Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

can a makaranta.
Ganin bata ce komai ba sai Sarkin noma ya gyara murya
ya ce.
.
"ina so ki kwantar da hankalinki Sadiya, ni dai kamar inda
iyayenki suka sanar dake, ina son ki ne tsakani na da
Allah, kuma daidai gwargwado Allah Ya rufa min asiri,
tunda ina jin a duk fadin qauyukan nan babu sama da ni
a dukiya da kadarori, kin ga ai sai mu yiwa Allah gdy.
Wannan motar da kike gani tawa ce, ina da motar kaya
tana gida, maganar abinci kuwa babu matsala, ba a ta6a
sauke tukunya a gidana ba, tuwon nan safe da rana da
daddare baya yankewa har ma sai ya ragu wasu sun xo
sun samu....ko ba haka ba Alh. Danqani?"
.
Daya mutumin ya tauna goro ya ce.
.
"qwarai kuwa Sarkin noma, wannan magana ni kaina
shaida ne, in dai abinci ne ba matsala.
.
Sarkin noma ya ci gaba.
.
"kuma muna nunawa iyalinmu gatanci, tunda dai mata
na dukan su ukun nan, in banda su ciro dawa a rumbu su
yi sussuka a turmi da kuma dakan fura, to ai ba sa wani
aikin wahala, kuma duk sanda naga da sarari 'yar
shinkafar nan dai a samu a dafa ko sau daya ne a wata a
ci.
.
.
Lp=31
>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 31
.
.
Kuma duk sanda muka ga da sarari 'yar shinkafar nan dai
a dan dafa sau daya a wata a ci."
.
Alh. Danqani ya ce.
.
"Qwarai kuwa Sarkin noma, wannan gsky ne."
.
Alh. Mamuda ya gyara babbar rigar shi ya ce da Sadiya.
.
"'Ya'yanmu ba wani wahala suma, domin kuwa in ban da
noma da kiwo ta bamu tura su ko'ina , basa xuwa su
nemo icen qonawa kuma ba kansu suke daukar taki su ka
gona ba. 'Ya'yana kawai ke samun irin wannan gatancin a
duk fadin qauyukan nan, sbd haka ki kwantar da
hankalinki ki daina wani hange-hange. Mu manya mu ne
ke riqe mace da mutunci amma yaran nan shaqiyan
banza ne in banda qarya basu san komai ba."
.
Alh. Danqani ya yi dariya ya ce.
.
"Sai fa shegiyar qarya ko sisi ba su iya dauka su ba mace
kudin samartaka."
.
"Sbd haka ki bani hadin kai, ni ne zan riqe ki da mutunci
riqo na amana, ki huta iyayenki ma su huta."
.
Dattawan suka ci gaba da kallon Sadiya wacce tayi shiru
tana sauraren su, suna tsammanin su ga tayi murmushi a
bisa wannan albishir da suke yi mata. A maimakon haka
sai Sadiya tayi tagumi tana kallon su tana xubar da
hawaye. Ba don komai ba sai don sanin cewar wannan
baqin mutumi dake a tsaye yana kallon ta ya gama cutar
da rayuwar ta ta duniya, tunda har ya saye iyayen ta suka
ba shi auren ta.
.
Sadiya ta ji ta gwammace ta mutu ta huta.
.
.
**~**
.
.
Amir ya kama hanyar Turunkawa yana ta sauri. Lkc-lkc ya
kan hadu da mutane, wasu zasu koma Gidan rijiya shi
kuma zai nufi Turunkawa. Yamma ta yi liqis sosai gari ya
yi sanyi, rana tayi ja ta kusa faduwa. Qwari da kuma
tsuntsaye suna koke-koke a gonaki da kuma saman
bishiyoyi.
.
Lkc da Amir ya fara hango qauyen rana ta fadi. Ya ci gaba
da tafiya yana tunanin abin da zai taras idan ya je, da
kuma abin da zai fara cewa da Sadiya. Ya san cewa
wannan tafiya ce mai wahala kuma yana cikin yanayi mai
tsauri a wannan lkc.
.
Amir ya shiga cikin qauyen kenan aka kira sallar magriba
a wani qaramin masallaci dake a gidan farko na qauyen.
Yayi wa mutanen da ya samu a qofar masallacin sallama.
Suka amsa mashi. Yawancin su tsofaffi ne suna a zaune in
da suka yi alwala ba su tashi ba. Amir ya roqe su buta
suka bashi, ya amsa ya ajiye jakar shi a gefe daya ya fara
alwala. Da yake basu san shi ba, kuma basu san me yake
tafe dashi ba, sai suka bi shi da kallo kawai. Sun san cewa
dai baqo ne, kuma koma daga ina ya fito ga alama yaron
kirki ne, ganin yadda yayi masu sallama, ya amshi ruwa
zai yi alwala su yi sallah tare.
.
Duk da qauyen bashi da girma, qananun masallatai uku
ne. A daidai lkcn da Amir ya bi mutanen suka shiga salla
ne ya ji kuma ana ta kiran sallah a wsu masallatan. Bai
san ko a wane gida Sadiya take ba a halin ynx, kuma bai
san ko su wane ne iyayenta ba. Ya bari ne sai sun fito
daga sallah sannan ya tambayi a inda gidan su yake.
.
Sun fito kenan, sai Amir ya dauki jakar shi ya qara shiga
cikin qauyen. Ya hadu da wani matashin saurayi dan
kimanin shekara goma sha uku. Amir ya tsayar da shi,
yaron ya bi shi da kallo cikin rashin sanin ko shi wane ne.
Amir ya tambaye shi.
.
.
Lp=32>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 32
.
.
Ya hadu da wani matashin saurayi dan kimanin shekaru
goma sha-uku. Amir ya tsayar dashi, yaron ya bi shi cikin
da kallo cikin rashin sanin ko shi wane ne.
.
"Don Allah ina ne gidan su Sadiya, wacce ke karatu a birni
amma ta dawo gida jiya?"
.
Yaron ya dube shi sosai cikin mamaki ya ce dashi.
.
"Gidan mu daya da ita. Yaya ta ce."
.
Amir ya dafa yaron cikin farin ciki, ya sake tambayar shi.
.
"Ashe kai qanin ta ne ma, ya sunan ka?"
.
Ya ce.
.
"Suna na Isma'il."
.
Amir ya ce dashi.
.
"Yauwa Isma'il, don Allah idan ka je ka ce da ita Amir ne
ya xo yana son ganin ta."
.
Yaron ya dube shi a tsorace ya ce dashi.
.
"An sa mata rana fa yau Malam."
.
"Rana!!"
.
Amir ya ji kalmar ta amsa kuwwa a dodon kunnen shi.
.
"wacce irin rana, ba jiya ta dawo gida ba?"
.
Yaron ya ce.
.
"daxu da safe aka sa mata rana ita da Sarkin noma,
sauran kwana takwas a daura auren, kuma baba ya hana
ta fitowa in dai ba Sarkin noma yaxo ba."
.
Amir ya ji xufa tana keto mashi. An sa wa Sadiya rana da
wani Sarkin noma? Ynx shi kenan an raba shi da xuciyar
shi wacce ke hade da numfashin shi? Tuntuni ya tabbatar
Sadiya tana daya daga cikin sassan jikin shi. Kuma babu
shakka raba shi da ita tamkar raba shi ne da ran shi.
.
Amir ya ji kasala ta kama shi, jikin shi babu qwari, ya ce
wa yaron a sanyaye cikin gajiya.
.
"Bari in baka wasiqa ka kai mata, ina nan ina jiran ka, ka
ce ta baka amsa ka kawo min."
.
Amir ya ciro biro da doguwar takarda daga aljihun jakar
shi, ya tsugunna a gefe guda daga jikin wani garman
shanu dake wajen. Isma'il qanin Sadiya yana tsaye yana
jiran shi. Amir ya riqa rubutun cikin sauri yana hawaye,
hawayen yana digowa akan takardar. Bayan ya kammala
sai ya nade ta ya miqawa yaron.
.
"Ka kai mata, idan ta karanta za ta baka amsa ka kawo
min."
.
Isma'il ya amshi takardar ya garzaya da gudu ya sha
kwana ya shiga cikin gidan su. Da xuwan shi ya fada dakin
mahaifiyar su ya samu Sadiya a zaune ita kadai tayi
tagumi, ta tasa kwanon abinci a gaban ta, amma ba ta ci
ko loma daya ba tun daxu.
.
Isma'il ya miqa mata takarda ya ce da ita.
.
"gashi in ji wani ya ce in kawo maki yana qofar gida."
.
Sadiya ta ji gaban ta ya fadi. Wane ne kuwa zai rubuto
mata wasiqa? Nan da nan ta ji tunanin Amir ya fado mata
cikin sauri. Sadiya ta warware takardar hannunta yana
rawa cikin qosawa domin tafa abin dake a cikin takardar.
.
Da budewarta ta ci karo da rubutun Amir sabon
masoyinta wanda xuciyarta ke tunani dare da rana.
.
.
Sadiya.
Ya kika dawo gida? Kuma ya juyayin halin da muka tsinci
kanmu babu zato ba tsammani. Ina fatan kina lafiya.....?
Na san cewar dole ne wannan wasiqa ta baki mamaki, a
qarshe za ki tsorata idan kika ji abin da zan sanar dake, to
amma idan kika tattara hankalinki waje guda ki ka yi
dogon tunani, za ki ga cewar ba wani abin mamaki ba ne.
Sadiya da farko zan fara da baki haquri, sannan kuma ina
mai neman afuwar ki bisa wani laifi da nayi maki zan
kuma sanar dake nan gaba kadan. Ina son ki sani cewar
nayi maki wannan laifi ne cikin rashin sani, kuma nayi
nadama sosai, nayi kuka sosai, nayi kuka mai yawa kuma
na gane kuskure na. Na dauki alqawarin idan har ki ka
yafe mani, har abada ba zan sake yi maki wani laifi ba, in
har muka cim ma burinmu kika zama mata ta.
Kafin in fadi maki laifin da nayi maki ina so ki bude
xuciyar ki, domin ki ji halin da na samu rayuwata a dalilin
rashin ganin ki. Tun lkcn da na rasa ki a makaranta,
xuciyata ta dimauta, sannan kuma duk wani abu da nake
yi a rayuwata ga mamakina sai na na ga duk tunaninki ya
buwaye shi. Duk wasu lokuta na na barci da na saba yi a
da a halin ynx duk mafarkin ki ya dabaibaye su.
Ba sai kin tsaya wahalar wasa qwaqwalwarki ba wajen
gano dalilin faruwa wadannan abubuwan gare ni. Ko ban
fadi maki ba kin san cewar wadannan abubuwan sun faru
ne a dalilin azabar son ki dake galabaita da ni.
Babu shakka Sadiya na kamu da ciwon son ki a ranar da
na fara ganin ki, kuma tun a lkcn na tabbatar har in bar
duniya ba zan ta6a daina son ki ba.
Sai dai kuma kash! Wani hadari wanda bamu yi tsammani
ba ya gifta wa soyayyarmu. Na samu labarin abin dake
faruwa duka, na san cewar iyayen ki sun yi maki miji a
daidai lkcn da nake fafutikar in mallakeki ki zama matata.
Wannan hadari da ya same mu laifina ne, domin kuwa
tun farko da ace ban guje ki ba, to da ynx muna nan cikin
dauwamammiyar soyayyarmu ta aure.
Sadiya ina jin kunyar sanar dake cewar ni ne Amir din
farko da aka ta6a bani auren ki na gudu na ce bana son ki
tun kafin in gan ki. A da na guje ki Sadiya, amma kuma
ynx gani na dawo wajen ki cike da alqawarin soyayya.
Gani a kusa dake ina jiran ki, ki miqo hannun ki ki tarbe
ni, ni ne masoyinki Amir. Ina sauraron......
.
Tun kafin Sadiya ta kai qarshen wasiqar ta fashe da kuka,
bata san lkcn da ta saki takardar ta fadi qasa ba.
.
"Amir!"
.
Ta kira sunan shi cikin tsoro da wasi-wasi. Dama Amir shi
ne mijina na farko da ya guje ni? Wannan wane irin
al'amari ne? In dai haka ne babu shakka ta yafe mashi,
domin ita dama tana son shi.
.
.
Lp=33
>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 33
.
.
In dai haka ne babu shakka ta yafe mashi, domin ita
dama tana son shi, shi ne ya guje ta.
.
Sadiya ta fita waje cikin sauri tana xumudin ganin
masoyin ta da yake waje yana jiran ta. Ta mance da
maganar auren ta da ake kai. Soyayyar Amir ta makantar
da idanun ta, ta mance da duk wasu matsalolin rayuwa
da ke damun ta.
.
Ta wuce mutanen gidan su dake waje a zazzaune, ta wuce
qanin ta dake tsaye yana kallon ta, ta nufi waje cikin
sauri. Sadiya bata tsaya ko'ina ba da fitowarta qofar gidan
su, sai ta fara waigawa tana kiran sunan Amir masoyinta.
.
A lkcn ne ya jiyo muryarta, nan da nan ya matso kusa
cikin gudu yana kiran sunan ta shima.
.
"Amir."
"Sadiya."
"Amir."
"Sadiya kina ina ne?"
.
Ba su riga sun yi arba da junan su ba, kafin masoyin ya
samu damar ganawa da masoyiyar shi, tuni har Mal.
Buba ya ji labarin abin dake faruwa. Nan da nan ya fito
daga cikin dakin shi a fusace yana riqe da babbar rigar shi
a hannu.
.
Amir da Sadiya sun kusa cim ma juna kenan suna
murmushin lale marhabin, sai Mal. Buba ya sa qafar shi a
fusace ya haure Sadiya ta fadi gefe guda. Ya tasamma
Amir a fusace yana gurnani kamar zaki. Ganin haka sai
Amir ya tsaya a tsorace, har xuwa lkcn da tsohon ya sa
hannu ya masge shi, ya sake ham6arin shi da qafa.
.
Nan da nan mutane suka fara fitowa daga cikin gida da
suka ji ana hayaniya. Mal. Buba ya riqe Amir da hannu
biyu yana ihu yana kiran matasa don su fito su taya shi
aikin casa wadannan yara marasa kunya da albarka.
.
"Me yake faruwa ne, Baba ya aka yi ne?"
.
Wani dan shi ya tambaya a kidime da ya qariso wajen.
Mal. Kalla da wasu tsofaffi suka firfito daga cikin masallaci
riqe da carbina. Mutane suka tsaya turus cikin kaduwar
fanin abin dake faruwa. Ga Sadiya a gefe tana kuka ga
kuma wani saurayi a hannun Mal. Buba ya riqe shi ram
yana yi mashi ihu da zage-zage.
.
"Me ya ke faruwa ne, Mal. Buba ya aka yi ne?"
.
Da ya ga mutane sun taru sai ya ce dasu.
.
"wannan dan banzan yaro ne ya xo ya kira Sadiya da
ranar ta akai, in fito sai naga yana qoqarin kama ta zai yi
mata shegantakar da suka saba yi a can birni. Ina su
Abashe, me kuke jira ba zaku lallasa shi ba kuka tsaya
kuna kallo na?"
.
Nan da nan matasa suka firfito da cikin gidajen su suna
sude hannuwa, wasu suna cin abinci ko wanke hannu
basu yi ba, suka fito jin ana ihu a waje. Mai suna Abashe
ya yi kukan kura ya cafi kwalar rigar Amir ya amshe shi
daga hannun Mal. Buba, ya dunqule hannu ya naushe shi
a fuska, ya fasa mashi hanci. Amir ya fadi qasa warwas!
Wasu samari da suka firfito, da xuwan su suma suka
shiga dukan Amir. Nan da nan suka yaga mashi kaya fata-
fata.
.
Tsofaffin dake wajen suka fara ba da haquri.
.
"ku tsaya, ku dakata haka nan kai Abashe. Ku rabu dashi
kada a xo a yi kisan kai muna kallo."
.
Mal. Buba dake baya yana kallo ya ce dasu.
.
"su kashe shi mana don ubanshi, ko dan gidan uban
wane ne, ai ya san an sa mata rana da Sarkin noma."
.
A lkcn ne Sadiya ta dago kai tana kuka, ta cewa iyayen ta.
.
"Amir ne!! Shi ne wanda aka daura aurena dashi kwanaki,
shi ne fa ya dawo ynx domin ya nemi afuwar laifin da ya
yi!"
.
Tun kafin ta kai qarshe mutane suka fara tambayarta.
"ke wanne Amir din? Kina nufin wannan shi ne taqadarin
yaron da muka bashi ke, ya yi mana wulaqanci ya zage
mu ta uwa ta uba?"
.
Sadiya ta ci gaba da kuka.
.
"Ku yi haquri, Amir ya yi haka ne cikin rashin sani, ya yi
kuskure a wancan lkcn amma ynx ya..."
.
Tana cikin basu haquri mahaifinta ya rugo aguje ya kai
mata duka a baya sai da ta ffadi qasa. Ya daka mata tsawa
a fusace.
.
"ynx don qaniyarki Sadiya, dama wannan Amir ne jikan
mai unguwa Mutawakkilu ya sake dawowa nan kika fito
wajen shi? Yaron da bai san mutunci ba, bai san ya ga
manya da girma ba? Tashi ki shiga gida shaidaniya mara
kunya."
.
Ya qara kai mata duka ta shige gida a guje tana kukan
baqin cikin halin da Amir yake ciki a hannun 'yan uwanta
mutanen qauye. Mal. Buba da ke tsaye yana jimamin jin
cewar ashe ma ynx Amir ne yaxo wajen 'yarsu, bayan a
da ya wulaqanta su akan ta, sai ya fara zagin matasan
dake riqe da Amir.
.
"kuna ji ana maganar cewar Amir ne yaron da ya
zazzagemu amma kuka tsaya kuna kallon shi? Ku
tambaye shi abin da ya sake dawowa yi a nan wajen 'yar
mu, me kuma ya sake dawo dashi ynx?"
.
Wani qato ya shaqewa Amir wuya kamar zai karya mashi
wuya, ya fara daka mashi tsawa.
.
"uban me ya sake dawo da kai wajen ta, iye? Fadi min ko
in kashe ka."
.
Tsofaffafin garin dake bada haquri da farko, da su ka ji an
ce Amir ne yaron nan da ya yi masu wulaqanci, ya aiko
masu da zagi, sai daya daga cikin su ya ce.
.
"To ai bamu sani ba, dama shine yaron nan da aka bashi
auren Sadiya ya ce baya son ta? In haka ne yaro yayi
wauta, me kuma ya sake dawo da shi ynx bayan an yi
mata miji? Gsky ne a bugi yaro, yayi lalata da yawa."
.
Samarin qauyen Turunkawa suka yiwa Amir jina-jina,
suka jefa shi a cikin wata kwata suka danna kan shi, da
suka ga sun galabaitar dashi sai suka qyale shi a kwance
cikin kwatar, kayan shi sun yi yaga-yaga.
.
.
Lp=3.
.
Yana kwance a qasa kayan shi sun yi yaga-yaga. Gaba ki
daya mutanen garn suka taru a wajen ana ta hayaniya.
Wadanda suka xo daga baya suna tambayar labari ana
mayar masu da zance. Dama tuntuni akwai wadanda
suke jin haushin Amir a garin, sa'ar da aka bashi Sadiya
aka hana su.
.
Wani baqin saurayi maji qarfi mai suna Garba Sidi da ya
xo daga baya ya samu labarin abin dake faruwa, sai ya ce
da samarin dake wajen.
.
"to in ce ko dai kun kashe shi kafin mu xo."
.
Abashe ya ce da shi.
.
"Ga dan banzan nan yana numfashi har ynxn."
.
Garba Sidi ya ce dasu a fusace.
.
"Yaron da ya zagi iyayenmu har ya tako ya xo garinmu
baku kashe shi ba tun daxun...me kuke jira dashi?"
.
Ganin idan aka bar Amir da samarin qauyen nan zasu iya
kashe shi, sai mutane masu dan hankali suka shiga
tsakani. Mutum uku suka hanzarta ciro Amir daga cikin
kwatar suka miqar dashi tsaye, suka tallabe shi yana
dingisawa, wasu kuma suna tare samari majiya qarfin
dake yunqurin cafkar Amir su amshe shi don ci gaba da
lallasa shi..
.
Da mutanen suka yi nesa da Amir sai daya ya ce dashi.
.
"kaga abin da ya faru da kai, to abin da zamu fadi maka
shi ne kada ka sake dawowa garin nan, ynx da ace da
qarar kwana, idan muka barka da yaran nan sai su kashe
ka a banza."
.
Suka raka Amir nesa kadan da garin, suka nuna mashi
hanya suka ce ya qoqarta yayi tafiyar shi, kada wani ya
biyo shi ya sake raunata shi. Suka ce ya kiyayi Sadiya ya
cire ta ran shi, suka shaida mashi cewar an riga an yi
mata miji kada ya sake xuwa inda take, Amir yana jin su
suna ta magana bai ce dasu komai ba, ko ina a jikin shi
radadi yake yi, hancin shi bai daina xubar da jini ba, har
mutanen suka tafi suka bar shi suka sake dawowa yana
tsaye a jikin wata bishiya dake bakin hanya, baya iya
ganin komai sai bishiyu da gonaki, haka suka koma abin
su, Amir ya shiga cikin daji bai san inda ya nufa ba. Da ya
yi nisa sai ya fadi a kusa da wani tsauni. Sai a lkcn ne ya
fara kuka da ya tuna halin da masoyiyar shi take ciki a
can gida.
.
Bai damu da azabar da ke azalzalar shi ba a dukanin jikin
shi, Sadiya yake tausaya mawa, yana xullumin wataqila
suna can suna dukan ta.
.
A lkcn da Amir ya kasance a kwance magashiyan a cikin
daji shi kadai a cikin dare yana kuka tare da tsuntsaye, ita
kuma Sadiya tana can ita ma a cikin daki, ta kifa kan ta
akan guiwoyin ta tana kuka kamar ranta zai fita. Tana
tausayin Amir tana xullumin irin raunin da mutanen
qauyen su suka ji mashi a lkcn da suke dukan shi.
.
Masoya biyu dake a wurare daban-danan basu tare da
juna suka raba dare suna ta kuka suna takaicin yadda
hadarin soyayya ya fadowa rayuwar su, suna begen juna
da kuma tausayin halin da kowannen su yake ciki.
.
.
A RA'AYINA NI ILIYAS, AMIR SHI NE JARUMIN MASOYIN
DA NA TA'BA KARANTA LABARIN SA CIKIN DUKANIN
LITATTAFAN DA NA KARANTA. BA WAI DON NA MANTA
BA. SAI DON YADDA YA FANSAR DA RAYUWARSHI WAJEN
FARAUTAR SOYAYYAR MASOYIYAR SHI FIYE DA SAURAN
JARUMAN DA NA NAZARCI LABARNSU.
.
.
Amir ya raku6e a cikin duhun ciyawa ya 6oye, ya san
cewar ba zai iya tafiya ya yi nisa da ruhin shi Sadiya ba,
komai tsanani ya gwammace ya kasance a kusa da inda
take, koda kuwa ba za a bar shi ya ganta da idanun shi ba.
.
Sadiya ta xamo kamar rayuwar shi, ta zamo numfashin
shi, ita ce xuciyar shi. Ta yaya kuwa zai amince ya tafi ya
bar ta? Mutane wadanda basu san radadi da azabar
soyayya ba, suna ta ganin laifin shi har suna iya cewa
dashi ya tafi kada ya sake dawowa inda take. Shi kuma
yana yana ganin ba zai iya yin bankwana ya tafi ya bar ta
ba. Ya san cewa tabbas idan ya tsaya mutanen wannan
qauyen zasu iya kashe shi. To amma shima idan ya tafi
yana ganin tamkar ya tafi ya bar ruhinshi ne, wanda
kuma ba rayuwa ba tare da ruhi ba.
.
Sbd haka zai ci gaba da zama a kusa da inda take har
abada, ba zai ta6a za6ar barin inda Sadiya take ba, sun yi
nasarar nesanta su ne kawai da gangar jikin juna, amma
ba zasu ta6a yin nasarar raba su da xuciyoyin junansu ba.
.
.
**~**
.
.
A ranar da wannan al'amarin ya faru wani ya garzaya
qauyen Maqera akan keke, ya shaidawa Sarkin noma
halin da ake ciki. Nan da nan Alh. Mamuda ya rikice, yasa
Jafaru ya fito da babur, ya goya shi ciikin sauri suka duro
Turunkawa gidan su Sadiya.
.
.
Lp=35.
.
Alh. Mamuda ya rikice ya sa Jafaru ya fito da babur aka
goyo shi cikin sauri suka duro a Turunkawa.
.
Sa'ar da ya xo komai ya kwaranye, mutane sun watse
daga wajen da al'amarin ya faru, sai dai matasa da suka
xo suka zagaye shi suna bashi labarin qoqarin da suka yi
wajen casa Amir domin ya sallame su. Sarkin noma ya ce
dasu.
.
"Ai ni baku yi min komai ba, tunda dai ban xo naga gawar
shi ba. Me ya sa baku kashe shi ba in ga abin da za a yi.
Matar tawa wani shaidani zai xo yana neman ta kuna
kallon shi har ya bar garin nan da qafafun shi, ba a
kwashe shi a sume ko a mace ba? Mene ne amfaninku a
garin nan kuna matasa?"
.
Abashe ya ce dashi.
.
"mutane ne suka shiga tsakani ranka ya dade. Amma ba
don su ba ai da tuni mun gama dashi."
.
Garba Sidi dake a gaba-gaba ya ce dashi.
.
"nima nayi takaici da na xo na same su tare dashi har
yana iya kallon mutane, ban xo da wuri bane ranka ya
dade, kayi haquri. Amma da a ce ina wajen ya xo, kafin
ma wani ya san abin dake faruwa ai da tuni na aikata shi
da wannan bahaguwar."
.
Ya daga hannun shi ya kaiwa iska naushi. Sarkin noma ya
ce.
.
"To an gaishe ku duk da haka, amma ban ji dadi ba gsky."
.
Ya sa hannu a aljihu ya ciro sababbi 'yan dari-dari guda
goma ya miqawa Abashe ya ce su raba a tsakanin matasa.
Nan da nan suka fara sa-in-sa akan kudin. Sarkin noma ya
shiga gidan su Sadiya domin ya gana da iyayen ta akan
wannan sabuwar matsala da ta fara kunno kai tun ynx
kafin a yi auren, tun ba a je ko'ina.
.
Da Mal. Buba ya fara zaunawa, tsohon ya bashi haquri
yana lallashin shi, ya ce dashi.
.
"wannan ba wata matsala ba ce Alhaji, quruciya ce kawai
ta yaran nan, ka kwantar da hankalin ka, wannan aure
tunda aka riga aka amshi maganar nan to ai ba gudu ba
ja da baya. Sadiya matarka ce kada ka damu."
.
Mal. Buba ya ci gaba da ba Sarkin noma haquri, domin
kuwa in har wannan magana ta lalace, bai san inda zai sa
kan shi ba. Akwai kudade da yawa da suka biyo ta hannun
shi na maganar auren, duk ya bi ta kansu ya murqushe
shi kadai, da yake shi ne wuqa shi ne nama a auren
Sadiya.
.
A qarshe sai Sarkin noma ya ce da Mal. Buba.
.
"Ni a ganina hanya daya kawai zamu bi mu shawo kan
wannan matsalar, kowa ma ya huta. In haka ne me zai
hana ba za a dawo da ranar daurin auren nan xuwa jibi
ba? Kun ga in Allah Ya kaimu gobe sai in je in siyo duk
abin da ake jira in kawo, nan da kwana biyu a daura aure.
Idan tana gidana wane shakiyin yaro ne zai bi ta can ya
nemi yi mata lalata?"
.
Mal. Buba ya ce.
.
"Shikenan ma kawai! Haka din ya kamata a yi, wannan
shawara ce mai kyau in dai ba za a takura maka ba."
.
Sarkin noma ya ce.
.
"Ba wani takura, ka shiga ku tattauna da mutanen gidan,
ku hadu ku yanke duk abin da ake buqata. Sai mu je da
mota birni mu qarasa sayo akwatunan da suka rage mu
aiko da kaya gobe a daura aure jibi."
.
Mal. Buba ya yi sauri ya shiga cikin gida, ya samu Mal.
Kalla mahaifin Sadiya suka ke6e suka fara maganar dawo
da daura auren Sadiya a kwana biyu masu xuwa.
.
Nan da nan suka daddale maganar bayan sun kira
mahaifiyar ta sun sanar da ita halin da ake ciki.
.
A qarshe sai Mal. Buba ya koma shaidawa Sarkin noma
sun shirya, xuwa kwana biyu su xo a daura aure. Nan da
nan magana ta watsu a ko'ina, an dawo da daurin auren
Sadiya da Sarkin noma kwana biyu.
.
Sadiya ta ji duk maganar da ake yi, to amma ita Amir take
tausayawa. Ba ta san ynx a wane hali Amir yake ciki ba.
Abin da Sadiya ta kasa tabbatarwa shi ne anya kuwa ita da
Amir za su iya rayuwa a wannan duniyar idan ba su tare
da juna?
.
.
**~**
.
.
Har ranar daurin auren Sadiya ta xo bayan an yi kwana
biyun, yana cikin dajin dake a bayan garin su bai je ko'ina
ba. Yana 6oye akan wata qaramar bishiya mai duhun
ganye, daga kan bishiyar yana iya hango mutanen dake
nesa wadanda suke wuce wa ta hanyoyin da suka ratso
cikin qauyen daga kowanne 6angare.
.
Rashin lfy mai tsanani da zazza6i sun kama Amir bayan
ciwon soyayyar dake damun shi. Yana kwance a saman
bishiyar cikin ganyaye, yana kyarmar sanyi le6en shi na
sama yana haduwa da na qasa, gashi hatta saukowa daga
bishiyar ma ynx wahala zai yi mashi. Baya iya motsa
komai a jikin shi, sai dai idanunshi kawai dake a bude
yana kallon mutane wadanda ke wucewa, kuma yana jin
maganganun su sama-sama.
.
Babu wanda ya sani ballantana ya xo ya ceci rayuwar shi
ya dauke shi. To amma koda ace an xo an dauke shi an
bashi magani da wahala ya warke, don kuwa xuciyar shi
ta kumbura, kuma jini

Please Login or Register in order to submit comment