Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aure nata da Amir wanda ko sunan shi
bata sani ba, kuma ba ta san a inda yake ba, kuma bata
san halin shi ba.
.
Sadiya tayi murmushi a 6oye, babu wanda ya gan ta.
.
"Amir kai ne mijina, baka sanni ba, nima ban san ka ba,
amma kuma gashi Allah Ya nufa mun zama mata da miji
masoyan juna. Ina son ka masoyina kuma mijina Amir."
.
.
**~**
.
.
Tun kafin Mallam Mutawakkilu ya dawo gida mutanen
qauyen Gidan rijiya da suka samu halartar daurin aure
suka dawo da labarin abin da ya faru.
.
"Amir baqo, shi ne aka ba auren Sadiya."
.
Amir yana cikin dakin da aka sauke shi tun kwana uku da
suka wuce, sai ya ji matan gidan suna guda suna ambatar
sunan shi, sbd haka sai ya fito don ya ji abin dake faruwa.
.
Da fitowar shi riqe da littafin karatu sanye da singileti fara
a jikin shi, sai ya ga matan gidan sun yo kan shi suna
cewa.
.
"Ango ka sha guda!! Ango ka sha qamshi!!!"
.
"me yake faruwa?"
.
Amir ya tambaye su cikin rashin fahimta. Matar Mai
unguwa kakar shi ta ce dashi cikin wasa.
.
"Wata kyakkyawar yarinya 'yar Turunkawa ta qwace
mana kai, ta kasa mu. Ashe dama ravo ne ya xo da kai
Amir, ashe dama kai ne mijin wannan yarinyar da za a
daurawa aure a Turunkawa."
.
.
Ashe dama kai ne mijin wannan yarinyar da za a daurawa
aure a Turunkawa."
.
Mata suka sake kaurewa da guda, matan gida qannen
mahaifin Amir suka fara qarasowa suna dariya suna
kallon Amir, wanda ya bi su da kallo sheqeqe kamar yana
tsammanin kan su ya kwance. Da Amir ya fahimci da
gaske dai suke yi ba wasa ba ne sai yayi tsaki ya koma
cikin dakinsa ya sa rigar shi, sannan ya dauko jakar shi ya
bude ya fara xuba kayan shi a ciki da sauri.
.
A daidai lkcn da Amir ya gama xuba komai a cikin jakar
sa ya sa takalmi sai ga Mai unguwa ya shigo yana gungura
tsohon keken shi da yayi faci a hanya yana sauri ya dawo
gida. Ya samu mata suna guda da shewa, ya san cewar
tuni labari ya iske su.
.
Amir ya fito da jakar shi a hannu ran shi a 6ace. Mai
unguwa Mutawakkilu ya dube shi ya ce dashi.
.
"tun ynx zaka je ka fadiwa abokan naka dake Zariya, na
dauka zaka dakata sai bayan an xo da amarya anjima...?"
.
Amir ya dakatar da tsohon cikin ladabi ya ce dashi.
.
"dakata Mai unguwa, ina son ka san cewa ni ba irin
yaranku na nan qauye ba ne, wadanda kuke juya su
yadda kuke so kamar dabbobi, basu san 'yancin su ba. An
fada maka aure hauka ne da zaka je ka sa a bani aure ba
tare da na sani ba? Ban ta6a ganin yarinyar nan ba, babu
soyayya a tsakaninmu, kuma bata a cikin jerin matan da
zan iya zama dasu a rayuwata. Haka ake yin aure?
.
Matan dake a cikin gida suka yi cirko-cirko suka daina
shewa da guda, suka dora hannuwa akan su suna kallon
yadda Amir yake fada wa Mai unguwa magana a cikin
fada, abin da basu ta6a ganin wani yaro ya yiwa babba ba
a cikin tarihin gidan. Amir ya ci gaba da cewa.
.
"idan zaku yi irin wadannan al'adun naku na qauye ai ya
kamata ku san da wa zaku yi, ju yi la'akari da rayuwata
mana. A jami'a nake karatu tare da turawa 'yan wasu
qasashen. Na yi kama da wanda zai auri wata 'yar qauye
jahila, wacce bata san komai ba? Wannan ai wulaqanci ne
kawai kun 6atawa mutum 'record' din rayuwa. Haka ake
yin aure? Idan ma auren nake so, irin wannan auren zan
yi?"
.
Wasu maza qannen mahaifin Amir suka tasowa Amir a
fusace suna zagin sa da suka xo suka iske irin
maganganun da Amir yake fadiwa tsohon su. Daya daga
cikin su ya dauko icce ya tasarwa Amir yana cewa.
.
"kai don ubanka wannan ba shi ya haifi ubanka ba, da
kake fada mashi irin wannan baqaqen maganganun? Ko
an fadi maka zama a birni hauka ne?"
.
Mai unguwa ya dakatar da 'ya'yan shi ya ce dasu.
.
"Kada wanda ya ta6a shi, ku rabu dashi. Ni nayi mashi
laifi, ba ku ba, kuma ni yake fadi mawa ba da ku yake ba.
Ba ruwan ku da shi. Kada wanda ya ta6a shi."
.
Amir ya ce da mai unguwa.
.
"zan koma makaranta, dama hutu ne ya kawo ni ba zama
nazo yi ba. Kuma har abada ba zaku sake gani na a garin
ku ba. In dai irin wannan 'relation' din naku haka yake, to
bani ba ku har abada."
.
Amir ya sa kai ya fice waje a fusace dauke da jakar shi.
Wasu daga cikin xuriyar mai unguwa Mutawakkilu suka
fashe da kuka ganin yadda Amir ya wulaqanta babban
dattijon su a gaban su.
.
Mai unguwa ya ji wani abu ya taso mashi wuya ya tsaya a
mogwaron shi. Ya dafe qirji ya nufi dakin shi cikin sauri,
'ya'yan shi suka bi shi a baya domin kuwa sun san cewar
ciwon xuciyar shi ne ya tashi.
.
Da shigar shi dakin ya fadi qasa sbd juwar da ta kwashe
shi. Mai unguwa bai damu ba da wannan zafin ciwon da
ya taso mashi, domin kuwa a yadda Malam Kalla ya bashi
wannan amana, ya mutunta shi, ya fifita shi akan 'yan
uwan shi dake rigima, ya ba jikan shi auren Sadiya. Bai
damu ba a ynx don baqin ciki ya kashe shi. Ko ba komai
ba zai sake rayuwa yana kallon fuskar mallam Kalla ba
alhalin Amir ya watsawa idanuwanshi qasa ba. Amir ya
gudu ya ce baya son Sadiya.
.
Babu shakka Amir ya wulaqanta su!!
.
.
**~**
.
.
Ba a dade ba da yin wannan kace-nace a tsakanin Mai
unguwa Mutawakkilu da Amir ba, nan da nan labari ya
koma kunnen mutanen Turunkawa. Wasu da suka samu
labari sun yi murna, domin kuwa basu ga dalilin da zai sa
ace duk yawan samarin dake son Sadiya a wannan
qauyen an tsallake su an bayar da ita a can Gidan rijiya
ba, kuma can din ma ba dan gari aka baiwa ba, dan birni
aka baiwa wanda ya kawo xiyara kuma zai koma.
.
Wannan labari ya 6atawa iyayen Sadiya rai babu kamar
Haj. Uwani wacce taxo daga Zariya. Sbd ta san cewar
rashin sani ne yasa Amir din da aka baiwa Sadiya ya ya ce
baya son ta, ta san cewar don bai ganta bane. Babu
shakka wannan Amir din ya wulaqanta Sadiya duk
matsayinta da kuma darajarta.
.
Nan da nan iyayenta maza da mata suka hadu a daki daya
domin tattaunawa akan wannan matsala. Buba qanin
Mallam Kalla shi ya fara magana cikin fushi yana cewa da
dan uwan shi.
.
"kome ya faru kai ka jawo mana shi Mallam Kalla. Ynx ina
amfanin a ce duk 'ya'yanmu dake a wannan qauyen, ka
hana kowa aure Sadiya ka kai ta daji ba dangin iya babu
na baba. Tun kan a je ko ina ga yadda abin ya kasance.
Ina amfanin irin wannan? Me zai hana a yi mana dariya a
garin nan?"
.
Mallam Kalla ya ce.
.
.
Lp=12
>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 12
.
.
Mallam Kalla ya ce dashi.
.
"to ni dai wannan aure na danqa shi ne a hannun
aminina Mallam Mutawakkilu kuma nace na bashi amana
ya za6o yaron da yaga ya dace a cikin 'ya'yanshi ko jikoki
mu bashi wannan aure, kuma duk wannan magana da
ake yi ba shi ne yazo ya samamu yace babu wannan aure
ba. Sbd haka ko Amir yana son Sadiya ko baya sonta bai
kamata mu dauki wani mataki ba tukuna, sai mu jira har
sai in Malam Mutawakkilu ne yaxo ya ce sun haqura a ba
wani ita, sannan sai mu san yadda zamu yi daga baya."
.
Haj. Uwani ta sa baki ta ce dasu.
.
"ni a gani na tunda haka wannan al'amari ya kasance,
kawai ku bani yarinyar nan mu koma Zariya ta ci gaba da
karatun ta, tunda kun ga zamanta a nan ton asiri ne a a
gare mu. Tun ynx kun ji irin maganganun da mutane ke
fadi.
.
Haire wacce bata ce komai ba ta sa baki.
.
"to yaya lamarin auren ta kenan idan kuka koma can?"
.
Haj. Uwani ta ce.
.
"to ni fa ban ga dalilin da zai sa ku riqa matsawa kan
wannan maganar aure ba. Tunda haka abin ya kasance
mu duka muyi haquri mu bata lkc ta za6i saurayin da
take so da kan ta domin ita ma hankalinta ya kwanta. Ba
sai ya zama dole a nan ba, ko a can Zariya ta samu
saurayin da take so shi kenan sai su xo a yi maganar aure.
Ni fa wlh na gaji da auren da kuke yiwa yaran nan na
sadaka. A bar Sadiya kawai ta za6i wanda take so, a
haqura da zancen wancan yaro da yace baya son ta ya
gudu. Ku bar mu mu koma mu ci gaba da zama tare, idan
hankalin kowa ya kwanta sai mu san me ya kamata muyi
kuma a nan gaba.
.
Mallam Kalla ya ce.
.
"wannan shawara ta Hajiya ita zamu bi, kawai gobe ku
shirya ta biki ku koma, duk abin da za ayi sai a yi idan
tana can, amma idan muna ganinta a nan hankulan mu
ba zasu kwanta ba.".
.
Da wannan suka daddale a nasu 6angaren, to amma a
can 6angaren Sadiya kwana tayi tana kuka sbd tsananin
baqin ciki. Me yasa wannan saurayi ya wulaqanta ni?
Sadiya ta riqa tambayar kan ta. Me yasa ya gudu ya bar ni
tin kafin yaxo in gan shi?
.
Sadiya tana cikin damuwa, domin kuwa ita ce amaryar da
bata ta6a ganin mijin ta ba, har kuma gashi za a dauke ta
a mayar da ita wani garin. Ita ce amaryar da ta riqewa
mijinta alqawari ba tare da ta6a ganin shi ba, kuma ta ji
tana son shi tun kafin ta san sunan shi. Amma kuma gashi
ya gudu ya bar ta sbd tsananin qiyayya.
An daura mata aure har an raba auren ba tare da ta san
ko waye mijin ba.
.
Sadiya ta ji tsoro ya kama ta, domin kuwa ta san Amir ya
tsane ta, baya son ta, bata san inda yake ba a halin ynxn,
amma kuma ko ma a ina yake ta san cewar yana can
yana jin haushin ta.
.
Da Haj. Uwani taga Sadiya tana kuka sai ta lallashe ta, ta
dafa mata kai ta ce da ita.
.
"ki yi haquri Sadiya. Kin cika 'yar halak, kun bi umarnin
iyayen ki, kuma kin kare masu mutunci. In Allah Ya so Ya
yarda wannan halaccin da kika yi masu ba zai ta6a tashi a
banza ba, za ki ga sakamako mai kyau tun a duniya, kuma
har abada ba za ki ta6a yin da-na-sani ba. Shi kuma
wannan yaro da ya guje ki, idan ma yayi haka ne don ya
tozarta ki, to ki sani ba zai ta6a yin nasara ba har abada.
Idan Allah bai tozarta bawanShi ba, to mutum bai isa ya
tozata shi ba. Kada ki damu!"
.
Da wannan nasiha Sadiya ta share hawayen ta, ta mance
da komai. Washe gari suka hada kayan su suka koma
Zariya. Da xuwansu Haj. Uwani ta yiwa mijin ta waya ta
sanar da shi abin dake faruwa. A ranar ya baro Kaduna ya
dawo gida, ya kwashi takardun Sadiya ya shiga jami'ar
Ahmadu Bello domin nema mata gurbin karatu a
matakin 'Diplima' da ake kan daukar sabbin dalibai
wadanda ke yin qananun kwasa-kwasai na shekara biyu.
.
Da yake yana da uwa a gindin murhu a cikin sati uku a
jerin sunayen farko, sunan Sadiya ya fito a cikin daliban
da aka ba gurbi a fannin shari'a.
.
Sadiya ita ma ta zama daliba a Jami'ar Ahmadu Bello. Ta
matso kusa da Amir bata sani ba.
.
.
**~**
.
.
Sai da Amir ya dawo makaranta da sati bayan komasi ya
kwaranye, sannan ya sanar da abokan shi abin da ya faru
dashi a lkcn da ya je qauyen su. Mustafa da Haidar suka
fara tuntsira mashi dariya suna tafa hannuwa.
.
Amir ya ce dasu cikin fushi.
.
"Ku fa banzaye ne wani lkcn, shi yasa tuntuni naqi fadi
maku wannan labarin. Bana son wani ya ji wannan
labarin domin kuwa sun gama 6ata mani tarihin rayuwa
ta. Kamar ni ace wai za a bani aure sadaka a qauye?" haba
mutanen nan ai sun lalata mani 'record'
.
Haidar ya ce dashi.
.
"to da aka xo maka da amaryar ka gan ta me ka ce
mata?"
.
Amir ya harare ashi.
.
"ni ne ma zan tsaya ganin iri ta? Bari ku ji in fadi maku, ni
ko sunanta ma ban sani ba har ynxn."
.
Mustafa ya ce.
.
"Ai ko don tarihi ma da ka tsaya ka gan ta, amma ina
amfanin a ce mutum ya yi aure har sun rabu da matar a
ce ko sunan ta bai sani ba.
.
.
Lp=13
>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 13
.
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin
ba.
.
.
"Ai ko don tarihi ma da ka tsaya ka gan ta, amma ina
amfanin a ce mutum ya yi aure har su rabu da matar
amma ko sunan ta bai sani ba, ballantana kuma ganin ta.
Ynx ko magana baku yi ba?"
.
Amir ya yi tsaki ya ce da mustafa.
.
"baku da hankali 'friends' to wai ku nufin ku in tsaya su ji
dadin liqa min ita in rasa yadda zan yi,? Su fa qauyawan
nan in suna wani abin, idan aka baka labari sai ka ce
qarya ne. Kawai ina nan ina shanawa ta 'campus'
'yanmata suna yi da ni, a ce kuma na auri wata 'yar
qauye, to in kai ta ina? Ai wannan ba qaramin abin kunya
ba ne idan na sake ma aka samu labari. Na san wata
babin ma har mujalla sai ta kai labarin don ta tona mani
asiri."
.
Haidar ya tattara hankalin shi ya ce.
.
"to ita dai rayuwa kamar idaniyar ruwa ce, ba a sanin
inda take 6ullawa. Ni a gani na da aka yi haka da ka tsaya
ka gan ta, me yiyuwa ta hadu kai ne baka sani ba. Wata
qila da ka tsaya ka gan ta ka ji tayi maka. Kaga da sai ka
taho da abar ka gida ku zauna, ka huta da wannan
wahalar da kake yi a wajen 'yanmatan jami'a kullum..."
.
Amir ya dakatar dashi ya ce.
.
"bana son irin wannan maganar Haidar, kai ma ka san
cewar ko na ganta ba zan so ta ba. Ba fa irin 'yanmatan
mu ba ne masu zafi dake a nan 'Campus', na fadi maku
'yan qauye ne. Wai ku baku ta6a ganin 'yan matan qauye
bane da zaku dame ni?"
.
Abokan shi suka sake fashewa da dariya suna ihu. Su
duka abin da basu sani ba shi ne, wannan baqauyiyar
yarinyar da suke yiwa dariya, tana nan a kusa dasu, ita
ma ta dawo birni ta zama 'yar jami'a.
.
.
**~**
.
.
Sai da hankalin kowa ya kwanta, komai ya lafa, sannan
Mai unguwa Mutawakkilu ya samu wata rana da daddare
ya je Turunkawa domin ya ba Mallam Kalla haquri bisa
wannan wulaqanci da Amir ya yi masu.
.
Bayan tsofaffin biyu sun gama gaisawa, sai Malam
Mutawakkilu ya ce da Malam Kalla.
.
"na xo neman afuwa ne akan laifin da muka yi. Tuntuni
nake son in zo to amma tun da wannan al'amarin ya faru
ban qara lfy ba, ciwon hawan jini na ne ya taso min. Sai
ynx na samu sauqi na ce to bari in xo neman
afuwa....Don Allah ku yi haquri."
.
Mallam Kalla ya ce dashi.
.
"Kada ka damu Malam Mutawakkilu, domin duk muna da
labarin abin daya faru tsakanin ka da wannan yaro. Kai
kan ka an ce babu irin rashin kunyar da bai yi maka ba
akan wannan magana. To abin ne dai duk mun yi shi cikin
rashin sanin abin da zai biyo baya. Ka san cewar su irin
wadannan nan yaran dake a maraya ba irin yaranmu
bane na nan qauye, su yara ne da idanun su suka bude,
abin da suke so to shi ake yi, abin da basu so to ba a yin
shi."
.
Mallam Mutawakkilu ya ce.
.
"to in ban da lalata irin ta dan zamani, mahaifin yaron
nan ya rasu. Ynx in ban da wannan karatu da suke yi
babu wata sana'a da suka dogara da ita, sai shegiyar
qarya cike da ciki. To sai naga cewar in aka bashi wannan
aure ai kamar an taimaka mashi ne, kaga ya huta da irin
wannan shegen auren nasu na qarya a yi ta kashe kudi a
banza, ana wani jera akwatuna da kayayyaki."
.
Mallam Kalla ya ce.
.
"kai ke nan da ka san haka, to amma su ai ba zasu ta6a
fahimta ba. Abin da suke so shi zasu yi, ko iyayen su naso
ko basu so."
.
Mai unguwa Mutawakkilu ya yi tsaki ya ce.
.
"ku yi haquri Mallam Kalla, wannan abu dai ya riga ya
faru."
.
"Ba komai, mu tuni mun haqura da wannan magana
dama, ynx ma yarinyar tana can sun koma Zariya ita da
qanwar tamu goggonta Haj. Uwani zata ci gaba da
karatun ta. Xuwa gaba idan ta samu wanda take so sai a yi
mata auren. Wannan abu ya wuce."
.
Ya sa hannu a aljihu ya ciro kudin sadakin da Malam
Mutawakkilu ya bashi tun a ranar da aka daura auren, ya
ce.
.
"Ga kudin sadakin nan da ka ba ni, dama ina ta son in
aika maka da su, to hali bai samu ba."
.
Mai unguwa Mutawakkilu ya ce.
.
"haba Malam Kalla, ai ka san baya halatta a kar6i wannan
kudi, sbd ita yarinya tana da rabin sadakinta a shari'ance
kasancewar auren da aka qulla. Sbd haka wadannan kudi
a bar su."
.
Mallam Kalla ya ce dashi.
.
"A'a, Malam Mutawakkilu, ai ba zai yiwu ba a ce za a bar
su gaba daya ba, sai dai a bar rabin."
.
"wallahi Malam ba zai yiwu ba in kar6i wadannan kudin,
na bar maka su a ba yarinyar har ga Allah.
.
.
**~**
.
.
Wata guda kenan da fara karatun Sadiya a jami'ar
Ahmadu Bello. Wata rana wani malami ya basu aikin
bincike ya ce su je labirari su yi nazari su xo mashi da
amsa. Sadiya ta dauki litattafan ta ta rungume su a qirjin
ta ta nufi labirari, tana tafiya sannu a hankali, sanye da
baqaqen kayanta riga da siket masu fadi da kuma gyale
shima yana qyalqyali da sheqi yana daukar idanu idan
tana tafiya. Wadannan kaya suna matuqar fito da
kyakkyawar surar ta musamman farat fatarta. Da kuma
yalwataccen baqin gashin ta.
.
Sadiya ta shiga cikin dakin karatun, wanda ke cike maqil
da dalibai maza da mata, kowanne a zazzaune suna
karatu, wadansu kuma suna a tsaitsaye a jikin kantocin
dake cike da litattafai nau'i daban-daban suna dubawa
suna neman littafin da suke so su karanta.
.
.
Lp=14
>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 14
.
.
Wadansu kuma suna tsaye jikin kantocin dake cike da
litattafai nau'i daban-daban suna dubawa, suna neman
litattan da suke son so karanta.
.
Sadiya ta nufi 6angaren da ake adana litattafan shari'a ta
fara dubawa sannu a hankali. A daidai lkcn da take kan
duba littafin sa sai ga Amir kamar an jeho shi ya shigo
cikin dakin karatun shima ya shigo zai yi nazarin wani
littafi da aka basu aiki a ciki. Amir ya wuce daliban dake a
zazzaune, ya nufi 6angaren kantocin da aka taskace
litattafai domin neman wanda ya ke buqata, Amir ya nufi
6angaren da Sadiya ke tsaye ta qurawa litattafai idanu
tana qoqarin gano wanda taxo nema a ciki. A daidai
wannan lkcn ne Amir ya sami kan shi tare da wata
kyakkyawar budurwa wacce ke tsaye a gefen shi tana
kallon litattafai bata san cewar yazo kusa da ita ba. Amir
ya bita da kallo cikin tsananin kaduwa domin kuwa tunda
yake a duniya bai ta6a ganin budurwar da tasa xuciyar
shi ta babirce ba a kallon farlo sai wannan budurwa dake
a tsaye.
.
Xuwa can kuma sai Sadiya ta gano littafin da tazo nema.
Ta kai hannu ta ciro shi a cikin kanta. Sannan ta fara
waigen inda zata zauna tayi karatun. Sai a lkcn ne ta lura
da kyakkyawan saurayin dake tsaye a gefenta ya qura
mata idanu ko qiftawa baya yi. Suka kalli juna, Amir ya yi
mata murmushi. Sadiya ta kawar da kanta tayi tafiyarta
xuwa inda zata zauna, domin kuwa ba kula samari taxo yi
ba karatu ta xo yi a halin ynx.
.
Sadiya ta zauna cikin nutauwa ta bude littafin ta fara
karantawa. Amir dake a jikin kanta nesa da ita yana
kallonta cikin qaton dakin karatun, ya cika da al'ajabin
kyawun budurwar, domin kuwa bai ta6a ganin budurwar
da ta burge shi a ganin farko ta tafi da xuciyar shi ba irin
wannan budurwa.
.
Tunda yake a duniya bai ta6a ganin wata mace wacce ke
saurin tafiya da xuciyar ma'aboci kallon ta ba irin
wannan budurwa. Gata kuma da nutsuwa, ba ruwanta da
kowa, ga ta can zaune ta samu wuri ita kadai, tayi nisa da
wurin da sauran dalibai suke zaune.
.
Gata can zaune sanye da kayan mutunci, kuma da ganin
ta kyawun ta ne irin na halitta babu wani alamar qyale-
qyale a fuskarta. Kai babu shakka irin wadannan 'yan
matan basu da yawa a duniya. Amir ya tabbatarwa
xuciyar shi.
.
Ya yi sauri ya dauki littafi ya nufi inda take zaune. Ya
zauna a kusa da ita, sannan ya yi mata magana a sanyaye
ya ce da ita.
.
"Baiwar Allah, ba za ki damu ba idan na maqwatace ki?"
.
Sadiya ta girgiza kanta ba tare da ta dago kan ta ta kalle
shi ba. To amma kuma a jikinta ta ji cewar wannan
saurayin ita ya qurawa idanu. Nan da nan ta ji ran ta ya
6aci domin kuwa ba ta son saurayin ya dame ta, kuma ba
ta son a qura mata idanu ana kallon ta. Ta dago kai suka
hada idanu ta ce dashi.
.
"Gsky bana son kallo malam da za ka bar ni in yi karatu
da na so."
.
Amir ya tambaye ta cikin murmushi.
.
"laifi ne don mutum ya tsaya kallon kyakkyawa irin ki,
musamman a irin wannan lkcn da irin ku basu da yawa a
duniya?"
.
Sadiya ta harare shi, akwai alamar ita ba irin sauran
'yanmatan da Amir ya saba yaudarar su da kalamai ba ne
suna rudewa akan shi. Ita wannan mace ce mai tsananin
hankali da kuma xurgin tunani. Shi kan shi Amir ya
fahimci haka a lkcn da ta sake dago kan ta tace dashi.
.
"Idan ba zaka damu ba don Allah ka bani wuri in yi
karatu, idan kai ba karatu ya kawo ka ba to ni shi ya kawo
ni."
.
Amir ya ji tsoro ya kama ahi domin kuwa babu wata
budurwa da ta ta6a yi mashi haka a duniya. Amir yana da
kwarjini da sa'a a wajen 'yanmata, kuma ya riga ya saba
samun nasara a duk lkcn da ya nemi soyayya. To amma a
wannan karon Amir bai samu nasara ba, domin kuwa
wannan kyakkyawar budurwar bata amshi soyayyar shi
da hannu bibbiyu ba, a wannan karon Amir bai samu
nasara ba, domin kuwa ga wata budurwa nan a zaune
tana hararar shi tana sanar dashi ya tashi ya bata wuri
kada ya dame ta.
.
Gashi kuma Amir ya kamu da ciwon son ta a cikin dan lkc
qanqani, ba irin soyayya ta wasa ba da ya saba yi yau da
kullum a cikin makarantar. Wannan soyayya ce ta gsky ta
kama shi babu zato babu tsammani. Ina ma a ce wannan
budurwa ta amince ta so shi. Babu shakka da ya riqe
mata alqawari har xuwa lkcn da zasu yi aure, kuma ba zai
ta6a wulaqanta ba.
.
Sadiya ta yi tsaki sannan ta tattara litattafan ta da ta xo
dasu ta dauki jakar ta ta kama hanyar ficewa daga dakin
karatun ba tare da ta sake kallon Amir ba da ke zaune
yana kallon ta. Amir ya yi sauri ya tashi ya bi ta a baya
cikin rudewa. Babu shakka wani mashi mai tsananin tsini
ya soke shi a xuciyar shi. Tunda yake bai ta6a jin radadin
soyayya mai xogi da dafi irin wannan ba.
.
Wannan soyayyar gsky ce yake yi mata, babu yaudara ko
cin amana, ya qarasa inda take a lkcn da ta fito daga
dakin karatun zata yi tafiyar ta. Amir ya ce da ita cikin
sanyin murya.
.
"Haba baiwar Allah!! Me yasa za ki guje ni a daidai lkcn da
na kamu da matsananciyar soyayyarki a xuciyata? Ya
kamata ki saurareni, kuma ki yiwa kalamaina fahimta mai
kyau.
.
.
Lp=15
>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 15
.
.
Ya kamata ki saurare ni, kuma ya kamata ki yi wa
kalamaina fahimta mai kyau. Wannan ba wani abu bane
da ba ki sani ba, ba ni kadai ba ne saurayin da ya fara
ganin ki ya ce yana son ki a duniya ba. Sbd babu wani
namiji da zai gan ki bai yi fatan ki zama masoyiyar shi ba.
Wannan shi ne abin da na ji a xuciyata tun a lkcn farko da
na dora idanuna a kanki. Ina son ki amince ki amshi
soyayya ta."
.
Sadiya ta dubi Amir bayan ta ji ya kai qarshe, sannan ta
ce dashi.
.
"Naji bayanin ka, to amma ina mai fargabar sanar da kai
cewar gsky ba zan iya amsar soyayyar ka ba. Bana jin zan
iya yin soyayya a daidai wannan lkc, sbd kaga ynx ina
buqatar in samu natsuwa in yi karatu bai kamata in
amshi soyayyar kowa ba, ka yi haquri."
.
Sadiya ta ce dashi.
.
Sadiya ta ci gaba da tafiya riqe da litattafan karatun ta,
iska na kada kayan jikin ta. Amir ya ci gaba da bin ta da
lalllashin ta.
.
"Ina son ki yarda cewa na zan iya daina son ki ba a
duniya. Zan ci gaba da son ki kamar yadda nake son ki a
halin ynx, har sai naga ranar da za ki tausayawa xuciya ta
ki amshe ni a matsayin masoyinki, kuma mijin ki in Allah
Ya yarda."
.
Sadiya ta ce da shi.
.
"ni kuma zan ci gaba da rashin son ka, kamar yadda bana
son ka a halin ynx. Kuma ba zan ta6a daina rashin son ka
ba har sai naga ranar da kai da kan ka za ka haqura ka
cire ni a xuciyar ka."
.
Sadiya ta tafi ta bar Amir a tsaye xuciyar sa tana quna da
tafarfasa. Ga Sadiya can tayi nisa bata buqatar ta sake
juyowa ta kalle shi, domin kuwa ba ta son shi, ba kuma ta
ta6a ganin shi ba sai a wannan ranar.
.
Amir ya daddafa a hankali ya koma dakin kwanan su dake
a cikin makarantar, zazza6in soyayya mai radadi ya kama
shi. Babu shakka Amir ya kamu da ciwon soyayya, kuma
ba zai ta6a daina son ta ba har abada.
.
.
**~
.
.
Lkcn da zata

Please Login or Register in order to submit comment