Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga ranar Amir ya watsar da ita, a dai
dai lkcn da take qoqarin sanar dashi wata magana mai
muhimmanci da kuma abin da mahaifinta ya ce a game
da soyayyarsu.
.
Daga baya Shema'u ta samu kanta sosai a cikin damuwa,
kuma tayi kuka mai yawa. Kuma tun daga lkcn sai ya
kasance duk san da mahaifinta ya ziyarceta sai ya
tambaye ta ina Amir din da take bashi labari?
.
Shema'u ta kasn ji tsoro ya kama ta, kuma hakan yana
sake bijiro mata da wata damuwa a cikin xuciyarta. Ta
kan ji kunyar ta fadiwa mahaifinta cewar Amir ya daina
son ta, bayan kuma ta dade tana sanar dashi
muhimmancin Amir a rayuwar karatun ta da kuma
zamantakewarsu matsayin saurayi da budurwa. Koda
yaushe idan aka yi mata zancen Amir sai dai tayi dariyar
qarfin hali ta ce.
.
"Amir yana nan lfy, kuma muna nan tare kamar kullum."
.
Bayan ta gama fadin haka a 6oye kuma sai ta fashe da
kuka, domin kuwa Amir ya dade da yi mata nisa, ya daina
kula ta. Kuma bata san lkcn da zai tausaya mata ya dawo
gare ta ba.
.
Domin ya dawo mata da mutuncin ta a wajen qawayenta
kada su rainata su ce masoyinta ya guje ta.
.
Domin ya dawo mata da barcinta wanda tuni ya dade da
barin idanun ta.
.
Domin ya dawo mata da farin cikin ta wanda tuni
damuwa da baqin ciki suka mamaye shi.
.
A ynx kuma Shema'u ta samu labarin sabuwar budurwar
Amir, kuma an fadi mata sunan ta da kuma sashen da
take karatu a jami'ar.
.
Sunan ta Ni'ima.
.
Shema'u ta ji bata son Ni'ima a rayuwar ta, kuma bata
son ganinta tare da Amir. Don haka sai ta fara saqe-saqe a
xuciyarta, tana neman hanyar da zata dauki fansa akan
Ni'imah wacce take zargin ita ce ta qwace mata saurayi.
.
Shema'u tana tsammanin ba don Ni'ima ba to da babu
abin da zai sa Amir ya guje ta. Bata san cewa Amir yana
da daruruwan mata a duniya ba, kuma da ace zata yi
haquri to a kwana a tashi ita ma Ni'ima zata wayi gari
Amir ya mance da ita, ya komawa wata tauraruwar
sabuwa.
.
Domin kuwa halin shi ne!!
.
To amma kuma Shema'u ba zata iya haqura ba, sbd
tsananin fushi da matsanancin son da take yiwa Amir, sai
ta ji ta tsani Ni'ima, a cikin wannan fushi da kuma
qudurin ramuwar gayyar dake a xuciyarta ne tayi
qoqarin gano dakin da Ni'ima take zaune a jami'ar.
.
A wani dare bayan an idar da sallan isha'i, qafa ta dauke a
wasu yankuna na makarantar, Shema'u ta bi dare a 6oye
ta la6e a hanyar da Ni'ima ke biyowa ta nufi dakin
kwanan su, a kowanne lkc idan ta dawo hira daga wasu
dakunan qawayen ta.
.
Ni'ima ta taho ita kadai zata shiga dakin su, bata san me
yake faruwa ba, sai ta ji an kwada mata kwalba a goshin
ta. Kwalbar ta fashe a goshin Ni'ima, a lkcn ne kuma ta
fashe da kuka mai dauke da kururuwa a cikin daren.
Shema'u ta tsaya tana kallonta cikin tsoro da ragowar
kwalba a hannunta, ita ma a tsorace take domin kuwa
bata ta6a aikata ta'addanci irin wannan ba, ko fada bata
yarda a yi da ita, domin kuwa bata son wani abu ya tayar
mata da hankali.
.
Gashi ynx kuma soyayya ta jawo mata zata yi kisan kai da
hannunta. Me ya same ta?
.
Sbd haka sai Shema'u ta fara kuka, ita ma maimakon ta
gudu sai ta tsaya tana kallon Ni'ima wacce ta dafe
goshinta, tana kuka kamar ranta zai fita. A haka har
dalibai suka firfito daga cikin dakunansu suka ritsa
Shema'u da kwalba a hannunta da kuma Ni'ima wacce
jini ya 6ata kyakkyawar fuskar ta tana kuka.
.
A cikin daren aka kama Shema'u aka kai ta ofishin
jami'an tsaro na makarantar, suka tuhumeta dalilin da
yasa za ta yi kisan kai. Shema'u ta dade tana kuka kafin ta
basu amsa da cewa saurayi ne ya hada su fada da Ni'ima.
.
"mun yi alqawarin aure ni da Amir, daga baya kuma sai
ya koma yana son ta, ya karya alqawarin da ya daukar
min....."
.
Kafin gari ya waye duk daliban da suke makarantar sun
samu labarin abin daya faru.
.
Wani saurayi ya hada wasu 'yan mata biyi fada, har daya
ta fasawa dayar kai da kwalba.
.
Aka tsare Shema'u sannan kuma akai Ni'ima asibiti. Lkcn
da Amir da abokan shi suka samu labari tun a cikin daren
suka gudu suka bar makarantar da alqawarin sai sun yi
sati daya basu dawo ba, sai komai ya lafa.
.
Haidar da Mustafa suka ce Kaduna zasu je su 6oye su
huta, shi kuma Amir ya ce wani qauyensu zai je mai nisa
ya zauna a can, don kada a je gidansu neman shi same
shi.
.
A haka wadannan hatsabiban samarin su uku suka rabu.
Mustafa da Haidar suka tafi Kaduna shi kuma Amir ya
xuba kayan shi a jaka ya goya ya nufi wani qauyen su mai
suna Gidan rijiya.
.
Shi kuma Amir ya xuba kayan shi a jaka ya goya ya nufi
wani qauyen su mai suna Gidan rijiya, mai tafiyar
kilomita wajen saba'in da daya daga birnin Zariya.
.
Da misalin qarfe goma sha daya ya sauka daga motar da
ta dauko shi daga zariya. A dai dai qauyen Gidan rijiya
akwai 'yan aca6a a wata tsohuwar rumfa. Nan da nan
suka tar6e shi suna tambayar shi qauyen da zai je. Daga
bakin titin xuwa qauyen Gidan rijiya tafiyar kilomita uku
ne. Amir ya hau babu bayan ya sanar da dan aca6an daya
dauke shi inda zai kai shi.
.
Suka cilla aguje suna zagaye ta6o da ruwan dake a
kwance kan hanyar qauyen. Kowane gefe Amir ya duba
amfanin gona ne ya fara girma a cikin gonaki. Ga
manoma nan suna ta aiki a gonaki, suna dago kai suna
kallon babur din da ya dauko Amir dan birni. Rabon da
Amir yaxo wannan qauye na kakannin shi tun mahaifin
shi ya matsa mashi ya xo wata ta'aziyya ta qanin shi daya
rasu.
.
To amma kuma su mutasnen qauyen da yake suna yawan
xuwa Zariya gidan su Amir, sun saba da shi kuma suna
yawan tambayar shi.
.
"Sai yaushe zaka xo qauye Amir?"
.
Bai ta6a cika masu alqawarin daya sha dauka cewar zai je
ba, domin kuwa baya son rayuwar karkara, yafi son ya yi
zaman shi a birni yana tsara kyawawan 'yan mata 'yan
jami'a. Ynx haka ma wannan xuwan kamawa tayi yaxo zai
yi 'yan kwanaki a dalilin abin daya faru a makarantar su,
don kada a kama shi ace shi ne sanadin hada 'yan matan
fada, har daya taso kashe daya a cikin su.
.
Amir bai san abin da zai faru ba a dalilin xuwan shi
wannan qauyen da yake rainawa, bai san cewar akwai
wani babban al'amari ba da yake jiran shi.
.
Wata soyayya tana nan tana jiran shi, sannan wata
kyakkyawar yarinya mai suna Sadiya tana nan a zaune a
gidan su tana jiran ta zama matar shi.
.
Duk lkcn da wata gagarumar soyayya zata qullu babu
shakka sai wani abu ya faru wanda zai zama sanadi. Da
ace Amir bai xo wannan qauye nasu ba, da babu abin da
zai sa har wani abu ya faru tsakanin shi da Sadiya 'yar
qauye.
.
Amma kuma gashi ynx ya xo!!!
.
Amir ya qosa ya isa can, domin ya zauna ya 6oye kada
wani abu yaxo ya dame shi, to amma kuma a can din ne
zai iske abin da zai dame shi, abin da zai canza mashi
halayen shi na yaudara da kuma zalunci. Babu shakka
Amir zai dawo ya baiwa mutane tausayi, domin kuwa ynx
ne soyayyar gsky zata baqunci xuciyar shi.
.
Ba irin soyayyar shi ta qarya ba, soyayyarsu ta 'yan
makaranta.
.
.
**~**
.
.
Gidan rijiya wani qauye ne wanda bai wuce gidaje ashirin
da shida ba, sai kuma jefi-jefin rugagen fulani dake kan
tsaunika a kusa da garin. Mazauna qauten su dukansu
manoma ne, shi yasa idan gari ya waye rana ta fito, da
zarar an gama karyawa sai kowa ya watse ya tafi gona, sai
qananun yara da 'yan mata za a samu suna wasanni da
guje-guje a cikin qauyen, wasu kuma suna tsaga qasa
suna 'yar gala-gala a bakin qofar wani injin niqa.
.
Mai unguwar qauyen wani tsoho ne mai suna Malam
Mutawakkilu. Shi ba ya xuwa gona, sai dai idan kowa ya
tarwatse sai ya dauko kujerarshi ta katako ya ajiyeta a
qofar gida ya zauna yana shan iskar damina, yana tsawata
wa yara da ke wasa idan sun dauko niqa don kada su
6arar da garin abinci.
.
Wani lkcn kuma idan baya jin kasala a jikin shi sai ya
dauki qaramar fatanya ya zagaya bayan gida ya nome
ciyawar jikin bango, ko kuma ya fita bayan gari ya tsinko
rama a wata gonar shi ta kusa da gida da kuma ciyawar
akwaki. Koda ace irin wannan aikin ya fito yi ya bar gida,
to baya wuce qarfe goma xuwa sha daya.
.
Mai unguwa Mutawakkilu shi ne kakan Amir wanda ya
haifi baban shi. Mahaifin Amir ya rasu ne a shekarar data
gabata. Kuma duk a cikin 'ya'yan da mahaifin Amir ya
bari a duniya, wannan tsohon kakan nasu yafi son Amir.
Domin kuwa tun Amir yana qarami idan aka xo dashi sai
tsohon ya kama hannun shi su riqa yawo a cikin qauyen.
Idan kuwa zasu koma ya sha ya dauki toron agwagwa ya
ba mahaifiyar Amir ya ce tayi wa jikan shi kiwo.
.
Har ynx da Amir ya girma ya zama saurayi, idan Malam
Mutawakkilu ya je Zariya gidan dan shi domin ya ga
jikokin shi, da zarar ya isa zai fara tambayar inda Amir
yake. To amma kuma shi Amir bai cika damuwa da
wadannan 'yan uwa nasu dake a qauye ba, kuma tun
sanda ya girma ya kai matsayin da ya kamata ace yana
xuwa xiyara, baya son xuwa.
.
Amma kuma yau kwatsam gashi yaxo!!!
.
A dai dai lkcn da dan aca6an ya shigo dashi cikin qauyen,
ya sauke shi a qofar gidan mai unguwa, a lkcn ne kuma
Malam Mutawakkilu ya dawo daga bayan gari dauke da
ciyawa da kuma qaramar fatanya. Tun daga lkcn da Mai
unguwa ya fahimci Amir ne dan aca6a ya dauko, sai ya
qaro sauri domin ya xo wajen, fuskar shi cike da fara'a.
.
Domin kuwa tsoho ne mai son wasa da dariya!!
.
Mai unguwa ya tarbi jikan shi Amir a lkcn da Amir din ya
baiwa dan aca6a kudin shi, baya ya sauka ya gyara zaman
qaramar jakar da ya goya a baya ta samari 'yan birni,
wannan karon ma Amir yana sanye da qananan kayan
daya saba dasu, farin wando da baqin takalmi sai kuma
riga kalar hanta.
.
.
A wannan karon ma farin wando ne da baqin takalmi sai
kuma riga kalar hanta.
.
"Amir yau kai ne a garin kamar daga sama haka....."
.
Mai unguwa ya fara tambayar shi cike da murna. Amir ya
ce.
.
"ni ne yau ba zato ba tsammani Mai unguwa."
.
"sannu da xuwa Amir."
.
Mai unguwa ya jagorance shi.
.
"zo mu shiga cikin gida mana, ai yau ne zaka sha aikin
cefane, dama amaren naka sun wanke tukwane kamar
sun san zaka xo..."
.
Amir ya bi shi a baya yana murmushi har suka shiga gida.
Matan Mai unguwa biyu, wasu tsofaffi ne dake zaune a
tsakar gida suna bakacen dawa wacce qwari suka shiga
cikin buhu suka lalata, suka dago kai da suka ji shigowar
Mai unguwa da jikansu dan saurayi Amir daga birni.
.
Mai unguwa ya ce dasu.
.
"ga sabon miji naxo maku dashi, kowacce ta tashi ta dora
tukunyar farfesu."
.
Tsofaffin suka fara yiwa Amir ba'a suna cewa.
.
"Ai mu tuni mun yi fushi....wane aure ne ba xuwa ba
saqo?"
.
Amir ya gaishe su sannan ya bar indasuke don kada su
6ata mashi kwalliya da qaiqayin dawa. Tsakar gidan yana
da fadi sosai domin kuwa akwai dakuna fiye da goma sha
uku, kuma yawancin su duk soraye ne, dakunan matan
'ya'yan mai unguwa, wato surukansa da suke a gida daya.
.
Jin kamar ana yiwa baqo sannu, sai matan suka fara
firfitowa daga sassan da suke a can lunguna suna leqowa
suna ganin Amir. Wasu a cikin su sun san shi, domin suna
xuwa gidan dan uwan mijinsu da ke a Zariya, wato
marigayi mahaifin Amir, wanda shi kadai ne wanda ya
tashi ya koma birni da zama tun yana matashi har girman
shi da manyantakar shi da kuma rasuwar shi, har kuma
gashi bayan bashi a raye 'ya'yanshi sun yi hankali suna
xuwa ana gaisawa dasu; tunda ga Amir yau yaxo koda
yake basu san abin da ya kawo shi ba.
.
Mai unguwa ya ja Amir suka nufi dakin shi dake fuskantar
wani garken tumaki. Da shigar su bayan sun gaisa sai mai
unguwa ya fara tambayar Amir halin da ake ciki a birni,
da yake mutum ne mai son hira. Amir ya fara sanar dashi
abubuwan dake faruwa tun daga matsalar wutar lantarki
xuwa tsadar kudin makaranta da sauran qananun
matsaloli da ba a rasa ba da suke fuskanta yau da kullum.
.
Daga nan sai Mai unguwa ya fara sanar da Amir yadda
suke jin dadin tasu rayuwar a qauye. Idan aka dauke
rashin hanyoyi masu kyau daga wani gari xuwa wani, sai
kuma tsadar takin zamani wanda ke kawowa manoma
cikas a sha'anin gonakin su.
.
Suna cikin hirar ne sai daya daga cikin matan Mai
unguwa, kakannin Amir, ta shigo da abinci a kwano, tayi
sallama ta miqa mashi kwanon. Ya amsa ya ce da ita cikin
wasa.
.
"kin riga su kenan, kin amshe mijin basu sani ba."
.
Tsohuwar tayi dariya ta ce.
.
"Ai dama can ni ce a gaban su, ni ce amarya 'yar lele."
.
Amir da Mai unguwa suka yi dariya. Bayan tsohuwar ta
tafi sai Mai unguwa ya ce da Amir.
.
"ku haka kuke so ku riqa rayuwar ku Amir, ace ku girma
har ku kai munzalin zama manyan mutane magidanta
amma ba za ku yi aure ba?"
.
Amir ya ce da Mai unguwa.
.
"Haba, nawa nake da za a ce har na girma ban yi aure ba?
Ka san fa mu a can birni gsky zai yi wahala kaga mutum
ya yi aure bai samu qwaqqwarar madogara ba. Sai
mutum ya gama karatu ya samu aikin yi ya nemi muhalli
sannan zai fara tunanin neman abokiyar zama."
.
Mai unguwa ya ce dashi.
.
"mu kuwa a nan ba ruwan mu, da zarar yaro ya kai
munzalin da zai iya noma abincin da zai ci shi da iyalin
shi, sai a yi mashi aure. Ynx kaga tsararrakin ka dake a
nan, jikokin mu, wani a halin ynx yana da 'ya'ya shida da
mata biyu wasu mata uku.
.
Amir ya ce.
.
Ta6!! Gsky suna qoqari, koda yake akwai banbancin
tsadar rayuwa. Kaga ku a nan babu ruwan mutum da
wahalar neman wurin zama, kuna da filaye a cikin sauqi
da zaku gina gida ku zauna. Amma mu ynx a can birni ko
daki daya ka ce zaka kama haya ka zauna wahala ne in ba
kana da aikin yi ba. Kuma kaga ku a nan ku ke noma abin
da zaku ci har ku sayar ku samu rarar kudin da zaku
toshe wasu matsalolin. Amma mu a can duk abin da
mutum zai ci sai dai ya saya, kaga kuwa ai mun fi ku
tsadar rayuwa, dole ne mutum ya shirya sosai kafin ya
fara tunanin yin aure."
.
Mai unguwa ya ce.
.
"Haka ne Amir, amma wani lkcn kuna dorawa kan ku
qarya idan zaku yi aure, shi yasa kuke shan wahala. Sai
kaga mutum ya dorawa kan shi aikin sayen akwatuna da
kuma kaya masu tsada. To amma mu a nan ba ruwan mu
da wannan dawainiyar, wasu ma a kwalla suke xuba kaya
kuma zaka ga iyayen yarinyar sun amsa cikin farin ciki da
gdy. Akwai auren da ake baiwa mutum sadaka ba tare da
ya kashe ko kwabo ba, sai dai kudin sadaki kawai, wanda
basu da yawa, bai wuce ace ka bayar da dubu daya ba,
duk sauran tarkace na al'ada an yafe maka, sai dai kaga
amarya kawai a dakin ka...."
.
Tun kafin mai unguwa ya kai qarshe sai Amir ya fashe da
dariya har da qyaqyatawa.
.
"Abin ya baka dariya ne kuma Amir?"
.
Amir ya saurara ya ce.
.
"haba Mai unguwa, ai naji abin ne kamar tatsuniya. Wane
irin aure ne wannan sai ka ce mutum zai auri kaza ba
mutum ba? Mu ynx a can birni wa zai baka aure sadaka?
.
.
>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 9
.
.
Wannan sai ka ce mutum zai auri kaza ba mutum ba? Mu
ynx a can birni wa zai baka aure sadaka? Gsky ko ana yi ni
dai to ban ta6a gani ba."
.
Mai unguwa ya ce.
.
"kaga kuwa ynx haka maganar nan da muke yi ni da kai,
akwai wani abokina a wani qauye nan gaba kadan da
namu, saura kwana uku ya aurar da wata yarinyar shi
mai suna Sadiya, kuma sadakar ta zai bayar. Har ynx bata
san wanda za a bata ba, sai ranar daurin auren wanda
rabon shi ya ratsa to shi za a bata. Kawai sadaki za a nema
shi kuma ya je ya gyara daki a gida, kuma ba wasu kudi
mai yawa za a nema daga gare shi matsayin sadaki, ko a
nan take sai mutum ya ciro ya bayar a daura auren.".
.
Amir ya dubi kakan shi cikin mamaki.
.
"To amma kuma su 'yan matan da ake yiwa irin wannan
auren suna amincewa da mazajen da ake basu haka
kawai babu soyayya? Basu ta6a ganin mutum ba a rana
daya ya zama mijin su?"
.
Mai unguwa ya ce da shi.
.
"mu yaranmu suna bin umarnin mu, basu qetare duk
wani abu da muka shimfida masu. Kune ku ka san wata
soyayya ku da ku ke zaune a birni, dole sai abin da kuke
so sannan iyayen ku zasu amince dashi. Ko suna so ko
basu so. To amma mu yaran mu basu damu da wannan
ba, suna jiran iyayen su ne su za6ar masu abokan zama
ko abokiyar zama, kuma babu wanda ya ta6a butsurewa
ya ce shi bai amince ba."
.
Ganin hirar zata yi tsawo Amir bai duba abincin da matar
Mai unguwa ta kawo mashi ba, sai ya bude kwanon ya
iske shinkafa ce da wake dafa-duka. Ya dauki cokali ya
diba ya kai bakin shi sannan ya ce da kakan shi.
.
"ko ina akwai al'adun da suka saba dasu, amma mu a can
gsky ba kowacce budurwa zata amince da wannan auren
naku ba."
.
Mai unguwa ya 6alli goro ya fara taunawa, ya ce.
.
"Kuma in kana tsammanin kamar don yaranmu basu
waye bane yasa suke amincewa, to abin ba haka yake ba.
Ita wannan Sadiyar da nake baka labari ita ma a garin ku
ta girma wajen wata qanwar mahaifin ta, kuma tayi
karatu sosai. Ynx ne da lkcn auren ta yayi mahaifinta ya
aika aka dawo da ita domin ya fi son tayi aure a gida.
Kuma sadaka zai bayar da ita, dole ne kuma ta amince
tun da dai haka iyayenta suka so."
.
Amir ya ce da kakan shi.
.
"bata san wanda zata aura ba, kuma saura kwana uku a
daura mata auren? To yaya ake yi kuwa wajen za6ar
mijin, mahaifin ta ne zai ce ga wanda zai ba, ko kuwa sai
ya yi shawara da 'yan uwan shi sannan sai su fitar da
mutum daya wanda suka ga yafi dacewa?"
.
Mai unguwa ya ce da Amir.
.
"duk ba yadda ba a yi, wasu mahaifin su ne ke cewa ga
wanda yake so ya ba 'yar shi, wasu kuma 'yan uwa ne ke
kawo nasu 'ya'yan su ce suna bara a basu. Ynx ita wannan
Sadiya da za a daurawa aure kwana uku, akwai mutane
da yawa wadanda suke son a basu. Ko kai ma ynx da zan
ce ina yiwa jika na bara, idan da rabo sai kaga an bamu."
.
Amir ya sake diban abincin ya kai bakin sa, sannan ya ce.
.
"Abin yana bani mamaki gsky."
.
Mai unguwa ya yi mashi dariya ya ce.
.
"idan kuma kana so sai in kai qoqon barana, in ce ina
yiwa jika na bara..
.
.
**~**
.
.
Qauyen Turunkawa ya yi cikar kwari da mahalarta daurin
aure, da yawan su sun yi dandazo ne a kofar gidan Mai
unguwar wato Mallam Kalla mahaifin Sadiya kuma
abokin Mallam Mutawakkilu kakan Amir mai unguwar
Gidan rijiya.
.
Daurin auren ya tara mutane masu yawa kamar yadda ita
ma Sadiyar take da manema masu yawa, akwai mutane
da yawa wadanda suka miqo qoqon barar su ga 'yan
uwan Malam Kalla don neman iri, wasu kuma kai tsaye
suka tura qoqon su ga Mallam Kalla tun kafin wannan
rana ta xo. To amma kuma wadanda Mallam Kalla yafi
mayar da hankali akan su mafi akasari yaran su ne na
gida 'ya'yan qannen shi, wadanda zasu kai su biyar kuma
kowa yana sa ran shi zai yi nasara.
.
Mutane suna ta shige da fice daga cikin gida xuwa waje, a
yayin da mata ke ta shewa musammam dangin Malam
Kalla, amma kuma 6angaren Sadiya da kuma mahaifiyar
ta, su suna daki ne a zaune suna jiran tsammanin wanda
zai zama mijin Sadiya.
.
Duk wanda ya shigo cikin dakin yaga Sadiya ya san cewar
ita ce amarya, tana zaune tayi shiru tana tunani, tayi
kwalliya da kayan atamfa masu kyau ruwan ganye
wadanda suka dace da kalar fatar ta. Sadiya matsaikaiciya
ce wacce ke da wadattaciyar fuska mai matsakaitan
kumatu dake lotsawa idan tayi murmushi. Baqin gashin
ta da aka kitse shi sirara ya xubo gadon bayan ta yana
sheqi da daukar idanu, sai kuma baqin tozalin da ta zizara
a fararen idanunta.
.
Kunyarta da natsuwarta sun yi dai dai da yanayin jikin ta,
da kuma sanyin muryarta. A yadda take zaune babu
komai a fuskarta. Babu alamar fushi ko damuwa bisa
kyakkyawar fuskar ta. Wanda duk yaga Sadiya zai sake
kallon ta sbd tsantsar kyawun ta.
.
Tayi shiru ne tana tunanin qawayen ta da ta baro a Zariya
wadanda duk cikin su babu wacce take da labarin
wannan aure da za a yiwa Sadiya.
.
Ita kan ta abin ya xo mata a bazata, don kuwa bata ta6a
tsammanin zata yi aure a dai dai wannan lkc ba, kuma ko
ba don haka ba Sadiya tana jin kunyar ta gayyaci
qawayenta 'yan birni su xo qauyen su su ga irin wannan
auren da za a yi mata.
.
.
Lp=10
>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 10
.
.
Sadiya tare da mahaifiyarta suna zaune a cikin dakin sai
suka ji kamar hayaniya ta kaure a tsakar gidan. Ana sa-
insa, qanin Mallam kalla Malam Buba yana tsaye a tsakar
gida yana fada yana cewa.
.
"Matuqar ba za a ba dana ba to sai dai a ba wani can a
waje, amma ba dai wani ba a nan gidan."
.
Wata tsohuwa kuma ita ma qanwar Mallam Kalla mai
suna Haire, wacce ita ta sha nono bayan Mallam Kalla ya
saki ta ce.
.
"To ai kuwa sai dai in wajen za a kaita, amma in dai ba za
a ba dana Amadu auren Sadiya ba, to ba a isa a ba wani a
cikin gidan nan ba, tunda abin son kai ne."
.
Mata 'yan biki suka yi cirko-cirko suna kallon manya suna
fada akan 'ya'yan su. Mallam Kalla ya shigo gidan a fusace
sanye da qatuwar malum-malum da rawani, ran shi a
6ace yana cewa 'yan uwan shi dake sa'in-sa a cikin gidan.
.
"Tunda dai ku ba zaku hada kanku ba, ba zaku hada kai
mu taru mu rufawa junan mu asiri ba, to zan je in bada
auren Sadiya ga duk wanda naga dama a waje tun da
haka ku ke so."
.
Haire ta ce dashi a fusace.
.
"Amma idan za a fadi gsky sbd Allah Yaya waya fara yi
maka magana yana neman iri?tun yaushe muka yi
maganar nan da kai kuma ka amsa min za a ba Amadu
yarinyar nan?"
.
Buba ya ce.
.
"kada ki fadi wannan magana Haire. Tun yarinyar nan
tana qarama nace ina yi wa Danladi riqon ta. Sai ynx
kuma da rana taxo za ki ce ga zance ga magana?"
.
Malam Kalla ya ce dasu.
.
"ba zaku mayar da ni mutumin banza ba, babu wanda
zan ba a cikin ku tunda dai ku ba zaku san kun girma ba.
Daya ba zai yi ma daya uxuri ba. To babu wanda za a
baiwa a cikin 'ya'yan naku, na fasa ma ajiyeta a gida, can
zan bayar da ita a cikin 'ya'yan abokaina, kowa ya huta
tunda haka ne."
.
Mallam Kalla ya ja shakwarar sa ya yi waje a fusace ya
koma zaure inda dattawa ke zazzaune sun kasa kwandon
goro da kuma tire, suna jiran a fitar da wanda za a ba
auren, a ba Liman izinin ya fara addu'o'in daurin aure.
.
Da shigar shi cikin zauren sai ya kira abokin shi Malam
Mutawakkilu daje cikin dattawan zauren. Ya taso suka
ke6e gefe guda a kusa da zauren. Malam Kalla ya ce
.
"Abin da nake so da kai Malam Mutawakkilu, ka za6i
wanda duk kake son a ba wannan yarinya daga 6angaren
ka."
.
Mai unguwa ya tambaye shi.
.
"Ya aka yi ne kai da 'yan uwan naka?"
.
Mallam Kalla ya ce da shi.
.
"Babu lkcn tsayawa yin dogon bayani ynx, kaga mun tara
mutane suna jira a waje, ka za6i wanda ka ke so mu ba
yarinyar nan na baka dama."
.
Mai unguwa ya yi tunani sannan ya ce.
.
"to ai duk yaran namu ne na cikin gida sun gama rufe
qofa, duk sun cika muta hudu-hudu. Ynx wa zamu ba
wannan aure?"
.
Mallam Kalla ya ce.
.
"Ko a cikin jikokin ka ko kuma yaran 'yan uwa wanda dai
ka yaba da hankalin shi, wanda zai riqe ta da mutunci."
.
Mai unguwa Mutawakkilu ya ce.
.
"To akwai wani jika na da ya xo daga birni, sunan shi
Amir, in haka ne sai a bashi, kaga tunda dama a can yake
zaune sai ya tafi da matar shi bayan an gama biki."
.
Mahaifin Sadiya ya ce.
.
"An bashi."
.
Daga nan suka koma zauren daurin aure. Mallam Kalla ya
ce wa Liman.
.
"Na ba Amir jikan abokina Mallam Mutawakkilu auren 'ya
ta Sadiya a bisa sadaki naira dubu hudu."
.
Mai unguwa Mutawakkilu ya yi mashi gdy, sannan ya ciro
kudi ya ajiye a gaban goro. Dattawa suka sa albarka a
wannan aure, Liman ya fara shirye-shiryen addu'a.
.
Minti biyar bayan haka Sadiya da danginta suna zaune a
daki, sai suka ji wani maroqi mai doguwar murya yana
cewa.
.
"Jama'a ku ji, kuma ku shaida. Malam Kalla mahaifin
Sadiya ya ba Amir jikan Mutawakkilu auren 'yarshi
Sadiya. Sbd haka Allah Yasa albarka a wannan aure, kuma
shaidanin da zai lalata wannan aure Allah Ya kawar dashi.
.
Mutane suka fara hayaniya suna tambayar wane ne kuma
Amir? Domin kuwa babu wanda ya san shi. Sadiya ta yi
ajiyar xuciya sannan ta fara addu'a a xuciyar ta.....Allah Ya
sa alheri a wannan

Please Login or Register in order to submit comment