Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take so hakan yasa sultana ta cire kayan Ta sa wasu kayan Ta ce zatai mata sannan ta fice,momy Ta bita Da murmushi kafin Ta dauki wayan Tana ganin hutunan datai mata, mikewa tayi Ta dakko Wata Waya sabowa a cikin kwali tare da fadin yata zanba,.

Aiki take a kitchen tana tuno dazo Da suka hadu Da sultan KO nashi na damuwa Da sai yasan wace oho taja tsaki ganin tana zufa yasa Ta cire dankwalin Ta bude fuska tare da fadin nasan ba zasu dawo yanzuba,.

Debo flower tai Tana jika kanwa sannan ta zuba kuka a cikin flower, tana juyawa Ta bayanta taji muryar sultan yana fadin sannu Da aiki sosai gabanta ya fadi tama rasa ya zatai tama manta da Dan kwalinta dake gefe jin yana takowa kawai Ta yanke hukunci Ta dauki wannan flower ta zuye a fuskarta gaba daya

By hajara Mami natty girl
πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ• πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘. * *MASARAUTAR MUCE 32*
πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```


*Sorry about those texts I sent you last night, my phone was drunk.*



ο»Ώο»ΏDa sauri yaja baya yana kallanta, anya bata sami matsalaba? Ya tambayi kanshi,kasa tai tare da fadin ina wuni ranka ya Dade? Hade rai yayi mekenan?maye hakan kin sami matsalane? Kuma wannan flour da kika zubar a bakacin kudin aikin ki na wannan watan, ajiyar zuciya Ta sauke gara haka dadai ya ga fuskarta,tsaki yayi Tara da juyawa tabar gun, kallan shi tai tare da dafe kirji thanks god ta fada tare da mikewa Ta nufi tap karkuma ya dawo ta fada sannan ta koma ta sawa kofar kitchen din key Ta kuma ta wanke fuskar sannan ta dauki dan kwadinta ta goge fuskarta, sannan ta bude taci gaba Da aikinta,.

Da sallama ya shiga dakin momy shi ya zauna a kan kujeran dakin tare da kwantar Da kanshi, kallanshi momy tai lafiya son naga kamar kana cikin damuwa? Ba komai mom kawai ina San hutawa anan ne, to kawai tace taci gaba Da abun Da take,.

Jinginar dakai yayi waccan yarinyar yake tunawa yama cuci kanshi dahar zai ce wai wannan yarinyar sultana ce yarinyar Da iya kayan jikinta abun kallo nema, ka sani KO Yar watace abune ya kawota wannan masarautar tunda bata San a ga fuskarta, tsaki yaja tare da fadin kai ina ba itta bace, kallan shi mom ta sake yi son waime ke damunka ne? Gyara zama yayi mom wai Dan Allah kin taba ganin wannan sultanan ya take fuskarta nake nufi? Kallan shi tai sosai eh na taba gani, yauwa mom ya take plz ya kamarta yake kawai inasan ganin fuskanta ne, saboda wannan dalili, dafe kai yayi kafin ya kalli mom wlh mom wata na gani yau shine nake tunanin KO ittace tunda ban taba ganinta a wannan masarautar ba Amman Na tambaye ta tace wai itta kawar Hindu ce kuma duk nasan kawayen Hindu, murmushi momy ta, to ka sani KO kawar tatace, aa mom Na kasa yadda da hakan ne shiyasa wlh, kallan shi sosai momy tai kodai ka kamu Da santa ne? Baice komaiba ya jinginar Da kai,.

OK naji indai sultana ce zaka sotane? Da sauri ya Mike ya kalli mom haba mom indai ittace gara Na mutu Da Santa bazan auri baiwata ba haba ai koke saikimun fada, hade rai momy tai dajin zancenshi tai mai banza batace komaiba ,kallan ta yayi ganin ta hade rai, murmushi yayi tare da karasawa kusa Da itta, mom sorry indai Na bata miki raine, kallan shi tai sultan sau nawa zan fadama sultana Ya na dauketa Amman har ka dinga fadan haka a gabana, rike hannunta yayi sorry bazan karaba, juyar dakai tayi naji Amman zaka aureta yarinyar ce take ban tausayi wlh, mikewa yayi tare da hade rai momy kiyi hakuri Amman bazan iya auren wannan yarinyar ba zanje IN nemo wannan yarinyar ta yau ya fada tare da komawa ya zauna, kallan shi tai nikuwa bazan Bada gudun mawaba ina gani so zai kasheka, murmushi kawai yayi,.

Da sallama sultana ta shigo daki Da cooler a hannunta ta ajjiye sannan ta fita ta dakko sauran abun Da zata dakko, zukunnawa tayi ta zubawa momy sultan baice komaiba kawai dai yasan yana San ci Allah yasa momy ta tambayashi KO zaici, shareshi momy Tai Dan tasan dan nata akwai San dan wake Amman yanzu tana fushi dashi bazata mai maganaba ba, sultana nan Ma batai mai maganaba illlah zama datai a kusa Da momy tana Dan sanna mata kafa, wayan kusa Da itta momy ta dauka ta mikawa sultana, dubamin wannan wayan lafiyar nake San ka duba, karbar wayan yayi wannan wayan daya taba shiyowa momy ce sanda yaje India bata taba amfani Da itta ba, karba yayi yana murmushi yau kuma San wannan wayance ta tashi yau aka Tuna da itta? Kallan shi tai ba surutu nace kaimun ba, murmushi yayi tare da kanna wayan yai dube duben shi sannan, kashe Kallan wayan yayi komai normal amma sim NE kawai babu, OK tace tare da kallan sultana, jeki karban waccan wayan!mikewa sultana tai ta karasa gunshi tare da zukunnawa ta mika hannu, baice komaiba yazo mika mata idonshi ya sauka kan zanen dake hannunta,kalln zanen yake sosai duk Da yayi dishi dishi

By hajara Mami natty girl
πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ• πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘. * *MASARAUTAR MUCE 33*
πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```
Kallan shi tai kafin ta kalli hannun Nata da sauri tai niyar daukewa yayi saurin riko hannun tare da daura mata wayan a tafin hannunta Amman bai sake hannunba, kallan shi momy tai tare da fadin maye haka? Kallan sultana yai suka hada ido tai saurin dauke ido gabanta na dukan Tara Tara sakin hannun yayi Ya jin gina jikin kujeran tare da lunshe ido wace sultana me tazo yi wannan masarautar wannan zanen hannun Nata ai MASARATAR MUCE ya fada a hankali,.

Mikawa sultana tai ta kaiwa momy wayan bata karba sai Kallan sultan datai son ka shirya gobe kafin ka kita aiki ka sauketa tasai sim kama siya mata sai kasa ta a texi ta dawo gida, Da sauri sultan ya kalleta Da mamaki bai gama mamakinba taji tace sultana wayarkice Na baki kyauta, sakin baki sultana tai tana kallan momy sai hawaye duk na farin ciki wannan wayan duk itta momy zataba, daura kanta a cinyar momy tai tare da fadin na gode momy Allah ya saka a rayuwa bansan Dame zan saka mikiba, murnushi momy tai batace komaiba, mikewa sultan yayi ya fice ba tare da yace komaiba, momy ta bishi Da tabe baki,.

Part dinshi ya nufa kawai yai kwanciyar shi,.
Sultana kuwa tsabar murna KO bangaren shi ba ta kallah ba Tana gun momy suna hira tana ta murnar Waya bata San indai su Zuwaira suka gani me zasu ce mata ba,.

Sai wajen magariba ta nufi dakinsu Da sallama ta shiga lokacin kuwa duk Sun dawo, zama tayi tare da fadin washhhh ta dakko wayan tare da mika musu, karba Zulai tai tana juyawa Zuwaira kuwa ta wani kafeta Da ido alamar karin bayani take so, murnushi sultana tai, uwar gidana ce taban kyauta, duk suka zaro ido suna kallanta murmushi baku yadda ba? Mum isah ai nasan zata iya baki cewar Zuwaira inama nace nake aiki agunta Amman fa karkice wai ina miki bakin cikine, batace komaiba sai murmushi take,.

1:00am wato cikin dare a hankali aka tura kofar dakin su sultana ta, sultana da tun dazu ta kasa bacci tana daukin Waya jin zaa turo yasa tai saurin tura wayan a karkashin pillow,.

Marka ce baiwar dake kula dasu kallan su tai duk ta haska su Da touch tana kallan su kafin ta sauke ajiyar zuciya tare da fadin duk bacci suke, bude kofan tai wasu mata suka shigo duk ta kasan ido sultana ke wannan kallan idon Allah, ...Tana gani suka saka mata wani abu a handkerchief sannan suka dauketa suka fice marka ta rufe kofa, Da sauri sultana Ta Mike tasa ta kallimi tare da daukan Dan kwali ta rufe fuska, ta dauki wayan ta, tabi bayansu,.

Suna yi suna juyowa Da taga alamar zasu ganta saita buye ,haka taita binsu har suka shiga wani bangare daban itta batasan bagaren wayeba tunda bata taba zuwaba,.

Da sauri ta shiga ta buye abayan wani daki, ajjiye Zuwaira sukai a kujeran parlor kafin suka fita,.
A hankali ta Sami gun buya Tana leke, Hafiz taga ya sakko tabbas ta ganeshi, sakkowa yayi ya tsaya ta Bayan kujeran Da Zuwaira take kafin ya saki murmushi, Ya dawo ya zauna kusa Da itta, kawai kallanta yake wai Da gaske itta yakeso wannan San kuwa bawai yaji yana San bata ta bane as santa yake Da aure,.

Da sauri sultana taja baya ta dakko wayanta ya zama dole ta fara aikinta yanzu video record zatai Da kyar ta binciko video sannan ta Fara,

Fridge yake ya dakko ruwa a garka ya na zuwa ya bude tare da yayyafawa Zuwaira, a hankali ta fara motsi kafin ta bude ido tun Tana kallo dishi dishi har idonta ya bude Da sauri ta mike tare da tsala ihu Hafiz yai saurin rufe mata baki,.
Sultana garin ta gyara, wayanta ta buge glass din dake bayanta

By hajara Mami natty girl
πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ• πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘. * *MASARAUTAR MUCE 34*
πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```


ο»Ώο»ΏDasauri tadanja baya tare da toshe baki tana zaro ido, kallan gun Hafiz yayi duk yadda akai akwai Wanda yake gun Dan haka kawai abun bazai fadi ba, kallan Zuwaira yayi ya bata wata uwar harara, duk ta tsure sai zaro ido take Dan a iya saninta itta ba anan take ba to me ya kawo ta nan, sakinta yayi kafin ya nufi gun da yaji karan, Da kyar sultana ta samu ta Sani kofa idonta ya sauka kan sarkan dake gefe Na stone kuma manya a hankali tasa hannu ta dakko sannan ta fara kokarin tsinkawa Da kar ta samu ta tsina ta rike a hannu tana adduar Allah yasa wannan abun Da take shirin yi yayi aiki saida ta tabbatar Da Ya kusa zuwa gunta kafin ta juya ba shiri ta zubar Da stones din, zuciya daya yake tafiya kawai sai jinshi yayi yasha kasa hakan Yasa yayi lass tare da fadin washhhhh yana runtse ido Da gudu sultana ta kwasa ta fice Hafiz yabi bayanta Da kallo koma waye yasan masu gadinshi zasu kamo Mai shi ya fada yaci gaba Da abun Da yake ji a jikinshi,.

Kallan shi Zuwaira tai a ranta Tana fadin Allah ya kara, ganin Ya kasa mikewa Yasa ta Tashi tazo ta kalleshi ta duka tsaki har zata wuce sai kuma ta dawo Tare da fadin ka fadawa dogaranka su barni na wuce, hararar ta yayi bama tayi tunanin taimaka maiba Tana Mai wani zance, Da kyar ya samu ya dago, kallan ta yayi magana nake San muyi dake ya fada tare da mikewa Da kyar, wacce irin maganace wannan Da zaka wani dakko ni daga makwancina ka kawoni nan AI wannan iskancine,.

Kalkanta yayi kafin ya saki wani murmushi ya karasa kan kujera ya xauna, zo ki zauna za muyi magana, banza ta Mai batace komai ba ,ta tsaya tana kallan idon Allah ,kallan ta yayi ganin taki zuwa yasa Ya dauki remote tare da kunna Tv ,ganin Ya kunna TV MA Yasa ta karasa ta zauna acan gefe dashi,. Kallan ta yayi bansan ya akai kawai naji daban akanki ba na kasance a wannan masarautar muddin naga Ya Mace tamun babu ruwana Da wata matsala sawa nake a kamomin itta kawai inyi yadda naga dama Da itta, sosai jikin Zuwaira Ya dau rawa, yaci gaba amm bansan dalilin Da Yasa ke naji bazan iya miki hakan ba kawai naji ina sanki Da aurene, a dan razane ta kalleshi ya daga mata gira Amman ba dole indai baki sona sai IN miki yadda nakewa sauran ba wata matsala bane,.

Dan Allah kayi hakuri ni wlh...... Sai kuma tayi shiru tabe baki yayi bawai sanki nake ba aa kawai inaa sanki Da aure ne karki wani damu Na baki time kije kiyi tunani ni kuma ina nan ina jiranki, mikewa yayi tai saurin mikewa ittama to Kasa a maidani gun kwanan plz, murmushi yayi aike Da fita anan sai gobe saboda ana mutuwa duk wanda Ya fita awannna lokacin kinga kuma ina sanki a raye feel free ki kwana anan ba abun Da zan miki Ya fada yana daga hannu amma fa wannan maganar ta zama sirrin tsakanin mu,.

Da sauri ta gada kai, murmushi yayi good, wani Daki Ya nuna mata zaki iya kwana anan, Da sauri ta daga kai tare da yin gaba ta bude dakin tasa lock Ta ciki, haka kai Da gwiwa tayi Tana kuka,.

Sultana kuwa Da gudu Ta fice, ganin ana gadin gun Yasa ta tsaya tana mai Da nunfashi kafin ta karasa a hankali Tana tafiya basuce mata komaiba Dan duk a xacensu wadda Hafiz Yasa aka dakko Mai ce, Tana fita daga bagaren ta sauke ajiyar zuciya,.

Tana fita wasu suka Fara binta a baya, juyowa tayi kartine har uku banda idonsu Wanda ba dugon imani ba abun Da take gani Da sauri ta Fara tafiya, tanaji dayan Na fadin ai kasheki zamuyi wannan umarnine daga sarki duk wadda hafiz Ya kuka kisa ne, zaro ido tai tare da kara sauri,. Tafiya take suma basu fasa binta ba saiji tayi An riko ta, kafin Wanda ya rikota Ya juya Ya Kalli sauran tare da fadin zanji Da itta , jin hakan Yasarm suka juya dan sun ganshi Da irin kayansu .
Tunda ya rikota tasan shine dan taji kanshin turaren shi handala tayi,. Rike hannutq yayi har part dinshi Da gani ranshi a bace yake hakan Yasa sultana ta fara tsorata,yana zuwa Ya hada ta da bango tare da kallon idonta, kafin yace dole yau ki fadan dalilinki Na fitowa Da daddare a wannan masarautar

By hajara Mami natty girl
πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ• πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘. * *MASARAUTAR MUCE 35*
πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```

ο»Ώο»Ώο»Ώο»ΏTsuru tsuru tai da ido, saboda yadda ya tasa ta a gaba har tanajin nunfashin shi, dan juyar da kai tayi yai saurin riko habarta, bani amsa inba hakaba wlh saidai mu ta tsayowa a haka muma kwana a haka ba damuna zai yiba, to sakeni sai in fada ma Ta fada Tana kallan shi, harara Ya bata kafin Ya saketa, ajiyar zuciya ta sauke ta na tunanin wacce karya zata shirga mishi kuma, kallan ta yayi ganin Tana tunani Yasa yai murmushi tare da fadin wlh kika sake kika mum karya nida kene, rau rau tai da ido kafin ta sami gu kusa dashi Ta zauna, uhmmmm dama dai wlh kasa bacci nai shine Na fito waje to dana fito shine nake yawo, shine wadancan suka ganni suka biyoni ni ba abun Da nai musu, ganin yadda ya hade rai Yasa tai kara tsorata baice komaiba kawai kallan ta yake ranshi a bace,.
Dan kara dubul bulcewa tayi wlh kadai bari in fada maka gaskiya wlh, dama muna bacci ne naga anzo an dauke Zuwaira shine Na biyo bayansu dan inga inda zasu kaita,hmmm yace tare da dauke kai, ya dauka ba zata fada Mai gaskiya ba,.

Kallan ta yayi, wato so kike a bataki kema KO?dan zaro ido tai Tana kallan shi, eh mana hakane inba haka maye naki Da zaki biyo bayansu inyaso koma Maye a hada dake KO? Ranka Ya Dade Zuwaira fa yar uwatace, tare muke a daki daya taya ina gani zaa dauketa ban biyo baya ba, haba ai ban cika kawaba, murmushi yayi ganin yadda take fada mai kenan zata iya yin komai game da kawarta wowww wannan abun Ya burgeshi friendshi kenan,. Dauke kai yayi Ya dauki system dinshi Da dama can a kunne take Ya ci gaba Da aikin shi,.

Kallan shi tai, kafin ta Fara magana a hankali ranka Ya dade na gode Da taimakon da kake ban na gode dafa tuni Na Dade da, mutuwa baice mata komaiba yaci gaba Da abun Da yake, Amman ranka Ya Dade wai taya kake fitowa a irin wannan lokacin ni abun naban mamaki fa, kallan ta yayi, kafin Ya dauke kai baki San komai game da wannan masarautar ba, MASARAUTAR MUCE baki San komai game da itta ba, tabe baki tai, wai masarautar suce,.

A kullun irin wannan lokacin ina fita ina zaga wannan masarautar saboda Inga ta,asar Da ake aikatawa tun ina yi a boye har yazo nake baiya na kaina har ya kasance nasan Wanda suke Da sa hannu a wannan abun, uhmmm to zaka fada mun dawa dawa ne suke Da hannu a hakan? Kallan ta yayi saboda ke wace? Dauke kai tayi Tare da fadin hmmmm, sai kuma Ya kalleta tare da fadin zonan sultana, kallan shi tai bata gane zonan ba, ganin Ya kafeta Da ido Yasa ta Mike ta Dan matsa kusa da shi, mikon hannunki wancan Ya fada yana nuna mata hannun hagunta, kirjinta ne Ya fadi, ran ka Ya Dade ban ganeba, eh cinye hannun Xanyi Ya fada yana kallan ta, kayi hakuri ranka Ya Dade Amman bazan iya baka hannunaba ai babu kyau Na miji Ya taba hannun Mace kuma ba badan dole ba aibanga abun Da zaisa IN zauna Da kai anan ba niba Matar ka ba, zaro ido yayi ni kike fadawa magana? Aa ranka Ya Dade ba magana nake fada maka ba yi hakuri indai Na bata maka rai, ajiyar zuciya Ya sauke kafin yace to muga hannun naki niba tabawa zanyi ba, kallan shi Tai kafin ta mika mai hannun, kallan hanun yayi sultana wannan zanen nake San karin bayani da gani bada lalle aka Yishiba so nake nasan Dame aka yi kuma kamar zanen masarautar mu,.
Dauke hannu tai ni haka Na taso naga hannun nawa, bansan daga inda yake ba, kallan ta yayi kafin yace zan iya ganin fuskarki sultana yana magana a hankali kamar ba shiba, gabanta ne Ya fadi ina ba zata yadda ba wlh, Dan Allah ranka Ya Dade kayi hakuri ni bazan iya budema fuskata ba tsorata zakai dan fuskata nada matsala, mikewa yayi Ya zauna kasan kusa Da itta, ni a hakan nake San ganin naki, gabanta banda dukan tara tare ba abun Da yake, Dan Allah ranka ya Dade kayi hakuri bana San abunda zaisa hankalinka Ya tashi Amman maye naka Na San dole sai kaga fuskata? Nima kawai Na tsinci kaina Da hakan ne Amman karki fassara dan ba sanki nakeba kkawa jikina yana ban ke kamar kina Da hadi danine saida naga wannan zanen ma, danja baya tai niba wani hadi Da nake dakai ni a jigawa nake Dan Allah kayi hakuri ,kallanta yake kafin ya fara tunani saima ta rainaka Ta dauka santa kake Amman ka tsaya kana wani damun dole sai kaga fuskarta alhalin ka wuce wannan gun, tashi daya yaji haushin kanshi ya mike ya koma kan kujera Ya hade rai karta raina shi

By hajara Mami natty girl
πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ• πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ‘‘
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘. * *MASARAUTAR MUCE 36*
πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•
πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘
πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ•πŸ•πŸ•
FANTASTICS START WRITERS (F S W)

Hajaramaminattygirl20.WordPress.com

```indicated to maman shukrah aunty ummi```
Binshi tai da kallo yadda ya wani hade rai kamar ba shine Wanda ya gama make mata murya ba,.

Shiru tayi tana tunanin koya Zuwaira zata kasance may be Ma yanzu Ya gama bata ta Yasa ta fito an kashe ta KO ma meyasa yake sawa ake kashe bayin Allah oho Mai Amman zataso jin dalili kuma Zuwaira ce kawai zata mata wannan taimakon,.bacci take ji Amman shi KO a jikinshi Ya wani bude system kamar ba dareba,hamma tayi Dan ya gani Ya nuna mata inda zata kwanta KO kallan inda take baiyiba, ta sake yin hamma Da karfi har saida yadan tsaya Da abun Da yake kafin yaja tsaki yaci gaba Da abun Da yake tabe baki tai kafin tai murmushi bari tadan tabo masifar shi, karayi tayi Tana salati, a hargitse Ya kalleta waike meke damunki kinzo sai damuna kike, ha,a kallan shi take yana mata masifa, ranka Ya Dade bacci nake ji shi yasa, to rike ki nayi kije kiyi kwanciyar ki mana, kallan shi tai sai kuma ta mike ta nufi kofa taga Ko zaice Ya dawo, ganin har taje kofa baice komaiba yasa ta dan Saki tsaki ta bude kofan, idonta na sauka kan duhun tai maza ta dawo,.

Shi kuwa Kallan ta yake yana Allah dai Yasa yarinyar nan ba ficewa zataiba dan yaga tana fama Da danye kai, kallan shi tai kafin tai sama inda ya nuna mata ranar,.

Washe gari Zuwaira Da wuri ta tashi Dan batai wani bacci bama, tana jin Hafiz Ya fice masallaci, ta Mike Amman sai Da take bari gari Ya danyi haske kafin ta fito ta kama

Please Login or Register in order to submit comment