Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, sbd kawai mun nufe ka da
alheri. Aure abin alheri ne, koda ace baka son Sadiya, bai
kamata a ce kayi mata wannan wulaqancin ba, kamata ya
yi ka same muyi maslaha, mu warware matsalar cikin
sirri. Amma sai ka wulaqantamu Amir, ka aiko mana da
zage-zage, ko Sadiyar ma baka gani ba. Ka kamo hanya ka
dawo birni. To wannan Sadiyar ce tsohuwar matar ka, ita
ce wannan Sadiya kuma da kake mutuwar so a halin ynx,
kuma an yi mata miji ynx aure za a yi mata."
.
Amir ya ci gaba da kukan nadama.
.
"ynx daga nan ba zan koma makaranta ba, zan koma
qauye in samu kakannina su je su roqi su Baba domin su
dawo min da mata ta, in har ban auri Sadiya ba rayuwata
tana cikin hadari."
.
"Ynx da wane ido zaka sake komawa wajen kakan ka? Da
wane ido zaka je gidanmu wajen mahaifin ta? Da wane
ido zaka kalli Sadiya ka ce mata kai ne din farko da ka
guje ta?
.
.
Lp=26>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 26
.
.
Da wane ido zaka kalli Sadiya ka fadi mata cewar kai ne
Amir din farko da ya gije ta, baka son ka ga irin ta? Kada
ka koma qauye neman Sadiya domin kuwa zaka dorawa
kanka aiki ne babba wanda ba zaka ta6a samun nasara
ba. Na tabbatar idan ka je ynx, musamman a irin wannan
lkc da ake maganar auren ta, sai sun ci mutuncin ka,
kuma sai sun rama abin da ka yi masu."
.
Amir ya ce da ita.
.
"na dauki alqawarin zan koma in nemi afuwa a wajen su
koda kuwa zan rasa raina ne a wajen neman ta. Haqiqa
nayi kuskure a rayuwata, domin kuwa na kasance mutum
mai karya alqawari kuma bana mutunta mutane. Daga
ynx na dauki alqawarin ba zan sake yaudarar wani
mutum ba ko mace ko namiji. Wannan abu daya faru da
ni na san cewar alhakin mutane ne da yawa, musamman
'yanmatan dana zalunce su nayi masu alqawarin zan aure
su daga baya na gudu na bar su, kuma na tabbatar basu
yafe mani ba. Na yi nadama.....kaico da irin wannan
rayuwa tawa...."
.
Amir ya sake fashewa da kuka. Haj. Uwani ta ji hawaye ya
xubo mata, tayi sauri ta koma cikin gida tana al'ajabin
wannan abu da ya faru tsakanin Amir da Sadiya.
.
Mustafa da Haidar wadanda ke tsaye jikin su babu qwari
suka kama Amir suka shiga dashi cikin mota suna bashi
haquri. Ya ce dasu.
.
"na tabbatar rayuwata ta fada cikin hadari abokaina,
kuma zai yi wahala in fito daga cikin wannan bala'i dana
fada. Alama ce dake nuna yadda zan fuskanci wahala da
uquba wajen nemo soyayyar Sadiya. Ina son wannan abu
da ya faru da ni ya zamo darasi a wajen ku. Domin kuwa
tare da ku nake yin wadannan halaye marasa kyau, tare
daku muke yaudarar 'yanmata, kun ga abin da ya faru da
ni, sbd haka ku kiyaye, ku tuba tun kafin irin wannan ta
same ku."
.
Haidar ya ce.
.
"Har abada na daina qarya, wallahi ba zan sake yaudarar
wata yarinya ba."
.
Mustafa ya share hawaye ya ce.
.
"Ni kwata-kwata ma na daina soyayya a rayuwata, indai
haka soyayya take zamowa a qarshe, to ba zan sake yarda
so ya kama ni ba. Wannan ai bala'i ne.
.
.
LKCN DA NA XO NAN WURIN A TYPING HAWAYE KE
SARTU BISA KUMATUNA. BAN SANI BA ZAN DAINA DAGA
YNX KO KUMA HAR QARSHEN LABARIN HAKA ZAN
KASANCE? BAN SANI BA.
"ALLAH SARKI AMIR."
.
Mayaudaran samarin uku sun yi nadamar munanan
ayyukan da suka yi a baya na yaudarar 'yanmata, sbd sun
ga ishara da idanun su. Yarinyar da Amir ya gudu ya barta
tana kuka cikin 'yan uwanta, a gaban iyayen ta ynx kuma
sun hadu yana bin ta yana kuka cikin azabar son ta.
Mustafa ya yi gsky da ya ce wannan soyayya ta zama
bala'i ga rayuwar Amir.
.
Da komawarsu Amir ya hada kayansa a gurguje ya yi
bankwana da abokanshi suna kuka, suka yafewa juna. Ya
hau mota ya nufi qauyen Gidan rijiya inda ya ce ba zai
sake komawa ba.
.
KU CI GABA DA RIQE WANNAN SADAUKARWAR SOYAYYA
TA AMIR A CIKIN XUQATANKU, NAN GABA AKWAI WASA
QWAQWALWA.
.
.
Ga Amir dai ya tafi nemo soyayya, ga kuma matsaloli can
suna jiran shi da wahalhalun rayuwa maras iyaka.
.
.
.
**~**
.
.
Da yamma liqis Amir ya isa Gidan rijiya, garin kakan shi
Mai unguwa Mutawakkilu. Amir ya ji kunya da nadama
sun cunkushe a xuciyar shi, a lkcn da yake tafiya a qasa
xuwa cikin qauyen bayan ya sauka a mota a bakin titi,
yana sagale da 'yar jakar shi yana wasi-wasin abin da zai
biyo baya. Da kuma tunanin sake ganin rabin ran shi
Sadiya.
.
Amir ya shiga cikin quyen ya iske mutane a zazzaune suna
shaqatawa, dandalin matasa daban, na tsofaffi daban a
gefe. Amir yayi masu sallama. Wasu suka amsa wadanda
basu san shi ba, wadanda kuma suka gane shi,
musamman xuriyar gidan kakan shi mai unguwa bin shi
kawai suka yi da kallo suna mamakin abin da ya sake
dawo dashi wannan qauyen, bayan cin mutuncin da ya
yiwa mahaifin su Mai unguwa.
.
Amir ya wuce xuwa gida. Wasu matasa jikokin Mai
unguwa suka bi bayan shi a fusace cike da alwasin in har
sake dawowa yayi don ya yiwa tsohon rashin kunya, to
sai dai a kwashe shi, amma sai sun karairaya shi.
.
Dama a wancan lkcn sa'a ya ci basu a gida suna gona, da
suka dawo ne suka samu labarin rashin kunyar da ya
yiwa kakan su. Sun ciji yatsa, domin kuwa da suna nan da
sun nunawa Amir su tsagerun qauye ne idan shi tsageran
birni ne.
.
Amir ya shiga gidan yayi sallama. Da shigar shi ya samu
mata a waje suna aikace-aikace, wata matar mai unguwa
tana tankade garin tuwo, wata kuma ta dauko buhun
ciyawa zata zazzagewa awaki wadanda ke ta miqa wuya
cikin qosawa.
.
Da suka dago kai suka ga Amir, sai kowacce ta tsaya da
aikin da take yi suka qura mashi idanu cikin mamakin
sake ganin shi, matan biyu suka yi mashi magana. Wacce
ke tankade ta ce.
.
"Yau a gari in ji maqi baqo?"
.
Daya kuma ta ce.
.
"Yau 'yan birni ne suka tuna da mu?"
.
Amir ya gaishe su cikin ladabi har yana duqawa qasa suka
amsa, a wannan karon babu wasannin jika da kakan da
suka saba yi da Amir idan ya xo, ko idan suka je birni.
Basu san me ya sake dawo dashi ba ynx, sun dauka har
abada ba zai sake xuwa qauye ba, kamar yadda ya fadi
masu a ranar da aka 6ata mashi rai a wancan karon.
.
Amir ya qarisa qofar dakin kakan shi mai unguwa.
.
.
Lp=27
>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 27
.
.
Amir ya qarisa qofar dakin kakan shi mai unguwa
Mutawakkilu, ya same shi a zaune yana jiqa busasshiyar
rama ramar d'aura danni a cikin qwarya. Amir yayi mashi
sallama cikin ladabi. Mai unguwa ya amsa bayan ya dago
kai yaga Amir. Ya tsaya da jiqa ramar cikin mamaki da
kuma fushi a lkc daya, ya qurawa Amir idanu. Amir ya
tsuguna a gefe guda ya gaishe shi, tsohon ya amsa. Akwai
alamar ya matsu ya ji abin da ke tafe da wannan jika
nashi a wannan karon.
.
"Har ynx baka huce bane, shi ya sa ka sake dawowa ynx
kuma ka buge ni Amir?"
.
Amir ya ce da tsohon.
.
"Wannan magana ta wuce Mai unguwa, tsautsayi ne
kuma ina roqon ku yafe mani, na san cewar nayi
kuskure."
.
Mai unguwa ya ce.
.
"Ai kai zamu ba haquri, sbd a zahiri kai muka wa laifi
tunda mun zalunceka mun hada ka aure da wata 'yar
qauye wacce bata dace da irin rayuwar ka ta 'yan birni
ba.".
.
Amir ya ce.
.
"Ba haka bane mai unguwa, shi wannan abu duka ya faru
ne a bisa kuskure da kuma tsautsayi. Daga baya na
fahimci ni ke da laifi, domin ku iyayena ne, kuna da ikon
ku za6ar mani abin duk da ku ka san yana da kyau a gare
ni, ko da kuwa bani so."
.
Kafin Mai unguwa ya sake cewa wani abu ne, samarin
gidan suka yo qungiya suka xo wajen a fusace. Wani jikan
Mai unguwa ya ce da Amir.
.
"kai mara mutunci, uban me ya sake dawo da kai gidan
nan? Ko ka sake dawowa ka kuma yiwa iyayen namu
rashin mutunci, kamar yadda ka saba?"
.
Wani faskeken qato qanin mahaifin Amir ya matso gaba a
fusace daga shi sai yagaggiyar singileti shudiya wacce ta
sha qurar gona, ya fara qoqarin kai mashi duka ya ce.
.
"Dan iska kawai mara mutunci, lkcn da ka zagi su baba ka
ci sa'a bani nan na je yammaci, wallahi da sai an kwashe
ka, shegu wadanda basu san darajar mutum ba, ka ce tak
ynx idan ka cika mara kunya, ynx nan a je a bizne ka."
.
Mai unguwa ya dakawa samarin tsawa ya ce dasu.
.
"kai ku qyale shi, komai ya wuce, ku tafi abin ku ku rabu
da shi."
.
Samarin suka tafi suna hararar Amir, wani a cikin su
wanda ya dauko iccen garman shanu ya jefar dashi a
tsakar gida. Amir yana tsugunne yana kallon su a gaban
Mai unguwa Mutawakkilu. Tsohon ya ce dashi.
.
"Yaya damuna a can birni, ana samun ruwa kuwa?"
.
Amir ya yi saurin cewa da shi.
.
"Eh, ana samu jefi-jefi, don ko jiya ma an yi ruwa da
safe."
.
Mai unguwa ya ce dashi.
.
"Ai wannan al'amari na bana sai addu'a. Abin da farko ya
so ya bamu tsoro, sai da aka yi kusan wata daya babu
ruwa a nan. Ni dai a iya wayau na abin da zan iya tunawa
ba a ta6a daukar lkc ana roqon ruwa irin na wannan
shekarar ba. Wasu gonakin sai dai a haqura dasu, duk fari
ya sa amfanin ya qone ya bushe wasu kuma sai dai a dan
kalaci abin da yayi saura. Kai bana mun ga jarabta a
duniyar nan."
.
Amir ya ce da shi cikin girmamawa.
.
"Abin haka yake a ko'ina, an samu qarancin ruwa bana."
.
Mai unguwa ya ce.
.
"To masifu ne gasu nan ta ko'ina sun cika duniya. Ya
kamata mutane su gane cewar wannan fa ishara ce a gare
mu a bisa 6arnar da muke yi kullum babu qaqqautawa.
Mutane idon su ya ya rufe wajen neman abin duniya,
zalunci da rashin da rashin mutunci ya zama ruwan dare
a wannan zamani. Yara sun 6aci da rashin tarbiyya da
futsara, manya kuma basu son maqwabtan su sai zaman
gaba da mugunta da yiwa juna hassada, babu wanda
yake son wani ya ci gaba, kowa kan shi ya sani shi kadai
sbd rashin adalci.
.
Ga xubar da jinin mutane da ake yi kullum, wasu
'yanmatan sun koma karuwai a gaban iyayen su ana
kallon su. Fasiqanci da badala ya karade ko'ina. Ba amana
a tsakanin mutane da abokan huldar su. 'ya'ya sun raina
iyayen su, sun zama abokan fadan su....ga abubuwa nan
marasa mara sa kyau barkatai Amir. To ka fadi min yadda
za ayi mu zauna lfy a haka ba tare da mun gyara dabi'u
da halayen mu ba."
.
Amir ya yi shiru yana sauraren tsohon. Yace
.
"Gsky ne mai unguwa, akwai matsaloli masu yawa da ke
tattare da mutane...."
.
Bai san me ya kamata ya ce da shi ba, domin kuwa
xuciyar shi akwai tunanin da take yi.
'Tunanin Sadiya'
.
Tsohon ya ci gaba da cewa.
.
"bayam matsalar ruwa da muka fada a ciki, ga kuma
matsalolin rashin albarkar dukiya. Ga abin nan dai kullum
ana nema kuma ana samu, amma babu albarka, 'yar
matsala kadan sai kaga ta xo tayi awon gaba da abin da
mutum ya yi shekara yana tarawa. Da ka samu kudi zaka
rasa inda suka nufa kamar kudin iska, duk wadannan fa
masifun ne, Amir, mutane basu ganewa. Sannan kuma
babbar matsalar da tafi damun mu ta wadannan
shugabannin namu marasa adalci. Da un haye kujerun
mulkinsu, kan su kawai suka sani da 'ya'yansu, idan
matsalarsu ta taso a rana daya zasu ware miliyoyin kudi
su magance ta, amma idan matsalar talakawa ce sai su
shekara suna zama taro da shawarwari ba zasu ta6a
mayar da hankali akan ta ba.
.
Shugaba daya sai ya tara abin da mutum milyan dari zasu
amfana dashi ya 6oye. Kullum muka wayi gari sai mun ce
gara jiya, a haka ake tafiya, baya tana fin gaba sauqi, gaba
tana fin baya tsanani da uquba. Me ya jawo mana
wadannan bala'o'i? Sbd mun kasance mutane masu
6arna da laifi.
.
.
Lp=28
>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 28
.
.
Sbd mun kasance mutane masu 6arna da laifi, mu ne
zamu gyara kanmu mu dawo mutane na gari. Idan muka
gyara halayenmu, da yardar Allah zamu samu sauqin
wadannan fitinu da masifu dake qara addabarmu a
kullum."
.
Amir ya ce.
.
"Gsky ne mai unguwa.
.
Ya ci gaba da lalla6a tsohon suna hira, har xuwa wani lkc
sannan ya ce da shi.
.
"Mai unguwa na xo ne dama in sanar da kai cewa ina son
Sadiya ynx, in son a ba iyayen ta haquri akan abin da nayi
bisa kuskure, na amince ina son ta."
.
Mai unguwa ya kalle shi cikin mamaki da al'ajabi.
.
"kana son ta kuma ynx? Ban gane wannan magana da
kake fadi min ba."
.
Amir ya ce dashi bayan ya duqar da kai.
.
"Sadiya 'yar wajen abokinka da aka bani auren ta a
watannin baya na ce bana so, ita nake nufi."
.
Mai unguwa ya ce.
.
"Kai da ba ka ta6a ganin ta ba, ta yaya kum ka ji kana son
ta ynx?"
.
Amir ya yi ajiyar xuciya ya ce da tsohon.
.
"Gsky ba zan 6oye maka ba Mai unguwa, naga Sadiya,
mun hadu a makarantar mu inda nake karatu a halin
ynx."
.
Ya kwashe labarin abubuwan da suka faru tsakanin sa da
Sadiya ya fadiwa Mai unguwa, har xuwan su gidan
qanwar mahaifinta dake a Zariya, da labarin da ta basu na
dauke Sadiya da aka yi za a yi mata aure a halin ynx. Amir
ya kai qarshe yana hawayen nadama. Tsohon yayi shiru
yana wasi-wasin abin al'ajabin da ya faru. Ya yi ajiyar
xuciya shima ya ce.
.
"Ta6! Lallai wannan al'amari shi ne hukuncin Allah. To
Amir wane tudu wane gangare kuma lamarin ya kasance
haka? Sadiyar nan fa da ka gani a birni ita ce wacce ka ci
mutuncin mu akan ta sbd kawai mun baka auren ta
kyauta, ita ce ka gani ka ke so a halin ynx?"
.
.
KAI WANNAN TSOHO DA MASIFAR MITA YAKE, ACE ABIN
DUNIYA BA ZAI WUCE BA A WURIN SHI?
.
Amir ya yi shiru bai ce komai ba cikin nadama, yana mai
alhinin yadda al'amarin ya kasance haka daga baya.
Tsohon ya ce.
.
"Rayuwar nan da ka ke gani haka Amir, kamar idaniyar
ruwa ce, babu wanda ya san ta inda take 6ulla. Kaga da
farko mune muka nemo maka auren Sadiya cikin sauqi
kana zaune, amma ka wulaqantamu ka ce baka son ta
'yar qauye ce, ka tozarta mu a idon duniya. Ynx kuma
gashi ka dawo mana kana kuka da gawaye mu taimake ka
mu sake xuwa mu nemo maka auren ta a karo na biyu."
.
Tsohon ya yi shiru yana tunani, xuwa can ya ci gaba da
cewa.
.
"bakin alqalami ya riga ya bushe Amir. Ynx haka iyayen
Sadiya sun yi mata miji, za su yi mata aure. Ka san cewa
ba zai yiwu mu sake xuwa wajen su mu tunkare su da
maganar auren ka da Sadiya ba, bayan wulaqancin da aka
yi masu a baya. Wannan ba zai yiwu ba Amir. Iyayen
Sadiya sun fusata sosai akan wannan cin mutuncin da
akayi mana, danginta sun yi kuka da idanunsu, akwai
mutane da dama wadanda ke son yarinyar nan, amma ka
hana su ita aka bamu, duk da cewar abota ce kawai da
zaman tare ya hada mu da su ba 'yan uwantaka ba.
Amma ka watsa masu qasa a cikin ido Amir. Kayi mana
kunya son ran ka. Da wacce fuska ka ke tsammanin wani
a nan zai sake komawa Turunkawa ya ce ya xo akan
maganar ka a sake baka auren Sadiya sbd ynx ka dawo
kana son ta? Wannan al'amari har abada ba zai ta6a
yiwuwa ba. Tun farko kai ka dauki wuqa ka da6awa kan
ka da kan ka. Ynx gashi wani zamani ya xo ka dawo kana
son matar da har abada ba zata ta6a zama matar ka ba
koda kuwa zaka ras ranka ne akan neman ta.
>=== "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 29
.
.
Ynx gashi wani zamani ya xo ka dawo kana son yarinyar
da har abada ba zata ta6a zama matarka ba. Ko zaka rasa
ranka akan wannan yarinyar Amir ba zaka aureta ba.
Kuma kai ka jawo ma kanka wannan matsalar tun farko."
.
Amir ya dafe kanshi a cikin tsananin azabar da yake ji a
halin ynx. Tabbas ya yi kuskure a baya. Ya fara kukan
nadama yana tausayawa rayuwar shi. Mai unguwa ya ci
gaba cewa.
.
"Mu din nan da kuke gani mutanen qauye akwai irin
namu hikimomin rayuwar wadanda suka sha banban da
irin naku. Mun san cewar irin wadannan aurace-arcen da
muke yiwa yaran mu a nsn tun suna qanqana, kuna ganin
kamar bamu waye bane. Muna yin haka ne domin mu
tsare su daga irin badalar da muke gani tana faruwa a
wasu wuraren. A nan zaka samu wani talaka ne bashi da
kudin aure, to don gudun kada irin su suyi yawa har su
fara yada 6arna a cikin al'ummar mu, shi ne muke basu
sadakar aure. Wannan shi ne gatancin da muka yi maka
Amir, amma sai ka kasa fahimtarmu kai a ganinka bamu
waye ba, ku 'yan zamani 'yan birni kune wayayyu. To ynx
ga sakamako nan ka fara gani tun ba a je ko'ina ba. Sbd
haka ka daina wulaqanta mutane, ka riqa girmama
al'adunsu domin baka san hikimomin dake ciki ba."
.
Amir ya share hawaye.
.
"Na gode da wannan nasiha da kayi min, na gode da
afuwar da kayi min. Amma duk da haka zan je garin su
Sadiya da kaina, in nemi afuwarta da kuma iyayen ta."
.
Mai unguwa ya ce.
.
"Ina sake gargadinka, kada ka kuskura ka je Turunkawa,
domin idan har iyayen Sadiya suka qyalla ido suka gan ka
komai ya faru da kai, kai ka jawo wa kanka. Ka cire
wannan yarinyar daga xuciyarka, ba matarka ba ce,
iyayenta b zasu ta6a baka auren ta ba."
.
Amir ya ce.
.
"na gode mai unguwa sai dai ku taya ni da addu'a, idan
kuma wannan yarinyar ita ce ajalina ku yi min addu'a
Allah Ya gafarta min, ina son ta, ba zan iya rayuwa ba tare
da ita ba, kuma na dauki alqawarin zan tafi har garin su in
nemi auren ta."
.
Mai unguwa ya ce dashi.
.
"to wannan kai ka daukarwa kanka, ni babu abin da zan
iya cewa a halin ynx, na dai fadi maka gsky."
.
Amir ya tashi ya yi mashi sallama dauke da jakar shi, ya
fita a cikin sauri. Iyalan mai unguwa Mutawakkilu suka xo
wajen mai unguwa baki dayan su suka tambaye shi abin
da ya sake dawo da Amir a wannan lkc. Tsohon ya fadi
masu abin da ya faru tun daga farko har qarshe, sannan
ya ja hankalin yara kan su bi duniya a hankali, ban da
rashi kunya, ya basu misali da irin sakamakon da Amir ya
samu.
.
Sbd haka Amir ya zama mai nacin soyayya, gashi nan ynx
ya kamas hanyar Turunkawa, zai tafi nemo soyayya duk
kuwa da hadarin da aka gargade shi zai iya cim mawa a
can.
.
.
**~**
.
.
Tun a satin farko da Sarkin noma ya miqa qoqon barar
shi wajen neman auren Sadiya, nan da nan sai Mal. Kalla
da Mal. Buba suka tara 'yan uwa suka sanar dasu wannan
abin alherin da ya same su, babu wanda ya yi jayayya
akan maganar, kowa ya amince a ba Alh. Mamuda sarkin
noma auren Sadiya.
.
A satin ya kawo kudin sadaki da kuma dukiyar auren da
suka sara mashi bai rage ko anini ba, duk da a ganin su
sun cika mashi kudin. A tarihin qauyen ba a ta6a aurar da
wata yarinya da tsadar sadaki ba kwatankwacin Sadiya.
.
A ranar da aka kawo kudin auren ne da safe, nan da nan
Mal. Buba ya shirya ya bazama birni dauko Sadiya, suka
dawo gida domin kuwa sun ga abin na yi ne, ba maganar
wasa ba ce.
.
Da Sadiya ta dawo gida ne ta samu maganar da ake yi har
komai ya yi nisa, har an kawo kudin auren ta iyayen ta
sun fara kacalcala su suna saye-saye. Sadiya ta ji tsoro ya
kama ta, ta ji duniya ta yi mata qunci, domin kuwa a
wannan karon iyayen ta sun sun shiga rayuwarta da
yawa. Ta samu labarin mutumin da za a bata wani tsohon
najadu ne, kuma matan shi uku ita ce ta hudu. Iyayen ta
basu damu ba sai faman haja-hajarsu suke yi suna
shawarwari, suna ta kasafin kudaden da Sarkin noma ya
aiko dasu.
.
Qanin mahaifin ta Mal. Buba shi yafi daukar maganar da
zafi-zafi. Tun a hanya da zasu dawo gida shi da Sadiya
yake yi mmata fada yana cewa.
.
"wannan mutumin daya fito ya nemi auren ki mutumin
kirki ne, duk fadin lardin nan babu wanda bai san shi ba
wajen yiwa mutane alheri, sbd haka kada ki kuskura mu
ji kin yi masa sakarci.
.
A wannan karon ita ma mahaifiyar Sadiya ba a bar ta a
baya ba, domin kuwa da Sarkin noma ya kawo kudin da
suka sara mashi naira dubu sittin, don a samu hadin
kanta ta jawo hankalin Sadiya, sai Mal. Kalla ya ce a ware
mata naira dubu ashirin, wannan nata ne tayi 'yan saye-
sayensu na mata.
.
Aka kira ta dakin da ake zaman shawara an xube kudin
akan tabarma, suna kallonsu suna xufa. Mal. Buba ya
qirgo dubu ashirin ya miqa mata, ta amsa hannunta yana
kyarma. A kaf shekarun da tayi zaune a wannan qauyen
bata ta6a ganin tulin kudi masu yawa irin wadannan ba.
.
Sau daya ta ta6a yin adashi aka bata kwasar jaka goma-
sha-hudu, shima sai da aka shekara ana yin shi, 'yar ribar
da take samu ce ta qosai da take yi da safe da kuma
surfen da take yi tana sayar da dusar in ta tare.
.
.
Lp=30>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 30
.
.
'Yar ribar da take samu ce ta qosai da take yi da safe da
kuma surfen da take yi tana sayar da dusar in ta tara.
.
A wannan karon sai gata ita kadai an dunqulo mata har
dubu ashirin, jaka dari fa kenan! Nan da nan tayi sauri ta
kai su daki ta qudundune su a cikin leda ta daga katifarta
'yar sale ta cusa su a qarqashi daga nesa, ta dora katifar
akan ledar, ta gyara ko'ina don kar a gane inda suke. Ta
jawo kayayyaki da tsummokara ta kila su akan katifar, ta
tsaya tana kallon wajen. Duk da haka bata yarda ta bar
dakin ba ko daidai da qyaftawar ido, tana nan kusa da
inda ta cusa kudin. Lkc-lkc tana daga katifar tana leqawa
don ta tabbatar ledar tana nan a inda ta ajiye ta?
.
Sadiya sun dawo gida ita da qanin mahaifinta babu
dadewa, sai mahaifiyarta ta fara yi mata fada tana cewa.
.
"Ynx ke dai ba yarinya bace qarama da za a saki a gaba a
yi tayi maki fada, kin riga kin mallaki hankalinki, sbd haka
kamar yadda babanki ya ce in tsare ki in ja kunnenki. To
kin dai ji abin dake faruwa. Wannan mutum gsky babban
mutum ne, sbd haka idan kin nema mana mutunci a
wajen shi to kin kyauta mana, idan kuma baki bi shi kin
nemo mana martaba dai mu kika jowo mawa, abin da ya
rage ynx kawai sai sa ranar daurin aure, kuma ina jin
gobe da safe zasu xo a yi magana."
.
Sadiya tayi shiru tana mamakin wannan abin al'ajabin
irin wannan rayuwa da ta tsinci kan ta a ciki. Ta san cewar
wasu 'yan qananun kudi suka rudi iyayen ta har suka
rikice haka suke rawar jiki akan wannan tsoho da yake so
ya aure ta, wato Sarkin noma. Talauci ya quntata tunanin
su, basa tunanin idan suka bata wanda bashi da kudi wata
rana zai iya samun wanda yafi na Sarkin noma. Ba ruwan
su da soyayyar Amir dake a xuciyar 'yar su Sadiya.
.
Sadiya tayi tagumi tayi shiru tana tunanin Amir sabom
masoyinta wanda ta baro a makaranta. Ta san cewar ynx
haka yana can yana neman ta ruwa a jallo, Amir ba zai
ta6a samun sukuni ba a rayuwar shi sai ya gan ta.
.
Sadiya bata son sa6awa umarnin iyayen ta, a lkc guda
kuma bata son ta rabu da Amir. Shi yafi dacewa da irin
rayuwarta, shi ne kawai zata zauna dashi ta more
quruciyarta, kuma ya debe mata kewar duk wani abu da
ta rasa.
.
Da misalin qarfe takwas da rabi na daren, qannen ta suka
rugo aguje suka same ta a dakin mahaifiyar ta zaune tayi
tagumi. Suka ce da ita.
.
"Sadiya ki xo Sarkin noma yana kira."
.
Ta ce dasu tana xuwa. Suka koma aguje suna murna, da
gani ta san cewar ya bi su da naira goma-goma ne
wataqila. Ta lura dai kowa yana son shi a gidan sbd kawai
yana da kudi. Kafin Sadiya ta tashi ta canza kayan jikinta
ne ta ji Mal. Buba qanin mahaifin ta ya fito tsakar gida
yana daka mata tsawa.
.
"wai ke wacce uwa kike yi ne a dakin Sadiya? Ashe ba aiko
ki je waje kin yi baqi ba?"
.
Nan da nan tayi sauri ta daura zani ta sa takalmi, ta
warware gyalen ta yafa a waje ta fita qofar gida. A lkcn da
ta fita ne ta same su a tsaye jikin wata (Bus) da suka xo da
ita, su biyu suna sanye da manyan kaya. Daya a cikin su
yayi siririn rawani wanda take tsammanin shi ne Sarkin
noman.
.
Sadiya ta qarasa wajen su tayi masu sallama a sanyaye,
suka amsa suna fara'a, sannan ta gaishe su cikin ladabi.
Gama gaisuwar keda wuya sai ta qyale su. Duk da babu
haske sosai a wajen ta ga fuskokin su. Sarkin noma shi
yafi razana ta, ta ga fuskar shi baqi wuluk kamar kwalta,
babu alamun sawaba ko rangwame tattare dashi, a qalla
zai kai shekaru hamsin, abokin shima tsohon ne zai iya
kaiwa hamsin. Dukanin su dattawa ne wadanda in a
duniyar mutanen kirki ne zasu iya zama kakannin ta
amma kuma ynx samarin ta ne.
.
Abokin Sarkin noma ya fara magana.
.
"mun san cewar kin samu labarin komi a gida Sadiya, sai
dai dan qarin bayani da ya kamata muyi domin ku
fahimci juna ke da sahibinki da yake sauraren abin da
zaki ce ynx."
.
Sadiya bata ce komai ba, tayi shiru tana tunanin yadda
rayuwarta zata kasance a haka tare da wannan tsoho, da
kuma makomar Amir masoyinta da ke

Please Login or Register in order to submit comment