sun shigo qauyen zasu dauki
amarya tare da 'yan biki. Yana iya jiyo hayaniyar su daga
nesa suna shewa da farin ciki, babu wanda ya san cewar
yana saman bishiyar a bayan gatin.
.
Amir ya ji tsoro ya kamashi lkcn da ya ji ciwon shi ya sake
yunqurowa fiye da na kowanne lkc a lkcn da yaga wasu
mata sun fito da Sadiya, tana tsakiyarsu tana tafiya tana
kuka tare da share hawaye, zasu shiga da ita cikin mota
su kai ta dakin mijinta wanda bata so.
.
Amir yana kallo suka shiga da ita cikin motar dake gaba,
mata sai guda suke yi da hanyaniya. Amir ya daga mata
hannu duk da ita ba zata iya ganin shi ba, bata san yana
nan a kusa da ita ba.
.
Shi kenan Sadiya sai wata rana, na gode da soyayyar da
kika nuna min duk da bamu dade tare ba.
.
Shi kenan Sadiya, saduwar alheri, Allah Ya zaunar dake lfy
ke da mijinki, da fatan za ki yafe min, nima na yafe maki.
.
Amir yana kallo aka tuqa motar aka tafi da Sadiya, sauran
motocin 'yan rakiya suka debi sauran mata suka bi bayan
motar da ta dauki Sadiya, ya ci gaba da dagawa motar
hannu da qyar jini yana xuba ta hancin shi da bakin shi,
kayan jikin shi duk sun yayyage yana a saman bishiyar a
6oye yana kuka.
.
Bayan sun tafi kowa ya 6ace sai Amir ya ji kamar an dauki
xuciyar shi ne an tafi da ita, ya ji baya son ma zama a
saman bishiyar. Domin kuwa ya tabbatar a ynx Sadiya
tayi mashi nisa. Ya yi alqawarin koda ace mutuwa zai yi to
dole ne sai ya kusanci inda take. Amir ya kamo reshen
bishiyar ya sauko da qyar ya fadi qasa. Ya fara rarrafawa
yana kama itatuwa da ganyaye a haka har ya yi nisa. Ya yi
alqawarin sai ya je har qauyen da Sadiya tayi aure, shima
zai raka ta kamar yadda sauran mutane suka raka ta. Ya
san cewar idan har ya mutu a can Sadiya ta samu labari
zata qara tabbatarwa da irin son da yake yi mata.
Wannan ce kadai soyayya ta qarshe da zai nuna mata a
halin ynx.
.
Ba zai mutu ba sai ya je garin da take, wannan shi ne
hanya daya da zai bi ya wanke kan shi bisa laifin da yayi
mata a baya.
.
.
**~**
.
.
Washe gari bayan an tashi biki da yake kwana daya aka yi,
sai 'yan uwan Sadiya suka koma gida, aka bar ta a zaune
tayi tagumi ta dora kanta bisa guiwarta tana ta kuka.
.
Sadiya ta ji tana matuqar jin tsoron gidan da aka kawo ta
da kuma dakin da aka ajiye ta. Duk da qyale-qyalen kayan
amarcin dake cike da dakin ba wani abu da yake bata
sha'awa. Bata so danginta suka tafi suka barta ba.
.
"ki daina kuka, ki yi haquri, ki bi mijinki Sadiya, mu zamu
tafi sai wata rana idan mun xo ganin ki."
.
Sadiya ta ji kamar 'yan uwanta sun kawo ta wani waje da
za a kashe ta. Bata ta6a zaton rayuwarta zata fada
tagayyara irin wannan ba. Har ynx masoyinta Amir
wanda aka hana ta shi ne kadai wanda xuciyarta take
hange. Sadiya tana matuqar tsoron wannan baqin
azzalumin mutumin da aka bata a halin ynx, iyayenta da
danginta suna can suna ta dariya, domin kuwa Sarkin
noma ya basu kudi, sun barta a dakin tana ta rusa kuka,
sun mance da ita.
.
Sarkin noma yana can tare da mutanen dake qauyen
yana kaiwa da komowa da babbar riga yana dariya.
Wannan rana ce mai kyakkyawan tarihi a cikin rayuwar
shi. Ya san cewar Sadiya bata son shi, to amma shi ina
ruwan shi da wata soyayya? Wannan sai yara 'yan
zamani. Shi dai ya san ya saye iyayenta, don haka bai
damu da irin zaman da zai yi da amaryar shi Sadiya ba.
.
Suna nan a cikin qauyen bayan rana ta dan fara dagawa,
ba zato ba tsammani sai ga wasu yara dake kiwon shanu
a bayan gari sun garzayo cikin qauyen aguje. Da aka
tambaye su abin da ya tsorata su suka dawo sai daya
daga cikin su ya ce.
.
"wani mutum ne rigar shi duk jini ya fadi a bakin hanya,
yana can a kwance.
.
Nan da nan mutane suka fara garzayawa aguje domin su
ga kowane ne. Sarkin noma shi ne a gaba, mutane suna
bin shi a baya. Da xuwan su bakin hanyar shigowa
qauyen, sai suka tsinkayi saurayin wanda yake ta aman
jini a kwance yana kallon rana, kayan shi sun yayyage duk
jikin shi rauni. Mutane suka yi baya a cikin tsoro da
tausayawa.
.
Sarkin noma ya kalli saurayin ya dan yi tunani sannan ya
ce da mutane.
.
"Wannan yaron shi ne yaron da ya je wajen mata ta
kwanakin baya a can gidan su, yaron nan dake birni, shi
ne ynx ya sake biyo ta nan."
.
Ya kalli samarin dake a wajen ya ce dasu.
.
"ku tattaka shi ya qarasa mutuwa, ba komai, ba abin da
zai faru.
.
Sadiya tana cikin dakinta tana kuka, tana alhinin rabuwa
da masoyinta daya wanda ba zata sake son wani namiji
kamar shi ba, sai ta ji yara sun shigo gidan suna bada
labari.
.
"Wani mutum ya fadi a bakin hanya, yana can a kwance
rigar shi duk jini."
.
Sadiya ta ji gabanta ya fadi, tayi sauri ta dago kanta a
tsorace.
.
.
Lp=37>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 37
.
.
Sadiya ta ji gaban ta ya fadi tayi sauri ta dago kanta a
tsorace. Bata san ko wane ne ba, amma kuma babu
shakka ta ji kamar ana fuxgar xuciyarta xuwa waje domin
ta je taga abin da yake faruwa.
.
Tana nan a cikin dakinta na amarci sai ta ji wani saurayi
ya shigo gidan yana bawa matan dake a gidan labari irin
na yaran da shigo daxu.
.
"mutane sun taru da yawa a wajen, amma babu wanda
ya san ko daga ina yake, ina tsammanin matafiyi ne
rashin lfy ta kama shi ya fadi a hanya."
.
Sadiya ta fito waje a tsorace. Maganar da saurayin yake
fadi tamkar yankan wuqa ne a jikin ta. Bata san kowane
ne ba to amma kuma haka kawai sai ta ji hankalinta ya
kasa kwanciya, tana son ta je ta ga kowane ne wanda ake
ta labarin ya fadi a hanya mutane sun zagaye shi.
.
Wata tsohuwa ta shigo gidan Sarkin noma a tsorace, ta ce
da matan dake tsaye suna sauraren labarin da ake ta
shigowa ana fadi masu.
.
"Jama'a gari babu lfy, kun ji abin da yake faruwa kuwa?
Wai an ce wani saurayi yana ta aman jini akan hanya.
Wasu sun gane shi, wai wani saurayi ne da ya je
Turunkawa suka yi fada da matasan garin suka bubbuge
shi kwanakin baya...."
.
Tun kafin tsohuwar ta kai qarshe Sadiya ta fashe da kuka,
tayi waje da gudu, domin kuwa ynx ta gane ko wane ne.
Amir din ta ne, Amir masoyinta!! Shi ne ciwon soyayya ya
jawo shi ya biyo ta har garin da ta yi aure.
.
Matan Sarkin noma da sauran mutanen gida suka fara
kuwwa suna cewa.
.
"mun shiga uku, jama'a amarya ta gudu, ku kira Alhaji ya
xo gida babu lfy."
.
Nan da nan da nan aka sa matasa da yaran gidan suka
bita suna kuwwa amma kuma Sadiya ta yi nisa, ta qosa ta
sake ganin Amir ruhinta.
.
.
Sarkin noma ya ci gaba da dakawa talakawan mutanen
wajen tsawa.
.
"na ce ku kashe shi, babu abin da zai faru.....
.
.
Page 38
.
.
Sarkin noma ya ci gaba da dakawa mutanen dake wajen
tsawa.
.
"na ce ku kashe shi, babu abin da zai faru, domin kuwa
rashin albarkar yaron nan tayi yawa, matar tawa zai biyo
har nan garin sbd su yaran zamani basu gaji kunya ba?"
.
Mutanen dake wajen suka kasa ta6a Amir, domin kuwa
jikin su ya yi sanyi, Amir yana kwance cikin jini ta baki ta
hanci, duk jikin shi rauni ne, da qyar yake numfashi,
saura kadan ya ce ga garin ku nan, ba zasu iya ta6a Amir
ba, domin kuwa ta6a shi da xummar cutarwa rashin
imani ne bayyanannne.
.
Suna nan a tsaye cirko-cirko tare da Sarkin noma wanda
ya fusata yana ta huci, sai ga Sadiya ta fado wajen da
suke, ta kutsa cikin mutane tana kuka ta ga Amir a
kwance cikin jini. Tan ganin shi ta fadi a gaban shi tana
kuka.
.
"Amir? Amir kai ne ka koma haka....?"
.
Ta tambaye shi a rude tana kuka da qarfi. Amir ya yi
qarfin hali ya fara qoqarin bude bakin shi yana qoqarin
ya kira sunan ta, yana kallon ta, a lkcn ne ya sake yin
aman jini. Sadiya ta dora hannuwan ta akai tana kuka a
tsorace. A halin ynx shi kan shi Sarkin noma ya yi
saranda.
.
.
NIMA A HALIN YNX DA NAKE TYPING HAWAYE KE SARTU
BISA KUMATUNA.
.
.
Amir ya fara shessheqar kuka, yana magana bakin shi
yana kyarma, ya ce da Sadiya.
.
"ki yi haquri ki yafe min..."
.
Ya saurara ya huta, sannan ya sake yunqurawa ya ce
.
"na zalunceki a wani lkc da ya wuce, na guje ki a cikin
rashi sani....ina neman afuwarki ki yafe min...."
.
Ya fara hawaye, ya dora hannuwan shi akan qirjinshi,
domin ya samu sauqin azabar dake damun shi a ciki.
Sadiya ta ce tana kuka.
.
"na yafe maka Amir duniya da lahira, nima ka yafe min..."
.
Amir ya yi ajiyar xuciya, wannan shi ne hadarin soyayya,
domin kuwa a wani zamani da ya wuce shi ne wanda
daruruwan 'yan mata ke son shi, shi kuma yana yi masu
wulaqanci, yana sa su kuka, yana karya masu alqawari.
Ga wani zamani kuma ya xo, Amir ya biyo yarinya daya
'yar qauye, ya rasa ransa akan ta bai same ta ba.
.
Amir ya daga hannayen shi biyu ya fara yiwa Sadiya
bankwana. Yun yana iya motsa idanun shi a qarshe sai ya
koma ya tsaya da motsi, Sadiya ta rusa kuka. Mutanen
dake wajen suka fara xubar da hawaye, shi kan shi Sarkin
noma mijin Sadiya sai da yayi tagumi.
.
"dama ashe haka ake yin wannan soyayya da yake jin
labarin ta shekara da shekaru? Shi bai san yadda abin
yake ba sai ynx.da a ce ya san haka zai ga wannan abin
tausayi me zai sa ya matsa sai ya auri Sadiya? Da tuni ya
barwa wannan saurayin ita. Sun yi auren su na soyayya."
.
To amma bakin alqalami ya riga ya bushe, Amir dai ya
riga ya rasu a gaban masoyiyar shi kuma a gaban mijinta,
a gaban mutane wadanda zasu zama shaida a matsayin
shi na masoyin gsky. Mutanen dake a wajen suka yi sauri
suka janye Sadiya suka kawar da ita, aka sa wasu mata da
suka tsaya a baya suna kallo, aka ce su mayar da ita gida
ta huta.
.
Suka qiqe Sadiya tana kuka tana waigawa baya tana yiwa
GAWAR MASOYINTA KALLON QARSHE, suka mayar da ita
dakin mijinta suna 6ata bakinsu wajen bata haquri.
Sadiya ta ci gaba da tunanin Amir.
.
"Allah Sarki Amir masoyin zamani. Ta tuno ranar da ya
fara ganin ta.
.
"Laifi ne don mutum ya tsaya yana kallon kyakkyawar
mace irin ki?"
.
Ya yi mata dariya yana so ya nuna mata sabuwar
soyayyar shi a gare ta.
.
Shi ne wanda ke ce mata.
.
"zan ci gaba da son ki Sadiya, kamar yadda nake son ki a
halin ynx, har sai naga ranar da zaki tausayawa xuciyata
ki amshe ni a matsayin masoyin ki."
.
Amir kenan gwanin iya kalaman soyayya, ya ce da ita.
.
"haba baiwar Allah, wai ke wacce iriyar mace ce? Ke fa ba
makauniya ba ce, kina sane da irin ciwon sonki da ya
kama xuciyata."
.
Sadiya ta tuno lkcn da abokan Amir suka xo suna bata
haquri kan ta taimaki abokinsu ta amshi soyayyar shi, da
kuma qawayen ta a makaranta irin su Rahma Sani da
Siyama Ibrahim sai kuma Ziyada Yazid sune suka fi hawo
hankalinta aka ta amshi soyayyar Amir. Kowa a birni yana
son ta da Amir, gashi yau Amir ya rasu a gabanta yana
mai neman afuwar ta yana kuka!
.
.
Sarkin noma da kan shi ya shiga gaba aka nemo mutanen
garuruwan Turunkawa da Gidan rijiya dangin Amir, aka
fadi masu labarin abin da ya faru har Amir ya rasa ran
shi.
.
Mai unguwa Mutawakkilu ya xo yana kuka, domin kuwa
duk a dalilin shi labarin wannan so ya samo asali. Shi ya
fara hada wannan soyayya, har abin ya zama matsala
daga baya.
.
A garin Maqera inda Sarkin noma yake aka rufe Amir tare
da mutanen da suka yi ta dukan shi a kwanaki uku da
suka wuce, domin kuwa a halin ynx jikin kowa ya yi sanyi,
kuma sun gane cewa laifin da Amir ya yi masu a baya bisa
tsautsayi ne. Kuma nadama ce ta dawo dashi qauyen ba
nufaqa ba.
.
Daga baya hr Zariya suka dunguma suka fadi yadda abin
ya faru daga farko har qarshe. Da labarin ya samu
abokan Amir a makaranta, sai da Mustafha da Haidar
suka kwana biyu suna kuka, suna tuno abokinsu wanda
ya rasu sanadin soyayya.
.
Da 'yanmatan dake a makarantar suka samu labarin
rasuwr Amir, Amir dan soyayya, wasu sun yi kuka,
musamman 'yanmatan shi...suna matuqar son shi.
.
.
Lp=39
Iliyas Ishak Gundutse > "TASKAR GIDAN LITTAFI"
>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 39
.
.
>=<><>=< KAMMALAWA >=<><>=<
.
.SANARWA!
Bayan wannan littafin akwai littafin dake dauke da ci
gaban labarin mai suna SADIYA wanda zamu ci gaba
dashi gobe in Allah Ya kaimu.
.
.
A halin ynx samari da 'yanmatan da suka samu labarin
mutuwar Amir, sun girgiza kuma sun ga ishara. Sun gano
cewar soyayya ba qarya ba ce, gaskiya ce akwai ta a raye
a xuciyar kowanne mutum. Don haka in dai akan soyayya
ne kowanne irin hadari zai iya faruwa ga masoyi. Tabbas
ba zasu ta6a mancewa da labarin Amir ba, shi ne jarumi
kuma malamin soyayya.
.
.
**~**
.
.
Da dare ya yi kowa ya yi barci, duk mutane sun kwanta
suna hutawa, duk sun mance da al'amarin da ya faru a
qauyen mai ban al'ajabi da kuma takaici. Dare ya yi babu
kowa a waje sai hasken farin wata da ya ke ci kamar rana
a tsakiyar sama da kuma motsin ganyaye da reshina a
jikin bishiyu tare da kukan tsuntsaye.
.
Sadiya ta bude dakinta ta fito xuciyarta a bushe. Sadiya ta
fito dauke da qunshin kayanta wadanda ta qulle su a cikin
zanin ta. Lkc ne ya yi da ta dade tana jira. Lkc ne ya yi da
zata gudu ta bar garin, ta gudu ta shiga duniya ta koma
wani garin. Domin ta yiwa mutanen da suka raba ta da
Amir nisa, domin ta yiwa baqin ciki dake damun ta
nisa.....domin ta yiwa garin da aka kashe masoyinta
nisa.....baqin gari wanda ba zata ta6a mantawa dashi ba.
.
A lkcn da wannan al'amarin ya farune ta shiga daki ta
zauna a ciki tana ta kuka ita kadai. Tun lkcn da wannan
al'amari ya faru ta fara 6oyewa mutane, bata son kowa
ya xo kusa da ita, domin kuwa duk irin su daya. Sune
suka kashe mata masoyin ta Amir. Tun a lkcn ta ji bata
son komai face rabuwa dasu. Ta riqa jira dare ya yi
domin ta fita ta bar gidan.
.
Sadiya ta fito ta bar gidan, babu wanda ya gan ta, ta riqa
tafiya ita kadai a cikin hasken farin wata, ta bar gidan bata
san inda zata nufa ba. Xuciyarta ta karye a dalilin alhinin
soyayya, kuma tunanin ta ya dabirce. Tana sa ran idan ta
tafi zata tsinci kanta a wani gari dake can gaba, ta na sa
ran zata tsinci kanta a wurin da babu wanda ya san ta,
ballantana ya dawo da ita, tana sa ran zata zauna a can
har abada....har mutuwar ta.
.
Don haka ita ma ta tafi, ta rabu dasu kamar yadda suka
raba ta da masoyinta. Don haka ita ma ta tafi ta bar su,
kuma ba zasu sake ganinta ba, don haka ita ma ta tafi ta
bar su!!
.
Sadiya ta tafi har ta yi nisa bata sake waigowa ba, Sadiya
ta tafi tayi nisa a cikin daji, bata damu da ciyayi da
bishiyun da take wucewa a hanya ba. Bata damu da
duhun da ya kan lullu6e ko'ina a sararin samaniya ba.
Bata damu da duwatsun dake bisa hanya ba, wadanda
suke ta yi mata rauni idan tayi tuntu6e dasu ba. Sadiya ta
tahi har ta yi nisa bata sake waigowa ba!!
.
Bata buqatar dan rakiya a lkcn da zata yi bankwana ta
canza gari a sakamakon tashin hankalin soyayya. Bata
buqatar wanda zai rakata sai inuwarta da ke biye da ita
suna tafiya tare.... Sadiya ta yi nisa!! Bata buqatar wanda
zai xo ya rakata sai hawayen dake biye da ita, idan wasu
sun xubo sai wasu su sake biyo bayan su. Sai kuma takaici
da damuwa dake a xuciyarta
.
A da can ba haka rayuwarta take ba. A da can tana
rayuwarta ne cikin farin ciki....tare da 'yan uwanta....tare
da iyayenta wadanda a ynx su suka kashe mata Amir, a da
can ba haka rayuwarta take ba, domin kuwa babu abin
da ya faru da ita cikin masifun soyayya. Sai da larurar
soyayyar Amir ta kama ta sannan duk wadannan
abubuwan suka shigo rayuwarta. Gashi ynx ta gudu ta
bar kow, ta nufi wata duniya mai nisa a cikin dare ita
kadai tana kuka....a da can ba haka rayuwarta take ba.
.
Ta tafi sai wata rana idan da rabon ganawa, idan wani ya
ganta a wani gari cikin mutanen garin su, ko kuma a cikin
'yan uwanta....idan tana raye. Ta tafi sai kuma wata rana,
idan da rabon ganawa, wataqila su gano inda take su
rarrashe ta su bata haquri. Ta tafi sai wata rana idan da
rabon ganawa.
.
Sadiya ta ci gaba da tafiya har tayi nisa, tun ana hangenta
har ta fara 6acewa a cikin dajin....a cikin daren. Sadiya ta
ci gaba da tafiya haka har ta hau saman wani tsauni dake
a can nesa. Farin wata ya haske ta kamar tsuntsuwa,
Sadiya ta ci gaba da tafiya har ta yi nisa tun ana iya
hangenta har ta..... 6ace.
.
.
Alhamdulillah.
Dukanin godiya ta tabbata ga Allah (SAW) da Ya bani ikon
Kammalawa wannan littafi mai suna
SO BAYAN RAI (Labarin Hadarin Soyayya)
.
Jinjina ga maigidan littafi
SHAFI'U DAUDA GIWA
.
Ina yaba maku
Sadeeq Shehu Shariff
Yusif Iliyasu Abdulkadir
Yarima A Gangariya
Shuraih Usman
Muhamammed Anas Bn'malik
Hassan Atk Tanko
.
Madallah da ku
Alh. Aminu Duniya Gafai
Hasheem Salees Adam Kayarda
Abubakar Isah Dibboncy
Usman SafUs Rano.
.
Ni
Iliyas Ishak Gundutse
(Madugun Taska)
ke sadaukar da wannan labari ga ahalin "TASKAR GIDAN
LITTAFI" gaba daya.
Sai kuma mun hadu gobe idan Allah Ya kaimu a ci gaban
labarin mai suna Sadiya

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment