Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koma gida bayan sun gama darasi. Suna
cikin tafiya ita da qawarta Rahma wacce suke xuwa
makaranta tare a kullum, kuma suke fadawa junan su
sirrin dake tattare dasu, sai Sadiya ta cewa Rahma.
.
"ban baki labarin wani saurayi ba dazun da muka hadu a
labirari naje karatu."
.
Rahma ta tambaye ta.
.
"Wane saurayi?"
.
Sadiya ta ce da ita.
.
"wani saurayi kawai da gani na ya kama kallo na, ya xo ya
zauna a inda nake karatu ya dame ni. Ba naga ba zai bar
ni in yi karatun ba sai tashi na fice, kawai sai mutumin
nan ya biyo ni wai ya ganni yana so na waye-waye....?"
.
Rahma ta sake tambayar ta.
.
"to ke kuma me kika ce dashi?
.
Sadiya ta ce.
.
"kawai ce mashi nayi ya yi haquri ynx bani da tym din
(luv), na samu dai na lalla6a shi, shi yake tabbatar mani
wai ba zai i gaba da sona, har sai ya samu nasarar shawo
kai na."
.
Rahma ta ce.
.
Me yasa to ba zaki tausaya ma shi ki so shi ba Sadiya?"
.
Ta yi murmushi ta ce da qawarta.
.
"haba Rahma, ynx ke har za ki iya bani shawara kan in yi
soyayya a daidai wannan lkcn? Kada ki mance da labarin
da na baki ko wata biyu ba yi ba aka daura mani aure da
wani saurayi, kuma sadaka aka ba shi ni. Amma saurayin
nan sbd wulaqanci, tun ma kafin ya ganni ya ce baya so
na ya gudu ya ba ni. Kina tsammanin bayan wulaqancin
da wannan saurayin ya yi min ba da dadewa ba, har zan
mance in amince in sake yin soyayya da wani? A dalilin
wulaqancin da wannan saurayin ya yi min, nayi alqawarin
ba zan sake yin soyayya da kowa ba, har in mutu ba zan
qara son wani saurayi a duniya ba."
.
Rahma ta ce da ita.
.
"bai kamata laifin wani ya shafi wani ba Sadiya, domin
kuwa shi wancan saurayin da ya yi maki wulaqancin ya ce
baya son ki babu abin da ya hada shi da wannan saurayin
da ya gan ki ynx a makaranta ya ce yana son ki. Bai san
cewar akwai wani saurayi da ya ta6a yi maki wulaqanci
ba, don haka bai kamata ki qi amincewa da soyayyar shi
ba. Ya kamata ki ji tausayin shi ki so shi."
.
Sadiya ta ce da qawar ta.
.
"gsky ba zan iya ba Rahma, tunda dai na sanar dashi gsky
to na fita haqqin shi, saura kuma ya rage nashi in ya ga
zai rufawa kan shi asiri ya cire ni a xuciyar shi, domin
kuwa ba zan ta6a son shi ba."
.
Rahma ta yi dariya ta ce.
.
"Har na ji ya bani tausayi duk da ban ta6a ganin shi ba."
.
Sadiya ta ce.
.
"Lkcn da na amince da soyayya mijina da ya gudu ya bar
ni duk da ban ta6a ganin shi ba, ni ma haka na zama abar
tausayi. Don haka ba laifina ba ne, laifin Amir ne da ya
wulaqanta ni, shi yasa ba zan sake amincewa da soyayyar
kowa ba har tsawon rayuwa ta."
.
Qawayen biyu suka tsallaka titi sannan suka dauki hanyar
layin su suna tafiya suna hira.
.
.
**~**
.
.
Lkcn da abokan Amir suka dawo da yamma sai suka
same shi a kwance shi kadai a cikin duhu a daki ya yi
shiru yana tunani, basu saba ganin Amir a cikin irin
wannan hali ba.
.
Mustafa ya zauna a kusa dashi a bakin katifa.
.
"Amir baka da lfy ne, amma ba ka yi mana waya mun xo
mun kai ka asibiti ba?"
.
Amir ya ce dasu.
.
"Baku da maganin rashin lfyr da ta same ni Mustafa, duk
duniya babu wanda zai iya bani wannan magani sai
wacce ta zama sanadiyyar fadawa ta cikin wannan
gagarumar cuta."
.
Haidar ya yi saurin tambayar shi.
.
"me kake son fadi mana Amir?"
.
.
Lp=16
>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 16
.
.
"Me kake son fadi mana ne Amir?"
.
Amir ya tashi ya zauna sannan ya ce da su cikin tsananin
nadama.
.
"Yau soyayyar gsky ta kama ni. Naga wata yarinya a
makarantar nan wacce kibiyar son ta ta kama ni, na
kamu da ciwon son ta a cikin qanqanin lkc. To amma
kuma cikin rashin sa'a da na sanar da ita, bata bani goyon
baya ba."
.
Mustafa ya dafe kai cikin mamaki suka dubi juna shi da
Haidar. Tunda suke basu ta6a ganin Amir ya nunawa wata
budurwa irin wannan so na gsky ba. Babu shakka wannan
wata yarinya ce ta musamman ta samu a cikin al'umma,
wannan kuma wace ce? Da gaske Amir yake son ta? Shin
wannan budurwa a ina take su je su gan ta? Mustafa ya
tambaye shi.
.
"Amir a wanne sashi wannan budurwa take mu je mu
gan ta?"
.
Amir ya yi ajiyar xuciya ya share xufa ya ce dasu.
.
"ban san ko a wane sashi wannan budurwa take ba ban
ta6a ganin ta a wannan makarantar ba sai yau. Amma
kuma nayi alqawarin komai wahala komai tsanani sai na
bi ta duk inda take na ci gaba da son ta. Koda kuwa hakan
na nufin in je garinsu in sanar da iyayenta. Ina sa ran in
Allah Ya yarda wannan yarinya ita ce mata ta. Ba zan ta6a
daina son ta ba sai na cim ma buti na koda kuwa zan rasa
raina ne akan son ta."
.
Haidar ya ce dashi.
.
"kai fa malamin soyayya ne Amir. Ka dade sanin illar
rashin sa'ar soyayya. In har mace ta nuna maka rashin so
tun da farko za ka sha wahala kafin ka samu nasarar juyo
da hankalin ta har ta dawo ta nuna maka soyayya. Anya
kuwa zaka iya jure wannan wahalar bayan duk nasarorin
da ka saba samu a baya?"
.
Amir ya tabbatar mashi
.
"Akwai soyayyar da ke da qima da matsayi, akwai kuma
soyayya wacce bata da qima. Duk lkcn da masoyi zai fara
neman sa'a a soyayya, ya kamata ya san ko akan wacce
soyayya zai yi gwagwarmayar. Da ace wata mace ce na
gani wacce qimarta da matsayinta basu kai in yi
gwagwarmaya akan son ta ba babu abin da zai sa tun
farko in damu kaina. Don kuwa akwai 'yanmata da yawa
a ko'ina a duniya.
.
To amma ita wannan da nake baku labari ta cancanta duk
wani namiji ya rude akan sonta, kuma matsayinta da
qimarta ya kai ayi gwagwarmaya sosai akan son ta. Irin
'yanmatan nan ne da ba a cika samun irin su a ko'ina
bane. Tunda dai ni ban ta6a ganin irin ta ba. Wannan
yarinya zara ce mai tsananin haske a cikin taurari."
.
Mustafa ya yi murmushi ya ce.
.
"Na amince da gaske kake yi Amir. Allah Ya sa ka dace ka
sami sa'ar shawo kan ta, muna taya ka farin ciki. Kuma
wannan ita ce matar ka."
.
Amir ya ji farin cikin goyon bayan su ya lulli6e shi.
.
"na gode sosai Mustafa, ku ci gaba da taya ni da addu'a
domin kuwa xuciyata tayi nisa matuqa akan son ta. Zan ci
gaba da son ta har qarshen rayuwata, kuma zan jure duk
wahalar da zan fuskanta a wajen nemo soyayyar ta."
.
.
MASU BIBIYA TA CIKIN WANNAN LITTAFI MAI SUNA SO
BAYAN RAI (LABARIN HADARIN SOYAYYA) INA SON KU
KALLI YADDA AMIR YA SADAUKAR DA XUCIYARSA
KACOKAN GA SADIYA, KU RIQE HAKAN A XUCIYARKU SBD
NAN BA DA DADEWA BA ZA A DANGANTA MATSAYIN
AMIR DA WANI WAJEN QWARIN SOYAYYAR SADIYA. A
LKCN KU NE ZAKU YI ALQALANCI.
.
.
ALBISHIRIN KU!!
TARE DA HAKA KUMA INA SON DUK WANDA YA NAZARCI
WANNAN SHAFIN YA AJIYE 'COMMENT' KO 'LIKE'. YAU
TAMKAR ZAMU YI HIRA DAKU NE MATSAWAR WANNAN
RANA, SBD ZAN KAWO SHAFUKA A QALLA HUDU KO FIYE,
BANA SON IN TA POSTING BA TARE DA NA SAN AN
KARANTA KO BA A KARANTA BA.
NAKU
Iliyas Is'hak Gundutse
(Madugun Taska)
.
.
.
LITTAFI NA BIYU
.
.
.
Kwana uku kenan tun sa'ar da Amir ya fara ganin Sadiya
har ynx bai sake ganin ta ba a makarantar. Amir ya koma
labirari ya zauna tsawon lkc yana tsammanin sake
ganinta amma kuma har akayi kwana uku bata sake
dawowa labirari tayi karatu ba ballantana ya sake ganin
ta.
.
Idan Amir ya gaji da zama a labirari sai ya kifa kan shi
akan teburi yayi shiru yana tunaninta idan ya fito kuma
cikin damuwa sai ya dara tambayar dalibai ko sun san
wata budurwa yayi ta kwatanta kamannin Sadiya, don
kuwa har suka rabu bai san koda sunan ta ba.
.
Duk da Amir bai sake ganin Sadiya ba, amma kullum da
ita yake kwana yana tashi a xuciyar shi. Yana tuno lkcn da
ta zauna tana karatu ita kadai sanye da baqaqen kayanta.
Kyawawan idanunta. Amir yana yawan tuno lkcn da ta
dago kai ta qura masa idanu ta ce da shi.
.
"Da za ka bar ni in yi karatu da na so."
.
A ina zai sake ganin wannan kyakkyawar budurwa
ma'abociyar kwantar da hankalin duk wani namiji da ya
saurari kalamanta? A ina zai sake ganin wannan
nutsttsiyar budurwa ma'abociyar karatu wacce bata son
mutane su xo su dame ta?
.
A cikin wadannan kwanakin Amir ya fita daga kamannin
shi, ya fara daina cin abinci sannan kuma ya daina karatu.
Amir ya daina shiga cikin abokan shi kamar yadda suka
saba zama suyi hira suna dararraku. Amir ya fi son ya
zauna shi kadai a halin ynx yana tunanin masoyiyar shi
wacce yake nema ruwa a jallo. Amma bai san inda zai je
ya gan ta ba.
.
Da farko abokan shi su Mustafa sun yi tsammanin Amir
zai haqura ya mance da wannan budurwa da ya gani,
tunda dai an neme ta amma ba a ganta ba.
.
.
Lp=17>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 17
.
.
Da farko abokan Amir su Mustafa da Haidar sun yi
tsammanin Amir zai haqura ya mance da wannan
budurwa da ya gani, tunda an neme ta ko sama ko qasa
ba a san wacce daliba ba ce a makarantar to amma ganin
yadda Amir ya rikice a dan qanqanin lkcm sai suka hada
kai domin taimaka mashi a gano inda take don ya ji
sauqi.
.
Shi kadai ya ta6a ganin ta, sannan kuma shi kadai ya san
kamannin ta, to amma kodayaushe idan yana tunanin ta
ya kan fadiwa abokan shi kamannin ta.
.
Kyakkyawa ce mai matsakaicin tsawo da kuma
matsakaiciyar fuska, sannan kuma tana sanye da
baqaqen kaya dogaye...."
.
Sbd haka Amir tare da abokan shi su Mustafa sun duqufa
neman Sadiya a kowanne lungu dake makarantar.
.
Wace ce fara kyakkyawa mai matsakaicin tsawo da kuma
matsakaiciyar fuska a jami'ar Ahmadu Bello dake a
Zariya?
.
.
**~**
.
.
Lardinan Turunkawa da kuma Gidan rijiya dukkan su
suna a qarqashin wani dagaci ne dake a qauyen Maqera
wato Sarkin noma Alh. Mamuda. Maqera wani faffadan
gari ne dake zagaye da rafuka da fadamu inda maharba
ke ke xuwa a kodayaushe suyi farautar tsuntsaye,
masunta kuma ke xuwa su yi su su kama kifaye suna
kaiwa garuruwan dake kusa dasu talla, wadansu kuma
soyawa suke yi a cikin gari mutane suyi dafifi suna saye.
.
Akwai zaratan matasa a qauyen maqera, wadanda in ba
lkcn damina ba ne suka damu tsofaffin garin wajen
wasannin qwallo a filayen dake a baqin qauyen inda wata
tsohuwar makarantar firamare take, da kuma wasu
gonaki da suke gyarawa duk lkcn da ruwa ya dauke
domin su samu qarin filayen qwallo.
.
Alh. Mamuda matashin dattijo ne dan kimanin shekaru
arba'in da biyar, wanda a qiyasin da ake yi duk shekara
yana noma hatsi kimanin tirela goma. Bayan nan kuma
yana da shanu da awaki a rigagen fulani, yana da motar
daukar kaya a kori-kura, sannan kuma yana da sabon
babur (Nanfang). Yana da mata uku, biyu tsofaffi daya
yarinya. Yana da 'ya'yan goma sha biyar, matar shi ta
farko tana da takwas ta biyun take da 'ya'ya biyar,
amaryar kuma take da 'ya'ya biyar.
.
Gidan Alh. Mamuda yafi kowanne gida qeruwa a cikin
qauyen domin kuwa a zagaye yake da kano babu rufin
laka, sannan kuma ko ina a jikin bangon gidan a shafe
yake da siminti babu inda mutum zai ga alamar tsakuwar
da aka rufe. Yana da faffadan falo wanda ke fuskantar
waje a falon ne ake shimfida tabarmi da kuma xube
mafitai na yin fifita. A nan talakawan qauyen ke zaunawa
bayan sun cire takalmansu a waje, sai su shigo cikin
ladabi su sanar dashi matsalolin dake tafe dasu, wadanda
suka hada da rigima tsakanin manoma da makiyaya,
matsalar ma'aurata miji da mata, ko fada da surikai rikici
akan amsar gona haya ko jingina, da kuma qananun
laifuka na gida wadanda ba sai an je birni an shiga caji
ofis ba.
.
Alh. Mamuda ya gaji wannan rawanin ne a wajen
mahaifin shi sarkin noma marigayi, sbd haka saratu biyu
yake riqe dasu, shi ne Sarkin noman lardinan dake a
wannan yankin nashi kuma shi ne dagacin garin maqera
da kewaye.
.
Alh. Mamuda yana da saurin fushi, kuma da yake ko bai
yi fushi ba idan mutum ya yi la'akari da jajayen idanun
shi da kuma baqar fuskar shi, to dole ne a ji tsoron shige
mashi. Yana son talakawa su riqa girmama shi, don kuwa
duk mutanen da yafi taimakawa a cikin mutanen shi to
irin wadanda suke xuwa ne su wuni a fadar shi suna
washe baki, suna yi mashi hira. Bayan ya sa an fito masu
da dambu ko dan gauda da mangyada, idan 'yan arziqin
suna kusa kafin su tafi sai yasa a gwada masu masara ko
dawa mudu uku a ba kowa ya ba kowa ya je gida a yi
masa tuwo.
.
Alh. Mamuda sarkin noma mutum ne mai budurwar
xuciya. Duk da ya fara manyanta a halin ynx, kuma ya na
da fadin rai a wajen talakawan qauyen, da zarar ya ga
kyakkyawar budurwa zai yi wahala ta wuce bai yi mata
magana ko wasa ba. Idan fulani suka shigo garin tallar
nono, a qofar gidan shi suke yin dafifi. Wani lkcn ya kan
sa su damo fura su shigo da ita cikin fada a rabawa
mutane, sannan su shiga da ita cikin gida su kaiwa iyalin
shi.
.
A halin ynx Alh. Mamuda yana zaune ne a qarqashin wata
bishiyar dorawa dake a qofar gidan shi. Tsawon lkc ya
qurawa hanyar shigowa garin idanu yana tsammanin
hango wani qanin shi da ya aika qauyen Gidan rijiya.
.
Da ya duba agogo sai ya ga aqalla Jafaru ya kai awa daya
da tafiya amma har ynx bai dawo ba, sai ya fara xullumin
wataqila bai samu damar ganin Malam Buba ba ne, qanin
Malam Kalla mai unguwar Gidan rijiya.
.
Akwai magana mai muhimmanci da Alh. Mamuda yake
son su tattauna shi da Malam Buba. Koda yake wannan
magana ce mai sauqi wacce bai yi tsammanin zai samu
wata matsala ba. Anya kuwa akwai wata yarinya da zai ce
yana so a duk fadin wannan yankin ya samu matsalar
rashin amicewar iyayen ta? Ba sai lallai yarinyar tana son
shi ba, maganar soyayya duk bata taso ba, ba sai lallai ya
je sun tattauna da ita ba, ko tana son shi ko bata son shi
in dai har Malam Buba qanin mahaifinta da kuma Malam
Kalla mahaifinta sun amince sun bashi auren ta, duk
sauran abubuwan da zasu biyo baya masu sauqi ne.
.
.
Lp=18
.
.
In dai har Malam Buba qanin mahaifin ta da Malam Kalla
mahaifinta sun amince sun bashi auren ta, to duk sauran
abubuwan da zasu biyo baya masu sauqi ne.
.
Alh. Mamuda ya fara jin labarin Sadiya ne a 'yan
kwanakin baya da suka wuce bayan an gama
ruguntsumin auren ta da wani saurayi da aka ce an bashi
ya ce baya son ta ya gudu ya bar ta. Ita kuma aka mayar
da ita birni wai zata ci gaba da karatu.
.
A cikin mutanen shi 'yan fada wani ya fara bashi wannan
labarin wannan yarinya, wacce ta girma a birni 'yar gidan
mai unguwa Kalla na Turunkawa.
.
"Ranka ya dade ai wato idan kaga yarinyar nan ba zaka
ta6a cewa 'yar gidan Kalla ba ce, duk inda ake neman
kyakkyawar mace in aka samu yarinyar nan to magana ta
qare. Amma suka ba wani yaro sadakar ta ya ce baya so.
Kai wannan yaro ya cika sakarci ranka ya dade."
.
Da Alh. Mamuda ya ji ana ta labarin wannan yarinya
Sadiya 'yar birni sai ya ji yana son ta, kuma in dai iyayen
wannan yarinya zasu bashi goyon baya to zai so su bashi
auren ta, nan da nan a yi maganar tunda dai zance ne na
kudi koma nawa ne zai kashe.
.
Da zarar ya sa an cika akori-kurar shi da buhun hatsi an
kai kasuwa zai gama hidimar, koda kuwa a cikin kwana
uku ne.
.
To amma dai ynx sai Malam Buba qanin mahaifin
yarinyar ya xo tukuna sannan zai san ko me zai faru akan
wannan lamari. Alh. Mamuda yana a zaune yana duban
hanya xuwa can sai ya hangi qyallin mashin din shi ya
shawo kwana, Jafaru ya goyo Malam Buba qanin Malam
Kalla. Sarkin noma ya yi murmushi kafin wani lkc sun
qaraso qofar gidan.
.
Alh. Mamuda Sarkin noma ya miqe a lkcn da Jafaru ya
kashe babur din ya suka sauko shi da Malam Buba.
.
"Sannun ku." ya ce dasu sau daya, nan da nan Malam
Buba ya amsa cikin ladabi.
.
"Sannu ran ka ya dade, barka da war haka."
.
Sarkin noma ya ce da Jafaru.
.
"ka je rijiyar bayan gida ka wanke min babur naga ya yi
qura, ina son zan fita dashi anjima."
.
Jafaru ya gungura babur din ya basu wuri. Sarkin noma
ya jagoranci Malam Buba suka shiga cikin falo, har xuwa
wannan lkcn Malam Buba bai san dalilin wannan kira da
'ranka ya dade' ya yi mashi ba. Bayan sun zauna sai
Malam Buba ya gaishe shi, amma bisa mamaki sai ya ga
Sarkin noma ya miqo mashi hannu, sun yi musabiha.
Tunda yake bai ta6a ganin Sarkin noma ya miqawa
talakansa hannu zasu gaisa ba.
.
Bayan Malam Buba ya natsu a zaune yana jiran ya ji
dalilin kiran da Alh. Mamuda ya sa aka yi masa,
musamman har da aikawa da babur a dauko shi. Sai ya ji
ya ce da shi.
.
"Dama na aika a xo da kai ne domin muyi wata magana
mai muhimmanci. Ba wani abu bane Malam Buba, akan
yarinyar nan ce 'yar wajen ku da aka ce an ba wani yaro
sadakar ta kwanakin baya ya ce baya son ta, to shi ne da
naji mutane suna ta maganar yarinyar cewar tana da
ladabi da biyayya, kuma an ce tana bin maganar manya,
sai naji ina da ra'ayi akan ta in babu matsala."
.
Malam Buba ya yi dariya ya ce.
.
"Ranka ya dade ai babu wata matsala, kuma naji dadin
wannan magana, na tabbatar shi ma mahaifin yarinyar
idan ya ji zai amince 100%, wannan ai abin arziqi ne Ran
ka ya dade."
.
Alh. Mamuda ya saki ran shi ya ce.
.
"To ni dai kam babu abin da zan ce sai dai in yi gdy dana
samu dama a wajen ku. Tunda magana a hannunku take
duk da ban ta6a ganin yarinyar ba, kuma ita ma bata san
ni ba, na san cewar in dai kun amshi wannan magana to
ba za a samu wata matsala ba, tun da ance yarinyar tana
jin maganar ku."
.
Mallam buba ya ce dashi.
.
"Ai mu tun a zamanin da ranka ya dade, gidanmu ya
samu asali wajen wannan, bamu ta6a haihuwar yaro yafi
qarfinmu ba. Ko wuta muka hada a rami muka ce su
shiga ba zasu ta6a yi mana musu ba, kome muka ce
muna so, su ma shi suke so. Sbd haka in dai kan wannan
yarinyar ne Sadiya to ka kwantar da hankalinka, kamar
ma ta zama matar ka."
.
Sarkin noma ya ce.
.
"Na gode sosai. Dama haka ake son gida ya kasance,
manya suna fadi a ji su, kuma ayi abin da suka ce suna
so."
.
Malam Buba ya ci gaba da murna yana tunanin wannan
abin arziqi daya same su babu zato ba tsammani. Ynx a
yadda yake da matsalar gonakin da zai noma, in har akayi
wannan aure ya san cewar gonar dai da zai yi aiki sai
wacce yake so, sai ta ishe shi. Sannan kuma a yadda suke
shan wahalar fitowa da hatsi daga gona xuwa gida idan
kaka tayi, ya san cewar in dai wannan aure ya tabbata to
babu shakka Alh. Mamuda zai sa motar shi ta je ta riqa
kwaso masu amfanin gonarsu kyauta.
.
Sarkin noma ya tambaye shi.
.
"to ynx Mal. Buba ya za a yi, naji an ce ita yarinyar ta sake
komawa birni, wai zata ci gaba da karatu? Ya kake jin za a
yi kuma tunda ga wannan magana tamu?"
.
Mallam Buba ya ce dashi.
.
"wannan karatu nata tsayawa dashi zata yi. Ni da kaina
zan je har can birnin in dawo da ita gida. Me ake da
karatun boko in mace ta samu miji? Dama mahaifin nata
ne ya matsa sai ta koma wajen qanwar tamu Haj. Uwani.
Amma ni dama can wannan karatun nata ba son shi nake
yi ba. Yarinya ya isa ace ta haihu uku amma tana gida
ynx.
.
.
Lp=19
>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 19
.
.
Kawai yarinya ta isa ta haihu uku amma a ce har ynx tana
gida.
.
Sarkin noma ya ce
.
"To ynx shi karatun wai ana samun aiki ne in an yi?"
.
Malam Buba ya ce.
.
"A ina fa suke samun aikin, ba gashi nan ba kullum muna
jin labarin suna xuwa yajin-aiki sbd rashin albashin kirki?
Abin da za a yi kenan, zan je in dawo da ita tunda ka nuna
kana son ta. Wannan magana ynx ita za a yi. Dama Allah
Ya qaddara matarka ce, shi yasa wancan taqadarin yaron
ya gudu ya ce baya son ta. Dama wani ai baya auren
matar wani."
.
Sarkin noma ya yi mashi gdy, ya tashi ya shiga cikin gida
ya sake fitowa. Malam Buba yana zaune yana jiran shi
sanye da kodaddiyar farar malum-malum. Sarkin noma
ya miqa mashi kudi a dunqule duk wazobiyoyi 'yan dubu
goma, ya ce da shi.
.
"ga wadannan ka yi kudin mota xuwa can birni ka dawo
da ita."
.
Malam Buba ya amshi kudin hannun shi na rawa, ya sa
hannu bibbiyu ya rufe su tamkar yana tsammanin zasu yi
fuffike su tashi sama. Ya yiwa Sarkin noma gdy, yana
neman fitar da aljihu daya qwaqqwara da ya kamata ya
adana kudin a ciki, domin kuwa a tsammanin shi duk
aljifan a huhhuje suke. Har suka yi bankwana shi da
Sarkin noma a lkcn da ya kira qanin shi Jafaru ya ce ya je
ya sake dauko babur ya mayar da Malam Buba gida,
kudin suna maqale ya hada su da babbar riga ya
rungume su kamar wanda ya tsinci jariri. Rabon shi da ya
riqe kudi a dunqule masu yawa irin wadannan tun bara
da wani dan maraqin shi ya kasa aka kira wani mahauci
ya xo ya raga mashi asara.
.
Da komawar Malam Buba gida ko hutawa bai yi ba ya
ruga fadamar dan uwan shi Malam Kalla ya sanar dashi
halin da ake ciki tun daga farko har qarshe. Nan take suka
yanke shawarar a cikin satin nan Buba zai je birni ya
dawo da Sadiya, domin a yi gaggawar yin zancen auren ta
da Sarkin noma wanda ya fito a halin ynx.
.
Su duka sun mance da labarin sabon karatun da ta fara a
Jami'a, to amma wa ke ta wani karatu? In dai 'yar zata
samu sa'ar shiga gidan Sarkin noma dagacin garin
Maqera da kewaye, in dai zai aureta, maganar digiri a
jami'a a kai shi bola.
.
.
**~**
.
.
Al'amarin soyayyar dake balbali a xuciyar Amir, kullum
abin sai qara ci gaba yake yi, bashi da wani tunani sai na
wannan masoyiya tashi wanda shi kan shi bai san a inda
take ba.
.
Abokan Amir sun fara jin tsoron wannan soyayya da ta
kama shi, suna kokonton mai yiwuwa aljana ya gani ya
rude akan son ta. Amir ya daina xuwa daukar darasi,
sannan kuma tuntuni ya daina karatu, sbd ko da a ce ya
bude littafin to ba zai ga komai ba a jikin littafin sai hoton
fuskar wannan kyakkyawar budurwa da ciwon son yake
ta faman nuqurqusar xuciyarsa.
.
Wata rana Amir yana cikin yawo a makaranta bai sani ba
har ya fito waje a bakin daya daga cikin manyan qofofin
shiga jami'ar, yana tunanin inda zai sake ganin yarinyar
da ta ajiye mashi hoton kyakkyawar fuskarta a cikin
xuciya. Kamar an ce ya dago kan shi sai ya hange su sun
tsayar da mota ita da wata qawarta, suna tsaye a bakin
titi.
.
Tana sanye da baqaqen kayanta da ya ganta dasu a
labirari a ranar farko da ya fara ganin ta. A wannan karon
ma tana rungume da dogayen litattafan ta na karatu,
iskar motocin dake wucewa ta kan titin tana daga
doguwar rigar ta da kuma gyalen ta mai shara-shara,
wanda yake bayyana hasken ta da annurin fuskarta. A
wannan karon dariya take yi suna hira da qawar tata.
.
Amir ya daga hannu yana qoqarin tsayar dasu a lkcn da
motar da suka tsayar ta ci burki a gaban su, yaron motar
ya bude qofar ya basu guri suka shiga ciki. Amir ya rugo
aguje yana tsayar da motar cikin daga murya, to amma
kuma hayaniyar dalibai wadanda suka yi dafifi a bakin
qofa, da kuma qarar motoci ya sa yaran motar bai ji ba.
.
Ya shiga ciki ya bugi motar, direban ya tuqa suka tafi.
Amir ya bi motar aguje kamar ran shi zai fita. Yayi saurin
tsayar da wani dan aca6a ya nuna mashi motar ya ce
yana son su cim mata kafin ta 6ace.
.
Tsirarin daliban da suka ga abin dake faruwa suka dubi
Amir cikin mamaki, lkcn da dan aca6an ya cilla dashi
aguje suka rufawa tsohuwar (Bus) din mai launin shudi
baya.
.
Sun yi tafiya a qalla tsawon minti biyu matar tana
kwarara gudu babur din bai samu nasarar cim mata ba,
xuwa can sai motar ta sa sigina alamar zata tsaya kenan a
daidai kan layin da Sadiya da qawarta Rahma za su shiga
cikin unguwar su.
.
Dan aca6an ya rage gudu tare da motar wacce ya manne
a bayanta tamkar zai dunguri banbar ta. Da motar ta
tsaya sai ya wuce ta ya tsaya a gabanta. Amir ya ciro
kudin shi ya bashi ya yi mashi gdy, sannan ya yi sauri ya
juyo ya dawo wajen da motar tayi fakin, a lkcn har Sadiya
ta fito saura Rahma dake a ciki, wacce take qoqarin
fitowa da yake a can gidan baya ta zauna.
.
KU HANZARTA YIN COMMENT DON IN SAN KUNA BIYE
ANJIMA KADAN ZAN CI GABA. WASU ZASU YI MAMAKIN
GANIN POST DINA DA YAWA YAU KASANCEWAR DOKA NE
YIN POSTING FIYE DA BIYU A TASKAR. NA ZARTA QA'IDA
NE SBD WASU DALILAI.
*AFUWAN*
.
.
Rahma ta fito a daidai lkcn da Amir ya qaraso bakin
motar, a lkcn ne kuma motar ta hau titi ta basu waje
aguje.
.
.
Lp=20
September 10 at 5:23 PM ยท "TASKAR GIDAN LI...
Rahma

Please Login or Register in order to submit comment